0% found this document useful (0 votes)
48 views172 pages

Kazamar Gida Complete-1

Jafar, a husband frustrated with his wife's lack of cleanliness and cooking skills, confronts her about her negligence in maintaining their home. Despite his anger and disappointment, he still harbors feelings for her as she is his wife and relative. The narrative explores the tension in their relationship, highlighting Jafar's internal conflict and his interactions with others, including a young woman named Ladi, who contrasts with his wife's behavior.
Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as DOC, PDF, TXT or read online on Scribd
0% found this document useful (0 votes)
48 views172 pages

Kazamar Gida Complete-1

Jafar, a husband frustrated with his wife's lack of cleanliness and cooking skills, confronts her about her negligence in maintaining their home. Despite his anger and disappointment, he still harbors feelings for her as she is his wife and relative. The narrative explores the tension in their relationship, highlighting Jafar's internal conflict and his interactions with others, including a young woman named Ladi, who contrasts with his wife's behavior.
Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as DOC, PDF, TXT or read online on Scribd
You are on page 1/ 172

afar yana tsaye a tsakar gidansa bayan ya fito daga

wanka ya kulle bandakin da mukulli wanda ya maidashi


wajen shigarsa shi d'aya domin hatta matar gidan bai
barinta ta shiga.
Gidan yake k'arewa kallo, rike yake da k'ugunsa.
Alokacin bai wuce goma na safe ba amma har lokacin
matar gidan bata da niyyar motsawa daga shimfida tun
bayan daya matsa mata tayi sallar asuba ta koma gadon
bata k'ara juyi ba ballantana takai ga tashi. Ya kai
kallonsa ga tukunya wacce ke cike da sauran abinci tun
na shekaranjiya,gasauran kayan wanke wanke nan da ta
bada wankinsu ga almajiri har ruwa ya dakesu sunyi
k'ura bata kwashesu ba. Cikin bakin ciki yakai dubansa
inda ta tula uban shara har ya cika dustbin yana zuba,ga
wani danko danko da k'asan gidan yayi wanda ke
tabbatar da ba a wankeshi sai iyakar abunda ruwan
sama ya wanke.
Ya girgiza kansa kawai ya ja kafarsa zuwa falon. Ko
yunkurin cire takalminsa baiyi ba hakanan ya taka kafet
din ya nufi dakinsa. Sai alokacin ya iya sauke numfashi
mai dad'i,wani k'arni falon yakeyi wanda shiyasa sam
bai kaunar matarsa tayi girki da kifi duk kuwa sanda tayi
toh zaman falon ya gagareshi kenan. Daman ya take a
kazanta ballantana ace tayi aikin kifi. Ranar babu zaman
falon.
Gaba daya Jafar bashi da inda zai zauna yaji sanyi a
gidansa daya wuce dakinsa. Duk da dakuna hud'u ne a
gidan da katon falo guda daya sannan bandaki har uku
ne amma kazancewarsu bazai bari ko kusa mutum mai
tsafta yayi marmarin shigarsu ba. Dakinsa da kanshi
yake gyarawa ya sanya turaren tsinke,wani lokacin idan
yaga lokacin kasuwa zai kure sai ya gyara gadonsa ya
kulle ya tafi da mukullin idan ya dawo yayi sharar tunda
yasan koda yabar mukullin bazata gyara ba saima ta
shige dakinsa ta kwanta ta k'ara hargitsa gadon a
cewarta duk gidan babu inda tafison kwanciya sai dakin
nasa.
Saida ya gama shirinsa tsaf ya sanya takalmansa
sannan yayi duba ga matarsa dake sharar bacci babu
abunda ya dameta. Cikin bakin ciki ya daki cinyarta da
karfi,a firgice ta farka tana susa,kallon rain in wayo ta
hau yi mishi. Shima harararta yakeyi
"Tashi ki koma dakinki zan fita na makara."
Ta ja tsaki tana wani marairaice murya irin ta masu
bacci
"Haba jafar(sunansa take kira kai tsaye),meye hakane?
Ka dauki alhakina wallahi."
Bai iya cewa komai ba,kayan daya cire ya shiga linkesu
ya ajiye a saman akwatinsa. Ta mike tsaye tana gyara
zaman zanin da tasha aikin girki dashi na dare har
lokacin shine a jikinta.
"Ai na tuna,gwara daka tasheni. Ashe yau suna muke
dashi a hotoro. Anti amina ai kasan ta haihu ko?"
Jafar dai gadonsa ya gyara tsaf ya jera filo. Jin da tayi
baice komai bane ta kara matsowa tana goge miyan
bacci
"Wai jafar bakaji bane?"
Sai lokacin ya dago ya dubeta,gaba daya tasha jinin
jikinta ganin yanda ya hade rai tamkar wanda aka
aikomasa da sakon mutuwa.
"SIYAMA!!!"
Ya kira sunanta a fusace. Ta turo baki don tasan sauran
zancen,fadan nan dai data tsana zaiyi. Ba tare data
amsa ba ta kauda kanta gefe.
"Siyama ke wace irin jinsi ce? Anya zan yarda ke din
mutum ce kamar sauran mutane? Na soma tsorata ni
Jafar kodai aljana na kawo gidana! Bakisan abunda ya
dace ba siyama, na soma yarda kanki ba daya bane!
Banda haka! Na tashi ko gaisuwar arziki ban samu
awajenki ba! Ke baki iya ki tashi ki taimakamin da ko
abin karin kumallo ba bayan kina sane cewa ba zama
zanyi gidan ba zan fita neman kudi ne. Kin kwanta
tamkar mai baccin mutuwa sai bacci kike shararawa!
Yanzu kuma daga tashinki don son ki kara tabbatarwa da
mutum ke cikakkiyar mara tunani ce shine har kike da
bakin tambayata fita unguwa! Toh wallahi muddin kika
sa kafarki kika fita daga gidan nan sai na sab'a maki
Siyama! Saikin raina kanki wallahi. Sannan wallahi na
dawo na sami gidan nan yana wannan tashin karnin sai
kinsan namiji kike aure ba wanda ya rako maza ba. Ga
shara can zan turo maki almajiri ki hadamishi ya zubar
ya wanke dustbin da parker din. Fita ki bani waje zan
rufe dakina."
Siyama ta riga ta gama kaiwa bango,a fusace ta fita
tana mai buga kofar da karfi. Har iska tana kad'o labulen
dak e jikin windon d'akin. Jafar ya girgiza kansa bakin
ciki goma da ashirin suka tarar masa. Ko shekara basu
rufa ba da aure amma matsaloli sunfi adadin kwanakin
dake cikin shekara guda yawa. Ya dauki wayoyi da
mukullin mashin dinsa ya fito. Gam ya rufe dakinsa da
mukulli ya jefa a aljihu ya fito. Tamkar zaiyi amai yakeji
dakyar ya shiga dakin nata.
Tana zaune ta hade rai,wayarta a hannu da alama kira
takeson yi. Ya bi dakin da kallo ya yamutse fuska,daki
duk tarkacen kaya babu inda mutum zai zauna yaji
sanyi. Bai damu da kallon da take watso mishi ba ya jefo
mata dari biyar
"Gashi sai dare zan shigo kada kisa girkin rana dani."
Da sauri ya fice domin ya gaji da jin warin dake busowa
ta bandakinta wanda ke a wangale.
Ya ja mashin dinsa waje ya rufe mata kofa.
Ihun kukan bakin ciki siyama ta sanya,banda Allah Ya
isa ba abunda take jerowa Jafar. A ganinta ai ya cuceta
ace matar yayanta guda ta haihu,haihuwar ma na fari
amma yace babu inda zataje.
Batayi wata wata ba ta lalubi lambar yayarta rumaisa ta
danna mata kira.
Ringing biyu,ana uku ta amsa.
"Hello siyama ya dai? Kin fito?"
Siyama ta ciji lebbanta,hawayen bakin ciki suka k'aru
"Ina fa! Jafar ya cuceni anti rumaisa,yace babu inda
zanje."
Rumaisa ta runtuma ashariya
"Amma jafar dan kaza kaza ne! Banda ya rainawa
mutane hankali yaushe akayi auren naku sannan duka
duka fitarki nawa ne da har zaice kin fiye yawo bazakije
ba? Yanaso ya soma raba zumunci tun ba'aje ko'ina ba?
Wallahi bai isa ba,rabu dashi bari na yiwa Hajiya
magana."
Siyama ta tare ta da sauri
"A'a don Allah anti rumaisa ki rabu dashi kawai. Na
amince bazan fita ba tunda yace zai dauki mataki
muddin na yarda na fito bada izninsa ba."
Rumaisa taja tsaki
"Banza uwar son miji,sai kiyita zama kin kare a haka
jafar yana juyaki. Ki buga ki bawa aminar hakuri,amma
tabbas ya dace ki tashi tsaye ki kwaci y'ancinki don
wannan ba yi bane!"
Daga haka rumaisa ta yanke kiran. Siyama ta sharb'i
kukanta har bataji sadda almajiri yayi ta kwada sallama
ba. Saida ta nutsu sannan taji. A fusace ta fito
idanuwanta cike taf da bala'i
"Wai lafiya ka ishi mutane da sallama? Menene?"
Yaron yace
"A'a maigidan ne yace nazo wai zan kwashe shara."
Ta harareshi taja tsaki,shi dai yaro duk ya firgita kada ta
kai mishi duka. Ta nuna inda dustbin din yake
"Ai gashican,kaje kayi ta kwasa."
Daga haka tayi dakinta ta rufe kofar ta soma kiciniyar
yin wanka saboda tsamin jikinta ya soma isarta. Idan
bata mance ba rabonta da wanka tun safiyar jiya da
Jafar ya matsa da bukatarsa,dolenta kuwa tayi wankan
da babu niyya ba don haka ba yanda a kwana biyun nan
takejin sanyin gari bazatayi ba. Ita kam tak'i jinin wanka
da ruwan sanyi kamar yanda take jin kasalar d'ora
ruwan zafi a risho.
Jafar kuwa tunda ya zauna a shago cikin kasuwa ya
kasa maida hankali sosai kan sana arsa. Tunaninsa
kacokam yana ga wannan muguwar halayya ta Siyama
wanda yake neman hanyar kawo karshenta. Toh kodai
'yar aiki zai nema mata ne? Saidai kuma ta yaya? Domin
tun farko saida ya nemi hakan a wajenta ta hayayyako
masa,wai ita sam bata son 'yan aiki nan da nan sai su
kwace maka miji su barka baki hangame. Karshe tace
tafison almajiri ya barta duk da dai hakan bai kwanta
masa ba sai don su zauna lafiya. Duk da d'abi'un
Siyama,yana sonta matuk'a. Y'ar uwarsa ce kuma
matarsa,ta yaya zai k'i d'iyar kanin mahaifinsa? Bayason
kai k'ararta kada ayi mishi kallon marar hakuri ace ko
shekara bata rufa ba ya soma k'orafi.
"Jafar wai yau lafiya kake?"
Ya dago kansa ya dubi abokin aikinsa,Ibrahim.
Murmushin yak'e yayi
"Lafiya,kaina ke d'an ciwo."
"Allah Ya sauwake toh."
Ya amsa da amin. Ya tuno a matsalarsa har da
yunwa,dole ya mik'e ya shiga cikin kasuwa don ziyartar
Ladi mai abinci. Yana son cin abincinta,gata dai
k'aramar yarinyar da bata fi shekaru goma sha shida ba
amma akwai tsafta hakanan abincinta zakaci shi lafiya
lau. Sam,bata da hayaniya irin ta sauran masu siyar da
abinci.
Tare sukeyin aikin dahuwar da mamanta,saidai kwana
biyu Maman babu lafiyar jiki,ladi keyi.
Har nauyi yakeji ace da m atarsa amma yana cin abinci
a waje duk saboda rashin tsaftar muhalli da rashin gyara
tukunya. Ladi har ta sanshi sosai saboda babu ranar da
baya zuwa shagonsu cin abinci.
Tunda ya shiga shagon ta hangoshi. Ta sakar masa
murmushi adaidai lokacin da take ajiye kwano taf da
abinci agaban teburin wasu. Ya maida mata martanin
murmushin kafin ya maida hankali kan wayarsa.
"Assalamu alaika. Barka da zuwa yayana. An iso lafiya?
Ya antina?"
Wani sanyi ya kwanta luf a zuciyarsa,abunda ya gaza
samu kenan a gidansa. A rayuwar Jafar yanason a bashi
girma muddin ya zamana ya girmewa mutum koda da
mintoci ne. Shiyasa Ladi take burgeshi,murmushi ya
k'ara sakar mata alokacin da yake amsa sallamarta.
"Wa alaikissalam 'yar nijar. Lafiya lau nake,ya jikin
mama?"
Ladi wacce har lokacin murmushi bai kaura daga kan
fuskarta ba ta bashi amsa
"Mama ai ta samu sauki sosai,mungode Allah. Watakila
ma gobe ka ganta tazo. Ai tana yawan tambayarka
kasan bata mance manyan customers d'inta."
Yayi 'yar dariyar yak'e saboda kunyar da yaji,kenan dai
har an sanyashi layin manyan customers? Hum! Siyama
ta cuceshi. Ladi ta katse mishi tunani
"Bari na hado maka abincin."
Tayi gaba ba tare data jira abunda zai umarci a
kawomasa ba. Toh menene bata sani ba tunda ba yau
ne ya soma zuwa shagonsu ba?
Minti biyu sai gatanan da saurinta,hannunta dauke da
kwanukan abinci ta ajiye agaban teburinsa. Lafiyayyen
tuwo ne da miyar danyar kub'ewa yaji nama da ganda
sai daddad'an kamshi ke tashi. Kallo d'aya ya yiwa
abincin babu wata wata ya soma ci bayan ya wanke
hannu da ruwan data ajiye.
Yana ci yana tunanin inama ace haka Siyamarsa ta iya
dahuwa,inama tana da tsafta koda rabin ta Ladi ce.
Yunwar daya kwaso ne ya mantar dashi inda yake,
hakan yasa bai dago ya kalli kowa ba har saida ya
kammala cin abinsa. Rabonsa da abinci tun jiya da rana
dayazo shagon Ladi ya narki shinkafa da miya mai d'an
karen dadi. Koda ya koma gidan da dare,bai iya cin
abincin Siyama ba saboda k'arnin kifi dake tashi.
Ladi kuwa tana wanke kwanuka saidai rabin hankalinta
yana ga Jafar. Tana tausaya masa sosai. Bata mantawa
a baya kafin Jafar yayi aure,ya kasance mutum ne mai
yawan wasa da dariya. Sukanzo harda abokan
kasuwancinsa su ci abinci a shagon har ma su jima suna
hirarsu kafin su tattara su koma cikin kasuwa. Saidai fa
ba sa ido ba,ta fahimci Jafar na baya dana yanzu sun
bambanta matuk'ar gaske. Wannan Jafar din ya
rame,bashi da wasan nan,dariyarsa bata tsawo. Idan
yazo daga gaisuwa ba abunda ke shiga tsakaninsu. A
zaton Ladi,aure ai yakan chanja rayuwar mutum daga
bakin ciki zuwa farin ciki saidai auren Jafar ba haka
yake ba.
Bata da hujjar cewa ba auren soyayya yayi da anti
siyama ba,don ita shaida ce akan yanda yake zuzuta
siyama a gabansu. Har suyita dariya ita da mama. Hatta
hotunan siyama ya tab'a nuna mata don har gajiya tayi
ta mik'a masa wayar ganin sunk'i k'arewa.
Duk da bata shiga hurumin da bai shafeta ba,saidai yau
kam taci d'amarar tambayar Jafar matsalarsa. Haka
kawai tana jinsa tamkar wani yayanta musamman daya
kasance bata da wani d'an uwa babba ko k'arami. Ita
kadai ce wajen mamanta. Don haka ta kife kwanukan a
kwando,ta gyara zaman hijabinta ta nufi inda Jafar ke
zaune yana kora ruwan lemo a cikinsa...
Xaki debo ruwan dafa kanki...Kujera taja ta zauna tana fuskantarshi saidai kuma
idanunta yana ga kwanukan abincin daya cinyeshi
tas tana kallo cike da mamakin yanda mutum
magidanci kuma sabon aure irin Jafar ace har zuwa
yanzu bai bar ziyartar shagunan abinci ba. Ya katse
mata tunaninta
"'Yar nijar abincinku yana k'ara dad'i koyaushe. Ai
na dauka Mama ce karfin girkin sai yanzu na
fahimci kema gwanar iyawa ce bayan kauracewar
mama daga shagon."
Tayi dariya ta jinjina kanta
"Kaji fa yayana hum,nasan duk iya girkina ai bana
kai antina ba ko?"
Yaji kamar da gayya tayi mishi tambayar. Kawai ya
basar kamar baiji ba. Hannu yasa a aljihu ya ciro
kud'i ya mik'a mata.
"Gashinan a ajiyemin d'an waken nan da rana zan
lek'o."
Ganin zai mike tayi saurin magana
"Ni kuwa yayana inason tambayarka."
Jafar ya koma ya zauna yana mai fargabar
tambayar da Ladi zatayi mishi duk da dai yasan ita
d'in yarinya ce wacce tasan ya kamata saidai
bayason tayi mishi tambayar abunda ya shafi
iyalinsa. Ai fa ta dauko hanyar hakan.
"Yayana na fahimci kana tattare da damuwa. A
kwanakin nan walwalarka ta ragu sosai,hirar nan ma
da kake d'an yi ka bar yinsa."
Jafar ya tsayar da dubansa ga Ladi,akwai ta da
saurin fahimta. Ya daure ya k'ak'alo murmushi
"Ke kam 'yar nijar ba dai fahimta ba. Kwana biyun
ne banjin dadin jikina wannan shine babban dalilin
chanjawata."
Ladi ta rausaya kanta ko kad'an bata yarda da
zancen Jafar ba.
"Ina mai baka shawara akan ka dunga kokarin
danne damuwarka ko don saboda mutane. Yanzun
nan sai su soma zargin wani abu daban wanda bai
zamto damuwarsu ba ,hakanan zasu sanya maka
idanu. Addu'a takobi ce ga muminai,matukarzaka
juri yinta toh ina mai tabbatar maka komai na
rayuwarka zai tafi daidai. Allah Ya magance mana
matsalolinmu gaba daya."
Daga haka ta mike ta had'a kwanukan bayan ta jefa
kud'in a aljihun Apron d'inta.
Anan zaune ta barshi yana binta da kallon
mamaki,zantukanta sun nuna lallai bata yarda da
hujjar daya bata ba. Ya zaiyi toh? Koda ace k'arya
bata daga cikin halayensa hakanan dai yake koyon
yinta ba don yaso ba. Ai abun kunya ne ma ace ya
soma fadin matsalar gidansa tun bai shekara da
matarsa ba. Maganar Ladi ta shigeshi sosai ya
k'udura a ransa dole ya rage zuwa shagon saboda
lallai batayi k'aryar ba, mutane sun soma gulmarsa
har akwai wani cikin abokan kasuwancinsu ya taba
jifansa da magana akan yayi aure bai bar kwasar
k'afa yawon bin abincin siyarwa ba.
Dakyar ya mik'e ya koma bakin aikinsa. Da ranar
ma bai iya dawowa yaci ba saboda nauyin da yakeji
akan maganganun Ladi.
Auren mace irin Siyama bashi da riba. Me za'ayi da
KAZAMAR GIDA?
********************
Jafar bai shigo gidansa ba sai k'arfe takwas na
dare. Zuciyarsa shige da fargaban kalar kazantar da
zai tarar. Ya faka mashin d'insa ya rufeshi sannan
ya shiga ciki.
Inji ne yake ta aiki,ya duba yaga an kawo wuta ya
chanja hanyar. Ya kashe injin,da gudunta ta fito
daga d'akin
"Wa...?" Ta fasa k'arasawa ganin Jafar ne. Tsaki
taja ta koma d'akinta. Jafar takaici ya isheshi,yakai
dubansa ga tsakar gidan,babu laifi tayi shara saidai
ba'a wanke dustbin d'in ba. Kaca kaca yake
jikinsa,yakai dubansa ga kayan wanke wanken. Bata
dauke ko cokali ba,saima wasu kayan da aka k'ara
lodasu a bakin makwararar ruwa. An wankesu an
barsu anan. Cikin fusata ya bita cikin d'akin. Babu
laifi falon domin k'arnin ya tafi sai abunda ba'a rasa
ba. Ga kayanta nan wankakku kwanansu biyar
kenan da kawosu daga wajen mai wanki amma
Siyama bata da niyyar maidasu mazauninsu.
Kansa yaji yana sarawa,ya dubeta. Shimi ce a jikinta
wacce daga kalar fara ta koma ruwan k'asa tsabar
datti,sai wani shegen dogon wando marar kyawun
fasali data sanya,kwakwa take b'antala da
hak'orinta. Tana ci hankalinta yana ga kallon wani
film na turawa.
Yasa hannu ya kashe socket din gaba daya ta jikin
bango kafin ya k'ara maido dubansa gareta. Kafin
yayi magana ta rigashi
"Haba Jafar,wai menayi maka ne? Wace irin tsana
kayimin da kake kokarin hanani sakewa a gidan
nan? Tun safe kake nemana da fitina ina kyaleka!
Wannan wace irin rayuwa ce! Matukar zaka cigaba
da musgunawa rayuwata bazan fasa gasa maka
magana ba!"
Siyama ke maganar a matukar fusace,da alama dai
tun safe tana kullace dashi. Tana kaiwa aya ta nufi
hanyar d'akinta tun batayi taku uku ba taji ya
damkota ya yo baya da ita. Nan ta zube akan
kujera. Ta dubeshi cike da masifa,da sauri ya tareta
cikin kaushin murya
"Idan kika k'ara cewa uffan siyama! Saina yi maki
dukan kawo wuk'a naga wanda zai kwaceki!"
Ta maida bakinta tayi shiru tana huci,tuni ta soma
kuka ita kam batasan Jafar mugun mutum bane sai
bayan aurensu. A baya tana daukarsa mutum mai
sanyi ashe dai munafuntarta yayi sai yanzu take
gane ainahinsa.
Cikin d'aga murya Jafar ya soma magana
"Siyama baki da hankali! Nace baki da hankali! Babu
ranar da zaki dawo hayyacinki sai nakai ga fallasa
irin rayuwar kuncin da nakeyi dake a wajensu Abba!
Nasan shi kad'ai ne zaiyimin maganinki! Dubi kayan
can Siyama(yayi mata nuni da yatsa)
,kwanansunawa ajiye anan?! Kiyi duba da suturar
dake jikinki! Haba siyama! Kin shayar dani mamaki
kwarai dagaske!
(Yaja hannunta da karfi zuwa tsakar gidan)
"Wa kike jira yazo ya adana maki kayan can a
kicin?? Wane bawa kika ajiye? Meyasa kika
bambanta da sauran mata ne? Ana batun kazaman
mata ban tab'a cin karo da KAZAMA irinki ba
Siyama! Kyawunki ya tashi a banza! Ina yi maki
kallon wacce tafi kowa iya k'ure adaka a baya ashe
kyalkyalin banza ce ke! Ni Jafar ba kazami bane
inason tsafta da mai yinta! Ina gaggauta baki
shawarar ki gyara idan kuwa bazaki gyara ba lallai
ki sani zan fayyacewa Abba irin zaman da mukeyi
dake!"
Yana gama fad'in haka ya bud'e d'akinsa ya shige.
Gaba daya ransa yana k'una,ya rage kayansa ya fito
da niyyar shiga wanka. Tana nan har lokacin a
durkushe tana kuka,ko kallonta baiyiba.
Gaba daya abun ya isheshi,kodayaushe ace mutum
da gidansa amma yana fargabar shigowa saboda
bai san kalar kazantar da zai riska ba? Ya ja tsaki
alokacin da ya fiddo k'ullin namansa a ledar da tun
shigowarsa take a hannunsa. Zama yayi yaci ya
koshi yasha ruwa. Sai a sannan ne nutsuwa ta zo
mishi,don har ga Allah a fusace ya shigo gidan.
Yana son Siyama saidai fa ya soma gajiya da
d'abi'unta,cikikuwa harda rashin daukarsa da k'ima
a idonta.
Yana kwance yana tunane tunane yaji ta turo kofar
ta shigo. A hankali ya lumshe idonsa,baya kaunar
ganin fuskarta ko kusa.
Yana jin lokacin data zauna a gefen gadon baiyi ko
niyyar bud'e idanunsa ba ballantana ya dubeta. Ta
narkar da muryarta
"Jafar."
Bai amsa ba sai ma ya juya mata baya. Ta cigaba
da magana
"Jafar kayi hakuri don Allah,nayi kuskure amma zan
gyara kaji? Don Allah kada ka sanarwa Abba."
Sai lokacin ya bude idanunsa,ba tare da ya juyo ba
yace
"Sau nawa kike fad'in zaki gyara Siyama? Sau nawa
zanyi ta bibiyarki,wane irin nasiha ne ban yi maki
ba? Inace har kasussukan wa azizzika na sayo maki
na kawo? Wane taimako ne banyi maki ba Siyama?
Haka kikaga hajiyarki tana yi? Ban taba zuwa gidan
hajiyarki na sami gidanku da kazanta ba,ke kanki
ban taba ganinki a hargitse ba. Menene dalilin
chanjawarki? Meyasa bakyason gyaran gidanki?
Siyama ya kikeso nayi? Abinci kansa ace na waje
yafi wanda za a girka a gidana dad'in d'and'ano?
Wace halaka kikeson jefa kanki da ni?"
Ya mike zaune ya juyo ya dubeta,ta chanja suturarta
zuwa doguwar rigar bacci. Hannunta ya riko yana
kallonta idanuwansa da suke a rine da bacin
rai,kamar mai shirin kuka yace
"Dubeni Siyama! Ki dubi mijinki! Ke yanzu ko a ido
bai chanja maki ba? Ina kikeso na samu nutsuwa da
farin ciki bayan a wajenki? Soyayyar da muke yiwa
juna da alk'awarurrukanda mukayi gabannin
aurenmu cewar zamu kyautatawa juna ina suka
tafi? Na gaji da zama da wannan
siyamar,nafisonSiyamata ta ainahi ta dawo. Domin
Allah Siyama ki chanja hali,ki gyara ki zamto mace
mai tsafta da kula da miji,ki fita layin kazaman
mata. Kinmin alk'awarin zaki chanja?"
Siyama wacce tayi lakwas tana sauraron Jafar har
yakai aya,tana kaunar mijinta sosai hakanan tana
tsananin kishinsa(kuji fa),ta share hawayenta
"Zan gyara Jafar,kaima don Allah ka rage fad'a
banaso yakan tunzura zuciyata."
Jafar yayi murmushi
"Ke kike sanyawa nayi maki Siyama. Amma ba don
naso ba nake aikatawa. Komai ya wuce."
Siyama ta saki murmushin dake k'ara fiddo da
kyawun halittar ta
"Nagode Jafar,na kawo maka abincin ne? Favourite
dinka nayi,tuwo ne."
Da sauri ya dakatar da ita,bai mance d'and'anon
miya nata ba
"No,bar abincin nan. Da safe saiki d'umama min
ko?"
Tayi murmushi.
****************
Da safe kamar kullum,Jafar ne ya soma tashi. Yakai
dubansa ga Siyama,tana kwance tana sharar bacci
tun bayan sallar asuba da sukayi jam'i. Murmushi
yayi ya girgiza kansa,ai mai hali dai baya fasa
halinsa. Ficewa yayi ya shiga kicin ya d'ora ruwan
wanka. Sannan ya tsaya a tsakar gidan kamar mai
tunani,sai kuma ya koma d'aki ya cire jallabiyarsa ya
fito daga shi sai gajeran wando ya soma aikin gidan.
Dakunanta ya soma gyarowa,ya had'a tulin kayan
wanki waje guda ya k'ullesu. Sannan ya fad'a
bandaki. Da gudu ya dawo baya yana numfarfashi.
Can dabara ta fado mishi,ya dauki d'ankwali ya
d'aure hancinsa ya fad'a ciki. Hankalinsa ya tashi
ganin ledojin pads a hanyar makwararar ruwan,da
alama ciki take turasu duk lokacin data fidda. Yaja
tsaki yafi a k'irga,gaba daya tsikar jikinsa ta tashi,ya
fito daga bandakin a guje jin da yayi amai yana taso
mishi kamar mai sabon ciki. Wurgi yayi da
dankwalin gefe yana maida ajiyar zuciya.
Innalillahi,ashe Siyama abun nata haka yayi yawa?
Gaskiya babu ta yanda zai iya kimtsa
bandakinta,dakyar ya dawo daidai sannan ya fada
d'aya band'akin,shi kam da sauki kawai wanki yake
buk'ata. Jafar ya zage ya durza ko'ina bayan yayi
flushing. Saida ya tabbatar ya wanku ya shiga na
ukun ya wankeshi tsaf.
Alokacin da ya sharo d'akuna ya dawo falo da niyyar
sharewa,yana yi yana tari saboda k'ura, Siyama ta
shigo tana murza idanu,ta dubeshi
"Ah,jafar ai da ka bari tunda nace zanyi ai zanyi ko?"
Jafar cike da takaici yace
"Fita Siyama,idan na kammala kizo akwai aikin da
zakiyi. Dubamin ruwana tukunna."
Ta juya ta fita zuciyarta cike da murna don daman
ta kwana tunanin ta inda zata soma wannan jan
aikin.
Bayan jafar ya had'e sharar har dana tsakar
gidan,ya zuba a shara sannan ya wanke hannunsa.
Siyama ta kashe ruwan ta barshi anan. Tana
kallonsa ya shiga d'akin ya fiddo turarukan tsinke ya
kunnasu ya sanya a duka d'akunan da falo. Nan da
nan k'amshi ya mamaye gidan. Sai lokacin ya
sharce gumi ya dubeta
"Zo kiga aikinki."
Suka shiga har d'akinta,ko'inayayi kyau sai k'amshi
da iska mai dad'i,Jafar bai karasa ciki ba yace
"Shiga bandakin nan Siyama,ki cire abunda kika
cuccusa wajen wucewar ruwa,ki gyara komai ki
wanke. Hakanan kicin yana bukatar gyaranki.
Tsakar gidan nan ma ki wankeshi please,banason
ganin wannan dank'o dank'on kinji ko? Sannan kafet
din falon nan dana ciro,zan sanya azo a dauka akai
wanki."
Ta gyada kanta,ranta babu dadi. Babban abunda ke
tayar mata hankali kenan. Itama kanta kyankyamin
band'akin nata takeyi. Murnarta ta ragu domin tayi
zaton ma ya gyara,kicin kuwa ko almajirinta ne zata
sanyashi ya gyara ya wanke tsakar gidan. Koda a
kudin cefane ne ai saita biyashi.
Jafar yayi wankansa ya shirya kamar
koyaushe,bayan ya tabbatar da tsabtar bandakinsa
ya fito ya kulle abinsa,cike da nishad'in ganin tsakar
gidan tsaf ya fada dakinsa. Nan kuwa bai tsaya yin
shara ba a zummar sai ya dawo daga kasuwa......
Hmm kap allah raba..!
Kwana biyu da yin haka,babu
laifi Jafar yaga chanji
domin yakan dawo ya tarar an
share gidan. Hakanan
dakunanta tun gyaran da yayi
musu har lokacin bata
b'ata ba amma sunyi k'ura
saboda iskar ruwa da ake
yawan yi. Bai ce mata komai
ba ya bita a hakan. Ai
da dai wannan shegen
kazantar ya gwammace
suyita tafiya hakanan da
kansa ya dunga gyara inda
baiyimishi ba.
*************
Tun ranar da Jafar yak'i
waiwayar shagon take cikin
damuwa. Ta rasa abunda
yake yi mata dadi. Tana
jin kanta a mai laifi,inama
bata nemi sanin matsalar
Jafar ba. Yanzu gashinan ya
kauracewa shagon nasu
duk da batasan dalilinsa ba
saidai kwarai tana
zargin kanta. Gashi har Mama
ta dawo,rashin
ganinsa baisa ta matsa da
tambaya ba tunda a
yanzu mijin aure ne. Saidai
tana mamakin yanda bai
zuwa su gaisa kamar yanda a
baya yakan yi koda
bazai ci abincinsu ba. Ladi ai
ta fita shiga damuwa
domin sau biyu tana zuwa
nemansa a shago don
mik'a mishi sauran chanjinsa
amma bata samunshi.
Babu zato babu tsammani,ta
shigo sanye da kayan
makaranta wanda aka dinka
hijibin har gwuiwa,ta
hangoshi zaune a shagon
yana cin abinci yana hira
da Mama hankali kwance.
Nan da nan ta sauke
ajiyar zuciya,da saurinta ta
k'araso ciki da sallama.
Sai a sannan ne Jafar yasan
da
shigowarta,murmushi yayi
mata
"'Yar nijar."
Tayi dariyar farin cikin
ganinsa,Jafar yana burgeta
sosai saboda mutuncinsa.
K'arasawa tayi ta
gaisheshi a ladabce ya amsa
cikin sakin fuska. Ta
juya ga sauran customers
nasu ta gaishesu sannan
ta maido dubanta ga Jafar
"Yayana nayi zaton fushi
kakeyi dani,don Allah idan
maganata ta rannan ta b'ata
ranka kayi hakuri. Da
ace nasan bazakaji dad'inta
ba,bazan yi ba."
Jafar ya girgiza kansa
"Baki b'atamin rai ba
Ladi,saidai wasu dalilaina ne
suka sanya nabar lek'owa.
Kiyi hakuri,ki bar zargin
kanki. Ai ke Ladi baki da wata
d'abi'a da zaki b'ata
ran mutum dashi,kina da
kaifin basira da hankali.
Uwa uba gaki mai tsafta
wanda.."
Ya sanyawa bakinsa
linzami,idan baiyi
takatsantsan
ba yanzu sai yayi furucin da
Ladi zata d'ago
damuwarsa. Don haka ya
share batun yana
murmushi
"Ke dai kada ki damu
kanki,bakiyi laifi ba kinji ko?"
Murmushinta ya fad'ad'u har
ana hangen hak'oranta
"Nagode yayana,bari na barka
ka kammala sannan
kada kace zaka biya fa. Har
yanzu chanjinka suna...."
Ya katseta da hanzari
"Na bar maki 'yar nijar. Ki
rik'esu ki siya powder."
Sukayi dariya,tayi gaba bayan
tayi mishi godiya.
Ranar kam zuciyarta fes.
*********
Da misalin hudu da rabi na
yammacin ranar
juma'a,Jafar yana tare da
abokansa na kasuwa suna
ta hira da shek'a dariya. Idan
suka sami customers
kuma sai hankalinsu ya koma
garesu.
Ibrahim ne ya katseshi
"Kaifa tun dazu wayarka tana
ringing."
Ya mike da sauri ya shiga
shagon ya zaro wayar
daga chaji zuciyarsa babu ko
d'igon damuwa,saidai
ganin lambar Rumaisa duk sai
ransa ya b'aci. Duk a
yayyun Siyama babu wacce
jininsu bai hadu ba
kamar ta. Itace kan gaba
wajen yiwa matarsa
hud'ubar rashin arziki,domin
da kunnensa yasha jinsu
a falo yayinda suke hira.
Ba'ason ransa ba ya
dauka,kafin yakai ga magana
ta rigashi
"Haba Jafar,kasan sau nawa
nake ta danna maka
kira ne? Wannan bayi
bane,saika dunga ajiye waya
a
kusa tunda dai kabar gidanka
ba lafiya."
Nan take gabanshi ya fadi
"Kiyi hakuri anti,wayar na
sanyata chaji ne. Meke
faruwa a gidan nawa?"
Ai saita soma fad'a
"Lallai Jafar,wannan ya nuna
baka kula da Siyama.
Banda haka ace tun safe
matarka take fama da
jikinta baka da masaniya?
Toh Allah Ya kyauta,idan
kaga dama kazo ka samemu
muna nan a asibitin
Getwell har Hajiya."
Ai bai jira komai ba ya mike
yana maida hularsa,ya
dubi ibrahim
"Zan tafi asibiti ne madam
babu lafiya,koda Alhaji
yayi kiranka please ka sanar
dashi."
Daga haka ya fice,abokansa
suna tambayar lafiya
saidai bai iya basu amsa ba.
Yana tuk'a mashin d'insa
yana tunanin Siyama.
Daman fa tun safe da ya nemi
hakkinsa ta gudu
daga d'akin zuwa
nata,acewarta bacci takeji
sosai.
Hakan yasa ta k'ular dashi
don hatta kud'in cefanan
anan kan kujera ya ajiye
mata. Yayi dana sanin
biyewa mace,inama alokacin
ya cusa kansa har
d'akin domin bincikar
lafiyarta. Duk da d'abi'un
Siyama fa yana sonta sosai
wannan ne babban
dalilin hakurin da yake da ita.
Yana tunane tunanensa yana
tuk'i har ya iso k'ofar
asibitin ya faka.
Ko ciwon me siyama takeyi..?
Kai tsaye ya shiga asibitin,duk
iya waige waigensa
bai hangosu zaune ba.
Wannan ya sanyashi fiddo
wayarsa ya dannawa rumaisa
kira. Bayan ta dauka ya
nemi sanin inda suke.
Lek'owa tayi,ya hangota ta
fito
daga hannun hagunsa.
Fuskarta a daure,suna hada
ido ta watsa mishi kallon
banza sannan tayi gaba.
Har zuciyarsa baiji dadin
hakan ba dolensa ya
hadiye sanin da yayi ta
d'arashi a shekaru babu
yanda ya iya mata.
Zaune ya iske
Hajiya,mahaifiyar Siyama.
Siyama tana
kwance akan cinyarta. Ya
k'arasa cikin ladabi ya
durkusa yana gaisheta. Hajiya
bata ko kalleshi ba ta
amsa a ciki
"Lafiya."
Bai wani damu ba daman tun
a baya Hajiya ba son
aurensa da Siyama takeyi
ba,kwarai taso 'yarta da
auren d'aya daga cikin yaran
masu hannu da shunin
dake rububinta. Saidai Allah
Yafi gaban haka,aure
kuma kaddararSa ce. Ko
bayan haka ma soyayyarsa
da Siyama da kuma karfin
zumuncin dake tsakanin
iyayensu maza bana wasa
bane.
Jafar dakyar ya iya yin
tambayarsa
"Yaya jikin nata?"
Kamar jira Rumaisa
takeyi,tayi saurin cafewa
"Bakinka baiji kunyar
tambayar...."
"Kiyimin shiru,baki ganin a
inda muke ne?"
Maganar Hajiya tasa Rumaisa
hadiye sauran zancen
tana mai kwafa. Kafin
waninsu ya samu damar cewa
wani abu,wani ma'aikacin
asibitin ya fito daga dakin
da suke fuskanta,suka maida
hankali gareshi yayinda
ya mik'owa Rumaisa takarda
"Ga result saiku mik'awa
Doctor."
Tayi godiya,fuu ta
wuce,Hajiya na biye da ita
rike da
hannun Siyama. Jafar baiyi
k'asa a gwuiwa ba ya
mara musu baya saboda
yasan rashin binsu ma wata
matsalar ce. Tausayin Siyama
duk yabi ya rufeshi,har
lokacin tunanin abunda ya
faru gareta yakeyi saidai
bai iya tsinkayar komai ba.
Bayan likita ta kammala
duba result ta d'ago tana
murmushi tace
"Na tayaku murna She's
pregnant."
Dam! Tamkar an soki kirjin
Jafar,jin da yayi jiri yana
son kwasarsa ne ya sanya
babu shiri ya zube kan
kujera. Allah shaida ba'a
bakin cikin samun ciki na
sunnah amma shi kam yaji.
Yana son Siyama,yana
son haihuwa saidai
hankalinsa yayi mugun tashi
jin
cewar ciki ne da ita. Yanzun
ma ya aka k'are da
kazantar ta balle kuma har a
samu rabon d'a? Ai fa
saidai Allah Ya sassauta.
"Jafar bakaji abunda akace
bane?"
Rumaisa wacce tun furucin
likita ta zubo masa na
mujiya domin jin abunda zaice
ta katse tunaninsa.
Ya d'ago kansa da sauri yana
washe baki wanda ba
don Allah bane,
"Naji Anti,farin ciki ne ya
hanani magana."
Sai kuma ya tuno da Hajiya a
wajen. Doctor ta
dubesu bayan kammala
rubuce rubucenta
"Oh wannan ne mijin nata?"
Har lokacin bai rufe bakinsa
ba
"Eh nine."
Ta gyada kai tana murmushi
"Congrats."
"Thank you."
Ta miko musu file
"Sai a siya mata wadannan
magunguna. Sannan
itama ta dunga kula da kanta
sosai. Ta kiyaye
k'aidar shan magani. Allah Ya
raba lafiya."
Sukayi godiya suka fito. Ya
saci kallon
Siyama,murmushita sakar
mishi har baisan lokacin
daya maida martani ba da
nasa murmushin wanda
ke had'uwa da zuciyarsa su
k'ara masa wani d'aci.
Yakai dubansa ga Rumaisa
"Anti kawo a amso
magungunan."
Ta mik'a mishi su kuma
sukayi waje.
Ya kammala ya fito ya iskesu
cikin motar
Rumaisa,magana sukeyi
amma zuwansa ne yasa su
yin shiru har saida yakai ga
tsarguwa.
Ya mik'awa Rumaisa
magungunan,ta karb'a a
wulakance.
"Jafar."
Da sauri ya russuna
"Na'am Hajiya."
"Inaso nasan irin zaman da
kakeyi da Siyama,nayi
mamakin yanda muka je gidan
da niyyar ziyartarta
saidai muka isketa kwance
cikin amai,gaba dayanta
kaca kaca. Wane irin zama ne
da har matarka bata
da lafiya tun safe amma ace
har ka iya sanya
k'afa...."
"A'a fa Hajiya,wallahi bai
sani..."
Cikin zafin nama Anti rumaisa
ta kaiwa bakin Siyama
bugu. A fusace Hajiya tace
"Shashashar banza kawai,ana
nema mata 'yancinta
'yar iskar yarinya tak'i
ganewa. Don ubanki inace ke
da bakinki kika sanar damu
tun bai fita ba kike a
wannan yanayin? Shine salon
ki maidamu yan iska
kike shirin k'aryatawa?"
Gama maganar Hajiya,ta
maida dubanta ga Jafar
wanda haushi ya
isheshi,yanda yakejin
zuciyarsa
inda ace ba mahaifiya take ga
Siyama ba, da babu
abunda zai hanashi barin
wajen.
"Kaga Jafar,ba ni daka raina
ba,ko Alhaji mahaifi ga
siyaman da kake tak'ama
shine jinin Alhaji Rilwan
(mahaifinsa.),bazai yarda da
wulakanci ba a aure.
Don haka tun wuri ka chanja
takunka don muddin ka
cigaba da tafiya haka zan fito
fili na nuna maka
dagaske nake bani kaunar
aurenka da Siyama. Ja
motar mu tafi."
Ta k'arashe tana mayar da
dubanta ga Rumaisa.
Rumaisa da zuciyarta tayi fes
da wannan wankin da
Jafar yasha a wajen
Hajiyarsu,ta gyara zama ta
rufe
k'ofa. Mik'ewa yayi har
lokacin bai samu damar
cewa uffan ba,yana duban
yanda Siyama tayi wani
rau rau da ido,Rumaisa ta figi
motar ta saitata suka
fice daga asibitin.
Ransa ya b'aci ba kad'an
ba,wai me Hajiya da
Rumaisa suke nufi dashi ne?
Yasan Hajiya tun farko
bata kaunar aurenshi da
Siyama wannan kad'ai ya
isa ya janyo mishi tsana a
wajenta. Toh ita waccan
uwar shishshigin baisan layin
da zai ajiyeta ba,ko ita
d'inma tana bayan Hajiyar
ne,oho.
Cikin fusata Jafar ya bar
asibitin bai dire ko'ina ba
sai k'ofar gidan mahaifinsa.
Barka da kwana..!
(4)
Da safe kamar kullum,Jafar ne ya soma tashi.
Yakai dubansa ga Siyama,tana kwance tana
sharar bacci tun bayan sallar asuba da sukayi
jam'i. Murmushi yayi ya girgiza kansa,ai mai hali
dai baya fasa halinsa. Ficewa yayi ya shiga kicin
ya d'ora ruwan wanka. Sannan ya tsaya a tsakar
gidan kamar mai tunani,sai kuma ya koma d'aki
ya cire jallabiyarsa ya fito daga shi sai gajeran
wando ya soma aikin gidan. Dakunanta ya soma
gyarowa,ya had'a tulin kayan wanki waje guda ya
k'ullesu. Sannan ya fad'a bandaki. Da gudu ya
dawo baya yana numfarfashi. Can dabara ta fado
mishi,ya dauki d'ankwali ya d'aure hancinsa ya
fad'a ciki. Hankalinsa ya tashi ganin ledojin pads
a hanyar makwararar ruwan,da alama ciki take
turasu duk lokacin data fidda. Yaja tsaki yafi a
k'irga,gaba daya tsikar jikinsa ta tashi,ya fito
daga bandakin a guje jin da yayi amai yana taso
mishi kamar mai sabon ciki. Wurgi yayi da
dankwalin gefe yana maida ajiyar zuciya.
Innalillahi,ashe Siyama abun nata haka yayi
yawa? Gaskiya babu ta yanda zai iya kimtsa
bandakinta,dakyar ya dawo daidai sannan ya
fada d'aya band'akin,shi kam da sauki kawai
wanki yake buk'ata. Jafar ya zage ya durza
ko'ina bayan yayi flushing. Saida ya tabbatar ya
wanku ya shiga na ukun ya wankeshi tsaf.
Alokacin da ya sharo d'akuna ya dawo falo da
niyyar sharewa,yana yi yana tari saboda k'ura,
Siyama ta shigo tana murza idanu,ta dubeshi
"Ah,jafar ai da ka bari tunda nace zanyi ai zanyi
ko?"
Jafar cike da takaici yace
"Fita Siyama,idan na kammala kizo akwai aikin
da zakiyi. Dubamin ruwana tukunna."
Ta juya ta fita zuciyarta cike da murna don
daman ta kwana tunanin ta inda zata soma
wannan jan aikin.
Bayan jafar ya had'e sharar har dana tsakar
gidan,ya zuba a shara sannan ya wanke
hannunsa. Siyama ta kashe ruwan ta barshi
anan. Tana kallonsa ya shiga d'akin ya fiddo
turarukan tsinke ya kunnasu ya sanya a duka
d'akunan da falo. Nan da nan k'amshi ya
mamaye gidan. Sai lokacin ya sharce gumi ya
dubeta
"Zo kiga aikinki."
Suka shiga har d'akinta,ko'ina yayi kyau sai
k'amshi da iska mai dad'i,Jafar bai karasa ciki ba
yace
"Shiga bandakin nan Siyama,ki cire abunda kika
cuccusa wajen wucewar ruwa,ki gyara komai ki
wanke. Hakanan kicin yana bukatar gyaranki.
Tsakar gidan nan ma ki wankeshi please,banason
ganin wannan dank'o dank'on kinji ko? Sannan
kafet din falon nan dana ciro,zan sanya azo a
dauka akai wanki."
Ta gyada kanta,ranta babu dadi. Babban abunda
ke tayar mata hankali kenan. Itama kanta
kyankyamin band'akin nata takeyi. Murnarta ta
ragu domin tayi zaton ma ya gyara,kicin kuwa ko
almajirinta ne zata sanyashi ya gyara ya wanke
tsakar gidan. Koda a kudin cefane ne ai saita
biyashi.
Jafar yayi wankansa ya shirya kamar
koyaushe,bayan ya tabbatar da tsabtar
bandakinsa ya fito ya kulle abinsa,cike da
nishad'in ganin tsakar gidan tsaf ya fada dakinsa.
Nan kuwa bai tsaya yin shara ba a zummar sai
ya dawo daga kasuwa.
na biyu da yin haka,babu laifi Jafar yaga
chanji domin yakan dawo ya tarar an share
gidan. Hakanan dakunanta tun gyaran da yayi
musu har lokacin bata b'ata ba amma sunyi
k'ura saboda iskar ruwa da ake yawan yi. Bai ce
mata komai ba ya bita a hakan. Ai da dai wannan
shegen kazantar ya gwammace suyita tafiya
hakanan da kansa ya dunga gyara inda
baiyimishi ba.
*************
Tun ranar da Jafar yak'i waiwayar shagon take
cikin damuwa. Ta rasa abunda yake yi mata dadi.
Tana jin kanta a mai laifi,inama bata nemi sanin
matsalar Jafar ba. Yanzu gashinan ya kauracewa
shagon nasu duk da batasan dalilinsa ba saidai
kwarai tana zargin kanta. Gashi har Mama ta
dawo,rashin ganinsa baisa ta matsa da tambaya
ba tunda a yanzu mijin aure ne. Saidai tana
mamakin yanda bai zuwa su gaisa kamar yanda a
baya yakan yi koda bazai ci abincinsu ba. Ladi ai
ta fita shiga damuwa domin sau biyu tana zuwa
nemansa a shago don mik'a mishi sauran
chanjinsa amma bata samunshi.
