Akhdari
Akhdari
LITTAFIN AKHDARI
A HARSHEN HAUSA
GABATARWA
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI, TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA GA
FIYAYYEN HALITTA ANNABI MUHAMMAD {SAW} DA IYALENSA, DA SAHABBANSA DA
WAƊANDA SUKA BISU DA KYAUTATAWA ZUWA RANAR SAKAMAKO.
1
2
MATNUL AKHDARI
FASULLA SHAFI
1. HUƊUBAR MAWALLAFI - - - 3
2
3
MATNUL AKHDARI
HUƊUBAR MAWALLAFI
3
4
MATNUL AKHDARI
kuma yana wajaba a gareshi da ya kiyaye dokokin Allah, kuma ya tsaya inda {Allah}
ya umurce shi da inda ya hane shi, kuma ya tuba zuwa ga Allah tsarki ya tabbata a
gareshi, tun gabanin yayi fushi dashi.
kuma sharuɗɗan tuba : yin nadama bisa laifin daya aikata, da yin niyyar ba zai sake
komawa zuwa ga wannan zunubi ba, cikin ragowar rayuwarsa, da barin aikata
wannan zunibin nan take, idan ya kasance mai cuɗanya da ita.
kuma bāya halatta gareshi da ya jinkirta tuba, kuma kada yace har sai Allah ya
shirye shi, domin wannan na daga alaman taɓewa da rashin rabo da shafewar
basirah.
kuma yana wajaba a gareshi da ya kiyaye harshensa daga alfasha da abun ƙi, da
mummunan magana, da rantsuwar saki, da tsawa ga musulmi, da wulaƙanta shi,
da zaginsa, da bashi tsoro ba tare da wani haƙƙi na shari'ah ba.
1
Alamomin balaga ga namiji sun ƙunshi fara gashin mara ko mafarki ko kaiwa shekaru goma sha biyar, ga mace kuma ukun da
suka gabata sannan da fara jinin haila.
2
Imani da Allah, da mala’ikunsa, da littafansa, da manzanninsa, da rana ta ƙarshe da imani da kaddara alherinsa da sharrinsa, sannan
da nisantan shirka.
4
5
MATNUL AKHDARI
kuma yana wajaba a gareshi da ya kiyaye ganinsa daga kallon haram, kuma baya
halatta gareshi da ya kalli wani musulmi, kallon da zata cutar dashi, sai fa idan ya
kasance fasiƙi neh, sai ya wajaba a ƙaurace masa.
kuma yana wajaba a gareshi daya kiyaye dukkan gaɓɓansa gwargwadon iko, kuma
yayi soyayya domin Allah, yayi ƙiyayya dominsa, kuma ya yarda domin Allah, yayi
fushi dominsa, kuma yayi umurni da kyakkyawan aiki, yayi hani da mummuna.
kuma baya halatta ga musulmi da yayi abota da fasiƙi, ko tarayya dashi, ba tare da
wata lallura ba.
kuma kada ya nemi yardar halittu wajen saɓawa mahalicci, kamar yadda Allah
tsarki ya tabbata a gareshi yace " Allah da manzansa suka fi cancanta su nemi
yardansu in sun kasance muminai. (suratut-taubah 09:62)”
1
Aibanta mutum a gabansa
2
Aibanta wani a bayansa
5
6
MATNUL AKHDARI
Manzon Allah (SAW) yace “babu biyayya ga abin halitta wajen saɓawa mahalicci”.
kuma baya halatta gareshi da ya aikata wani aiki fashe ya san hukuncin Allah
cikinsa, kuma ya tambayi malamai, yayi koyi da masu bin sunnan annabinmu
muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi. Malaman dake shiryarwa
bisa ɗa’a ga Allah, kuma suna tsoratarwa daga bin shaiɗan.
kuma kada ya yardar wa kansa abun da fallasassu suka yardar wa kansu, waɗanda
ruyawarsu ta ƙare cikin rashin ɗa’a ga Allah. kaicon bakincikinsu, kaicon tsawon
kukansu ranar alƙiyamah.
Muna rokon Allah tsarki ya tabbata a gareshi, da ya datar damu ga bin sunnar
annabinmu kuma shugabanmu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a
gareshi.
6
7
MATNUL AKHDARI
kuma dukkansu basu inganta saida ruwa mai tsarki mai tsarkakewa, kuma shine
wanda launinsa, ko ɗanɗanonsa ko ƙanshi sa bai sawya ba da abinda ke
nisantan sa a rinjaye, kamar mai, ko man dabbobi, ko romo, ko ƙazantar
dabbobi, ko sabulu, ko dauɗa da makamantansu.
1
Ruwan mai tsarki neh mai tsarkakewa.
7
8
MATNUL AKHDARI
kuma duk wanda ya tuna da najasa alhali yana sallah, toh ya yanke sallar, saifa idan
yana tsoron fitan lokacinta.
Duk wanda yayi sallah da ita (tufafi mai najasa) sannan ya tuna bayan ya idar da
sallan, toh zai maimaita sallan, matuƙar lokacinta bai fita bah.
