0% found this document useful (0 votes)
99 views39 pages

Boyayyen Sirri THS by Jasmine.

Uploaded by

msaleadamu121
Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as TXT, PDF, TXT or read online on Scribd
0% found this document useful (0 votes)
99 views39 pages

Boyayyen Sirri THS by Jasmine.

Uploaded by

msaleadamu121
Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as TXT, PDF, TXT or read online on Scribd
You are on page 1/ 39

馃尨馃尨*BOYAYYEN SIRRI*馃尨馃尨

(The Hidden Secret)


Story and Writing
Asmau Bint Abubakar
By
馃尭 Jasmine 馃尭

*馃實 MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION 馃摎馃枈*
*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko


da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.馃馃徎```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

*Wannan labarin kirkirarren labarine banyi dan wata ko wani ba Wanda yaga labarin
yazo dai dai danasa toh akasine ban yarda a chanzamin labari ba Wanda ya chanza min
ban yafeba.*

*BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM*

Dajine sosai da yake cike da dogaye dakuma gajerun bishiyoyi wanda ganyayyakinsu
suka kasance koraye sharr.

Idan mutum ya shigo cikin wannan daji da fari zaiyi tunanin Montane Forest ne
saboda yadda dajin yakasance a tsare, wanda za'ayi tunanin wasune suka tsarashi
amma bahaka bane tsantar ikon Allah ne kawai.
Idan kashigo wannan daji farkon abinda zaka fara arba dashi shine, wasu dogayeb
bishiyoyi tsirarru sai kuma ciyayi matsakaita. Yanayin gurin akwai sanyi sosai
saboda yawaitar ruwan sama da ake samu a arean, wanda a take mutum musamman ma
wanda ya karanci Ecology zai alkinta yanayin gurin dana Montane Forest.

Amma abin bahaka yake ba, domin idan kayi tafiyar 20km a cikin wannan wuri, zaka
kara haduwa da wani waje mai ban sha'awa. Matsakaitan bishiyoyine masu fala_falan
dakuma korayen ganye sune a wannan waje, sannan a kasan ko wacce bishiya akwai wasu
kananan shukoki masu matukar kyau da birgewa. Zamu iya alakanta yanayin wanna wuri
dana Mangrove Swamps.

Tafiyar kusan 11km zakayi a wannan yanayi kafin ya sadaka da wani wuri wanda yake
yanayi da dazuzzukan da muka saba gani da shiga, amma shi wannan waje ciki yake da
shukoki kala daban-daban da kuma tsirarun dabbobi da suke rayuwa a wajen.
A takaice dai wannan forest yanada three different regions.

A wani guri wanda yake kamar garden saboda yawan bishiyoyi kayan marmari da ya
kayata wajen, a gefe guda kuma ga magudanar ruwa da yake ta zuba.. Idan ka kalli
gefe guda kuwa, wasu kyawawan duwatsune a jere, wanda. Yanayin jeruwarsu ya
forming matattakala dazata fitar da mutum daga wannan kebabban waje.. Wanna
kenan....

Acan wata kusurwa kuwa, wata matashiyar yarinyace a zaune akallah shekarunta na
haihuwa bazasu wuce 16yrs ba. Fara ce sosai kuma kyakkyawa ta gaske, domin zamu
iya jerata a sahun matan da ake musu lakani da EPITOME LADIES saboda kyawun fuska
da na jiki da Allah yabasu.

A zaune take kan wani dutse dake gefen ruwan, yayinda tazura kafafunta a ciki tana
wasa dasu. Gefenta kuwa wani matsakaicin kwandone data cikashi da kayan marmari.
Sanye take da kaya irin na kabilar Yoruba wanda kalarsu yake sky blue, yayinda
kugunta, hannayenta, kafafunta daku wuyanta suke cike da beads masu matukar kyau. A
sama kanta kuwa wata hulace maikyau data rufe mata saman kai, yayinda ake hango
gashinta baki sidik kuma dogo daga inda hular bata rufe bah.

Ajiyar zuciya ta sauke tareda share kwallar data zubomata, tarasa wani daliline
yasaka suke rayuwa a wannan wuri?? Most at times idan ta tambayi mahaifiyarta bata
samun gamsashshiyar amsa.
Tanaso tasan wacece ita?.. Suwaye danginta??.. Dalilin dayasa sukabar cikin mutane
yan'uwansu suke rayuwa a tsakanin dabbobi?. Su biyune kawai mutanen dasuke rayuwa a
wannan wuri, domin bata taba ganin wani jinsinsu yashigo wannan daji ba.

"I want to know the hidden secret" tafada cikin siririyar muryarta mai dadin
sauraro..

Tafiya takeyi a hankali tamkar wacce take tsoron taka kasa yayinda tabi wata
siririyar hanya da zata sadata da gidan da suke rayuwa a ciki. Wani abu taji yana
bimata kafa, bata ko kula menene ba tazura hannu ta janyo.
Wani koren snake tagani dan karami, babu alama tsoro ko firgici a tattare da ita
yayinda take kara rikeshi sosai a hannunta tareda zubamishi dararan
idanunta."Bantaba ganinka a yankinnan ba ga dukkan alamu kaidin sabon kyankyasane
kuma yau kafara shawagi" tafada a hankali tanamai jujjuyashi a hannunta. Kwantar
dakai maciji yayi akan yatsunta tare da rufe idanu a hankali.
A iya tsowon zaman datayi a wannan daji babu wata alama da dabbobin sukeyi wanda
batasan fassararsu ba, hakan ne ma yasata tsugunawa tare da mikar da hannun nata
dayake rike da macijin a kasa, a hankali kuwa ya sulale tare da shigewa cikin
ciyayin dake waje..

Daukan basket din tayi tare da cigaba da tafiya tana tunanin yadda tun tasowarta
bata da wasu abokan hulda sai dabbobi, bawai batajin dadin rayuwar dasu bane amma
tanasan taga ta kasance a cikin jinsin mutane yan uwanta amma tana gani kamar
wannan ne burinta guda daya wanda kuma bata tunanin zai cika.
Duk da kasancewarta wacce take rayuwa a daji hakan bai hanata sani duk wani abu
daya shafi zamani ba, kama daga Ilimin boko dana addini, ado da kwalliya, girke-
girke, gyaran jiki dadai sauransu domin kuwa maamanta daki guda taware mata domin
karatu wanda ta wadatashi da duk wani abu da mai neman ilimi zai bukata.
Babu wani abu namore rayuwa da babushi a gidan da suke sannan a duk lokacin da suke
bukatar wasu abubuwan, maama dakanta take shiga can cikin gari tanemu musu wanda a
duk sanda tayi irin wannan tafiyar sai ta kwana saboda nisan dayake tsakanin dajin
da cikin gari.
Tanada tarin tambayoyi da dama datakeso tayiwa maamar tata amma bata samun dama.

Adaidai nan ta iso wani karamin compound mai dauke da wani ginin laka mai kyau
sosai, dakuna guda ukune ta gefen dama idan mutum yakalla, sai wani madaidaici
wanda sukeyin girki aciki, daga can gefe guda kuwa toilet ne matsakaici. Duk da
kasancewa da laka akayi ginin amma hakan bai hanashi yin kyau ba.
Ta gefen hagu kuwa wata rumface ta kara maikyau wacce akayi ginin laka a cikinta
aka fitar da shape din kujeru wanda za'a iya zama a huta.
Gefe da gefen compound din kuwa zagaye yake da ornamental plant masu kyau wanda
suke fitar da wani kamshi mai dadi.

A tsaye take tana karewa wajen kallo dakyau yayinda wani sashi na zuciyarta yaketa
kokarin karyata tunaninta nacewa maama ita kadai tayi gini gamida tsara wannan
waje. Dole akwai wani ko wasu da suka saka hannu.
Amma suwaye? Tamnayar da tayiwa kanta kenan wacce tasan bata da amsarta, domin dai
tun tasowarta bawanda ta taba gani ya tako inda suke."kodai hakan na nufin maaman
kadai tayi ginin" wani sashi na zuciyarta yafada, gorgiza kai tayi a hankali tana
mai fadin"Inaaa! Impossible! Not maama alone " a cikin zuciyar tata.

Dafata da taji anyine yakatse mata tunanin datakeyi wanda koda bata juya ba tasan
mahaifiyarta ce, toh wama zai dafata haka idan ba maamar ba. Babu wani dayake zuwa
musu balle tayi tunanin ko baki sukayi sannan kuma dabbobin datake tarayya dasu
tunkafin isowarsu takeji sahunsu ko kukansu.
Katseta maamar tasakeyi ta hanyar fadin"Ife mi"(My love ).

Juyuwa tayi tana kallon matar da a kalla shekarunta zasu haura 35yrs wacce take
sanye da black Arabian gown mai adon stones a jiki. Zubinta kuwa sak na fulani
asali saboda kyau da haske.

Murmushi tayi wanda yasa dimple dinta lotsawa sosai tace"Iya mi"(My mom).

"Why are you standing here Princess" maamar tafada sanda take jan hannunta domin su
karasa rumfar dake compound din. Zaunar da ita tayi kana itama ta zauna tana fadin
"You look too worried my Princess Eraj"..
Kallon maamar tayi wacce ta ajiye mata ruwa tanamai kokarin zuba mata abinci tace"
Maa why do you like referring me with Princess isn't Eraj alone not ok for you?
Nidai banso" takarasa fada tana shagwabe fuska.

Ita kuwa dataketa kokarin hadawa Eraj din abinci tace"Why shouldn't I call you
Princess when you're from a royal family, people will call you with that even if I
didn't"..

A firgice Eraj ta tashi ta isa ga maamar ta riketa gam tareda fadin"Royal family??
Did you just said something about my family??? Tell me Maa please don't say no"
takarasa fada da yanayi tausayi a fuskarta.
Maama da batasan sanda zancen zucinta yafito fili ba ta kalleta tare da mika mata
plate din abincin tace" Kici abinci Ife you haven't eat something since morning"
takarasa fada tana shirin mike ta fice a rumfar.

Riko mata kafa Eraj tayi hawaye nabin fuskarta tace"Maa please".. Dagota tayi tare
da share mata hawayen take bin fuskarta kana tazaunar da ita akan kujera tana
fadin" Not this time again, kici abinci kawai"..

Ko gezau Eraj din batayi ba bare taci abincin da maama ta ajiyemata.

Har maama tasakai zata fice sai kuma ta dawo saboda sanin datayi cewa indai bata
amsawa Eraj tambayarta ba, toh ba abincin zataci ba sannan zata karawa kanta damuwa
akan wacce take ciki na rashin sanin danginta. Zama tayi tare da cewa" Yes Eraj
you're from a royal family" ..

Da gaste maama. Tafada cikin kwababbiyar hausarta irinta yara,domin a duka yarukan
da maama ta koya mata hausa ce kawai bata wani iya sosai ba. Tanajin duk abun da
za'a fada amma wajen mayarwa ne ake samun mushkila.

Kallon diyar tata tayi wacce lokaci guda tsantsar farinciki ya bayyana a fuskarta
saboda jin wani abu daya danganci danginta. Zataso ace kamar yadda Eraj din take
marmari dason ganin danginta suma ta bangarensu ya kasance hakan.
Saidai kash!! tasan abune mai matukar wuya, musamman idan ta tuna irin bakar wuyar
datasha agun dangin mahaifin Eraj din. Sam bazata iya barin 'yar tata tayi kallar
rayuwar da tayi ba, wannan dalilin ne ma yasaka ta zaba musu wannan waje a matsayin
gurin da zasuyi rayuwa.

Ajiyar zuciya mai karfi ta sauke kana takalli Eraj wacce ta zuba mata idanu tana
jiran amsarta, murmushi tayi gami da cewa" Yes Ife! Your dad is the first son to
the king of *UMUAPALA* *ROYAL* *KINGDOM* and he's the heir of the throne after his
father.. I hope kingane reason dina na kiranki Princess " takarasa fada tana kallon
Eraj din kana tamike ta nufi hanyar ficewa.

"Iya Miiiiii" taji anfada wanda hakan yasakata juyuwa da nufin yimata magana, amma
me, gabanta ne yabada wani sauti rass rasss sannan fuskarta yanuna alamun tashin
hankali.

07048961623

Kallon Eraj tayi da take zaune tana rike da kunnuwa sannan ta turo baki gamida
kyabe fuska. Hakan da tayine yasata tunawa da yar'uwarta Afeeyah wacce duk lokacin
da take bukatar wani abu a wajenta hakan da Eraj tayi itama shi takeyi sak.
Take taji wasu hawaye masu zafi suna zubo mata, wata irin kewar gida taji yana zuwa
mata from nowhere.

Shin akan wani daliline Abbu zaice karta kara waiwayen danginta. Abunda ta
aikata ko a musulunci bai haramta ba, kawai dai al'adace irinta hausa fulani da
basason bada aure ga wani yare daban wanda banasu ba. Kullum da kewar gida take
kwana take tashi, tanaso taga iyayenta da yan uwanta amma babu damar hakan.

Sam bazata taba mancewa da furucin Abbu ba sanda yake cewa" Kitafi Aysha na
yafemiki duniya da lahira amma kisani idan wata matsala ta faru kika waiwayeni ko
wani a cikin dangina bazan yafemiki ba kuma tsinuwata zata tabbata a kanki, tashi
kitafi"..
Kukan da taketa kokarin hadiyewa ne ya kwace mata, take kuwa ta cigaba da rerashi
tamkar wata karamar yarinya.

Idan da sabo yakamata ace izuwa yanzu Eraj tasaba da ganin kukan mahaifiyarta, amma
ina, takasa sabo da hakan. A duk lokacin da zataga maama tana kuka hankalinta yana
tashi sosai, takan rasa meyake mata dadi a duniyarnan. Batada kowa sai mahaifiyarta
a yanzu shiyasa sam bataso tana ganinta cikin damuwa.
Kukan itama tafara mara sauti tana maijin takaicin kasancewar rayuwarsu a haka.

Saida sukayi mai isarsu kafin maama ta tsagaita tare da dago Eraj share mata
hawayen fuskarta tace"Its enough Princess, not this time again. Kici abinci kizo ki
watering plants dinki". Takarasa fada tanamai ficewa a rumfar.
Eraj kuwa ta dade a zaune kafin ta tsakuri abincin taci, rufe sauran tayi kana
tamike ta nufi gurin shukokin domin yimusu ban ruwa.

KADUNA STATE

Tun daga nesa ya hangota tana tafe hawaye nabin fuskarta, koda ta karaso inda yake
murmushi tamai gamida fadin" Uncle dama fah......."

A firgice yatashi daga baccin daya daukeshi akan sallaya tun bayan daya gama azkar
dinshi na safiya, kallon agogon dakin yayi yaga har karfe 8:30am yanamai mamakin
yadda akayi yayi irin wannan baccin haka.
Take kuma mafarkin dayayi ya dawomai wanda kimanin tsawon wata shida kenan yana
irin wannan mafarkin kuma ga dukkan alamu yarinyar taimako take bukata.

Hakanna Allah yayimishi wannan baiwar wanda a duk sanda yayi mafarkin mutum toh
tabbas cikin biyu akwai daya, kodai wanda yayi mafarkin dashi nason ganinshi ko
kuma yana bukatar taimakonshi. Amma ita wannan yarinyar fa bai santa ba kuma bai
taba ganinta ba kawai dai abinda zai iya cewa shine, yanayin yarinyar yana yimishi
kama da wani nashi wanda baisan kowaye ba.

Ya dade a zaune kafin ya mike ya nufi toilet domin yin wanka, koda yafito shiryawa
yayi cikin wasi dark blue din suit da suka yimishi kyau sosai suka kara fito mishi
da kamaninshi tsab na saurayi dan shekara talatin. Daukar wayoyinshi yayi tare da
jakar laptop dinshi yanufi part din Umminsa.

Kamar koda yaushe a zaune ya sameta ta dasa hoton wata matashiyar yarinya tana
kallo yayinda hawaye yake bin fuskarta.
Zama yayi a gefenta tare da kawar da hoton daga ganinta. Kallon dan nata tayi
hawaye na cigaba ta zubomata tace" A ina zanganta ne Abjal, jikina yana bani bata
mutu ba amma bansan a inda zan ganta ba" takarasa fada gamida fashewa da kuka.

Rarrashinta Abjal din ya cigaba dayi kamar koda yaushe, tare da fadamata kalamai
masu sanyaya rai.

Turo kofar dakin akayi hade da sallama, wani dattijon mutum ne mai sallamar wanda
alamu suka nuna shine maigidan. Abjal ne kadai ya iya amsa sallamar tare da gaishe
da mahaifin nasa cikin nutsuwa, daga bisani kuma ya mike yana fadin"Abbu zan wuce
office, ummi sai nadawo".
Kai kawai ta gyada yayinda Abbu koma yamai addu'ar dawowa lafiya.