Ta shigo sanye da kayan makaranta wanda aka
dinka hijibin har gwuiwa,babu zato ba
tsammani,ta hangoshi zaune a shagon yana cin
abinci yana hira da Mama hankali kwance. Nan
da nan ta sauke ajiyar zuciya,da saurinta ta
k'araso ciki da sallama. Sai a sannan ne Jafar
yasan da shigowarta,murmushi yayi mata
"'Yar nijar."
Tayi dariyar farin cikin ganinsa,Jafar yana burgeta
sosai saboda mutuncinsa. K'arasawa tayi ta
gaisheshi a ladabce ya amsa cikin sakin fuska.
Ta juya ga sauran customers nasu ta gaishesu
sannan ta maido dubanta ga Jafar
"Yayana nayi zaton fushi kakeyi dani,don Allah
idan maganata ta rannan ta b'ata ranka kayi
hakuri. Da ace nasan bazakaji dad'inta ba,bazan
yi ba."
Jafar ya girgiza kansa
"Baki b'atamin rai ba Ladi,saidai wasu dalilaina
ne suka sanya nabar lek'owa. Kiyi hakuri,ki bar
zargin kanki. Ai ke Ladi baki da wata d'abi'a da
zaki b'ata ran mutum dashi,kina da kaifin basira
da hankali. Uwa uba gaki mai tsafta wanda.."
Ya sanyawa bakinsa linzami,idan baiyi
takatsantsan ba yanzu sai yayi furucin da Ladi
zata d'ago damuwarsa. Don haka ya share batun
yana murmushi
"Ke dai kada ki damu kanki,bakiyi laifi ba kinji
ko?"
Murmushinta ya fad'ad'u har ana hangen
hak'oranta
"Nagode yayana,bari na barka ka kammala
sannan kada kace zaka biya fa. Har yanzu
chanjinka suna...." Ya katseta da hanzari
"Na bar maki 'yar nijar. Ki rik'esu ki siya
powder."
Sukayi dariya,tayi gaba bayan tayi mishi godiya.
Ranar kam zuciyarta fes.
(5)
*********
Da misalin hudu da rabi na yammacin ranar
juma'a,Jafar yana tare da abokansa na kasuwa
suna ta hira da shek'a dariya. Idan suka sami
customers kuma sai hankalinsu ya koma garesu.
Ibrahim ne ya katseshi
"Kaifa tun dazu wayarka tana ringing."
Ya mike da sauri ya shiga shagon ya zaro wayar
daga chaji zuciyarsa babu ko d'igon
damuwa,saidai ganin lambar Rumaisa duk sai
ransa ya b'aci. Duk a yayyun Siyama babu wacce
jininsu bai hadu ba kamar ta. Itace kan gaba
wajen yiwa matarsa hud'ubar rashin arziki,domin
da kunnensa yasha jinsu a falo yayinda suke hira.
Ba'ason ransa ba ya dauka,kafin yakai ga
magana ta rigashi
"Haba Jafar,kasan sau nawa nake ta danna maka
kira ne? Wannan bayi bane,saika dunga ajiye
waya a kusa tunda dai kabar gidanka ba lafiya."
Nan take gabanshi ya fadi
"Kiyi hakuri anti,wayar na sanyata chaji ne. Meke
faruwa a gidan nawa?"
Ai saita soma fad'a
"Lallai Jafar,wannan ya nuna baka kula da
Siyama. Banda haka ace tun safe matarka take
fama da jikinta baka da masaniya? Toh Allah Ya
kyauta,idan kaga dama kazo ka samemu muna
nan a asibitin Getwell har Hajiya."
Ai bai jira komai ba ya mike yana maida
hularsa,ya dubi ibrahim
"Zan tafi asibiti ne madam babu lafiya,koda Alhaji
yayi kiranka please ka sanar dashi."
Daga haka ya fice,abokansa suna tambayar lafiya
saidai bai iya basu amsa ba.
Yana tuk'a mashin d'insa yana tunanin Siyama.
Daman fa tun safe da ya nemi hakkinsa ta gudu
daga d'akin zuwa nata,acewarta bacci takeji
sosai. Hakan yasa ta k'ular dashi don hatta
kud'in cefanan anan kan kujera ya ajiye mata.
Yayi dana sanin biyewa mace,inama alokacin ya
cusa kansa har d'akin domin bincikar lafiyarta.
Duk da d'abi'un Siyama fa yana sonta sosai
wannan ne babban dalilin hakurin da yake da ita.
Yana tunane tunanensa yana tuk'i har ya iso
k'ofar asibitin ya faka.
Kai tsaye ya shiga asibitin,duk iya waige
waigensa bai hangosu zaune ba. Wannan ya
sanyashi fiddo wayarsa ya dannawa rumaisa kira.
Bayan ta dauka ya nemi sanin inda suke.
Lek'owa tayi,ya hangota ta fito daga hannun
hagunsa. Fuskarta a daure,suna hada ido ta
watsa mishi kallon banza sannan tayi gaba. Har
zuciyarsa baiji dadin hakan ba dolensa ya hadiye
sanin da yayi ta d'arashi a shekaru babu yanda
ya iya mata.
Zaune ya iske Hajiya,mahaifiyar Siyama. Siyama
tana kwance akan cinyarta. Ya k'arasa cikin
ladabi ya durkusa yana gaisheta. Hajiya bata ko
kalleshi ba ta amsa a ciki
"Lafiya."
Bai wani damu ba daman tun a baya Hajiya ba
son aurensa da Siyama takeyi ba,kwarai taso
'yarta da auren d'aya daga cikin yaran masu
hannu da shunin dake rububinta. Saidai Allah Yafi
gaban haka,aure kuma kaddararSa ce. Ko bayan
haka ma soyayyarsa da Siyama da kuma karfin
zumuncin dake tsakanin iyayensu maza bana
wasa bane.
Jafar dakyar ya iya yin tambayarsa
"Yaya jikin nata?"
Kamar jira Rumaisa takeyi,tayi saurin cafewa
"Bakinka baiji kunyar tambayar...."
"Kiyimin shiru,baki ganin a inda muke ne?"
Maganar Hajiya tasa Rumaisa hadiye sauran
zancen tana mai kwafa. Kafin waninsu ya samu
damar cewa wani abu,wani ma'aikacin asibitin ya
fito daga dakin da suke fuskanta,suka maida
hankali gareshi yayinda ya mik'owa Rumaisa
takarda
"Ga result saiku mik'awa Doctor."
Tayi godiya,fuu ta wuce,Hajiya na biye da ita rike
da hannun Siyama. Jafar baiyi k'asa a gwuiwa ba
ya mara musu baya saboda yasan rashin binsu
ma wata matsalar ce. Tausayin Siyama duk yabi
ya rufeshi,har lokacin tunanin abunda ya faru
gareta yakeyi saidai bai iya tsinkayar komai ba.
Bayan likita ta kammala duba result ta d'ago
tana murmushi tace
"Na tayaku murna She's pregnant."
Dam! Tamkar an soki kirjin Jafar,jin da yayi jiri
yana son kwasarsa ne ya sanya babu shiri ya
zube kan kujera. Allah shaida ba'a bakin cikin
samun ciki na sunnah amma shi kam yaji. Yana
son Siyama,yana son haihuwa saidai hankalinsa
yayi mugun tashi jin cewar ciki ne da ita. Yanzun
ma ya aka k'are da kazantar ta balle kuma har a
samu rabon d'a? Ai fa saidai Allah Ya sassauta.
"Jafar bakaji abunda akace bane?"
Rumaisa wacce tun furucin likita ta zubo masa na
mujiya domin jin abunda zaice ta katse
tunaninsa. Ya d'ago kansa da sauri yana washe
baki wanda ba don Allah bane,
"Naji Anti,farin ciki ne ya hanani magana."
Sai kuma ya tuno da Hajiya a wajen. Doctor ta
dubesu bayan kammala rubuce rubucenta
"Oh wannan ne mijin nata?"
Har lokacin bai rufe bakinsa ba
"Eh nine."
Ta gyada kai tana murmushi
"Congrats."
"Thank you."
Ta miko musu file
"Sai a siya mata wadannan magunguna. Sannan
itama ta dunga kula da kanta sosai. Ta kiyaye
k'aidar shan magani. Allah Ya raba lafiya."
Sukayi godiya suka fito. Ya saci kallon
Siyama,murmushi ta sakar mishi har baisan
lokacin daya maida martani ba da nasa
murmushin wanda ke had'uwa da zuciyarsa su
k'ara masa wani d'aci. Yakai dubansa ga
Rumaisa
"Anti kawo a amso magungunan."
Ta mik'a mishi su kuma sukayi waje.
Ya kammala ya fito ya iskesu cikin motar
Rumaisa,magana sukeyi amma zuwansa ne yasa
su yin shiru har saida yakai ga tsarguwa.
Ya mik'awa Rumaisa magungunan,ta karb'a a
wulakance.
"Jafar."
Da sauri ya russuna
"Na'am Hajiya."
"Inaso nasan irin zaman da kakeyi da
Siyama,nayi mamakin yanda muka je gidan da
niyyar ziyartarta saidai muka isketa kwance cikin
amai,gaba dayanta kaca kaca. Wane irin zama ne
da har matarka bata da lafiya tun safe amma ace
har ka iya sanya k'afa...."
"A'a fa Hajiya,wallahi bai sani..."
Cikin zafin nama Anti rumaisa ta kaiwa bakin
Siyama bugu. A fusace Hajiya tace
"Shashashar banza kawai,ana nema mata
'yancinta 'yar iskar yarinya tak'i ganewa. Don
ubanki inace ke da bakinki kika sanar damu tun
bai fita ba kike a wannan yanayin? Shine salon ki
maidamu yan iska kike shirin k'aryatawa?"
Gama maganar Hajiya,ta maida dubanta ga Jafar
wanda haushi ya isheshi,yanda yakejin zuciyarsa
inda ace ba mahaifiya take ga Siyama ba, da
babu abunda zai hanashi barin wajen.
"Kaga Jafar,ba ni daka raina ba,ko Alhaji mahaifi
ga siyaman da kake tak'ama shine jinin Alhaji
Rilwan(mahaifinsa.),bazai yarda da wulakanci ba
a aure. Don haka tun wuri ka chanja takunka don
muddin ka cigaba da tafiya haka zan fito fili na
nuna maka dagaske nake bani kaunar aurenka da
Siyama. Ja motar mu tafi."
(6)
Ta k'arashe tana mayar da dubanta ga Rumaisa.
Rumaisa da zuciyarta tayi fes da wannan wankin
da Jafar yasha a wajen Hajiyarsu,ta gyara zama
ta rufe k'ofa. Mik'ewa yayi har lokacin bai samu
damar cewa uffan ba,yana duban yanda Siyama
tayi wani rau rau da ido,Rumaisa ta figi motar ta
saitata suka fice daga asibitin.
Ransa ya b'aci ba kad'an ba,wai me Hajiya da
Rumaisa suke nufi dashi ne? Yasan Hajiya tun
farko bata kaunar aurenshi da Siyama wannan
kad'ai ya isa ya janyo mishi tsana a wajenta. Toh
ita waccan uwar shishshigin baisan layin da zai
ajiyeta ba,ko ita d'inma tana bayan Hajiyar
ne,oho.
Cikin fusata Jafar ya bar asibitin bai dire ko'ina
ba sai k'ofar gidan mahaifinsa.
Ta zuba masa ido tana hankalta da tarin
damuwar dake kwance a saman fuskarsa. Adaidai
lokacin yake amsa gaisuwar kannensa,sannan ya
k'arasa har inda mahaifiyarsa ke zaune,cikin
ladabi irinta Jafar ya russuna a gabanta ya
gaisheta. Hajja ta amsa har lokacin idanuwanta
basu kaura daga kan fuskarsa ba. Gefenta ya
zauna yana mai yamutsa fuska alamar gajiya.
Hajja ta umarci d'aya cikin kannensa data kawo
mishi ruwa.
Saida Jafar yasha ruwan nan mai sanyi sannan
ya iya sauke numfashi.
Hajja ta jefo masa tambaya
"Babana menene ya faru na ganka cikin
damuwa?"
Jafar ya shafi sumar kansa yana murmushi a
wahale
"Babu komai Hajja,Siyama ce bataji dad'i ba. Ina
kasuwa anti rumaisa ke sanarmin,a asibiti ma na
iskesu har Hajiya. Amma jikin yayi sauki sun
maidata gida."
Hajja cikin nuna jimami tace
"Assha, ai fa naji yarannan sunce Rumaisa tazo
sun fita da Hajiyar(dayake gidansu Jafar da nasu
Siyama suna facing juna) ashe wajenta suka
nufa,meya samu ita Siyamar?"
Jafar ya d'an tab'e baki
"Wai juna biyu take dauke dashi."
Cike da mamaki hajja take dubansa
"Wai fa kace?"
Yayi saurin gyara zancen
"A'a,juna biyun ne Hajja."
Ta saki fuska "Alhamdulillah,nayi murna. Allah Ya
rabasu lafiya,saika kula da ita sosai don Allah."
Jafar ya gyada kansa,Hajja dai ta lura ba rashin
lafiyar Siyama kad'ai bane damuwar Jafar,don
haka tace
"Babana akwai abunda ke damunka bayan
wannan,ka sanarmin menene ke faruwa? Idan
bani da maganin abun sai na bika da addu'a."
Tayi shiru cikin yanayin damuwa,ba yau ne farkon
fara ganinshi cikin yanayi haka ba saidai batason
sanya ido duk da tana zargin zamantakewarsu da
Siyama sanin halin da akayi auren Hajiyarta
bataso.
"Hajja bakomai,kaina yake ciwo ne. Ina kasuwa
rashin lafiyar Siyama ya taso ni,amma yanzu
komai da sauki. Idan da abinci a zubomin."
Ya k'arasa yana kwantar da kansa jikin
kujera,idanuwansa a lumshe,bayason ganin
hajjarsa cikin damuwa ko yaya ne balle kuma ace
sanadinsa ne ta shigeshi. Yana ji sadda
tace"Allah Ya yaye maka." A zuciyarsa ya
amsa,ta kwalawa kanwarsa kira sannan ta bata
umarnin kawo mishi abinci. Jafar kuwa ya rasa
takaiman abunda zai kokawa, bakaken
maganganun da Hajiya ta gasa mishi ko kuwa da
KAZAMAR GIDAnsa? Dakyar ya iya k'ok'arin
had'iye damuwarsa saboda ganin Hajja tana
neman sanyawa kanta tunani duk a dominsa.
Bai bar gidan ba sai bayan isha'i bayan ya shiga
sun gaisa da Alhajinsa yake sanar dashi dalilin
barinsa shago da wuri. Alhaji yace sam,basuyi
waya da ibrahim ba ballantana ya sanar mishi.
Shima yayi farin ciki da cikin Siyama a karshe
sukayi sallama ya tafi ko kallon gidansu Siyama
baiyi ba tunda yasan Abbanta baya garin don
haka babu sauran wanda zai shiga dominsa.
**************
Koda ya dawo ya sameta tana baccin a d'akinta.
Ya rufeta saboda sanyi sannan ya wuce d'akinsa.
A daren bacci b'arawo ne kawai ya saceshi.
Tun Jafar yana daurewa Siyama har yazo ya
share zancen suka d'inke kamar basu ba.
Matsala ta farko daya soma cin karo da ita tun
samun cikin Siyama,bai wuce k'azantar jikinta
daya k'aru ba. Dole ya kauracewa hada shimfid'a
da ita,idan kuma yaga cutar zatayi mishi yawa
yakan rok'eta akan ta taimaka tayi wanka,harma
da kanshi ya d'ora mata ruwa,sai ta gama
kumbure kumburenta zatayi,kamar da gaske za'a
d'ore a hakan sai kuma ta bar yi. Koda ya dora
ruwan hakanan saidai ya hakura. Akan dole ya
sabarwa kansa da azumin litinin da alhamis.
Sunfi sati uku rabon da wata mu'amalar kwanciya
ta shiga tsakaninsu,hakanan kowannensu yana
nasa d'akin.
Siyama ta bar yin kowane gyara ga jikinta,idan
kuwa unguwa ta kamata saidai ta goge
hammatarta da ruwan alimun da lemun
tsami,alokacin ne zata kokarta ta sharce gashinta
wanda Jafar bai tab'a ganinsa a kitse ba. Duk
wani kwaskwarima Siyama tasan yanda zata
yishi muddin ta tashi fita unguwa.
Yanzun ma fitar ce ta taso mata,wai zataje
gidansu daganan su wuce biki can a dangin
hajiyar tasu. Yana tsaye gaban madubin d'akinsa
yana aikin gyara sumarsa,ta shigo d'akin.
K'amshin da yaji ya bugi hancinsa ne ya sanyashi
waigowa. Murmushin takaici yayi ya k'are mata
kallo tun daga k'asa har sama. Anci riga da
siket,fuskar nan an wanketa da kwalliya daidai da
zamani. Bai tab'a sanin ta mallaki kyakkyawan
leshin nan ba sai a yau. Ya ganta tamkar
Siyamarsa sak ta baya, abun bakin ciki harda
wadannan kwalliye kwalliyan aka yaudareshi
baisan kyallin banza bane.
Murmushi ta jefeshi dashi,ya girgiza kansa yana
tab'e baki kafin ya juya ya cigaba da shirinsa.
Hannuwanta yaji ta bayanshi
"Jafar banji kace nayi kyau ba?"
Ya lumshe ido ya bude,ta madubi suka kalli juna.
Murmushi ya k'ara yi a karo na biyu
"Kinyi kyau,da ace haka kike zama a gidanki da
ba haka ba. Kwalliyarki ai ta fita unguwa ce."
Ta sakeshi ta jingina da bango yayinda take
dubanshi yana zura riga
"Jafar kenan,nikam kana bani mamaki yanda
bakason yimin uzuri. Baka ganin yanda nake
fama da kaina? Kwalliyar ma dole ce ta sanyani
yinta a yanzun,kowane sutura zan saka inajin
kaina a takure wallahi."
"Siyama kenan,kafin ki samu cikin kuma menene
yake hanani yimin? Ko an fadamaki mazan waje
sun fini bukatar kwalliyarki? Burinki ki k'ure
adaka ki fita amma bakisan kiyimin a gida ba
ko?"
Ya tabe baki yana daga kafada
"Ai shikenan,zan auro wacce zata dunga bani
kulawa."
Ai saita daure fuska
"Zaka fara ko? Daman ku maza duk abunda
matanku zasuyi maku bakwa tab'a gani. Duk
kokarin da nakeyi baka gani Jafar. Ni banyi
korafin yanda bakason cin abincina ba matukar
ba shinkafa da wake nayi ba,sai kai keda bakin
cewa banason yi maka kwalliya? Sau nawa ka
bani kud'in kayan kwalliyar?"
Jafar dake shirin sanya hula ya tsaya cak yana
kallonta,mamaki ma ta bashi. Ta dauke idonta
daga gareshi fuskarta a kumbure
"Siyama har kina da bakin gayamin haka? Ai
kuwa idan har kika shaideni akan bana siya maki
kayan kwalliya duk da har yanzu akwai sauran na
lefenki bakiyi adalci gareni ba. Hakanan sau nawa
na baki kud'in wanke gashi kike biyan bashi
dasu? Sau nawa kikayimin karyar zakiyi kunshi na
ciro kud'i na baki,kin tab'a yi? Bani mantawa
bikin Kawarki daya tashi kad'ai ne sadda na
soma ganinki da kunshi a kafarki tun bayan na
bikinki daya goge. Siyama ke ta dabance ma
acikin kazaman matan,bansan irinki ba! Girkin da
kike magana a zatonki zan iya cin cima marar
dad'in d'and'ano ne? Ke komai da mata sukeyi ke
bakiyinsa,baki iya ba sai afkin karance karance da
kallace kallace. Duk a banza Siyama,banga
amfanin ilimin boko dana arabin da kikayi ba.
(7)
Bazan iya cigaba da zama kodayaushe ina yawon
zuwa gidan abinci ba,ya rage naki ki gyara kanki
ko kuma abunda kike gudu ya faru."
Har ya kai k'arshe bata da niyyar cewa komai.
Binsa kawai takeyi da kallo,fargabanta ya k'aru.
Kada dai ace dagaske Jafar auren zaiyi? Tana
ganin ya fita waje, tayi saurin daukar wayarsa.
Duk iya lalubenta bata ci karo da lambar wata
budurwa ba 'bare' wacce bata sani ba yan
uwansu ne zallah wadanda itama ta sansu. Tana
shirin duba b'angaren sak'onni ya shigo. Yana
kallonta saima ta bashi dariya yayi murmushi
"Fito muje,ba saikin wahalar da kanki ba Siyama.
Bani da budurwa bana sha'awar yin wani auren
amma ina sha'awar mace mai tsafta wacce ta iya
girki da kwalliya. Wacce zata bani kulawa da
girmana a matsayin mijin aurenta. Matukar zaki
zama irin haka toh wallahi fargaba ba naki
bane,domin babu macen da zata burgeni. Ke
kanki kinsan bana ra ayin mata biyu. Amma
kuma a yanzu na soma chanja ra ayi matukar
bazaki gyara ba."
Ya d'auki wayarsa data ajiye,ko kallonta baiyi ba
ya fito.
"Kin tsaya,nace ki fito zan rufe d'akin ko?"
Ta fito a sanyaye tana duban fuskarsa dake a
had'e,ya rufe d'akin gam da mukulli tayi azamar
riko hannuwansa. Bayason duban kwayar
idanunta yanzun nan sai fushinsa ya sauka. Ta
narkar da murya
"Jafar nasan bana kyautata maka,kayi hakuri don
Allah. Ni yanzu ya kakeso nayi? Duk ka
sanyayamin jikina Jafar,kaima kasan ban taba
son wani mahaluki ba saikai,irin son da ko kusa
bana marmarin wata ta kusanci inda..."
Ya katseta yana dariya,wallahi Siyama fa ta
rainashi. Yo banda raini har ma ta tsaya tana
tsarashi akan abunda yasan ba gaskiya bane. Shi
yasan ba kud'i ne dashi ba sai rufin asirin
Allah,ba wani kyau ne dashi ba na azo a gani
domin a kyawun ma Siyama ta tsereshi ba kusa
ba. Zai iya yarda tana sonshi saidai bayan
aurensu ta rage sonshi tunda har bazata iya
faranta mishi ba hakanan sonta ya ragu a
zuciyarsa saboda sabbin halayenta da yaci karo
dasu bayan auren.
"Kina b'atawa kanki lokaci,kin sameni ina bacci
kin matsamin nayi sauri nayi wanka ana
jiranki,yanzu kuma zaki tsaidani ina fa da wurin
zuwa Siyama. Taho mu wuce,idan muka dawo sai
ayi maimaicin karatun ko Allah zai sa yau nayi
dace."
Ya janye hannuwansa yayi gaba,ta bishi a baya
gwuiwa sake.... !
Zaune suke akan benci gaban gidan
amininsa,Haris. Kwanansa d'aya da dawowa
daga Gusau garin iyayensa. Hira sukeyi na bayan
rabuwa,Haris yace
"Ina amarya Siyama? Ka k'i kawota su gaisa da
Ummina ko?"
Ya harareshi
"Ita Ummin meya hanata kawo mana ziyara?"
Haris yayi dariya
"Zaka take gaskiya kenan? Ummina fa zuwanta
biyu gidan a rufe ba kowa kodai ka manta ne?
Idan zumuncin na gaske ne kaine yafi dacewa ka
dauko Siyama itama tasan hanyar gidana."
Jafar ya mutsistsika hancinsa
"Wannan kuma sai damar hakan ta samu. Ni
yanzu ka saurareni inada muhimmin batun da
nake neman shawararka akai."
Haris ya nutsu yana gyara zaman 'medical glass'
d'insa
"Ina sauraronka."
Jafar ya numfasa ya labarto mishi kad'an daga
cikin matsalar da yake fuskanta a wajen Siyama.
Ya k'ara da cewa
"Nifa na soma gajiya Haris,a ganina lokaci yayi
da zan sanarwa iyayenmu. Watakila idan anci
sa'a ta ji maganarsu."
Haris kallonsa kawai yakeyi,tun soma jin irin
matsalolin da amininsa ke fuskanta, ya gyara
zaman gilashinsa yafi sau biyar. Ba don shi da
kansa ke sanar mishi ba babu abunda zai
hanashi k'aryatawa. Bayan kammala sauraron
Jafar yafi mintuna biyu kafin ya motsa bakinsa.
"Jafar kana nufin dukkan abubuwan daka lissafo
halayan Siyama ne babu abunda ka k'ara akai?"
Jafar yayi murmushi
"Da ace kasan Jafar a makaryaci Haris,shine
zakayi wannan tunanin. Kai shaida ne akan son
da nake yiwa Siyama,ta yaya zanyi mata k'age?
Haris shawara zaka bani,menene ya kamata nayi
na kawo k'arshen matsalar nan?"
Haris ya numfasa
"Kaicon Siyama,na tausayawa rayuwarka Jafar.
Babbar matsala ce wannan wanda ba kowane
namiji ne zai iya juriyarsa ba. Hakika cigaba da
rayuwa a haka ba shine mafita ba,baka da laifi ko
a wurin Allah tunda har kayi mata nasiha ka
kuma bita da fad'a amma duk da hakan tak'i
chanjawa. Shawarar da zan baka itace,ka kai
maganar zuwa ga yayarmu anti Habiba(firstborn
a d'akinsu Jafar). Ka fayyace mata komai na
tabbata bazata rasa taimakon da zatayi gareka
ba amma kada kace zaka sanarwa iyayenku,ka
manta da yanda akayi auren ne ba'a son ran
Hajiya da wasu ba? Ko kuwa so kake ayi maku
dariya?"
Jafar ya jinjina kai,hakika shawara ma tana da
dad'i. Ba da ban Haris ba,da tuni ya aikata ba
daidai ba.
"Hum,damuwa ta sanyani gaza yin tunani mai
kyau. Inda ace baka tunasar dani ba,nasan bazan
bi takan anti habiba ba. Nagode da wannan
shawarar,in sha Allah gobe zanje har gida na
sameta."
Haris ya amsa
"Yauwa kokaifa,kasan fa halin wasu matan,yanzu
kana kai k'ararsu maimakon su shiga taitayinsu
sai wani sabon salon ya b'ullo. Gwara abi abun
sannu sannu ko Allah zaisa a dace. Wallahi abun
bai bar bani mamaki ba."
Jafar ya girgiza kansa
"Don baka gani bane,ni nasan yanda nake fama.
Wai kuma a hakan ne ake cewa ana kishina."
Haris yayi dariya
"Kaicon Siyama,Allah Ya gyara."
(8)
Anti Habiba salati takeyi tana k'arawa lokacin
data gama sauraron maganganun da suke fitowa
daga bakin Jafar.
"Wannan abu dame yayi kama? Amma kuwa
Siyama ta bani kunya,inajin wai wai a bakunansu
Husna(d'iyarta) kafin aurenku ashe gaskiyarsu
suke fad'i? Eh lallai Siyama ta cika KAZAMAR
GIDA."
Jafar ya dubi Antinsa da mamaki
"Oh anti,har su Husna sun sani amma babu
wanda ya tab'a sanar dani?"
Ta harareshi
"Tayaya za'a sanar maka kakana? Ni kaina ban
yarda ba da suka sameni da zancen. Koda ma an
fad'amaka yanda ka zama majnunu Siyama ai ba
yarda zakayi ba. Ko ka manta furucinka a baya
na tuna maka? Cewa fa kayi Siyama ta mamaye
dukkanin b'angarorin dake jikinka. Toh waye mai
karambanin tarar ka da wannan zancen kakana?"
Ya tuntsire da dariya,daman yasan muddin ya
kawo laifin Siyama wajen antinsa zaiji magana
tunda har da ita cikin masu bashi shawarar ya
hakura da ita alokacin da Hajiyar Siyama ta hura
wutar kiyayyarta ga auren nasu. Amma ina! Son
da yake yiwa Siyama bai bari yaji shawarar
kowannensu ba. Ga kuma rabo daya riga ya
rantse.
"Oh antina,nikam na kawo kaina. Nidai a
taimakamin da mafita abar tuna baya."
Ta tab'e baki
"Zanje gidan naka,nafison na ganewa idona kafin
musan abunyi idan ta kama sai mu maidata
makaranta." Ta k'arashe da wasa.
Jafar ya k'ara sanya dariya,
"Haba anti,yarinyar da tayi hadda? A dai nemo
wani hanyar."
"Shikenan zan zaunar da ita muyi magana,Allah
Yasa a dace."
"Amin amin antina."
Ya jima a gidan anti habiba suna hirarsu da
dariya domin antin tasa badai raha ba amma fa
sam bata da kyau yayinda aka tab'ota. Tana da
zafi ainun.
Misalin uku da rabi na ranar Talata. Siyama tana
zaune a tsakar gidanta ta bararraje tana aikin
karatun wani sabon littafi wanda takanas taje
bakin asibiti ta siyo,tana yi tana taunar cingam
abinta. Zanin atamfa ne a jikinta da bak'ar T-
shirt,kanta ko dankwali babu.
Gefenta kayan wanke wanke ne tuli guda k'uda
yana ta zarya akansu.
Daga d'aki kuwa,almajirinta Dauda ne ke faman
shara bisa umarnin uwardakin tasa.
A haka Anti Habiba tayi sallama ta shigo gidan.
Siyama ta mike da sauri,tabbas saida gabanta ya
fad'i ganin anti habiba a daidai wannan lokacin
da bata tab'a tsammani ba. Ta hau kame kame
"Wa alaikissalam,oyoyo anti. Ashe kina tafe
amma Jafar bai sanar dani ba. Sannu da zuwa."
"Jafar?"
Anti Habiba ta nanata a ranta,suna ne mai girma
a zuri'arsu tunda ya kasance sunan mahaifin
Hajja. Ashe har a yanzu akwai matan dakan iya
kiran sunan mijinsu gatsal basu ko jin nauyi a
bakinsu?
Tana amsa gaisuwar Siyama tana k'arewa gidan
kallo,ko iyakar wannan sun isa a kira Siyama
KAZAMAR GIDA. Mamaki takeyi na yanda gidan
mutum ke a haka har ma ta iya d'aukar littafi
tayi zaman karatu.
"Anti ya kika tsaya? Ki shigo ciki."
Anti habiba ta jinjina kanta,ta cusa kanta a
falon,daidai lokacin da Dauda ya kwashe shara ya
fito daga k'uryar d'akin Siyama.
"Na kammala Hajiya,sauran ina?"
Siyama ta dubi anti habiba wacce ta zuba mata
ido tana sauraron abunda zata ce. Ta dubi Dauda
tana 'yar dariyar borin kunya
"Uhum,kayi wanke wanken tukunna."
Bayan fitar Dauda,anti habiba ta girgiza kanta ta
soma magana cikin tsabagen takaici.
"Haba Siyama! Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!
Siyama kin bani kunya. Ashe haka kike? Kaiconki
Siyama,menene amfanin iliminki? Gidanki kaca
kaca ace har kina da damar daukar littafi kiyi
zaman karatu? Kafin ma akai ga littafi,ki k'arewa
jikinki kallo daga sama zuwa k'asa ai ko wata
jahilar ta fiki kyawun duba. Uban me kike d'auka
a karatun? Wane darasi ne aciki dake nuna ayi
rashin tsafta? A baya koda kud'i aka cemin na
yarda zaki aikata wannan shiriritar ni Habiba
bazan amince ba! Inayi maki kallon 'yar kwalliya
kuma 'yar kwalisa,menene dalilinki na chanja
akalar rayuwarki yanzu? Ace almajirinki shine zai
maki dukkan ayyukan gida? Ina laifin ma sharar
tsakar gida da cefane,amma ina shi ina tsallake
falonki har ya taka zuwa k'uryar d'akinki
sirrinki?!"
Siyama duk ta tsure,tasan anti habiba bata
dakyau wajen fad'a,ai kuwa sai yi takeyi babu
kakkautawa. Tun Siyama tana durkushe har ta
zauna ta soma sheshshekar kuka.
Karshe kuma ta shiga nasiha.
"Tsafta takan k'arawa mace daraja ta
musamman a wajen mijinta. Babu namijin da a
duniya zaiso rashin tsafta. Toh ni yanzu abunda
yafi dauremin kai shine,tayaya kike ibada? Kina
sane kuma kin karanta a makaranta komai na
addini baya tafiya saida tsafta ko? Zaman aurenki
ya sunansa?"
Anti habiba tana girgiza k'afa tayi kwafa
"Tab! Siyama kina da aiki."
Ta fad'a tana girgiza kanta,can ta k'ara dubanta
fuska a yamutse
"Batun girki kuma fa Siyama? Kina kokarin yiwa
mijinki?"
Siyama tana mutsistsika idanunta sai lokacin ta
samu karfin gwuiwar tankawa
"Inayi anti amma Jafar bai damu da cin abincina
ba."
Anti ta fusata
"Kika k'ara ambaton sunansa a gabana wallahi
sai bakinki yayi jini yanzun nan! Ke ba abun
kunya bane ki dunga kiran sunan mijinki babu
sakayawa ba komai? Kai wallahi nayi tirr da
halayenki. Ko a litattafan da kike karantawa
banda kiji ana kiran honey,darling sweety ko
kuma baban wance ko wane bakijin komai! Badai
ki tsinci mace mai tarbiyyar arziki ba tana kiran
sunan mijinta ba Siyama. Yanzu haka babu
alamar jikinki yaga ruwa. Ji gashinki yanda yake
tamkar dambun da babu mai. Gida babu gyara
babu komai,a haka wane namiji ne zai so ya
zauna har ya ci abincinki? Allah Yasa ma kin iya
girkin ba jagwalgwalo kawai kikeyi ba."
Anti Habiba ta cigaba da yi mata nasiha mai
ratsa jiki har tana tsoratata akan matukar bata
gyara ba toh fa wataran a kwana a tashi Jafar
aure zaiyi.
(9)
Bata bar gidan ba saida ta sanya Siyama a gaba
ta gyara komai tana taimaka mata. Ta tsaya a
gabanta har tayi girki anti tana fadan ai data
dunga daukar litattafan soyayya gwara ta nemi
na koyon girki. Ta sanyata tayi wanka,a wajen
sutura ma abu ya gagara. Yawancinsu duk riguna
ne zanin sun kod'e. Masu kyawun kuma babu
wanki. A karshe dai dakyar aka samu riga da
wando marasa nauyi ta sanya.
Bayan kammalawa anti ta dubi ko'ina, babu
sauran gyara,sannan ta kalli Siyama.
"Toh yanzu ko kefa Siyama,kin koma tamkar
wata sarauniya. Inda haka mijinki yake tarar dake
tsaf tsaf me zai sanyashi fargabar dawowa gida
akan lokaci?"
Siyama tayi murmushi tana sunne kanta k'asa,a
karshe anti tayi mata sallama ta tafi bayan tayi
mata alk'awarin aiko mata da spices da litattafan
girke girke na boko dana hausa....!
Tun shigowarsa yake bin ko'ina na farfajiyar
gidan da kallo. Ganin da yayi ko'ina fes sai
k'amshi ke tashi ya fahimtar dashi antinsa tazo.
Murmushi ya saki yana duban sararin samaniya
yanda ake walkiya da iska mai ni'ima da sanyi.
Fatansa Allah Yasa rayuwarsu ta d'aure a haka.
"Barka da zuwa."
"Unbelievable!" Jafar ya fada a ransa,ya d'ora da
hamdala. Kallonta yakeyi tun daga sama har
k'asa,tayi masa kyau sai k'amshi ke tashi daga
jikinta.
Mamakinsa bai k'aru ba saida tasa hannu ta
karb'i ledar hannunshi.
"Bismillah mana." Siyama ta fad'a,nauyi sosai
takeji ta k'ara kiran sunan nashi hakanan tana jin
kunyar kiransa da wani sunan da bata saba da
bai saba jin ta kirashi dashi ba. Ta gwammace ta
bar kiransa kwata kwata,gwara tayi zancenta kai
tsaye.
Ya bi bayanta,har kofar d'akinsa. Ya mik'a mata
mukullin da yake had'e dana mashin d'insa. Ta
karb'a ba tare data dubeshi ba domin idanuwansa
har lokacin sun gaza barin kallonta. Bayan sun
shiga,Siyama ta taimaka mishi wajen rage suturar
dake jikinsa. Jafar jinsa yake tamkar ba shi ba.
Yana murmushi yace
"Nagode,ya babynmu?" (Kuji fa,yau Jafar harda
tambayar baby?!)
Murmushin itama tayi alokacin da yake tab'a
cikinta.
"Lafiyarsa kalau,bebin da ake mantashi?'
Dariya yayi yana mai juyawa ya fita, ganin ya
nufi kicin tayi saurin dakatar dashi cikin
sassanyar murya
"Ai na dafa maka ruwa na had'a,yana
band'akina."
Duk da yasan bazai taddashi da kazanta ba
yau,hakan bai hanashi jin fad'uwar gaba ba. Ya
bita a baya har d'akin,band'akin a wanke a bushe
tsaf. Yayi wankansa ya shirya,a'a, sai ya k'ara
cin karo da lafiyayyen abinci an jera mishi. Ya
zage yaci sosai,ita kanta ta lura yau mijin nata
yafi koyaushe farin ciki.
Daren ranar sun farantawa juna,fatan Jafar bai
wuce Allahu Yasa Siyama ta d'aure a haka ba.
Baisan har yanzu akwai sonta mai yawa haka a
ransa ba sai a wannan daren......!
*******
"Nifa ba don komai na damu dashi ba,abunda
kike zargi don Allah ki bari. Kwanansa goma sha
shida fa rabon da ya ziyarci shagonmu koda da
niyyar gaisuwa ce. Shiyasa na damu amma ba
don komai ba."
Ladi ce ke wannan zancen,kanta akan cinyar
Mahaifiyarta.
Mama tayi dariya
"Yanzu menene ya kawo dogon bayanin nan? Toh
naji ba sonshi kikeyi ba,saidai kin damu dashi
ko?"
"Eh,a matsayinsa na yayana."
Mama ta girgiza kanta tana mai tufkewa diyarta
ta gashi
"Au haba,ashe yayanki ne? D'an babanki ne ko
d'ana?"
Ladi ta mike zaune tana turo baki cike da
shagwab'a
"Toh mutunci fa mukeyi,kema kinsha cewa yana
da mutunci. Tayaya zaki had'a irina da namiji
irinsa?"
Ta langab'ar da kai tana tab'e baki cikin sanyi
tace
"Yafi k'arfina,ya kere ni Mama. Irinmu sai marasa
gata."
Mama taji tausayin diyarta ya tsirga mata
zuciya,ta kamo hannunta
"Waya fadamaki Sarah? Kina da Allah. Hakanan
ni mahaifiyarki ina tare dake. Ba don ma mutuwa
mai raba tsakani ba,da yanzu mahaifinki yana
nan tare damu. Sannan ke ba macen k'i
bace,bamu da kud'i bamu da kyau. Amma
zuciyoyinmu masu kyau ne. Watarana zakiyi
mamakin mijin da zai nemi aurenki Hadiyya. Kada
ki dauki zancena a hagunce,ba lallai sai mai kud'i
ba,kodayaushe addu'a na Allah Ya kawo maki
mijin da zai jib'anci al'amuranki,zai baki kulawa
har karshen rayuwarsa."
Ladi ta sunkuyar da kanta tana murmushi
"Allah Yasa mamana."
"Amin Hadiyya. Don haka ba Jafar ba,sai kiga
Allah Ya had'aki da wanda yafi Jafar. Ai shi Allah
babu ruwansa da kud'i ko talauci,matukar Ya
kaddaro zaka auri mutum koda ace shine sarkin
masu kud'in duniya,ko kuma shine wanda yafi
kowa talauci."
Ladi ta jinjina kanta,tabbas gaskiya Mama ta
fad'a. Ta damu da lamuran Jafar,hakanan tana
tsoron ya kasance wannan yanayin da takeji a
zuciyarta game dashi shine SO. Ambaton hakan
saida gabanta ya fad'i.
Ta k'ara maida kanta cinyar mama idanuwanta a
lumshe,murmushi dauke akan fuskarta.
"JAFAR"
Ta maimaita sunan cikin ranta,a hankali ta soma
ayyano kamanninsa. Dogo ne,baya daga layin
kyawawa saidai bazaka kirashi mummuna ba.
Yana da cikar suma,bashi da wani hanci saidai
masha Allah akwai idanuwa.
Ta muskuta tana murmushi har a lokacin,duk
shigar da Jafar zaiyi ita kam burgeta take. Bata
fiye ganinsa da kananun kaya ba sai jefi jefi. Toh
a ajiye duka wadannan ma a gefe,haka kawai
take kaunarsa. Halayensa sukan burgeta
matuk'a. Bashi da girman kai,baya daukar duniya
da zafi. Yakan dauki kowane mutum da
daraja,baya kyashin bawa kowa girmansa
matukar ya girme masa. Wannan yasa shima
mutane kan ga mutuncinsa sosai,ciki kuwa harda
ita. Bata tab'a cin karo da namijin da ya burgeta
ba irinsa. Kodayaushe bata sakarwa customers
fuska,don batason abunda zai janyo wani cikinsu
ya gayamata zancen banza kamar yanda wani ya
tab'a gigin yi. Tun daga lokacin ta chanja fuska.
Jafar kuwa yawan zuwansa ne ya sanya ta saba
dashi,saida ta lura shi d'in kamilin mutum ne
sosai kuma yakan girmama mamanta. Abunda ya
janyo mishi samun matsayi babba a zuciyar
Ladi....!!!!
(10)
Rayuwar Jafar da Siyama sai godiyar Allah domin
a kashi d'ari na k'azantarta,ta rage ashirin. Har
lokacin dai shine mai yiwa kanshi gyaran d'aki da
band'aki. Tun wata rana da tace ya bar mata
zatayi. Dadi ya cikashi ya cire mukullayen daya
had'asu dana mashin d'insa ya damk'a mata.
Saidai fa ya dawo yaga ba daidai ba,domin saika
ka rantse yarinya mai shekaru goma tayi
gyaran,k'asan ma sai k'arni,da yayi magana tace
ai daga mopper d'inne. Band'akin ma tashin
k'arni yake,nan ma tace ita kam batasan
matsalar ba. (Alhalin Dauda ne mai wankin toilet
d'in).
Tun ranar ya daina bar mata mukullayensa
acewarsa nauyi yayi nata yawa ga ciki ga
ayyuka? Hakan yayi mata dad'i,har ma alokacin
ta kasa b'oye farin cikin nata.
Watarana suna zaune a falonta,Siyama tana
kwance tayi matashi da cinyarsa tana game d'in
Candy Crush a wayarta. A hankali kuma yake
shafa gashinta yana bin d'akin da kallo. Ya dubi
sama yanda yaga Yana ta cika d'akin. Girgiza
kansa yayi ya dubeta
"Siyama na tambayeki mana."
Ta dubeshi alamar tana saurare
"A gida bakya yiwa Hajiya aikin komai ne?"
Ta tab'e baki tana girgiza kanta
"Gaskiya Hajiya bata sanyani aiki,komai sai 'yar
aikinta ce takeyi. Sannan kaima shaida ne
batason bacin raina,koda an sanyani wani aikin
girkin,musamman ma yaya hanif yafi kowa
matsamin anan bangaren. Matukar na b'ata raina
Hajiya sai tace nayi zama na. Sukan yawaita yin
fad'a da Hajiya akan ta hanani koyon aiki
musamman girki wai wannan ba yi bane. Amma
Hajiya saita bud'e mishi wuta. Akwai sadda
Hajiya ta fita unguwa,Abba ya shigo ya hangi
Saude a kicin tana fama da girkinsa. Ya k'araso
d'akin Hajiya ya iskeni ina chatting. Wallahi Jafar
saida ya zanemin jikina,sannan yace daga
wannan ranar kada na k'ara tsallakewa har a
gama aikin abinci bai ganni a kicin d'in ba.
Tun daga ranar na soma jagwalgwalawa har na
iya kad'an kad'an,don sai naji muryar Abba nake
fad'awa kicin d'in.
Kafin auren su anti rumaisa,sune masu yiwa
Hajiya gyara sai bayan anyi musu ne Saude keyi.
Hum,a wannan lokacin Hajiya shiyasa tafiso nayi
aure da wani mai kudin wanda acewarta saidai
ina kwance ayimin kowace hidima."
Jafar ya jinjina zancen bayan ta kammala,
"Ke kuma kika nace sai talaka ko?"
Ta muskuta tana duban fuskarta
"Kaima kasan alokacin ko yankani za'ayi,bazan
fasa sonka ba."
Yayi murmushi kawai.
********
Misalin takwas na dare sukaci kwalliya ya
dauketa a mashin sai gidan Haris. Dayake sun
san da zuwansu,suna isowa Haris ya fito ya
tarbesu da murna. Ya dubi Siyama
"Amarya munyi maki fushi."
Tayi dariya "Ayi hakuri,kaga mai laifi nan."
"Kuma fa gaskiyane. Ku k'araso mana."
Suka shiga,kamshi mai dad'i ya bugi hancinsu.
Komai tsaf yake gwanin sha'awa. Yaron Haris
mai suna Aliyu yana rarrafe abinsa. Jafar ya
d'agashi cak yana mishi wasa sai b'angala dariya
yakeyi. Yana son yaron,ji yake tamkar shine ya
haifeshi. Haris yayi ciki yana kira
"Ummina! Ummina!!"
Jafar ya saci kallon Siyama wacce ke k'arewa
gidan kallo cike da sha'awa. Ita kanta komai na
falon ya burgeta,saidai ta soma tunanin Kawai
don Ummin ta kasance 'yar gidan masu hannu da
shuni shiyasa falonta ya k'awatu batasan cewa
gyara ma wani abun bane!
Suka dawo tare da Ummi. Matashiya ce bata
wuce shekarun Siyama ba,ashirin da biyar. Taci
ado cikin doguwar rigar nan ta kanti 'yar yayi.
Fuskarta ba wata kwalliya tayi ba daga hoda sai
lipgloss data sanya amma tayi kyau. Tana
murmushi ta zauna kusa da Siyama daidai
lokacin da Jafar ke zolayarta
"Uwargidan Rahma."
Ummi ta harareshi tana dariya
"Wacece Rahma? Na gayamaku bana kishi da
ita."
Haris da Jafar sukayi dariya,Jafar yace
"A'a fa maman Aliyu,kada fa kiga abu ya tashi
gadan gadan ki nuna bakisan zance ba."
Ummi ta tab'e baki had'e da dariya
"Ai na gayamaka ko Albarka ne sunanta ni Ummi
bata gabana. Yaje yayi aurensa mana. Nidai ka
gayamasa kada ma ya had'ani da ita zaman gida
d'aya."
"Ballantana ma ba auren nayi niyyar yi ba."
Haris yayi saurin fad'a cike da fargaba. Ya tuna
farkon ranar da ta daga wayarsa yana band'aki
jin mai kiran tace rahma ce, a daren basu kwashe
da dad'i ba.
Ummi dai ta mik'e tana jan hannun Siyama
"Ku kuka sani, nidai na fadamaku sharad'ina
amma ban hanaku aurenku ba. Kawata zo muje
ciki ko?"
Jafar wanda ke dariyar mugunta ba tare da ya
lura da hararar da Haris ke watso mishi ba yace
"Toh bari nayi mishi rakiya zance."
Bata ce uffan ba,haushin Jafar duk ya cikata.
Ummi itama fa akwai kishi.
Suna shigewa,haris ya kai mishi duka
"Kaidai anyi d'an iska,wallahi yau fa ka had'amin
bomb. Shikenan yau za ayimin bore."
Suka sanya dariya
"Ai gwara dai ka fad'a mata tun abu baizo ya
kankama ba."
Haris ya girgiza kanshi cike da damuwa
"Nifa ina ganin na fasa auren nan tunda Ummina
bataso na hakura. Ranar nan nake gayamaka
kada kaso kaga da yanda muka shirya da ita."
Jafar ya girgiza kansa ya zama serious
"Ba don raya sunna kakeson yi ba dana baka
shawarar ka hakura. Kai bari na fadamaka,kaga
Siyama ta isheni a rayuwa. Banga wata a duniya
da zata isheni kallo ba. Koda Allah Ya kaddaro
zan k'ara aure ko?"
Ya tab'e baki yana girgiza kansa
"Badai don inaso ba,sai don KADDARA."