8
9
MATNUL AKHDARI
Duk wanda ya manta farilla cikin farillan alwala, toh idan ya tuna da wuri, zai
wanke gaɓan da duk abun da biyo bayanta, amma idan akwai jinkiri, toh zai wanke
gaɓan ita kaɗai, kuma ya maimaita duk sallan daya sallata da alwalan.
9
10
MATNUL AKHDARI
Amma idan ya bar sunnah, toh zai aikata ta domin sallolin dake gabatowa, ba tare
da maimaita sallolin da suka wuce ba.
Kuma duk wanda ya manta da wani lum'ah, toh zai wanke ta da niyya, kuma idan
yayi sallah kafin nan, zai maimaita sallansa.
Duk wanda ya tuna da kuskuran baki da shaƙa ruwa bayan ya fara wanke fuska,
toh kada ya koma ya aikata su, sai ya kammala alwalansa.
kuma yana wajaba a tsefe yatsun hannu yayin alwala, kuma tsefe yatsun ƙafa
mustahabbi neh. Yana wajaba a tsefe gemu mara cika yayin alwala komabayar
cikakkiya, kuma yana wajaba tsefe gemu yayin wanka koda cikakkiya ce.
10
11
MATNUL AKHDARI
Sabubbah sune : bacci mai nauyi, suma, māye, hauka, sunbanta, shafan mace idan
an nufaci jin daɗi ko an ji daɗin, da shafan azzakari da tafin hannu ko da tafin
yatsu.
Duk wanda yake kokwanto kan hadasi toh alwala ta wajaba a gareshi, saifa idan ya
kasance mai yawan waswasi neh, toh babu komai a gareshi.
kuma shi maziyyi wani ruwa neh mai fita yayin sha'awah ƙarama ta hanyar tunani
ko kallo ko waninsa.
11
12
MATNUL AKHDARI
FASALI CIKIN ABUBUWAN DA BASU HALATTA BA GA
MARA ALWALA
Kuma bāya halatta ba ga mara alwala da yayi :
1. Sallah.
2. Ɗawafi.
3. Shafan mushafin alƙur'ani da hannunsa ko da sanda ko makamantansu.
4. Shafan allon alƙur'ani saifa ga ɗalibi ko malamin da zai kyautata shi.
Hukuncin yaro wajen shafar Alƙur'ani kamar babba yake, Amma laifin yana ga
wanda ya miƙa masa alƙur'anin.
Kuma duk wanda yayi sallah batare da alwala ba da gangan, toh kafiri neh, Muna
neman tsarin Allah daga haka.
12
13
MATNUL AKHDARI
Duk wanda yayi mafarkin yana jima'i amma ba abin daya fita daga jikinsa, toh babu
komai a gareshi.
Duk wanda yaga maniyyi bushesshe a tufafinsa, baisan sanda ya fitar dashi ba, to
sai yayi wanka ya maimaita sallolin daya sallata bayan baccinsa ta ƙarshe cikin
wannan tufafin.
13
14
MATNUL AKHDARI
14
15
MATNUL AKHDARI
Duk wanda ya manta da wata lum'ah ko gaɓa cikin wankansa, toh ya gaggauta
zuwa ga wanke ta yayin da ya tuna, koda bayan wata ɗaya neh, kuma ya maimaita
duk sallolin daya sallata gabaninsa.
Idan gaɓa mai lum'an ta dace da gaɓan alwala kuma an wanke ta yayin alwala, toh
hakan ya isar masa.
15
16
MATNUL AKHDARI
Bāya halatta ga mai janaba da ya shiga masallaci, ko yayi karatun alƙur'ani, sai dai
aya ɗaya ko makamancinta domin neman tsari ko makamancinsa.
kuma bāya halatta ga wanda baya iya wanka da ruwan sanyi, da yayi jima'i da
matansa, har sai ya tattali nā'uran tafasa ruwa, sai fa idan mafarki yayi, toh babu
matsala a gare shi.
16
17
MATNUL AKHDARI
17
18
MATNUL AKHDARI
Abubuwa dake warware taymama ɗaya suke da abubuwan dake warware alwala.
Kuma ba'a sallar farillai biyu da taymama ɗaya, amma ya halatta ayi sallolin nafila
masu yawa da taymama ɗaya.
18
19
MATNUL AKHDARI
Duk wanda yayi taymama domin sallan farilla, ya halatta yayi sallan nafila da ita,
haka taɓa alƙur'ani mai girma da ɗawafi, da karatun alƙur'ani idan yayi niyyar
hakan kuma ya sadata da sallah kuma ya zanto lokacin sallar bai fita bah.
kuma ya halatta a aikata duk abin da aka ambata a baya da taymaman sallan
nafila, amma banda sallan farilla.
Duk wanda ya sallaci sallan isha'i da taymama, ya halatta yayi sallan shafa'i da
wuturi da ita ba tare da wani jinkiri ba.
Wanda yayi taymama domin janaba toh babu makawa sai yayi niyyarta.
19
20
MATNUL AKHDARI
Mātā dangane da jinin haila sun kasu gida uku, farrariya1, sababbiya2 da mai ciki.
Mafi tsawon al'adah ga fararriya kwanaki goma sha biyar neh, ga sabbabiya kuma
gwargwadon al-adarta, idan jinin ya cigaba da zuwa, sai ta ƙara kwanaki uku,
matuƙar bai wuce kwanaki goma sha biyar bah3.