Bayan ficewar Abjal din ne Abbu yadawo kusada ita yana kara share mata hawaye
yanacewa" Fatimah nasan gaba daya laifina kike gani akan wannan al'amarin amma ni
furucin danayi bada wata manufa bane kuma tunkafin ta bar gidannan ma nariga na
janye. Amma kiyi hakuri ki fawwalawa Allah komai zai sama mana mafita. Insha Allahu
indai tanada rai za'a ganta.

"Kanada tabbacin za'a gantane, yarinyar da take da shege zuciya da riko. Na tabbata
bazata taba zama a inda tasan za'a ganta ba, nina haifi Aysha kuma babu wani
halinta da bansani ba. Muddin aka haramta mata yin Abu toh har abada bazata taba
yiba bare kai kuma dakayi mata barazanar tsinuwa, tayaya ma zata fara waiwayo mu".
Ummi takarasa fada cikin jimami.

Girgiza kai Abbu yayi hade da cewa"Kuskure dai anyi kuma anyi nadamar yinsa, mubar
komai a gurin Allah yana sane damu". A haka dai ya cigaba da lallashinta harya samu
hankalinta yadan kwanta, sannan suka Mike domin zuwa dinning room suyi breakfast.

Shikuwa Abjal bayan fitarsa direct private hospital din da Abbu ya gina masa ya
nufa, wanda da kanshi yazabi a saka ma asibitin suna *AYSHATUL HUMAYRAH SPECIALIST
HOSPITAL*. Hakan kuwa ba karamin faranta ran ummi yayiba.
Koda ya isa direct office dinshi yanufa batare daya duba patients ba kamar yadda
yasaba.

Kishigida yayi akan sofa yanamai tunanin mafita ga matsalar Ummi tashi gefe guda
kuma tunanin yarinyar dayake yawan mafarkinta ya dameshi.
Dole yana bukatar su zauna da yayarshi domin tattauna matsalolin nashi, lallai zuwa
Jos yakamashi.

Daukan wayarshi yayi tare da dialing din numbar dayayi saving da Big Sis, ringing
biyu ta dauka tana fadin"Autan ummi ince dai ba wrong dial kayi ba"..
Murmushi yayi mai sauti kafin yace"Toh kodai na kashe ne"..

"Yi hakuri auta res dinmu, dafatan katashi lafiya". Tafada tana dariya.
Gaisawa sukayi sosai kana daga bisani Abjal din yace"Inason nashigo garinku weekend
hope dae kunanan".
"Babu inda zamuje auta res Allah yakawoka lafiya" tafada daga dayan bangaren. Kafin
su cigaba da hira wanda yawanci tsokanan junane a ciki daga bisani kuma sukayi
sallana.

Ganin yasama ma kanshi mafita ne yasa ya mike ya nufi wards domin duba patients.

FOREST

Washegari kuwa bayan sungama daily routine dinsu, zama sukayi a rumfa suna hira
cikin nishadi kamar basuda damuwar komai.

Gyaran murya maama tayi wanda ke nuni da akwai abinda takesan fada, hakannan yau
takejin kwarin gwiwar sanar da diyar tata tarihinta.
Zama tayi sosai tace"Tashi ki zauna kinji Princess, yau inaso na amsa miki duk wasu
tambayoyinki da kika dade kina jiran amsoshinsu"

Eraj najin haka ta zauna ta tattaru duk wata nutsuwarta tare da maida hankalinta
kacokan gurin maama.

*Story and Written By*�


*Asmau Bint Abubakar*

```Tuna Baya```
Asalin sunan mahaifinmu Sa'ad Abdul_Jalal Sa'ad wanda mutane sukafi sani da Alhaji
SAS, sunan SAS din yasamu asaline tun daga kuruciyarshi a lokacin da suke
makaranta. A maimakon a kirashi abokanshi su kirashi da asalin sunanshi sai suka
abbreviating dinshi yadawo SAS sunan kuwa ya bishi har girma.

Ya kasance 'da ne a gurin Alhaji Abdul_jalal da Hajiyah Aysha, bayanshi akwai


kannensa biyu Afeeyah da Ibrahim Khaleel sai kuma babban wansu Saleem.
Mahaifansu yan Gombe State ne acikin wani gari Deba, kasuwanci ne yadawo da
mahaifinsu garin Kaduna inda ananne kuma ya kafa zuri'arshi.
Yatara arziki daidai gwargwado hakanne yasa 'yayanshi basu taso cikin wahala ba.
Babban dansu Saleem a yanzu haka yana aikine a Federal High Court dake Abuja
kasancewar shidin babban Barrister ne, anan cikin garin suke zaune da matarshi da
kuma yaranshi biyar Safwan, Sakeenat, Sa'ad, Safeeyat da autansu Sulaiman.
Hakanan yake sha'awar duk wani suna daya fara da harafin S, sannan kuma sam yaki
yarda a boye ma yaran suna.

Daga Bar. Saleem kuma sai mahaifinmu wanda shi tun yana karaminshi yakeson business
kuma abinda ya karanta kennan. Bayan kammala karatunshi kuwa yafada harkar business
din kuma cikin lokaci ya daukaka.
A wata tafiya dayayi ne zuwa Egypt ne suka kulla soyayyah da Fateemah harya nemi
izinin aurenta a gurin iyayenta. A cikin watannin da basu gaza hudu ba iyayenta
sukazo har Naija sukayi bincike a kanshi kafinnan suka amince aka daura musu aure
ya tattaro matarshi suka dawo Nigeria.

Kanwarshi Afeeyah kuwa a Kano tayi aure inda take da yara biyu sannan kuma tana
aikinta na likitanci. Sai autansu Ibrahim Khaleel daya kasance Engineer sannan shi
anan cikin garin kaduna yake aikin kuma yake zaune da matarshi da yaronsu daya
Junaid. ```wannan kenan```

Saida iyayenmu suka shekara biyar da aure kafin mahaifiyarmu tasamu ciki wanda
yabata matukar wahala, domin har doctors sun yake shawarar a cireshi amma fir taki
yarda.Cikin ikon Allah kuwa daya fara girma sai laulayi ya ragu sosai.
Cikinta na wata8 sukayi wani mummunan rashi na Alhaji Abdul_jalal da kuma Hajja
Aysha sakamakon hatsarin mota da sukayi akan hanyar dawowarsu daga Gombe.
Tun bayan rasuwar ne kuma yaran suka kara hada kansu sosai duk da kasancewar wasu
basa gari amma hakan bai hana su gudanar da family meeting duk karshen wata ba,
domin kara zumunci a tsakaninsu da kuma 'yayansu.

Saida cikin Ummi(Mahaifiyarmu) yakai wata goma har yana kokarin wucewa kafin ta
haifi 'ya'yanta biyu duka mata kyawawa sosai. Tubarkallah.
Bayan ranar suna ta zagayo aka radawa yara sunan Aysha da Afeeyah(Ni da kanwata
kenan).

Tun bayan haihuwar mune kuma arzikin Abbu yakara habaka sosai fiyema da da, inda
yakara bude wasu masana'antu tare da zuba hannun jari a companies da dama.
Haka muka taso cikin so da kulawar iyayenmu dama dangi gaba daya.

Kallon Eraj maama tayi tace" Ina fatan dai kina gane kan labarin danake baki, i'm
just telling you about my family background first."
Daga mata kai kawai Eraj ta iya yi domin itakam wannan person to person history din
baganeshi takeyi ba. Main abinda takeson sani shine dalilin rayuwarsu a tsakiyar
daji kuma tsakanin dabbobi.

Bata ko kula da yanayin Eraj dinba ta cigaba:

Shekararmu shida a duniya Ummi takuma samun wani cikin, a lokacin mukuma muna Basic
1. Saboda tun kafin mu cika shekara 2 Abbu yasaka mu a makaranta.
Bayan wata tara kuwa Ummi ta santalo kyakkyawan yaronta mai tsananin kamada ita
wanda aka radawa suna Abdul_jalal amma muna kiranshi AbJal.
Tun kanshi kuma Ummi bata kara haihuwa ba.

Duk da kasancewar mun tasone cikin gata amma iyayenmu basu gaza ba wurin bamu
ingantacciyar tarbiya bisa ga koyarwar addinin Islamah.
Sannan Abbu ya kafa mana dokar yin yare biyu kacal, either English koh Arabic. Sam
yace bai yarda mu dinga hausa ba saida dalili mai karfi.
Wannan yasa inhar akaga munyi hausawa toh bama gidane kokuma munyi wasu bakin.

A takaice dai zan iya alkinta rayuwar gidanmu da rayuwar da tafi kowanne dadi a
lokacin.

Story and Written By


Asmau Bint Abubakar
Jasmine

Akwai watarana da muke hanyarmu ta dawowa daga islamiyyah wani saurayi ya tare
Afeeyah akan yana sonta, bamu ko saurareshi ba muka cigaba da tafiya har muka iso
anguwanmu. Ganin yaki barinmu ne yasa Afeeyah ta tsaya tana gayamai cewa ita fah ba
soyayyah bane yanzu a gabanta yayi hakuri ya tafi, amma sam yaki tafiya.
Ana haka saiga motar Abbu ta sawo kai cikin anguwan, ganinshi kuwa ba karamin
kidimamu yayi ba. Take Afeeyah tacema saurayin ya tafi don Allah gobe ya jirata a
hanyar islamiyyah, jin hakan dayayi ne yasa yayi mana godiya tare da juyawa ya
tafi. Mukuma muka kara sauri domin shigewa gida.

Abbu ko ruwa bai shaba bayan shigowarshi ya kiramu ya fara mana masifa tamkar zai
aro baki, sosai yake mana fada tare da kashedin kar mu sake ya kuma ganinmu da
wani.
Ganin bashida niyar daina masifarne ya Ummi yin magana tace"Haba Alhaji kayi hakuri
mana su din fa 'ya'ya mata ne, rayuwarsu a gida kalilance dole za'a kaisu gidan
wani bawai zamu ajiyesu bane muyita kallonsu. Amma idan kace karsu kula kowa
tayayane zasu samu miji suyi aure in badai kuma aurwn dole zakayi musu ba, dama dai
cewa kayi su fitar da tsayayyaye guda daya ai yafi. Koda ace ba yanzu zasuyi auren
ba.
Wani mugun kallo Abbu ya watsa mata kana yace cikib fusata"Kingama! Nace kingama 銆倀
oh ki bude kunnenki ki jini da kyau, kinga wadannan yaran" yafada yana nunamu kafin
ya kuma cewa" Inada tsari akan mazajen da nakeso su aura. Bazanje ina aurawa
'ya'yana namijin da ko cikakkkiyar wankan tsarki bai iya ba, wayayyun maza zasu
aura wa'yanda suka jiko da ilimin boko dana addini. Kina yimin kallon dan boko koh?
Toh wallahi koda ace wanda yakeda certificate na ph.d ne zaizo neman auren daya
daga cikinsu inhar bashi da wadataccen ilimin addini bazan bashi auren ba.
Tukunna ma yarannan yaushe sukayi girman da har zasu tsaya da samari? Yanxu ne fah
suke JSS3 , idan ma zasu fara tsayuwa da samari ae sa bari sufara karatun degree
dai".
Sai dayayi fada sosai kafin yadau ruwan da ummi ta ajiye mishi yasha, sannan yakuma
kallo mu yace"Ku tashi ku tafi kar kuma a kara maimaita irin haka"
Da toh muka amsa mai sannan muka bar falon.

Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya wata rana da dadi watarana kuma akasin haka.
Har muka shiga ajin karshe na secondary kuma a lokacinne mukayi saukar Al Qurani.

```Mafarin Alamarin```

Wata ranar asabar ne na tambayi Abbu zuwa gidan Uncle Khaleel kuma ya lamuncemin
naje na wuni aca. Kasancewar nasan Afeeyah basa shiri da matar Uncle Khaleel din ne
yasa banyi mata tayin zuwa ba na shirya na tafi abuna, domin ni Allah ya hada
jinina dana Aunty Suhaima kusan kowani lamari na rayuwata da ita nake shawara.
Hakanan naji sha'awar na tafi a kafa duk da kuwa Abbu ya bani kudin mashi amma
saboda ba wani nisa ne da anguwarsu ba yasa kawai na yanke shawarar tafiya a kasan.
Banyi nisa a tafiyar ba wani bakin hadari ya taso wanda da alama ruwan gab yake da
fara sauka. Hakadai na cigaba da tafiya ina addu'ar kar ruwan ya sauko har saina
isa, sai dai kash, ban ko kara tafiyar minti biyar ba ruwan ya fara sauka da
karfinshi.
A barandar wani shago dana gani a rufe na fake har ruwan daya kusa awa daya yana
zuba ya tsagaita.

Bayan tsayuwar ruwan ne da kaman minti goma nafito na cigaba da tafiya, gab da zan
tsallaka titin dazai sadani da anguwarsu Aunty Suhaima ne naga wata bakar wallet
mai kyau a gefe, ga dukkan alamu garin gudun ruwane mamallakinta ya yasar da ita.
Harnayi gaba zan wuce kuma nadawo dauka, sakamakon tunanin danayi nakar wasu marasa
gaskiyan su tsinta kuma suki bibiyar maishi. Karkabeta nayi tare da zurata a cikin
jakata na cigaba da tafiya.

Murna Mami (Aunty suhaima) tayi sosai daganina, cikin shiri nasameta da alama fita
zatayi.
Bayan mun gama gaisawane take cemin"Aysha kin ganni cikin shiri koh, wallahi wata
kawatace ta haihu zanje suna tunda kinzoma sai mutafi tare"
Girgiza kai nayi saboda ni sam banason shiga cikin taro, kana na cemata"A'a mami
dama wuni nazo yimiki tunda bakyanan kawai zan wuce gida."

"Ai baza ayi hakaba Aysha kiyi zamanki zankira Abbun naku yabarki ki kwanamin nasan
bashi da matsala" Takarasa fada tana mikewa kafin ta kuma cewa "Idan kinji yunwa ki
shiga kicin ki tafasa wani abin, insha Allah nima da la'asar zan dawo."

Ko bayan fitanta kwanciya nayi ina huce gajiyar tafiyan kafa danayi. Kwatsam saina
tuna da wallet dinnan, dauko jakata nayi tare da cirota. Koda na bude ba wasu
abubuwa bani a ciki face kudaden da a kallah zasu kai dubu 15 sai passports da kuma
wani ID card.
Koda na duba jikin card din hoton wani fari kuma kyakkyawan matashi nagani daga
kasa kuma
An rubuta *Dr. Adekunle Ayomide* sannan numbers.
Nadade a zaune ina kallon Card din kafin daga bisani na yanke shawarar yin amfani
da telephone din su Mami na kira numbers din jiki. Tashi nayi jiki ba kwari saboda
zuciyata danaji tana harbawa da sauri na isa kusa da table din da telephone din
yake ajiye. Number daya na kwafa tare dayin dialing.... Yadan jima kafin naji
alaman an daga amma ba'ayi magana ba.

Daurewa nayi nace"Assalamu Alaikum"

Jimm! Kafin naji wata sassanyar murya nacewa" This is doctor Kunle speaking how may
I help".
Cikin harshen danaji yayi amfani dashi nagaya mishi dalilin kiran.

Sai kuma naji yace"Praise the lord" kasa-kasa naji muryar wasu sun amsa mai
da"Hallelujah"....

Wani irin tashi tsaye Eraj tayi wanda har ya tsorata Maama cikin ina ina tace"My
fa..ther maama kuma Non_Muslim"

"Sure Non_Muslim then." Maama tafada tana share hawayen dayake zubomata da gefen
zaninta.

Bayan ta share hawayen dake zubo matane ta cigaba.

Bayan nayi mai kwatancen gidan mami ne kamar yadda ya bukata, sai na tashi nayi
sallah kafin yazo.
Minti 30 tsakani ya kira yace gashi a kofar gidan. Koda na fito shi kadai nasame
shi jingine da motar danayi tunanin tasace, gaisawa muka karayi sannan na mika
mishi wallet din. Godiya yayimin sosai sannan muka dan fara hira kaman dama can
munsan juna.

Duk da kasancewar naji abinda yafada sanda muke waya, amma ganin wata karamar sarka
a wuyanshi mai 鉁濓笍 ya kara tabbatarmin da shidin ba musulmi bane. A kalla mun shafe
awa daya da rabi muna hira kafin yace min zai tafi amma nayo kokari na kirashi da
numbar gidanmu idan na koma, saboda na gayamai nan din ba gidanmu bane. Hakadai
mukayi sallama ya tafi.