Haris yayi murmushi
"Nikam son Rahma nakeyi. Jafar ni kaina koda a
mafarki ban taba zaton bayan Ummi zanso wata
d'iya mace ba,duba dai ka gani. Ummi bata rage
a komai ba,tana da tsafta ladabi da biyayya.
Tana bani kulawa sosai da sosai,kawai dai a
lokaci guda Allah Ya sanyamin kaunar Rahma a
zuciyata."
Jafar ya jinjina kansa,shima fatansa Allah Yasa
matarsa ta gyara d'abi'unta. Babu laifi dai a
yanzu ana kokarin bashi hakkinsa,ana kulawa
dashi,saidai har yanzu tsaftar ragaggiya ce ba
kad'an ba.
Sukayita hira abinsu.
A d'aki ma Ummi albums na biki dana sunan
Aliyu ta ajiyewa Siyama. Tana kallo suna hirarsu.
Can Ummi ta fito ta jera abinci akan kafet bayan
ta shimfida leda.
Suka had'u gaba daya,sai lokacin ummi ta
sakarwa Jafar har suna dariya don d'azun ma
kishi ne.
Basu bar gidan ba sai goma da mintoci na dare.
Siyama ta samu alheri mai yawa a wajen Ummi
dana sutura dana kaya! Tayi godiya sosai,suka
rakosu har wajen mashin d'in Jafar sannan suka
koma ciki.. !.
KAZAMAR GIDA *******11
Ladi tana daga cikin d'an d'akin da suke ajiye
kayayyakin kwanukansu da tukwane harma da
sauran tarkacensu na girki,kamar daga sama taji
muryar Jafar suna gaisawa da Mama. Tayi wuf ta
fito har tana kokarin fad'uwa. Suna had'a ido ta
sauke ajiyar zuciya tana murmushin farin ciki.
Kamar bashi ba,yayi y'ar k'iba.
Jafar yana dariya yace
"Yar nijar kwana biyu?"
Ladi fuska a sake ta gaidashi,taji dad'in ganinshi
har ma ta kasa b'oyewa. Bayan sun gaisa tace
"Yayana ai kaine ka b'uya,shiru ba'a ganinka."
Jafar ya shafi sumar kansa
"Ya za'ayi,sai a hankali. Yau ai ganinan ko? Ya
karatun?"
Ta d'ago ta dubeshi tana murmushi
"Karatu alhamdulillah gashi muna ta shirye
shiryen zana jarrabawar karshe na sakandire. A
sanyamu a addu'a."
Ya bud'e baki
"Ikon Allah,yanzu Ladi har zaki kammala
sakandire? Kina kankanuwa dake?"
Taji babu dadi,ita fa bata daukar kanta a yarinya
kwata kwata. Saidai gaskiyarsa,shekaru sha
bakwai ai dole a kirata yarinya. Ta wayance da
dariya cikin marairaicewa tace
"Yayana shekaruna sha bakwai fa."
"Oh kina nufin kicemin kin girma ko?"
Ya k'arashe yana dariya. Itama dariyar tayi ta
mike
"Oh yayana,nikam bance ba. Za'a kawo wani abu
ne?"
Yana murmushi yace
"Bani favourite d'ina saidai fa bada yawa ba."
Cike da farin ciki ta juya,Mamanta tana ta aikin
zuba abinci a farantai ta sanar mata yanason
tuwo. Kafin mama ta zuba ta mik'awa masu
zaman jira nasu sannan ta koma ta karb'o mishi.
Duk abunda takeyi idanuwanta bini bini suna
gareshi. Hankalinsa yana kan wayarsa har ta
dawo ta ajiye mishi. Yayi godiya. Ta koma ta
zauna anan wajen Mama. Tana yi tana satar
kallonshi daga ta lura zai kallo inda take sai tayi
saurin maida kanta ga kwanukan dake gabanta.
Can jimawa kuma ta k'ara kallonshi.
Mama tana lura da ita,murmushi kawai tayi cike
da tausayin Hadiyya. Lallai kam ta fad'a son
maso wani wanda k'arshensa bai fiye zama mai
dad'i ba.
Sai bayan Jafar yayi musu sallama zai tafi ne,tayi
saurin bin bayanshi. Mamanta ta bita da kallo
tana mai mamakin me kuma ladi zata gayamasa?
Fargabarta kada ya zamto zata ce sonshi
takeyi,amma idan hakane bata kyautawa kanta
ba.
Ita kuwa Ladi saida ta bari sun matsa kad'an
daga shagon tace
"Yayana daman cewa zanyi ko zaka bamu
lambarka,kaga daka jima baka lek'omu ba duk
mun damu saidai sanin da mukayi kana da iyali
bamu takura ba. Inda hali ko zaka bamu
lambarka sai a dunga gaisawa wataran saboda
irin haka ko?"
Jafar bai kawo komai ba,murmushi yayi yace
"Kuma nima nayi wannan tunanin,naso sanin
gidanku sadda Mama tayi rashin lafiya. Allah
baiyi ba."
Ya karb'i wayarta,'yar Nokia ce k'arama "express
music" secondhand ce. Ya shigar da lambobinsa
ya mik'a mata yana murmushi
"Gashinan 'yar nijar."
Tayi godiya,sukayi sallama yayi kasuwa.
Mama ta dubeta cike da zargi,Ladi ta sakar mata
murmushi.
"Me kikace mishi?"
"Bakomai fa mama,lambarsa kawai na karb'a
saboda irin haka idan ya tafi mukaji shiru kinga ai
da dad'i muji ko lafiya, ko?"
Mama ta tab'e baki,suka cigaba da aikinsu.
Cikin ikon Allah,rayuwa tana tafiya har aka shiga
watan azumin Ramadan. Lokacin watannin cikin
Siyama hud'u da kwanaki.
Alokacin Siyama ta k'ara zama malalaciya,bata
son yin aikin komai kullum cikin bacci take. Ta
k'ara k'iba abinta. Jafar kam hankalinsa ya
karkata sosai wajen kula da ita,baya takura mata
akan aiki. Hakanan yake lallab'awa suna ragewa
tare da Dauda. K'arshe ma ganin an yiwa
kannensa hutu ya nemi alfarma,Hajja tace
sam,dakyar dai, da kuma sanya bakin Alhajinsu
ne, Hajja ta bashi damar tafiya da Bahijja. A
hanya suna tafe a mashin ya dubi Bahijja ta
gilashi fuskarsa a daure
"Saura kuma kiyi recording abubuwan da zaki
tarar ki barbazamin sirrin gida. Ki iya bakinki."
Bahijja dariya taso kubce mata,toh wai wanene
ya gayamishi ma basusan Anti Siyama KAZAMAR
GIDA ce ba? Tun kafin auren babu abunda basu
sani ba tare dasu Husna don ko rannan taji Hajja
tana mita bayan taje gidan. Lallai ma Jafar
baisan kazantar Siyama ta gama cika danginsu
ba.
Hankalin Bahijja ya tashi kwarai ganin yanda
gidan ya koma wai ma a hakan don Jafar yana
tattarawa. Tana yamutsa fuska har ta soma
kyankyami,anya zata iya sati biyun nan kamar
yanda Hajja ta fad'a? Jafar ya dubeta gira a
had'e
"K'araso ciki kin tsaya kina kalle kalle."
Ta shiga da sauri. Siyama tana kwance tana
amsa wayar yayarta rumaisa. Batun wani biki
sukeyi daya danganci can dangin Hajiyarsu da
za'a gudanar bayan sallah. Da murnarta ta tarbi
Bahijja.
"Ina su Hajja? Yau kifin ruwa kece kika yarda
zakizo gidana? Lallai my J kayi kokari."
Bahijja sai yak'e takeyi,tamkar ta mik'e ta rufeta
da duka takeji. Ita kanta Siyamar a hargitse
take,ko ita da bata da kyawun fuska ta fita tsaf
tsaf. Jafar ya mike
"Ai Hajja tana tausayamaki ne,kinga ga azumi ya
nufomu ga ciki hidimar sai tayi maki yawa."
Ya dubi Bahijja
"Shiga ki ajiye kayanki ki fito ki hau gyara. Ni zan
koma kasuwa."
Bahijja ta mik'e
"Yaya a dawo lafiya."
Tayi jim ta gani ko Siyama zatace wani abu koda
addu'ar ne amma ina,saima tambayar data
jefowa Bahijja.
"Allah Yasa Hajja ta baki gasarar tawa."
Bata ce mata uffan ba tayi d'aki,gadon a gyara
yake,hakanan d'akin a share. Ta tabbatar da
wuya idan ba Jafar ne yayi ba.
********12
Haka Bahijja tayi zaman bauta a gidan,sannan
iyakacin kwanakin da tayi ta gama jin kaunar
Siyama ta sire a ranta. Banda ma jininta ce babu
yanda zatayi da ko hanyar da take bi bazata kalla
ba. Ta gama k'uluwa a lokacin da azumi yakai
sati biyu cif amma Jafar ya hanata tafiya ko'ina
yace ya sanarwa Alhajinsu cewar bazata koma ba
sai bayan azumi. Wayyo! Tamkar Bahijja ta d'ora
hannu akanta. Babban abunda yafi bata bakin ciki
idan an ajiye kazantar Siyama gefe bai wuce
yanda ko kusa bata kula da girki da komai na
mijinta ba amma an iya idan ya dawo ayita
nad'ewa a jikinshi kamar mage ko kunyar Bahijja
bataji. Batasan amfanin karatun littafi ba ga wasu
mutanen! Daga mazan har matan mafi yawansu
sunfi mayarda hankulansu ga nishad'in dake a
littafin ba wai darusussukansa ba! Ina amfanin
mace mai bin bokaye tana daukar littattafan
hausa ta karanta amma bata daukar darasi ko
d'aya? Ina amfanin maza masu wulakanta
matansu sannan suna karatu amma komai baya
shiga kwakwalwarsu na darasi. Meye amfanin
karatun da akeyi ba a koyi da darussan cikinsa?
Ta girgiza kanta cike da bakin ciki lokacin da ta
janyo littafin da Siyama ke karantawa a
yanzu,ZURFIN CIKI.
Tsaki taja,Allah wadaran wasu matan. Tabbas
Siyama tana bukatar gyara sosai a rayuwarta a
sanin da tayi cewar yayanta fa d'an kwalisa ne
tun yana gidansu. Tana jiye mata tsoron kada
watarana ya gaji. Ta tab'e baki ta maida littafin
mazauninshi ta cigaba da jan casbaha tana
salati....!
*********
LADI...!
Ladi tana tsaye,Mama tana yi mata gargad'in
kada ta fita yanzu zasu je su dawo daga dubiyar
wata makwafciyarsu da yaronta ya k'one a
asibiti.
"Yanzu zan dawo ki tabbatar kin rufe..."
"Wai Binta kodai muyi gaba ne?"
Muryar makwafciyarsu Harira ya katse Mama.
Tayi saurin ficewa Ladi na yi musu addu'ar
dawowa lafiya. Bayan sunyi nisa,ta dawo da
saurinta ta rufe k'ofar. Cikin d'oki ta bud'e jakar
makarantarta ta fiddo katin mtn da take faman
ajiyarsa kusan sati biyu da kwanaki kenan da
niyyar kiran Jafar. Sai yau ta samu damar.
Bayan ta tabbatar da katin ya shiga ne,ta lalubo
lambar Jafar ta danna kira. Lokacin k'arfe hud'u
na yamma,ta tabbatar yana kasuwa. Kasancewar
azumi ne,basa fita sai bayan la'asar hakanan sun
d'aukarwa kansu hutun shiga kasuwa ranar
Alhamis da juma'a don su samu dama sosai na
yin ibadarsu. Jafar kuma rabonta dashi tun kafin
azumi.
Wayar tayi ta ringing ba'a dauka ba har ta katse.
Cikin damuwa ta soma kok'arin k'ara danna kira
sai kuma gashi ya biyo baya. Saida taji fad'uwar
gaba,dakyar ta iya d'auka.
"Salamun alaikum."
Ta amsa cikin siririyar murya. Ta k'ara da cewa
"Yayana barkanka da yammaci,ya azumi ya
kasuwar?"
Jafar dake tsaye yana k'ok'arin fiddowa wasu
'yan mata material ya amsa
"Yauwa barka dai,mun gode Allah. Saidai ban
gane me maganar ba."
Tayi dariya cikin wasa tace
"Hadiyya ce."
Jafar dayake hankalinsa yana ga aikinsa,yace
"Banganeki ba,amma ki bani mintuna ina zuwa."
Ya ajiye wayar suka cigaba da maganar kud'i da
yan matan,sun jima suna bugawa k'arshe ya
hak'ura ya siyar musu a farashi mai sauki sauki.
Saida ya sallamesu ne,ya zauna ya d'auki
wayarsa,lambar ya gama k'arewa lambar kallo
"Hadiyya?"
Mamaki yakeyi,toh wacece kuma Hadiyya? A ina
ta samu lambarsa? Ya tab'e baki ya k'ara danna
kiranta kamar yanda yace mata.
Ladi dake zaune tana duban wayarta,tuni
zuciyarta ta kissima mata wata
shawara,murmushi kawai takeyi tana mai fatan
Allah Ya bata nasara ta ida nufinta na alheri.
Kwatsam kiransa ya k'ara shigowa,tayi saurin
d'auka. Bayan sallama Jafar ya sake maimaita
tambayarsa cikin muryarsa tausassa
"Malama Hadiyya,ko zan iya sanin wacece ke? A
ina kika samu lambata?"
Ladi ta k'ara kwantar da muryarta
"Ba lambar yayana Abdullahi bane?"
Ya girgiza kanshi tamkar tana ganinshi
"No,bashi bane. Am sorry,wrong number kikayi
dialing."
"Ayya,bakomai nagode."
Bayan sun ajiye wayar ne,ta tsaya tsam tana
kallon wayar,kwallah ta cika idonta. Anya hanyar
da take shirin bi zata b'ullar da ita? Ko zata tura
masa sak'o ta sanar dashi cewar Hadiyya itace
Ladi? Zuciyarta sai k'arfafa mata gwuiwar yin
hakan takeyi,saidai kuma bata da kuzarin aikata
hakan tafi kaunar Jafar yasan tana sonshi akan
su cigaba da zumunci matsayinsa na customers
nasu.
Daga haka ta share batun ta ajiye wayarta ta hau
aikin abincinsu na shan ruwa.....!
*********
Har akayi kwanaki biyar,azumi yana cikin kwana
ashirin da d'aya. Bata k'ara kiransa ba,sai ana
ashirin da biyu ta tsara text na barka da shan
ruwa ta aika mishi a k'arshe ta sanya sunanta
Hadiyya.
Shi kuwa lokacin yana faka mashin d'insa ne ya
dawo gida. Jin shigowar message,yaja tsaki.
Yana tunanin watakila ya chanja layinsa daga
Mtn zuwa Airtel. Ya gaji da sakonni marasa kan
gado da suke yawan turowa. Don haka bai ko
bud'e ba ya share.
Ya tarar Bahijja tayi komai ta jera musu akan
leda a k'asa. Bayan sunyi mishi sannu da zuwa
ne ya shige d'akinsa. Saida ya soma kokarin
sanya wayar a chaji ne ya lura message fa bana
kamfani bane. Ya d'auka ganin lambar da yake
tunanin ya tab'a saninta. Bayan ya kammala
karantawa a k'arshe yaga sunanta. Abun ya
tsaya a ranshi,toh ita kuma wannan yau d'inma
kuskuren ne ko kuwa dai tana sane? Oho. Ya
tab'e baki har zai goge sai yaga kyan yayi mata
godiya. Don haka ya aika k'aramin sak'o gareta
"Jzk Allah khair. Sm 2 u."
Daga haka ya jona chaji ya tafi domin shan ruwa.
********13
Ta nanata yafi sai talatin,sanyi ya mamayeta
domin har ta fidda rai jin da tayi shiru baice
komai ba. Mama ta tsura mata ido ganin tana ta
doka murmushi
"Lafiya? Ko kema an maki kyautar dubu talatin
d'inne a waya?"
Tayi dariya ta girgiza kai,ai wallahi Jafar ya fiye
mata dubu talatin.
"Ko kusa,kawai labarin ban dariya kamfanin mtn
suka aikomin ne."
Mama ta gyada kanta batace komai ba.
Tun daga ranar kullum Ladi saita turawa Jafar
sak'on gaisuwa,har ta soma gundurarshi. Ita
kuwa wannan 'yar godiyar da yake turo mata ne
takejin dad'insa sosai. Saida taga har tayi sau
uku bai turo ba yasa ta ja da baya gudun kada fa
ya soma ganin bak'inta....!
RANAR SALLAH...
Ya had'e cikin farar shadda tasha surfani. Yana kokarin
dora hularsa ne idonsa yakai kanta ta madubi. Tana kwance
abinta akan gado da tsohon ciki,daga ita sai riga da wando
na bacci kan ko d'ankwali babu sai kyalli yake sakamakon
relaxer daya takura mata sukaje da Bahijja aka sanya
musu. Kallonsa kawai takeyi babu abunda ke yawo a
idanuwanta sai zallar tsananin so da kaunarsa. Murmushi
yayi ya d'aga mata gira
"Kallon nan fa?"
Ta kauda idonta tana basarwa ta hanyar zuro kafafuwanta
k'asa da mik'ewa tsaye
"Uh uh,ina laifi a ciki don na kalli mijina? Kyau kayimin."
Yayi dariya yana mai janyota jikinsa
"Zan tafi masallaci,bayan addu'ar haihuwa lafiya,wacce
kuma kike bukata?"
Ta tureshi kad'an tana turo baki
"Kishiya."
Haka kawai yaji gabanshi ya fad'i ba tare da yasan dalili
ba. Ya dad'a janyota yana murmushi
"Ita kike so?"
Ta harareshi
"Itace banaso kuma kaima shaida ne."
Ya shak'i k'amshi gashinta yana mai lumshe ido
"Bari fargaba Siyama,banda ra'ayin ajiye mata biyu kinji
ko?"
Tayi murmushi tana mai sauke ajiyar zuciya,ita kanta tasan
Allah Ya d'ora mata son Jafar sosai. Ganin yana kokarin
fad'awa wata jahar tayi saurin tureshi
"Kai kam bansan sunanka ba,ka fiye takura mutum. Zaka
makara fa."
Yayi saurin duba agogo,ya ja karamin tsaki
"Kinga kuwa na kusa."
Ya d'ora hularsa ta zauna daram,wayoyinsa biyu,da
karamar Nokia da BB ya sanya a aljihunsa. Ya dubeta
"Shikenan,sai an sauko."
Ta gyada kanta yayi gaba domin kuwa tun zuwan Bahijja ya
bar tafiya da mukullinsa acewarsa kada ta sanya ido takai
maganar gidansu ya zama tsegumi.
Daga masallaci Jafar gidansu ya soma zuwa. Wajensu
Siyama ya fara shiga. Hajiyar Siyama da ma aikatan gidan
sunyi kace kace suna aikin sallah. Yayi sallama ya shigo.
Kallo d'aya tayi mishi ta had'e fuska don daman tunda taji
labarin Bahijja tana wajen Siyama ranta ke a b'ace a
cewarta don me Siyama bata fad'a mata tana neman
mataimakiya ba. Haka tayi kiran Siyama ta bud'e mata
wuta,har da fad'in matukar bazata fita harkar gidansu Jafar
ba wadanda sam ba kaunarta sukeyi ba toh lallai kuwa tana
tare da wahala. Siyama ko Jafar bata fad'awa ba gudun
kada ransa ya b'aci.
Ya durkusa ya gaisheta,ta amsa dakyar. Ya cigaba da yi
mata fatan alheri na kammala azumi lafiya amma tayi
burus dashi. Ganin haka ya mike yana amsa gaisuwar ma
aikatan kafin ya juya ya shige sashen Abba.
Abba yana zaune yana amsa waya,shima yaci adonsa na
idi,babbar rigarsa tana ajiye a gefe. Jafar yayi sallama ya
shiga,saida Abba ya ajiye wayar sannan ya dubeshi fuska a
sake.
Bayan gaisuwa ya tambayi lafiyar iyalinsa,Jafar ya amsa
mishi da kowa lafiya. Abba ya jinjina kansa
"Ina fatan babu wata matsala?"
Jafar yayi saurin amsawa
"A'a Abba,komai Alhamdulillah."
"Toh Masha Allah,sai a cigaba da hakuri. Allah Yayi maku
albarka."
Yaji dadin addu ar ya amsa da amin,sun jima suna hira
kafin Jafar yayi masa sallama ya fita zuwa gidansu.
Yana kwance akan kujerar Hajja ne wayarsa tayi k'ara. Ya
janyota ya duba. Lambar Hadiyya ce kamar yanda yayi
saving. Ya manta rabon ma da ya tsinci sak'onta a
wayarsa,ya manta da lamarinta gaba d'aya. Kamar bazai
amsa ba saidai ya danna yana mai karawa a kunnensa
"Assalamu alaikum."
Ya fad'a cikin sanyin murya,ta amsa da nata muryar data
kere nashi a sanyi da kuma dad'i.
"Wa alaikassalam,barka da sallah Abokina. Anyi sallah
lafiya?"
"Aboki?" Ya nanata a zuciyarsa,saima ta bashi dariya,yayi
murmushi
"Alhamdulillah,saidai ni sunana Jafar not Aboki."
Tayi 'yar dariya
"Madallah da wannan daddad'an sunan. Ina fatan ban
matsawa rayuwar yaya jafar ba?"
Haka kawai yaji ta burgeshi,yayi murmushi karo na ba
adadi
"Kin kusa dai Hadiyya. Kema ina fatan kinyi sallah lafiya?"
Ta marairaice murya
"Ka sanyayamin jikina yaya jafar,kayi hakuri don Allah.
Wallahi hakanan naji kawai jinina ya hadu dakai a tun ranar
dana soma jin muryarka."
Ya girgiza kai kamar tana ganinshi
"No,is ok. Kada ki damu kanki ai mutum rahma ne. Nagode
ki gaidamin 'yan gidan naku saida anjima."
Yayi saurin katsewa,daidai lokacin Hajja ta shigo dauke da
kulolin abinci yayi saurin karb'ar mata ya ajiye.
"Ikon Allah,daman kazo ne?"
"Na shigo Hajja,naga kuna aiki ne shiyasa na zauna na d'an
huta."
Ya gaisheta,suka d'an tab'a hira kafin ya wuce wajen
Mahaifinsa. Nan ma ya jima sannan yayi musu sallama ya
tafi.
Lafiyayyun girke girke ya tarar,yasan aikin Bahijja ne.
Siyama itama anci kwalliyar sallah. Bahijjah ta gaisheshi ya
amsa mata,sannan ta basu waje ta koma domin cigaba da
tattare kicin d'in......!
***********
Shak'uwa ta fara neman shiga tsakanin Jafar da Hadiyya.
Har ya zamana Jafar kan d'auki wayarsa yayi kiranta idan
yaji shiru kwana biyu. Yanason hira da ita, tasan abunda ya
dace ta fad'a tasan wanda bai kamata ba. Hakanan akwai
ta da barkwanci wannan tasa sau da yawa idan Siyama ta
b'ata ransa yakan mance idan yana tare da ita.
Akwai sadda Haris ya iskeshi a shagonsu yana waya yana
tuntsirar dariya. Ya zuba masa ido har ya kammala,ya lura
da mace yake wayar. Jafar ya dubeshi yana harararshi
"Menene kuma kakemin wannan kallon?"
Haris bai bar kallon nashi ba ya sauke ajiyar zuciya yana
murmushi
"Ina kallon sabuwar soyayya ne."
Jafar ya ja tsaki,ibrahim dake jera atamfofi ya hau dariya.
"Kaima dai ka kula kenan Haris,ni ai dayake ya rainan wayo
k'aryatani yayi da cewar yar uwarsa ce."
Jafar ya girgiza kanshi yana tab'e baki
"Kudai kam banda sa ido baku ajiye komai ba. Hadiyya
tamkar kanwata na dauketa. Wani abu?"
Sukayi dariya,Haris yace
"Babu komai kam,ai daman da haka da haka ko ya kace
Ibrahim?"
Ibrahim dariya kawai yake yana kallonsu. Jafar ya daki
cinyarsa
"Banason sharri,yarinyar tana da hankali. Garin neman layin
wani yayanta ne muka had'u ta waya shine muke gaisawa
amma kun kama kuna juya magana. Taso kayimin rakiya."
******14
Suna dariya Haris yana fad'in
"Ahaf,ai na fadamaka daga haka daga haka za'aji sabuwar
magana,'yar ina ce?"
Ya d'aga kafad'a bayan ya mik'e tsaye
"Ina na sani? Ban tambayeta komai nata ba."
Suka kama tafiya,Haris yace
"Wai ina zamuje? Nifa na kusa komawa ofis kafin Baffa ya
bincika yaji bana nan ya hau fad'a."
"Yunwa nakeji,yau dai saika d'and'ana girkin shagonsu
mama da nake yawan baka labari."
Haris ya zaro ido
"Au,wai kai har ila yau baka bar zuwa ba?"
Jafar cike da damuwa yace
"Ta yaya zan bari bayan waccan kazamar gidan bata
chanja ba? Nikam abubuwanta sun isheni. Kana gani fa
hatta anti tazo takanas tayi mata fada da nasihu amma a
banza. Haka akeso na zauna na k'are rayuwata?"
Haris yace
"Tab! Toh Allah Ya kyauta. Siyama kuma sai addu'a abun
yayi tsamari."
"Barta ta cigaba dai,zanyi maganinta matukar bata gyara
ba."
Haris ya kalleshi. "Me zakayi?"
Jafar yayi mishi wani irin kallo kafin yayi murmushi,Haris
tuni ya d'ago zancen,ya nunashi da yatsa
"Kasan Allah ka rufawa kanka asiri,baka ganin yanda na
rame kwana biyu? Aure ba abune mai sauki ba,yanzu haka
ma baro ummina cikin fushi. Gaba daya ta tashi
hankalinta,musamman ganin yanda akayi gyara gyaran
gida,sai ta hau fad'an wai meyasa banyi ba tun a baya
saida zan k'ara aure? Hakanan dole saida ta sanyani a
gaba na kaita taga gidan Rahma taga baifi nata komai ba
sannan hankalinta ya d'an kwanta. Toh yau da safe kuma
ganin katunan daurin aure duk saita hargitsemin. Zaman
ofis ne ya gagareni shiyasa ka ganni anan. Banason bacin
ran Ummina ko kusa,ji nakeyi tamkar na fasa auren nan
saidai inason Rahma sosai."
Jafar yayi dariya ya girgiza kai
"Allah Sarki,maza muna hakuri. Ta ko'ina ba sauki saita
Allah. Kayi hakuri fa,na tabbata zafin kishi ne don kanta
zata zo ta sauko. Kaidai ka dunga kokarin kwatanta adalci
domin Allah. Ai Ummi akwai hankali,na tabbata yanzun ma
kishi ne kawai amma ka d'an bata lokaci."
Ya jinjina kansa daidai lokacin da suka iso shagon. Ta
hangoshi batasan lokacin data saki ajiyar zuciya mai k'arfi
ba had'e da murmushi musamman ma idan ta tuno da
yanda yake hira da ita a yanzu sosai ta waya. Suka zauna
bayan sunyi sallama. Mama tana dariya tace
"Ikon Allah,yau dai kaine mutum na farkon soma ziyartar
shagon nan cin abincin rana Jafar. Barkanku da zuwa."
Suka dubi juna shi da Haris sukayi murmushi. Haris yana
mamakin yanda har suka saba da amininsa har haka.
Ladi ta nufosu a nutse,ta durkusa ta gaishesu murmushi
yak'i yankewa akan fuskarta. Suka amsa ta nemi sanin
abunda suke buk'ata Jafar ya harareta cikin wasa.
"Yau kuma sai an tambayeni?"
Tayi dariya
"Lah yayana ai gani nayi kaida bak'o....."
"Wannan aminina ne Haris sunansa. Ba bak'o bane saidai
ba'a nan kasuwa yake zaune ba."
Ta k'ara duban Haris wanda ke k'are mata kallo tayi
murmushi
"Ayya,barka da zuwa yaya haris, kai kuma me za'a kawo
maka?"
Ya girgiza kansa zaiyi magana,Jafar ya tareshi da sauri.
"Kawo mishi tuwon shima."
Bayan tayi gaba,Haris ya harareshi
"Kanason k'ara jawomin fitina kenan ko? Ban koma gida ba
nasan dole Ummina ta nemi sanin inda naci abinci."
Jafar yayi dariya
"Yau fa d'aya Haris, so nakeyi ka d'and'ana girkin mutanen
nan wallahi akwai dad'i sannan komai nasu a tsaftace. Ji
yanda wajen ke tashin k'amshi kamar ba'a kasuwa ba."
Haris ya gaskata tsaftarsu da idonsa,kafin ya k'ara duban
Jafar
"Amma buzaye ne ko? Sunyi kama da buzaye wallahi
musamman Maman,naga ita bak'a ce d'iyar."
Kafin Jafar ya bashi amsa, ta dawo dauke da kwanuka,ta
ajiye ta dauko wasu ta k'ara ajiyewa gaban Jafar,sannan ta
ajiye musu ruwa da lemo mai sanyi dana wanke hannuwa
kafin ta juya ta koma bakin aikinta. Duk rabin hankalinta
yana ga Jafar sai murmushi takeyi.
Sai lokacin Jafar ya bashi amsarsa
"Buzaye ne mana,'yan nijar ne saidai mahaifinta ne d'an
garin nan shi kuma ya rasu. Shine suke cigaba da
rayuwarsu anan."
Haris ya jinjina kanshi kawai saboda dad'in abincin daya
soma fusgarshi.
Mama ta tab'ata,a firgice ta dubeta
"Wai bazaki raba kanki da tunanin Jafar ba? Sai kije ki
sallami wadancan(tayi mata nuni da wadanda suka shigo)
Ladi tayi farr da ido,ta sauke ajiyar zuciya. Jafar yana
neman kasheta da salon gayunshi. Ta taka a sanyaye zuwa
wajen mutanen da suka shigo.
Koda su Jafar suka kammala suka fito,santi kawai Haris ke
zubawa. Yana yabon girkin.
"Wannan bashi da bambanci dana Ummina,gaskiya sun iya
abinci lafiyayye."
Jafar yana jinsa har ya rakashi wajen motarsa. Banda
murmushi babu abunda yakeyi saidai baice komai ba.
Bayan Haris ya shiga ya zauna ne ya dubi Jafar cike da
tsokana yace
"Kodai da ita zamuyi ta biyu ne?"
Yaja tsaki ya harareshi
"Amma dai kaima sai a barka,so kakeyi na zama abin nuni a
kasuwa. Mijin mai abinci ko? Bata burgeni bazan iya
aurenta ba."
Ya k'arashe yana juya kansa, Haris yayi dariya
"A'a fa,kada azo..."
"Sai munyi waya. Dan iska kawai."
Yana fad'in haka ya bar wajen suna yiwa juna dariya. Jafar
abun ma dariya ya bashi,me zaiyi da Ladi yana da kamar
Siyama? Ai koda zaiyi aure bazai auri irinsu Ladi ba da suke
yini cikin kasuwa......
*********15
Ranaku suna ta ja har Allah Ya kawo ranar da aka yaye su
Ladi daga sakandire. Yan uwan mahaifinta sun zo tayata
murna. Ranar tayi murna marar misaltuwa saidai tana jin
kewar rabuwa da aminiyarta Basma wacce zata tafi can
Zaria garin iyayenta acan zatayi jami'arta. Babu wani sirrin
Ladi da Basma bata sani ba,daidai da wannan zancen na
Jafar tasan da zamanshi. Koda ace Ladi tayi niyyar
karaya,tayi niyyar sanarwa Jafar gaskiyar lamari,Basma
takan hanata tana mai karfafa mata gwuiwa akan cewar
wataran sune da nasara tunda da zuciya d'aya take sonshi.
Sati d'aya da yayesu daga sakandire,Basma tazo har nan
gidansu Ladi tayi mata sallama,suna kuka suka rabu
saboda tsananin shakuwar da sukayi bayan sun daukarwa
juna alk'awarin yin waya don bincikar lafiyar junansu
akowace rana..
Yan uwan baban ladi,Malam mukhtar,ko kusa basu
takurawa yaransu akan lallai bayan kammala sakandire
zasu aurar dasu. Wannan ne yasa sam ladi bata samu
matsala ba wajen bayyana ra'ayinta na son cigaba da
karatunta a fannin business admin. Sun bita da addu'ar
fatan alheri. Mama itama tana da burin d'iyarta ta cigaba
da karatunta acewarta ko nan gaba zatayi alfahari da
Ladi,musamman ma saboda yan uwanta na Nijar fa sam
basu so aurenta da Mukhtar ba a cewarsu bahaushe ne
kuma d'an nijeriya basu fiye rik'on aure ba. Ganin ta nace
dole sai shi d'in ne suka aura mata shi da sharad'in babu su
babu ita. So ya rufe mata ido ta amince.
Bayan rasuwar Mukhtar ko kusa batayi gigin zuwa inda
suke ba kamar yanda suma basu damu da ita ba. Ta dauki
lamarin a matsayin don tana marainiya ne shiyasa
kawunnanta sukayi mata haka. Wannan yasa koda wasa
bata kara marmarin komawa gida nijar ba,hakanan ta dauki
yan uwan Mukhtar tamkar nata babu mai nuna mata
kyama...!
*********
Cikin ikon Mahalicci,shak'uwar Jafar da Hadiyya takai har
shi da kansa yakai ga tambayarta garin da take da zama.
Gabanta ya fad'i,duk da cewar wani dadi ya mamaye
zuciyarta,gab'ar da take zaman jiran zuwansa kenan. Tayi
shiru kamar bazata ce komai ba.
"Baki jina ne?"
Ta muskuta sosai akan tabarmar da take zaune a tsakar
gidansu
"Um na'am,ina jinka yaya j."
"Toh baki ban amsa ba."
"Ni 'yar kano ce."
Yace "Ashe gari d'aya muke,kayya meyasa baki sanarmin
tun wuri ba na kawo ziyara dutsen dala?"
Sukayi dariya,ta tuna hirarsu ta rannan ashe fa aljana yake
kiranta. Cikin wasa tace
"Ai kuwa kamar kasan muhullina kenan,kodai nazo yanzu
ka ganni?"
Ya girgiza kansa tamkar tana ganinshi,cikin dariya yace
"No,ki rufamin asiri malama. A wace unguwa kike ne?"
Sanin da tayi bai tab'a sanin unguwarsu bane ya sanyata
fad'a kai tsaye
"Ni 'yar Yakasai ce."
"Baki da nisa sosai da kasuwar da nake ma. Kinsan wani
abu Hadiyya?"
"Saika fad'a yaya j." Ta amsa gabanta yana dukan tara tara,
tana tsoron abunda zaice.
"Allah ne mai had'a bayinSa ba tare da sun san takamaiman
dalilin had'uwar tasu ba. Haka kawai nake jinki a raina
tamkar wata 'yar uwata ta jini Hadiyya. I want to know
more about you,shiyasa nakeson kawo maki ziyara idan har
kin amince."
Ai batasan menene tsoro da fargaba ba saida Jafar yayi
wannan furucin,ita kam ai ta shiga uku. Ta yaya ma za'ace
ta baiwa Jafar damar zuwa gareta tun yanzu alhalin bata
gama tabbatar da cewa soyayyarta ta zauna a zuciyarsa
ba? Gaskiya da sake,tana kunyar had'uwarsu a wannan
lokacin.
"Shirun fa?"
Tayi wal da ido,ya taho da ruwan hawayenta. Ta shafesu
tana mai kokarin saita muryarta
"Ka gani yanzu bana Kano,nazo hutu Zaria gidan kakannina
amma ka bari da zarar na dawo zan maka kwatance har
kofar gidanmu. Ni kaina ina jinka sosai a raina yaya j fiye
ma da yanda kakejina. Banajin har na mutu zan bar jin
abunda kemin yawo a zuciyata da jinin jikina game dakai."
Ta fad'a tana mai rufe idanuwanta,wutar kaunar Jafar na
k'ara ruruwa a zuciyarta. Takanyi nadamar b'oye mishi
gaskiyar ainahin wacece ita da tayi. Tana tsoron ranar da
zai fahimta,lallai babu yanda za'ayi ya cigaba da mu'amala
da marar galihu mai siyar da abinci a kasuwa irinta.
"Bari nayi sallah Hadiyya."
Ya kashe kiran,kawai saita fashe da kuka tana mai
tausayawa kanta. K'arya bata da amfani ko kusa,yanzu
gashi tana nadamar aikinta. Tana yaudarar kanta ne,saidai
bazata tab'a samun namiji irin Jafar ba. Ya dace ace ta
fuskanci rayuwarta,ya kamata ta fidda rai a kansa.
Ta janyo wayar ta kasheta gaba d'aya. Saida tayi kukan
tausayawa kanta a karshe ta share hawayenta ta mike don
d'ora alwalar sallar magrib. Mama batanan ta fita zuwa
gidan gaisuwa.
**********
BAYAN WATANNI BIYAR
"Siyama zata koma gida har acan zata haihu. Banason ta
haihu ba kusa dani ba,tunda ta shiga watanta zan tafi da ita
can wajena."
Hajiyar Siyama ke wannan bayanin ga Jafar,wanda
shigowarsa gidan kenan da yammacin ranar juma'a ya
isketa zaune tare da Siyama a falo.
Abu d'aya ne baiji dad'insa ba,yanda ko kusa bata tashi
sanar mishi ba sai a yau,a yau d'in ne kuma takeso su
wuce. Amma bayan hakan ko kad'an bai damu ba,toh
daman tunda cikinta ya tsufa ai ko mutuwa zaiyi yana
naci,babu abunda take tsinana mishi. Duk yanda zai rok'eta
da magiyar duniya amma ko kad'an Siyama burus takeyi
mishi k'arshe ma ta juya mishi baya tayi kwanciyarta.
Hakanan yake hak'ura ya kwanta don tuni ya ajiye dokarsa
na kada ta k'ara shiga d'akinsa a gefe. Abunda ya riga ya
sani yana sonta.
"Kana jina kayimin kunnen uwar shegu,ko kana son ka
nunamin ban isa bane tunda ba ni na haifeka ba?"
Hajiya tayi maganar cikin bacin rai,da sauri Jafar yace
"Ba haka bane Hajiya,bakomai kuje. Allah Ya sauketa
lafiya."
Bata ko amsa ba ta dubi Siyama
"Tashi muje ki had'o kayanki."
Jafar ya bisu da kallo sa'ilin da suka tura kansu k'uryar
d'akin. Ya mik'e yayi nashi d'akin.
Acan kuwa,kayan Siyama gaba d'aya Hajiya ta rasa na
kirkin da zata daukar mata. Sai banbamin fad'a takeyi tana
tsaki.
"Kedai Allah Ya sauwake maki Siyama,ace kayanki babu
kyawun duba kowanne babu wankakke? Shi Jafar bai iya
bayar da wankin matarsa bane? Ko menene?"
Siyama ta hau kumbura fuska
"Yana bayarwa,an kwana biyu ne ba'a bayar ba."
Hajiya ta tabe baki
"Ke kika janyowa kanki. Tun farko babu irin kashedin da
banyi maki ba akan ki gujewa auren wannan shegen yaron
ke kuma kika nace mishi. Yanzu ai gashinan duk kin kod'e
kamar ba kece 'yar gayun nan ba wacce samari da dattijai
suka dunga rububinta. Ko haihuwa bakiyi ba duk kin koma
wata tsohuwa. Yarinya ina hango maki jin dad'i a gidan
Bash d'an gidan hakimi. Wannan yaron babu irin dukiyar da
bai kashe akanki ba,duba abubuwan arzikin da ya dunga
aikomana don ma Abbanki yakan hana a karb'a saidai nayi
dabarar kira nace ya mik'a gidan yayarki rumaisa. Amma
kika gujeshi,yanzu ai gashinan ya auri 'yar fillo suna Dubai.
Ke kam talauci saidai...
"Ehem ehem."
Gyaran muryar Jafar tayi saurin katse maganarta,duk da ta
tsorata ta hau basarwa
"Tafi,ga mayen yana kiranki. Dad'in abun dai gaskiyata
nake fad'a. Atoh "
Siyama dai ta fice ta bar Hajiya da surutan borin
kunya......!
*******16
Tuni ya juya ya koma d'akinsa,bai damu da sanin
fad'an da Hajiya ke yi ba. Domin bazaiyi mamaki
ba,tana da illolin da idan ya kama har duka sai a
had'a mata dashi.
Ya juyo ya dubeta lokacin data shigo
"Kina bukatar wani abu ne?"
Sanin da tayi komai na bukatar jariri Jafar ya siya
ya sanya ta girgiza kanta
"A'a."
Ya jinjina kanshi,ya zaro kud'i har dubu goma ya
mik'a mata
"Ki rike wannan a hannunki koda wata bukatar
zata tashi. Zan dunga kiranki muna gaisawa.
Allah Ya raba lafiya."
Yana magana ne fuska a had'e,kasancewar sun
kwana biyu yana fushi da ita. Jikinta a sanyaye
ta karb'a ta had'o da hannunshi ta rike k'am,ya
dubeta cikin mamakin hawayen daya gani suna
zubo mata,ya daure yace
"Toh menene na kukan?"
Ta kwantar da kanta a kafad'arsa cikin sanyin
murya tace
"Kayi hakuri don Allah ka yafemin my j. Banason
na tafi na barka kana fushi dani."
Ta d'ago tana dubansa,shima duk jikinshi yayi
sanyi
"Ko ka manta yanda haihuwa take?"
Ya shafi fuskarta
"Kada ki damu Siyama,idan nace zan iya fushi
dake nayi k'arya,komai ya wuce tun ranar da
akayi. Na chanja maki ne ko don gaba ki gane
kurenki,haramun ne juyawa miji baya a shimfid'a.
Nima son zuciyata ta sanyani kasa yin adalci
gareki,na manta cewa ke a yanzu abar lalla.."
"Yau naga sabon iskanci ni Maimuna! Ni zaku
mayar yar iska? Bazaki fito bane daga d'akin nan
muyi abunda zamuyi mu tafi?"
Jafar ya saketa
"Jeki kawai sai munyi waya."
Ta juya da sauri ta fita. Tana shiga falon Hajiya
ta rankwasheta
"Kedai Allah Ya sauwake maki,ki cigaba da sakin
jikinki har sai ya rainaki."
Siyama ta turo baki
"Kud'i fa ya bani."
"Har nawa?"
"Dubu goma."
Hajiya taja tsaki tayi cikin d'aki
"Matsiyaci kawai,mecece goma?"
Siyama cikin rashin jin dad'in furucin Hajiya ta
bita d'akin. Saida suka kammala komai sannan
Hajiya ta yiwa Abba waya ya turo mata direbansa
bayan ta sanar mishi Jafar ne yace ta tafi da
Siyama saboda haihuwa. Yayi na'am da zancen
saidai yaso kwarai ace a wajen Hajjah zata zauna
tunda dai duka d'aya ne amma bayason tashin
hankalin Hajiya Maimuna sai ya bar zancen haka.
Bayan tafiyarsu Jafar ya fice daga gidan bai dawo
ba sai goman dare. Gidan yayi masa fad'i,ya
amince cewar ko yaya mutum yake toh tabbas
rahma ne. Yanzu da babu Siyama duk sai yaji
babu dad'i. Daidai lokacin ne ya kunna wayarsa
daya mik'a wurin chaji d'azu bayan fitarsa.
Sak'onnin Hadiyya har biyu ne suka shigo. D'aya
gaisuwa ce da tambayar ko lafiya ta bugo taji
wayarsa a kashe,dayan kuwa gaisuwar juma'a ce.
Murmushi yayi,shima fa yayi kewar kanwar nan
tasa. Babu wata wata ya danna mata kira.
Ladi dake kwance ta kasa bacci saboda damuwar
rashin jin Jafar gashi yau juma'a basuje kasuwa
ba bata sanyashi a ido ba. Wayarta ta soma
vibrating, taga shi d'inne kuwa. Tayi mamakin
ganin kiransa,ta dubi Mama dake bacci ta mike
sad'af sad'af zuwa d'ayan d'akinsu dake a
matsayin falo.
"Assalamu alaikum,ba dai kin soma bacci ba
deeya?"
Tayi murmushi mai sauti
"Wa'alaikassalam yaya j,idanuna biyu ina tunanin
meke faruwa dakai na kira bata shiga ba. Gashi
yanzu kuma nasan ka koma cikin iyalinka ko?"
Ta k'arasa cikin sanyin murya,maganar ta
shigeshi. Yasan hadiyya tana da zak'in
murya,saidai jin na yanzun yake kamar yafi na
koyaushe. A hankali ya lumshe idanuwansa
"Iyalina bata nan,kinsan ta shiga watan
haihuwarta. Al'adar bahaushe yasa aka daukemin
mata,har sai ta haihu tayi arba'in."
Ladi ta sanya dariya mai had'e da farin ciki,tace
"Ashe kuwa kwana biyu yaya j zakayi kewa. Na
tausaya maka,sorry."
Yayi murmushi,
"Zanyi maganinki,gwarani. Keda ko samarin baki
dasu?"
Ta lumshe ido ta bud'e
"Haba,gaka nan."
Ta fad'a a hankali,ya gyara zamanshi akan gado
"Banji ba?"
Tayi dariya
"Tunda ina da yaya j ai shikenan,idan lokacin
auren yazo sai na bawa ko waye damar fitowa."
"Kina nufin bazakiyi auren soyayya ba?"
Cikin damuwa tace
"Da wuya na samu wanda nakeso. Yaya j nifa ba
'yar kowa bace, ba wani kyau ne dani ba. Shi
kuma wannan da nakeso ya keremin ta
ko'ina,baisan ma ina sonshi ba sannan yana da
matarsa kana ganin zai aureni ne?"
Zuciyarsa ta soma zargin wani abu, shi kansa ya
kasa tantance abunda yakeji akanta. Yasan bai
wuce shak'uwarsu ba,amma meyasa yakejin wani
abu a kanta ne? Ya daure yace
"Waye wannan deeya? Na tabbata ko waye yana
sonki. Deeya halayenki suna dakyau,ko kadan a
yanzu ba a fiye auren kyau ba. Domin babu
abunda aka fi tsinta sai munanan d'abi'u masu
farraka ma'auratan da matsaloli daban daban.
Kada ki yarda duk runtsi kiyi auren da babu
soyayya Deeya,matukar kikayi hakan,zaki iya yin
dana sani marar misaltuwa."
Kwallah ta cika idonta
"Kana nufin kowaye bazai gujeni ba yaya j?"
"Kwarai kuwa."
"Koda ya kasance kaine wannan mutumin?"
Dam!.........
:
Gabansa ya fad'i da jin tambayar da Hadiyya ta watso
mishi. Ya daure ya k'ak'alo 'yar dariya
"Kedai akwai ki da wasa,haba ni dan adam me zanyi da
aljana ina da kamar Siyama?"
Ya fad'a cikin son maida zancen wasa. Tayi dariyar itama
wanda ya taho da ruwan hawaye ta jinjina kanta zuciyarta
na tururi,ta daure tace
"Sau nawa kuma akayi hakan? Kaga sai a k'ara dank'on
zumunci "
Yayi dariya
"Lallai kam."
Daga haka ya bagarar da zancen kamar bai fahimci iyakar
gaskiyarta take fad'a ba. Tun ba yau ba ya fahimci son da
takeyi mishi hakanan bayaso ko kadan ya gaskata yanayin
da yakeji game da ita.
Itama Hadiyya ganin ya share maganar ne ya sanyata yin
dana sani. Tasan shikenan Jafar bazai tab'a sonta
ba,daman zuciyarta ke yaudararta har ma take ganin kamar
so ne yasa mu'amalarsu tayi k'arfin da har ya nemi sanin
gidansu. Ashe ashe ba haka bane. Ji tayi gaba d'aya hirar
ta gundureta,don haka ta katseshi da fad'in
"Bacci ya taho yaya j,zan kwanta saida safe."
Jafar shi kansa yana bukatar tunani,don haka ba musu
sukayi sallama ya jona wayar a chaji. A sannu ya maida kai
ya kwanta zuciyarsa cike da tunani. Hadiyya sonshi takeyi?
Meyasa baiji haushinta game da hakan ba kamar yanda
yakejin haushin sauran yan matan irinta masu nuna suna
kaunarsa? Toh kodai shima yana sonta ne?
Ya girgiza kanshi da sauri ya k'ara muskutawa
"Bazai tab'a yiwuwa ba. Bayan Siyama babu wata d'iya
mace da zan nunawa so. Babu!"
Ya fad'a a fili,cikin son kawar da tunane tunanensa,yayi
addu'oinsa ya rufe ido har bacci ya daukeshi.
*******17
Batayi mamakin ganin Mamanta tsaye a kanta ba saboda
kukan da takeyi mai k'arfi ne. A firgice Mama ta k'araso
falon ta zauna tana dubanta.