Sannan ga mai ciki {mafi tsawon aladanta} bayan cikin yakai watanni uku, zatayi
jinin kwanaki goma sha biyar, bayan cikin yakai watanni shida zatayi jinin kwanaki
ishirin.
Idan jinin ya yayyanke, sai ta harhaɗa kwanakin har sai al'adanta ya cika.
Kuma sallah da azumi da ɗawafi basu halatta ba ga mai haila, haka taɓa alƙur'ani
mai girma, da shiga masallaci, kuma zata rama azumi banda sallah. kuma ya
halatta ta karanta Alƙur'ani.
1
Wacca ta fara jinin haila
2
Wacca ta saba yin haila
3
Misali mai al’adar kwanaki biyar sai ta kara kwanaki uku yakai kwanaki takwas, idan ya wuce haka ya zama jinin ciwo, mai aladar
kwanaki goma sha uku ta kara kwanaki biyu.
20
21
MATNUL AKHDARI
Amma, Idan jinin ya ɗauke kafin hakan, koda a ranar haihuwa neh, zatayi wanka ta
fara sallah, sannan idan jinin ya dawo, kuma tazaransa da jinin farko yakai kwanaki
goma sha biyar, toh sabon jinin haila neh, idan bai kai kwanaki goma shabiyar ba,
to zata haɗashi da jinin farko {jinin biki} domin cigabansa neh.
21
22
MATNUL AKHDARI
Lokaci mukhtari1 na sallar azahar yana farawa sanda rana tayi zawaali2 zuwa sanda
inuwa tayi daidai da tsawo, mukhtari na sallar la'asar na farawa daga sanda inuwa
tayi daidai da tsawo {karshen lokacin azahar} zuwa lokacin da rana tayi fatsi fatsi,
lokaci lalurinsu3 kuma zuwa faɗin rana.
Lokaci mukhtari na sallar asubah na farawa neh daga ɓullowar alfijr zuwa haske
madaukakiya, lalurinsa kuma zuwa ɓullowar rana.
Duk sallar da ba'ayita a lokacinta ba, kamar yadda ya gabata, toh ta zama sallar
ramuwa.
Wanda ya jinkirta sallah har lokacinta ta fita toh yana da zunubi mai girma, saifa
idan ya kasance mantuwa neh ko bacci yayi.
1
Lokaci mukhtari shine lokacin farko daya dace ayi sallan farilla
2
Idan rana ta wuce tsakiyan sama
3
Lokaci laluri shine lokacin dake farawa bayan ƙarewan mukhtari, Jinkirta sallah zuwa lokaci laluri bai dace ba.
22
23
MATNUL AKHDARI
Ba'a yin sallan nafila bayan sallan asubah har sai rana ta ɗaukaka, haka bayan sallar
la'asar zuwa sallar magriba, da bayan ɓullowar alfijir saifa sallan nafilan dare ga
wanda bacci ta rinjaye shi.
kuma {ba’a nafila} daga lokacinda limami ya zauna kan mimbari ranan juma'ah, da
bayan sallan juma'ah har sai ya fita daga masallaci.
23
24
MATNUL AKHDARI
kuma makruhi1 neh yin sallah cikin dogon wando, face akwai wani {riga ko mayafi}
a samansa.
Duk wanda tufafinsa ta samu najasa, kuma bai samu wata tufan da zaiyi sallah da
ita bah, kuma bai samu ruwan da zai wanke tufafin ba, ko baida tufafin da zaisa
yayin wanke mai najasar, kuma yana tsoron fitan lokaci, toh yayi sallah da tufafi
mai najasan.
Kuma baya halatta a jinkirta sallah daga lokacinta saboda rashin tsarki, kuma duk
wanda ya aikata haka ya saɓawa mahaliccinsa.
1
Makruhi shine aikin da babu zunubi ga wanda ya aikata, amma akwai lada ga wanda bai aikata bah.
24
25
MATNUL AKHDARI
Duk wanda bai samu tufafin da zai suturce alauran sa ba, toh yayi sallan tsirara,
kuma duk wanda yayi kuskuren alƙiblah, toh zai maimaita sallan idan lokacinta bai
gushe ba.
kuma dukkan hukuncin da zaisa a maimaita sallah cikin lokaci, toh hukuncin baya
aiki kan sallar ramuwa da ta nafila.
25
26
MATNUL AKHDARI
1
Daidaita a tsaye bayan ɗagowa daga ruku’u da daidaita a zaune bayan ɗagowa daga sujada
26
27
MATNUL AKHDARI
1. Tada Iƙaamah
2. Karatun surah
3. Tsayuwa dominta
4. Asirtawa inda ake asirtawa
5. Bayyanawa inda ake bayyanawa
6. Cewa sami'allahu liman hamida
7. Dukkan kabbara sunnah ce face kabbaran harama
8. Tahiyyu biyu
9. Zama dominsu
10. Gabatarda karatun fatiha kafin surah
11. Sallama ta biyu data uku ga mamu,
12. Kuma bayyana sallama wajibi neh
13. Salati ga Manzon Allah (SAW) a tahiyan ƙarshe.
14. Sujada bisa hanci da tafukan hannaye da gwiwoyi da yatsun duga dugai.
15. Da sanya shamaki ga liman da mai sallah shi kaɗai, kuma mafi ƙarancin
shamakin ta zanto meh kaurin sandar mashi, tsawonta kuma zira'i ɗaya, sannan ta
zanto mai tsarki, tabbatacciya ba mai kawo waswasi a rai ba.