Tun daga lokacin kuna shakuwa mai karfi ta shiga tsakanin, yawanci a gidan mami
muke haduwa amma tun dana fara school a KASU sai yazama munfi haduwa a can. Kuma
duk wannan lamarin Mami ce kawai tasani domin hatta Afeeyah bata ta6a sanin ina
tare dashi ba.

A takaice dai saida.mukayi shekara biyu muna alaqar da.muka kasa bata sunan
soyayyah, abota ko shaquwa. Kwatsam! Wata rana muna hira a gidan Mami yake cemin
yanada sha'awar ya musulunta amma baisan yadda zaiyi ba, bansan dalili ba amma dai
jinayi ba'a tabayimin albishir mai dadin wannan ba.
Tashi nayi da sauri naje na samu mami da maganan wanda itama ta nuna murna sosai
domin tana yawan fadamin cewa" Aysha nidai wannan yaron yana birgeni wallahi kawai
matsalan addinin shi ne damuwan".
Take tabani umarnin na shigo dashi falonta, bayan na shigo dashi ne nikuma na wuce
dakin mami. Sun dade suna magana kafin mami ta kirani na rakashi, bamu wani jima ba
yamin sallama ya tafi.
Bayan tafiyar shine mami ke cemin ta hadasu da baffanta kuma yace yaje gida ya
sameshi indai da niyya daya yakeson shiga musuluncin to a yau za'a sashi ya karbi
kalimatush shahada.

Eraj idan nace zan baki tarihina daki daki lallai bazamu kareshi a wata 2 bama,
shiyasa nakeso na fadamiki main abubuwan da zasu amsa miki duk wata tambayar da
zatazo kwakwalwarki.... Maama kenan take fadawa Eraj da gabadaya jikinta yayi
sanyi.

Daga mata kai Eraj din tayi alamun ta cigaba kawai.

In takaice miki Princess a shekara daya da mahaifinki yayi a musulunci yasan


abubuwan da ko wani da aka haifeshi cikin musuluncin baida iliminsu.
Duk wani abu daya kasance haram baya taba aikatawa.

Hakadai rayuwa ta cigaba da tafiya har zuwa lokacin daya nuna sha'awar aurena.
Koda na shawarci mami sai tacemin ba wani matsala bane kawai na directing dinshi
gurin Abbu.

Hakan kuwa akayi sukazo shida Baffan Mami wanda yayimai bayanin waye mahaifinki da
kuma abinda yake tafe dasu. Duk wani hadisi da ayoyi da basu haramta auren wanda ya
musulunta ba saida Baffa yayima Abbu bayani a kansu amma sam yaki amincewa cewarshi
bazai taba bama tubabbe auren 'yarshi tsarkakakkiya ba.
Haka suka tashi jiki ba laka suka tafi.
Shikuwa Abbu bayan shigowarshi gida ya kirani yamin dukan da saida nayi sati ina
jinya.

Zuwansu Baffa uku amma sam Abbu yace bai yarda ba duk kuwa da kasancewar Baffan
yazo dawasu abokanshi malamai sunyiwa Abbun bayani sosai.

Ganin mun rasa mafita ne yasa Mami ta yanke shawarar kiran Uncle Saleem ta fadamai,
koda tayimai bayani sosai fada yayi tayi akan rashin gayamai akan lokaci sannan
yace zai kira Abbun kawai dai su fara shirye shiryen su na mata domin aure kaman
anyishi angama indai har ya bincika ba samu yaron da laifin 6oye musu komai ba.

Kasancewar Uncle Saleem Barrister ne yasa cikin kankanin lokaci yagama duk wani
bincikensa akan familyn mahaifinki domin har Ibadan yaje da kanshi yayi bincike
sosai akan ```UMUAPALA ROYAL KINGDOM```, kuma bai samu wata matsala ba in banda
kawai kasancewar dayawa daga cikinsu ba musulmai bane.

Saida yagama hada duk wasu bayanai kafin yakira Abbu, bayan sun gaisa ne yafara
cewa" Sa'ad yaushene kafara adawa da abinda Allah da kanshi ya halatta nasan dai
kanada sani daidai gwargwado amma kake takeshi. Toh bawai kiranka nayi muyita jan
zance ba, na kirakane na shaida maka cewa a matsayina na wanda yake da iko dakai
dakuma 'yar taka na bada aurenta kuma nanda satikai hudu za'a daura ta tare a
gidanta". Bai ko jira yaji mai zaice ba yakashe wayar.

Kasancewar daga Abbu har kannenshi basa take umarnin babban wan nasu ne yasa dole
ba yadda ya iya ya amince, amma ya kudurta a ranshi cewa ko kwandalarshi baxai
kashe a kaina ba.

Tun ana kirga satika har anzo an fara kirga kwanakin aurena da mahaifinki.
Duk tsawon lokacinnan da aka dauka ina rayuwa ne tamkar mara galiho saboda kyara da
tsangwama da ahalin gidanmu sukemin, domin hatta Ummi da take tausayamin a farkon
lamarin sam ta daina shiga sabgogina. Afeeyah kam dama tun da akace ansa ranar
aurena ta tattara ta kuma dakin ummi, AbJal ne kawai yake rarrashina wani lokacin
idan yasameni ina kuka shima kuma sai ya tabbatar Abbu baya gidan.

Duk wanda yaji labarin aurena da wanda zan aura sai ayita kushe lamarin, dayawa
daga cikin danginmu kuwa dama Abbu yakirasu Yace basai sunzo ba domin shikam ba
taron aure ake a gidanshi ba taron zubarmai da kima ne, hakan yasa hatta Afeeyah
kanwarshi tace babu ita a taron.
Mami ce takeyin komai daya shafi auren nawa, sai ana gobe daurin aurene Uncle
Saleem da matarshi suka iso.
Koda yaji abinda Abbun yayi nakin gayyatar dangi yayi fada sosai daga bisani kuma
ya kikkira maza da yasan zasu iya hallarta daurib auren.

Washegari kuwa bayan sallar juma'a aka daura mana aure da mahaifinki inda wani
muslem dan garinsu yazo yayi waliccin auren.
Gidanmu kuwa ba wanda zaiyi tunanin wai sha'ani akeyi.

Uncle Saleem ne dakanshi yace zaikaini har dakin aurena, sannan yacewa mami idan
angama dani nazo mu tafi.
Fada irin na uwa mami da matar Uncle sukayimin kafin su mikar dani muka nufi falon
Abbu inda muka samesu zaune su uku suna hira. Koda mami tacemai gani yayimin fada
kwafa yayi kafin yace"Aysha na jamiki kunne a kan aurennan kinkiji, toh kisani
nikam na yafe miki duniya da lahira amma wallahi duk randa wata matsala da sameki
kikayi kokarin zuwa inda nake ko gurin wani daga cikin dangina bazan yafe miki ba
kuma tsinuwata zata tabbata akanki".
Ko kafin na farfado daga suman wucin gadin danayi jin furucin Abbun naji Ummi
takara da cewa"Wanda yakiji ae bazai ki gani ba"..
Jiki ba laka su mami suka dago ni daga durqushen danake ina risgar kuka muka fita,
har cikin motar Uncle suka sani sannan mami tacemin indai inada wata matsala na
kirata. Ban iya magana ba saboda kukan da yaci karfina.

Haka inaji ina gani Uncle yaja motar yabar cikin gidanmu mu wanda a ranar ne nayi
mishi kallon karshe.
Har gidan daya kasance mallakin mahaifinki Uncle yakaini sannan ya rike hannuna har
cikin bedroom din danasan shiya siyi komai na ciki.
Nasiha yayimin mai ratsa jiki sosai sannan ya ajiyemin wani envelope da kudi a
ciki, daganan yamin sallama ya tafi yana mai kara jaddadamin idan akwai wani abu
nakirashi.

Nan ya tafi yabarni ina kukan da har yau ya kasa tsayawa..... Takarasa fada tanamai
fashewa ta wani irin marayan kuka.

Kankameta Eraj tayi suka cigaba da kukan tare, a kalla sunkai minti 15 a haka kafin
maama tace" Princess tashi muje sallah lokaci yayi"..

Bayan idar da sallarsu ne Eraj ta wanke musu fruits kawai suka sha.

Kallon ta maama tayi tace" Nasan zuciyarki na zargin wai ko mahaifinki yaci amanata
ne amma sam bahaka bane bashi da laifi ko daya. Wannan labarin family na dakuma
yadda na auri mahaifinki na baki, ki nitsu dakyau ki saurareni yayinda zan baki
tarihin dangin mahaifinki domin kina bukatar sanin kowa da komai".

Da toh Eraj ta amsa kana


maama ta fara da:

*UMUAPALA ROYAL KINGDOM*

A kingdom known for its abundance wealth, history background and said to harbour
powerful men who had fought alot of wars and have emerge victorious.

Kingdom ne dayayi suna ba iya a cikin birni da kauyukan garin Ibadan ba hatta da
makotan jahohi sunsan da zaman wannan masarautar saboda tarin dukiya da suka tara
dakuma karfin iko.Tun kaka da kakanni ake mulkar wannan masarauta.
Al'adar kuwa shine duk dadewan da sarki zaiyi a mulki baza'a taba saukeshi ba
harsai ya mutu tukun a bama dansa na fari royar crown din. Idan kuma ya kasance
first born dinshi ba namiji bane, toh bayan mutuwarshi za'ayi zabe inda mutanen
palace zasu zabi wanda sukeso ya cigaba da mulkarsu. Sannan bayan za6en kuma
majority carry the votes.

A haka ake samun sarakunan kuma suke shudewa har mulkin yazo kan kakanki, wanda shi
kadai ne da namiji a familyn su sauran duk matane. Hakan yasa batare da anyi za6en
ba aka nadashi sarki.

King Ayomide shine kakanki sannan ya kasance sarki na 52 a cikin kingdom din.
Matanshi uku ne Queen Iteoluwa, Queen Oyegbemi sannan Queen Adesua.
Queen Iteoluwa itace farko kuma itace wacce ta haifi mahaifinki Adekunle da
kannensa mata guda hudu Busayomi, Adaobi, Omotola da Funke.
Wacce ta kasance ta biyu kuma Queen Oyegbemi ce 'ya'yanta biyu kacal Yemisi da kuma
Kehinde, Inda a lokacin datazo haihuwar Kehinde ne ta rasa ranta. Hakan yasa
akabarwa Queen Iteoluwa rikon 'yayan.
Sai kuma Queen Adesua da takeda yara Shida duka maza Ayinde, Adetukunbo, Olamide,
Oladapo, Alasia da kuma Adedeji.
A takaice dai mahaifinki yanada siblings 11 inda ya kasance first born of the
family.
Dukaninsu sunyi karatu ne mai zurfi sosai domin wasu ma ba a kasar sukayi karatu ba
kama daga mazan har matan.

Mahaifinki ya kasance Nephrologist consultant ne da kasashe da dama sukeson yayi


aiki dasu amma sam yaki amincewa saboda yanaso kasarshi ma ta moreshi, sannan kuma
yanada sha'awan zama a North shiyasa ya kar6i offer din yin aiki da KASUTH. Wannan
shine farkon dalilinshi nazama a garin Kaduna.
And that's just the brief I can say about ur family background.

Bayan aurenmu da wata biyune yace dani yanason muje Ibadan mu zauna kona shekara
biyu yadda zansan danginsa sosai, banyi mishi jayayya ba saboda nasan ko na zauna a
Kadunan ba wani nawa da zan dinga gani.
Mami kawai naje nayima sallama sannan na kira Uncle na shaida mishi, gaba dayansu
fatan alkhairi sukamin da fatan Isa lafiya.

Ranar wata lahadi kuwa muka wuce Ibadan. Mun isa cikin darene hakan yasa dayawa
basusan da zuwanmu ba.
Washegari bayan mun gama baccin gajiya muka shirya domin zuwa gaisheda familyn.
Kasancewar tun kafin muyi aure yake koyamin yarensu dakuma wasu daga cikin
al'adunsu ne yasa sam banji fargabar yanda zan gaishe suba. Amma can kasan zuciyata
ina tsoron irin tarbar da zasuyimin domin ya gayamin cewa sanda yazo musu da batun
musuluntarshi tashi hankali akayi sosai kafin daga.bisani aka sasanta saboda a
cikin kundin tsarin kingdom din akwai inda akace kowani mutum na cikin masarautar
yanada daman yin addinin da yakeso. Batun aure kuwa dama yacemin basu nuna dokinsu
akai ba domin suna ganin kaman zai kawu musu wani sauyi ne a cikin ahalinsu.

Gabadaya duk wani wanda yake alaqa da jinin King Ayomide a cikin masarautar saida
mukaje mukayi gaisuwa kafin daga bisani muka kuma part dinmu. Nayi mamakin yadda ko
a fuska basu nunamin banbancin yare ko addini ba hakan yasa nayi murna sosai domin
a zatona sun karbeni ne da hannu bibbiyu.

Sai abin bahaka yake ba domin kuwa gadar zare ce sukayi mana.

Na shekara daya cib a *Omuapala Royal Kingdom* batare dana fuskanci ko wacce irin
matsala ba kuma a sannan ne nasamu ciki.
Kehinde yaron Oyegbemi data rasu a Egypt yayi karatunshi kuma a can ya cigaba da
aikinshi saidai yana zuwa hutu lokaci zuwa lokaci. Abinda basu sani ba kuwa shine
Kehinde yadade da musulunta sanadiyar wani abokinshi balarabe.
Shi kadaine kawai muka saba sosai saboda yawan waya da mukeyi da kuma videos calls
kusan duk weekend idan Kunle yana gida.

Kwatsam! Watarana King Ayomide ya kira Kunle yake cemai akwai wani babban hospital
a India da suka nemi offer din yin aiki dashi kuma yarigada ya amsa musu, don haka
yake umartarshi daya shirya cikin satin biza dinshi zata fito. Koda yayimai maganar
tafiya dani sai yace sam bazai yiwuba yabarni anan in yaso yadinga zuwa hutu koda
bayan each six month ne.

Koda mahaifinki yasameni da maganan ban wani damu ba, sanin da nayi cewa babu wata
matsala dazan fuskanta. Haka na karfafa mishi gwiwa ak
bi umarnin mahaifin nashi.

Kamar yadda King Ayo yafada biza din cikin kwana biyu ta fito inda tafiyar takama
ranar laraba. Duk da yasan cewa babu abinda zan bukata amma yabarmin kudi sosai.
Ranar laraba kuwa da karfe shida jirginsu ya daga zuwa India.

Haka na zauna nikadai a part din kamar mayya sai da daddarene Kehinde yakirani muka
danyi hira.
Harnayi na kwanta bacci yafara daukata naji ana budemin kofar side dina, koda na
fito falo wasu nagani da fuska a rufe.
Kafin nakai gayin magana kuwa harsun rufemin baki tare da daukana suka fara tafiya.
Sam bani da karfin dazan iya yimusu jayayya saboda tunda nasamu ciki duk dare da
zazzabi nake kwana wanda yake kashemin jiki sosai.
Munyi tafiya mai dan nisa kafin muka shiga wani gida wanda yake acan bayan gidajen
maids, saida suka danganani da wani daki tukun kafin su saukeni.

Wani abu nagani kamar lilo amma na karfe sannan ata kasanshi garwashine yake taci
sosai, bangama tunani ba naji wata murya kaman na King Ayo yana bada umarnin a
daureni mana cikin harshe Yoruba, sai alokacin na juya sosai ina kallon dakin amma
ga mamakina duk wani daya kasance dan cikin familyn kingdom dinne yana wajen kama
daga matanshi dakuma yaranshi idan kika dauke Kunle dayake India dakuma Kehinde
dayake Egypt.

Bansamu damar yin magana ba saboda bakina dayake kunle, daukata naji ankuma yi
sannan aka nufi gurin wannan lilon dani. Hannuwa na aka fara daurewa a sama sai
kafata da aka dora akan wani karfe domin daurewa.
Wani azababben zafine ya ziyarceni sakamakon wutan garwashi dayake kasan karfe.
Ko bayan da aka daureni gabadaya naga sun nufi hanyar fita yayin da akabar wasu
biyu domin gadina.

Tun inajin zafin dayake ratsani harna daina fahimtar komai wanda alama ce ta suma
danayi. Ruwan sanyi sosai naji an watsamin amma a maimakon naji sanyin nadan samu
saukin zafi da azabar danakeji.