"Ladi kina cikin hayyacinki kuwa? Meke faruwa ne?"
"Bakomai mama,um...um...nayi mummunan mafarki ne."
Mama tace
"Haba Ladi shine saiki dunga kuka haka kamar ba musulma
ba? Addu'a ya kamata kiyi,sannan ko menene kika gani ai
iyakarsa mafarki ba wai gaske ba. Allah Yayi mana tsari da
sharrukan dake cikin mafarkanmu,Ya tabbatar mana da
alhairansa."
Dakyar ta iya amsawa,mama tace
"Tashi muje ki kwanta,kafin nan ki d'ora alwala"
Tabi bayan mamanta bayan ta kashe wayar ta ajiye anan
kan kujera. Bata marmarin sake bud'e wannan wayar,bata
da amfani tunda wanda takeso baya sonta. Ta tabbata
cigaba da sauraron Jafar k'arin tashin hankali ne ga
rayuwarta. Ka hak'ura da duk wanda zai nuna baya
sonka,shine mafita...!
Kwana uku da yin haka tsakanin Jafar da Hadiyya. Ya shiga
damuwa kwarai na rashin samunta a waya. Har mamakin
lamarin yakeyi,toh menene kuma na damuwa har haka?
Daman ai koda bata barshi yanzu ba wataran dole fa zatayi
aure su rabu. Saidai wannan baisa ya bar damuwar rashin
samun wayar Hadiyya ba. Gashi ko gidansu bai tab'a zuwa
ba,kamar yanda ko a hoto basu san junansu ba ballantana
ya sanya ran wataran zai iya had'uwa da ita.
Ita kuwa Ladi kacokam ta maida hankalinta ga karatunta
duk da cewa can k'asan zuciyarta tunanin Jafar ne
mamaye. Kwana ukun nan ko shago bata bin Mama suje
tana fakewa da gajiyar makaranta. Babban dalilinta na
gujewa shagon bai wuce fargabar yin tozali da Jafar
ba,batason ganinsa ya fama mata wani mikin. Daman
yanzun ma wane irin wahala ce bata sha? A kwana ukun
nan gaba d'ayanta ta rame,tsananin kewar muryarsa takeyi.
Saita dauko wayarta a yini fin sau goma da niyyar bud'ewa
amma data tuna cewar son maso wani takeyi wanda takeso
bai damu da ita ba kawai sai ta fasa. Ta koyawa kanta
yawan duba darussan makarantarsu,babban takaicinta ga
Basma tayi mata nisa balle ta nemi shawararta. Ita kad'ai
take kid'a da rawarta. Mahaliccinta kad'ai Yasan
matsalarta.
******
Ranar wata litinin ta yanke shawarar zuwa kasuwa ko don
kautarwa da Mama damuwar da ta sanyawa zuciyarta akan
rashin sanin dalilin chanjawarta.
Ganinta kuwa ba k'aramin farin ciki yasa Mama ba. Ladi
tayi iyakar kokari wajen danne damuwarta saboda Mama.
Cikin ikon Allah ma sai ya zamana a ranar ko k'eyarsa bata
gani ba.
*****
Bama shagonsu Ladi ba,ko kasuwar Jafar bai lek'o shigeta
da wuri ba sakamakon kiran daya samu daga Hanif,inda ya
sanar dashi Siyama ta haihu da asuba anan asibiti. Farin
ciki marar misaltuwa ya mamaye Jafar,cikin fad'a yace
"Amma meyasa tunda aka mik'ata asibitin babu wanda ya
sanarmin?"
Hanif yayi dariya
"Toh inda an sanar maka me zakayi? Ai fad'ar haihuwa yafi
dad'i akan nakuda. Ka garzayo dai kaga d'anka mai kama
dakai."
Jafar yayi tsalle ya sauko daga gadon. Tuni ya mance da
damuwar da yake ciki na rashin jin Hadiyya.
Acan kuwa,daga Hajiya sai Amina matar Hanif ya tarar.
Lokacin karfe bakwai da rabi na safe.
Jafar yayi murnar ganin Siyama da d'ansa cikin koshin
lafiya. Anan waje ya zauna yayi ta kiran 'yan uwa da
abokan arziki bai damu da yanda Hajiya ke kananun
maganganu ba. Wai ko nauyinta baiji ba ya sungumi
jaririnsa har yana sumbata.
Kafin kace me,tuni yan uwa sun cika asibitin. Hajja kanta
saida tazo.
Jafar bai bar asibitin nan ba sai wajen uku na rana,saida
yaci abinci yayi nak sannan ya tafi kasuwar cike da farin
ciki. Ko ta kan shagonsu Mama bai bi ba,hankalinshi duka
yana ga mai jego da d'ansa.
Da yamma aka sallamesu suka koma gida. Wannan yasa
Jafar yana barin kasuwa bai zarce ko'ina ba sai gidansu...!!
Yakai mintuna talatin suna hira da Hanif a babban falon
Hajiya,saidai babu niyyar za'ayi mishi magana da mai jego
ko kuma a mik'o mishi d'ansa. Hanif yaje har wajen sau
uku saidai amsar an musu wanka,tana cin abinci,ana
gyarawa baby jiki. Can dai yaga abun bana k'are bane dole
ya mik'e,hanif ya dubeshi
"Ba dai tafiya ba?"
Jafar yayi murmushi
"Eh zan shiga gida daganan zan wuce."
Da sauri Hanif ya mik'e
"A haba ko baby baka gani ba? Jira don Allah bari nayi
musu magana."
Jafar ya koma ya zauna,yana jiyo shewar Rumaisa dasu
Amina matar hanif. Hira sukeyi hankali kwance.
Hanif ya shiga ya samesu,ganin Siyama zaune kawai,yaron
yana cikin gadonshi ransa ya b'aci.
"Ke wane irin iskanci ne tun d'azu mijinki yana zaman
jiranki amma kin gaza fitowa? Idan ma baki da niyyar zuwa
ai saiki bashi yaronsa ya gani ko?"
Siyama ta mike don daman Hajiya ce ta hanata fita tun
d'azun sai fad'a takeyi ita bazata dauki rashin kunyar jafar
ba,akan wane dalili zai dunga yin zarya daga haihuwa?
Ganin Hajiya batanan yasa ta fito,Hanif tuni yayi gaba da
jaririn a hannu. Jafar ya karb'eshi yana dubansa,babu
abunda ya bambantashi da yaron sai haske kawai da zai
nuna masa. Sanyin dad'i ya mamayeshi yana jin kaunar
yaron matukar gaske tana k'ara shigarsa.
"Ina wuni."
Ya d'ago ya dubeta fuskarsa dauke da murmushi
"Lafiya lau mai jego,ya jikin?"
Ta d'an yatsine fuska
"Jiki da sauki."
Ya lura tana cikin fushi,sai ya tambayeta
"Yaya dai? Akwai wata damuwa ne?"
Ta girgiza kanta har lokacin bata saki fuskarta ba
"Don Allah my j kada ka rinka zuwa akai akai,Hajiya har ta
soma fad'a. Wai duka duka yaushe aka rabu a asibiti har ka
biyomu? Ka bari sai mu dunga gaisawa a waya,koda ta
kama zakayimin magana mai muhimmanci sai muyita a
waya amma.."
Kallon da yake jifanta dashi ne ya hanata k'arasawa
"Shine dalilinki na k'in fitowa ko?"
Ya jinjina kanshi,duk wani murna da ya taho da ita da
d'okin ganinta da d'ansa nan da nan ta kau. Ya mike ya
mik'a mata yaron,ya sanya hannu a aljihu ya fiddo kud'i ya
ajiye mata.
"Shikenan,nagode. Amma ki sani koda ban nemi ganinki ba
zan nemi ganin d'ana wannan kuma babu mai hanani. Ke
kam naji duk sadda kika bukaci ganina sai ki sanarmin.
Amma bazan yarda da sharad'in nan ba daga haihuwa yau
yau a kafamin shi. Bamai yiwuwa bane."
Ya juya ya fice rai a b'ace. Siyama taja tsaki,shi dai Jafar
batasan irinshi ba. Banda zuciya babu abunda ya ajiye.
Magana bata kai ta kawo ba zaiyi fushi. Ta mike ta koma
d'aki.
*******
Hajja ta jefo mishi tambaya bayan ta gama lura da
yanayinsa
"Kai kuma meya faru?"
Ya girgiza kai ya ja numfashi,nan ya labarta mata yanda
sukayi da Siyama. Cike da mamaki Hajja tace
"Ikon Allah,daga haihuwa yau yau d'innan har an soma kafa
doka? Allah dai Ya kyauta. Saika kiyaye don a zauna lafiya.
Kaga kuma haihuwar fari ce,mata zasuyita zuwa saika rage
shiga gidan."
Baice komai ba,Hajja ta ja shi da wata hirar game da tsarin
da yayi nakai kayan barka a al'adance,
"Nikam bansan yanda kukeyi ba Hajja. Abunda yafi zan
bawa anti kudad'e idan yaso sai ta had'a a mika musu."
Hajja ta gyada kanta
"Hakan yayi,Allah Ya k'ara rufa asiri."
"Amin."
*******18
Bazata iya kashe kanta ba,ta lura tayi nisan da batajin kira
akan sonsa. Wannan yasa tana dawowa daga shagonsu ta
bud'e wayarta. Tayi mamakin jin shigowar sakonni har uku.
Na farko daga kamfanin mtn ne,na biyu dana uku an turosu
ne jiya da yau. Na biyun gaisuwa ce da tambayar lafiyarta
daga Jafar. Na ukun kuwa,sanar da ita haihuwar Siyama
yayi. Taji dad'in k'aruwar daya samu,don haka ta ajiye
wayar da zummar idan ta idar da sallar isha'i zata aika
mishi sakon taya murna.
Tana idarwa,mama ta lissafa kud'in adashi ta bata akan
takai mata gidan hindatu mai adashi. Taji dad'in wannan
aiken tasan ta samu damar siyan kati. Ta rarumi wayarta
da hijabi ta fito. Saida ta soma biyawa ta sayi kati ta
sanya,ta nemi gefe ta tsaya. Sak'o ta rubuta mishi ta aika
sannan ta cigaba da tafiya kasancewar akwai 'yar tazara
tsakaninsu da Hindatu mai adashi.
Babu dad'ewa wayarta ta soma vibrating ta duba,murmushi
ya kwace mata zuciyarta na bugawa da sauri sauri. Yaushe
rabonta da jin muryarsa? Da sauri ta d'aga tare da sallama.
"Deeya! Ina kika shiga ne kika manta da yaya j,bakya ko
tunanin halin da zan shiga? Tabbas nayi fushi dake mai
yawa."
Ta gimtse dariyarta,ta k'ara yin sallama a karo na biyu jin
da tayi bai amsa na farko ba. Ya amsa mata,a hankali tace
"Yaya j,bari na isa gida zan maka flashing,yanzu ina kan
hanya ne."
"OK."
Ta kashe wayar,tana mai jin wani irin farin ciki. Nan fa ta
d'aga k'afarta har ta isa gidan Hajiya hindatu mai adashi.
Injinsu sai aiki yakeyi,tana zaune a falon. Suka gaisa ta
mik'a mata kud'in,Hajiya hindatu taji dadi,
"Shiyasa nakeson Binta,bata wasa. Takan bayar akan
lokaci."
Dariya kawai Ladi tayi sannan ta tambayi Jamilah,diyarta.
Ta nuna mata d'aki. Da saurinta ta nufi d'akin. Jamila tana
band'aki,wannan ya bata damar dannawa Jafar kira. Ko
minti d'aya batayi ba ya biyo bayanta.....
"Deeya! Kinsan kin mini laifi ko?"
Ta narkar da murya,lokacin da Jamila ta fito suka sakarwa
murmushi.
"Nasan ban kyauta ba yaya j,ayimin afuwa."
Ya sauke ajiyar zuciya har tana jiyo hucinsa,
"I miss you so much wallahi,Deeya inajinki a raina fiye da
tunaninki. Please yaushe zakimin iznin zuwa gidanku?"
Yayi furucin ba tare daya shirya ba,zai iya rantsuwa ba tare
da kaffara ba,yayi kewarta sosai. Burinsa bai wuce ya
ganta ba ya kuma san kowacece.
Ladi tayi shiru gabanta yana fad'uwa.
"Deeya"
Ta dubi Jamila wacce ke sallah,
"Na'am."
"Meyasa bakyason mu had'u ne? Kina zaton zumuncinmu
zai cigaba da kasancewa a haka ba tare da mun had'u da
juna ba?"
Ta lumshe ido,ai tafishi son yasan da zamanta. Tafishi son
zumuncinsu yafi haka nisa.
"Kinyi shiru."
Ta numfasa "Kayi hakuri yaya j,lokaci ne. Da kaina zan
maka izni zuwa gidanmu."
"Har yaushe ne Deeya? Sai kinga na fad'i ba rai ko?"
Baisan lokacin da yayi furucin ba,saidai yasan hakika yana
jin Hadiyya a ransa sosai. Baya zaton sonta yakeyi,duk da
dai yanayin da yakeji a ransa game da ita makamancin
yanda yakejin SIYAMA ne.
Ta dauke wuta d'if na 'yan dakiku,maganarsa take
nanatawa a zuciyarta cike da mamaki. Gani takeyi kamar a
mafarki,me yake nufi?
"Yanajin abunda nakeji?"
Har batasan sadda maganar dake zuciyarta ta fito fili ba.
"Kema kina jina a ranki dagaske Deeya?"
Ai batasan lokacin data mike tsaye ba har Jamila wacce ke
addu'o'i ta dubeta a razane.
"Lafiya?"
Ta rufe baki saboda dariyar farin ciki daya taho mata. Ta
girgiza mata kai tare da shige band'aki.
"Ina jinka sosai yaya j,fiye da tunaninka."
Yayi shiru kad'an kafin yace
"Nagode deeya,nagode. Saikiyi kokari ki bani iznin zuwa
gidanku don Allah. Kinji ko?"
"In sha Allah yaya j,ka d'an bani lokaci kaima."
"Shikenan Deeya,bari na barki haka."
"Toh yaya j,agaishemin da antina da bebina."
"Zasuji in sha Allah."
Daga haka sukayi sallama,tayi hamdala yafi sau biyar
sannan ta fito. Jamilah ta ajiye darduma akan katifarta.
"Wai yau wane mai sa'an ne da har ya samu kika
saurareshi?"
Ta harareta tana dariya
"Oho maki,nidai saida safe. Nasan mama tana can tana
fushin dad'ewata."
Jamila tayi dariya
"Au dama ba hira kikazo muyi ba? Lallai ma,muje na rakaki
toh tunda na gane waya ta tsayar dake."
Ladi ta lumshe ido kad'an kafin ta bud'esu tayi gaba. Hajiya
hindatu bata falon don haka tayi gaba,har saida suka d'anyi
nisa da tafiya ita da Jamila kafin tayi mata sallama ta
k'arasa.
Mama tayi fad'an dad'ewarta,kafin kuma ta sauko ta
hakura.
Ranar bacci b'acci b'arawo ne kawai ya sace Ladi,abunda
ke gabanta bai wuce kiran Basma ba domin neman
shawarar yanda zata warware kanta awajen Jafar.
*********
Tun daga wannan ranar,waya bata yankewa tsakanin Jafar
da Hadiyya......
Yaro yaci suna Umarul Faruk. Ranar anyi buduri sosai. Su
Anti Habiba ma da matan DM ba'a barsu a baya ba.(lol).
Ranar kam Siyama ta fito sak da ita babu wanda zai kalleta
yayi kiranta da sunan Kazama.
Jafar ma yinin gidansu yayi don ranar baiyi nisa ba. Yana
nan tare da Haris wanda shima ya kawo Ummi da Rahma
amaryarsa wajen sunan. Har Jafar yana tsokanarsa
"Kaga angon Rahma uban 'ya'yan Ummi. Wato dai Allah Ya
taimakeka kan matanka ya had'u hankali kwance sai
mulmula uban k'iba kakeyi."
Sukayi dariya,Haris yace
"Ba dole ba. Ai Ummina ta shayar dani mamaki. Ban tab'a
zaton haka zata dauki lamarin da sauki ba. Kasan farko
farkon nan daman sai namiji yayi hakuri saboda dole ne
daman su nuna kishinsu. Ita kanta Rahma da make tsoron
kada ta rikitamin gidana sai gashi ta bani mamaki ba
k'ad'an ba. Tana bin Ummi tana bata girmanta a
matsayinta na yayarta."
Jafar yayi murmushi
"Dole hankalinka ya kwanta."
Cikin tsokana yace
"A'a toh,kaidai zauna kada kayi auren nan."
Jafar ya shafi sumarshi yana murmushi
"Bar batun auren nan a gefe."
Haris yana kallonshi yace
"Ina kanwarka ta waya?"
Jafar ya gyara zamanshi akan motar Haris
"Ka tab'omin inda yakemin k'aik'aiyi. Ita nake zurawa ido.
So nakeyi tayimin iznin zuwa gidansu mu gaisa kaga sai
zumunci ya d'ore."
Haris yayi dariya yayi dariya,Jafar ya daure fuska
"Zaka fara ko? Menene na dariyar?"
Haris ya girgiza kansa
"Akwai wata a k'asa tsakaninka da kanwarnan taka. Duk
yanda akayi dai sonta kakeyi."
Jafar ya kauda kansa gefe,ba tare da ya dubeshi ba ya
tab'e baki yana d'aga kafad'a
"Zai iya yiwuwa hakan ne. Kasan har yanzu bana gane
feelings na So. "
Haris ya d'an bugi kafad'arsa yana dariya,har saida ya
bawa Jafar dariya. Yana murmushi ya kalleshi
"Mene abun dariya? Kaifa d'an iska ne. Toh idan ma sonta
nakeyi akwai wani abu a ciki?"
Sukayi dariya,Haris ya nunashi da yatsa
"Gwara dai daka fad'i gaskiya. Amma babu wanda zai tsaya
har yayi mintuna yana sauraron hirarku yace wai ba
soyayya kukeyi ba. Kaidai kace mun kusa shan biki."
Har lokacin murmushi bai yanke daga fuskar Jafaru ba. Ya
sauko daga saman motar
"Ya danganta."
Haris dariya yakeyi,ya gama yarda amininsa ya fad'a
tarkon soyayya sai fatan Allah Ya sanya alheri. Ashe dai
shiyasa ba'ason mutum ya zama mai CIKA BAKI,gashi
dalilin hakan Allah Ya jarabceshi da son wata bayan
Siyamar da yake ikrarin bazai tab'a son wata bayanta ba.
********19
Ranar Alhamis,itace ranar da Ladi ta yiwa Jafar iznin zuwa
gidansu. Farin ciki da d'okin son ganinta sun hanashi
saka.Wannan yasa a daren litinin bayan magriba yana
isowa gidansa. Yayi wanka abinsa ya shirya cikin manyan
kaya banda babbar riga. Ya feshe jikinshi da turare sannan
ya fito ya soma haramar tafiya.
Tunda yayi kiranta a waya ya sanar mata isowarsa ta tsinci
cikinta da rud'ewa,gaba d'aya ta kasa nutsuwa har saida ta
ziyarci band'aki ta rage cikinta. Ta fito ta k'ara duban
fuskarta madubi duk da kwalliyar data sha wannan baisa
tabar fidda gumi ba. Kai k'arya batayi ba rayuwa. Mama
tana daga zaune tana kallonta cikin nazari
"Wai yau wane mai sa'an ne har ake ta gyare gyaren fuska
saboda shi?"
Ladi tayi dariyar yak'e
"Lah,Mama wanda kike yawan jinmu muna waya ne fa."
Mama tayi murmushi
"Ikon Allah,shine zaizo kenan? Allah Ya kawoshi lafiya. Saiki
kama kanki duk da dai bansanki da rawar kai ba."
Hamidah tayi murmushi
"Toh Mama zan kiyaye."
Kafin Mama tayi magana wayar Ladi tayi k'ara,ta amsa
cikin jin fargaba. Jafar ke sanar da ita ya iso kantin datayi
mishi kwatance dashi.
"Toh zaka ga wani gida daga gefen hagun kantin,nan ne
gidan. Ganinan fitowa yaya j."
Sukayi sallama,ta juya ta dubi mamanta,sukayi murmushi.
Na Ladi kam baije ko'ina ba domin ita kad'ai tasan yanda
hantar cikinta ke kad'awa.
"Mama saina dawo."
"Toh kada ki zauna,ku tsaya nan jikin gidan."
"Toh."
****
Hankalinsa yana kan k'ofar,zuci zucin ganin Deeya yake.
Burinsa yayi tozali da ita.
A sannu ya dunga jin k'amshi yana bugar hancinsa,wannan
ya k'ara sanya Jafar tattara hankalinsa ga k'ofar,murmushi
nsa mai bayyana hakoransa yake fitarwa. Ji yakeyi kamar
ya fad'a zauren ya janyota waje. A sannu ya hangi kafarta
na dama ya soma fitowa kafin ita d'inma ta fito gaba
d'ayanta. Baisan lokacin daya mik'e daga kan mashin
d'insa ba
Duk da kallon da yake binta dashi na tsantsar
mamaki,wannan bai hana Ladi k'ara nufoshi ba dauke da
murmushinta wanda ya sauya kama zuwa na mai nishin
kash.
"Assalamu alaika yaya j."
Tayi namijin kokari wajen yin furucin sallama
gareshi,yayinda Jafar yayi mutuwar tsaye ba tare daya iya
amsawa ba. Ya d'ago yatsansa ya nunata
"Ladi!! Kada dai ace kece Hadiyya?!"
zuciyarta na fat fat,ta daure ta runtse idonta
"Kayi hakuri yaya j,kwarai kuwa nice Hadiyya."
"No!!! I cnt believe it! Ladi meke faruwa ne?"
Tuni kwallah ta cika idonta,ta waiga taga mutanen wurin
harkokin gabansu kawai sukeyi. Ta fiddo wayarta ta bud'o
sak'onnin da suka dunga musayarsu ga juna. Ta mik'a
masa cikin rawar murya ta ta mik'a mishi
"Wannan kad'ai ya isheni shaida yaya j. Na rantse da Allah
zuciyata bata nufinka da sharri."
Ya kalleta kafin ya sanya hannu ya karb'i wayar,ransa yayi
tsananin b'aci. Jikinsa ya hau rawa,ya kauda kansa ya
mik'a mata wayarta. Yayi shiru zuciyarsa na k'una,kafin ya
d'ago jajayen idanunsa wadanda bacin rai ya rina ya
dubeta,tuni Ladi ta soma ruwan hawaye
"Nasan ni hakika mai laifi ce yaya j,nasan nayi abunda
addininmu ya haramta. Ina rokon gafararka,kayi uzuri ga
zuciyar data riga ta gama tsumuwa da soyayyarka. Wallahi
yaya j...."
"Dakata!! Banason jin komai daga gareki. Tsakanina dake
akwai Allah! Kin cuceni Ladi,kin cuceni!"
Daga haka ya hau mashin d'insa,da sauri ta dafe kan
mashin d'in har tana had'awa da hannuwansa kafin ta
kautar da hannuwanta da sauri. Durkusawa tayi
gwuiwoyinta a k'asa tana kuka sosai gaba d'aya 'yar
kwalliyar tarbar mijin kazamatuya goge
"Kada kayimin haka yaya j,bakasan wahalar dana sha akan
kaunarka ba. Yaya j bakasan yanda zuciya da gangar jikina
suke azabtuwa a dalilin kaunarka ba. Yaya j rashinka a
rayuwata ba k'aramin tashin hankali bane a gareni. Idan da
gaske kake kanason Deeya,me zai sanyaka ka guji Ladi?
Yaya j me zanyi ka yafemin laifina? Ko menene na shirya
yinsa amma domin Allah kada ka barni."
Yayi tsai yana dubanta,har ta soma tunanin ya hakura
saidai taji ya tayar da mashin d'insa da saurinta ta mike
tsaye tana kokarin tsayar dashi. Ya girgiza kanshi
"Kin yaudareni Ladi! Bazan taba cigaba da mu amala dake
ba...!"
Daga haka ya ja mashin d'insa inda yabar Ladi cikin
tsananin nadama. Ta yarda SO BABBAR CUTA ne!!!!!!
Da gudu gudu ta shige gidansu ta fad'a jikin mamanta tana
kuka. Cikin tsananin gigita Mama ta d'ago fuskarta tana
salati
"Yau ni Binta na shiga uku! Ke menene? Meya faru?"
Sai kuma ta mike da saurinta ta fito waje tana lek'e amma
idonta bai gane mata kowa tsaye a kofar gidan nasu ba. Ta
dawo da sauri tana jijjiga kafadar Ladi
"Ki tashi ki gayamin me yayi maki? Wanene?"
Ladi ganin yanda Mama ta rud'e ya sanya ta sassauta
kukanta
"Mama ki zauna zan fad'amaki komai."
Mama ta zauna jiki sanyaye
"Ina sauraronki,kiyi azamar sanar dani kada jinina ya hau."
Ta dubi mamanta
"Yaya jafar ne yazo."
Mama ta zaro idocike da mamaki
"Jafar dai na kasuwa? Menene ya kawoshi?"
Ta tambaya cike da zargi,Ladi ta daure ta zayyane mata
dukkan abunda ke faruwa. Bata kai k'arshe ba taji Mama ta
wanke mata fuska da kyakkyawan mariwanda ya sanya
Ladi zaro ido rike da fuska tana kallon mahaifiyarta. Tunda
ta taso Mama bata tab'a kai hannu kan fuskarta ba,bata
tab'a yunkurin marinta ba sai yau.
"Kin bani mamaki Hadiyya! Lamarin nan ya sanyamin
tsoronki! Ina maki kallon mai hankali ashe har yanzu
kuruciya yana yawo a kanki?! Waye Jafar! Waye shi? Me
yake dashi da har yafi sauran maza?!! Akanshi kika
sab'awa Ubangijinki! Kikayi k'arya!!!! Ashe zaki iya aikata
abu har haka ba tare da sanina ba? Ina tarbiyyar dana
kwashi shekaru ina baki? Akan soyayya kinyi fatali da ita?!!
Wace riba kika tsinta da hakan? A yanzu ki fadamin me
Jafar yayi maki a karshe? Wallahi kin bani kunya! Ba
shakka kin zamo mini abun tsoro,matukar auren kikeso dole
ne ayi maki tunda har zaki iya wannan aikin akan da'namiji
A fusace Mama ta fad'a d'akinta. Nan ta bar Ladi tana rusa
ihun kuka,tana mai cike da dana sanin biyewa zuciyarta.
Ashe ba'a soyayya ta dole? Bata yiwuwa da k'arya? Tabbas
mafi yawan son da za'a dunga karyace karyace babu komai
a karshensa sai bakin ciki da bala'o'i.
Gaba d'aya taji ta tsani kanta,ta tsani aikin data aikata.
Yanzu meye ribarsa? Wane sakamako ta tsinta a karshe?
"Astagfirullah!"
Ta fad'a a fili sannan ta mike tayi d'akin.
********20
Allah ne Ya tserar dashi. TaimakonSa ne ya maidoshi gida
lafiya. Dakyar ya iya bud'e d'akinsa ya shiga.
Zubewa yayi a k'asa yana mai sauke ajiyar zuciya akai
akai. Zafi yakejin zuciyar tana masa, damuwa da bakin ciki
sun tarar masa. Har lokacin bai bar ganin yanda lamarin ya
kasance ba a idonsa. Wani sa'in sai ya d'auka ko mafarki
yakeyi. Ashe daman Ladi ce Hadiyya?!!! Innalillahi
Ya dafe kansa da hannu biyu ya runtse ido a yayinda
yakejin ya tsani abunda ta aikata! Ladi kam ta cuceshi.
Kafin kace me,tuni kansa ya soma sarawa. Duk da hakan
bai bar cigaba da matsawa kwakwalwarsa da tunani ba.
Kalamanta suna yawo a kwakwalwarsa,da yanda suke
daukar lokuta mai tsawo suna hirarraki duk zantukan
soyayya. Oh Jafar! Har tsawon wane lokaci ya dauka yana
soyewa da Ladi mai abinci?.
Toh wai ma ya akayi ta samu lambarsa? Yayi shiru yana
tunanin,nan da nan ya tuna ranar da Ladi ta nemi lambar
wayarsa.
Ya lumshe ido yana dafe goshinsa
"Ya Salam!"
Ya fad'a a bayyane,wayarsa ta soma k'ara ko kallonta baiyi
ba har ta tsinke aka k'ara kira. Ya duba,ganin Siyama ce ya
sanyashi d'agawa dakyar.
"Ina jinki Siyama."
Ta ja tsaki
"Bacci ka soma ma? Lallai Jafar,kana sane cewar yau gaba
d'aya bakayi kirana ba bayan kasan na kusa arba'in gashi
har yanzu bakayi batun dinkunan da akeyi na yawon
arba'in ba."
Damuwa ta k'ara yawaita,ya rufe idanuwansa yana mai cije
lebbansa na k'asa kafin ya samu damar furzar da numfashi
"Kina neman ninkamin damuwa akan wacce nake ciki.
Please whatsoever ki bari da safe sai muyi maganar yanzu
ina fama da ciwon kai. Ya Faruk?"
Maimakon ta amsa sai ta hau magana cikin zafi zafi
"Ba damuwarka bace,da ace ka damu dashi ai da babu
abunda zai hanaka kirana da safe. Wallahi Jafar duk wasu
take taken ka a kwanakin nan ina lura dasu. Duk ka bi ka
chanja,yanzu don Hajiya tace ka bar zuwa laifi tayi ne? Na
tabbata yanzu baka damu da...."
Yayi azamar kashe wayarshi gaba d'aya domin hakika
bashi da wannan lokacin na sauraron shirme da shiriritar
Siyama,abubuwan dake gabanshi ma matsala ce babba. A
daddafe yayi sallar isha'i sannan ya kwanta. Nan ma
zuciyarsa tace bai isa ba,bazai barta da damuwa ba
idanuwansa su runtsa,duk sanda zai rufe ido fuskarta yake
gani. Ga tsananin ciwon da kanshi yakeyi dole saida ya
mik'e ya sha magani. Lokacin ko karfe tara batayi ba ma
hakanan bashi da karfin da zai k'ara fita daga gida.
****
Acan kuwa yana katsewa Siyama kiran,tayi kwafa ta k'ara
bibiyarsa saidai cikin rashin sa'a wayar a kashe. Rumaisa
wacce bata sati d'aya bata zo gidan ba,tana daga zauna
akan kafet ta dubeta fuska a daure
"Ya kukayi?"
Siyama ta dubeta
"Bansan me Jafar yake nufi ba anti,wai cewa yayi na
kyaleshi yaji da damuwarshi. A karshe ma kafin nakai ga
karasa magana ya kashe wayar gaba daya."
"Kajimin d'an kaza kaza!!!!,(ta antayo mishi ashariya). Lallai
wuyansa ya isa yanka! Hajiya da alama bashi da niyyar
bada kud'ad'en nan,gashi dai kowa a dangi zuba ido yake
yaga irin kwalliyar da zata ci bayan arba'in. Haba
Hajiya,kayan Siyama meye mararbarsu da tsummokarai?
Banda kala uku na fitar suna da yayi,banga wasu masu
kyawun fita unguwa ba a kayanta duk taci ubansu."
Hajiya dake rike da Faruk ta gama goge mishi kashi da
wiper ta chanja mishi famfas ta tab'e baki tana mai nuna
Siyama sakarce
"Ai kinga wannan! Wallahi duk abunda ke faruwa ita ta
janyowa kanta. Ta biyewa soyayyar banza gashinan tana
rayuwar bakin ciki. Don ubanta an gayamata yanzu a
wannan zamanin ana yin auren wata soyayya? Soyayyar
wofi kawai,ke bari kiji na fadamaki nan da kike ganina ban
yarda na auri ubanku ba saida na tabbatar yana da gidan
rana. Allah Ya jikan indo(mamanta) bata tab'a runtsawa ba
saida ta tabbatar na sameshi don hutu take hangomin. Ai
d'an hutu sai gidan hutu. Ban tashi nasan wata wahalar
rayuwa ba,family namu gaba d'aya,familin Abba Tukur
babu inda ba'asan mu ba a fad'in garin nan saidai bak'o. A
zamanin marigayi Abba Tukur mahaifina wane irin tashen
arziki ne baiyi ba? Shiyasa bana shiri da marasa hannu da
shuni. Ke kam kin yiwa kanki,har kunya nakeji kawayena da
yan sa idon gidanmu su zo suga yanda kike jego da yaronki.
Kin yiwa kanki Siyama,kin bashi fuska ya rainaki."
Siyama tuni ta soma hawaye,ita kam tana son mijinta
batajin dad'i zantukan Hajiya saidai fa akan dinkunan nan
za'ayita da Jafar. Domin kuwa dole ne ya bayar da
kud'ad'e.
Rumaisa tace
"Yanzu Hajiya dai kiyi mishi magana don Allah."
Hajiya ta mike ta kwantar da yaron a gadonshi
"Shikenan,gobe zan nemeshi."
Daga haka suka shiga hira,duk munanan shawarari suke
bawa Siyama akan Jafar. Kiran da Abba ya shiga kwalawa
Hajiya ne ya sanyata fita da sauri. Sukayi shiru a tsorace
Allah Ya baijisu ba dai.
Fuska a had'e ya dubi Hajiya
"Ina Rumaisa?"
Hajiya ta juya ta kwala mata kira,a d'arare ta fito daga
d'akin,yaronta na uku,Mannir yana tare da Abba. Ta
durkusa
"Gani."
"Wallahi daga yau kika k'ara zuwa gidan nan a kwanakin
nan sai na sab'a maki! Wannan ai sakarcin banza ne,ace
ganin mijinki matafiyi ne shikenan daga haihuwa kinyita min
zarya a gida? Toh ina mai tabbatar maki zan b'ata maki rai
wallahi!! Ki tashi ki ja yaranki ku barmin gida.! Munafuka
kawai!! Ina sane da halayyarki,duk rashin kunyar da kike
yiwa kishiyar surukarki da ita kanta surukar taki duk yana
dawowa kunnena! Bari shi Nuran ya dawo,tunda yana
tsoranki ni zanyi maganar!"
A fusace yayi d'akinsa ya barsu anan jugum jugum,da gudu
gudu Rumaisa ta had'a kawunan yaranta su biyar ras suka
tafi.
Ladi ta damu kwarai da yanda Mama ke d'aure mata fuska
,ta rasa ta ina zata soma bata hakuri. Har magana tayi
kwana biyu amma har lokacin Mama bata sake mata ba.
Koda an tashesu daga makaranta,idan taje shagon ba bata
wani sakar mata fuska ko kad'an. Dayake tun soma zuwa
makarantar Ladi,Mama ta nemi mataimakiya anan
unguwarsu,Saratu. Itama bazawara ce mai yara har uku
mijinta ya rasu. Tana samu kwarai ta karkashin
Mama,daman rayuwace ta wahala sai dakyar take samun
abunda zataci da yaranta bayan tayi wankau.
Rannan dai Mama na zaune akan darduma bayan ta idar da
sallah,Ladi ta matsa gefenta ta zauna. Mama ko kallonta
batayi ba ta k'ara tamke fuskarta.
" Mama don Allah ki yafemin ki bar fushi dani. Nayi maki
kuskure babba amma in sha Allahu bazan k'ara ba. Nayi
matukar yin nadama."
Mama ta tabe baki
"Yo kada kiyi ma Ladi,ai yin naki ma na dole ne. Don baki
samu yanda kikaso ba. Ba'a yiwa namiji rawar kafa haka.
Kije kiyi tayi na daina sanya baki ."
Hawaye suka zubowa Ladi ,ta kwantar da kanta akan
cinyar Mamanta
"Nayi nadama,nasan na aikata ba daidai ba. Bani da mai
rarrashina a duniya sai ke,domin Allah ki yafemin. Bansan
yaushe na fara son yaya jafar ba,amma nayi maki alkawari
daga yau zan yakiceshi a zuciyata. Ki tayani addu'a."
Mama cike da tausayawa ta shafi gashinta
"Zan tayaki,ki manta dashi. Allah Ya yaye maki sonshi idan
ba alheri. Kamar yanda na sha gayamaki ne Matar mutum
kabarinsa. Yanda dole sai ya shiga kabarinsa haka dole sai
ya aureta. Mu dage da addu'a."
Murmushi Ladi tayi,taji dadin maganar Maman nata.
Hawaye suka k'ara gangaro mata ,tayi imanin cire Jafar a
ranta ba k'aramin aiki bane. So kenan ,ba wuya ya
shiga saidai cireshi aiki ja ne .
KAZAMAR GIDA ********21
Anti Habiba ta kurawa Jafar ido tana mamakin yanda ya
rame. Shi kuwa abincin data sanya aka kawo mishi kawai
take narka. Rabonsa da abincin kirki tun ranar daya baro
unguwarsu Ladi. Saida yaci ya k'oshi sannan ya d'ago yana
shan ruwa ya dubi yayarsa. Murmushin yak'e tayi mishi
kafin tace
"Sannu,ka zama gwauro na kwanaki gashi har ka rame."
Jafar shima murmushin yayi yana shafa wuyansa
"Ni kaina ina mamakin ramata antina,mai yiwuwa harda dan
rashin lafiyar da nayi a kwanakin nan ne."
Ta jinjina kanta
"Hakane,Allah Yasa mu dace."
"Amin antina."
Ya d'anyi shiru kafin ya d'ago cike da damuwa ya dubeta
"Anti ga wata matsala fa ta bullo min."
Anti ta fiddo ido cikin fad'uwar gaba tace
"Allahu,meke faruwa kuma Kakana?"
Jafar ya yamutsa fuska kad'an yace
"Hajiyar Siyama tayi kirana jiya,ta bud'emin wuta akan dole
sai na kawo kud'i an dinkawa Siyama kayan fita yawon
arba'in. A cewarta wai tunda ba suturar arziki nake yiwa
Siyamar ba ai ya dace nasan abunda ya kamata nayi mata
kafin ranar ko don gudun abunda munafukai zasu ce cikin
danginsu."
Anti habiba batasan sadda ta runtumo ashariya ba kafin
tayi istigfari daga baya
"Har sun sanyani ashariya,wai me mutanen nan suka
daukemu ne? Na k'ara gaskata cewa Hajiya Maimuna
batasan abunda ya kamata ba. Wannan wane irin sabon
tsirfa ne! Toh wallahi Kakana idan na samu labarin ka bayar
da ko tsinke sai ranka yayi mugun b'aci. Wannan zubda
girma da mutuncin da me yayi kama? Hajiya Maimuna tana
da ilimi amma batasan tayi aiki dashi ba? Toh barni dasu,
zanje har gidan na samu Siyama."
Ta inda anti habiba take shiga batanan take fita ba. Kana
ganinta kasan ta dauki zafi sosai. Jafar dai shiru yayi don
ma bai gayamata gorin arzikin da Hajiyar ke yi mishi ba ai
da baisan yanda antin zatayi ba. A karshe ta k'ara
gargadinshi akan kada ma ya sanarwa Hajja domin tana iya
cewa ya basu don a zauna lafiya.
Da wannan sukayi sallama akan Antin zataje gidan da
kanta.
"Assalamu alaikum."
Ta amsa gami da waigowa don ganin mai sallamar,nan da
nan ta chanja fuska ,Anti Habiba ta lura da ita saidai ta
share ta k'arasa tana mai zama akan kujera.
"Hajiya ina wuni,ya yammaci."
Cikin halin ko'in kula Hajiya ta amsa a takaice
"Lafiya."
Kafin anti habiba tayi wata magana,Siyama ta fito sanye da
riga doguwa na material. Kitson nan tun na suna shine har
yanzu a kan nata bata tsefeshi ba. Ganin Anti Habiba saida
gabanta ya fad'i,ta daure cikin sakin fuska ta k'arasa
"Anti sannu da zuwa."
"Yauwa Siyama,sannunki kema ya jego? Ina d'an namu?"
"Bai jima da kwanciya ba."
Anti habiba ta gyada kanta
"Ki daina kwantar dashi,da zarar yamma tayi anfison a
goya yaro ko a rikeshi a hannu. Allah Ya kiyaye."
"Toh anti,bari na kawomaki ruwa."
Bata hanata ba,bayan fitarta ta dubi Hajiya tana murmushi
"Hajiya magana nazo muyi."
Hajiya wacce har lokacin bata saki fuskarta ba ta dubeta
kad'an sannan ta dauke kanta tare da rage sautin TV da
take kallo.
Wannan ya nunawa Anti cewar tana sauraronta.
"Naji wani sabon al'amari ne daga bakin Jafar akan sai
yayiwa ankon fita yawon arba'in wanda ko kusa ni ban
tabajin inda akayi wannan ba ko a al'adance. Toh
kasancewar kinsan shirme na kannenmu na yara mata
yanzu naga gwara nazo da kaina naji koda saninki ne
Siyama ta tafka wannan kuruciyar ko kuwa dai ta rufeki
ne?"
Tunda tayi kiran sunan Jafar a maganar,Hajiya ta soma
jifanta da wani gira, tana mai k'ara hade gira. Saida
takai aya sannan Hajiya ta soma magana cike da gadara.
"Tushen zancen daga uwar Siyama ta fito ba Siyamar ba.
Kayane Jafar zai yiwa Siyama domin duk cikin kayanta
daga na lefe zuwa na suna da yayi banga wata tsiyar da
Siyama zata sanya ta shiga zuri'ar Abba Tukur da sunan
yawon zumuncin arba'in ba Habiba. Don haka idan ma wai
turoki yayi don ya nemi alfarmar a janye wannan bamai
yiwuwa bane,d'iyata bata tab'a sanya k'aramar atamfa ko
leshi ta shiga taron mutane ba saida taje gidan Jafar.
Wannan abun kunyar bazan k'ara bari a maimaita mini shi
ba ni Maimuna. Gwara ki tashi kije ki ja mishi kunne ya cika
umarnina ya sauke hakkin dake rataye a wuyanshi."
Tana maganar ne hankali kwance har ma tana chanje
chanjan channels,tuni Siyama ta dawo daga kawo ruwa ta
dire tana gefe jiki ba kwari ganin yanda anti habiba ta gama
fusata. Wannan yasa Hajiya tana kaiwa aya,ta cafe
"Haba Hajiya,wannan irin magana bai dace yana fitowa
daga bakinki ba. Inace da Jafar da Siyama duk d'aya ne a
wajenki..."
Da sauri Hajiya ta dakatar da ita
"A'a a'a,menene had'in kashi da fura? Gyara maganarki
Habiba. Kada ki manta Siyama d'iyar cikina ce."
"Naji wannan,toh amma ku sani,Jafar yayi iyakar kokarinsa
akan d'iyarki tun kafin zuwan wannan rana. Kada ma kiji
da wai,tun suna saurayi da budurwa babu kalar hidimar da
Jafar baya yiwa Siyama gatanan zaune ki tambayeta.
,abar wannan batun ma,ke Siyama kiyi rantsuwa da Allah
Jafar bai siya maki suturu masu tsada daidai karfin
aljihunsa? Wane irin kulawa kike baiwa suturinki? Toh
hajiya kafin ki soma zagin Jafar ki soma zagin
Siyama,domin ni tunda nake a rayuwa ban taba cin karo da
wacce bata damu da kula da komai na rayuwarta ba sai
Siyama. Alhamdulillah,Jafar bashi da arzikin siyan manya
sufofi da shaddodi a haka Jafar bai fasa yi mata siyayyan
kaya na adon fuska da jiki. Ko cikin kala ukun da Jafar yayi
na suna,Hajiya saidai ki take gaskiya amma a matsayinki
na wacce ta saba d'ora super da sauran tsadaddun yaduna
da sarkoki kinsan Jafar ya sayi abunda yafi karfin aljihunsa
hakanan rago har biyu ya samarwa d'ansa na sunansa.
Idan duka wadannan basuyi maku ba sai ki k'ara sanya
diyarki a d'aki ki bata ilimi akan zamantakewar aure,babban
abunda ke kod'ar da suturunta bai wuce kasacewarta
muguwar k'azama ba! Amma nayi rantsuwa ba zanyi
kaffara ba ko tsinke na Jafar ba zaku samu ba idan yaso
tayi yawo tsirara!"
Daga haka anti ta mike tayi hanyar fita,Hajiya ta kurma ihu
"Nashiga uku ni Maimuna! Habiba ashe ke yar iska ce
bansani ba? Ni kike gayawa bakaken maganganu? Shegiya
wacce batayi gadon arziki ba. Wallahi har gidan uwartaki
zan shiga,daman haka kike?"
Tuni Anti habiba tayi waje,daman saida ta soma shiga
gidansu ta gama yininta sannan ta shiga ko hajja batasan
kudurinta kenan ba. Titi kawai ta nufa ta hau mota ta tafi.
Hajiya sai ashar takeyi,Siyama banda kuka babu abunda
takeyi. A fusace ta kai mata bugu
"Yar iskar yarinya! Duk kece kika janyomin wannan bakin
cikin! Amma wallahi kowa yaci tuwo dani miya tyuy yasha
(hope hakane)!"
A fusace tayi dakinta sai gata ta fito da mayafi akanta tayi
hanyar waje,ganin haka da sauri Siyama ta rikota tana kuka
"Don Allah Hajiya kada kije gidan,abar maganar kayan."
A fusace ta wanke mata fuska da mari ta tureta
"Allah Ya sauwake da hali irin naki Siyama! Banza
shashashar wofi kawai wacce batasan a tab'a uwarta ba
taji zafi. Toh na rantse yau sai na rama akan Fa'iza.!!!"
Daga haka tayi waje tabar Siyama anan tana kuka,can
kuma ta jiyo kukan Faruk ta mike ta nufi wajensa.
Hajja tana zaune akan darduma tana lazumi yayinda
Bahijja ke gefe tana koyawa kannenta aikin makaranta
kasancewar tuni ita ta kammala sakandire har ana shirye
shiryen aurenta.
Babu sallama babu komai ta bankad'o labulen ta fad'o
d'akin. Gaba d'aya suka dubeta a tsorace,saida gaban
Hajja ya fad'i don tasan ko menene ba alheri ne ya kawota
ba.
"Gurinki nazo Fa'iza,ashe kin haifi 'yar iskar yarinya
wacce bata ganin mutuncin na gaba da it a acikin yaranki
banda labari?"
Da sauri Bahijja ta mike ta ja kannenta sukayi d'aki ranta a
b'ace tasan cin mutuncin mahaifiyarsu za'ayi kawai.
Hajja ta shafa addu'arta kafin ta dago ta dubi Hajiya dake
faman huci
"Meyayi zafi haka Hajiya Maimuna? Anyi wani abun ne?"
"Kaji munafuncin banza,wallahi Fa'iza saidai ki rainawa
wata saunar hankali ba ni Maimuna ba. Har kin isa ki turomin
Habiba gidana taci min mutunci? Wacece ita? Me akayi
akayita? Ai wallahi ko ke baki isa ki nunamin yatsa ban
karyashi ba balle kuma 'yar cikinki.! Duk asirce asircen da
kukayi kuka kukuta yarinyar nan ta zauce akan d'anki baiyi
maku ba sai kun biyoni gida da cin zarafi saboda nace Jafaru
ya yiwa Siyama kayan fita yawon arba'in?!!"
Hajiya tayi ta zazzaga rashin mutunci kamar yanda ta
dungayi a baya lokacin bikin Jafar da Siyamar. Ran Hajja
yayi tsananin b'aci,mace mai hakuri bata ce komai ba har
Hajiya ta kammala sannan ta samu bakin magana
"Haba Hajiya Maimuna,kinsan da ace nasan abunda ke
faruwa da duk hakan bazai faru ba ko? Menene abun zafi
ciki? Ai inda shi kanshi yaron ya sanarmin da an dad'e da
biya muku bukatarku. Amma kiyi hakuri za'a kawo,sannan
zan yiwa yarinyar magana.."
"Mtsww,kada ma kiyi don Allah Fa'iza,karkari na samu
Rilwanun da kanshi naji ko da saninshi kike sanyawa
acimin zarafi har gidana."
Daga haka Hajiya ta fice kamar zata tashi sama don
masifa.
Tana fita Hajja ta kirawo Bahijja wacce ke kukan bakin ciki
daga d'aki na wannan cin zarafin da akazo aka yiwa
mahaifiyarta.
"Bahijjah bakya jina ne?!"
Da sauri Bahijja ta fito daga d'akinsu ta durkusa
"Na'am Hajjah."
Hajja ba tare data dubeta ba tace
"Kiramin layinta!"
Ta fada,nan da nan Bahijja ta gane wacce ake nufi
kasancewar Hajjah bata ambaton sunan Habiba
amatsayinta na babbar d'iyarta. Ta dubi Hajja
"Hajja a kashe wayarta."
Hajja ta kara daure fuska tamau
******22
"Yayi kyau,burinta ya cika anzo har gida ancimin zarafi. Ki
kiramin babana kice maza yazo yanzu inason ganinsa."