27
28
MATNUL AKHDARI
1
Māmu shine mai bin liman sallah
28
29
MATNUL AKHDARI
MAKRUHAN SALLAH
1
Khushu’i ya ƙunshi ƙanƙan da kai da tsoron allah da natsuwa da maida hankali a sallah.
29
30
MATNUL AKHDARI
Sallah tana da haske mai girma, wacca zukatan masallata ke haskaka da ita, amma
ba’a samun wannan haske sai masu khushu’i a sallar su, saboda haka idan kazo yin
sallah, ka nisantar da zuciyarka daga lamarin duniya da abinda ke cikinta, kuma ka
shagaltu da ganawa da ubangijinka, wanda kake sallah domin neman yardarsa.
kuma ka ƙudurta cewa sallah ƙanƙan da kai neh da tawadu’u ga Allah maɗaukaki,
ta hanyar tsayuwa da ruku’u da sujjada, saboda haka ka kula da sallarka domin
tana cikin ibadu mafi girma, kada ka bar shaiɗan ya shagaltar da kai daga sallar ka,
har zuciyarka ta toshe kuma ya haramta maka daɗin haskenta, saboda haka, ka
lizimci dawwamar da khushu’i a sallarka, domin lallai sallah tana hani daga alfasha
da abunƙi, saboda khushu’in masallaci cikinta, kuma ka nemi taimakon Allah,
domin lallai shine fiyayyen mai taimako.
30
31
MATNUL AKHDARI
FASALI CIKIN HALAYEN SALLOLIN FARILLA
Sallar farilla tana da halaye bakwai ababen jerantawa wanda ake aikatawa cikinsu,
huɗu cikinsu wajibi neh {jerantasu}, uku kuma mustahabbi neh, halaye huɗun daya
wajaba a jerantasu :
Jerantawa tsakanin waɗannan halaye huɗu wajibi neh, idan mai sallah nada ikon
sallah a wani hali sannan yayi sallar a wani hali na daban, toh sallarsa ta ɓaci.
Halaye ukun da mustahabbi neh jerantasu, shine duk wanda bai iya sallah a halaye
huɗun da suka gabata yayin sallar yana kwance a ɓangaren jikinsa ta dama, sannan
a ɓangaren hagu, sannan a gadon bayansa. Idan ya sassaɓa cikin halaye ukun nan,
sallarsa bata ɓaci bah.
Kuma dogaron dake lalata sallah shine dogaron da masallaci zai faɗi idan an cire
madogaran, amma idan bazai faɗi ba, toh wannan dogaron makruhi neh.
31
32
MATNUL AKHDARI
Amma gameda sallar nafila, ya hallatta mai ikon tsayuwa ya sallaceta a zaune,
saidai yanada rabin ladar wanda yayi a tsaye, kuma ya hallata ya fara sallar a zaune
sannan ya miƙe, ko ya farata a tsaye sannan ya zauna, saifa idan ya shigeta da
niyyar tsayuwa, a wannan halin zama baya halatta.
32
33
MATNUL AKHDARI
FASALI CIKIN RAMA SALLAH
Kuma baya halatta ayi sakaci wajen ramawa, duk wanda a duk rana yake rama
sallar kwanaki biyar1 toh ba mai sakaci bane.
kuma zai rama sallar neh bisa ga halin data kuɓuce masa, idan ta kasance sallar
zaman gida, zai ramata a matsayin sallar zaman gida, idan ta kasance sallar halin
tafiya ce, zai ramata a matsayin sallar halin tafiya, duk ɗaya neh mazaunin gida
yake ko matafiyi yayin rama sallar.
Kuma jerantawa tsakanin hādirai {sallar wannan lokacin} da rama salloli kaɗan
wajibi neh, kuma salloli kaɗan sune salloli huɗu ko ƙasa da haka.
Saboda haka duk wanda zai rama salloli huɗu kaɗai ko ƙasa da haka, wajibi neh ya
fara rama sallolin kafin aikata sallar wannan lokacin, koda lokacin sallar zai fita.
Kuma rama sallah ta halatta a dukkan lokuta na rana da yini, da yayin ɓullowar
rana, da lokacin faɗuwarta.
1
Salloli ashirin da biyar
33
34
MATNUL AKHDARI
Kuma wanda zai rama sallah bazai yi sallar nafilah ba, haka sallar walha, da sallan
daren ramadan.
Duk {sallolin nafila} basu halatta gareshi ba face shafa’i da wuturi, da sallar idi biyu,
da sallar kisfewar rana, da sallar neman ruwa.
Kuma ya halatta ga masu rama sallah dasu rama cikin jam’i, idan halin sallolinsu ya
zanto irin ɗaya.