Haka na kwana a daure a wajen, suma kuwa bazan iya kirga saunawa nayi ba, duk sanda
na suma kuwa da ruwan sanyi sosai ake tashina inafatan Allah yakawomin dauki,
sannan lokacin salla nayi nake yin niyya na gabatar da sallahta a kowani yanayi da
na tsinci kaina.
Ko bayan dasuka fito dani daga wannan dakin wani suka kara kaini mai tsananin duhun
gaske domin koh tafin hannuna bana iya gani, sannan ga kwari masu cixo mai azabar
zafi. Kullum ana bani ruwa kofi daya, abinci kam dama sai bayan kowani kwana uku
nake samu.
Nayi kimanin wata guda a wannan dakin kafin a fito dani, a lokacin kuma cikin
jikina watansa shida yana kokarin shiga na bakwai.

Ko bayan da aka fito dani sam bana iya gani komai saboda dadewar da nayi a cikin
wannan bakin dakin, hakan yasa kawai na runtse idona. Domin tun danaga ban mutu ba
nasan tabbas wannan din kaddarata ce.

Banyi kokarin tirjiya ba lokacin danaji sun tubemin kaya tare da tsumani cikin wani
abu danayi tunanin man gyada ne, sosai nakejin zafi tamkar danyar fata ta man yake
shiga. Bayan sun gama ne kuma aka dauramin towel dako cinyata bai gama rufewa ba,
babu batun pant bare bra haka aka jani zuwa wani falo.
Kamar yadda na gansu ranar da aka daukoni haka yauma nasake ganinsu duka.
Cikin zuciyata nake addu'an Allah yakareni daga sharrin da zasu sakemin.

Muryar King Ayo ne naji yana magana kamar haka" Bazamu yarda wani bare yazo ya
gurbata mana tsarin Kingdom ba, sannan kuma bahaushiya wanda ta kasance cikin yaren
da sukafi kowa makirci, sanadiyan zuwaki yasa magajin wannan sarauta ya canja
addinin da mukeyin shi tunda dadewa, dan haka muka yanke shawarar hukuntaki sannan
mukoraki ki kuma zuwa yankin ku. Cikin jikinki kuma jibi kafin ki tafi zamu cireshi
a bainar jama'a mu nuna musu cewa mun isa da ahalinmu. Ku tashi ku kaita part
dinsu."
Sam maganar korata bai dameni ba kamar yadda naji yace za'a ciremin ciki a bainar
jama'a, haka aka jani har zuwa part dinmu sannan aka rufeni ta baya tare da zuba
securities domin yin gadina.

Jan jiki nayi izuwa bathroom nayi wanka da ruwan dumi sosai sannan na gasa jikina,
koda nayi wankan naji dadi sosai hakan yabani damar yin sallolin da bansamu damar
yi ba a ranar.
Koda na idar bantashi ba zama nayi ina nema agaji a wurin Allah. Nadade kafin na
rarrafa kitchen na nemawa kaina abinci.

Laifin iyayena kawai nake gani domin da basuyimin baki ba dana kasance cikin
kwanciyar hankali, musamman Ummi ma.
Daki na koma nafara hada kayana ina tunanin inda zan nufa bayan sun koreni inazan
nufa.

Uncle Saleem wan Abbu ne idan naje gidanshi to tabbas tsinuwar Iyayena zata tabbata
a kaina, Mami kam ban kawota cikin lissafina bah kasancewarta matar Uncle Khaleel
itama. Rasa mafita nayi hakan yasa na fashe da kuka mai karfi. Sannan nafara addu'a
a bayyane" Yah Allah ga baiwarka nan tana tsakanin bukatar taimakonka, Allah ka
kubutar dani da Abinda yake cikina karka basu damar kashe shi, Allah nasan baka
bacci kuma kanasane sa halin danake ciki. Nasan kaine ka kaddara abubuwa suke
faruwa dani, Allah ina kara gode maka a cikin kowani hali dana tsinci kaina aciki,
Alhamdulillah ala kulli halin" duk cikin yaren da yanzu ya gama gaurayemin harshe
nake wannan addu'a wato yoruba language.

Juyuwa nayi a kidime jin an amsamin da Ameen Ameen tare da cewa Allah ya amsa
addu'arki Aysha.

Kehinde ne a tsaye jikin kofar bedroom dina, duk kuwa da kasancewar ban taba
ganinshi a zahiri ba amma yawan video calls din damukeyi yasani ganeshi da sauri,
bai bari nayi magana ba yace"We don't have time to talk now Aysha let's do this
quick and leave this Kingdom" ya karashe fada yana harhadamin sauran kayayyakin da
yasan zan bukata.
Hakan yasa nagane lallai babu wanda yasan dazuwanshi har yake shirin taimakamin.

Cikin sauri ya dauki jakunkuna biyu ya fita dasu, jim kadan sai gashi ya dawo
daukan daya akwatin yayi tare da cewa na biyu shi. Wata kofa mukabi ta cikin
kitchen wacce duk tsawon zamana bansan da ita ba, sai gamu mun bullo ta wani waje
inda yayi parking din mota.
Shiga motar mukayi sannan ya tasheta da mugun gudu.

Gudu yakeyi da motar sosai har mukayi tafiya mai nisa sosai, gani kamar munbar
cikin garin Ibadan ne yasani cewa ya sassauta gudun.
Kallon daya yamin yamaida hankalinshi kan tukin dayakeyi kafin yace" My people are
sometimes very wicked, especially those that are still Christians. Idan suka duba
sukaga kin gudu gurin bokan dake cikin masarautar zasuje yayi bincike ya gano inda
kike, bayan haka kuma zaiyi asirin dazaisa da kafarki ki kuma cikin Kingdom din
harsai sungama abinda zasuyi dake kafin su baki umarnin tafiya. Amma akwai makarin
asarin dole inda zaki kasance yazama gurine da babu mutane ko suke zirga_zirga Ina
nufin dae dole daji zaki koma da rayuwa harna wani lokaci. Yanzu ga phone dina kiyi
amfani da ita ki kira wani relative dinki domin yasan halin da ake ciki inda hali
saina fadamai inda zamu hadu". Duk wannan maganar dayakeyi hankalinshi na bisa
hanya sannan baidena gudun bah.

A hankali nafara gayamai abubuwan da suka faru tun haduwana da danuwanshi har
aurenmu.

Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace" Shikenan idan al'amuran sun daidaita za'a nemi
mafita, yanxu dai musamu muyi nesa da inda zasu iya ganoki duk wasu maganganu
muyisu after".
Gyada kai kawai nayi tare da jingina bayana da jikin kujerar na kwanta tare da
lumshe idanu.

Haka mukayi ta gudu a hanya kasancewar darene yasa babu motoci sosai saidai trucks
da muke gani jefi jefi.

Story and Written By


Asmau Bint Abubakar
Jasmine

```Ramadan Budget```
```kada ki bari sai Ramadan yaxo kafin ki fara tunanin abinda zaki girka, ki tsara
komai tun yanxu hakan zai baki damar samun isasshen lokacin Ibada. Ga wasu hanyoyi
kadan da zakiyi Ramadan budget```
```Food Timetable```
```Kiyi timetable din duk wani abu dakikeso ci tun daga farkon Ramadan har
karshensa hakan zai baki daman samar da duk wani abu dazaki bukata a lokacin
azumin. Wanda hakan zai saukaka aikinki sosai tunda already kinsan abinda zaki
dafa a kowace rana```... ZAN CIGABA A NEXT PAGE 馃槏

Daidai wani gurin da naga alama a zamanin baya dutse ne amma a karaba shi biyu
akayi titi(Jos to Baushi) yayi parking. Kallon agogon dake jikin motar yayi wanda
ya nuna karfe 11:45am."Lalle munyi sauri a tafiyar nan kalli agogo." Yafada yana
nunamin agogon.

Hankalinshi ya maida kaina kafin yafara magana,"Aysha dole anan zaki cigaba da
rayuwa kafin komai ya daidaita domin idan bahaka ba zasu iya ganoki a ko ina kike,
dole zaki fuskanci abubuwa da dama amma hakan shi kadai ne mafita. Idan zamuje
yanxu tsakiyar dajine da bakowa yasani ba hasalima mutane da yawa basusan dashi ba
kamar yadda abokina ya shaidamin".
Jinjina kaina nayi tareda fadin "Bansan da wani baki zan gode maka bah kehinde
abinda kawai zan iya cewa shine Allah yasaka maka da mafificin alkhairai... Amma
baka gayamin yadda akayi kasan halin da nake ciki bah. ".Na karashe fada ina lumshe
ido saboda gajiyan zaman mota da nakeji a jikina.

"Nayita kiran numbers dinku baya shiga har Kunle dayake kasar India,nayi tunanin
idan ya landing zai kirani amma shiru har tsawon sati biyu hakan yasa na yanke
shawarar kiran king Ayo na tambayeshi number din dazan samu kunle da ita. Bayan
nakira shine yake gayamin cewa ae Kunle bawai aiki ya tafi ba kawai yasaka a
tsareshi ne a wata kasar har sungama kudurinsu tukunna, a nan yake gayamin irin
hukuncin da suke miki har shawarar da suka yanke akan cikinki. Hankalina ya tashi
sosai harnayi tunanin nabar komai na dawo Naija a lokacin amma na hakura saboda
nasan ko nazo bazan iya kubutar dakeba harsai kwanakin da suka deba na horaki sun
cika. Na riga nasan duk wata al'ada ta Kingdom din shiyasa na tsaya na shirya komai
cikin nitsuwa. Wani old friend dina nakira wanda yake garin bauchi nayimishi
bayanin komai tare da rokonshi ya bincikamin wani ke6e66en gurin dazaki iya zama.
Cikin sati ukun da yace nabashi yakirani yake sanar dani angama komai domin. Babu
bata lokaci na nemi biza na taho Nigeria batare da sanin kowa ba, a bauchi jiginmu
yayi landing inda Basheer yazo ya daukeni mukaje gidanshi. Bayan na hutane muka
nufu nan gurin inda a hanya yake gayamin yasamu aiki da AMAAL COMPANY a America
sannan yakusa tafiya. Ko bayan danaga gurin daya zaba nayaba sosai saboda is very
safe saidai kananan animals da baza,a rasa a wajen ba. A gurin muka tare muna kara
gyara wasu abubuwan har zuwa jiya da yayimin sallama ya wuce America ni kuma na
wuce Ibadan. Gidan dazaki zauna yana bayan wannan dutsen sannan a tsakiyar daji
yake bansan kozai miki ba"..

Godiya nayimishi sosai domin yamin abinda family dina nasan a yanxu bayimin zasuyi
ba. Gefe guda kuma tausayin Kunle ne fal raina.

Haka ya dauki kayayyakin nima nadau wasu muka fara tafiya, mun dade muna tafiyan
kafin mu iso wurin a lokacin kuma na rigada na fama galabaita, ga gajiyar wuyan
danayi kwana da kwanaki inasha, ga zaman mota sannan ga wannan doguwar tafiyar
musamman daya kasance ina dauke da cikin da ya fara tsufa.
Sallar asuba da muka rasa a hanya muka fara biya kafin nan ya kawomin wani bowl
cike da fruits. Sosai nasha fruits din saboda yunwar danake ji, sannan nasha
magungunan daya hadamin. Bayan nagama ne yace na shiga daya daga cikin dakuna biyun
na huta.

Kwanciya nayi akan katifar dake shimfide a dakin, bada dadewa ba baccin gajiya ya
kwasheni.

```Ramadan Budget```
```Bayan kinsamar da jadawalin abubuwan da zaki dafa a cikin azumi saiki samar da
duk wani abu dakike bukata daidai yadda kikeso sannan ki duba a ciki wayanda kike
bukatarsu in large quantity kamar kayan kunu da na shayi sannan kayan miya. Misali
idan kunun gyada yana cikin jadawalin girke-girkenki zaki iya samu gyadarki ki
soyata sannan ki kai a nika mike ita iya quantityn da kikeso, kinga duk lokacin
dazakiyi kunun gyada babu bukatar zuwa markada gyadar.
Sannan wake, ki surfa wakenki ki dayawa wanda zai kwana biyu saiki wankeshi sosai,
sannan ki bazashi a rana ya bushe, idan ya bushe saiki kaishi inji a nika mikishi
yayi laushi sosai idan kin dawo dashi saiki saka rariya ki kara tankade shi sannan
ki ajiye. Duk sanda zakiyi kosai ko alala saiki debo garin waken ki kwabashi saiki
zuba markadadden kayan miya a kai sannan kiyi hadin kosai ko alalar, shima hakan
zai saukaka miki sosai.
Gero ma ko dawa haka zakiyi mishi kikaishi surfe da daka da kayan yajinki a ciki,
duk lokacin dazakiyi kunu saiki debo ki dama kayanki.
Zanyi bayani sosai yadda za'ayi ajiyar kayan miya yadda bazai lalace ba a next
page``` To be Continue.....

_____Nasamu kwanciyar hankali sosai a zaman danakeyi a wannan guri sannan Kehinde
yana kara fad'akar dani akan rayuwa a daji tare da koyamin matakan kare kai idan
wani abu yakawomin hari duk da cewa bamu da tabbacin akwai wani abun cutarwa a
gurin. Kasancewar cikin jikina ya shiga watan haihuwane yasa dole Kehinde ya zauna
tare.da ni harzuwa lokacin dazan haihu, baya nisa sosai da gurin saboda nakuda zata
iya zuwamin a kowani irin lokaci.
Wata ranar Juma'a bayan ya tafi salla ne a cikin gari nafara nakuda, yafaramin ne
kadan kadan harnazo bana iya fahimtar abubuwa. A baranda nake ina murkususu a kasa
bazan iya misalta irin azabar danakeji ba alokacin domin numfashi har daukewa yake
yana dawowa, cikin zuciyata nake addu'oin neman sauki tare da fatan Allah ya
turomin wanda zai iya taimakona duk da banida tabbacin akwai wanda zaizo idan ba
Kehinde ba. Hakan na daure ina cigaba da neman taimakon Allah.

Tsakin danaji ne kamar na maciji ne yasani juyawa cikin hanzari, kamar yadda nayi
tunani kuwa macijiya ce a gefena kallo daya nayi mata nagane mace ce kuma ta tsofa
domin kuwa dogowace sosai ta kanannade jikinta guri daya yayinda harshenta ke waje
yana karkadashi. Wannan abu dana ganine yasa naji lokaci daya ciwon na neman barin
jikina yayinda nake tunanin mafita, kamar cikin mafarki haka naga ta jawo jiki
harkusa dani sam nakasa motsa koda yatsane bare nayi tunanin guduwa. Suman da ake
cewa na zaune shi nayi lokacin da tafara hawa jikina hasbunallahi wani'imal wakil
kawai nake iya furtawa a kasan raina, saidai a maimakon naji shigar dafi jikina
sainaga ta fara nannade jikinta a kasan cikina wanda nan take kuma naji marata tayi
wani irin zugi na sakanni sai kuma ta daina. Dogon numfashi naja sannan na saukeshi
lokacin danaji kamar abu na shirin fitowa daga jikina, bansan ya akayi ba amma
saidai naji kamar ana umurtana dayin nishi.
Nishin kuwa nayi mai karfi sannan naji abu yayi futtt! ya fado duk da ban duba ba
nasan abinda ke cikina ne ya fito duniya, wani dogon nishin nakara.ja a karo na
biyu naji fitowar wani jaririn ko jaririyar. Numfashi nafara fitarwa da sauri kafin
a karo na uku naji fitar wani abin mai kama da mahaifa. Gama hakan keda wuya naji
macijiyarnan tafara motsawa harta gama ficewa a jikina ta kuma gefe ta kanannede
jikinta kamar farkon zuwanta, tsoron danakeji ne naji ya kau cikin sauri kuma na
daga zanin dake jikina ina duba jariran da suka kasance jinsin mata, hawaye ne naji
yana bin fuskata yayinda bakina yake furta Alhamdulillah!.
Da sauri kuma na rarrafa na dauko jakar haihuwar da.muka tanada da kuma towel,
daukarsu nayi daya bayan daya na yanke musu jibiya harzuwa lokacin kuma basuyi kuka
ba.
Kehinde ne ya karaso da sauri wanda dawowanshi kenan daga cikin gari, cikin sauri
yafara basu taimakon gaggawa kasancewarsa likita. Cikin ikon Allah kuwa daya tafara
kuka amma dayar ko motsawa batayi, bayan gwajegwajen dayayi da tsirarun kayan
aikinshi ne yadago ya kalleni lokacin ina rike da wacce take kukan.
"I'm sorry Aysha she couldn't make it saboda wahalan dasuka sha aciki, But
Alhamdulillah one is alive". Yafada yana sharce hawayen da na zallan tausayine.