Jafar yana kasuwa ya samu kira daga Hajjah. Da hanzari
ya dauka. Jin muryar Bahijja ya sanyashi tambayar ko
lafiya. Cikin rawar murya ta sanar dashi kiran Hajja.
Hankalinsa ya tashi,da azama yayiwa Ibrahim da sauran
mazauna gaban shagon sallama ya nufi hanyar tafiya.
Tana daga kofar wani kantin siyarda kayan shafe
shafe,kamar ance ta d'aga idonta ta hangoshi yana shirin
ficewa daga bakin kantunan da take. Gabanta ya
fad'i,rabonta dashi tun ranar daya kawo mata ziyara. Da
sauri ta kauda kanta cikin matsanancin tashin hankalin
ganin yanda ya rame. Kwallah ta cika mata ido,
"Kanwata ga chanjinki."
Ta karb'a ta rarumi ledar mayukanta ta bar wajen.
Soyayyarsa sabuwa na nukurkusarta,saidai ta daukarwa
kanta alk'awarin daina shiga huruminsa koda hakan illah ce
ga zuciya da gangar jikinta. Saukinta ma ya dauke kafarsa
kwata kwata daga shagon nasu.
Cikin taimakon Ubangiji,aka had'a dubu hamsin
aka kaiwa Hajiya batare da sanin Abba ba domin
muddin yaji har kanin nasa rilwanu sai ya
b'atawa rai.
Tana cika arba'in,yan uwan sukaje sukayi mata
gyaran gida a daren Abba yace lallai saita koma
duk da ba haka Hajiya taso ba,so tayi sai
washegarin ranar. Jafar jinsa yakeyi tamkar wani
sabon ango ,gaba daya ya mance da batun
wata damuwa da suka haddasa mishi. Ranar kam
ya gwangwaje abinsa.
Rayuwarsu ta cigaba da tafiya a haka,Jafar yana
jin tsananin kaunar Faruk a zuciyarsa,kullum ya
dawo cikin yi mishi wasa yake. Bashi da matsalar
cima,saboda miya cikin cooler Hajja ta aikomusu
saidai suyi ta dahuwar shinkafa ko macaroni
suci. Dauda ya dawo kan aikinsa,hatta wankin
kayan Faruk shine keda alhakin yinshi. Sai bayan
da miya ta k'are ta soma shiga kicin. Girkinta na
farko bayan dawowarta sai ya zamana yafi na
baya rashin dadi sakamakon babu abunda take
tsinanawa a zaman da tayi na arba'in saidai taci
ta kwanta. Loma d'aya yayi ya mike,ta dubeshi
lokacin da take zaune tana shayar da Faruk
"Menene kuma?"
Ya yamutsa fuska
"Miyarki tayi tsami ga gishiri yaso yayi
yawa,menene ya janyo tayi duhu haka ma?"
Ta tab'e baki
"Ni kaina bansan tayi yawa ba saida na kammala
kasan ni banason yin d'and'ane."
"Allah Ya kyauta,nikam na koshi bazan iya ci
ba na gwammace nasha shayi. "
Ya fice, ta harareshi tayi kwafa ta rufe da tsaki.
Ai mai hali baya fasa halinsa. Ta ayyana a ranta.
Ta janyo taci cokali daya da sauri ta furzar tana
mai hanzarin kwara ruwa a bakin nata. Tasan
gaskiya ya fad'a amma saidai yayi hakuri,ita bata
saba da girki ba a gidansu babu abunda Hajiya ke
sanyata don ma tana sonshi ne take damuwa.
Sati uku da dawowar Siyama ya zamewa Jafar
kamar shekaru uku cikin masifa. Kazantarta ya
ninka na baya, haka zai shigo ya tarar da famfas
da aka cirewa yaro akan hannun kujera ba'a
dauke ba,ga karnin tumbud'i da yaronsa keyi ba
don babu turaren sanya mishi ba. Tun yana
d'okin dawowa gidan yazo ya daina. Kwata
kwata sai yaji shayin ya ginsheshi,don babu ranar
da baya sha. Hakan yasa dole ya koma gidan
jiya,yawon gidajen abinci. Saidai kamar asiri,baya
gamsuwa da abincin inda ya koma zuwa,babu
abunda yake muradi sai daddadar miyarnan ta
Maman Ladi. Gashi a gefe guda kwata kwata
bayason nufar shagon. Da dai yaga babu gata
saita Allah,rannan yana fitowa daga shagonsu
misalin karfe uku na rana,cikin jin wata
azababbiyar yunwa kawai sai ya nufi shagon
gabansa yana dukan uku uku. Bayason
ganinta,yafiso yayita danne abunda yakeji a
zuciyarsa...bayason ya bayyana a ganinsa abun
kunyane a gareshi. Kada ma ace Haris yaji
labari.... Da wannan tunanin yayi kundunbalan
dakewa gami da yin sallama da tura kansa
shagon.....!
Nan mutanen wajen suka dubeshi,yayi musu sallama kafin
ya zauna cike da mamakin ganin wata budurwa a
maimakon Ladi. Ta k'araso gareshi
"Sannu da zuwa,me za'a kawo maka?"
Kafin ya bata amsa Mama ta fito daga d'an store din da
suke ajiyar kaya. Ganin Jafar ta fadada fara'arta tana mai
k'arasawa,Jafar ya russuna kamar yanda ya saba ya
gaisheta ta amsa fuska a sake
"Jafar sai kuma aka nema aka rasa,amma baka kyauta ba
ai ko gaisawa saika leko ayi."
Yayi murmushi
"Ayi hakuri Mama,ni kaina banji dadin abunda nayi ba."
Tayi murmushi ta dubi Sarah
"Had'o mishi tuwo."
Bayan tafiyar Sarah,ta dubeshi
"Jafar ashe wautar da Ladi ta aikata gareka kenan? Kayi
hakuri,wallahi ban samu labarin ba sai bayan da komai ya
fito. Da ace na sani da bazan barta ba ta aikata maka ba."
Jafar yayi murmushin yak'e,faduwar gabansa ta k'aru jin ta
ambaci Ladi.
"Bakomai Mama,komai ya wuce."
Daganan Mama tayi mishi addu'ar fatan alherin haihuwar
da matarsa tayi sannan ta koma bakin abincinta.
Sarah ta jera mishi komai,ganin ruwa kad'ai ta kawo ya
tambayeta lemo. Ta juya ta dauko mishi ta ajiye sannan ta
bar wurin. Jiki a sanyaye ya soma cin abincin yana ji kamar
ya tambayi Mama inda Ladi take saidai yana jin nauyin
hakan. Ya fahimci sam bata wajen.
Sanye da atamfa orange,dinkin riga da siket ya zauna tsaf a
jikinta. Ta yafa wadataccen mayafi bak'i hakanan
takalminta bak'i,fuskarta kana gani kasan a gajiye take
domin kuwa daga makaranta take. Tana kokarin shiga
shagon ta hangoshi zaune yana cin abinci cikin nutsuwarshi
da kan burgeta matuka. Ta dafe kirjinta dake bugu da
sauri,cikin azama tayi baya ta koma. Bataso ta had'u
dashi,gaba d'aya yanzu tsoronsa takeji. Ga matsananciyar
kunyar abunda ta aikata gareshi,banda ma abu irin nata. Ina
ita ina Jafar? Matashi kyakkyawa daidai gwargwado,gashi
bai rasa abun hannu ba ai itama tayi ganganci. Waje ta
samu a gefe ta tsaye,takai kusan mintuna biyar tana sak'e
sak'en da dube duben hanya har saida ta tabbatar da ya
fice daga shagon sannan ta sauke ajiyar zuciya ta shige.
Koda taje nan Mama ke sanar da ita zuwansa. Murmushi
kawai tayi wanda iyakarsa lebbanta,daganan ta zauna taci
tayi nak ta huta kafin ta taimaka da wasu aikace
aikacen,idanuwanta sun gaza daina ganinsa. Soyayyarsa
mai zafi tana k'ara cika zuciyarta....!
******
Tun daga wannan ranar Jafar ya shiga zarya shagon abinci.
Babban burinsa bai wuce yayi tozali da Hadiyya ba wanda
zuwa yanzu ya gaza hakura da dukkan wani yanayin da
yake tsintar kansa ciki game da ita. Ita kuwa Hadiyya saima
ta dauke kafarta daga zuwa shagon tana fakewa da
makaranta,Mama bata fiye matsa mata ba akan sai taje
saboda yarda da tayi akan tabbas karatun ne yake hanata
zuwan.
Har akayi sati biyu a hakan amma Allah bai sanya sun
had'u ba. Abun yana matukar damun Jafar wannan ya
janyo har yakan chanja lokutan ziyararsa saidai fa bata
chanja zani ba sai ya soma zargin kodai ta daina zuwa ne
gaba d'aya? Yana jin nauyin tambayar Mama batunta
amma ya gama shiga damuwa ta karshe akan rashin
ganinta.
*****
BA ZATO BA TSAMMANI......
******23
Bata tab'a kawowa zaizo a wannan lokacin ba. Ganin har
uku da rabi ta wuce ya sanya batayi wani tunani ba ta tura
kanta cikin shagon da sallamarta. Da sauri ya d'ago kansa
yana mai ajiye kofin ruwan daya sha akan tebur. Ido
cikin ido suka dubi junansu. Babu wanda baiji shock ba
kamar yanda gabansu ya bada dam a lokaci guda. Wani
kallo da ya jefata dashi batasan lokacin data rausayar da
idanuwanta ba sannan tayi azamar kauda su gefe tana mai
sunkuyar da kanta cikin mutuwar jiki ta k'arasa ciki sosai
va tare da tayi yunkurin koda gaisheshi ba. Sarah ta dubeta
"Yau dai kin makara Ladi."
Tayi murmushi tana mai ji a jikinta ita yake kallo hakan
yasa bata ko waiga ba balle ta damu da sanin adadin
mutanen dake wajen.
"Bari kawai Sarah,yau ana rana. Zama nayi cikin masallaci
na d'an huta kafin nayo gida,gobe kam lakcar yamma
garemu. Ina mama?"
"Taje gida tuni,ko kin manta yau zasu amshi lefan Rabi'a
?"
Ta dafa kanta
"Kash,wallahi na manta ai da ban shantake ba nazo na
taimaka maki."
Sarah tayi dariya
"Haba babu komai ai. Kinsan na saba da wankau balle
kuma wannan aikin da nake mishi kallon wasan yara?"
Sukayi dariya,kamar ance ta juya tayi ido hud'u dashi. Ta
kasa dauke kwayar idonta daga cikin nashi,wani yanayi
kakkarfa yana zagaye dukkan jikinsu. Ga mamakinta sai
taga ya sakar mata murmushi,ta lumshe ido ta budesu a
zatonta she's dreaming saidai har lokacin bai gushe ba
yana yi mata. Tayi hanzari kauda fuskarta ta juya
baya,hawaye suka taho mata tana mayarda ajiyar zuciya da
sauri da sauri.
"Kanwata."
Tayi tarr da idanuwanta,Sarah ta tabota
"Kije ki amso kud'in."
Sarah dake wanke wanke ta fad'a,dolenta ta juya ta nufeshi
kanta a k'asa....!
Ta russuna kamar yanda ta saba tana jiransa ya miko
kudin. Jin da tayi shiru ne ya sanyata dago idanuwanta taga
dalilin tsayuwarshi. Karaf suka hada ido ya kara sakin
murmushi kafin yace
"Kanwata yau baza'a gaisheni ba? Ko kinfiso nace DEEYA?"
Ta dubeshi cike da mamaki,gabanta yaci gaba da dukan
tara tara,sai kuma ta daure fuska tana mai kauda kanta.
"Ina wuni."
"Bazan amsa ba tunda saida na rok'a."
Ta dan tabe baki,batace komai ba. Ya miko mata kud'in ta
karb'a tare da mikewa
"Ki tausayawa yaya j,ki bude wayarki anjima zanyi kiranki
please."
Bata juyo ba balle ta bashi amsa.saidai tayi gaba cike da
mamakinshi. Shi d'inne kuwa? Ta adana kudin tana mai
murmushin mugunta. Abunda bai sani ba tun lokacin da
abun ya faru ta yankewa kanta cigaba da amfani da Sim
din,a niyyarta ma tabar rike waya saidai sanin hakan ba
mai yiwuwa bane saboda matukar amfaninta gareta,ga
Basma dake yawan kiranta a layin mama tana korafin bata
samunta. Dole saida ta ciro wayar ta karya layin da bata
muradinshi kwata kwata kafin tayi restoring dinta. Wayar ta
dawo kamar ranar aka soma amfani da ita. Ta sayi sabon
layi ta sanya har Mama tana murmushi ganin abunda tayi.
Batasan lokacin daya bar shagon ba kasancewar ta juya
masa baya. Saidai har suka tashi bata bar mamakin abunda
ya faru ba. Idan ta tuno irin kallon da yakeyi gareta,da kuma
sassanyar murmushinsa duk sai taji ranta yayi haske wani
irin nishadi takeji har Sarah saida ta fahimci hakan. Take
tsokanarta
"Wai yau wane albishir akayi maki a makarantar ne?"
Murmushi kawai tayi ba tare data bata amsa ba. Soyayya
kenan,da wuya da dadi....!
*****
Ya dunga kiran layin ana cewa a kashe,zuciyarsa duk babu
dadi. Yaci burin jin muryarta mai sanyashi nutsuwa. Yayi
kewar muryar ba kad'an ba,kusan wata daya kenan
rabonshi da gani da jin muryarta. Sai yau ya ganta yaga ta
kara kyau a idanunsa. Ya lumshe ido yana murmushi sadda
kamanninta ke dawo masa.
Bak'a ce saidai ba can ba,tana da siririyar fuska,hancinta
bai cika tsawo ba saidai bata daga layin marassa hanci
irinna o'o ,ya lura tana da gashi sakamakon koda ta
rufeshi baya rufuwa hakanan gashinan yayi kwance a
saman goshinta. Idan ana maganar diri,nan ma baza'a bar
Hadiyya a baya ba. Kallo d'aya ya isa gamsar da mutum
macece. Ashe dai Hadiyya ba abar yarwa bace?
"Jafar! Jafar!!"
Jin muryar Siyama yaji a tsakar kansa tana kwala mishi
kira tare da jijjigashi. Yayi firgigit ya dawo hayyacinsa yana
kallonta
"Lafiya?"
Ta harareshi tana mai jan karamin tsaki
"Me kake tunani ne tun dazu nake kiranka amma shiru? Ka
fita Haris yana sallama dakai a waje."
Ya mik'e yana mai takaicin halin rashin kunya irin na
Siyama da sam bata iya tauna magana ba kafin ta fad'eshi.
T-shirt ya zura akan singiletinsa sai wando iyakar gwuiwa.
Lokacin ba'a jima da yin sallar Magriba ba,ya fita yana
mamakin abunda zai kawo Haris gidansa adaidai wannan
lokacin.
Yana zaune cikin motarsa ya zuro k'afa d'aya waje. Jafar
ya zagaya ya shiga ciki ya zauna sukayi musabaha. Ganin
fuskar Haris da alamun damuwa yace
"Lafiya na ganka wani iri kuwa?"
Haris ya sauke ajiyar zuciya
"Dole ai ka ganni haka,Ummina ce take neman rikitani da
daren nan."
"Toh,menene ya faru?"
"Kishin fa? Akan tayi kirana har sau biyar ban amsa ba
kuma sanin da tayi ina gidana ne ya sanyata zargi. Nayi
rarrashin duniya tak'i saukowa. Bayan wannan kuma na
kara laifi,kwana biyun da nayi gidan Rahma ayyuka sunmin
yawa na kasa lekawa wajensu saidai waya kaga dole nayi
laifi. Nidai yanzu taimakamin zakayi muje ka bata hakuri ko
zata hakura na gaji da wannan horon rashin kulani da
takeyi wallahi na damu sosai na gaza samun kwanciyar
hankalina."
Jafar yace
"Shikenan,kayi jirana na chanja kaya."
"Kai haba,muje kawai mana."
Jafar ya harareshi yana kokarin bude motar
"Ta yaya zanje gaban suruka a haka? Nida zanyi sulhu
saita rainani."
Sukayi dariya sannan Jafar ya koma ciki. Ya sanya dogon
wandon jeans,ya chanja t-shirt sannan ya leka Siyama.
"Madam bari muje mu dawo."
Ta tsaida idanunta gareshi tana k'are mishi kallo. Yayi fes
dashi sai kamshi yake. Zargi ya d'arsu a zuciyarta,kada dai
zance Jafar zaije?
"Ina zakaje?"
Kallo d'aya ya yiwa kwayar idanunta ya hango matsanancin
kishi,wani shu'umin murmushi yayi yana kasheta da
kallonsa mai rikita gangar jikinta
"Wajen kanwarki zaimin rakiya,yanzu zamu dawo."
Da sauri ta nufoshi ai kuwa ya juya ya fita a guje yana
dariya ya barta tana huci. Ta kasa zaune,wai meke faruwa
ne? Ya Salam,no!!! Jafar bazai taba aure ba!!! Bai isa ba!!!!!!
Bazai sanya Hajiya da yan uwana suyimin dariya ba!!!!! Har
abada!!!!! Nawa ne ni kad'ai!! Babu wacce ya isa ya so!!!
****
"Yana sona,yana kaunata. Naga hakan a kwayar
idanuwansa. Bazan barshi ba saidai zan bashi wahala
kamar yanda ya wahalarmin da zuciyata. Saidai ina burin
zama matar yaya j!!! Allah Ya azurtani da samunshi
matsayin mijina!!!"
Cewar Ladi kenan a ranta,tana zaune ita d'aya a falonsu
yayin data zubawa lambarsa ido wanda ta riga ta haddace a
kwakwalwarta,tana kallo tana murmushi....!!!!!!
******24
Dakyar Jafar ya lallaba Abida ta hanyar nasiha da ban baki
har dai ta sauko sai gashi itace har da hira da dariya. Haris
kamar ya shige jikinta tsabar jin dadi. Jafar kam wannan ba
bakon abu bane a wajenshi,yasan soyayyarsu sosai don
Haris bai kunyarsa. Ya mike tsaye yana duban agogon
bangon
"Sha daya saura? Lallai na zaunu a gidan nan,nasan
madam tana can a cike."
Haris ya mike tsaye yana dariya
"Ahaf,Allah Sarki madam,munyi mata laifi kam."
Jafar na dariya yace
"Don ma bakasan me nace mata bane."
Ya basu labarin yanda sukayi,dariya duk suka sanya har
Ummi. Kafin Ummi tace
"Lallai ka b'allo ruwa Jafar. Kishi babu sauki."
Jafar yayi murmushi kawai ya dubi Haris
"Sai kazo ka mayar dani ko?"
Haris ya harareshi
"Gaskiya saidai na baka mukullin idan yaso da safe sai
nazo na karb'a. Bazan iya fita ko'ina ba nabar Ummina."
Ai sai ran Ummi ya k'ara sanyi sosai,tayi wani murmushin
jin dadi.
Hakan kuwa sukayi,ya rakashi har kofa. Anan ma Jafar ya
dubeshi cike da damuwa
"Kasan Allah,nima na soma tunanin k'ara auren nan. Na gaji
da halayyar Siyama."
Haris yace
"Wai har yanzu bata chanja zani bane?"
Ya tab'e baki kad'an yana mai numfasawa
"Ta ina fa? Abun ma sai k'ara gaba yakeyi Haris. Nikam na
gaji,zan auro wacce ta iya tsafta da girki ko don na more
rayuwar aure. Ko a wajen Allah bani da laifi,bayan da auren
sama da d'aya ya zama halal,na bawa Siyama dama da
yawa don ta gyara saidai hakan ko kadan bai samu ba duk
hakurin da nakeyi da ita. Babu mai tsaidani gun k'ara auren
nan saidai idan Allah Ya kaddaro bazanyi bane."
Haris cikin damuwa da tausayawa Jafar yace
"Gaskiyane,ni shaidane akan hakurin da kayi. Toh kana da
wacce zaka aura ne?"
Jafar ya basar tamkar baiji ba yana mai kauda kansa gefe
kafin ya juyo
"Wai ya ciwon k'afar Hajiyarmu ne? Na kwana biyu ban leka
ba amma inason shiga wajen gobe. Ga babbar sallah baifi
saura wata biyu ba."
Haris yayi dariya
"Hajiya sunje Jeddah a k'ara duba kafar watakila aiki za'ayi
mata. Tare da Yaya Muttaka suka tafi. Baka bani amsar
tambayata ba,wacece amaryar?"
Jafar ya hau sosa karan hancinsa yana murmushi kafin ya
yamutse fuska
"Wai ma meye ruwanka? Kai malam nifa inada kishi ok?
So,ka rabu da wannan maganar ma,bazan iya gwada maka
ko wacece ba yanzu. Saida safe."
Ya fada motar yana kokarin tayarwa,Haris yana tuntsira
dariya
"Dan iskan karya,idan tayi wari zanji ne. Gama kumbiya
kumbiyarka..."
Jafar yana dariya yaja motar ya bar layin ba tare da ya
bashi amsar komai ba.
Ya kalleta yaga tana faman huci ta cika tayi fam,yayi
mugun murmushi
"Zaki bani hanya na shige ko kuwa dai anan zamu kwana?"
Ta kauce tayi ciki a zuciye,har lokacin bai bar murmushinsa
ba. Bayan ya rufe kofar ya shiga ciki. Yana kokarin bud'e
d'akin yaji muryarta
"Jafar baka isa ka k'ara aure ka kawo wata gidan nan ba
wallahi. Har ni zakayiwa haka?"
Baice mata uffan ba har ya shige ya soma rage kayan
jikinsa
"Ina magana kayi shiru? Nasan duk wannan zugar daga
Haris take. Ganin da yayi ya k'ara aure shine yake neman
ya doraka a hanyar daya bi ko? Toh wallahi ku sani,ni ba
Ummi bace da kuka rainawa hankali ita kuma ta iya dauka!
Dole ne ayau na shaida maka ni Siyama ni kadai ce
mallakinka....."
"Ke wai baki da hankali ne? Kin cikamin dodon kunne,ga
bacci inaji. Please get out?!!!"
Ya fada cikin daga murya don tun yana dariya har ta soma
bashi haushi. Ta juya sumi sumi ta fice tana kunkuni,ashe
dai dagaske yake auren yake nema. Lallai Jafar mugun
butulu ne,duk yanda ta bijirewa zabin hajiyarta ta amince
zata zauna dashi a halin da yake na wanda bai ajiye komai
ba shine don tsabagen rainin hankali har yake da bakin ce
mata yaje wajen kanwarta?
Daren kwanan bakin ciki Siyama tayi,batasan tana son
mijinta ba sai yanzu.
******
Bayan sati daya da yin haka,dakyar tabar fushinta ta sauko
da Jafar ya shaida mata wasa yakeyi.
Zuwa lokacin ya gama kaiwa kololuwar damuwa na
rashin ji da ganin Ladi. Gaba daya ta dauke kafarta daga
shagon,gashi yana jin kunyar Mama bazai iya tambayarta
komai game da Ladi ba.
Ladi kuwa duk da cewa tana zumudi da son yin tozali da
yaya j,wannanbaisa ta amince ta kuma bayar da kanta ba.
Tana sane take mishi hakan,taci sa'a lokacin suna kan
rubuta exams,da wannan ta fake ta cewa Mama bazata
samu damar zuwa shago ba har sai sun kammala.
*****
Wata ranar alhamis Ladi ta dauki matsananciyar kwalliya
cikin wani rantsetsan material kalar orange. Mai adon
duwatsu,riga da siket ne sun zauna cif a jikinta. Ta tufke
gashinta da manyan ribbons guda biyu ana hangensu ta
cikin wadataccen mayafin data yafa a saman kanta.
Hannunta rike da wayarta sai karamar jakarta data ratayo a
kafad'a tana shirin sanya kanta cikin shagon sukayi kicibus
dashi yana shirin fitowa.
Kamshin turarensa ya bugi hancinta da sauri taja baya ta
d'ago tana dubansa. Ya ganta a rashin zato da
tsammaninsa. Tuni ya fidda ran sanyata a idonsa a wannan
ranar ma ganin ya kwashi fiye da mintuna talatin saboda
son yaga sunyi arba.
Ya gama sace zuciyarta,a yau saita kara ganin ya kara kyau
agareta. Da wannan farin cikin ta fada shagonsu.
******
Karfe takwas na dare sai gashi yayi kiranta. Lokacin tana
cin abinci,har ya gama ringing bata dauka ba. Ana biyu ne
ta amsa kiran
"Assalamu alaikum."
Ya amsa da sauri ya k'ara da cewa
"Ina kika shiga inata kira deeya? Ko aljanar ta hau kanki?"
Tayi dariyar maganarsa
"Hum,har yanzu kana yimin kallon aljana kenan?"
Shima dariyar ya danyi
"Ai kece kika kira kanki da aljana kinga kuwa bani da laifi
ko? Ina fatan Deeya ta yafewa Yaya j dinta?"
"Sai batun yafiya kakeyi,alhalin ko kusa ni bansan lokacin
da kayimin laifi ba yaya j. Laifina ne ba naka ba,ni yafi
cancanta na baka hakuri ba kaine yafi dacewa ka bani ba."
Yayi murmushi ya kara gyara zamanshi a cikin motar Haris,
wanda ke tuk'i yana sauraronsa.
"Kada ki damu Deeya,donta ni na yafemaki ban rikeki a
zuciyata ba kinji?"
Wani sanyin dadi ya mamaye zuciyarta
"Naji yaya j,nagode."
"Yauwa ko kefa deeyata,yaushe zanzo muyi magana?"
Ladi ta ture kwanon tuwonta
"Duk sadda kazo ina maraba dakai."
Yayi murmushi lokacin daya dubi Haris wanda ya tsaya a
kofar gidan iyayensa.
"Shikenan deeya,gobe in sha Allah zan shigo."
"Toh yaya j."
Daga haka sukayi sallama.
Haris ya dubeshi yana murmushi
"Menene matsalarka kai kuma?"
Jafar yayi furucin yana harararsa da murmushi dauke akan
fuskarsa.
Hakan ya bawa Haris damar tuntsirewa da dariya
"Menene kuwa banda abun boye daya fito fili. Daman na
jima ina zargin soyayya kukeyi da wannan kanwartaka.
Dole Ibrahim yaji wannan maganar ma don ya tayani
dariya. Wato yanzu har gidansu ma ka sani?"
Jafar ya tabe baki hadi da murmusawa
"Kana da aiki fa malam,toh idan ma soyayya mukeyi
menene a ciki? Kai karewa ma aurenta nakeson nayi idan
Allah Ya yarda."
Haris ya bude baki cikin mamaki
"Wai daman rannan dagaske kakeyi da kace mini kanason
kara aure? Wacece wannan data ture gwamnatin Siyama?"
Jafar ya girgiza kansa
"Babu wanda ya isa ya ture gwamnatinta a zuciyana kaji
ko? Yauwa,kabar zancen nan ma please. Itama nata
bangaren ta samu wanda banyi zaton akwai shi ba a
zuciyata."
Haris yayi murmushi
******25
"Ince dai ka taba ganinta kada kaje kaga ba daidai ba."
"Na taba ganinta mana."
Jin Haris zai kara wata tambayar ne ya sanyashi saurin
fitowa
"Malam mu shiga mu gaida Hajiya dare yana yi mana."
Haris ya fito yana dariya kafin su shiga.
Hajiya Ummuhani taji dadin zuwansu sosai,ta dubi Jafar
"Daman ana ganinka Jafaru? Ya wajen su Hajja?"
Jafar yana dariya ya amsa mata,yayi mata sannu da
dawowa gami da tambayar lafiyar kafarta.
Sun jima har abinci sukaci,kafin tayi musu nasihohi a
karshe suka nufi bangaren Alhaji Muniru nan dinma
gaisuwa ce da tambayar iyali. Shima ya dora da nashi
nasihohin akan tsoron Allah a karshe sukayi musu
sallama....!
********
Mama ta kasa kunne tana sauraronta har ta kammala
jawabinta. Tayi murmushi
"Ai shikenan,Allah Ya tabbatar da alheri. Sai ki kiyaye kada
ki sake karya ta shiga cikin mu amalarku. Kiyita addu'ar
neman zab'in Ubangijinki."
Hadiyya tayi murmushi ta gyada kanta
"In sha Allah zan dage da addua mama,kema ki tayani."
"Kullum cikin yinta nakeyi."
Daga nan suka cigaba da hira abinsu.
****
Taci kwalliya cikin riga doguwa na leshi ja. Tayi kyau abinta
tsaf. Ta feshe jikinta da turare. Cikin takun burgewa ta isa
ga Mamanta
"Mama saina dawo."
Ta dago kanta daga kwanciyar da tayi ta dubi diyarta tana
murmushi
"Lallai an fito. Toh saiki kula ki tsare mutuncinki. Ki kiyayi
harshenki da abubuwan da addininmu ya haramta. Allah
Yayi albarka,kya gaidamin d'an nawa."
A kunyace Hadiyya ta amsa da toh sannan ta fita. Wannan
karon kujeru biyu ta fitar musu dashi. Yana zaune saman
mashin dinsa yana danne dannen wayarsa. Ta ajiye a jikin
bangon gidansu sannan ta karasa gareshi,yanda ya zuba
mata mayatattun idanuwansa ne yasa dole ta kauda nata
idanun daga gareshi.
"Assalamu alaikum."
Ya katseta,ta amsa gami da russunawa kadan ta gaisheshi
ta tambayi lafiyar iyalinsa,ya amsa har lokacin kwayar
idanunsa sun gaza barin kallonta.
"Bismillah yaya j."
Ta mike sosai ta shige gaba yana binta har wajen kujerun.
Bayan sun zauna ne ya jata da hirar makaranta sannan
yace
"Allah Sarki,kinga kamar nima banyi karatun nan ba. Gashi
aiki ya gagaremu samu."
Sai lokacin ta dubeshi
"Daman kayi karatu har zuwa jami'a?"
"Nayi Deeya,accounting na karanta."
Cike da mamaki tace
"Lallai,amma ban taba kawowa ba kayi wani nisa a karatu
ba yaya j."
Yayi murmushi
"Inada kwalin degree a ajiye Deeya,matsalar kasarmu ce.
Alokacin dana kammala karatuna naci wuya wajen neman
aiki. Wannan yasa a karshe Abbana yace na dunga binsa
kasuwa. Yanzu gashi har ya bude wasu shagunan,nine
babba ana wannan kasuwar."
"Allah Sarki,ai da kasan ka kara gwada sa'arka tunda kaga
abun dace ne."
Ya daga kafada kadan
"Um,da haka ma. Allah Ya taimakemu dai."
"Amin."
Jafar ya numfasa yana mai rage sautin muryarsa
"Deeya."
Ta amsa tana mai jin dadin muryarsa na zagaye sassan
jikinta
"Na'am."
"Kiyi hakuri da abunda ya faru a farkon lokacin dana gano
kece Hadiyya,raina ne ya baci a lokacin ba wai sonki ne ya
ficemin a raina ba kin gane ko? Ni yanzu a shirye nake da
zarar mun fahimci juna kinmin izni na turo magabatana ayi
zancen aure. Ni Jafar matukar kikaji nayi furucin soyayya
ga mace toh babu yaudara ko karya a ciki. I mean
it,inasonki. Bayan matata,babu wacce na taba so saike.
Ban taba yaudara ba,in fact banma iya yinta ba,so please
don't try it on me ,nasan bazan iya jurewa ba."
Tayi murmushi mai wahalar da Jafar,baisan Ladi tana da
kyau ba saida ya fada tafkin kaunarta.
"Ni kaina ban taba soyayya ba Yaya j,banma iya yaudarar
ba ballantana na gwada a kanka. Abunda ya faru kuma a
baya ni ce mai laifin,ka gafarceni kuskure ne."
Haka sukayita hirarsu kamar kada su rabu.
******
Soyayya mai tsafta ta cigaba da gudana a tsakaninsu.
Shakuwa mai karfi har ya zamana baya iya danne sirrin
dake ranshi duk sa'ilin da sukayi arba. Wani sa'in yakan
bita har makaranta idan ya jita shiru.
A gefe ga Hajiya Siyama kazamatu tana kara
tab'arb'arewa...........
A yanzu Jafar bai fiye takura kansa da damuwar kazantarta
ba. Saidai yaja tsaki ya gyara,wataran kuwa Dauda ke
taimakonsa.
Ana cikin haka har babbar sallah tazo,ya zauna a dakinsa
yayi jugum yana tunani. Fargabarsa bai wuce ya siyo rago
ba ya kawo,amma idan Siyama ta soya ya zamana yak'i
ciyuwa. Can kuma sai dabara ta fado mishi ya zaro
wayarsa ya dannawa Hajja kira. Kara daya biyu ta dauka.
Bayan sallama da gaishe gaishe ne,ya sanar da ita yanason
ta turo masa Bahijja saboda aikin nama tunda yasan masu
taimakawa Hajjah da sallah suna da yawa. Hajjah tace
"Ba nak'i ayi hakan ba,ni abune na kananun magana
banaso. Kayi wa ita Siyamar magana idan ta amince sai a
kawota."
Jafar cike da mamaki yace
"Hajiya,Siyama ce zata k'i zuwan Bahijja kuma?"
Hajjah ta danyi shiru,Jafar baisan cewa Siyama ta jima
rabonta da cikin gidan nan. Kusan sau hudu tana zuwa
gidansu saidai ta bada yaro a kawo mata. Ita kanta batasan
abunda ya jawo wannan chanjin ba.
"Hello Hajjah kina jina?"
"Kaidai kayi yanda na gayamaka."
Daga haka ta kashe wayar,ya tsaya sororo yana bin wayar
da kallo har Siyama ta shigo goye da Faruk dake bacci.
"Kai kuma lafiya kuwa?"
Ya danyi murmushi
"Hum,barni da Hajja mana,wai nace a turo Bahijja ta
taimaka miki da aikace aikacen sallah tace na nemi izninki
shine abun yake bani mamaki. Yaushe kuka fara 'yar haka
da Bahijjar taki?"
"Kada ki kuskura ki kara barin yar iskar nan ta kara zuwar
maki gida. Wani munafuncin ne nasu na daban."
Hudubar da hajiyar ta taba yi mata kenan,nan da nan ta
daure fuska
"Menene kuma na neman iznina? Kawai dai Hajja batason
turomin ita ne,nikam barshi ma mantawa nayi ban
fadamaka ba Hajiya zata aikomin mutum biyu zasu
taimakamin. Ba saita zo ba."
Jafar ya mike tsaye,yana zargin wannan chanji na Siyama
domin a kwanakin nan rashin kunyarta kara yawaita yakeyi.
Baice komai ba har ta fice daga dakin. Ya girgiza kanshi ya
mike da niyyar ficewa kasuwa don daman ya kammala
shirinsa tsaf.
******
*****26
Tun ana gobe sallah,hadiyya suka tafi hutun zuwa kasuwa.
Abun yazo mata da dadi saboda anyi musu hutu.
Kwatsam da yamma suna zaune ita da Mama suna lissafin
kayan cefane sukaji sallamar Basma. Wani ihun murna
Hadiyya ta saki ta rukunkumeta suna dariyar farin cikin
ganin juna.
Mama sai murmushi takeyi,ita kanta taji dadin ganin Basma
domin tunda ta tafi Zaria, makaranta bata kara zuwa garin
ba sai yanzu.
Basma ta saki Hadiyya tayi wajen mama,itama rungumeta
tayi tana mai gaisheta. Mama ta rike hannunta tana
murmushi mai bayyana hakora
"Yan makaranta,saukar yaushe?"
Basma tana dariya tace
"Dazu dazun nan na iso Mama. Mun sameku lafiya? Ya
shirye shiryen sallah?"
"Lafiya kalau mungode Allah. Sallah kam,gatanan ta iskomu
sai fatan Allah Yasa muyita lafiya."
Basma tana murmushi ta amsa da amin. Hadiyya ta dubeta
"Taso muje."
Mama ta dakatar da ita ta hanyar harara
"Ni zan fita cefanen? Rike kudin kuje "
Suna dariya suka fice daga gidan bayan Hadiyya ta zura
hijabinta a jiki.
A hanya hira kamar suyi me? Hadiyya ta labarta mata
yanda take soyewa da Jafar a yanzun,Basma dadi ya rufeta
"Kinga amfanin addu'a Hadiyya. Ga wanda zai gane,ya saki
komai ya kama addu a don takobin mumini ce. Nima
gashinan da karfin addua mahaifin Bash ya sauko amince
da batun aurena dashi. Allah dai Yayi mana jagora."
Hadiyya ta amsa da amin. Sukayita hira har suka isa inda
zasuje.
*****
Bayan Sallah da Kwanaki......
Sallamar Shukra da Fatima ta maido da hankalin Siyama
daga kallon da takeyi. Ihu ta saki ta rukunkumesu cikin jin
dadin ganinsu. Fatima ta tureta saboda nauyin cikin dake
jikinta
"Ke taimaka ki matsa so kikeyi nayi haihuwar da ban shirya
ba?"
Siyama ta harareta
"Yo idan kin haihu a gidana ai daidai kenan,ko kin mance
rabonki da gidana tun bikina?"
Suka zauna Fatima tana yamutsa fuska yayin da take
karewa falon kallo
"Siyama fruits kikasha amma baki gyara falon ba?"
Shukra taja tsaki
"Kedai wallahi dama Nazifa aka sanya maki. Haba,ko yaya
kikaga datti sai kinyi magana? Siyama bani ruwa idan da
abinci ki hado don ko abincin rana banci ba wannan matar
ta azazzaleni da waya."
(Shukra da Fatima aminan juna ne kuma kawaye ga
Siyama. Tare sukayi karatun firamare zuwa sakandire sun
shaku da juna sosai duk da dai akwai bambancin
halayya,Fatima duk ta fisu hakuri da sanin ya kamata)
Siyama tace
"Shareta aminiyata,ai Fatima sai a hankali. Wannan da kece
uwata bansan ya zanyi ba. Kina fama da jikinki amma baki
bar neman rigima ba."
"Atoh dai."
Fatima dai baki ta tab'e
"Ai daman halinku daya baku da bambanci,sai ku koyi
hankali yanzu tunda sai an soma tara zuri'a."
Shukra tayi dariya,Siyama dake kicin tana tayata.
"Toh ai tunda muna kyautatawa a shimfida ai inajin magana
ta kare ko?"
"Bata kare ba,tsafta da kwalliya da girki suma wani abu ne.
Uwa uba ladabi da biyayya."
Siyama wacce ta ajiye faranti cike da nama dayan kuma
lemo ne da ruwa tace
"Toh wannan ai mai sauki ne tunda ana kokartawa ko ya
kikace aminiyata? "
Shukra wacce ta bararraje akan kafet ta gama kwankwadar
ruwa tana shirin sanya nama a bakinta ta gyada kai
"Wallahi fa. Bar wannan Nazifar,ita na lura batasan wahalar
dake cikin aikace aikace ba tunda su biyu ne wajen mijinta."
Daga haka ta jefa nama a bakinta tana tauna, Fatima tana
kokarin shan ruwa,Shukra ta dakatar da ita sakamakon
naman data furzo waje .
"Lafiyarki kuwa?"
Shukra tayi saurin bude lemo tasha,sannan ta dubi Siyama
"Allah Ya isa amma,kin kasheni da raina. Wannan wane irin
nama ne mai wari haka? Dame kikayi suyarshi? Mts,wallahi
Malama yunwa nakeji nikam idan da biredi bani na afa ko
zan samu naji daidai."
Siyama ta harareta
"Yau kuma salon wulakancin naki kenan? Wane irin wari a
abunda aka soyashi kwanan nan?"
Shukra ta turawa Fatima farantin
"Don Allah ci kiji saiki tabbatar ko sharri nayi gareta. Kema
ki dauki kici."
Fatima tunda ta doshi bakinta dashi batayi marmarin kaiwa
bakinta ba ta maidashi. Siyama ta tauna ta hau yamutsa
fuska
"Oh ni Siyama,a wane roba aka sanyamin naman nan? Ni
kaina sai yanzu naji warin. Kodai shiyasa Jafar bayaci?"
Cike da mamaki suka dubeta,Fatima tace
"Amma kin bani kunya,yau kuma mijin naki ne kike kira
haka? Ina laifin kiransa da baban faruk? Ta yaya naman
nan ma zai ciyu Siyama? Gaskiya baban faruk yana fama."
Haka sukayi mata ca,duk rabin fadan Fatima ke yi,Shukra
kuwa biredi da lemo take dank'ara abinta. Idan Fatima ta
hado da nata kalar kazantar sai ta hayayyaji tace batasan
da wannan ba.
Haka dai a karshe sukayi sallama suka tafi,Siyama bakin
cikin lalacewar naman yafi komai nukurkusarta. Ta ja tsaki
yafi sau nawa hakanan ta tattara ta ajiye.
******
Watanni biyu da kulluwar soyayyar Jafar da Hadiyya,ya
shirya sanarwa iyayensa batun aurensu...........
Baiji wata fargaba ba kasancewar yasan iyayensa suna da
saukin fahimta ko kadan basu da daukar zafi musamman
kan abunda yake halal.
Daren litinin ya shiga gidan. Yaci sa'ar samun iyayen nasa
zaune a falon Abbansa.
Ya karasa cikin ladabi ya russuna ya gaidasu. Cikin sakin
fuska suka amsa mishi da tambayar iyalinsa.
"Duk suna lafiya."
Ya danyi shiru bayan ya gyara zama ya zauna, Mahaifinsa
ya dubeshi yana nazari
"Ya dai malam,akwai magana ne?"
Ya shafi sumarsa yana murmushi
"Daman zuwa nayi na sanar maku inason k'ara aure."
Cike da mamaki Alhaji ya dubi Hajja wacce tayi shiru batace
uffan ba. Ya maido dubansa ga Jafar
"Aure fa kace malam? Yanzu kai zaka iya rike mata biyu?"
Jafar har lokacin bai dago kanshi ba yana mai jin nauyi bai
iya amsa mishi ba. Can kuma Alhaji ya numfasa
"Toh! A ina ita kuma yarinyar take?"
Ya numfasa cikin jin dadi
"Anan Kano take unguwar yakasai."
Alhaji ya jinjina kanshi
"Shikenan,zanyi tunani sannan ina mai shawartarka ka
dage da adduar neman zab'in Allah,idan lamarin mai
tabbatuwa ne mai alheri ne,Allah Ya tabbatar. Komai na
lamuran duniya yana bukatar a nemi zabin Ubangiji,mutum
zaifi ganin daidai cikinsa. Allah Yayi jagora,kaje zamu ga
abunda hali yayi."
Daga haka sukayi sallama,Jafar ya tafi cike da kwarin
gwuiwar samun muradin zuciyarsa.
*****
Sati daya da yin hakan,Alhaji tuni sun gama amincewa da
dan uwansa (mahaifin siyama) akan batun auren Jafar. A
cewarsa ai k'ara raya sunnar ma'aiki ne babu wani laifi."
Da wannan suka kirayi Jafar sukayi mishi nasiha mai ratsa
zuciya akan ya kwatanta adalci,sannan ya sanar da
matarsa. Abba kuwa yace babu dalilin da saita amince zaiyi
aure,jafar ya nemi izni wajen yarinya aje ayi maganar aure
kawai amma koda Siyama bata kwantar da hankalinta ba
babu abunda za'a fasa!
****27
Haris ya zubawa Jafar ido jin wani zance kamar a
mafarki.......
Jafar murmushi kawai yakeyi yana shafar sumarsa. Haris
ya girgiza kansa
"A baya idan naji kana batun k'ara aure,ban taba kawowa
dagaske bane. Koda na kawo da gaske kakeyi zakayi aure
ban zaceshi anan kurkusa ba."
Jafar ya daga kafada kadan
"Kasan lamarin Ubangiji,ni kaina banma yi zaton zan kara
son wata diya mace ba bayan Siyama,sai gashinan Allah
Yayi."
Haris ya jinjina kansa yana mai gyara zamansa a kujerar da
yake zaune akai cikin shagonsu Jafar.
"Haka yake,Hadiyyar ce dai?"
Jafar ya lumshe ido kadan yana murmushin jin dadin an
kirayi sunan masoyiyarsa
"Itace, nayi maganar turo magabatana gareta,tace na jira
mahaifiyarta zata sanarwa yayyun mahaifin nata
kasancewar mahaifinta ita ya rasu. Duk lokacin da suka
yanke sai aje."
Haris yana dariya,suka tafa
"Dakyau mutumin,kace babu kama hannun yaro. Toh
yaushe za'a kaini na ganta?"
Jafar ya harareshi
"Waikai akanme ja matsu daka ganemin matata ne?
Wataran ai za'a hadu ko?"
Haris ya juya ga ibrahim
"Jimin wannan zancen ibro,yanzu ni haka nayi mishi? Inace
saida na nuna maku hoton Rahma?"
Ibrahim yayi dariya
"Gaskiyane,kuma muka yaba."
Jafar ya tabe baki
"Malam ni ba haka tsarina yake ba kaji ko? Bana son nuna
iyalina kafin na auresu."
Haris yana dubansa cike da zargi
"Eh amma duk da haka kasha kaini wajen Siyama kafin
aurenku.."
"To naji,akan wannan dai ra'ayina ya chanja. An daina
wannan yayin."
Sukayi dariya,Haris ya amsa da
"Toh,idan dai lokaci yazo zamu ji mu gani."
Haka sukayita hira abinsu.
*****
Mama ta samu yayan mahaifin Ladi,Mamman tayi mishi
maganar zuwan magabatan Ladi. Yayi farin cikin jin
haka,babu bata lokaci yace zai sanarwa sauran yan uwan
maza koda a gobe ne sai suzo.
Bayan Ladi ta gama sauraron bayanin Mama,ta sauke
ajiyar zuciya tana mai jin wani sanyin dadi yana ratsa
zuciyarta. Mama ta kara da cewa
"Saiki buga ki sanar mishi ko?"
Murmushi tayi ta amsa da toh.
Ta sanarwa Jafar shima cikin zumudi yaje ya samu
mahaifin Siyama,kasancewar komai na ragamar auren ya
koma hannunsa. Ya sameshi a falonsa yayi mishi batun sun
amince a turo gobe. Abba yana murmushi yace
"Kai madallah,shikenan Allah Ya kaimu goben sai muje."
Jafar ya amsa,sannan ya mike ya fita.
Hajiya dake daki ta fito ta zauna gefen Abba tana kallonshi
"Abban Siyama,maganar me naji kuna yi kaida Jafar?"
Ya daure fuska tamau
"Banason ana shigarmin maganar da babu ruwan mutum
ciki."
Ta tabe baki
"Yo,laifine don na tambaya?"
Bai kara cewa komai ba,bayason tasan zancen yanzu sanin
rashin hankalinta yanzun nan saita yiwa Siyama hudubar
shaidan a tadawa Jafar hankali.
Ita kuwa Hajiya wacce taji Abba yana batun zasuje
gobe,tunanin inda za'aje takeyi,karshe dai ta watsar da
zancen.
*****
Nan ma Jafar ya sanarwa Hajja,tayi shiru kafin tace
"Ka sanarwa Siyama?"
Ya girgiza kai
"Ba yanzu ba hajjah."
"A'a,lallai ka sanar mata banaso ta tsinci maganar a waje
abun ya zamto rigima. Ka samu ka sanar mata ta hanyar
data dace."
"Toh Hajjah."
*******
"Alhamdulillah,kai naji dadin wannan zancen Kakana. Na
manta rabon dana tsinci kaina cikin tsabar farin ciki irin
wannan. A ina yarinyar take?"
Anti habiba ke tambayar cikin tsabagen farin ciki
"Anan garin take, Yakasai."
Anti habiba baki yaki rufuwa
"Ai gwara ka k'ara auren nan kakana kaima hankalinka ya
kwanta. Ko babu komai za ayi maganin wadannan marasa
tsoron Allahn. Yanzu dai kenan muna gama hidimar bikin
Bahijja sai naka? Gida daya zaka hadasu?"
Jafar cikin damuwa yace
"Toh,ganinan dai. Inason hadasu amma ina tsoron kada
Hadiyya tak'i don yarinya ce gwanar tsafta,bazata so
kazanta ba."
"Ka hadasu kakana,zaifi. Kada ka damu,babu abunda zai
faru. Yanzu ka sanarwa ita Siyamar?"
"A'a tukunna,nafiso sai an sanya ranar."
Ta jinjina kanta tana murmushi
"Tabbas gwara hakan,Allah Yasa ayi muna raye."
"Amin anti."
******
Wata biyu aka sanya bikin Hadiyya da Jafar.......
****28
Har lokacin Jafar ya kasa sanarwa Siyama batun aurensa.