Idan mai rama sallah ya manta adadin sallolin da ake binsa, toh zaiyi ta ramawa
adadi mai yawa har ya zanto baida kokwanto {cewa wanda ya sallata sunfi wanda
ake binsa yawa}.
34
35
MATNUL AKHDARI
FASALI CIKIN SUJJADAR RAFKANUWA
Sujjadar rafkanuwa1 a sallah sunnah ce, ga duk ragi {tauyewa} da akayi a sallah,
za’ayi sujjadu biyu kafin sallama bayan kammala tahiyya, sannan a sake wata
tahiyar ta daban sai ayi sallam. {sujjadar ƙabli}
Ga duk ƙarin da akayi a sallah, za’ayi sujjadu biyu bayan sallama, sai a sake tahiyya,
sannan ayi wata sallamar. {sujjadar ba’adi}
Kuma duk wanda yayi ragi kuma yayi ƙari a sallah, toh zaiyi sujjadar ƙabli.
Kuma duk wanda ya manta da sujjadar ƙabli har yayi sallama, toh sai yayi sujjadun
{yayin daya tuna} idan babu jinkiri, amma idan an daɗe ko ya fita daga masallaci,
toh sujjadar ta lalace, kuma sallar ma ta lalace matuƙar sunnoni uku ko sama da
haka ya rage, idan ba haka ba, toh sallan bata lalace ba.
Duk wanda ya manta da sujjadar ba’adi, to zai aikata ta {duk sadda ya tuna} koda
an shekara.
Duk wanda ya rage farilla a sallansa, toh sujjadar rafkanuwa bata wadatarwa,
kuma duk wanda ya rage mustahabbi toh babu sujjadan rafkanuwa a gareshi.
1
Sujjadar rafkanuwa itace sujjadar ƙabli ko ba’adi
35
36
MATNUL AKHDARI
Ba’a aikata sujjadar ƙabli sai an rage sunnoni biyu ko sama da haka, amma sunnah
ɗaya ba’a mata sujjadar ƙabli, saifa wajen asirta karatu da bayyanawa.
Duk wanda ya asirta inda ake bayyanawa toh zaiyi sujjadar ƙabli, duk wanda ya
bayyana inda ake asirtawa, zai yi sujjadar ba’adi.
Kuma duk wanda yayi magana a sallah da rafkanuwa toh zaiyi sujjadar ba’adi.
Duk wanda yayi sallama yayin da yayi raka’o’i biyu bisa rafkanuwa, toh zaiyi
sujjadar ba’adi {bayan ya cike sallansa}.
Duk wanda ya ƙara raka’a ɗaya ko biyu a sallansa {da rafkanuwa} zaiyi sujjadar
ba’adi, duk wanda ya ƙara raka’o’i a salla adadi tamkar raka’o’in sallan, toh
sallansa ta lalace.
Duk wanda yayi kokwanton cikan sallansa, to yazo da abinda yake kokwanto a
cikinta.
Kuma duk kokwanto cikin ragi a salla kamar tabbatar dashi neh, saboda haka duk
wanda yayi kokwanto kan rage raka’ah ko sujjada, toh zai aikata ta sannan yayi
sujjadar ba’adi.
36
37
MATNUL AKHDARI
Duk wanda yayi kokwanto kan sallama, toh yayi sallaman {yayin daya tuna} kuma
babu sujjada a kanshi idan babu jinkiri, amma idan an daɗe toh sallar ta lalace.
Kuma mai yawan waswasi a sallar zaiyi watsi da waswasinsa, kuma bazai aikata
abinda yake waswasi kansa ba, amma zaiyi sujjadar ba’adi, duk ɗaya neh yayi
kokwanto neh kan ƙari ko ragi.
Duk wanda ya bayyana ƙunūtu babu sujjada a gareshi, saidai yin haka da gangan
makruhi neh.
Kuma wanda ya karanta sura a raka’o’i biyun ƙarshe babu komai a gareshi.
Kuma duk wanda ya saurari ambaton annabi muhammad (SAW) alhali yana sallah
sannan yayi masa salati, toh babu komai a gareshi koda yayi hakan neh da gangan
ko da mantuwa, ko a tsaye yake, ko a zaune.
Kuma duk wanda ya karanta surori biyu ko sama da haka a raka’a ɗaya, ko ya fita
daga wata surah zuwa wata, ko yayi ruku’u kafin kammala karatun surah toh babu
komai a gareshi cikin dukkan halayen.
Duk wanda yayi nuni da yatsa ko kansa alhali yana sallah toh babu komai a gareshi.
37
38
MATNUL AKHDARI
Kuma duk wanda ya maimaita fatiha da rafkanuwa, toh zaiyi sujjadar ba’adi, idan
kuma da gangan neh to sallansa ta ɓaci ga zance mafi rinjaye.
Duk wanda ya tuna da karatun surah bayan ya durƙusa zuwa ruku’u, toh kada ya
koma yin karatun, { ya cigaba da sallansa}
Kuma duk wanda yayi kuskuren asirtawa ko bayyanawa {sannan ya tuna} kafin
ruku’u, toh sai ya maimaita karatun idan hakan ya kasance ga surah ce kaɗai, toh
sai ya sake karatun suran kuma babu sujjada a gareshi, idan ya kasance da karatun
fatiha toh zai maimaita sannan yayi sujjadar ba’adi.