Kuka na fashe dashi mai ta6a zuciya, nikam babu abinda zance ma Allah saidai godiya
amma tabbas naga rayuwa iri iri.

Tattara gurin Kehinde yayi tare da kimtsa babyn mai numfashi. Sannan ya hadamin
ruwan dumi nayi wanka.

Ko bayan dana nutsuwa daukar yarinyar nayi domin yimata addu'a kamar yadda naga
Kehinde yayi dazo lokacin dayake cemin yayi mata huduba da suna *Ayshat* with
tribal name *Ohunene* and nickname *Eraj*. Kallonta nayi sosai lokaci guda naji
tsananin sonta yana shiga cikin kowani lungu da sako na jikina, kamar mu daya sak
saidai idonta irin na Kunle ne masu shige dana mage. Tunanin yadda mahafinta yaci
burin ganin wannan rana nake amma gashi ranar tazo lokacin dayayi nisa da ganinta.
A bayan dakunan mu aka binne jaririyar da batazo da rai bah idan wanda yakasance
kamar mahaifi a garesu yayi mata sallah.

Haka muka cigaba da rainon *Ayshat Adekunle Ayomide* *(Eraj*) har tsawon watannin
biyu, lokacin ne kuma Kehinde yayi shirin komawa Egypt saboda yawan kira dayake
samu na nemanshi da akeyi. Kafin tafiyarsa ne yake gayamin akwai wani mutum daya
samu karayar arziki kuma anyi mishi shaidan kwarai sosai don haka ya yanke shawarar
bude masa shagon saida kayan masarufi da sharadin duk wata za'a dinga raba ribar da
akasamu biyu yadau daya yabashi daya kuma ya amince, sannan yace na shirya muje
naga gurin saboda mutumin ya ganni a matsayin wacce zata dinga karban kudin. Sannan
yacemin yayi hakanne saboda koda watarana.abun hannuna zai kare.

Hakan kuwa akayi domin har gidan mutumin mukaje sannan muka garzaya shagon dayake
mai girman gaske wanda yake cike da kayayyakin masarufi daban daban, daganan
Kehinde ya shaidamai nice zanke zuwa ina karban kudin duk wata sannan muka dawo.

Washegari ranar juma'a Kehinde ya shirya domin tafiya da alkawarin cewa bazai
dadeba zaidawo yaga halin.da muke ciki sannan yabarmin.waya da zamu dinga
communicating dashi, babu irin addu'a ta alkairi da baiyiwa Eraj ba lokacin daya
dauketa yana magana mai kama da wasiyya. Haka dai yayi mana sallama ya tafi wanda
shima karshen ganina dashi kenan.

Tun ina kirga kwanaki har sati daya tayi amma banga kira Kehinde ba hakan yasa na
yanke shawarar kiranshi, number dinshi na Nigeria nafara gwadawa amma bai shiga bah
hakan yasa nakira number dinshi na kasar Egypt. Saida nakira sau biyu kafin ana
ukun aka daga muryar mace naji bayan mun gaisane nake tambayanta mai wayar, amma
amsa data bani ne ya matukar gigitani banbari nakarasa ji bah nakashe wayan ina
sakin kuka mai karfi, shikenan bangon dana jingina shima yafadi. Take kwalwata ta
tariyomin maganar matar dake cewa" Allah yayi masa rasuwa sanadiyar plain crash
dasuka samu lokacin da jirginsu yake landing a kasar Egypt"... Nayi kuka sosai
tamkar raina zaifice a jikina kafin na hakura na danganawa Allah lamurana tareda
yima Kehinde addu'ar samun aljannah.

Haka na cigaba da rayuwata ina.rainonki sannan duk bayan wata daya ko biyu nake
zuwa shagon da Kehinde ya ginama mallam Lawal nake karban kudin sannan nasiyo
abubuwan bukata, Hakadai na cigaba da rayuwa nida 'yata saidai lokaci zuwa lokaci
wannan macijiyar data tayani nakuda tana zuwa visiting dina.
Saboda yawan zuwan da takene yasa kuka saba sosai har taka dauraki kan jikinta tana
miki wasa da kanta.

Kinada shekara 10 ne a duniya nasamu wani labarin mai dadi na musuluntar King Ayo
wanda yasa kusan duka mutanen cikin Kingdom din yin mubaya'a, amma duk da haka
banyi tunanin komawa dake ba saboda su Yoruba People duk addininsu da karfin
imaninsu sam basa yada al'adarsu.sannan sunanan Akan bakansu na rashin son auren
wani yare idan ba nasu ba. Ina bibiyarsu ne ta hanyar shafinsu na dandalin sada
zumunta nazamani na Facebook kuma duk wani abu dayake wakana ina sani amma har
izuwa wannan lokaci ban taba samun wani bayani na abbanki ba wanda nakasa
tantancewa yana raye ko ya mutu.

*Cigaban Labarin*

Kuka Eraj takeyi sosai har tana shidewa sam bataga laifin Maama bah a cikin wannan
labarin saima tsantsar tausayinta daya kamata, lallai ita din uwace da kuwa zaiyi
fatan samun irinta. Duk da kasancewarsu a haka amma tabata tarbiyya da ilimin da ko
cikin ahalinta ta rayu bazasu bata kamarsa ba, duk da cewa kuma karatunta online
takeyinshi inda takeyin Islamic classes a *Noor Online Islamic School* sannan
modern education classes a *Learn at home* hatta kwalliya da gyaran jiki duk ta
koyesu online domin labtop guda maamar ta ajiye mata na karatu. Duk wani sha'awar
rayuwa cikin ahalinta ya kau cikin zuciyarta so take ya rayu ita kadai da maamar.

Dakyar maama ta samu Eraj ta daina kukan sannan sukaje suka kwanta kasancewar dare
ya ratsa sosai. Asuba ta gari Maama N Eraj.

A bangaren AbJal kuwa shiri yake sosai na tafiya Jos domin su tattauna da yayarshi
akan matsalan Ummin tasu domin wani lokacin saita dinga abu tamkar bata cikin
hayyacinta.

07048961623*馃尨 BOYAYYEN SIRRI*馃尨


(The Hidden Secret)

*Story and Written By*


*Asmau Bint Abubakar*
*Jasmine*馃尭馃尭

*MANAZARTA WRITTERS ASSOCIATION*馃摎馃枈锔�


*M*. *W*. *A*
_Putting smile on our readers faces_
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp
____________________________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Page 18*

___Sai wajen 茩 arfe uku na rana ya shirya ya nufi Omuapala Royal Kingdom, babu
tazara sosai da inda ya sauka hakan yasa cikin 茩 an 茩 anin lokaci taxi 蓷 in ya iso
dashi inda ya ajiyeshi nesa ka 蓷 an da katafare kuma babbar 茩 ofar mashiga
masarautar. Bayan ya sallami mai taxi 蓷 in ne ya 茩 arasa inda wasu 茩 arfafan mutane
ke sanye da kaya iri 蓷 aya gaba 蓷 ayan su hakan ya tabbatar mai da masu tsaro 茩 ofar
ne, zuciyarshi cike da tunanin yadda zai gamsar dasu su barshi ya shiga.

Isowarshi kusa dasu yayi daidai da isowar wasu tsadaddun motoci guda biyar a jere
duka ba 茩 a 茩 e sa 蓳 anin da tsakiya data kasance kalar ruwan toka, gefe ya raku 蓳 a
gudun kada ya shige musu hanya amma ga mamakin shi bayan wucewar motoci biyun gaba
a maimakon ta tsakiyar tayi gaba sai yaga anyi ribas ta dawo inda yake a tsaye
sannan aka zuge gilashin window na 茩 ofar baya.
Ganin wanda ke cikin motar ne yasa murmushin jinda 蓷 i ya su 蓳 uce mai, bakowa bane
face Kunle 蓷 an uwan Kehinde.
Da sassarfa ya 茩 arasa kusa da motar inda aka bu 蓷 e mishi 茩 ofar.

"Alhaji Bashir ashe dai zan iya gane duk tsayin shekarun nan da bamu ha 蓷 u ba.
Tunda gaba 蓷 aya ka daina zumunci damu gashi mu kuma bamu da address 蓷 inka." Cewar
Mr. Kunle bayan shigar Alh. Bashir cikin motar

"Abubuwa ne suke yimin yawa acan amma yanzu alhamdulillah tunda nasamu transfer an
dawo dani 茩 asata za'a cigaba da zumunci".

"Dama ba anan kake aiki ba? ".

"Ehh wallah a branch 蓷 in AMAAL dake USA nake amma yanzu sun dawo dani Nigeria."

Daidai nan motar tayi parking a farfajiyar aje motoci na 蓳 angaren da suka shiga.
Gabanshi aka cika da kayan ciye 虏 bayan shigarsu cikin main falo wanda aka cika shi
da kayan 茩 yale 虏.
Ganin Mr. Kunle baiyi mai maganar Kehinde bane yasa ya yanke shawarar tambaya shi
bayan sun kammala cin abinci.

"Nikam koh mutumin nawa baya 茩 asar ne". Inji Alhaji Bashir

Cikin mamaki yake kallonshi. Kafin yace

"Baka da labarin abinda ya faru ne."

"Gaskiya bansani ba wani abun ne ya faru."

Fuskar Mr. Kunle ne ta chanja lokaci 蓷 aya damuwa ta bayyana akan fuskarsa, cike da
rashin kuzari yace

"Allah yayi mishi rasuwa 16 years da suka wuce ya samu plane crash a hanyarshi ta
komawa Egypt."

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun." fa 蓷 in Alhaji Bashir lokaci 蓷 aya kuma hawaye
suka fara zarya a fuskarshi tamkar 茩 aramin yaro.

Sun da 蓷 e suna 茩 ara jimamin mutuwar Kunle kafin daga bisani suka mi 茩 e domin isa fa
蓷 ar King Ayo, tun a hanya Alhaji Bashir ke ganin sauyi a tattare da wannan
masarauta kaman ginin masallaci daya gani ga kuma maids da sukayi shiga ta mutunci
ba kamar yadda ya sani ba a da can. Kasa daurewa yayi ya tambayi Mr. Kunle

"Nikam meke faruwa a kingdom din naku ne naga sauyi sosai.? "

Murmushi jinda 蓷 i yayi wanda ya 茩 ara mishi kyau tamkar wani matashi.

"An da 蓷 e da samun wa 蓷 annan sauyukan, tun bayan rasuwar Kehinde ilahirin kingdom
蓷 in suka kar 蓳 i shahada."

"Gaskiya naji da 蓷 in wannan batu sosai Allah ya 茩 aramana imani gaba 蓷 aya."

"Ameen thumma Ameen."

King Ayo yaji da 蓷 in Alhaji Baahir sosai nan aka zauna ana hira wanda yawancinta
abubuwan ilimi ake tattaunawa.

Sai da ya zaga duka sashin manyan gidan sannan suka koma part 蓷 in Mr. Kunle inda
suka zauna da farko.

"Amma batun iyalinka yanzu komai ya daidaita koh.?" cewar Alhaji Bashir 蓷 in bayan
sun zauna

"Dama kasan da batunta ne.?" cikin mamaki inda yasan zancen yake tambayarashi.

"Sosai ma ai shekarun baya tare mukayi hidimar matsalar da Kehinde."

Tashi yayi daga inda yake ya dawo kusada Alhaji Bashir 蓷 in cike da son 茩 arin
bayani yace

"Wace irin matsala kuma.? Yanzu haka fa shekarunta 16 itama da 蓳 ata kuma babu
wanda yasan inda take daga mu har danginta, walau tana raye ko ta mutu."

Shima Alhaji Bashir 蓷 in cike da mamakin furucin shi yace


"Kana nufin baku 蓷 aukota a wannan dajin bane ko me.?"

"Kayimin bayani yadda zan gane Bashir kana nufin kasan inda Aysha take."

"Ehh sosai ma indai Kehinde ya rasu ne kafin matsalolin su kau to tabbas bai samu
daman fa 蓷 awa wani inda take bane, amma ai dani aka kaita wurin da zata zauna ko ba
ita bace tabar nan da juna biyu."

"Itace wallahi tashi muje dan Allah." gaba 蓷 aya ya fice a cikin hayyacinshi jan
hannun Alhaji Bashir kawai yake

Fa 蓷 ar king Ayo ya wuce kai tsaye still hannunshi ri 茩 e a cikin na Alhaji Bashir 蓷
in.

Hanya kawai ake basu ganin tamkar baya cikin hayyacinshi.

"Papa! Papa!! Papa!!!."

Mamaki sosai King Ayo yaji na irin kiran da Mr. Kunle yake mishi domin sunan daya
kirashi dashi tun na yaranta ne kafin yayi wayo domin a yanzu kam duka yaranshi da
jikoki da _Your Highness_ suke kiranshi.

Bai gama mamaki ba yaji ya rungumeshi a tsakiyar Jama'an dake gurin hakan ya
tabbatar mai lallai abin farin cikin daya samu 蓷 an nashi mai girma ne.

"Aysha, Aysha, Aysha." shine abinda kawai yake iya furtawa.

Shima king Ayo a ru 蓷 e ya furta kalmar "Aysha."

Tunawa da inda suke ne yasa shi zaunar da 蓷 an nashi tare da tambayarshi abinda ke
faruwa, gayamai yayi cewa Alhaji Bashir yanada masaniyar inda hakan yasa ya maida
kallonshi ga Bashir 蓷 in cike da son 茩 arin bayani.

Nan dai yafa 蓷 a musu abinda yasani game da lamarin har zuwa lokacin da yayi sallama
dasu ya bar 茩 asar.
Farin ciki, tausayi, nadama tare da dana sani shiya mamaye zu 茩 atansun. Take kuma
King Ayo ya bada umarnin a shirya private jet da sunyi sallar la'asar zasu wuce
garin Bauchi.

Cikin mintuna 茩 alilan labarin ganin Aysha ya zagaye gaba 蓷 aya Kingdom 蓷 in.

Kamar yadda King Ayo ya fa 蓷 a suna idar da sallah tawagar masu tafiya suka wuce
airport bayan sun tsaya a hotel 蓷 in da Alhaji Bashir ya kama ya 蓷 au kayanshi.

Dayawa daga cikin familyn sunso ayi tafiyar dasu amma King Ayo ya hana ganin basuda
tabbacin ganin Ayshan.

Ha 蓷 a 蓷蓷 a 蓷 un motoci ne sukazo 蓷 aukarsu daga masarautar Bauchi bayan jirginsu ya


landing saboda sanar da zuwan nasu da King Ayo yayi.
Nan suka 蓷 unguma izuwa fadar sarkin Bauchi.

Bayan angama gaishe 虏 suka 蓷 an taba abubuuwan motsa baki da aka ajiye musu.
Lokacin ne kuma King Ayo ya samu damar ke 蓳 ewa da Sarki Muhammad Sani sannan ya
bayyana mishi dalilin zuwan nasu, nan suka yanke shawarar barin tafiyar zuwa gobe
tunda yamma tayi.

Shidai Mr. Kunle baiso hakan ba amma dole ya bi umarnin mahaifinshi.


Washegari kuwa tun 茩 arfe goma motocin masarautar Bauchi suka hau kan hanyar zuwa 茩
aramar hukumar Toro ta jihar cikin jagorancin Alhaji Bashir.

Saboda matsawar da King Ayo yayi ne yasa da suka isa basu 茩 arasa gidan hakimin
garin ba wanda ya shirya ma zuwansu kai tsaye hanyar da Alhaji Bashir yanuna musu
suka bi bayan anyi parking 蓷 in motocin.
Yawan shekarun da aka 蓷 auka yasa dakyar ya gano hanyar saboda 茩 arin bishiyoyi da
dajin ya samu.

Gidan yananan kamar yadda ya sanshi saidai yawan shukoki da farfajiyar wajen ya 茩
ara samu.

Dukkansu mamaki ne ya 茩 ara jikasu tare da tausayin yadda mutum zaiyi rayuwa a
tsantsar daji irin haka.
Sun jima nma tsaye daga can nesa da gidan kafin suka 茩 araso.

Turus! Suka tsaya ganin 蓷 akunan a kulle ga tsakar gurin dayayi datti alamun an da 蓷
e ba'a share ba.
Da sauri dogarawan sarki suka share rumfar wajen tare da shimfi 蓷 a 茩 ananun kafet da
suke tafe dashi, har zuwa lokacin kuma babu wanda ya tanka.

Umarni Sarki Muhammad Sani ya bayar akan a 蓳 alle kwa 蓷 on dake jikin 茩 ofofin,
batare da 蓳 ata lokaci ba fadawan suka balle. Sai a lokacin Mr. Kunle da Alhaji
Bashir suka mi 茩 e domin shiga 蓷 akin.