Haka kawai yaji yana tsoron bacin ranta. Acikin sati uku ya
kammala had'a lefensa tsaf da taimakon kudaden daya
samu wajen Abban Siyama da Alhajinsa. Komai ya
kammala don Anti Habiba ya damkawa,duk da alokacin
bata zama saboda shirye shiryen da suke na auren Bahijja
wanda alokacin sauran kwana biyu kacal. Sun tsara ana
kammala hidimar bikin Bahijja za a mika lefan Hadiyya.
Suna zaune a falon anti habiba bayan ya kammala ganin
lefen yana murmushin jin dadi ya dubeta
"Masha Allah,komai yayi kyau antina."
Tayi dariya
"Ai kam,kaya sunyi kyau. Saidai har yau ka gaza kawomin
kanwartawa na gani ko?"
Yana murmushi ya shafi sumar kansa
"Kiyi hakuri antina,zan kawo maki ita kafin ku soma bikin
Bahijja."
Ta jinjina kanta
"Ai shikenan toh,Allah Yasa."
"Amin."
****
Hakan kuwa akayi,takanas Jafar ya hayo d'an adaidaita
sahu suka dauki Basma da Hadiyya zuwa gidan Anti
Habiba. Dayake mai adaidaitan d'an gida ne,har kofar gidan
anti habiba ya kaisu. Anan suna iske Jafar zaune yana hira
da wani kanin mijin anti habiba,Suleiman. Ganinsu yasa
suka mike,Jafar yana kashe Hadiyya da wani irin kallo da
su kadai sukasan ma anarsa. Ta dan lumshe masa ido tana
murmushi,ai sai ta rud'ashi. Ji yayi kamar ya sumbaci
idanuwanta da suka sha ado da eyeshadow tayi fes da ita.
"Sannunku da zuwa."
Maganar Suleiman ce ta katse mishi tunani,ya bar kallon
Hadiyya,ya maida dubansa ga Basma yana amsa
gaisuwarta. Hadiyya ma ta gaishesu. Suleiman yana
dariyar zolaya ya dubi Hadiyya
"Ko ba'a fadamin ba nasan kece amaryarmu don na lura da
kallon da ogan ke jifanki dashi."
Jafar da Basma sukayi dariya,shima yana tayasu. Hadiyya
murmushi kawai tayi tana mai satar kallon Jafar. Ya daga
mata gira
"Ashe zaka iya ganeta. Ku shigo ciki."
Jafar yayi gaba,suna biye dashi. Anti tana zaune bayan ta
kammala yiwa amarya bahijja gyaran jiki taji sallamarsu.
Cikin fara a ta amsa,
"Maraba lale da amaryarmu. Bismillah ga wuri ku zauna."
A kunyace suka soma kokarin zama a k'asa,anti tayi saurin
dakatar dasu
"Kai haba dai a kasa? Maza ku hau saman kujera."
Dakyar suka zauna,Hadiyyah ji takeyi kamar kasa ta tsage
ta shiga.
Anti tana murmushi ta amsa gaisuwar da sukeyi gareta
kafin ta hau duban fuskokinsu. Hadiyya dake faman
sussune kanta ta zurawa ido
"Na gano amaryar tamu,d'agomin fuskarki na ganki sosai
mana."
Jin haka yasa Hadiyya kara jan gyalenta,Jafar ya karasa ya
soma kokarin janye mayafin
"Bari ki ganta sosai antina."
Suleiman na dariya yace
"Kaidai baka da kunya wallahi."
Hadiyya ta hau dariya ciki ciki,anti ta maka mishi filon
kujera
"Ina fa yaga ta kunya? Ku tashi ku fita ku barni da
kanwata."
Jafar yana dariya suka fice da suleiman. Daidai nan Bahijja
ta fito daga daki,tayi wanka saboda kurkum da tayi,duk
saita chanja ta kara haske da kyau. Ganin wadanda ke
zaune ta fadada fara'arta
"Ashe yayar tawa ta iso. Bari a kawo maku ruwa."
Tayi kicin da sauri,anti ta dubi basma tana murmushi
"Menene sunanki ke?"
"Basma."
Ta gyada kanta ta maida dubanta ga Hadiyya
"Kinga Hadiyya ki saki jikinki,ki daukeni tamkar yayarki.
Menene na wannan noke noken iye? Don Allah ki saki jikinki
damu muna kaunarki."
Hadiyya ta gyada kanta,har Bahijja ta dawo dauke da ruwa
da lemo sai cin cin da meatpie. Ta ajiye musu
"Toh amaryar yayana,bismillah."
Ta soma zuba lemun ta mika mata,anti habiba ta mike jin
tsayuwar mota
"Inajin yaran nan ne suka dawo daga makaranta bari na
gani."
Ta fita,Bahijjah data mikawa Basma ta dubi Hadiyya
"Saiki bude fuskar don Allah kinga dai ni kanwarki ce babu
kunya tsakaninmu ko ya kikace Basma?"
Basma ta gyada kanta tana dariya
"Hakane yar uwa,mene sunanki?"
Bahijja tayi murmushi
"Bahijja,aurena jibin nan za'a soma."
Sai lokacin Hadiyya ta bude fuskarta ta dubi Bahijja tana
murmushi a kunyace
"Allah Sarki,ashe kece Bahijja?"
Bahijja take karewa fuskar hadiyya kallo tana mai yaba
kyawunta mai sanyi ta fadada fara'arta
"Nice anti deeya. Masha Allah,ashe don kinsan kina da kyau
shiyasa kika k'i nuna mana fuskar taki ko?"
Sukayi dariya,
"Ba haka bane nauyin anti nakeji wallahi."
"Toh karki damu,indai anti ce wallahi babu ruwanta. Sau da
yawa itace abokiyar shawarata ma."
Haka Hadiyya suka sake sunata hira da Bahijja kamar sun
san juna. Dawowar anti ya sanyasu Hadiyya yin shiru.
Ta dubi fuskar Hadiyya dake a bude
"Inye,ashe haka amaryar tamu take da kyau. Lallai dole ki
dunga boye fuskarki."
Murmushi kawai Hadiyya tayi.
Sun jima wajen anti sannan suka fito bayan anti ta cikasu
da kyautuka.
A zauren gidan jafar ya tsare Hadiyya da hira. Kamar kada
su rabu yakeji dakyar ta lallabashi sukayi sallama,wanda ya
kawosu ne ya maidasu. Nan ma kafin a ja adaidaitan ya
jima tsaye,karshe ma yace mata zai shigo anjima.
******
Duk wannan budurin da akeyi,Hajiya Siyama bata da
labarinsa har sai ranar yinin Bahijja........
***29
Yanda akayi ta samu labarin shine..
Suna zaune a falon Hajiya tare da yayyenta. Rumaisa,Amat
mai biwa Rumaisa sai Aisha sannan Anti amina matar Yaya
hanif sai Siyama da Fatima kawar siyama. Daga gidan bikin
Bahijja suke,sun dawo gidan domin sallah. Sun idar sai
kuma hira ta b'arke ana yi ana tuntsira dariya. Akwai
sauran jama'a a falon kowannensu sha'anin gabansa
yakeyi. Sid'if sid'if Shukra ta shigo kamar wacce kwai ya
fashewa a ciki.
Ta nemi kusa da Fatima ta zauna,gumi yana wanke
fuskarta. Fatima ta ankara da hakan,wannan yasa ta jefo
mata tambaya
"Wai lafiyarki kuwa?"
Tambayar ta janyo hankalin Siyama da yayyunta
kasancewar da d'an karfi Fatima ta tambaya. Shukra ta
muskuta ta dubi Siyama
"Uhum,wai daman Jafar aure zaiyi shine baki ko sanar
damu ba?"
A razane duk suka fiddo idanu ,Siyama ta rike kirjinta
dake bubbugawa
"Me kike fad'i haka? Banason zolaya Shukra,musamman
ma akan kishiya. Please stop it."
Shukra a sanyaye tace
"Haba Siyama,na taba yi maki wasa irin wannan? Abunda
na jiyo ne na fadamaki."
Rumaisa a hanzarce tace
"Yi mana bayani yanda zamu gane Shukra."
Shukra ta hadiyi miyau kamar wata marar gaskiya tace
"Ina cikin bandakin Bahijja ina alwala sai na jiyo anti habiba
tana hira da wannan kawartata mai yawan sanya medical
glass,maganar bikin Jafar. Take cewa ai bayan bikin nan za
a kai lefe,bikin sauran wata daya da satittika."
Wani irin ashar Siyama tayi,ai saita dora hannu a kai ta
rushe da kuka. Fatima ta harari Shukra
"Kinga abunda zaki janyo mana ko?"
Shukra kafin tace wani abu,sukaji Anti rumaisa da amat sun
soma zage zage. Siyama kuwa ihun kuka takeyi. Wannan ya
janyo hankalin mutan gidan har Hajiya. Suka shigo suna
tambayar ko lafiya? Nan anti amina tayi karfin halin sanar
musu abunda ke faruwa. Ai sai Hajiya ta fisu shiga bacin
rai.
"Amma wannan abune da bazata sab'u ba,bazan yarda ba
wannan cin fuska ne!! Kema yar banzar yarinya da kikace
sai shi yau ga abunda ya sakamaki dashi!!"
Rumaisa ta figi hannun Siyama basu dire ko'ina ba sai
gidan Hajja! Cike da bala'i ta shiga kwalawa habiba kira
kasancewar kusan sa'anni ne. Wannan ya janyo hankalin
jama'ar gidan suka fito. Anti Habiba dake d'aki ta fito tana
gyara zaman daurin dankwalinta zuwa gaban goshi sanin
kanun zancen kasancewar tana sane tayi batun a kunnen
Shukra. Tasan yarinya ce da bazata iya rufe maganar ba
saita fesawa aminiyarta.
*************
"Menene kike daga murya wajen kirana Rumaisa?"
Rumaisa tana huci idonta ya rufe don bala'i ta nuna anti da
yatsa
"Kedai wallahi anyi girman banza! Ace harda hadin bakinki
wajen yiwa Siyama wannan cin fuskar! Ko kunyar yanda
Siyama ta bijirewa Hajiyarta bakuji ba kuke shirin kullawa
Jafar wani auren? Eh lallai wannan munafuncin yakai inda
yakai! Toh ina mai tabbatar maki in har muna raye Jafar
bazaiyi wannan auren ba. Sai kunsan mu zuri'armu
bamusan kishiya ba ballantana musan da zamanta a doron
kasa! Can dai gasu gada!"
Hajjah ta taho da sauri
"Haba Rumaisa,da girmanki da komai kike magana kamar
yarinyar goye? Don Allah kiyi hakuri...."
"Domin girman Allah Hajja ki rufe bakinki! Ai ni walki ce,
daidai nake da kug'un kowa!"
Ta juya a fusace ga rumaisa
"Da kike ikrarin ku zuri arku ba'ayi maku kishiya,toh ki zuba
ido yau za'a fara akan autarku! Da ranki da lafiyarki babu
abunda za'a fasa rumaisa! Auren Jafar da Hadiyya kamar
anyi an gama ne! Ke baku isa ku hana ba. Har kin fini sanin
bakwason auren Jafar da siyama? Saidai ni na fadamaki
wannan saboda nice nan Siyama ke takowa ta kawomin
kokenta alokacin da ake fitinar auren! Babu wani babi na
alkur ani ko hadith da yake nuni da cewa kishin mace yana
haramtawa namiji karin wani auren wanda yake na sunnah.
Takaicina daya da kakana bai sanar da matarsa zai kara
aure ba,na baki hakuri anan Siyama. Wannan auren baya
nufin wulakantaki.....!"
"Ke dallah can tsohuwar munafukar banza ki rufe mana
baki. Habiba baki taba kaunar jinina ba! Nasan hudubar
uwarku ce! Dake aka shirya wannan makircin,wallahi kunji
kunya! Dole Jafar ya bani takardar Siyama domin bazan
amince da wannan tozarcin ba.!
Hajiya data shigo take wannan kwakwazon. Nan fa gida ya
rincabe,Amarya Bahijja kukan bakin ciki takeyi kawai,a
gaban kawayenta wannan abu ke faruwa,ranar bikinta. Tuni
aka sanya mai daukar video ta tsaya cak. Fada har da 'yar
doke doke tsakanin rumaisa da anti habiba. Nan anti habiba
tayi mata lilis dakyar aka finciketa. Hajjah ta wanke
fuskarta da mari,babu tsoron Allah Hajiya ta mari Hajjah
cikin zafin rai. Anti Habiba batayi wata wata ba ta rama
marin a fuskar Hajiya. Nan fa Anti Amat ta tunzura ta kai
hannu ta mari anti habiba.
"Ai uwa batafi uwa ba.!!"
Manya da yara kuka sukeyi na bakin ciki,da gudu Bahijja ta
fito kofar gida,yayi daidai da tsayuwar motar Abban
Siyama. Ai kawai saita nufi wajenshi...
Ya fito daga motar,ganin Bahijja a guje ne ya sanyashi yin
turus. Cike da mamaki ya rike hannunta
"Ke Bahijja meke faruwa ne?"
Bahijja ta nuna mishi kofar gidansu,murya na rawa tace
"Abba fada sukeyi,su anti habiba da Hajiya."
"Innalillahi...! Rilwanun baya ciki?"
"Ya fita tun safe."
Da sauri sauri Abba ya nufi gidan,lokacin Jafar da Haris
suka iso a motar Haris din. Cikin mamaki da rikitarwa suke
duban abunda idonsu take hange. Amarya bahijja na kuka
wiwi,ga Abba cikin rashin hayyaci ya shige gidansu gadan
gadan. Suka dubi juna,da sauri suka fito daga motar bayan
Haris ya faka suma suka mara musu baya.
Tsananin tashin hankalin da Abba ya riska ne ya sanyashi
doka salati. Wannan ya janyo hankalin mutanen
wajen,Hajja tuni daman ta shige daki tana hawayen bakin
cikin wannan tozarci da Hajiya Maimuna tayi mata gaban
surukanta da yaranta harma da kawayenta. Hajiya
ummusalmah babbar aminiyarta tana gefenta zaune tana
bata hakuri. Acan tsakar gidan kuwa Amat da Habiba ne ke
cacar baki har da doke doke, Aisha tana tayata. Tsawar da
Abba ya daka musu ne ya sanyasu nutsuwa. Rumaisa na
gefe jini sai zuba yake daga bakinta da Anti habiba ta yiwa
lahani. Kowannensu numfarfashi yakeyi,sai kokarin daura
dankwali. Haris da Jafar hankalinsu ya tashi,gashi babu
wanda yasan dalilin wannan fadan. Kafin Jafar ya
ankara,yaji an cakumi wuyar rigarsa. Da sauri yakai duba
gareta,Siyama ce take dubansa cike da bala'i a kwayar
idanunta,hawaye da majina shab'e shab'e
"Wallahi saika sakeni jafar! Bazan iya cigaba da zama dakai
ba tunda ka nunamin halin munafuncin maza toh nikam....."
Ba zato taji an fincikota an kwasheta da mari,Abba ne a
zuciye ya aikata hakan yana hucin bakin ciki. Sai lokacin ya
fahimci silar fad'an.
"Ashe baki da hankali?! Har na hana yayyenki Su hanu ke ki
nunamin ban isa dake ba?!! Toh wallahi zan sab'a maku
gaba d'aya! Duk ku ficemin daga nan,sannan na kara jin an
kara tashin zance saikun raina kanku."
Abba ya juya zai fita,sai ga Alhaji ya dawo. Cike da mamaki
bayan Abba ya karaso wajenshi yake tambayarsa abunda
ke faruwa. Abba ya girgiza kansa
"Menene banda jahilcin mata? Kai jafaru bud'e sitroom din
nan."
Jafar a sanyaye ya bud'e,yasan akan auren da zaiyi ne ake
wannan bala'in a gidan nan. Haris zai fita, Abba ya dakatar
dashi
"Haba Haris kamar wani bare? Zauna mana."
Abba ya tarasu duka har da Hajja. Alhaji dai mamaki ne ya
cikashi saboda har lokacin baisan da faruwar komai ba sai
binsu da kallo yakeyi. Bahijja har lokacin kuka takeyi,itama
Siyama ba'a barta a baya ba. Kuka takeyi harda
sheshsheka a ganinta ita yafi dacewa tayi kuka ba kowa ba.
Wannan masifar duk ita za'a bari ta kwana a ciki. Jafar da
auren wata?
Abba yayi gyaran murya ya soma da duban Bahijja.....
***30
Abba ya dubi Bahijja dake rusar kuka
"Ke Bahijja,bar kukan nan ki sanar dani abunda ke faruwa."
Bahijja ta tsahirta kukanta 😭sai sheshsheka da
takeyi. Cikin rawar murya tayi musu bayanin komai,tana
zuwa inda aka mari mahaifiyarta sai sautin kukanta ya
k'aru sosai. Ran iyayen idan yakai dubu toh ya b'aci. Jafar
hankalinsa ya tashi jin cewa an mari mahaifiyarshi,yaji ya
k'ara tsanar mahaifiyar Siyama ba kad'an ba. Hajjah dake
hawayen bakin ciki ta sunkuyar da kanta k'asa. Nan Alhaji
ya mike ya isa ga anti habiba ya kai mata hauri a kug'u
"Kajimin yar iskar yarinya! Hajiya maimuna sa'arki ce da
zaki d'aga hannu ki mara?!!"
Abba ya dakatar dashi
"Kaga zauna Rilwanu,banga laifin Habiba ba,ai d'an
mutunci bazaiga an d'aga hannu an mari uwarsa ba ya iya
kauda kansa ba. Laifin duk ba nata bane,wadannan
fitsararrun sune masu laifi. Ke kuma..(ya juya ga Hajiya
maimuna) kin nunamin har yanzu da sauranki a ilimin
addini maimuna! Da girmanki da hankalinki! Keda zaki
tsawatar musu idan sunyi wannan aika aikar ace kece mai
biye musu? Toh bari kiji na fadamaki! Aurena na Jafar,babu
mai hanashi a cikinku! Aure ne koda jahilin kishin diyarki zai
kasheta toh babu abunda za'a fasa! Idan kuma kin musa sai
mu gani!!"
Hajiya Maimuna ta hayayyako
"Naji ban hana jafar aure ba! Amma kuna sane da cewar
tun a farko ba kaunar auren nan nake ba ko? Toh ya zama
dole idan har bazai fasa kara aure ba lallai ya saki Siyama
na aura mata wanda... "
"Hajiya Maimuna!!!"
Tsawar Abba ya firgitasu duka har ita kanta Hajiyar.
Ya nunata da yatsa zuciyarsa na rawa saboda tsabar bacin
rai,da kakkausar murya yake magana
"Wallahi wallahi kinji rantsuwar d'an musulmi,muddin kika
sa Jafar ya rabu da Siyama toh zamana dake yazo karshe!!
Sannan don uwar siyamar kada tayi hakuri ta zauna gidan
mijinta,koda wasa ta tayar maka da hankali a gidanka ka
sanarmin sai ta raina kanta!"
Ya karashe da maida zancen kan Jafar. Sannan ya koma
kan su Rumaisa
"Ku kuma manyan banza da wofi kun baro gidajen
mazajenku kunzo ku tayar mana da hankali. Gaba dayanku
wane irin abu ne baku tsinanawa da kuke zaton banda
labari? Toh wallahi idan naji koda wasa kun taka kunje
gidan Jafar da Siyama saina sab'a maku! Shashashan
banza! Ku tashi ku bani wuri!"
Suka mike gaba daya banda su Hajiya da Hajjah,nan ma
Abba ya maida Jafar yace su zauna. Bayan fitarsu anti
habiba ya dubi Hajjah
"Hajiya ina mai baki hakuri akan wannan abu daya faru,kiyi
hakuri komai ya wuce don Allah."
Hajja ta jinjina kanta tana murmushin karfin hali
"Bakomai Alhaji,ya wuce. Saidai da ace da hali Jafar yabar
batun aurensa ko don a zauna lafi..."
"Haba Hajiya,keda kanki kike fadin haka? Toh ai idan hakan
ta faru wadannan sakararrun sun ci galaba kenan,auren
nan baza'a fasashi ba saidai idan Allah ne baiyiba. Kibar
wannan zancen ma kwata kwata don Allah."
"Shikenan Allah Ya sanya alheri."
Jafar wanda ya rasa meke mishi dadi,idanuwansa sun ciko
da kwallah na bakin cikin marin da aka yiwa mahaifiyarsa a
bainar jama'a hannunsa dafe da kansa ya kasa cewa
uffan,Hajiya ta gama kaiwa bango. Ji takeyi kamar ta
shak'o mijinta tsabar bakin cikin abunda yayi gareta na cin
fuska. Hawayen bakin ciki kawai takeyi,bata taba ganin
wanda bai shayin gasawa matarsa magana ba duk da
cewar tana da tarin arziki ba sai shi.
"Jafar kaima kada ka fasa shirye shiryen aurenka! Kuma
ban yarda daka raba musu gida ba! Ka hadasu guri guda
idana mutuwa zatayi don bakin ciki tayi! Kaidai kaji tsoron
Allah wajen kula da hakkin kowannensu! Tashi kuje,Allah
Yayi maku albarka."
Jafar da Haris suka fice, nan aka bar iyayen. Ta inda Abba
ya shiga batanan yake fita ba,saida yayiwa Hajiya tas
sannan ya k'are da nasihu. A karshe suma suka sallamesu.
Cikin sanyin jiki Alhaji ya dubi Abba
"Kaji wannan kaddara,daga maganar auren Malam komai
na gida yana neman lalacewa. Abunda na hanga kenan
shiyasa nace ya nemi amincewar ita Siyamar...!"
Abba ya dakatar dashi
"Kaga Rilwanu,mun wuce wannan bangaren. Babu abunda
zai hana wannan auren idan har ina raye,kai wallahi koda
bana raye ban amince a fasa wannan auren ba.."
"Alhalin ma in sha Allah kana raye yayana. Idan bakanan ya
zan iya da wannan rigimar?"
Sukayi dariya,kafin su shiga hirarsu ta yan uwa.
******
Jafar cike da damuwa ya dubi Haris
"Gaba daya kaina ya dauki chaji Haris,ji nakeyi kamar na
saki Siya..."
"Kul! Kada ka kara ambaton hakan. Komai fa yayi zafi
maganinsa Allah. Duk da wannan rikicin idan Allah Yaso sai
kaga anyi auren kuma an zauna lafiya. Naji dadin hukuncin
da Abba ya yanke,gaba daya bai bi ra'ayin diyarsa ba. Ya
yanke hukunci bada son zuciya ko ganin Siyama diyarsa ce.
Idan kace zaka saketa koda bazai nuna maka a fili ba toh
hakika a ransa bazaiji dadi ba kuma kai dinma baka kyauta
mishi ba. Na tabbata ma Alhaji bazai amince da hakan ba.
Kaidai ka zama jarumin namiji a gidanka,ka tsaya tsayin
daka wajen kwatanta adalci. Allah Ya albarkaci auren
nan,shine kawai addu'ar daya dace muyi."
"Amin amin,wallahi kaina ma har ciwo yakeyi banajin zan
iya komawa kasuwar nan."
Haris cike da tausayi yace
"Ko gida zan maidaka ne?"
"Hakan ma yafimin,zuwa yamma sai na leka kasuwar."
Daga haka suka fada mota suka bar unguwar.
Shukra cikin adaidaita sahu tana faman hada zufa yayinda
Fatima ke zazzaga masifa.
"Gashinan kin janyo tashin hankali a gida, yanzu bansan
halin da ake ciki ba. Irin wannan ba'a fada Shukra,amma
dayake bakinki bai gani yayi shiru gashinan kin janyo tashin
hankali. Na tabbata har gobe Siyama bazata bar kallonki
amatsayin wacce ta kawo mata mummunan labarin auren
Jafar ba."
Shukra ta hadiyi miyau
"Toh ni na dauka ta samu labari ne,kuma meye laifi don na
fada iye?"
Fatima ta ja tsaki tana waige waigen hanya
"Yanzu gashinan kin kusa kashemin aure,inda abun nan
yakai ga kisa kuma muna wajen dole a rankaya damu police
station. Gashi fitowar ma SATAR HANYA ce nayi."
Shukra ta harareta
"Ai,ashe ma gwara ni tunda ni na tambayi zuwa dubo jikin
umma ne. Mtsw,ke gwara ma da muka baro gidan nan
bayan biki sai muje dannar kirji. Gashi kinga leda uku na
taho dashi na kayan rabo,ke kuwa ko d'aya,na baki ne?"
Fatima ta mika hannu ta karba ta sanya a katon jakarta ta
zuge zif. Unguwarsu daya hakanan layinsu daya ne,don
haka waje guda suka sauka ...!
******
Siyama ta dauki gaba mai tsanani da Jafar,tun yana binta
yana bata hakuri gami da lallabata har ya watsar da
lamarinta ya hau gyare gyaren gidansa. Koda ya kawo mata
akwatin kayan fad'ar kishiya ko kallonsu batayi ba,sunfi
kwana uku ajiye a falon karshe da kanshi ya kaisu d'akinta
ya adana. Tuni an kai kayan lefen Hadiyya tun bayan
tarewar Bahijja da sati d'aya. A yanzu kuwa gashi biki
saura satittika.
A can ma yan uwan mahaifin Hadiyya mata,kullum cikin
shiri sukeyi. Mama tabar lekawa shago bisa cewar
Sarah,akan ta zauna taji da hidimar biki har a kammala ita
da babbar 'yarta Maryam zasu kula da shagon. Lokacin
saura sati biyu biki. Hadiyya abun ya hade mata biyu,ga
makaranta ga shirye shiryen biki. Har lokacin Jafar bai
kawo Haris sun gaisa ba saboda yasan ya taba cikawa
Haris baki akan bazai auri mai siyarda abinci ba!
Basma tuni ta koma makaranta,da zummar idan biki ya
kasance cikin weekend toh lallai zata shigo. Kullum cikin
dirke dirken tarkacen mata Hadiyya takeyi,dana wajen
matar yayanta Sunusi d'an yayan mahaifinta,da kuma na
wajen mamanta. Ga gyaran jiki da akeyi mata.
***31
Kwanci tashi babu wuya har aka soma shagalin bikin
Hadiyya da Jafar. Ranar da aka daura aurensu kuwa,murna
da farin ciki wajensu ba'a cewa komai. Har dinnerparty anti
habiba ta shirya wanda zai kasance a washegarin ranar
daurin auren saboda cusawa su Hajiya bakin ciki. Karin
takaicin ma har katin gayyata ta aikamusu. Yaron data aika
kuwa yasha zagi da mari, koda yazo ya sanarmata dariya
kawai tayi ta bashi hakuri gami da tila mishi kud'i wanda
yasa shi sakin ranshi.
Hadiyya ta tsaya sororo kamar wata wawuya tana duban
Jafar ba tare data karbi katunan da yake mik'a mata ba. Ya
shafi gefen fuskarta
"Hey,lafiya dai? Meya faru? Ko bakyason party?"
Ta sauke ajiyar zuciya gami da girgiza kanta tana
murmushin yak'e
"Ba haka bane yaya j,ina mamakine kawai tunda ban taba
jin kacemin akwai dinner party ba."
Yayi dariya yana mai bude tafin hannunta ya sanya katunan
"Sha kuruminki,ni kaina yazomin a ba zato. Antinmu ce ta
had'a mana kinsan tana sonki da yawa har ina mamaki
gami da taya uwargidana kishi."
Hadiyya ta harareshi a wasance
"Toh ai jini ne ya had'u,kullum fa sai mun gaisa da anti ta
waya. Nima wallahi ina kaunarta sosai,ko don bansani ba
don banda wata yar uwa babba ne?"
Yana murmushinnan mai k'ara fisgar zuciyar Hadiyya zuwa
gareshi ya matso sosai gareta cikin rad'a ya soma magana
daidai saitin kunnenta
"Ke dince you are very special Deeya. Babu wanda zai ganki
baiji yana sonki ba shine babban dalilin da yasa nake
tsananin kishinki."
Daga haka ya sumbaci kunnenta,da sauri ta tureshi jikinta
yana b'ari,ajiyar zuciya ta shiga saukewa akai akai,tunda
take babu namijin daya taba kusantarta har haka.
Murmushin love ya hau sakar mata, ta sauke kanta kasa
tana wasa da katunan. Ya riko hannunta,
"Oh deeya,meye na rikicewa har haka? Yaya j ne fa? Your
husband."
Ta soma kiciniyar kwace hannunta kamar zatayi
kuka,idanuwanta sukayi narai narai ta hau girgiza mishi kai
"Domin Allah ka rabu dani yaya j,kada wani yazo wucewa
kaga fa a zaure muke."
Yayi murmushi,ya saki hannunta.
"Shikenan zan kamaki gobe ne. Inace dai gobe zaki tare
daga gidana mu wuce wajen party?"
Ta fiddo ido
"Ai ba'a gama jere ba,gaskiya saidai ji..."
Ya buge bakinta
"Baki isa ba wallahi Deeya,ke zanma sanarwa Anti tun
azahar ya dace a kawomin matata. Kinci sa'a ma da ban
daukeki yanzu ba mun tafi."
Sukayi dariya,haka dai tamkar kada su rabu akarshe sukayi
sallama.
*****
A falo ya iske Siyama kwance tana sharb'ar kukan daya
zamto abin yinta kodayaushe. Tausayinta mai karfi ya
ratsashi,wannan soyayyar nata dake zaune daram a sak'on
zuciyarsa ta motsa gaba daya. Ya isa gareta da niyyar
rarrashi ta zabura taja baya
"Kada ka sake ka tabani Jafar,na tsaneka! Wallahi ina dana
sanin auren..."
Da azama ya rufe mata baki da nashi, saida ya tabbatar ya
kashe mata jiki sannan ya zauna sosai ya sanya kanta a
kirjinsa
"Nayi maki laifi Siyama,saidai kada ki manta aure kaddarar
Allah ne. Wallahi banyi nufin yin wannan auren ba domin na
tozartaki ba. Ina sonki sosai Siyama bazan daina sonki ba.
Kin kasance yar uwata kuma jinina,a kanki na soma sanin
zafi da zak'in soyayya. Ta yaya kike zaton zan gujeki?
Wallahi baki bar raina ba. Don Allah ki kwantar da
hankalinki,kwanakin nan ina cikin matsanancin
kewarki,meyasa akan wata zaki fasa kyautatawa mijinki?
Kinason fushin Allah Ya sauka akanki?"
Ya cigaba da lallabata cike da dabarunsa,ita kanta tayi
kewar mijinta sosai wannan yasa zafin dake zuciyarta ta
ragu inda yayita yi mata alk'awurwura da dama.
******
Washegari tun karfe tara na rana Basma ta iso Kano.
Hadiyya taji dadin ganinta sosai. Basma ta bude baki cikin
mamakin yanda Hadiyya ta chanja,bakin fatar nan nata ya
ragu sosai.
"Aminiya kece kuwa? Kinyi fresh dake."
Hadiyya tayi farr da ido
"Amarya nake fa."
Sukayi dariya,Basma ta dubeta
"To yaya? Akwai dinar?"
"Kwarai,yanzu haka anti zata aikomin kayan daya kamata
na sanya anjima. D'an aiken ma yana hanya."
Basma tace "Ok shikenan,Allah Ya kaimu."
*****
Kyawun da Hadiyya tayi ba'a cewa komai. Wani hadadden
brown lace anti ta aiko mata,gown akayi mata ya zauna cif
a jikinta. Ga head nan darkbrown shima yayi cif a kanta.
Basma ta fente fuskarta da kwalliya saita koma tamkar ma
ba ita ba. Hotuna sunfi kala goma Basma tayi mata,fad'i
takeyi Hadiyya kamar bake ba wallahi. Gyaran jikin nan ya
karb'eki.
Takwas daidai Jafar yayi kiran Basma a waya ya shaida
mata sun iso,lokacin dukka yan matan sunyi gaba sune
karshen fita.
Haris wanda shike tuk'in sai kwalala idanu yake
yanason yaga amaryar. Wacce ya gani yayi matukar bashi
mamaki har don saboda razana baisan lokacin daya saki
salati ba. Jafar yayi saurin rufemishi bakin cikin rad'a yace
"Malam dallah kayimin shiru,kada kace komai tukunna."
Haris ya nutsu yana kallon Jafar ta madubin gilashi,Jafar ya
daure fuska yana share hanci duk kunya ta cikashi. Daidai
nan suka iso,Basma ta bude gidan gaba ya shiga, Hadiyya
ta zauna a baya.
Suka dubi juna,gaba daya saida sukaji wani shock. Ta
sauke ajiyar zuciya ta kauda kanta saboda nauyin kallon da
yake binta dashi.
"Amaryarmu barka da dare. Allah Yasa alheri."
Ya fada yana tuk'i,Hadiyya ta amsa a ciki ciki saboda
kunya. Hannun Jafar taji cikin nata,ta lumshe ido da sauri
tana mai sakin ajiyar zuciya. A tsorace ta soma kiciniyar
kwacewa saidai fa babu dama domin ba rikon wasa yayi
ba,ya kwanto kad'an zuwa saitin fuskarta
"Ki bini a hankali kafin na fasa hakura da tarewarki ayau
Deeya. Kinci sa'ar Anti tace nayi hakuri kya tare a gobe
badan hakan ba da babu wanda zan amince yamin haka."
Tayi kokarin juyowa taga babu dama kasancewar
numfashinsa har akan wuyanta tana jin saukarsa.
"Don Allah ka matsa."
"Yayi murmushi yaja baya gami da saita zamansa ba tare
daya saki hannunta ba."
Suna isa kofar wajen ta soma jin wani mugun faduwar
gaba,har ya kaita ga dafe kirji. Kamar ance ta waiga,sukayi
ido hud'u da fuskar da bazata tab'a manceta ba.
Na shiga uku? Meya kawota nan?!!!!!
***32
Taci uban kwalliya kamar ba ita ba. Saidai ta rame
sosai,amma tsantsar kyawu kam akwai shi. Ta sanya wani
leshi wanda tunda Hadiyya take a rayuwarta bata tab'a
ganin irinsa ba. Maroon lace ne yasha adon kananan
duwatsu,ta tako a hankalo tana nufosu. Ba Hadiyya kad'ai
ba,daidai da Jafar da Haris saida sukayi mamakin ganinta
musamman ma Jafar wanda bashi da labarin zuwanta.
Bata ko dubi Jafar ba ta mik'awa Hadiyya hannu kwayar
idanuwanta fes a cikin na Hadiyya
"Assalamu alaiki."
Hadiyya tana murmushi da baikai zuci ba a tsorace ta amsa
"Wa alaikisallam."
Ta fada tana mai mik'a mata hannu,wani laushine da
hannun Siyama tamkar auduga. Ai duk saita raina
had'uwarta,ta dan russuna ta gaisheta
"Anti barka da dare."
Siyama ta saki hannunta tana murmushin da ya k'ara fiddo
tsantsar kyawunta. Banda kamshi babu abunda ke tashi a
jikinta.
"Uwargida ran gida,shine baki sanar damu zakizo ba
ballantana mu biya mu taho dake?"
Tayi mishi wani irin kallo mai kama da harara,Jafar dai ya
gaza cewa uffan.
"Hum,sai kace marar gata? Nima ina da yan uwan da zasu
kawoni Haris. Na hutashsheku."
Daga haka ta jefi Jafar da wani irin kallo kafin tayi
murmushinta wanda keda tarin ma'anoni
"Ango kasha kamshi."
Yayi murmushin shima,tabbas in har da gaske Siyama ta
sauko babu wanda zai kaishi farin ciki. 'Yar aikin anti amina
rike da Faruk ta iso
"Anti kuka yakeyi."
Ta karbeshi,daidai lokacin da anti habiba ta iso
"Ya kuka tsaya kakana? Dare yana yi. Bismillah."
Tayi furucin ba tare data ko dubi Siyama ba,ta shafi gefen
kumatun Hadiyya
"Masha Allah amaryarmu kinyi shar dake."
Hadiyya tayi murmushi tana sunne kanta. Jafar ya kara riko
hannunta,akan idon Siyama. Ta hadiyi miyau cikin bakin ciki
tayi azamar barin wajensu yayinda tunowa da wani abun ya
sanya tayi murmushin mugunta gami da danne hawayen
dake kokarin zubo mata.........!!!!
Har aka kammala dinner party,Hadiyya bata da nutsuwa ko
kad'an. Ba Basma ba,daidai da Anti habiba da Jafar sun
kula akwai abunda ya b'ata ranta. Wannan ya sanya ko
bayan fitowarsu Anti habiba ta ja hannunta suka keb'e
"Menene ya b'ata ranki amaryarmu?"
Hadiyya ta kakalo murmushi yayinda kwalla ya ciko idonta
"Bakomai anti."
"Look Hadiyya,yanzu matsayin kanwa kike agareni. Ki
sanar dani ko an maki wani abu? Ki gayamin ma me
Siyama ke ce maki ne dazu?"
Hawayen da take mak'alewa ya zubo,tayi dariya kad'an ta
girgiza kanta
"Ba abunda tacemin anti,kawai na soma tunanin rabuwa da
Mamana ne."
Anti ta sauke ajiyar zuciya ba don ta gama yarda da
maganar Hadiyya ba,ta rungumota
"Kiyi hakuri kanwata,daman rayuwar haka take. Ko aure
baiyi sanadin rabuwarku ba,toh fa akwai mutuwa. Kinji ko?"
Ta gyada kanta,anti tayi murmushi ta share mata hawaye
"Yauwa ko kefa,ki daurewa ranki kada ki bari yayar taki ta
gano lagonki. Kedai ki dage da addu'ar tsari da zaman
lafiya a gidan mijinki. Mijinki yana sonki sosai,kiyi amfani
da wannan damar wajen kyautata mishi."
Hadiyya ta gyada kanta kafin ta amsa da toh. Daga haka
suka koma inda su Jafar suke.
Siyama da amininta tuni sunyi gaba abinsu.
Haris ya matsa kusa da Jafar har yana dukan kafad'arsa da
nashi
"Shegen sama,ya akayi ka zamo mijin mai siyar da abinci?
Ko ka manta kalamanka na baya? Kai kafi karfinta?"
Jafar ba tare daya dubeshi ba yayi murmushi
"So gamon jini ne,nima ban taba tsammanin zan
aureta,Allah Yayi saita zama matata ne."
Ya jinjina kansa
"Gaskiya ne, Allah Ya baku zaman lafiya toh. Saidai ya akayi
Ladi ta koma wacce kuke wayar nan?"
Jafar ya harareshi
"Gulmar kuma sai tayi yawa malam,whatsoever she's now
my wife and I love her,so,abar maganar dogon labari ne
wanda bazaka tab'a jinshi ba."
Sukayi dariya,
"Ai shikenan,na hakura da ji. Ai idan ka lura su kansu
abokan kasuwancinka sunyi mamakin wannan auren naku."
Jafar ya tabe baki
"Sai suyi,barsu su fadi abunda duk sukaga zasu iya
fad'i,nikam ba abunda zai sa na rabu da Hadiyya in sha
Allahu saidai mutuwa."
Murmushi kawai Haris yayi.
****
A mota suna zaune tare da Jafar,Basma da Haris suna
daga kofar gidan su Hadiyya suna hirar duniya. Jafar ya
karkato sosai yana dubanta da mamakin ganin yanda ta
daure fuska tamau babu ko alamun fara'a akan fuskar nata.
"Wai Deeya menene ya b'atamin ranki ne? Please tell me."
Ta kauda kanta tana duban waje,yayi azamar sanya
hannunsa ya karkato da fuskarta ta runtse ido domin daidai
da dubanshi batason tayi
"Wallahi saikin gayamin abunda ya bata maki rai ko kuma
muyita zama a haka."
Ta cire hannunsa akan hab'anta tana mai bud'e
idanuwanta,jikinsa yayi sanyi ganin yanda suka kad'a
sukayi ja ga kyallin ruwan hawaye daga cikinsu. Cikin
sassanyar murya yace
"Deeya! Me yayi zafi ne? Meke damunki?"
"KARKI KASANCE MAI DAUKAR MAGANA! KADA KI ZAMA
MAI YAWAN KAI KARAR ABOKIYAR ZAMANKI GA MIJINKI!
LALLAI WANNAN KAN RAGEWA MACE K'IMA A IDON
MIJINTA!!"
Kalaman mahaifiyarta kenan a daren jiya,taji bazata iya
sanar dashi ba,ta k'ak'alo murmushi mai ciwo
"Bakomai Yaya j..."
"A'a deeya! Dubi kwayar idanuwanki,hawaye ne fa! Menene
ya faru ki gayamin don Allah idan ma nine zan baki hakuri
wallahi bansan na aikata ba. Deeya banason bacin ranki ko
kadan,ko fatin bai maki dad'i bane?"
Tayi saurin girgiza kanta ganin yanda yabi ya tada
hankalinsa
"A'a duk fa ba wannan bane. Kawai ina tunanin rabuwa da
mamana ne."
Ya had'e jikinsu
"Kiyi hakuri Deeya,nayi maki alkawarin kular maki da
Mama. Hakanan zamu dunga ziyartarta akai akai kinji ko?"
Tayi murmushi ta runtse ido
"Toh nagode Yaya j."
Daga haka ta zare jikinta
"Yaya j dare yana yi. Zan tafi."
Shiru yayi kawai yana binta da murmushi,kallon yayi mata
tsauri wanda dole yasa ta kauda idonta. Ba zato taji ya
sumbaci kumatunta yana mai dafe kanta
"Allah Ya albarkaci rayuwar aurenmu Deeya,madallah da
mace kyakkyawa mai kyawun hali. Nagode Allah da
Yayimin baiwar samunki a matsayin matata. Saida safe,ki
gaishemin da Mamanmu."
Tayi murmushi,tana matukar son Jafar a ranta dole taji
bazata iya dogon fushi dashi ba.
"Zataji in sha Allah."
Daga haka ta bude kofa ta fita, ganin haka Haris ya taho
"Toh amaryarmu sai kuma gobe insha Allah idan munzo
dauke abarmu ko?"
Sukayi dariya kafin suyi sallama. Ta jera ita da Basma
zuwa cikin gidan.
****33
Basma ta dubi Hadiyya dake cire kayan adonta
"Ni kuwa Aminiya daman inason tambayarki,me Siyama ke
gayamaki ne d'azu da kuna zaune?"
Hadiyya ta k'arasa cire kayan jikinta tayi daura kirji kafin ta
zauna tana karkato ga dubanta ga Basma wacce ta baza
kunnuwa tana jiran amsarta. Cikin yanayin damuwa
ta zayyane mata dukkan abunda Siyama tace da ita. Basma
ta ja dogon tsaki,cike da bakin ciki ta kalli nuna Hadiyya da
tafin hannunta
"Yanzu ke saboda Allah akan wannan banzan maganar kike
shirin b'atawa kanki ranar tarihi wanda muddin ya tafi bazai
dawo ba? Haba Hadiyya,why are you acting like a child? Ki
bud'e kunnuwanki ki saurareni,wannan kad'an ne daga
makircin mata! Zanyi maki uzuri tunda baki tab'a zama
cikin wasu da suke rayuwar kishi ba! Amma kada kiso kiga
antina Na'ima dake zaune a Zaria. Wallahi basa jituwa da
maman kasim uwargidanta. Amma kada kiso kiga kissar
karya da takeyi a gaban idon uncle Junaid. Hadiyya duk irin
wadannan abubuwan ya dace tun yanzu ki koyi yak'i
dasu,kada ki bari ko kusa taci nasara akanki. Kada ki yarda
Siyama ta gano lagonki tun yanzu! Ki zage damtsenki,kada
fa wani kusancinsu ya rud'aki ki dunga tunanin gaskiyane
abubuwan data zayyano maki cewa Jafar baya sonki kin
gane ko?"
Hadiyya ta sauke ajiyar zuciya yayinda taji ranta ya soma
yin sanyi,
"Na fahimceki aminiya,shiyasa shawara take da dadi.
Amma akwai abu daya daya dauremin kai. Ya akayi Siyama
tasan ni na shigewa Jafar alhalin..."
"Hadiyya inace kinsan tarihin yanda aure ya kullu tsakanin
Sayyada Khadija r.a da Manzon rahma s.a.w ko?"
Hadiyya ta gyada kanta,Basma tayi murmushi
"Toh Alhamdulillah,kada ki kara tayar da hankalinki akan
wannan maganar ma domin Allah. Wannan bazai zamo
hujjar da za'a ce Jafar baya sonki ba. Idanuwan Jafar sun
isa kad'ai wajen gamsar dake irin matsanancin soyayyar da
yake maki. Hadiyya bake ba,duk wanda zai zauna daku na
mintoci sai yayi kiranki da mai sa'a saboda soyayyar da
mijinki ke nuna maki. (Please and please) ki kwantar da
hankalinki,ki nutsu kiyi ibadar aure. Ki ture wannan shaci
fad'in na Siyama a gefe kiyi amfani da abunda ke da
idanunki suka gani kuma suka gamsu dashi. Jafar zaki
zauna dashi ba Siyama ba,saboda haka ki dage wajen
karantar halayyar mijinki,zaifi maki kyau da zama riba a
rayuwarki."
Hadiyya tayi murmushin jin dad'i,kaunar aminiyarta ya k'aru
a zuciyarta. A gefe kuma tsananin kaunar mijinta da burin
zama dashi ke nukurkusarta. Haka dai Basma ta cigaba da
bata shawarwari,sun jima kafin bacci ya daukesu...... !!
******
Tunda asuba Mama ta sanya diyarta a gaba tayi ta nasiha a
gareta akan tayi hakuri ta zauna da mijinta da danginsa
lafiya.
"Kada ki yarda kiyi wani abu da mijinki zaiga bak'inki
Ladi,ki bawa matarsa girmanta a matsayinta na
uwargidansa. Ki bishi sau da k'afa. Wannan shine gatan
dana rasa Ladi,yau gaki ina maki nasiha akan zaman aure
saidai a baya nikam babu mai farin cikin aurena da
mahaifinki. Yau gashi babu ranshi amma bani da ikon
takawa naje ga yan uwana bisa cireni daga zuri'arsu da
sukayi. Kinga bani da labarin iyayena suna raye ne ko sun
mutu."
Mama ta tsaya sakamakon sheshshekar kukan data soma
yi,Hadiyya itama kukan takeyi ta k'ara rukunkume
kafafuwan mamanta. Tausayinta ne ke ratsa zuciyarta,tana
jin inama ace babu abunda zaisa tayi nisa da Mamanta
suyita rayuwarsu tare. Mama ta dafa kanta tana jan majina
"Ya isa Ladi,kibar kukan nan. Na tabbata wataran sai labari.
Allah zai kawomin karshen wannan halin da nake ciki. Kedai
kiyi amfani da nasihu na. Allah Ya baku zaman lafiya."
Hadiyya ta dago kanta fuskarta har ta kumbura saboda
tsabar kuka,ta dubi mamanta
"Mama meyasa ke bazaki je Nijar d'in ba? Na tabbatar
zuwa yanzu Abbanki ya sauko ya bar fushi bakya tsoron
fushinsa ya janyo maki matsala? Hakkine a kanki kibi
iyayenki? Mama kada fa lokaci yayita k'ure maki baki nemi
gafararsu ba?"
Mama tayi murmushi mai ciwo
"Kin manta Ladi,Mahaifina yace duk ranar dana tako mishi
gida tsinemin zaiyi. Wannan dalilin ne ya sanya bansan
komawa,amma ina kewarsu sosai. Fatana Allah Ya huci
zuciyarsa."
"Ameen."
Cewar Hadiyya cikin tausayawa mamanta.
******
Karfe takwas da mintoci aka mik'a Hadiyya gidan mijinta
Jafar. Itama fallen dakuna biyu aka bata inda d'ayan ya
zamana falonta,d'ayan kuma k'uryarta.
Kofar Siyama a gark'ame take, hakanan fitilunta a kashe
wannan ya bawa masu kawo amaryar mamaki,anti kuwa
murmushi tayi sanin kishi ne ya kori Siyama. Ta tabe baki
kawai.
Zuwa karfe tara kowa ya watse,Basma ma duk yanda
Hadiyya taso ta tsaya har angwaye su zo amma ina tak'i.
Saidai tayi mata alk'awarin zuwa da safe kafin ta fice Zaria.
Hakanan aka bar Hadiyya ita d'aya shiru. Mintuna kusan
biyar tana nan zaunen taji sallamar Jafar da abokanansa.
Nan da nan ta k'ara jan gyalenta ta rufe fuskarta. Sun
d'anyi barkwancinsu kafin suyi addu'o'i a shafa. Sannan
suka fita gaba daya har Jafar,yayi mamakin ganin dakin
Siyama a rufe,ya dubesu da murmushin yak'e
"Inajin dai ta kwanta ne."
Da haka suka juya yayi musu rakiya sannan ya dawo ciki.