Idan kuma yayi ruku’u toh {ya cigaba da sallansa} sai yayi sujjadar ƙabli idan
asirtawa yayi wajen bayyanawa, ko sujjadar ba’adi idan bayyanawa yayi wajen
asirtawa, koda ko surace kaɗai ko fatiha.
Kuma duk wanda yayi dariya a sallah toh sallansa ta ɓaci, duk ɗaya neh da gangan
yayi koda rafkanuwa, kuma babu mai dariya a sallah face rafkananne, mai wasa,
Shi mumini idan ya himmatu da yin sallah, yana nisantar da zuciyansa daga komai
koma bayan Allah, kuma yana barin tunanin duniya da abunda ke cikinta, ya
halarto da zuciyansa ga buwayan Allah, da girmansa, kuma ya raurawar da
zuciyansa, ya tsoratar da kansa kan girman Allah, wanda girmansa ya ɗaukaka,
wannan itace sallan masu taƙawah {tsoron Allah}!.
38
39
MATNUL AKHDARI
Kuma babu laifi ga wanda yayi murmushi, kuma kukan mai tsoron Allah abun
gafartawa neh, kuma duk wanda yayi sauraro kaɗan ga mai magana yayin sallah
toh babu komai a gareshi.
Duk wanda ya miƙe a raka’ah ta biyu {maimakon zaman tahiya} toh idan ya tuna
kafin hannayensa da gwiwoyinsa subar ƙasa, toh sai ya zauna kuma babu sujjada a
gareshi.
Idan kuma ya koma ya zauna bayan barin ƙasa da rafkanuwa koda gangan, sallansa
tayi, amma zaiyi sujjadar ba’adi.
Duk wanda yayi busa cikin salla da rafkanuwa, zaiyi sujjadar ba’adi. Idan kuma da
gangan neh to sallansa ta ɓaci.
Duk wadda yayi atishawa a sallah toh kada ya shagaltu da faɗin Alhamdulillah,
kuma kada ya maida ma wanda ya gaida shi {wanda yace masa Yarhamakallahu}.
Amma idan yace Alhamdulillah, babu matsala a gareshi.
Kuma duk wanda yayi hamma cikin sallah toh ya rufe bakinsa, kuma kada yayi tofi
sai a tufafinsa kuma ba tare da fidda sautin harafi ba.
39
40
MATNUL AKHDARI
Duk wanda yake kokwanton hadasi ko najasa yayin sallah; sannan yayi tunani na
lokaci ƙanƙani sai ya tabbatar da tsarkinsa, toh babu matsala a gareshi.
Kuma duk wanda yayi waiwaye a sallah da rafkanuwa toh babu matsala a gareshi,
amma yin haka da gangan makruhi neh, idan kuma ya juya wa alƙibla baya toh zai
maimaita sallan {domin ta lalace}.
Duk wanda yayi sallah da tufafin alhariri, ko da zoben zinari, ko yayi sata yayin
salla, ko yayi kallo zuwa ga haram, toh shi mai saɓo neh, amma sallansa tayi.
Kuma duk wanda yayi kuskuren karanta alƙur’ani, da kalman da bata cikin ƙur’ani,
toh zaiyi sujjadan ba’adi, idan akwai kalman a ƙur’ani toh babu sujjada a gareshi
saifa idan ya sawya lafazin kalmar ko ya lalata ma’ananta, sai yayi sujjadan ba’adi.
Duk wanda yayi gyangyadi yayin sallah, toh babu sujjada a gareshi, amma idan
baccinsa tayi nauyi toh zai maimaita alwala da sallan.
Kuma nishin mara lafiya a sallah abun yafewa neh, kuma gyaran murya domin
lallura abun yafewa neh, idan kuma domin fahimtarwa neh to makruhi neh, amma
bata lalata sallah.
Duk wanda aka ƙwala masa kira sai yace subhanallah, toh haka makruhi neh,
amma sallarsa ta inganta.
40
41
MATNUL AKHDARI
Kuma duk wanda ya tsaya cikin wata ayah, kuma babu wanda ya tuna masa, toh ya
barta ya shiga ayah ta gaba, idan ya kasa karanta ayan dake gaba, toh yayi ruku’u
amma kada ya buɗe mushafin alƙur’ani ya duba, saifa idan hakan ya kasance cikin
suratul fatiha domin babu makawa sai an karanceta, da mushafin alƙur’ani ko
waninta.
Idan ya bar ayah {a suratul fatiha} da mantuwa, zaiyi sujjadar ƙabli, idan kuma ya
bar sama da ayah, toh sallansa ta lalace.
Kuma duk wanda ya yi buɗin karatu ga wanda ba limaminsa bah, toh sallansa ta
lalace, kuma ba’a buɗin karatu ga limami har sai ya jira buɗin, ko ma’anar karatun
ta lalace.
Kuma duk wanda yayi tunanin duniya kaɗan cikin sallah, toh ladansa ta ragu amma
sallansa bata ɓaci ba.