Dakin farko suka shiga wanda babu wasu tarkace a ciki sai babbar katifa 蓷 aya da 拼
an 茩 ananun tarkace, fita sukayi a wannan 蓷 akin suka shiga na biyun.

Kayan aiki na girki ne a gefe 蓷 aya sannan 蓷 aya gefen kuma tarin takardune da kuma
kwandona na sa 茩 a.

Gaban takardun Mr. Kunle ya 茩 arasa tare da 蓷 aukan wani exercise book ya ka 蓷 e
kurar jiki sannan ya duba gaban littafin.
Name:Aysha Adekunle Ayomide
Class: Jss2
School: Learn at home online school

Abinda ya gani a jikin littafin kenan wanda ya 蓷 aure mishi kai domin dai yasan ba
takardun Ayshansa bane, hoton da Alhaji Bashir ya mi 茩 amai ne ya katse mishi
tunani.
Hoton Maama ne da Eraj, murza idanu yayi domin 茩 ara tabbatarwa still abinda ya 茩
ara gani kenan.
Gabas ya kalla tare sayin sujjadar godewa Allah kafin suka fito a 蓷 akin domin nuna
masu King Ayo abinda suka gani.

Ga samu ga rashi, suna murnar gano inda Aysha take gashi basu ha 蓷 u da ita ba, nan
dai aka shiga tattauna yadda za'ayi kafin suka yanke shawarar kiran Barrister
Saleem domin sanar dashi abinda ke faruwa saboda zumu 蓷 i yasa suka manta fa 蓷 a
mishi tun farko.
Magana sukayi da King Ayo wanda nima bansan me suka fa 蓷 a ba.
Shima magana ya ra 蓷 awa Sarki Muhammad Sani kafin suka umarci sauran tawagar dasu
mi 茩 e domin tafiya.

Cikin Bauchi suka koma kai tsaye kuma airport suka wuce domin tafiya garin Abuja
kamar yadda King Ayo ya umarta.
Shidai Mr. Kunle baisan abinda ke faruwa ba domin tunda ya ri 茩 e wannan hoton
baisaki ba illa hawayw da yakeyi yana kallon hoton.

Mintuna 茩 alilan jirginsu ya 蓷 aga zuwa birnin tarayya.


**********************

Kamar koda yaushe su biyu suka fito daga gate 蓷 in makarantar hannunsu ri 茩 e dana
jun.

"Yau fa Granny masa zatayi da miya Bestie kizo muje kawai mu kwashi garar nan
tare." cewar Eraj

"Amma baki da kirki sai yanzu zaki gayamin.* Aymana ta fa 蓷 a tana mai hararta

"Nima da safen nan nake sani kinsan da zan fa 蓷 a miki ai, kawai kizo muje sai a
kira Mummy a waya a gayamata. "

"Amma dai kinsan dole direba zaizo koh, saiki jira yazo na fa 蓷 a mishi tukun inyaso
a 茩 ara kiran Mummy a fa 蓷 a mata." Aymana ta fa 蓷 a.

Saida suka jira direban Aymana yazo kafin suka hau motar gidansu Eraj 蓷 in suka
wuce.

Da gudu suka nufi falo bayan direba yayi parking motar tamkar wasu 茩 ananan yara.
Sam basu kula da tarin motocin dake farfajiyar gidan ba.

Hayaniyar da suka jiyo a falon ba 茩 i ne yasasu nufar gurin domin a tunaninsu ahalin
gidanne a ciki kamar yadda suka saba wani lokacin idan sauran jikokin gidan sunzo
acan suke tarewa.

Eraj ce a gaba Aymana na binta baya tana mata amshin wa 茩 ar da takeyi.

_Ashe o ri mi mo toro ko so_

_All I want is happiness_..

Mutanen data gani a falon ne ya sata tsayawa tare da baza ido tanason gani wanda ta
sani a cikinsu saida bata gane kowa ba illa Kakanninta da Maamarta.

"Muje mana Bestie kin tsaya a hanya idan bazaki wuce ba matsamin ni na wuce." Fadin
Aymana dake bayanta, batare da taga mutanen cikin falon ba.

Kafin ta samu damar bata taji an rungumeta sosai tamkar za'a maidata ciki, hakanan
kuma taji batasan wanda ya rungumeta ya saketa, kusan mintuna biyar kafin taji an
saketa.
茒 aga ido tayi tare da kallon mutumin daya saketan wanda ya sunkuya yayi sujjadar
godewa Allah.

Cikin falon ta 茩 arasa tare da nufar inda Maama take, zama tayi tare da fara gaishe
da mutanen da yaren hausa saidai 茩 alilan daga cikinsu ke amsa.

Hajiya Farida dake gefe ne ta matso da bakinta saitin kunnen Eraj 蓷 in tace.

"Danginsu mahaifinki ne wa 拼 annan sukazo ganinki kuma basajin hausa kiyi musu
yarenku nagado."

Cike da farin ciki ta koma gefensu tana gaidasu 蓷 aya bayan 蓷 aya cikin yara da suke
fahimta.

Nan dai akayita hira tare da neman gafarar Maama akan abinda aka aikata mata.

Tsohuwar soyayyah ce ta motsa tsakanin Maama da Abban Eraj, nan suka wuce garden
din dake cikin gidan aka fara hirar soyayyah.

Ita kuwa Eraj abin nema ya samu tana tare da 茩 annen mahaifinta da King Ayo tana
zuba shagwaba tamkar dama sun saba da juna.

Sai yamma lis sukayk shirin tafiya bayan an tsaida magana zasu dawo nan da sati
biyu domin maida auren iyayen Eraj, cike da kewa suka rabo da juna musamman 蓳
angaren Eraj da takeji tamkar ta bisu amma babu dama tunda sun kusa fara
jarrabawarsu ta chanjin aji.

Bayan tafiyarsu ne Bar. Saleem ya kira 茩 anninshi a waya wato mahaifin Maama, bayan
ya 蓷 auka gaishe da yayan nasa ya fara yi. Cikin basarwa da nuna har yanzu yana
fushi dashi Bar. Saleem 蓷 in yace.

"Na tsaida rana Aysha zata koma gidan mijinta nan da sati biyu, zaka iya gayawa
mutane domin su tayaka 蓷 ebe mata albarka." batare da ya jira amsarshi ba ya katse
kiran.

A 蓷 aya bangaren kuwa Abbu dake zaune a falonshi tare da Ummi da AbJal ne ya mi 茩 e
tsaye daga zaunen da yake ri 茩 e da wayar a hannunshi.

"Yaya, Yaya." ya fa 蓷 a cikin 蓷 imauta saidai jin shiru ne ya tabbatar mishi da cewa
ya katse kiran.

"Meke faruwa ne.?" Ummi ta tambaya

"Ashe Yaya yasan inda Aysha take duk tsawon lokacin nan yanzu gayamin yake wai zata
koma gidan mijinta."

"Ayshana dan Allah da gaske kake karka cemin mafarki nake." Ummi ta kuma fa 蓷 a tana
mai ri 茩 e Abbu gam.

"Da gaske mana tunda gashi ya fa 蓷 a da bakinsa. Ku shirya mu tafi Abuja yanzu nasan
har yanzu fushi yake damu."

*Jasmine*
07048961623

*🌴BOYAYYEN SIRRI*🌴
(The Hidden Secret)

*Story and Written By*


*Asmau Bint Abubakar*
*Jasmine*🌸🌸

*MANAZARTA WRITTERS ASSOCIATION*


*M*. *W*. *A*
_Putting smile on our readers faces._
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp
____________________________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Page 20*

____Kai tsaye gidan Bar. Saleem suka nufa bayan isarsu cikin garin Abuja ƙarfe tara
na dare.
Parking AbJal yayi a harabar gidan bayan mai gadi ya bude musu gate.
Dukkan su suna zaune a falo suna kallon labarai yayinda Eraj ke kwance a dogowar
kujera tayi matashi da cinyar Hajja Farida tana bacci.

Sallamar da sukaji ne yasa suka maida hankalinsu ƙofar shigowa, Hajja ce kadai ta
amsa sallamar shikuwa Bar. Saleem kai ya kauda tare da fadin.

"Aysha shiga ciki ki kwanta kinada aiki gobe."

Babu musu Maama ta mike domin itama batayi maraba da zuwan nasu ba.

Sosai sukayi mamakin canjawar ƴar tasu ganin yadda tayi ƙiba tai kyau tamkar wata
matar hamshaƙin dan kasuwa, Ummi kuwa so take taje ta rungume diyar tata saidai
idon Bar. Saleem ya hanata.

Sosai Hajja ta sake fuska suka gaisa shikuwa a ciki ya amsa gaisuwan da suka mishi.

Hayaniyar da takeji sama sama ne ya farkar da ita tare da tashi zaune daga kwancen
da take tana ƙarewa mutanen dakin kallo, ganin ta tashi ne yasa Bar. Saleem tasowa
daga kujerar da yake yazo ya mikar da ita tare da kama hannunta suka nufi hanyar
dakin daya kasance mallakinta batare da yayi magana ko ya barta tayi ba.

Kaduwa, firgici tare da mamaki suka dirar musu a lokaci guda ganin Eraj din domin
da ba suga shigar Maama ba tabbas cewa zasuyi wannan itace Aysha da suka sani.
Shikuwa AbJal tunani ya shiga na inda yasan yarinyar, nan take mafarkinta da yakeyi
ya dawo mai.

Hajja ta mike tare da nufar kitchen domin sama musu abu mara nauyi da zasuci
kasancewar daga tafiya suke ga kuma dare da yayi, sauran farfesun naman kai da
sukayi ta warming tare da zuba shi a kula sannan snacks da kuma drinks da ta jera
akan tire sai kayan shayi data zuba a cikin wani ƙaramin kwando.

Suna nan yadda ta barsu da alama mamakin bai gama sakesu ba. A dinning ta jere
kayan sannan tazo ta bukaci su karasa domin su ci.

Ummi ce tayi karfin halin tambayarta tace.

"Hajiya Farida wace yarinya ce nagani yanzu ta tashi anan."

Murmushi tayi sannan tace" Allah sarki, Eraj kenan jikar mutanen Ibadan."

Murmushin fuska kawai Ummi tayi domin ta fahimci magana ce Hajja keson fada musu a
fakaice.

"Kina nufin yar wajen Aysha ce.?" Abbu ya tambaya

"Ehh" tabashi amsa a takaice sannan ta cigaba da cewa.

"Ku karasa dinning din kuci wani abu mana sai ku karasa sashin can ku huta bari
nasa Audu mai wanki ya kintsa muku wajen, kai kuma AbJal shugaban gauraye ka karasa
sashin baki ." tafada cike da tsokanan AbJal din.

Murmushi kawai ya mata sannan ya miƙe ya nufi dinning din, ita kuwa Ummi dakin da
taga Maama ta shige ta nufa saidai ko da ta tura kofar a rufe ta jita hakan yasa
cikin rashin kwarin gwiwa suka wuce dining da Abbu.
Bayan sun gama ne suka wuce dayan part din gidan kamar yadda Hajja ta fada musu.

Washegari kuwa tun ƙarfe bakwai na safe Ummi ta iso babban falon gidan domin ta
jira fitowar masu gidan amma a badini fitowar yarta take jira tare da wacce akace
jikarsu ce, saidai hausawa kance idan ka iya sammako wani a tafe ya kwana domin dai
Maama bakwai din ma baiyi ba tabar cikin gidan bayan ta shaidawa Eraj cewa iyayenta
ne mutane da tagani Abbu, Ummi da kuma AbJal.

Toh fa! Ƴa mai kishi uwarta, tunda Eraj taji wannan batu ta daure fuska tare da
kushe zuwan nasu. Saidai Maama ta gargade ta data tabbatar taje ta gaishesu kafin
ta wuce makaranta.

Fitowar Hajja kenan daga kitchen ta tarar da Ummin zaune a falo, gaisawa sukayi
sannan Hajja ta mata ya gajiyan hanya kana ta mike ta nufi dakin Eraj.

Samunta tayi cikin shirin ta na tafiya makaranta tana saka safa a kafarta.
Gaisheta Eraj din tayi cikin fara'a da tsokanarta kamar yadda ta saba.

"Ki fito kiyi breakfast Nuhu ya kaiki yau kakan naki bazai samu kaiki ba tunda yana
da baki." Hajja ta fada.

Tabe baki kawai tayi sannan tace.


"A foodflask zan zuba fa Granny idan naje zamuci da Aymana, nasan itama baci
zatayi daga gida ba."

"Ku koyi yin abu batare da juna ba fa, bazaku dawwama a haka ba musamman ke da kike
da masu daukarki ta ko ina. Ga kakanninki ma sunzo inajin Zaki bisu kaduna kiyi
weekend."
Tace tana mai mikewa.

Itama Eraj din mikewa tayi kana tace.

"Babu inda zan bisu ni, idan ma korata kikeyi to babu inda zani ina nan tare dake.
Idan na tashi tafiya Ibadan din ma tare zamuje."

Dariya kawai Hajja tayi domin wani lokacin Eraj idan tayi wani abu tamkar yarinya
ƴar shekara 5.

Tare suka fito tana rike da hannun Hajjan.

Ƙura mata ido Ummi tayi sosai tana kara ganin tsantsar kamanninsu da Ayshanta.

"Ina kwana." Eraj ta katse mata tunanin da takeyi.

Murmushin jindadi tayi kafin tace.

"Lafiya lau kishiyata kin tashi lafiya."

Da lafiya kawai ta amsa domin bata gane abinda take nufi ba.

"Kiyima Abbunsu magana muyi breakfast anan idan kuma yafiso akai muku can ne sai a
hada muku." Hajja keyiwa Ummi maganar.

"Bari nayi mishi magana a hadu gabaɗaya kawai."


Ta fada tana mikewa.

Yayinda Hajja ta kira AbJal a waya domin ya fito suyi breakfast din.

Bayan gaishe² ne Eraj da Hajja sukayi serving din kowa.

Tea kawai ta zuba kadan a kofi tafara kurba a hankali.

"Ki zuba abinci kici fah kafin na saba miki, idan kuma baso kike yau Nuhu direba ya
kaiki makarantar ba." Fadin Bar. Saleem yana kallon Eraj din.

Shagwabe fuska tayi sannan tace.

"Allah kuwa Granny banajin yunwa ne kuma fa idan naje makaranta zamuci da Aymana,
kayi hakuri ka kaini kaji. Idan ba haka ba fa punishment za'a sani idan nayi
latti."

Murmushi yayi kana yace.


" Ba'a magana fa idan anacin abinci ko ba haka kike cemin ba. Yau nima hutawa zanyi
ga Uncle dinki AbJal yakaiki."

Cike da sha'awa suke sauraron hirarsu yayinda suke fatan su kasance da jikar tasu
da sukeji a yanzu soyayyarta tafi ta kowani jika da suke dashi.

Maida kallonta tayi kan AbJal tace.

"Uncle AbJal kaima an sanka a TV ne."

"Aa ba'a sanni ba nidai ko a radio ma ba'a sanni ba." AbJal ya fada cikin dariya

"Gaskiya bazai kaini ba Granny kaga nayi latti kuma tunda ba'a sanshi a TV ba
punishment zan sha." kamar zatayi kuka tayi maganar.

Dariya sukayi duka kana ya miƙawa AbJal key din mota yace.

"Abdul saukemin ita a British kafin ta kashe min kunnuwa da surutu."

Karbar key din yayi tare da mikewa yana fadin.

"Little Angel ki sami a mota nayi gaba."

Saida yakai bakin kofar fita kafin Eraj ta gama kurɓe sauran shayi tare da daukan
lunchbox dinta.
Kiss tama Hajja a kumatu tare da fadin.

"Tsohuwata mai ran roba na tafi a yimin delicious kafin na dawo."

Kallon Bar. Saleem tayi sannan tace.

"Yau munyi fada Granny sai na dawo zamu shirya."

Da addu'ar dawowa Lafiya suka bita sannan tafi ta da gudu a falon tamkar ƙaramar
yarinya.

Sosai Abbu da Ummi sukaji ba dadi na halin ko in kula da Eraj din ta nuna musu,
✍🏼
saidai sun danganta hakan da kuskuren da suka aikata tunda fari..........