Kofar Siyama ya hau bugawa saidai burus tayi tak'i
bud'ewa. Har ya juya zai tafi ne yaji kukan Faruk wannan ya
tabbatar mishi tana jinshi.
"Siyama! Siyama!!'
Ya ambata cikin sanyin murya.....!!!
Tana jinsa tayi burus dashi,idanuwanta sunyi jazur sun
kumbura saboda tsabar kuka. K'arar wayarta ya katseta,shi
d'inne dai,tayi saurin kashe wayar gaba daya.
Jin k'arar wayar da katsewarta ya k'ara tabbatar mishi lallai
Siyama tana ciki. Hankalinsa ya tashi ba don komai ba sai
don rashin sanin takamaiman halin da take ciki. Ya tabbatar
ko yaya take bata cikin hayyacinta. Har ya d'aga hannu da
niyyar k'ara buga k'ofar a fusace ta bud'e,bakinta a bud'e
tana shirin soma magana yayi saurin rufe mata bakin da
hannunsa kafin ya rikota yana mai sanya jikinsa sosai cikin
d'akin.
K'arar buga k'ofar yayi daidai da faduwar gaban daya
risketa. Ta bud'e mayafin dake lullub'e a kanta hawaye
wani yana bin wani akan kuncinta. Kishi kumallon mata
ne,komai dake faruwa akan kunnenta. Jin rufe kofar ya
tabbatar mata binta yayi cikin dakin. Ta share
hawayenta,sai lokacin ma ta k'arewa d'akin kallo.
Alhamdulillah,lallai kam kwalliya ta biya kudin sabulu. A yau
babu wanda zai kalli dakin Hadiyya ya kawo ita d'in wata
diyar talaka ce ba saboda komai na dakin na zamani ne
sosai. Duk da dai yayan mahaifinta ne ya dauki nauyin gado
da kujerun amma Mamanta ba ba'a barta a baya ba wajen
gyarawa d'iyarta d'akuna. Kayan kicin dinta ma wasu da
yawa komawa akayi dasu,aka ajiye mata wasu a d'akinta
sakamakon kicin d'insu guda d'aya ne ita da Siyama.
Wannan yasa ba abunda aka jera mata a kicin gudun
rigima.
Bacci kawai take sonyi saboda tsabar gajiyar dake tattare
da ita.
Acan kuwa Jafar yayi ta rarrashin Siyama da kalamai masu
sanyi har saida yaga ta sauko. Itama don kissa ta dunga
shishshige mishi tana wani shagwabe muryarta hankalinsa
gaba d'aya ya tafi gun Deeyarsa. Dakyar Siyama ta barshi
ya fito tabi bayanshi da kallo tana murmushin mugunta. Ta
tabbatar Hadiyya ta gama kai wa bango. Gefe guda kuma
wani irin matsanancin kishinsa ke nukurkusar zuciyarta.
Tana son Jafar,so bana wasa ba. Shine first love
nata,bayan shi ma bata tab'a sanin kowane d'a namiji ba.
Shine ya koya mata soyayya,yau gashi can zai kwana a
d'akin wata ba ita ba. Yayi kyau yayi fresh a wannan ranar
sai tashin kamshi yakeyi. Ji take tamkar ta tashi taje ta
hanashi shiga d'akin Hadiyya.
"INA KARA GARGADINKI AKAN KADA KI NUNA MISHI
WAUTARKI KO KUMA TSANANIN KISHINKI GARETA! ZAMU
SAN ABUNYI."
Zantukan anti rumaisa suka fado a ranta,ta hau gyada kai
tamkar kadangaruwa. Wannan ne ya samar mata nutsuwa.
KAZAMAR GIDA***34
Motsin da taji ya sanyata duban kofar d'akin. Daidai lokacin
da take daka uban hamma, idanuwanta kuwa kallo d'aya
zakayi musu ka tabbatar bacci ne fal a cikinsu. Ya k'araso
ciki yana murmushi agareta,ta maida martani a kunyace
gami da kautar da kanta gefe guda. Yana shirin rufo k'ofar
ne ya jiyo jiniyar gidan wani hamshakin mai kud'i dake nan
bayansu wanda ya bashi tabbacin cewa an kawo wuta,dole
ya fita ya chanja layin bayan ya kashe injin ya maidashi
gefe.
Ya rufe kofar ya dubi Hadiyya da murmushi dauke akan
fuskarsa
"I'm sorry Deeyana,na barki ke d'aya."
Ta girgiza kanta tana murmushi kawai ba tare da tace uffan
ba. Ya karasa ya dad'a karfin fankar d'akin sakamakon
zafin da akeyi sannan ya janyo ledar da Haris ya ajiye musu
d'azu. Bayan ya ajiye a k'asa ne ya dubeta cikin murmushi
"Bismillah matata,nasan kina dauke da yunwa. Sauko mu
motsa bakinmu."
Ta marairaice sa'ilin da take lumshe idonta alamun dai
bacci kawai take buk'ata.
"Yaya j banjin yunwa saidai bacci."
Ya girgiza kai
"Ban yarda ba Hadiyya,me kikaci ne duka duka da har zaki
ce haka? Taso kafin nazo."
Ta mike a sannu ta iso kan kafet d'in ta zauna. Kadan
sukaci domin shima hankalinsa yana ga Hadiyyar tasa.
Suka d'an sha lemo da ruwa. Saida ta tabbatar masa tana
da alwala kafin ya umarceta data tashi suyi nafila. Daga
nan yayi addu'o'i bisa koyarwar addini.
Ganin yanda Hadiyya ta rud'e sosai ne ya sanya Jafar bai
nemi wani hakkinsa ba banda dai abunda da ba'a rasa ba
daga bisani ya kashe musu fitilu shima ya rage
kayan jikinsa kamar yanda tun farko ya rarrashi Hadiyya
tayi sannan suka kwanta. Bacci ne cike da gajiya sukeyi,sai
a wannan lokacin itama Siyama baccin ya dauketa bayan
data bar jin kowane motsi daga d'akin.
Koda safe ma bata ga wata alama da yayi nuni da cewar
wata mu'amala ta shiga tsakaninsu ba. Dadi ya
turnuketa,lallai ta gaskata kalaman Jafar da yace itace
wacce yafi so yafi sha'awa a rayuwarsa. Zuciyarta wasai ta
mike bayan fitar Jafar daga d'akinta tayi azamar goge
hammatarta da lemun tsami ta zura doguwar rigar atamfa.
Nan ta fad'a band'akinta na falo ta goge baki da fuskarta
harma da k'afafuwanta sannan ta fito ta dauki kwalliya.
Faruk dake bacci ta dubeshi ta yamutse fuska ganin famfas
dinsa ta cika tam,ashe fa ta manta famfas tun na yamma
ne data sanyamishi. Taja tsaki ita kam tana bukatar yar aiki
ko don kada Hadiyya ta rainata. Haka ta mike tana kamshin
turaren humra ta fito tsakar gidan. Suka ci karo da Hadiyya
wacce fitowarta kenan daga wanka tana sanye da
zunbulelan hijabi. Gaban Hadiyya ya fadi,takan rasa
meyasa takejin faduwar gaba aduk lokacin da tayi arba da
Siyama. Ta daure ta saki murmushi cikin sanyin muryarta
ta gaisheta
"Anti barka da asuba. Kin tashi lafiya?"
Siyama ta banka mata harara wai bandakin da mijinta kadai
ke shiga bai barinta ta shigarasa yau ga wata can tazo har
tayi amfani dashi,kishi ya cika zuciyarta,kamar bazata
amsa mata ba saidai ta amsa sanin da tayi Jafar yana daga
ciki kuma zai iya jinsu.
"Alhamdulillah amarya,ya bak'unta?"
Daga haka bata saurari amsarta ba ta fad'a kicin sai kace
abun arziki zata tsinana.....!
Hadiyya murmushi kawai tayi ta nufi d'akinta. Tana shiga
taci karo da jikin mutum. Wannan yasa ta dago ta
dubeshi,murmushi ya sakar mata,kafin ya soma yunkurin
yin wani abu tuni ta kauce tayi gefe tana mai marairaicewa
"Don Allah ka bari nayi shiri cikin nutsuwa mana."
Jafar yayi murmushi,tuni ya rigayeta wanka domin shi ya
saba da wankan wuri. Yana sanye da kananun kaya marasa
nauyi.
"Ai banyi komai ba tukunna Deeya,yau bazan lek'a k'ofar
gida ba kwata kwata. Ina nan tare da sahibata."
Ta harareshi a wasance yayi kamar zai cafkota tayi azamar
hayewa gadon da siririyar muryarta kamar na baby tace
"Wayyo yaya j,domin Allah kayi hakuri."
Yayi dariya
"Sai tsoro kamar farar kura. Shikenan idan kin kammala ki
sameni a sashen yayarki muyi kari,ok?"
Ta gyada kanta
"Toh."
Ya sakar mata murmushi ya juya ya fita a nishad'ance.
Kicin ya soma lek'awa,gabansa ya fadi ganin Siyama na
fasa kwai acikin kwano,har kwai zata soya daman? Ta juyo
ta dubeshi,yayi azamar sakar mata murmushi na yak'e
yana mai shigowa sosai ciki
"Madam kwai zaki soya ne? Kawo na taimaka maki."
Tayi farr da ido,daidai lokacin Faruk ya soma kuka,ya
dubeta
"Barshi zanyi,tafi kiji dashi."
Ta sauke ajiyar zuciya,farin cikin wannan irin kulawar da
Jafar keyi mata ne ya sanyata jin wani dadi har tana ganin
tamkar Jafar bai damu da Hadiyya ba sai ita. Yana ganin ta
fita ya sauke ajiyar zuciya gami da hamdala. Tuni ya had'a
komai ya soye kwan tas,kamshinsa ya cika ko'ina. Yayi
azamar kammalawa ya sanya a cooler,lokacin ruwan Lipton
data jona a heater ya tafasa ya sauke ya juyeshi shima a
filas. Yana gama haka ya jera komai akan katon
faranti,daidai cokula da kofunan da zasu bukata sannan ya
fito. Ya dubi kofar d'akin Hadiyya,tabbas bata gama ba
balle ta fito yayi murmushi ya nufi d'akin. Ya sameta tana
kokarin shafa jan baki,da sauri ya karb'a
"Kawo nan ki gani,nine da wannan aikin."
Tayi kokarin turjewa yayi azamar rikota sosai zuwa jikinsa
ya hau kiciniyar shafa mata a lebbanta. Ta tsuke bakin tana
mai kauda kanta gefe,murmushi yayi ya k'ara kai hannunshi
ta juyar zuwa d'ayan bangaren. Abun yaso ya bashi dariya
"Wai deeya bazaki tsaya bane? Shikenan bari ki gani."
Yakai jan bakin lebbansa tayi saurin rikewa,wannan yasa
suka dubi juna. Sirrin dake ran kowannensu ya fito a zahiri.
Ta d'anyi k'asa da kanta
"Me kake shirin yi ne?"
Ya k'ara rike hannunta
"Shafawa zanyi sai na sammaki a naki lebban ko laifi ne?"
Ta harareshi kadan kafin ta girgiza kanta
"Ka tab'a ganin inda namiji ya kwaikwaiyi mata idan ba dan
daudu ba?"
Yayi murmushi ya ajiye janbakin
"Hakane fa tawan,toh bari kiga yanda za'ayi bar jan bakin
nan ma banaso."
Kafin ta ankara,sako mai girma ya ziyarceta daga
wajenshi,har bata iya kaucewa ba kamar yanda basu iya
saita kansu ba.
"My J!"
Muryar Siyama daga waje ya katse musu hanzari,da azama
Hadiyya ta matsa baya,suka hada ido ya sakar mata
shu'umin murmushi sannan yayi gyaran murya
"Fito muje muyi kari."
Ta kalleshi ta gefen ido,ya gyara zaman rigarsa ya fice daga
d'akin. Murmushi ta saki soyayyar mijinta ya k'ara mamaye
zuciyarta.
*****35
Wani banzan kallo ta watsa mishi ganin yanda duk ya
sauya. Tasan mijinta,babu yanayin da zai shiga bazata
d'agoshi ba. Idanuwanta suka kad'a saboda matsanancin
kishin Jafar,saidai kafin takai ga cewa komai Hadiyya tayi
sallama. Wannan ya sanyata saita fuskarta gami da kakalo
murmushi ta janyo hannun Jafar
"Zauna yaya j,lokacin karin ka yana neman wucewa. Sannu
fa bakuwarmu."
Jafar yayi murmushi,baiyi mamakin wannan sauyin na
Siyama ba tunda yana da labarin yanda mata ke sauya
halayyarsu marasa kyau aduk sadda wata ta shigo gudun
kada ta hango wallenta. Yabi falon da kallo ya girgiza
kanshi,wa zaice KAZAMAR GIDA ce? Komai an gyarashi
harda turaren tsinke aka sanya. Faruk ma sai kamshi
yakeyi yaron yana kwance yana wasa da remote.
Bayan sun zauna,ta hadawa jafar,Hadiyya itama taja kofi ta
tsiyaya ruwan tea kadan tasa siga. Yana lura da ita,ta
shanye ruwan tea din bata da niyyar cin kwan. Wannan ya
sanyashi yin magana
"Kefa bamason bak'unta,meye abun wani jin kunya. Ga
kwai nan antinki ta soya maki kici ko yaya ne."
Siyama ta dubeshi da harara,yayi kamar bai gani ba. Ta
cigaba da kora biredi da kwai a cikinta tana dannawa da
ruwan shayi. Hadiyya kuwa jin wannan ya sanya ta gutsiri
kwan tayi mishi loma biyu sannan ta mike bayan ta goge
hannunta da tissue. Yayi kamar zai riko hannunta saidai
tunawa da Siyama a wajen ya fasa
"Kada kice kin koshi?"
Tayi murmushi lokacin data sanya hannu ta dauki Faruk
"Eh na koshi yaya j."
Daga haka tayi hanyar waje
"Ji mana,ajiyeshi zan bashi abinci ne."
Cewar Siyama wacce tayi maganar kusan a fusace.
Wannan ya sanya jikin Hadiyya yayi sanyi,aikuwa dai tana
ajiye Faruk ya gantsara kuka. Tana shirin k'ara
daukarshi,Siyama tayi azamar dauke d'anta. Cikin rashin jin
dadi Hadiyya ta fice tana mai tabe baki mai nuni da ita ta
sani. Jafar bayan fitarta ya dubi Siyama
"Menene haka Siyama? Laifi ne idan ya dauki Faruk? Inace
itama babarsa ce?"
Ta kalleshi a shek'e
"Babu abunda ya had'ata dashi. Ni nayi nakudar abina."
Ya jinjina kanshi kafin yaja karamin tsaki shima ya mike
"Ok naji wannan."
"Ina kuma zakaje?"
Ya kalleta kafin yayi hanyar fita
"Na koshi ne."
Kafin ta samu bakin magana tuni ya fice.
Bakin ciki ya turnuketa,ta janyo wayarta a fusace ta
dannawa anti rumaisa kira...........
Ringing uku ana hud'u ta amsa.
"Ya akayi Siyama?"
Cikin muryar kuka Siyama tace
"Nidai Anti ya dace a dauki matakin nan,ina
tsoron kada Jafar yafi karfina anan gaba. Kinga
Hajiya tace bazata kara sanya hannunta cikin
harkar aurena ba tunda ni na janyowa kaina. Anti
ku kadai kuka ragemin don Allah ku taimakamin
banason ganin Jafar da wata."
Tana kaiwa nan hawayenta suka
kwaranyo,Rumaisa taja dogon tsaki wanda
sautinsa ya karad'e kunnen Siyama,cikin fad'a
fad'a take magana
"Kedai kam ko kusa baki da hakuri Siyama. Kema
kinsan barin wannan shegiyar a gidan aurenki
abun kunya ne garemu. Kinsan su Habiba bazasu
bar goranta mana ba. Ki nutsu ki kwantar da
hankalinki kedai abunda nakeso dake matukar ta
fita daga girki idan zaki karb'i naki kizo kafin
kowacce mu'amala ta shiga tsakaninku. Ai
abunda yasa ma a baya banyi niyyar baki wannan
taimakon ba don ina ganin ke d'aya ce amma
tunda abun yazo da haka toh kuwa dole ne mu
tashi tsaye kyam da kafafuwan mu."
Siyama ta sauke ajiyar zuciya tana
murmushi,sa'ilin kuma da anti ta cigaba da
zancenta
"Nasan halinki Siyama,nasanki da shegiyar
kazanta da son jiki. Toh watsar da wannan duka
idan kuwa kin gaza yin hakan ina mai tabbatar
maki zata rainaki ne."
Siyama ta tab'e baki ta marairaice
"Toh nifa anti kema kinsan ban saba da aikin
wahala.."
"Ajiye wannan gefe,mun gama magana da talatu
mai kawomin 'yan aiki kwanan nan zata nemo
maki."
Siyama taji dad'i sosai
"Yauwa antina,Allah Ya barmin ke."
Rumaisa tayi dariya ta kashe wayar.
*****
Acan kuwa soyayya kawai Jafar me gurza da
matarsa. Baiyi niyyar yi mata komai ba yanzun
ma sakamakon yasan rana ta soma yi
kodayaushe zata iya samun ziyara daga 'yan
uwanta. Ai kuwa dai suna cikin hirarrakinsu na
soyayya suka tsinci karar kwankwasa kofar
gidan. Jafar ya mike ba'a hayyacinsa ba,ita kuwa
kunya ce ta hanata motsi har saida yabar d'akin
sannan tayi azamar gyara shimfid'ar ta hau
d'aura d'ankwalinta. Tana jin muryar,Basma ce.
Ai da gudu ta fito tana murnar ganinta. Basma ta
tureta da hararar wasa
"Kinji ki? Sai kace ba jiyan nan muka rabu ba?"
Hadiyya tayi murmushi,suka shige falonta wanda
sam Hadiyya bata shiga ba sai a yanzu. Yayi
kyau sosai,an zuba mata kaya har dasu kayan
kallo. Bayan sun zauna Jafar ya lek'o suka gaisa
da Basma kafin ya koma d'akin ya barsu anan.
Basma tayi ta k'are mata kallo tana dariya k'asa
k'asa,Hadiyya ta daure fuska cikin wasa
"Toh kuma wannan dariyar fa ta mecece?"
Wannan yasa ta fito da dariyarta a fili
"A'a fa,naga kin chanja kinyi kyau ba dole nayi
dariya ba."
Suka sanya dariya,Hadiyya ta d'aka mata duka
"Shegiya,a kwana d'aya ko yini banyi ba me zai
chanja ni?"
Basma batace komai ba banda murmushin da
takeyi
"Uhum,kyaji dashi. Mama tace na gaisheki sosai."
Cikin tausayi Hadiyya tace
"Allah Sarki mamana,nasan dole zatayi kewata.
Yanzu ko waye zai dunga kwana a wurinta?"
Basma ta dafa kafad'ar Hadiyya tana murmushi
"Kwantar da hankalinki,Kawu Nuhu ya bata
d'iyarsa Najwa. Tun daren jiya take sanar mana.
Yau da safe har gidansa taje tayi godiya sosai. Ai
wallahi da haka ake samun dangin miji da anji
dad'i. Dangin mahaifinki suna kaunar mamanki
sosai Hadiyya."
Hadiyya wacce ke kwalkar farin ciki ta sharesu
tace
"Alhamdulillah,kaunar da sukeyi mata fa yawa ne
da ita. Don wallahi Kawu nuhu yaso aurenta
sosai bayan rasuwar Abbana amma sam mama
tak'i. Ke a yanda naji labari ma da farko ya
dauke mata nauyin komai na hidimar gida saidai
bata bashi fuska ba ko kusa karshe ma tace ta
yafe. Ina mai tabbatar maki ba don komai take
gudunsa ba sai gujewa matarsa duk da cewa anti
Karima mai kyawun halayya ce amma sam Mama
tak'i a ganinta abun kunya ne aikata hakan."
Basma cike da mamaki ta girgiza kanta
"Lallai,amma Mama da gaskiyarta domin wannan
zamanin sai kiga kishi ya maida nagari mugu. Ke
baki ma fad'amin ba,mutuniyar taki tayi maku
abun kari?"
Hadiyya ta tab'e baki,nan ta labarta mata komai
da yanda sukayi akan d'anta Faruk.
"Tun daga yau? Amma wannan bata da wayo.
Kedai ki bata girmanta koda a bayan idon mijinki
ne domin munafunci ba abunyi bane."
KAZAMAR GIDA PART ****36
Ta zura hannu a jakarta ta dauko wata bakar
leda ta ajiye a cinyar Hadiyya
"Sak'o inji Sarah,tace na kawo maki sannan don
Allah kada kiyi wasa da shansu."
Ta karashe zancen cikin sigar zolaya,hadiyya ta
harareta. Ta mike ta adana ledar anan falo
sannan ta dawo. Ganin Basma na gyara zaman
mayafinta tace
"Menene haka?"
"Kin manta yau zan wuce Zariya? Yanzu ma sauri
sauri zanyi naje gida na dauki abunda zan dauka
nayi gaba. Ki bari tunda ga waya hannunmu ai ba
matsala ko?"
Hadiyya cikin rashin jin dadin tafiyar
aminiyarta,ta rakota har k'ofa. Basma ta sanya
takalmi tana dubanta
"Rakani mu gaisa."
Suka dunguma d'akin Siyama. Turus sukayi ganin
ko kofi bata d'auke ba na wanda sukayi amfani
dashi bata falon ma. Basma tayi ta sallama
amma tayi burus dasu. Wannan ya jawo hankalin
Jafar ya fito ganinsa ne yasa suka dawo baya.
Ya dubi Basma
"A'a dai Basma, har zaki tafi daga zuwa?"
Basma tana dariya tace
"Wallahi kuwa,kasan makaranta zan koma a yau
acan Zariya."
Ya gyada kansa. Sukayi sallama ta tafi kafin ya
ja matarsa cikin d'akin sukayi makwas abinsu.
Siyama ta sauke labulenta taja tsaki
"Munafukan banza kawai."
Ta fad'a a fili......
Kwanan Hadiyya biyar a gidan nan,saidai ta soma gane
rashin iya girkin Siyama. Hakanan take daurewa taci ko don
mijinta wanda shima ta gani yana wannan kokarin,karkari
dai idan sun gama ya fita ya nemo mata wani d'an abun.
Sharan tsakar gidan da wanke wanke harma da wankin
kayan yaron ta lura wannan dai yaron da suke cewa
Dauda,shi keda alhakin yi. Abun yakan bata mamaki ya
daure mata kai har takan rasa aikin da Siyama keyi banda
ta jagwalgwala girki ta hakimce abinta a falo saidai kayi ta
jin k'arar talabijin daga falon nata.
Yau ma ya kasance juma'a bayan fitar Jafar zuwa gidansu
domin ziyartar iyayensa,Hadiyya tana kwance a falonta
bacci ya soma fisgarta taji wayarta ta dauki k'ara. Ta mike
tana mai buga hamma,Jafar ne. Fuskarta dauke da
murmushi ta dauka
"Salamun alaikum my j,an sauko daga juma'a lafiya?"
"Wa'alaikissalam matar J, gashi har na dauko hanyar gida.
Kinsan bana iya nisa dake yanzu ko kad'an."
Tayi murmushi tamkar yana ganinta ta bud'e baki zatayi
magana kenan ta hango inuwar mutum jikin labulenta. Cike
da mamaki ta cigaba da maganarta
"Yaya j kenan,shikenan saika dawo."
Ya amsa da ok sannan sukayi sallama,da saurinta tayi wuf
ta mike ta fito tsakar gidan. Cikin tsananin rud'ani da rashin
zaton fitowar nata ya sanyata saurin kai hannu akan kayan
wankin Faruk da basu isa ace sun bushe ba ta wayance da
d'aukar wata riga sannan tayi hanyar d'akinta.
Mamaki ya hana Hadiyya cewa uffan,ta girgiza kanta gami
da basarwa ta hanyar shigewa d'akinta. Gado ya fad'a cike
da tunane tunane a zuciyarta,wai me kenan? Siyama kuma
lab'e takeyi mata? Tunaninta ya katse jin k'arar mashin d'in
Jafar. Cikin d'aguwa da son ganinsa ta mike tana lek'ansa
ta taga. Ya shigo ciki da sallamarsa,saidai ya soma nufar
d'akin Siyama,bayan ya duba lafiyarsu ya ajiye mata leda
k'ulli d'aya sannan ya fito zuwa d'akin Hadiyya. Siyama ta
ja tsaki cikin tsabagen bakin ciki,anya zata iya dannewa
kuwa kamar yanda Anti rumaisa ta gargadeta? Ta sauke
ajiyar zuciya,ji takeyi tamkar tayi hauka a kwanakin nan. Ta
ja tsaki,ai wallahi tunda yana da kud'in siyo kaji ya kawo
musu toh ita kam bazata kara yi musu girki ba tunda ba
baiwarsu bace. Cikin takaici ta janyo ledar ta bud'e,gata
kwadayayya kamar aminanta😂daman fa sai hali
yaso d'aya k'awance ke tafiya daidai😜. Nan ta
soma ci,saboda dad'in kazar ta manta da kudurin dake
zuciyarta na yin lab'e.
******
Hajiya tana zaune a falonta tana karkad'a kafafuwanta,tun
aninta bai wuce ta yanda zata raba auren Siyama da Jafar
ba. Ta gaji da ganin Siyama tana auren da babu wani
shanawar rayuwa. Gashi itace karama kuma mafi soyuwa a
ranta duk a cikin 'ya'yanta. Sallamar Hajiya Shema'u ce ta
katseta. Ta maido hankalinta gareta,ta sauke ajiyar zuciya.
Hajiya shema'u😨 ta shigo. Babbar aminiya ga
Hajiya Maimuna. Tana taunar cingam na rashin mutunci
wanda ita inda sabo ta saba dashi,ta shigo ta zauna da
d'aurin nan da ake kira da Ture Kaga Tsiya a kanta. Ta dubi
Hajiya Maimuna shek'ek'e
"Yau kuma waya tab'oki Hajiya Maimuna? Kada kicemin har
yanzu kin kasa komai akan batun auren wannan
tsinannen?"
Hajiya ta sauke ajiyar zuciya,ta girgiza kanta
"Bari kawai hajiya shema'u,aikin gama ya gama. Auren nan
an yishi,idan da abunda yanzu ke damuna bai fice yanda
Siyama zata fita a hannun Jafar ba. Kinsan abun mamaki?
Wallahi har yanzu yaron nan Bash d'an gidan hakimi yana
nan akan bakansa na auren Siyama."
Hajiya Shema'u ta zaro ido
"Ke banason karya Hajiya Maimuna,ya akayi wannan ta
b'ullo? Daman sun dawo daga kasar wajen ne?"
Hajiya tayi shu'umin murmushi
"Sa wasa,Bashir sun dawo. Jiya na leka wajen bikin Nana
Hafsah kanwarshi naga matarsa Amal ina fitowa waje na
ganshi. Ganina ya taso ya gaisheni tare da yimin ruwan
nera,anan ne ya k'ara marairaicemin yana rokana akan
wallahi ko yanzu Siyama ta yarda ta amince dashi zai
aureta. Shi dai burinsa nayi yanda zanyi ta fito,koda zata ce
ya saki Amal to babu abunda zai hanashi. Ke sai lokacin na
hakikance lallai yaron nan ba karamin so yake yiwa yarinyar
nan ba. Dayake ita kuma yar iskar kanta ce ya mak'alewa
wannan matsiyacin nifa kaina duk ya k'ulle nemomin mafita
Hajiya Shema'u don batun da nake maki na amince d'ari
bisa d'ari zan yiwa Bashir wannan aikin shine dalilin da
d'azu naji alert na kud'i har dubu d'ari biyar a matsayin
somin tab'i. Kinga kuwa damuwa da tunani sun kamani
Hajiya Shema'u. Nifa daman rayuwar daula nafison
kowacce d'iyata tayi balle kuma shaleleta Siyama."
"Wai wasa kikeyi min haka?"
Hajiya taja tsaki
"Mene dalilina na yin wasa irin wannan? Ke har lambarta ya
nemi na bashi kuma na bashi saidai nace fa yayi taka
tsantsa da wannan matsiyacin mijin nata."
Hajiya Shema'u tayi wata iriyar dariyar jin dadi kafin ta
mikowa Hajiya hannu suka cafke. Ta dauki jakarta tana
mikewa
"Zo mu shiga daga ciki kedai akwai mafita."
Ba musu Hajiya tabi bayanta har kuryar d'akin Hajiyar.
Bayan sun zauna ne Hajiya Shema'u ta dubi Hajiya
"Mafitar shine mu samu Siyama da wannan zancen. Ki aika
mata dubu d'ari biyu asusunta na banki wannan shine
hanya ta farko da zamu soma shawo kanta. Kinsan dai
dolenta ta rikice da tambayarki dalilin turo mata wadannan
kud'ad'en masu yawa ko? Anan ne saiki nemi yi mata
bayani saidai bai kamata ki sanar da ita bukatar Bash ba
tun a farko,kawai dai kice kyauta ce yayi mata kinga zamu
barta cikin tunani ko?
*****37
Sauran aikin Rumaisa zaki d'ora akai tunda itama naga ta
tsotsa a nononmu babu abunda bazata iya aikata mana ba.
Abun yi dai kiyi kiranka Rumaisa yanzu ki nemi ganinta
koda ba yau tazo ba ki tabbatar dai kinyi mata bayani ki
sanya ta kwad'aitar da ita irin daular da zata shiga matukar
ta amince da kashe aurenta ta auri Bashir d'an hakimi."
Hajiya ta sauke ajiyar zuciya irin na wacce ta samu
mafita,tayi dariyar jin dad'i da farin ciki
"Kada kiso kiji yanda na samu sauki a zuciyata. Amma a
farko na kasa aiwatar da kowane irin tunani sai shirme da
tunane tunanen soma ziyartar bokaye."
Hajiya shema'u taja tsaki had'i da tab'e baki
"Bar wadannan yan iskan banda suci kud'inmu su kwanta
ba abunda suka iya sai karyace karyacen banza. Kin manta
ne da zan kori atika (kishiyarta) daga gidana wane irin
kashe kudade ne banyiba tun kafin shigowarta har
bayansa? Ba don nayi mata sharrin da Alhaji ya ganewa
idanunsa na ganin kwarto a d'akinta ba ai da tuni bai
sallamata ba. Don haka malama abunyi na kan gaba shine
mu zuge Siyama. Idan har ta hau ta zauna har tana
sauraron Bashir toh ko ita kadai zata iya yin abunda zatayi
ta fito daga gidan Jafar."
Hajiya tayi wani murmushi
"Hajiya shema'u,Siyama fa bata k'i ta mutu ba akan ta rabu
da Jafar. Tana masifar sonshi,anya hak'anmu..."
"Yaci ya gama Hajiya."
Hajiya shema'u ta katseta a hanzarce,kafin ta d'ora da
fad'in
"Don Allah kibar yin mugun baki mana,waye zai k'i naira?
Kedai kirawo Rumaisa kiyi yanda nace sannan kada ki
dauki lokaci baki yiwa Siyamar transfer na kud'ad'en ba."
Ba musu ta dauki wayarta ta kira Rumaisa ta nemi ganinta.
Rumaisa ta amsa
"Gobe zan shigo hajiya."
Daganan sukayi sallama...!
****
Washegari asabar da misalin karfe sha biyu da mintoci na
rana sai ga Rumaisa ta dira a gidansu.
Ta shiga saidai Hajiyar tana sashen Abbansu,wannan ya
sanyata cin burki a d'akin hajiyar gami da kwanciya saman
gadonta. Takai mintuna biyar kafin Hajiya ta shigo. Ganinta
a sanyaye ya sanya cike da mamaki Hajiya ta k'arasa
gareta,wannan yasa Rumaisa mikewa zaune
"Ke kuma lafiyarki na ganki wata iri?"
Rumaisa ta sauke ajiyar zuciya
"Bari hajiya,bakin ciki ne ya isheni Nura ya biyawa uwarsa
da kishiyarta kujerar makkah ban sani ba,sai jiya da
daddare da zasu tashi ne na tsinci labarin daga sama.
Raina ya baci,ace ko ni bai taba biyamin ba amma ya
biyawa wadannan munafukan? Kwanakin nan ban ganewa
lamuransa gaba d'aya ya soma juyamin baya fa."
Hajiya ta tab'e baki
"Kai Allah dai Ya kyauta,saiki k'ata cin d'amara ki kwato
yancinki."
"Ina naga kud'in yin aiki Hajiya?"
Wani murmushin mugunta Hajiya Maimuna tayi kafin tace
"Sha kuruminki Rumaisa,ko nawa ne zaki samu saidai kafin
aje ko'ina ki bud'e kunnuwanki ki saurareni."
Rumaisa wacce ta rud'e da farin cikin samun kud'in yin aiki
ta matso sosai tana sauraron jawaban Hajiyarta. Ta gaza
boye mamakinta,baki bud'e take kallon Hajiya
"Hajiya,yanzu bash don rashin zuciya yana nufin bai hakura
da Siyama ba?"
Hajiya tayi dariya
"Yo ina fa? Yana ganin 'yar kyakkyawa bayan ma haka ai so
ba k'arya bane ba Rumaisa. Kedai ki zage damtsenki kiyi
mana wannan aikin ina mai tabbatar maki kud'ad'en da
zamu samu ba kad'an bane ballantana ma idan ace Siyama
ta bada had'in kai ya kika hangomu?"
Suka sheke da dariyar farin ciki har suna tafi kamar ba 'yar
fari ba. A karshe Rumaisa tace
"Gaskiyane hajiyarmu,wannan abu mai sauki ne. Daman
munyi zata zo gidana akan wani maganin mallaka da zan
bata ta yiwa Jafar yanzu kam na fasa wannan auren ya
fiyemana rayuwar tsinancewa da talauci a gidan Jafar."
Hajiya tayi murmushi
"A'a toh,gwara dai ku dawo hanya. Abunda daman nake ta
kokarin ganar da ita kenan tun farko amma tak'i fahimta
yanzu sai ta yiwa kanta fad'a."
Sukayi dariya,Rumaisa bata yarda Abba ya ganta ba tabar
gidan zuwa nata.....!
Tana kwance tana kallon film lokacin karfe hudu na yamma
saidai ko girki bata da niyyar dora musu na rana balle akai
ga na dare. Shayi ta had'a ta sha abinta tayi nak. Faruk ma
shayin ta bashi.
Dauda ya kammala gyaran kuryar dakinta ya fito. Ta
dubeshi
"Tafi da kayan nan kicin saika tattara falon."
Ya amsa da toh,bayan fitarsa wayarta ta soma k'ara,ta
janyota tana mai k'arewa lambar kallo cike da mamaki,ita
dai kam bata tab'a ganin irin wannan lambar ba mai (zero)
sifili har guda hud'u a jere ba. Ta kasa dauka saboda tsoro
don ba yau ne ta soma jin labarin cewar ire iren lambobin
nan na kungiyar asiri bane. Wannan yasa har ta yanke bata
d'aga ba. Ta sauke ajiyar zuciya tana shirin maida wayar ta
ajiye ne wani kiran ya k'ara shigowa saidai wannan wata
lambar ce daban. Hankalinta ya kwanta da wannan lambar
don ba irin ta farko bace. Ta d'aga
"Hello."
"Hi My sweet."
Muryar data amsa mata ne ya sanyata mikewa tsaye cikin
gigita,ta dafa kirjinta dake bugu da sauri sauri.
"Bash? A ina ka samu lambata?"
Ta tambayeshi a mamakince gami da azamar lek'awa
tsakar gidan ta hanyar tagar d'akin.
Wani dariya yayi kafin yace
"Ba abune mai wuya ba a wajena,kinsan dai irin
mahaukacin son da nakeyi maki ko? My swee..."
"Dakata Bash,domin girman Allah kada ka k'ara gangancin
kiran wayata. Wallahi ina son mijina ka taimakeni kada ka
haddasa min fitina a rayuwar aurena."
Tana kaiwa karshen zancen taji karar mashin d'in Jafar
kasancewar angwanci yake ci baya dad'ewa ko a kasuwar.
Cikinta ya kad'a,lokacin Bash ya soma magana
"(Cool your mind) my sweet. Bakiyi mamakin yanda akayi
har yanzu na kasa cireki ba daga raina? Ki tausayamin
wannan karon ki amshi soyayyata kinji..."
Cikin fushi ta dakatar dashi
"(I'm warning you Bash!) Daga rana irinta yau kada ka k'ara
neman layina ko kuma na had'aka da mijina."
Jin motsin tahowa ya sanyata azamar kashe wayar gaba
d'ayanta ta jefa akan kujera,daidai lokacin Jafar ya karaso
cikin d'akin da sallama. Murmushin yak'e tayi tana mai
wayancewa da komawa ta zauna amma har lokacin
gabanta bai bar dukan uku uku ba.
"Lafiyarki kuwa? Da wa kike waya?"
Ta dubeshi a tsorace,ganin kallon da yake mata ya sanyata
rud'ewa,saidai ta dake ta wayance da muskutawa tana
fuskantar talabijin
"Waya kuma wace iri? Da wa zanyi waya? Karar tv dai kaji."
Ya jinjina kanshi duk da dai bai yarda ba saboda yaji
muryarta tana magana a fusace saidai baisan me take fad'i
ba. Bayason bincike wannan yasa ya share maganar.
"Ok,me kika girka ne?"
Ta daure fuska
"Kaina ke ciwo shiyasa banyi girki ba."
Cike da mamaki ya bud'e baki zaiyi magana sai ga Dauda
nan da tsintsiya ya shigo ciki. Ganinsa yayi shiru,
"Kai fita muna magana."
Sum sum Dauda ya fice daga d'akin,fuska a daure ya
dubeta
"Amma meyasa bakiyi mata magana ba ko ruwan shayi sai
ta d'ora maku ku sha? Haba Siyama,sai ku zauna da
yunwa?"

*****38
Ta dafe kai don alal hakika kan nata ya soma sarawa
dagaske. Ji takeyi Jafar duk ya takura mata,so takeyi yabar
d'akin ta nemo mafitan wannan matsalar dake son wargaza
rayuwar aurenta.
"Bakya jina ne?"
Ta ja karamin tsaki
"Don Allah ka rabu dani,nikam na sha shayi kaje ku nemi
abunda zakuci kaina ya dameni."
Ta mike tabar falon,yayi kwafa ya dauki Faruk dake wasa a
falon babu alamar tayi mishi wanka lura da yanda rigarsa
take da datti sannan tun na safe ne.
Siyama tayi makwas akan gadonta tana cike da tunane
tunane,a ina Bash ya samu lambarta ne? A saninta ko Nana
hafsah bata da lambarta toh waye ya bashi? Da azama ta
fito ta dauki wayar ta kunna,karar alert na shigowar sak'o
ya dauki hankalinta. Cikin gigita ta mike ganin anyo mata
transfer na kud'i har dubu d'ari biyu. Ta duba dakyau taga
daga lambar account din Hajiyarta ne. Hankalinta bai
kwanta ba saida ta danna mata kira........!
*****
"Ya akayi Siyama?"
Cikin rawar murya ta jefeta da tambaya
"Hajiya naga sak'o daga banki dake...."
Dariyarta ce ta katseta
"Kinyi mamaki ko autana? Naki ne mallakinki. Kyauta ce
daga d'an hakimi saboda yace bai nan akayi bikinki ya baki
wannan a matsayin gudunmuwarsa."
Siyama ta zaro ido,kwalla suka cika mata ido. A tsorace
tace
"Hajiya meyasa zakiyi haka? Akan wane dalili za'a karb'i
kud'insa? Yanzu..."
"Ke mahaukaciyar banza kiyimin shiru nace ko?!!! Wai ke
meyasa kodayaushe ana baki kina k'in karb'a? Meye laifi
idan yaron nan yayi maki kyauta?"
Ta hau sintiri a d'akin,ga fanka na juyawa saidai gumi da
hawaye sun gaza tsaya mata. Ta dafe kanta kafin ta yarfe
hannunta
"Bakisan waye Bash ba Hajiya,yana da naci kamar tsufa.
D'an akuya ne wallahi! Kirana yayi da zantukan banza
Hajiya! Ina ya samu lambata?!!"
Hajiya ta daka mata tsawa wacce ta gigita ta
"Idan kika k'ara zaginsa sai nayi mummunan furuci gareki!!
Wawuyar banza da wofi! Wallahi kika sake kika sanarwa
Jafar maganar kud'i ko wayar da yayi maki sai na sab'a
maki!"
Hajiya ta kashe wayar,wannan ya sanya Siyama rud'ewa
sosai,ta zube a kasan kafet ta soma risgar kuka. Wannan
wace irin masifa ce? Anya Hajiya tasan abunda takeyi
kuwa? Lallai ta yarda akan kud'i babu abunda Hajiya bazata
aikata ba koda ace ya sab'awa shari'a ne.
*****
Acan kuwa,Jafar ya kawo ruwan zafi suka had'a shayi
abinsu sukaci. Hadiyya dai sai mamaki takeyi,a kwanakin
nan taga abubuwa da yawa a wajen Siyama,ciki kuwa harda
shanyan undies dinta da taga Dauda yana yi mata. Bayan
lura da tayi kusan rabin hidindimun gidan shine mai daukar
nauyinsu. A yanzu kuwa jin da tayi Jafar yace kanta ne
yake ciwo ya sanyata kokwanto. Tasan Jafar bai samu
dawowa da rana ba jiya toh wannan ma duk ciwon kan ne
ya hanata girki? Ita kam ba don Jafar yana hanata ba da
tuni ta soma d'ora tukunyarta. Amma lallai yau da daddare
ita zatayi girkinta babu ruwanta da jiran Siyama.
"Tunanin me kikeyi?"
Jafar ya katseta,tayi azamar girgiza kanta
"Ko d'aya."
Ta wayance da mikewa ta fita da kofuna da cokulan da
suka b'ata. Saida ta wankesu tas ta shigo ta tattara inda
sukayi karinsu kafin daga bisani ta d'auki Faruk tayi hanyar
waje. Jafar wanda ke kishingid'e saman kujera yana
kallonta cikin tsananin burgewa da sha'awa yace
"Ina zaku gudu ku barni?"
Tayi murmushi ta dubeshi kad'an
"Wanka zamuyi gwara ka amso mana kaya."
Ya maida mata martanin murmushin yana mai cigaba da
jifanta da salon kallon nan dake rud'a tunaninta. Tayi
azamar dauke kanta ta fice zuwa band'akinsu
Ya lumshe ido yana mai jin wani dad'i yana ratsashi,yau
shine da wannan sa'ar? A kyautata mishi,a tsaftace
muhallinsa? Kai babu abunda zaice ga Ubangijinsa sai
hamdala. Ya gama biya mishi bukatarshi ta duniya,samun
mace irin Hadiyya a wannan rayuwar abu ne mai wahala.
Gashi wai har yau shine abokansa ke cewa yayi
k'iba,hakanan ma antinsa d'azu daya lek'a mata tayi ta
mamakin sauyawarsa. Hajjah kuwa banda albarka babu
abunda take sanyawa Hadiyya ko babu komai tana kula da
d'anta,ya samu nutsuwar zuciya.
Cikin nishad'i ya mike ya fito ya nufi d'akin Siyama. Tana
zaune cikin d'akinta tana kuka,saidai jin sallamar Jafar ya
sanyata mikewa da saurin fad'awa band'aki ta b'ame. Ya
karaso d'akin,a zatonta zai nemeta saidai ba hakan bane
don shima fushi yake da ita. Dakyar ya samo mahad'in
rigar daya zakulowa Faruk,sannan ya fice bai ko damu da
yasan halin da Siyama ke ciki ba. Abunda ya bawa kansa
shine dai ta zagaya bandaki. Saida ta daina jin motsinsa
sannan ta fito a gurguje ta leka ta tagar falonta. Daidai
lokacin Hadiyya ta fito rike da Faruk tayi mishi wanka ta
sanya,Jafar ya bita d'akin rike da kayan a hannunsa.
Ta saki labulen ta zauna gami da yin tagumi,hawayen bakin
ciki suka zubo mata. Wannan fa shine zafi biyu. Da me
zataji ne? Ta ina zata b'ullowa Bashir? Wallahi tana son
Jafar,batajin koda da sakan zata iya barinshi. Bata k'i
rayuwar jin dad'i ba saidai bazata iya kiyasta adadin kaunar
da take yiwa mijinta ba. Jafar fa na daban ne,duk macen
data sameshi ba shakka taji dad'inta. Har ta kammala bata
sami mafita ba,karshe ta bar abun a zuwan idan ta kaiwa
anti rumaisa ziyara gobe saita nema mata mafita..!
******
"Akan me? Me akeyi a gidan Antin da zaki fita?"
Cewar Jafar fuska a daure tamau,ji tayi kamar ta d'ora
hannu aka tayi kuka. Cikin marairaicewa
"Domin Allah ka barni naje Jafar,bata da lafiya yau kwanaki
uku kenan."
Ya tab'e baki ba don ya yarda da hakan ba saidai kawai
ganin damarsa yace
"Saikin dawo."
Ta sauke sassanyar ajiyar zuciya wanda har saida ya
kalleta,saita wayance ta hanyar yin murmushi
"Nagode."
Ya gyada kai daman ya sallameta da kudin cefane ya mike
cike da mamakin yanda a yau Siyama tayi sanyi, babu
wannan tsiwar ko rashin kunyar,a haka ya fice ya bar gidan.
*****39
Tafi minti uku rike da kanta bayan kammala
dogon bayanan anti rumaisa,ta rasa kalar tunanin
da zatayi. Banda innalillahi wa inna ilaihirraji'un
babu abunda take nanatawa a zuciyarta. Anti
rumaisa ta katseta ta hanyar dafa cinyarta
"Bud'e kunnuwanki ki saurareni kanwata,yanzu
soyayya ba shine rayuwar aure mai dadi ba. Idan
miji yana da kud'i toh babu sauran wani bayani.
Don haka ki kauda wani batun shirme na soyayya
a ranki, wallahi ina mai tabbatar maki matukar
kika yarda kika rabu da Jafar kika auri Bashir toh
hakikanin gaskiya kina da sa'a. Aikin
banza,wallahi da ina da babbar 'ya budurwa babu
abunda zai hana na sharewa Bashir hawaye na
aura mishi ita. Ke irinsu Bashir ba mazan yar wa
bane kinji ko? Shima don dai yana da naci kamar
kuturu amma Allah na tuba me zaiyi dake?
Malama ki saki jikinki babu abunda Bashir bazaiyi
maki ba ko menene shi. Bakiso ki ganmu muna
watayawa ne?"
Siyama da bakin ciki ke nukurkusa ta dubi Anti
rumaisa cikin tsabar takaicin maganganunta
"Wai anti kunsan menene so kuwa? Meyasa
kodayaushe kuke yunkurin rabani da Jafar?
Meyasa bakwa kaunar farin ciki na? Wallahi ni
kud'in bash baya gabana,ko a baya bai rufemin
ido ba ballantana kuma yanzu. Nikam kome
za'ayimin bazan rabu dashi ba saidai..."
Bakinta taji ta buge,anti cikin fushi da fad'a tace
"Toh wacce bata gaji arziki ba. Ai ke kam na lura
ko kina kwance aka kawo maki dukiya tashi
zakiyi ki gudu. Shashasha kawai!"
Siyama dai kuka takeyi,karshe anti ta koma
lallab'awa
"Haba kanwata,baki ganin dad'in da muke hango
maki ne? Zan baki lokaci nan zuwa sati kiyi
tunani sosai ki nutsu. Ga dai Jafar nan da kike
ikrarin kina sonshi son da bazaki iya rabuwa
dashi ba,gashinan ya k'ara aurensa ya share
lamuranki. Ke kuma bazaki iya cireshi daga
rayuwarki ba,ko wannan ya isa nuna maki cewar
ke kad'ai ke son Jafar bakya gabansa a yanzu.
Tunda yayi aure na tabbata idan kikayi nazari
zaki fahimci ya chanja maki. Allah dai Yasa ya
nemi ma wani hakkinsa a wajenki da kike wani
rawar jikin karb'ar girki yanzu."
Ta mike tayi d'akinta,Siyama ta zuba uban
tagumi tana mai nazarin jawaban antin....!
*******
Misalin takwas na dare ya tarasu a falon Siyama.
Saida ya soma da nasiha akan hakuri da
girmama junansu kafin ya gangaro batun girki. Ya
dubi Siyama
"Madam kwana nawa kika ganin ya dace ku
dungayi?"
Siyama ta yamutse fuska
"Kwana bibbiyu yayi."
Yayi murmushi,a ransa baiso hakan ba ya
tabbatar zai dunga kewar amaryarsa hakanan dai
don ba yanda zaiyi ya hakura
Ya dubi Hadiyya
"Hakan yayi maki?"
Tayi murmushi ta gyada kanta
"Komai antina ta yanke yayimin."