Kuma duk wanda ya ture wanda kebi ta gabansa, ko yayi sujjada a ɓangaren
goshinsa, ko yayi sujjada a naɗi ɗaya ko biyu na rawaninsa, toh babu matsala a
gareshi.
41
42
MATNUL AKHDARI
Kuma Liman na ɗauke rafkanuwan mᾱmu1, saifa idan {rafkanuwan) ya kasance kan
farillah.
Idan mᾱmu ya rafkana baiyi ruku’u bah, ko an matse shi, ko yana gyangyaɗi
{angaje} sanda akayi, kuma hakan ya kasance ba’a raka’an farko ba, toh idan ya
tsammaci rizƙan liman kafin ɗagowansa daga sujjada ta biyu, yayi ruku’u ya cigaba
da sallan.2
Amma idan bai tsammaci rizƙan limamin bah, toh yayi watsi da raka’an, ya cigaba
da bin limaminsa, saiya rama raka’ah ɗaya bayan sallaman limamin a maimakonta.
Kuma idan ya rafkana baiyi sujjada ba, ko yayi gyangyaɗi ko aka matse shi, har
liman ya miƙe ga sabuwar raka’a, toh sai yayi sujjadar idan ya tsammaci rizƙar
liman kafin yayi ruku’u, amma idan bai tsammaci rizƙar limamin ba kafin ruku’u,
toh yayi watsi wa wannan raka’an ya miƙe ya cigaba da bin limaminsa, sannan ya
rama raka’ah ɗaya bayan sallaman limamin.
Kuma cikin halayen da suka gabata {inda mᾱmu zai rama raka’ah ɗaya}, toh babu
sujjadar rafkanuwa a gareshi, saifa idan ya kasance kokwanto yayi kan ruku’u ko
sujjadar, toh zaiyi sujjadar ba’adi.
Kuma duk wanda maciji ko kunama sukazo masa alhali yana sallah, saiya kashe,
toh babu matsala a gareshi, saifa idan ya ɗauki lokaci mai tsawo ko ya juya baya ga
alƙiblah, toh zai yanke sallah {domin ta lalace}.
1
Mᾱmu shine mai bin liman sallah.
2
Idan haka ta faru a raka’an farko to sallan ta lalace, sai mamun ya sake kabbaran harama yabi limaminsa.
42
43
MATNUL AKHDARI
Kuma duk wanda ke kokwanto shin yana sallan wuturi neh ko raka’a ta biyun
shafa’i, toh ya maidata raka’a ta biyun shafa’i, kuma zaiyi sujjadan ba’adi sannan
yayi wuturi.
Kuma duk wanda yayi magana tsakanin shafa’i da wuturi da mantuwa toh babu
matsala a gareshi, amma yin haka da gangan makruhi neh, amma babu matsala a
gareshi.
Kuma ga masbuƙi1, idan bai samu raka’a ko ɗaya ba tareda liman, toh kada yayi
sujjadan ƙabli ko ba’adi tare dashi, Idan kuma yayi sujjadan to sallansa ta lalace.
Idan kuma ya samu raka’ah cikakka ko sama da haka {tare da liman}, toh zaiyi
sujjadar ƙabli tare dashi, sannan ya jinkirta ba’adi har sai ya ramo raka’o’in daya
rasa, sannan yayi sujjadan bayan sallama. Idan yayi sujjadan ba’adi kafin cike
sallansa da gangan, to sallan ta lalace.
Idan masbuƙi yayi rafkanuwa bayan sallaman limami toh hukuncinsa ɗaya yake da
mai sallah shi kaɗai.
Kuma idan masbuƙi ya samu sujjadan ba’adi ta janibin limaminsa, sannan sujjadan
ƙabli daga wajensa, toh sujjadar ƙablin ta wadatar.
1
Mᾱmun daya rasa wasu raka’o’i a sallah.
43
44
MATNUL AKHDARI
Kuma duk wanda ya manta da ruku’u sannan ya tuna yayin sujjada, toh zai miƙe
tsaye, sannan anso ya maimaita karatun ƙur’ani, sannan yayi ruku’u ya cigaba da
sallansa, sai yayi sujjadan ba’adi.
Kuma duk wanda ya manta da sujada ɗaya, sannan ya tuna bayan miƙewa {ga
sabuwar raka’ah}, toh sai ya koma a zaune yayi sujjadan, saifa idan ya kasance yayi
zama kafin miƙewansa, toh bazai sake zaman ba.
Duk wanda ya manta da sujjadu biyu, toh zai gurpana yana sujjada ba tareda ya
zauna ba, kuma a duk halayen da suka gabata zaiyi sujjadan ba’adi.
Idan ya tuna da sujjada bayan ya ɗago kansa daga ruku’un raka’an dake gaba da
ita, toh ya cigaba da sallansa, kada yayi sujjadan, sannan yayi watsi da wannar
raka’ar ya ƙara raka’ah ɗaya, yana mai gini kan abinda ya sallata, Kuma zaiyi
sujjadar ƙabli idan mantuwar ta kasance neh cikin raka’o’i biyun farko bayan ƙulla
raka’ah ta uku.