*🌴BOYAYYEN SIRRI*🌴
(The Hidden Secret)

*Story and Written By*


*Asmau Bint Abubakar*
*Jasmine*🌸🌸

*MANAZARTA WRITTERS ASSOCIATION*


*M*. *W*. *A*
_Putting smile on our readers faces._
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp
____________________________________

Hearty Dedicated This Page To Miss CEO🥰 MANAZARTA WRITERS


ASSOCIATION❤️❤️❤️ Can't Heart You Less💗💞💕💖

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Page 21*

....... Tsakanim jini ɗaya dai akace sai Allah, domin dai cikin ƙanƙanin lokaci
Abbu da Yayan shi suka sasanta kansu bayan ya mishi faɗa sosai akan abinda suka
aikata ɗin.
Nan akayita bugawa ƴan uwa da basusan batun dawowar Maama ba aka shaida musu.

Kafin yamma gidan Bar. Saleem ya cika maƙil da ƴan uwa na nesa da kusa, har Afeeyah
da take garin Jos ta hallaro da iyalanta.
Hira aka shiga yi sosai yayinda burin kowa yayi abinda zai birge Eraj da Maama,
ba'a tashi zaman hirar ba saida aka tabbatar an yafewa juna tare manta abinda ya
wuce.

Kwanan su biyu duk suka watse inda aka fara shirye² na komawar Maama gidan mijinta,
inda duka gidajen biyu keta shiri ba kama ƙafar yaro ba ma kamar mutanen Ibadan ba.
Domin haɗaɗɗiyar traditional wedding ake shiryawa tamkar auren fari ne Mr. Kunle
zasuyi.

Mami da Hajja ne suka yi tsaye wurin kimtsa Maama cikin shiri na musamman.

Yau ta kama safiyar laraba inda ranar juma'a za'a ɗaura auren, tuni gida ya fara
cika da ƴan uwa na nesa waɗanda ke kusa ne dai basu ƙaraso ba sai gobe irinsu
mutanen Kaduna domin dai Abbu baiyi kutse wajen cewa akawo shagalin bikin gidanshi
ba gudun kada ya kuma aikata wani laifin ga yayan shi.
Daga gurin ɗaurin auren kuma za'a wuce da amarya da ƴan uwanta garin Ibadan cikin
jirgin da aka tana da domin tafiya dasu.

Eraj ce ta fito cikin shirinta na zuwa makaranta tana gyara zaman jakar dake
bayanta.

Wata wacce take sa'ar Eraj ne daga cikin ƴan matan dake falon a zaune tace.

"A mutu a boko yau ma zakije kenan makarantar kenan.?" ta tambaya ciki da tsokana.

Hajja dake dining tana haɗama Eraj shayi ne ta ɗago ta kallesu kana tace.

"Ai dai tafiku masu zaman banza, bawani abin zaku mana ba amma kunƙi zama a gida
kuje makarantar, ina laifin idan kun dawo daga makarantar ranae Juma'a duk a kawo
ku tunda dai aure kawai za'a ɗaura anan shagalin duk a can garin za'ayi."

"Hajja wai kema kina nufin tafiya zakiyi zuwa Ibadan.?" wata ta kuma tambaya

"Yo me zai hanani zuwa, tunda suka bi al'adun mu ai muma sai mubi nasu. Ta haka ne
za'a ƙara sanin juna sosai har zuwa lokacin da zakiga an janye wannan baƙar aƙidar
na wani baya auren yaren wani." Ta faɗ tana mai miƙa ma Eraj Cup ɗin hannunta
sannan itama ta zauna a kujerar da Eraj ɗin ta zauna.

"Gaskiya tattalin arzikin zai girgiza saboda yawan mutanen da zasu halarci bikin
nan."

"Waya gaya miki.? Garin Ibadan da kewayenta fa a ƙarƙashin ikonsu take, baya ga
hakama su al'adar Yoruba ba kamar namu ban, suna da tsantsar riƙon zumunci da
abota. Duk talaucin da mutum ke ciki idan ya tashi aurar da ƴar shi bashi da
fargabar komi na abinda zai ciyar da mutanen da zasu halarci bikin, wani har a gama
taron bikin a watse bazai ɗora ko butar shayi bace a gidanshi, komai ƴan uwa da
abokan arzikine zasu ɗauki nauyin yinshi." cewar Hajja

"Wallahi ni jikina har kyarma yake wani lokacin, ji nakeyi kamar ranar nan baza
tazo ba. Wata ƴar ajin mu ta taɓa faɗa min fili guda ake barwa kowasu ƴan uwa
najiki kama daga kan yara, ƙanne, yayyu, ƙawaye, Uncles da Aunties duk su baje
kolin fasaharsu a rawa. Shiyasa nake ɗokin zuwa Ibadan ɗin nan musamman nasu daya
kasance na royal family abun zai ƙayatar sosai." Faɗin Amlah da take sa'ar Eraj ƴar
ƙanwar Maama dake Jos wato Afeeyah.

Taɓe baki Hajja tayi tana mai hararanta kana tace.

"Ai idan jikinki baiyi ƙyarma ba sai anyi tunanin rashin lafiya ke damunki, hakanan
ƴan garinku suke ai tamkar jikokin dujjal ba dama kuji kiɗa sai kun taka."

Dariya sukayi gaba ɗaya falon.

"Zan baki mamaki Hajja ranar bikin nan har fili zan shigar dake ki taka." cewar
Amlah

"Allah ya kiyasheni." Ta faɗa tana mai miƙewa domin raka Eraj waje inda Nuhu ke
jiranta.

***************

Zaune yake a office ɗin da aka ware musu na corpers idanun shi a lumshe kamar mai
bacci, sosai zuciyar shi ke azalzala mishi ya bayya na mata soyayyar shi amma ya
kasa saboda rashin ƙwarin gwiwa.

Na farko dai ganin ƙarancin shekarunta ne yasa yayi tunanin bazata fahimce sosai
ba, abu na biyu kuma ganin bai daɗe zuwa makarantar ba gani yake kamar zai jawowa
kanshi abun kunya wajen dalibai dama malaman.
Shawarar dai da zuciyar shi ta daɗe tana bashi ya kuma aminta da ita wato yabari
sai ya gama service ɗinshi a makarantar sai ya bayyana mata kafin lokacin itama ta
kusa yin candy dinta.

Da wannan shawarar ya aminta kana ya miƙe ya ɗau littattafin darasin dazai gabatar
ya fita a office ɗin.

Zaune suke ƙasan wata bishiyar mangoro dake farfajiyar filin makarantar suna cin
abincin da Aymana tazo musu dashi, potato balls ne wanda yaji haɗin nama da ƙwai.

"Aymana amma dai ranar Friday bazamu zo school ba, nagaji da abubuwa da ake ta
gudanarwa bana ciki duk da bawai nasa ba bane." Faɗin Eraj tanamai kai loma baki

Jinjina kai Aymana tayi tare da kyaɓe baki kana tace.

"Kin kai da nisa, daga yau muda zuwa school sai mun dawo daga Ibadan ko kin manta
gobe zamuje wanke kai da saloon ne."

Gyaɗa kai tayi batare da ta kuma magana ba.


Basu wani ƙara jimawa ba aka kaɗa ƙararrawar komawa aji, inda suka miƙe tare da
tattare komatsan su suka nufi class.

*************

Cike da annushuwa yake waya da jikan nashi wanda ya kasance ɗa ne ga yarinyar


ƙanwarshi wato Adesua.

Zaman wayar ya gyara a kunnenshi kana yace.

"Yanzu Muhydeen baza kayiwa kanka faɗa ba ka dawo ƙasarka ka cigaba da aiki itama
ta more ka ba.?"

Cikin zazzaƙar muryarshi ya fara magana a hankali tamkar mai waya da mace.

"Your Highness na gaya maka nan da wani lokaci zan dawo gida Nigeria da aiki, ka
ƙara haƙuri nima lokacin kawai nake jira."

"Toh ya batun aure ko kana nufin haka zamu zuba maka ido muna kallonka."

"Shima a ƙaramin lokaci Your Highness zanyi insha Allah."

"Shikenan kada kabari dai na yanke hukunci da kaina."

Nan suka ƙara taɓa hira kafin suka aje wayar.

Murmushi King Ayo yayi domin shi ya yanke hukunci inhar Muhydeen bai kawo matar
aure ba toh shikam ya zaɓa masa.

*RANA BATA ƘARYA*


_(Sai dai uwar ɗiya taji kunya)_

A yau ranar Juma'a 23/07/2017 aka sake ɗauren auren Ayshat Sa'ad Abdul_Jalal da
mijinta Adekunle Ayomide a masallacin Annur dake wuse a garin Abuja, ɗaurin auren
ya samu halartar manyan mutane sosai kama daga na ƙasar mu Nigeria har waɗanda
sukayi karamci suka taho daga wata ƙasar domin halartar wani ɗaurin aure. Sarakuna,
Ƴan siyasa, Ƴan kasuwanni, Manyan hafsoshin tsaro da dai sauransu.

Kowa so yake ya isa ga King Ayo, Mr. Kunle, Bar. Saleem, Alhaji Sa'ad da sauran
shaƙiƙan masu taron domin a shaida zuwan shi.

Ƙarfe biyu aka ɗaura auran dan haka zuwa biyu da rabi duk anfara tafiya reception
na maza da Bar. Saleem ya shirya a wani katafaren garden daya gaji da haɗuwa wato
_HUSFAT GARDEN_.

Wayyo Allah naira tayi kuka a wannan garden din, abinci babu kalan da babu daga kan
na hausawa, yarbawa, larabawa, da na ƙasashen turawa.
Ko ina ka wulga kawai abinci ne iri daban daban ga nama da aka sarrafashi kashi
kashi.

Anci an sha anyi hani'an sannan aka fara watsewa inda wasu irinasu Vt. Ibrahim
Yahya, Eng. Sulaiman Hassan, Dr. Usman Abubakar, Capt. Ahmad A Musa, Bar. Adam
Idris dama sauran mutane masu zalama ke ta jidar katon katon na drinks da sauran
abincin da ba'a taɓa ba suna sawa a boot. A cewarsu wai zasu rabawa masu buƙata
(amma na cikin su). Lol.

A gida kuwa anata shirye² tafiya garin Ibadan harda ƴan uwansu da sukazo daga
Gombe, duk da Abbu ya su zauna kasancewar duk sun manyanta musamman Iya Ladi da
tafi kuwa zaƙewa amma sunƙi dole aketa shirin dasu.

Su Bar. Saleem kuma sai washegari zasu wuce da tawagarsa.

Ƙarfe 3:45 motoci sukayi ta jidar mutane zuwa airport inda jirginsu zai tashi 4:00
daidai.

Kamar yadda aka tsara ƙarfe hudun jirginsu ya keta hazo zuwa gari mai tarin Ni'ima
Ibadan, tafiyar awa ɗaya jirginsu ya landing.

Abu na manya akace saida harkar girma domin hatta airport ɗin saida aka mishi ado
na musamman. Jirgin na tsayawa wasu maids suka iso tare da shimfiɗa wani lallausa
carfet kalar golden mai azabar kyau tun daga ƙofar saukowa daga jirgin har zuwa
bakin motar da amarya zata shiga.

Motocin da sukazo taryarsu bazasu ƙirgu ba kasancewar su dayawa kuma ga harkar


girma data shigo ciki.

Nan mutane suka ɗunguma cikin motoci aka fara tafiya.

Ta ko ina idan suka wuce ado ne hakan ya kuma tabbatar musu da sunzo fadar girma da
arziki.

Baki sake suke kallon titin da suka shigo wanda a farko kafin shigowar titin akwai
sign board dake rubuce da _This way to Omuapala Royal Kingdom_.

Nan fa mutane suka fara zuba ƙauyanci na ganin kyau da tsaruwar titin tamkar a
✍🏼
ƙasashen waje......

*Jasmine*🌸🌸
07048961623

*🌴BOYAYYEN SIRRI*🌴
(The Hidden Secret)

*Story and Written By*


*Asmau Bint Abubakar*
*Jasmine*🌸🌸

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*


*M*. *W*. *A*
_Putting smile on our readers faces._
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp
___________________________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Page 22*

__Tun daga titin dazai sada mutum da ORK za'a gane tabbas wannan babbar masarauta
ce sannan sun gaji arziki, fasalta tsaruwar ginin wannan fadar ba abu bane mai
sauƙi domin dai wani zaiyi tunanin fadar sarauniyar ingila ne saboda yanayin tsari
da kyawun wajen.

Nan baƙin suka yita zuba santi har lokacin da aka sada su da masaukin da aka
tanadar musu, babban gida ne mai ɗauke da sashi daban daban wanda yake a cikin
Kingdom ɗin.

Bayan sun huta ne kuma aka fara shigo musu da coolers na abinci nau'ika daban
daban, nan suka ware tumbi suka kwashi gara son ransu har saida suka bari.

Washe gari kuwa tun safe aka yi decorating ɗin wajen da za'a gudanar da shagalin
bikin, sosai gurin ya tsaru kamar ba'a gida Nigeria ba.

Ƙarfe huɗu aka fara gudanar da shagalin inda aka fara da buɗe taro da addu'a sannan
jawabin godiya tare da gabatar da manyan baƙi, daga nan kuma aka ba amarya da ango
damar isowa su zauna.

Cikin tafiyar ƙasaita da jan hankali suka fara ratso cikin filin su uku, shigar
kayan yoruba sky blue akayi wa Maama yayinda shima Mr. Kunle kayan shi suka kasance
fari da ratsin skyblue ɗin sai Eraj da aka shirya cikin wata haɗaɗɗiyar dinner gown
fara mai ratsin skyblue itama.

A jere suke tafiya inda suka saka Eraj wacce ke ɗauke da wedding flower a tsakiya,
saida suka fara zagayawa suka gaida jama'a kafin suka ƙarasa ga royal chair ɗin da
aka tanadar musu.

Jawabai aka cigaba da saurara daga mutane daban daban kafin daga nan aka ba ma masu
traditional dance damar shigowa.

Waɗanda suka fara shigowa matasan mata da maza na cikin Kingdom ɗin ne, inda sukayi
shigar su ta al'ada, irin shigowar da sukayi kaɗai abin birgewa ne.
Tsarin yadda suka tsaya a filin shine, a kowani layi mutum huɗu ne, mace a farko
sai namiji a bayanta sannan wata macen sai wani namijin. Freestyle sukayi kowa da
irin tsayuwar sa.

Minti ɗaya minti biyu shiru basu canja daga tsayuwar ba har mutane sun fara mita,
MC ne ya tashi da nufin yin magana saida kafin yace uffan yaji sowa na tashi,
waigawa yayi inda ake sowar domin ganin abinda yasa akeyi, idon shi basu yi tozali
da kows ba sai shahararren matashin mawaƙin nan wato KOREDE BELLO shima cikin
shigar yarbawan da alama sai yazo baje tasa kolin ne.
Bai gama mamaki ba yaji an karɓi mic 🎤 ɗin a hannun shi.

A inda suke jere shima ya tsaya tare da ɗagawa mutane hannu, take kuma DJ ya saki
sauti cikin waƙar One and Only da KOREDE BELLO ya rera, lokaci guda suka fara
takawa inda shi da kanshi yake ƙara rera waƙar ta cikin Mic🎤 ɗin daya karɓa. Waƙar
mai baitin:

_Laye laye laye my one and only oo, laye laye laye, e le lemi oo, laye layelaye._
_Ahhh ife ti aniii ah kogbodo osuno laye, hold me hold onto me, olu mi fe hi temi,
ife ti anni aah kogbodo osuno laye._
_Because today is today that the Lord has made it, and what God join together omo
no to carry go_........
(Loll mai son ji da gani ya garzaya youtube @korede bello ya ganewa idon sa waƙar
one and only.)

Sosai suke taka rawa cikin tsari, dukkansu taku irin ɗaya sukeyi sannan tare suke
juyawa kowani lokacin. Sun daɗe suna cashewa kafin su fita a filin.

Haka dai akayi ta shagulgula har zuwa lokacin da aka bada damar cin abinci, kalolin
abinci sai wanda mutum ke so zaije ya ɗiba komai a wadace, masu zalama kuwa har da
guzuri suka yi.

Sai wajen ƙarfe tara na dare aka gama watsewa daga taron.
Washe gari kuma baƙi suka fara watsewa inda kowa ya tafi da kayan arziki da
souvenirs. Sao dai muyi fatan zaman lafiya mai ɗorewa ga iyayen Eraj.

**********************

*BAYAN SHEKARU HUƊU*

_Abuja Nigeria_.

Kyawawan ƴan mata ne su biyu suka fito daga shagon saloon na _HUSFAT BEAUTY TOUCH_,
ɗaya daga cikin su wacce ke sanye da riga da skirt na atamfa ke riƙe da key ɗin
mota yayinda wacce ke zubi da Deepika Padokune ke sanya da pitch ɗin abaya inda
tayi rolling da da gyalen rigar, hannun ta riƙe da wata tsadaddiyar chain bag.
Kai tsaye gurin wata mercedes benz baƙa suka nufa inda ɗaya buduwar da buɗe musu da
remote ɗin motar dake hannun, batare da ɓata lokaci ba suka shiga tare da tashin
motar suka bar farfajiyar wajen.

"Eraj wai ke baza ki iya cire girman kai ki kira bawan Allah nan ba, haka zaku yi
aure babu fahimtar juna a tsakanin ku.?" cewar Aymana da ke tuƙi hankalinta akan
hanya.

"Kamar yadda yakejin biyayya zaiyi nima haka nakeji, dan haka idan bai neme ni ba
nima bazan taɓa neman shi ba."

"Me yasa tun da farko baki gaya musu bakya so ba."

"Ko nace bana so ma babu wani da nakejin zan iya tsayawa dashi shiyasa kawao na
amince."

"Ni dai ina baki shawara, aure babu fahimtar juna ana samun matsala."

"Za mu fahimci junan ai idan mun tsinci kan mu a ɗaki ɗaya."

Dariya Aymana tayi tana mai kaima Eraj duka kana tace.

"Allah ya shiryaki wallahi, bansan waya koya miki surutu haka ba."

"Zama da maɗaukin kanwa."

✍🏼
Dariya suka kuma yi gaba ɗaya.........

By
Jasmine
07048961623

*🌴BOYAYYEN SIRRI*🌴
( The Hidden Secret)

*By*
*Jasmine*🌸🌸

🖊️
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*📚
*M*. *W*. *A*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


..... Bikin Eraj ne ya taso da ɗan uwanta Muhydeen, dan haka ta kowanne ɓangare
shirye-shirye akeyi sosai. Sai dai duk waɗannan abubuwan da akeyi Ango da Amarya
basu taɓa ganin juna ko magana da juna ba ko da ta waya ne.

King Ayo ne ya haɗa wannan auren bayan ya nemi amincewarsu su duka biyun, da kanshi
ya raba musu lambar wayar juna kasancewar Muhydeen ba a ƙasar yake ba, sai dai har
zuwa yanzu da kwanaki kaɗan suka rage a fara shagulgulan bikin, Ango da Amarya basu
san juna ba.

A ɓangaren Eraj wacce a yanzu take matakin ƙarshe na jami'a inda take karantar Law,
taƙi kiran Angon nata ne saboda aji irin na mata, a ganinta shi ya kamata ya fara
nemanta wannan dalilin ne ma yasa bata damu ta kira sa ba.

Shikuwa Ango ba haka abin yake ba a ɓangaren shi, domin a cewar shi auren biyayya
kawai zaiyi, amma idan ba haka ba a rasa dawa za'a haɗa shi da ita sai wacce ta
girma tsakanin dabbobi. Duk da yasan laifin danginsa ne amma ai sai a haɗa ta da
wani daidai ita ba shi da yake da matsayi da muƙami a idon duniya ba, yana tunanin
ko turanci bata gama koya ba, yanzu ai abin kunya ne ace wai matar dazai aura
batasan ya za tayi magana da turanci ba, shi da kusan gabaɗaya abokan shi ba ƙasar
suke bama bare suji yaran da takeyi, dukkansu a ƙasar waje suke da zama wasu daga
ciki ma larabawa ne da turawa, wannan dalilin ne ya hana shi kiranta domin a
tunanin shi bazata gane abinda zai faɗa, toh idan ya kirata mai zaice mata ne.
Aure dai ya aminta dashi amma yasha alwashin ana gama bikin zai koma inda yafi wayo
yabar musu ita tunda yaji ance karatu takeyi, a tunanin shi dai makarantar yaƙi da
jahilci take zuwa.

************************

Tun saura kwanaki goma biki mutanen Kaduna, Kano, Gombe da Abuja suka wuce Ibadan
domin a fara gabatar da shirye-shirye da su, sun samu tarba mai kyau inda aka ware
musu ɓangare guda da zasu zauna.
Sosai ake shiri tamkar ba'a taɓa aurar da wata jika ba a ORK, masu gyaran jiki uku
aka zube domin su gyara amarya sosai, cikin kwanaki ƙalilan kuwa ta chanja gaba
ɗaya ta koma tamkar wata balarabiya.

Yau saura kwana biyar a fara shagulgula kuma yau ne tawagar ango da abokan sa zasu
iso ƙasar Nigeria, sosai aka shirya tarbar baƙin turawa da larabawan da cimar data
dace ta yarukansu.
Tun ƙarfe 11:00ns suka iso kasancewar tafiyar safiya sukayi, nan aka cika su ta
kalolin abinci.

Suna zaune a babban falon ɓangaren da aka sauke su wanda ke ɗauke da ɗakuna daban-
daban bayan sun gama cin abincin, akalla zasu kai su ashirin ko su fi hakan. Wani
kyakkyawan saurayi ne yace.

"Deen ba zaka kira mana amaryar mu gaisa ba ne."

Shiru wanda aka kira da Deen ɗin yayi kanshi a ƙasa yana danna waya, wani a cikin
su ne ya kuma cewa.

"Na ƙosa na ga wannan gimbiyar da tayi nasarar sace zuciyar Deen."

Sai a lokacin ya ɗago kanshi ya kalle su, wooow shine abinda na furta sakamakon
arba da nayi da kyakkyawar fuskar shi tabbas marabar su da matashin jarumin fina-
finan India Bellamkonda Sreenivas kaɗan ce.
Cikin sanyin murya yace.

"Idan ban kira ba fah."


Nan suka yimai caaa aka kowa na faɗin lallai ya kira musu amarya su ganta.

Shiru yayi tana tunani, domin ba kiran nata bane bayason yi, yana gudun tazo ta
kunyata shi a gaban abokan shi ne, shawara ya yanke zai kira a turo ta amma kafin
tazo zai bar ɗakin domin baisan da wani ido zai kalli abokan nashi ba idan ta
kunyata shi.
Waya ya ciro ya kira ƙanwar mahaifiyarshi, bugu biyu ta ɗauka bayan ya gaisheta ne
yace ta turo amarya zasu gaisa da abokanshi, da toh ta amsa kana ta kashe.

Miƙewa yayi ya fita bayan ya shaida musu tana zuwa, kai tsaye sashin mahaifiyar sa
ya nufa.

A can ɓangaren kuwa Anty Mimi ce ke tsaye tana shirya Eraj cikin wani cotton lace
pitch colour, ɗinkin riga da skirt fitet, da kanta ta mata simple makeup inda
Aymana tayi mata ɗaurin ɗankwali mai kyau, farin gyale da takalmi ta saka sai
ƙaramar purse ɗin ta fara mai kyau.

Ita da Aymana da kuma wasu maids biyu suka nufin sashin da suke, da sallama suka
shiga falon inda musulman cikin su ne kaɗai suka amsa sallamar.

Cikin harshen turanci suka fara gaishe su ɗaya bayan ɗaya, Kamal wanda yake
bahaushe a cikinsu ne yace.

"Larabawan nan fa basa jin turanci, kuyi musu yaren su zasu fi fahimta." ya faɗa
cikin raha.

A zaton Eraj da abinda ya faɗa da gaske ne, hakan yasa ta sauya harshe zuwa larabci
ta fara gaidasu, haka ma Aymana.
Wata suwa Kamal ɗin yayi bayan da ya gama yiwa Eraj video coverage lokacin da take
larabci, kana yace.

"Amma dai a ƙasar larabawa kike zaune."

Dariya Aymana tayi tace.

"Ƙasar larabawan Abuja koh."

"A'a kar muyi haka dake sister, ki gayamin gaskiya a wacce daular larabawan kuke da
zama."

"Da gaske fah, ko sai wanda ya zauna a ƙasar larabawa ne kaɗai yake larabci."

"Gaskiya Deen yayi dacen amarya komai kin haɗa kamar shi, Allah ya bada zaman
lafiya." Inji wani daga cikinsu.

Kamal ne ya kuma cewa.

"Amma idan an gama bikin dake zamu wuce koh.?"

"Ku wuce ina da ita, karatun nata kuma fa.?" Cewar Aymana.

"Ajiye karatun zatayi." Ya faɗa cikin raha.

"Ai idan kuka mana haka baku kyauta ba, sai da tazo shekarar ƙarshe tana gab da
zana jarabawar zama cikakkiyar lauya kuma ku katse ta."

"La'ila ashe da lauya nake zaune shine na saki baki ina zuba surutu."
Dariyar sukayi duka, daga nan kuma su Eraj suka miƙe domin tafiya, Kamal ne ya kuma
cewa.

"Toh amarya sai mun haɗu a wajen taro, ga wannan ku ƙara saboda hidima." ya faɗi
haka yana miƙawa Eraj rafar kuɗi, kanta ta kauda batare da ta karɓa ba, Aymana ce
ta karɓa tare da faɗin.

"Godiya muke, Allah ya saka da alkhairi." nan taja hannun Eraj suka fice.

Bayan fitarsu ne kowa ya fara faɗin albarkacin bakinsa game da dacen da suke ganin
Deen ɗin yayi na matar aure.

Yana kishingiɗe akan gadon mahaifiyar sa kiran Kamal ya shigo wayar shi, batare da
tunanin komai ba ya kara wayar a kunne.

"Guy kazo akwai labari fah, ashe haka amaryar taka take shine baka faɗa mana ba."
cewar Kamal.

Rass! Rass! Kirjinsa ya bada sauti, kada dai abinda yake gudu ne ya faru, kada fa
ace yarinyar nan ta je ta zuba musu shirme ne.

"Baka jina ne."

"Ina zuwa yanzu Mr. Parrot bana son takura."

Cikin sanyin jiki ya miƙe tare da nufar site ɗin da suke, zuciyarshi a cunkushe
✍🏼
yana tunanin da wani ido zai kalli abokan nashi......

By
Jasmine
*🌴BOYAYYEN SIRRI*🌴
(The Hidden Secret)

*By*
*Jasmine*🌸🌸

🖊️
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*📚
*M*. *W*. *A*

A zaune ya same su duka, kowa da abinda yake yi, Kamal wanda ke dakon zuwan shi ne
yace.

"Guy baka da kirki wallahi, shine baka faɗa mana haka amaryar taka take ba, gaskiya
kai kam ka gama dacewa. Matso ka gani har selfie nayi mana tare." ya ƙarasa faɗi da
zolaya.
Zama yayi a kujera batare da ya tanka ba, hannu ya sa ya karɓi wayar da Kamal ɗin
yake miƙo mai.
Hoton farko Eraj ce a zaune tana murmushi dimple ɗinta ya fito sosai, yayinda
Aymana ke tsaye ta dafa kafaɗar ta alamu magana takeyi da wani domin sam hankalinta
baya kan Camera ɗin, haka duka sauran hotonan suke kuma duk tare aka ɗaukesu
shiyasa bai gane wacece Eraj ɗin ba.
Miƙawa Kamal wayar yayi batare da yace komai ba.

"Ai baka gama gani ba, ga video ɗin da na mata lokacin da take larabci, ashe
balarabiyar baturiya zaka aura." cikin raha yake maganar.
Ƙura ma wayar ido yayi babu ko kyaftawa lokacin da yake kallon video ɗin, sosai
yaji ta burge shi, lokaci ɗaya kuma zuciyarshi ta cushe cike da haushin kanshi
wanda ya rasa meye dalili.
Wayarsa ya zaro tare da tura hoton sannan ya goge na cikin wayar Kamal ɗin.

"Malam ya haka.?" cewar Kamal bayan ya karɓi wayar.

"Banga dalilin da zaka ajiye hotonan matata a wayar ka ba."

"Sannu wanda yafi kowa kishi."

"Naji dai ai halalina ce."

Hira suka cigaba da yi duk akan yadda bikin zai kasance, sai la'asar kafin wasu
daga cikinsu suka miƙe domin sauke farali.

💦💦💦💦💦💦💦💦

Washegarin da za'a fara gudanar da shagalin bikin ne ango ya samu damar ganawa da
amaryar tashi, yana zaune a wani ƙasaitaccen falo yana jiranta bayan ya aika da
saƙon son ganin ta.
Hannunta ɗauke da faranti ta shigo wanda ke ɗauke jug da cups sai fruit salad da
snacks a gefe, ido ya ƙura ata ko kyaftawa bayayi har baisan lokacin da ta iso
gaban shi ta ajiye farantin ba, zama tayi a kujerar dake fuskantarshi kana tace.

"Ina wuni." cikin sanyin murya.

Tasowa yayi daga kujerar da yake ya iso gabanta ya zauna tare da riƙe kunnuwanshi
biyu yace.

"I'm sorry for everything, ayimin afuwa Mrs. Deen."

Kyakkyawan murmushi tayi kana tace.

"Anyi maka uzuri."

Shima murmushin yayi, a hankali ya cigaba da janta da hira, lokaci kaɗan suka saba
tamkar wasu daɗaɗun masoya.
Sun jima suna hira kafin ya barta ta tafi dakyar saboda nemanta da akeyi a cikin
gida, sannan shima ya miƙe ya nufi wurin abokan shi.

Bazan iya fasalta muku yadda bikin ƴaƴan gatan nan ya kasance ba, amma tabbas anyi
shagali sosai, naira tayi kuka tamkar a ƙasa ake tonota, mutane kuwa sun sami
kyaututtuka na souvenirs babu adadi.
Bansan ya akayi ba amma dai naga amarya da ango sun haɗe kansu tamkar Romeo and
Juliet saboda so da tarairayar juna da suke yi tun bayan da suka gana da juna.
Biki yayi biki, Alhamdulillahi anyi taro lafiya an gama lafiya sai fatan zaman
lafiya ga ango da amarya.

🤰🤰🤰🤰🤰🤰🤰🤰

Zaune take tayi daidai a tsakar kayataccen falonta wanda yaji kayan alatu na more
rayuwa, tana sanye ne da armless shirt pink wacce ta bayyana karamin cikin da take
dauke dashi sai wando three quater fari data sanya. Plate ne a gefenta wanda ke
dauke da yankakkun fruits tana cin shi da fork lokaci zuwa lokaci yayinda rabin
hankalinta ke ga jaridar da take karantawa.

Sallamar da akayi ne yasata dagowa tare da maida hankali kan kofar shigowa,
tattausan murmushi tayi tare da kokarin mikewa.

"Kada ki wahalar min da baby basai kin taso ba."


"Ladan ne bakaso na samo.?" Ta tambaya cikin shagwaba.

"Wane ni banaso ki wahala ne kawai."

Zama sukayi tare akan kujerar inda ta zauna akan kafafunshi.

"Ka dade ka barni ina ta kewarka."

"Sorry Cherie kinji, nafara mana shirin tafiya Nigeria ne."

"Da gaske Cherie"

"Ehh inaso ayi komai damu ne tunda bikin aminiyarmu za'ayi."

"Kamar kasan dazu Aymanan ta kirani tanamin korafin yaushe zamu taho yau biki saura
2weeks. Amma idan an gama bikin acan zaka barni har sai na haihu ko."

"Haba Eraj din Maamanta, bazan iya barinki a wani waje alhalin ni bana nan ba."

"Na missing din gida sosai musamman forest life dina."

"Kada ki damu Baby a forest zamuyi honeymoon tare da babyn mu,shima yaji abinda
Mummyn shi taji da take yawan kewar forest din nan."

"Inasonka habibi."

"Nima haka habibaty." Ya fada yana mai daukarta suka shige bedroom.

Sati na zagayowa suka wuce Nigeria domin halartar bikin Aymana da za'ayi da corper
din su na makaranta wanda a yanzu yake aiki da wani babban company a Abuja
Nigeria...

*TAMMAT BI HAMDULLAHI, NAN NA KAWO KARSHEN LITTAFIN BOYAYYEN SIRRI THS. KURAKURAN
DANAYI A CIKI ALLAHINA ROKON KA YAFEMIN, ABINDA NA RUBUTA DAIDAI ALLAH KABANI
LADARSA.*

*GODIYA TA MUSAMMAN*.

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION._

_JASMINE'S NOVEL LIBRARY._

_RUKHSANA FANS CLUB._

_RAHAMA'S NOVELS PALACE._

*BAZAN MANTA DAKU BA*.

_BINTA UMAR ABBALE._(CEO MWA)

_XAYYEESHERTHUL HUMAERATH._(CEO NWA)

_MHIZZ JIDDERH._(JJ LUV)


_ABUBAKAR SADID ALQURAYME._ (ABBANA)

KUNA DAYAWA BAZAN IYA AMBATON KU DUKA BA, ALLAH YA SAKA MUKU DA ALKHAIRINSA YABAR
ZUMUNCI A TSAKANIN MU.

You might also like