Zaiyi sujjadar ba’adi idan bata kasance cikin raka’o’in biyun farko bah, ko ta
kasance cikinsu amma ya tuna kafin ƙulla raka’ah ta uku domin karatun fatiha da
surah basu kuɓuce ba.
Kuma duk wanda yayi sallama alhali yana kokwanton cikan sallansa, toh sallan ta
ɓaci.
44
45
MATNUL AKHDARI
kuma rafkanuwa a sallan ramako ɗaya yake da rafkanuwa a sallan cikin lokaci.
Rafkanuwa cikin sallan farilla daya yake da rafkanuwa cikin sallan nafila, saifa a
wurare guda shida
1. Karatun fatiha
2. Karatun surah
3. Bayyana karatu wajen asirtawa
4. Asirta karatu wajen bayyanawa
5. ƙarin raka’ah
6. Mantawa da wasu rukannan sallah
Ga duk wanda ya manta karatun fatiha a sallan nafila sannan ya tuna bayan
ɗagowa daga ruku’u toh ya cigaba da sallansa, sannan yayi sujjadan ƙabli, saɓanin
sallan farilla inda zaiyi watsi da wannan raka’an ya kawo wata maimakonta, kuma
sujjadan rafkanuwansa zai kasance kamar yadda muka ambata a mas’alan wanda
ya manta da sujjada.
Kuma duk wanda ya miƙe ga raka’ah ta uku a sallan nafila, idan ya tuna kafin yin
ruku’u, toh ya zauna ya sallame sannan yayi sujjadar ba’adi.
45
46
MATNUL AKHDARI
Idan bai tuna ba har yayi ruku’u toh ya ƙara raka’ah ta huɗu sannan yayi sujjadan
ƙabli {domin ya rage sallaman raka’o’i biyun farko}.
Saɓanin sallar farilla, inda zai zauna duk lokacin daya tuna, yayi sallama, sannan
yayi sujjadar ba’adi.
Kuma duk wanda ya manta da wani rukuni cikin sallan nafila, kaman ruku’u ko
sujjada, kuma bai tuna ba har yayi sallama da lokaci mai tsawo, toh bazai maimaita
sallan ba, saɓanin sallan farilla inda zai maimaita komin tsawon lokaci.
Kuma duk wanda ya yanke sallan nafila da gangan, ko ya bar raka’ah ko sujjada da
gangan, toh zai maimaita ta komin tsawon lokaci.
Kuma duk wanda yayi ajiyar zuciya a sallah, toh babu matsala gareshi, saifa idan
yayi furuci da wani harafi {sai yayi sujjadar ba’adi idan da rafkanuwa neh}.
Idan limaminka zai miƙe a raka’ah ta biyu {maimakon zaman tahiya}, toh kace
subhanallah, amma idan ya rabu da ƙasa to ka bishi ku cigaba da sallan.
Idan kuma ya zauna a raka’an farko ko ta uku {maimakon miƙewa}, toh ka miƙe ka
jira shi a tsaye kada ka zauna.
46
47
MATNUL AKHDARI
Idan limaminka ya miƙe bayan yin sujjada ɗaya, toh kace subhanallah kada ka miƙe
tare dashi, saifa idan kaji tsoron zai ƙulla raka’ah, {zai ɗago daga ruku’u}, toh sai ka
miƙe ka bishi, {raka’anku ta farko wacca ba’ayi mata sujada ba ta baci, saboda haka
ta biyun ta zama ta farko} sannan kada ka zauna tare dashi cikin raka’ansa ta biyu
{raka’ar da limamin ya tsammace ta ta biyu wanda a haƙiƙani itace ta farko} ko na
huɗunsa {raka’ar da limamin ya tsammace ta ta huɗu amma a haƙiƙani itace ta
uku}. Idan yayi sallama toh ka ƙara raka’ah ɗaya maimakon raka’ar da kayi watsi da
ita, sannan kayi sujjadar ƙabli.
Amma idan kun kasance cikin jam’i toh abinda akafiso shine ku gabatarda ɗaya
daga cikinku ya limance ku wajen cike sallar.
Idan limami zaiyi sujjada ta uku toh kace subhanallah, kada kayi sujjadar tare dashi,
kuma idan limami ya miƙe ga raka’ah ta biyar, toh wajibi neh ga duk wanda yake
da yaƙini ko kokwanton hakan daya bishi, wanda kuma yakeda yaƙinin ƙari ce toh
wajibi neh ya zauna. Idan wanda ya wajaba ya miƙe ya zauna, ko wanda ya wajaba
ya zauna ya miƙe, toh sallansa ta lalace.
Kuma idan limami yayi sallama kafin cike sallansa, waɗanda ke bayansu sai suce
subhanallah!, idan limamin ya gamsu dasu toh sai ya cike sallan, idan kuma yana
kokwanto sai ya tambayi aadilai biyu, kuma ya halatta suyi magana.
Idan limamin nada yaƙinin cikan sallan, to yayi watsi da hukuncin aadilan ya
sallame sallan, saifa idan mutane {masu ganin sallar bai cika ba} suna na yawa, toh
sai yayi watsi da yaƙininsa, ya koma zuwaga fahimtansu.
47
48
MATNUL AKHDARI
المصادر و المراجع
Email : [email protected]
48