Tsakin siyama ya fisgi hankulansu,suka dubeta.
Ta kauda kanta zuciyarta cike fal da kishin
Hadiyya tamkar ta shak'ota takeji. Ga wani uban
kwalliya da taci, Siyama kuwa a yau banda hoda
ba abunda ta shafawa fuskarta don har lokacin
bata cikin nutsuwarta. Jafar ya girgiza kanshi
cike da takaicin wannan hali na tsaki da Siyama
take yawan yinsa.
Fuu ya mike ta shige d'aki ta barsu anan
zaune,ganin haka Hadiyya ta mike a sanyaye zata
fita.
"Muje na rakaki."
Suka fita tare,Siyama bakin ciki tamkar ya
kasheta. Tabbas ta soma amincewa Jafar ya
daina sonta. Bai damu da ita ba yanzun tamkar
babu wata soyayya data gifta tsakaninsu.
Hawaye suka taho mata,wayarta tayi k'ara
alamar shigowar sak'o. Ta dauko ta bud'e
"I wish to spend all the rest of my life with you.
Leave everything and come to me my sweet
angel,I promise to always keep you happy. I can't
stop myself from loving you. Please help me!
Save my life! From Bash."
Ta mike a firgice,ta karanta yafi sau biyar,ta
kama kanta
"Na shiga uku,wannan wace irin kaddara ce?"
Ta fad'a a fili,jin taku ya sanyata kashe wayar
gaba d'ayanta. Tayi azamar ajiyeta cikin dirowa
ta fito falon. Daidai lokacin Jafar ya shigo ya
dubeta cike da zargi
"Lafiya ke kuma? Me ya biyoki kika fito daga
d'akin kamar wata marar gaskiya?"
Ta basar ta hanyar harararsa da kauda kai
"Kace haka mana tunda ka tafi d'akin matarka
sai kaje can ka kwana ina ruwana."
Yayi murmushi sanin da yayi kishi ke damunta.
Ya rufe kofar sannan ya bita cikin d'akin bayan
ta kinkimi Faruk da yayi bacci saman kujera.
A daren Siyama bata iya runtsawa ba,bata damu
da yanda Jafar ya shareta ba bai nemi tayi mishi
komai ba,hankalinta ya karkata ga Bashir,ta rasa
ina zata sanya kanta. Tunani ya dabaibayeta,me
Bash ke nufi da ita? Wannan bala'in da me yayi
kama?
"Wai lafiyarki kalau kuwa Siyama?"
Ta d'an firgita domin kwata kwata batasan
idonsa biyu ba,ta wayance da juya mishi baya
"Ina ruwanka ne? Banjin baccin ne."
Ya juya bayansa
"Ai shikenan sai kiyita istigfari da salati."
Tana jinsa ta shareshi,ita kam batasan ma me ya
dace tayi ba,karshe sai tabi shawararsa wajen yin
abunda yace dakyar bacci ya d'auketa.
Washegari Jafar yana fita,Siyama ta dannawa
Bashir kira.
Yana zaune a bakin ruwa(swimming pool) anan
farfajiyar gidansa yana busar sigari yana fesar da
hayakin a sama. Wani irin sanyin dadi yakeji a
k'asan ransa,tabbas burinsa na mallakar abunda
ya jima yana muradi ya kusa cika. Karar da
wayarshi ta soma ya katseshi,ya d'ago a nutse
ya duba,murmushi ya saki kafin ya d'aga wayar.
"Hello my sweet lady."
Cikin bacin rai Siyama ta soma magana
"Bash ka fita hanyata,ka rabu da rayuwata don
Allah. Inason mijina,kada ka k'ara gangancin
kirana a waya. Kud'i kuwa yanzun nan zan fita
zan maido maka kayanka banaso! Bana
ra'ayinka! Just leave me alone please!!"
"Calm down My sweet,menene abun daukar zafi
haka? Naji zan fita a rayuwarki muddin zakiyimin
wani taimako guda d'aya!"
Da hanzari tace
"Fad'i ina sauraronka."
"Ki yarda ki fito na aureki."
"Naga alama jahilci yana d'awainiya dakai
Bash,ya kamata ka koma makaranta domin ka
koyo tarbiyya da ilimi irin na addinin musulinci.
Kaidai kam na kula bazaka taba daina akuyanci
ba. Toh ka sani cewar babu abunda zai rabani da
auren jafar sai mutuwa. Wallahi ko kafi kuda naci
ni Siyama nafi karfinka har abada!"

****40
Ta kashe wayar a fusace ta wurgata kan kujera.
Zaman dirshan tayi a tsakar falon,taja tsaki yafi
sau nawa. Yanzu shawarar wa zata nema ne?"
Nan da nan aminanta suka fad'o mata. Ta janyo
wayarta tayi kiran Fatima sanin da tayi duk
cikinsu ta fisu nutsuwa . Cikin rashin sa'a
wayar Fatima a kashe saboda fama da matsalar
rashin wuta da sukeyi a kwanakin nan,wannan
yasa ta nemi Shukra ba don ta so ba .
Ko ringing daya bata cika ba Shukra ta dauka.
"Ya akayi uwargidan Jafar,ko amaryar ta fara
gasaki?"
Shukra ta fad'a cikin wasa,Siyama ta rufe ido ta
bude
"Wannan da sauki akan matsalar dake tunkaroni
Shukra,ina bukatar taimakonki don Allah."
Nan ta zayyane mata halin da take ciki,shukra
hankalinta ya tashi.
"Subhanallahi,wannan wace irin masifa ce? Toh
ke kuwa ki chanja layinki mana idan yaso ki
maida mishi kud'insa. Abu na gaba kuma kada ki
sake ki dauki dukkan wasu shawarwari na Hajiya
ko anti rumaisa. Wannan abune daya shafi
rayuwarki. Kada kiyi wasa da hakkokin dake
kanki na addininki Siyama. Aure fa ba abun wasa
bane."
Shukra tayita bata shawarwari har ta
gamsu,karshe sukayi sallama.
******
Da gudu gudu Hadiyya ta shiga gidansu. Tana cin
karo da Mama ta rukunkumeta cikin
matsananciyar murna. Mama tana murmushin
farin ciki ta tureta
"Nikam zaki fad'ar dani."
Sallamar Jafar ta katse mama, mama tayi saurin
gyara zaman dankwalinta
"A'a ashe tare kuke shine kika barshi a waje?
Sannu da zuwa d'ana."
Jafar fuska a sake ya karasa yana mai durkusa a
ladabce ya gaida mama. Ta amsa itama cikin jin
dadin ganin yanda duk sukayi kyau. A karshe
bayan sun taba hira kad'an ya mike yace zai tafi
sai zuwa la'asar zai dawo daukarta. Ta mike tayi
mishi rakiya har zaure sannan ta dawo wajen
mamanta.....!
"Ya zamanki da Siyama,ina fatan dai babu wata
matsala ko?"
Hadiyya ta girgiza kanta
"Babu ko d'aya mama,saidai abu d'aya ne ke
tayarmin da hankalina."
Mama ta fuskanceta sosai
"Me kenan?"
Cikin damuwa Hadiyya ta d'an yamutsa fuskarta
"A sati biyun nan da nayi a gidan na kula anti
siyama tana da karancin tsafta ga son jiki.
Babban abunda ke damuna bai wuce yanda koda
na tsaftace tsakar gida da madafar girkinmu ba
toh wallahi mama sai ki rantse ba'ayi gyaran
komai ba muddin zata shiga tayi dahuwa toh ba
shakka sai komai ya lalace. Kuma fannin girki
ma..."
"Ya isa Ladi,kiyi hakuri domin Allah. Taje ta
k'araci kazantarta da rashin iya girkinta. Kedai ki
zage damtse wajen kula da mijinki shine
wajibinki. Koda zata b'ata sau goma,kiyi hakuri ki
gyara tunda a yau kukayi bak'o yazo yaga ko'ina
kaca kaca tkanta bazai kira Siyama kad'ai
kazama ba,kema baza'a cireki ciki ba. Saidai ma
ayi maku jam'u,a kiraku KAZAMAN GIDA."
Hadiyya ta jinjina kanta
"Hakane Mamana,Allah Ya barmin ke. Wallahi duk
sa'ilin da abu ya shigemin duhu matukar zan
nemi shawararki ko kuma ta Basma sai naji wani
sanyin dad'i."
Mama tayi murmushi ita kanta tana kaunar
d'iyarta sosai. Haka sukayita hira,suna cikin yi
Sarah itama ta shigo da yaranta maza su uku
kowannensu da kayan makaranta sai Najwa
itama yarinya mai shekaru goma ta shigo. Gaba
daya tare suke zuwa makaranta. Ihun murna suka
hau ganin Hadiyya amarya. Haka aka had'u
akayita hira har Jafar ya iso. Nan ma suka gaisa
da Sarah yake tambayarta kwana biyu
kasancewar yanzu mama ta chanja sana'a na yin
wainar siyarwa anan zauren gidanta,ita kuwa
Sarah mai mik'awa mutane. A haka suke rufawa
junansu asiri,Sarah kullum cikin fatan alheri da
addua takeyi ga Mama domin yanzu ta dauketa
matsayin uwarta tunda Sarah kwata kwata koda
zata girmi Hadiyya toh baifi da shekara d'aya ba.
A karshe dai sukayi sallama Hadiyya kamar tayi
kuka haka ta baro mamanta.
******
Har kawo wannan lokacin,Siyama bata bar samun
barazanar raba aurenta da Jafar ba daga Hajiya.
Ga anti rumaisa zuwanta wajen sau uku gidan da
nata kalar masifun. Gashi duk da ta chanja layin
wayarta bata tsira daga Bashir ba don tuni ya
samu lambarta na yanzun. A wannan lokacin
Siyama bata tantama cewar wajen Hajiya yake
samu. Gaba daya bata cikin nutsuwarta.
Watarana da magriba tana tsaye gefen titi tana
jiran abun hawa saidai abun bakin cikin ta gaza
samun wanda zai kaita can unguwarsu. Faruk
yana goye a bayanta yayi bacci,ga wani tashin
hankalin na hadari da iska mai karfi da akeyi. Ya
dubi hanyar layinsu Fatima,akwai nisa sosai
domin kuwa acan karshen layin suke kafin ta
koma ma wani aikin ne. Hankalinta a tashe tana
ji inama batazo sunan jaririn da Fatima ta haifa
ba yanzu gashinan ruwa yana neman sauka. Bata
ankara ba taga mota ta tsaya a gabanta. Tayi
duba ga motar,ba'a ganin wanda ke ciki tayi
azamar yin gaba tana jan tsaki. Yayi saurin tarar
gabanta. Gabanta ya bada dam! Saboda wanda
ta gani,yana sanye da bak'ar t-shirt sai wandon
jeans blue, ga wani d'an iskan aski a
kansa,hannunsa time da karan sigari ya yar ya
murjeshi da k'afa. Ya zuba mata ido yana
murmushi,fari ne dogo saidai siriri ne sosai bashi
da jiki.
Siyama wacce cida na ruwa ya k'ara rikirkitata
tayi azamar kauce masa zata wuce,yayi azamar
k'ara shan gabanta
"Har yaushe my sweet zata dunga gudu na? Ki
taimaka ko ba don ni ba ki shigo na kaiki kinga fa
an soma yayyafi. Please Siyama."
Ta bishi da wani malalacin kallo ta nunashi da
yatsa
"Wallahi Bash ina mai gargadinka ka fita a
harkata. Kai jahilin ina ne da baisan..."
Karfin da ruwan saman ya k'ara ne ya hanata
k'arasa jawabinta,yayi daidai da canyara kukan
Faruk dake nuni ruwa ya soma tab'ashi. Da sauri
Bash yace
"Oh no! Siyama please shiga mu tafi ko saboda
yaron nan!"
Dole tayi azamar shiga ta kunto Faruk daga
bayanta. Sanyin Ac ya ratsasu,da azama shima
ya shigo motar ya rufe. Hankalin Siyama ya
tashi,gaba daya ta rasa nutsuwarta. Tsoro da
fargaba suka mamayeta,kwallah ta cika idonta.
"Anya banyi kuskuren shiga motar Bash ba?"
Ta fad'i a ranta,daidai lokacin daya harba motar
titi yana wani murmushi.........!!!*****41
"Siyama!"
Ta runtse idonta saboda wata irin tsanarsa daya mamaye
zuciyarta. Ta juyo a fusace
"Look Bash,ban hau motarka ba domin ka jani da maganar
banza ba. Zaifi yi maka kyau ka kame bakinka."
Bashir yayi wata dariya irin ta 'yan duniya kafin ya dubeta
"Kiyi hakuri Siyama,saidai bazan fasa sanar maki abunda ke
raina ba. Siyama har yanzu da kuruciyarki,babu wanda zai
ganki yace kin haifi wannan bebin ba. Siyama ban taba son
Amal ba,hakimi yayimin auren huci haushi akan hanani
aurenki da Abbanki yayi ne. Ke kanki shaida ce akan babu
macen data tsaremin gabana saike. Amal batasan yanda
zata kula da miji ba ko kadan,a komai bata gwanance ba ke
na takaice maki......"
"Ya isa Bash! Na gaji da sauraron wadannan shirmen
zantukan da kakeyi! Ka tsaya na sauka bana bukatar
taimakonka."
Kafin ta kara magana wayarta tayi k'ara,a firgice ta zarota
daga (purse) d'inta,ta zaro ido ganin da tayi Jafar ne.
Bash ya dubi wayar kafin ya maida kansa ga titi yana
murmushi
"Ki d'aga mana,nasan rival dina ne ko?"
Ta harareshi kafin tace
"Don girman Allah kayi shiru."
Ya tabe baki kawai,ta d'aga murya na rawa.
"He..hel..lo."
"Siyama kina ina ne? Bakya ganin ruwan da akeyi?"
Ta had'iyi miyau ta saci kallon Bash,hankalinsa yana gareta
saidai idanuwansa suna ga titi. A sannu ta maida kanta ga
kallon hanya,sun kusa unguwarsu.
"Ganinan taxi na hau,ina nan tafe."
Dariyar da bash yayi ce ta sanyata zaro ido jikinta ya soma
kad'uwa,wannan yasa Jafar yin tsai yana sauraro.
Hadiyya tana gefenshi zaune tana zuba mishi abinci ta
tsaya cak tana duban Jafar a tsorace ganin yanda nan take
ya daure fuska,ya mike tsaye rike da waya a hannunshi.
Baya zaton zai taba mance mai muryar nan ko don bakar
wahalar daya sha akanshi a yayin neman aurensa na fari.
Cikin kakkausar murya yace
"Siyama muryar wa nakeji? Ki gayamin gaskiya kina ina?"
Cikin sa'a suka tsaya a danja,tayi azamar bud'e kofar ta fita
da sauri daga motar
"Gani a hanya,akwai fasinjoji ka bari na iso Jafar bansan
amsa waya a waje."
Tayi azamar kashe wayar ta tsallaka,lokacin yayyafi akeyi
ruwan ya ragu. Bash ya sauke gilashin motarsa kafin yakai
ga wani yunkuri tuni ya fad'a wata adaidaita ba tare data
fad'i takamaiman inda zatayi ba. Allah Ya bata sa'a tana
hawa aka basu hannu.
Ta dunga sauke ajiyar zuciya cike da tsabar rud'u,ta k'ara
kudundune Faruk cikin zaninsa saboda sanyin da gari yayi.
"Hajiya bansan fa inda kika nufa ba."
Ta waiga bayanta,ranta yayi sanyi ganin bash baya biye
dasu. Ta sanarwa direban unguwarsu,tayi sa'a nan hanyar
ya nufa. Wayarta ta hau k'ara,ta ja tsaki ganin Bash ne. Ta
kashe wayar gaba d'ayanta.
Acan kuwa Jafar ya rasa nutsuwarsa,wani azababben kishi
ke cin zuciyarsa na iyalinsa. Hadiyya ta ajiye (serving
spoon) dake hannunta tana kallonshi
"Lafiya kuwa? Fatan anti siyama suna lafiya?"
Ya gyada kansa,sai lokacin ya tuna bashi kadai bane a
d'akin. Ya kakalo murmushi
"Lafiya Deeyana,suna hanyar gida. Cigaba da zubamin."
Ta sauke ajiyar zuciya.a sanyaye ta cigaba da zuba mishi
sannan ta ajiye a gabanshi. Tare suka ci abinsu,hankalinsa
ya kasu gida biyu. Meke shirin faruwa? Meyasa yaji murya
irin ta Bash? Meya had'ashi da matarsa yanzu?
Siyama kuwa mai adaidaita yana tsayawa a kofar gidan,ta
soma laluben (purse) dinta
"Nawa ne kud'in..."
Sauran maganarta ta mak'ale sakamakon tashin hankalin
daya rufar mata. Babu (purse) dinta babu dalilinsa......!
"Hajiya dari zaki bani."
Ya maimaita a karo na biyu ganin da yayi kamar bata jishi
ba. Yayi daidai da fitowar Jafar daga gida. Wannan ya
sanya Siyama d'ago kanta tana dubanshi. Shima ita yake
kallo cike da zargi,tunda yaji k'arar tsayuwar mota ne yasa
ya fito don ganin wanda ke dauke da ita. Tayi azamar
fitowa ta karasa wajensa
"Kaga na yarda fos d'ina,don Allah sallameshi. Bari na
shiga ruwa yana tab'a Faruk."
Tayi wuf ta shige,ya k'arasa wajen mai adaidaita sahu ya
dubeshi
"Nawa ne kud'inka?"
"Dari ne."
Jafar yayi tsai yana dubanshi,
"Daga ina ja daukota?"
Mai adaidaita wanda tuni ya tayar da mashin d'insa yace
"Daga nan wajejan gadon k'aya,kaga zuwa nan rijiyar zaki
kuma ita kad'ai ai sai d'arin."
Jafar ya zura hannu aljihu ya dauko d'ari biyu ya mik'a
mishi,
"Bani chanji,amma wa kaga ya sauketa ne?"
Cikin gundura da wannan tambayoyin mai adaidaita sahun
ya mik'a mishi chanji
"Malam ta yaya zan sani ne? Anan junction na ganta ko?
Kawai ta fad'o adaidaita sahuna tace min rijiyar zaki zan
kaita."
Jafar yayi murmushin takaici
"Shikenan abokina kana iya tafiya nagode."
Da karfi ya ja ya tafi,Jafar ya juya ya koma ciki ya kulle. Kai
tsaye ya nufi d'akin Siyama. Tana zaune da daure kirji tana
cirewa Faruk kayan jikinsa da suka jik'e. Ya dubeta ta
dubeshi saidai zuciyarta na bugu da sauri da sauri.
"Kika cemin taxi kika shiga?"
Ta maida dubanta ga abunda takeyi tana mai hade gira
"Eh mana,anan gadon kaya na sauka na hau adaidaita sahu
saboda daman ragemin sukayi ganin ana ruwa kuma ba nan
suka nufo ba."
Ya jinjina kansa,
"A garin yaya kika yarda fos dinki?"
Ta soma yarfa hannu cikin jin zafi
"Don Allah ka rabu dani,ni kaina bansan inda ta fad'i ba."
Bayason zuciyarsa ta cika zarginta. Yaso ya tambayeta
akan muryar bash da yaso yaji saidai kuma yabar abun a
ransa. Bata kara yarda ta dago sun hada ido ba domin gani
takeyi kamar rashin gaskiyarta zai fito a zahiri. Tana jin
sadda ya juya ya fita daga d'akin. Kawai saita zuba uban
tagumi. Fatanta ya kasance a titi ta yarda fos d'inta ba a
motar Bashir ba. Ta kunna wayarta sak'o ya shigo.
Gabanta ya fad'i
"Kin manta (purse) dinki anan motata. Zuwa da safe zan
shigo na kawo maki my sweet. Hope kin isa gida lafiya?"
Cikinta ya bada wani sauti,ta runtse ido cikin tsabar bakin
ciki. Tayi azamar aika mishi sako
"Ka barshi banaso! Ka rufamin asiri ka fita daga rayuwata.
Dan iska kawai."
Ta aika mishi,nan take ya maido martani
"Hahaha! Sarkin tsoro. Shikenan amma tabbas ganinki a
yau ya k'ara kid'imani ya dace ki gaggauta samar mana
mafita."
Taja tsaki ta kashe wayar gaba d'ayanta. Wannan shine
babban tashin hankalin da Siyama bata tab'a cin karo da
irinsa ba tunda take a rayuwarta. Ga azalzalar da Hajiya
keyi mata,ga anti rumaisa. Abun bakin cikin daidai da
sauran yayyunta sun goyi bayan Hajiya,Hanif ne dai take
zargin baida masaniya akan halin da ake ciki.
******41
Hanif ne dai take zargin baida masaniya akan halin da ake
ciki.
***
Hajiya ta dubi aminiyarta
"Hajiya shema'u ya dace musan abunyi,wannan
kinibabbiyar yarinyar bazata taba taimakamana burinmu ya
cika ba. Dole ne sai mun hada da malamai."
Hajiya shemau cikin mamaki matuka tace
"A'a,wai anya kuwa Jafar haka yabar Siyama? A wannan
zamanin banga macen da za'a nuna mata arziki ba ta
gujeshi. Yanzu fisabilillahi da gaske ta mayar mishi da
kud'in nan?"
Hajiya tayi kwafa cikin fushi
"Bar yar iska,hanata nayi shine ta maidoshi asusuna. Ai
wallahi nikam na tsani zuri'ar Hajiya Binta. Gaba d'ayansu
matsiyata ne kuma matsafa. Banda tsafi,ya za'ayi Siyama
zata guji tarin arziki ta nanik'ewa matalauci? Hajiya
shema'u ki taimakeni da wannan aikin ki kaini wajen
kowane malami matukar bukata zata biya toh fa shikenan
zamu biyashi ko nawa ne."
Hajiya shemau ta jinjina kanta tana taunar cingam
"Kada ki samu damuwa yar uwa, komai zai daidaita. Yanzu
zanyi waya da Malam yahuza duk yanda mukayi zakijini."
Ran Hajiya yayi sanyi kad'an,
"Yauwa yar uwa,a rabasu. A sanya mata tsanar Jafar a
ranta. Soyayyar da take yi mishi ya koma kan Bashir."
Haka sukayita kulle kullen su kafin su rabu.
Sunyi magana da Malam inda yace zai musu aiki amma a
aikomishi kud'i ta asusunsa. Nan ya bayar da lambar
asusunsa na banki a karshe yayi musu alk'awarin zai musu
aiki.
*******
Misalin karfe tara na safe,Jafar yayi shirin kasuwa saidai
hankalinsa yana ga Hadiyya wacce gaba daya batajin dadi
tun jiya. Ya isa gareta ya janyota jikinsa,cikin muryar
tausayi yace
"Anya zan iya tafiya na barki a wannan yanayin Deeya?
Tashi ki shirya muje asibiti idan yaso daga nan sai na wuce
ke kuma ki dawo."
Ta kara kwanciya a kirjinsa tana kukan shagwaba
"A'a nidai Yaya j...."
"No Deeya,har zuwa yaushe ne zakiyita zama haka? Tun
jiya nake lallab'aki muje kin k'i yau dai dole ki shirya mu
tafi."
Ya soma kokarin cire mata kaya kafin ya kaudata ya bude
kwaba ya ciro mata doguwar rigar abaya. Ya taimaka mata
ta zura sannan suka fito yana rike da hannunta. Siyama ta
fito daga kicin ta gansu,wani kallo ta watsa musu batace
komai ba tayi hanyar d'aki.
"Zan kaita asibiti ne yanzu zamu dawo."
Kishi ya mamaye zuciyarta,kada dai cikine da ita? Ta tabe
baki ta juya zuwa d'akinta. Jafar ya girgiza kansa, Hadiyya
kam zuwa yanzu bata damun kanta da sai sun zauna lafiya
da Siyama tunda ta kula halinta ne bazata sauya ba. Bata
kaunarta batason ko kadan ta dunga shiga harkarta
wannan yasa ta watsar da ita.
Jafar ya rufe kofofin dakunan Hadiyyah sannan ya fidda
mashin d'insa yaja suka bar gida. Yana zaune cikin motarsa
yana hangensu,murmushi ya saki.Motarsa ya bud'e ya
fito,kai tsaye ya nufi cikin gidan.
****
Sun kai titi kenan Jafar ya laluba aljihunansa,
"Subhanallah,kinga garin sauri na mance wallet d'ina ko?"
Hadiyya cikin jin ciwo ta dubeshi
"Ai da sauki tunda bamuyi nisa ba. Ka koma ka dauko Yaya
j."
Ya juya kan mashin d'insa..........
Ta juya baya tana kokarin juye indomin data girka a faranti
babu zato taji hannuwa akan kugunta. Cikin tsabar firgita ta
juyo ta tsorata ainun da ganinsa har numfashinta yana
barazanar daukewa. Da karfin tsiya ta tureshi,bakinta yana
rawa tace
"Ba..sshhh....menene ya kawo ka gidana? Fitar min tun
banyi maka ihun b'arawo ba wallahi! Ka fita!!!"
Ko kusa bai gigita ba,ya kara marairaicewa
"Ki taimakeni Siyama. Wallahi na k'ara d'imautuwa da
bukatarki a tun lokacin da muka rabu wallahi ban k'ara
baccin kirki ba. Siyama save my life,ki bani abunda nakeso
I promise to...."
"Ka fitar min daga gidan aure! Kai dan..."
Bakinta ya kafe sa'ilin daya rungumota. Ta hau kiciniyar
kwacewa,daidai lokacin taji sallamar Jafar. Hankalinta yayi
mummunan tashi,shi kansa Bash sai yayi azamar sakinta.
Da gudu ta fito daga kicin d'in har tana firgita Jafar dake
kokarin bude kofar dakin Hadiyya. Haki takeyi kamar wacce
tayi tseran gudu,ga gumi da take fitarwa. Shima bash yayi
saurin sanyo kai yana haramar fita saidai ina! Tuni sukayi
ido hudu da Jafar. Ya dake iya dakewa yana shafar
sumarsa. Jafar ya dubi Siyama kafin ya dubi Bashir. Jikinsa
ya hau rawa,idanuwansa suka sauya launi. Cikin mugun
zafin nama ya shak'i wuyan Bashir,murya a d'age ya soma
magana
"Meya kawoka gidana don ubanka?!!! Me kake nema a
wajen matata? Daman kai kwartonta ne? Ka gayamin!!!"
Tuni Bashir ya soma kakari,siyama ta dora hannu akanta
tana ihun kuka. Da gudu Hadiyya ta shigo,tayi matukar
kaduwar ganin Jafar ya shak'i wuyan mutumin da bata taba
ganinshi ba. Nan tayi kan Jafar tana ihu
"Wayyo Allah,Yaya j ka sakeshi kada ka kasheshi. Wayyo
Allah!"
Duk iyakar yinta amma ina Jafar bai saki bash ba,tuni Bash
ya soma zaro idanuwa. Ganin babu sarki sai Allah tayi wuf
ta fita tana ihun neman taimakon jama'a. Nan aka shigo
gidan,wasu matasa uku sukayi nasarar janye Jafar dakyar.
Yana ihun fad'in
"Ku barni na kasheshi! Ku rabu dani nace!! Dan iskan karya!
Shege wanda baisan mutuncin aure ba!!"
Siyama ta shige dakinta ta rufe ruf sakamakon firgita da
tayi. Dakyar mutane suka janye Bash daga gidan,cikin
matukar jin kunya yabi layin ya shiga motarsa sai nunashi
akeyi ana gulmarsa. Matan cikin gida harda lek'e. A fusace
ya bar unguwar.
Hadiyya ta kori yaran da suka rage ta rufe gidan da mukulli
saboda masu tururuwar zuwa kallo. Jafar ya hau bugun
kofar Siyama yana kukan bakin ciki
"Kin cuceni Siyama! Ki fito ki tafi na sakeki bazan iya zama
da kwartuwa ba! Mai yawon bariki! Har cikin gidanki na
sunnah saikin kawo kwartonki.! Allah Ya isa tsakanina dake
Siyama! Na tsaneki! Ki fito tunda ba gidan ubanki bane.."
Hadiyya tayi azamar rufe mishi baki cikin matsanancin
kuka,Jafar baya cikin hayyacinsa. Ya buge hannunta yana
mai daka mata tsawa
"Ki rabu dani Deeya! Ki kyaleni na kori wannan 'yar iskar
daga gidana!"
Hadiyya tana kuka ta kara matsawa ta jashi
"Don Allah Yaya j kazo muje. Don Allah kabar yanke hukunci
cikin fushi."
Dakyar Jafar yabi Hadiyya zuwa d'akinta yana fad'a ji
yakeyi tamkar zai mutu don tsananin kishi da bakin cikin
Siyama.
"Da me na rageta Deeya?! Menene bana mata?!! Me wani
zai fini?!! Deeya mata macuta ne! Maha'inta ne!!!"
Hadiyya cike da matsanancin mamaki take kuka,amma
Siyama ta b'ata wayonta. Taji bata ganin girmanta.
*****
Siyama tunda Jafar yayi furucin saki gareta taji hawayenta
sun tsaya cak!
"YA KASHEMIN AURE!!!"
Itace kalmar da take ta nanatawa! Gaba daya ta kasa
katabus,Faruk sai kuka yakeyi saidai ko kusa hankalinta
baya tare da ita.......!****43
Saida Jafar ya fice daga gidan sannan Hadiyya ta isa ga
kofar Siyama ta hau bugu.
"Anti Siyama! Anti Siyama!!"
Siyama ta dawo hayyacinta daga dogon tunanin data shiga.
Sai lokacin taji kukan Faruk wanda shine dalilin daya sanya
Hadiyya kwankwasa mata. Siyama tayi azamar mikewa ta
lek'o ta tagar d'akin. Sukayi ido hud'u da Hadiyya. Cikin
dauriya daga ciwon kan da takeji ta cize lebbanta
"Ki bud'e Yaya j yabar gidan nan."
Siyama tayi azamar bude kofarta,ta janyo hannun Hadiyya
zuwa falon sannan ta rufe kofar gam saboda tsananin tsoro
da fargaba. Hadiyya ta dauki Faruk ta soma jijjigawa,Siyam
a ta zauna cikin tagumi sunkai mintuna uku a haka kafin
Siyama ta soma magana cikin sanyin murya.
"Wallahi Hadiyya ban aikata laifin da Jafar ke zargina ba
akai. Nasan kema ba lallai ki yarda da zancena ba amma
ga wannan ki karanta."
Siyama cikin hawaye ta janyo wayarta ta bud'o sak'onnin
da Bash ke aiko mata ta mikawa Hadiyya wayar. Hadiyya a
sanyaye ta karb'a ta soma karantawa d'aya bayan d'aya
yayinda hawaye suke kara ambaliya akan fuskarta. Ta
mik'awa Siyama faruk sannan tayi zaman dirshan akan
kafet ta zuba uban tagumi.......
"Nasan cewar nayi babban kuskure da ban sanar da Jafar
ba Hadiyya,saidai rashin sanin ta inda zan soma ne ya
hanani cewa komai gareshi. Jafar bai tambayeni dalilin
chanja layin wayata ba,da ace ya nemi sani watakila a
lokacin na iya sanar mishi wannan bibiyata da Bash
yakeyi."
Siyama ta d'an tsagaita da maganarta tana mai share
hawaye,Hadiyya wacce ta jingina kanta jikin kujera saboda
sarawar da yakeyi ga zazzab'in dake jikinta. Tayi shiru tana
sauraron Siyama. Nan Siyama ta fayyace mata tun lokacin
da Bash ke bibiyarta har zuwa yau d'innan,saidai bata
sanar da ita da sanya hannun mahaifiyarta ba ko yayarta.
Saida ta gama sannan ta share hawayenta
"Nayi imanin Allah zai min sakayya tsakanina da bash. Na
barwa Allah komai."
"Kiyi hakuri anti siyama,Allah bazai bar bash ba zai maki
sakayya. Gaskiya ne baki kyauta ba da tun farko baki sanar
da Yaya j ba. Na tabbata zai fahimceki,yanzun ma lokaci
bai kure ba anti Siyama. Idan Yaya j ya dawo ki nemi
gafararshi kiyi mishi bayani wannan sak'onnin ma sun
isheki shaida. Allah Yana tare da duk mai gaskiya. Ki yiwa
Yaya j uzuri yanzu,yana cike da bacin rai da kishi ne. Duk
abunda ya fad'a cikin fushi ne,duk da bansan takamaiman
abunda ya faru ba amma ina da tabbacin yaya j abun kona
mishi rai yayi."
Siyama tayi murmushi mai ciwo tana girgiza kanta saidai
batace komai ba,karshe dai Hadiyya ta mike ta nufi dakinta.
Allah Ya taimaketa tana da maganin ciwon kai ta dauka ta
sha. Asibitin da ba'aje ba kenan,ta jawo wayarta tana kiran
layukan jafar saidai duk a kashe suke. Hankalinta ya tashi
ga azababben zazzabin da takeji,ga kuma tausayin anti
siyama sannan rashin sanin inda mijinta yake. Haka ta
kwanta ta kudundune cikin bargo tun tana gwada kiran
wayarsa har dai batasan sa'ilin da bacci ya dauketa ba
saboda zafin ciwon da jikinta keyi.
Ta yafa mayafinta bayan ta goye Faruk,tana hawaye ta
tsayar da idanuwanta akan hotunansu na aurenta da Jafar
wanda suke manne har uku a bangon falon. Hawayenta ya
k'aru,Allah kad'ai ne zai shaideta akan son da take yiwa
mijinta,yau gashinan ta rabu dashi bisa sharrin da
shaidanin nan yayi gareta.
Ta goge hawayenta ta fita daga gidan. Kanta yana kasa
saboda tsabagen kunyar yanda mutane suke nunota suna
surutai duk da batasan me suke fad'i ba amma nan da nan
ta tsargu. Da sauri saurinta har tana tuntub'e tabar
layin,bataci wuyar samun adaidaita sahu ba. Ko cinikin kirki
bata tsaya sunyi ba ya shige,kuka sosai takeyi har suka isa
unguwarsu. Tayi ta kwatanta mishi gidansu har bakin kofa
ya kaita.
Gabanta ya hau bugu ganin Abba zaune yana karatun jarida
anan kofar gidan. Ya tsaya yana dubanta harda cire gilashin
idanunsa,ji tayi kamar ta saki fitsari......!
Ta dauke idonta daga gareshi tayi azamar biyan mai
adaidaita sahu yabar wajen. Gari yayi luf luf babu rana
tamkar lokacin ba karfe sha daya na safe ba. Ya kasance
asabar.
Kanta a kasa tazo ta gaban Abba zata wuce,a sanyaye ta
durkusa ta gaisheshi. Abba ya amsa har lokacin bai bar
kallonta da mamaki ba. Ya rufe jaridar hannunshi
"Ke kuma lafiya na ganki a hargitse hakanan?"
Ta kakalo murmushi
"Lafiya Abba."
Ya jinjina kanshi yayi shiru,can kuma ya tabe baki kadan
"Allah Ya sauwake toh,shige ciki."
Ta mike tayi ciki,sai lokacin ya lura da kayan jikinta. T-shirt
ne sai zanin data d'aura ga mayafi marar kauri. Mamaki ya
rufeshi,tabbas Siyama ba lafiya take ba,daman yayi
mamakin fitowarta da wuri haka. Maganar Alhaji ce ta
katseshi
"Yaya mu tafi ko?"
Abba ya mike yana ajiyar zuciya,daman daurin aure zasuje.
Suka hau mota sukayi gaba.
*****
Hajiya tana sashen Abba acan Siyama ta isketa. Kallo d'aya
ta yiwa Siyama taji sanyi a ranta
"Ke kuma lafiyarki kuwa? Wannan wace irin shiga ce? Kodai
bakyajin dadi ne?"
Siyama wacce kiris take jira,kawai saita zube a k'asa ta
fashe da kuka.
"Ke! Ki gayamin me Jafar d'in yayi maki ne? Kukan nan na
menene?"
Cikin sheshsheka Siyama tace
"Ya sakeni Hajiya,Bash ya kashemin aurena."
"Alhamdulillah."
Hajiya ta fad'i a ranta,a fili kuwa taja tsaki
"Toh menene abun kuka? Shi kadai yake namiji ne? Kedai
wallahi kina da matsala babba ma a rayuwa,menene ciki
don kin rabu da tsiya? Ai wannan abune na farin ciki.
Daman nasha sanar dake baki kamaci Jafar ba,yau
gashinan keda kika amince dashi ga abunda yayi maki.
Daman kiris yake jira kiyi mishi laifin da baikai ya kawo ba
ya koraki gidanku. Tunda dai a yanzu ya auri wata ai dole
ne ya wulakantaki. Ki share hawayenki ki watsar da
batunshi,bari uban naki ya dawo saina sanar mishi."
Da sauri sauri Siyama ta mike tabar d'akin zuwa falon
hajiya sakamakon jin da tayi zuciyarta bazata iya daukar
wadannan kalaman na hajiyarta ba. Bakin ciki ya turnuke
zuciyarta,tabbas batasan a matan ma me zata kirawo
hajiyarta ba,abun nata kuma yayi yawa sai du'a'i. Ta lura bil
hakki dagaske takeyi bata bakin cikin mutuwar aurenta da
Jafar. Wannan wace irin uwa ce da zata iya zab'ar abun
duniya akan farin cikin 'yarta? Haka Siyama tayi ta tunane
tunane har dai daga karshe ta mike domin gabatar da nafila
don kaiwa Ubangiji kukanta.
*******
Haris ya zubawa Jafar ido wanda ya dafe kansa da
hannuwansa yana mai cike da tunani. Sai zufa yake
had'awa. Ganin haka ya tsiyaya mishi ruwan sanyin daya
kawo mishi
"Karb'i kasha Jafar."
Ba musu ya karb'a ya shanye ruwan tas yayinda sanyin ke
ratsa zuciyarsa. Sunfi minituna uku saidai Jafar bashi da
niyyar cewa komai har Haris ya gaji yace
"Wai Jafar menene ya faru? Tunda kazo bakayimin furucin
kalma koda guda d'aya bane wanda zai fahimtar dani
matsalarka ba,ka daure ka kwantar da hankalinka ka
samarwa kanka nutsuwa Jafar. Meya faru?"
Ya d'ago kod'ad'd'un idanuwansa ya dubeshi cikin
kakkausar murya yace
"Na saki Siyama."
Haris ya zaro ido a tsorace
"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Kasan abunda kake fadi
kuwa Jafar?"
Jafar ya dauke dubansa daga kallon Haris,yayi murmushi
mai k'ona zuciya
"Babu k'arya Haris,na saketa."
Haris cikin fad'a yace
"For what reason Jafar?!!! Me tayi maka? Bata da
magabatana da bazaka kai k'ararta ba? Baka gudun
abunda mutane zasu ce akan wannan d'anyen aikin da
kayi?"
Jafar a fusace ya dubeshi
"Kabar saurin yankewa mutum hukunci batare daka saurari
uzurinsa ba! Siyama yaudarata takeyi,kwarto ta kawomin
har gidana....
******44
"Kwarto fa kace?!!! Anya Siyama zata aikata wannan laifin?"
Jafar ya girgiza kanshi
"Daman ba lallai ka yarda ba sai idan kaji wanda na tarar a
gidan. Ba kowa bane illa bash."
Haris yayi tsai yana duban Jafar a mamakince, yana
nanata sunan a ransa. Tabbas yasan waye bash. Tsohon
saurayin Siyama ne wanda akan shi Hajiya ta tsani auren
Jafar da Siyama. Akanshi ne kuma akayita rikice rikice.
Saidai anya zai amince Siyama ce ta kawoshi gidan?"
Ya girgiza kai cikin shakku
"A yaya ka tarar dasu?"
Jafar ya labarta masa komai. Haris yayi murmushin takaici
"Ka bani mamaki daka iya yankewa matarka hukunci babu
wani kwakkwaran bincike Jafar. Ya kamata ka nutsu ka
bincika gaskiyan al'amari. Ka zaunar da Siyama ka
tambayeta menene.."
"Kaga Haris, bash bazai san hanyar gidana ba sai ta
wajenta hakanan bash bazai iya shigomin gidana ba saida
izninta. Kada kaso kaga yanda suka rud'e da tsabar
kad'uwa a ganina da sukayi. Gaba daya basu so hakan ba.
Saidai Allah Yayi niyyar tona musu asiri ne kawai. Hum,ashe
wannan ne dalilin da yasa bata nemana a matsayinta na
mijinta? Bata bani hakkina aduk lokacin dana nema? Daman
tana da wanda ta ajiye a gefe take yiwa biyayya? Ni kuma
ta daukeni shashashanta a gefe? No haris, duk da
matsanancin son da nake yiwa Siyama na hakura da ita
Haris. Bazan iya cigaba da zama da ita. Na jima ina hakuri
da ita kai kanka ka sani kuma ba don komai ba sai saboda
son da nakeyi mata. Amma yanzu kam na hakura."
Haris ya kula Jafar kishi ke damunshi bazai fahimci komai
ba yanzu. Can kuma kamar wanda aka tsikara ya mike
"Oh kaga na manta fa ashe deeya batajin dadi zan kaita
asibiti,shikenan sai munyi waya."
Ya kama hanyar fita Haris ya dakatar dashi
"Jafar."
Wannan yasa ya juyo
"Kayi tunani sannan inaso ka bincika al'amarin nan. Idan da
hali ka boyewa su Abba maganar ka rufa mata asiri ko ba
don halinta ba."
Jafar ya gyada kansa
"Zanyi amfani da shawararka,nagode."
Daganan sukayi sallama.
*******
Shi kuwa Bash bayan fitowarsa daga gidan Jafar. Yana
sharara mahaukacin gudu na jin zafin cin mutuncin da Jafar
yayi mishi har bai ankara da babban motar data sanyo kai
ba kawai sai jin sautin k'arar buguwa mutane sukayi. Saiga
motar Bash a karkashin babbar motar nan. Nan mutane
suka fasa salati. Mata masu raunin zuciya a wajen tuni sun
soma fidda kwallar tausayin ganin yanda mai rai ya koma.
Bash yayi kaca kaca dashi,kafarsa d'aya ta fita, ga kayan
cikinsa a waje. Ko shurawa baiyi ba a wajen nan. Take
anan akayi kokarin janyeshi. Mai motar cikin ikon Ubangiji
babu abunda ya sameshi saidai na gefenshi daya samu
raunuka a goshi saboda buguwar da sukayi bata wasa ba.
Dakyar aka iya janye babban motar. Yan sanda suka laluba
cikin motar duk da ta talitse har Allah Ya basu ikon fiddo
wani id card dake motar. Anan fa sukayi gaggawar tafiya
dashi kamfanin da yake aiki bayan sunbi kwatancen dake
jikin idcard din
Acan kuwa sukayi nasarar samun babban yayansa Nabil.
Yayi matukar kaduwar ganin yanda kaninsa ya koma har
kuka saida yayi. Dakyar suka lallab'ashi ya tashi suka nufi
gidansu Bash.
Jimawa kadan labarin mutuwarsa har a rediyo. Hankalin
kowa a gidan hakimi ya tashi. Bakajin komai sai koke koke.
Amal sumanta yakai uku saboda ba karamin so take yiwa
mijinta ba duk da irin cin kashin da yakeyi gareta.
Rayuwar kenan! Shiyasa mutum ya shuka nagari don
baisan ranar mutuwarsa ba!!!!!
******
"Meke faruwa ne Siyama?"
Siyama dake durkushe gaban mahaifinta ta kasa cewa
komai sai kuka. Hajiya tayi wuf tace
"Ai ga irinta nan,shiyasa tun farko banso auren nan ba
saboda rashin mutuncin yaron nan. Yanzu gashinan ya
sako mana ita bayan daya auri wacce yakeso."
Cikin mamaki abba ya dubeta sannan ya dubi Siyama
"Sakinki yayi? Me kikayi mishi?"
"Yo me..."
"Hajiya maimuna rufemin baki! Tashi ki fita! Bake na
tambaya ba!"
Tsawar da yayi ya rud'asu gaba daya,sum sum Hajiya ta
mike a fusace tabar falon. Ya maido dubansa ga
Siyama....!
In sha Allah yau zamu kammala...IN SHA ALLAH!!!!
Ya maida dubansa ga Siyama bayan fitar Hajiya.
"Ke nake sauraro. Menene ya hadaku da mijinki har ya
fusatashi ya yanke wannan hukunci?"
😪Siyama kanta a k'asa ta kasa cewa komai. Tsoro
ne ya mamayeta. Toh wai me zata cewa Abban ma? Bayan
ta riga tasan ko za'a yanka naman jikinta da wuk'a bazata
iya furtawa Abba komai dangane da lamarinta da Bash ba.
"Da alamu dai baki da gaskiya Siyama. Saidai ki
sani,matukar na gane kece mai laifi ba shakka hukuncinki
mai tsauri ne tunda kin nuna baki da tawakkali. Kin kasa
tsaida hankalinki ki zauna da abokiyar zamanki lafiya ko?
Shikenan tafi zanji komai daga bakin Jafar d'in."
Ta mike tana kuka mai karfi ta fice. Lokacin data shiga
falon Hajiya kukanta ne ya tsaya cak ganin yanda Hajiyar
ke doka salati hannunta d'aya rike da waya d'ayan kuwa
rike da kanta. Wannan ne yayi dalilin daukewar kukanta sai
faman numfarfashi,ido a waje take duban Hajiya cikin jan
k'afa ta k'arasa gareta.
"Menene ya faru Hajiya?"
Ai kawai saita yarda wayar ta hau dukan siyama iyakar
karfinta tana kuka.
"Shegiya kawai,kin kashemin d'an 'yar uwata! Kedai wallahi
ina mai takaicin haihuwarki Siyama. Wallahi.."
"Maimuna!!"
A firgice tabar dukan Siyama ta dubeshi,Siyama wacce take
ihun kuka wanda a dalilin hakan ne ta jawo hankalin Abban
nata zuwa falon. Ya karasa shigowa ciki
"Menene haka wai? Meya faru? Akan wane dalili zaki
dokarmin d'iyata?!!"
Cikin kuka hajiya tace
"Akan soyayyarta gashinan ya mutu yabar duniyar."
Wani irin faduwar gaba ya dirarwa Siyama. Ta zaro ido tana
dafe kirji. Bash ya mutu?!!! Allahu Akbar. Ai saita kara
fashewa da kuka,lallai Allah abun tsoro ne.
Abba yayi salati gami da yi mishi addu'ar samun rahmar
Allah. Ya dubi Hajiya cike da takaici
"Shine akace maki Siyama ce ta kasheshi? Kedai bansan
lokacin da zaki dawo hankalinki ba. Ke kuma tashi kiyi d'aki
muddin ta kika k'ara dukanta zan dauki mataki. Maganinki
kenan kin kaso aurenki yanzu wace riba kika samarwa
kanki a gidan? Kadan kika soma gani."
Abba ya fada sannan ya fita a fusace. Hajiya tayi zaman
dirshan tana zage zage da ihun kuka kafin ta mike ta koma
d'akinta.
******
Jafar akan hanyar zuwa gidansu bayan ya mik'a Hadiyya
asibiti ya dawo an sanar musu tana dauke da juna biyu.
Farin ciki ya danne masa kaso hamsin na bakin cikin da
Siyama ta d'urma mishi a jiya da safe. Duk yanda Hadiyya
taso tayi mishi zancen siyamar ma ya gujewa hakan,ya
gargadeta akan kada ta kuskura tayi mishi maganar baya
bukatarta.
Gabansa ya fad'i da ya iske Abba a sashen Alhajinsa. Ya
daure ya k'arasa cikin falon yana ji inama sashen Hajja ya
soma nufa,kila ya kaucewa tambayoyin Abban Siyama. Ya
gaishesu a ladabce,Alhaji ya daure fuska murtuk kamar bai
tab'a dariya ba wannan yasa Jafar shan jinin jikinsa.
"Baba yaushe ka soma yanke hukunci ba tare..."
"Ya isa Rilwanu,wannan magana ce tsakanin nida d'ana."
Abba ne ya katse alhaji daya soma magana,kafin ya maida
dubansa ga Jafar yana murmushi irin na manya*****45
"Jafar menene ya had'aka da matarka har ka yanke mata
wannan hukuncin?"
Cikin jin nauyi Jafar yayi k'asa da kanshi,har abada bazai
taba iya sanarwa su Abba abunda ya faru ba. Bayason
tozarta Siyama.
"Jafar yi magana mana."
Ya rikice ya rasa mafita,nan take kuma ya chanja laifin
nata. Zuwa ga halayenta daya tsana wanda ya nuna sune
silar daukar matakin.
Nan ya kwararo musu halin kazanta da rashin ganin
girmansa da Siyama keyi. Ya kammala jawabinsa harda
k'ararta daya kawo wajen anti.
Ba zato Alhaji ya daukeshi da mari,
"Kaga d'an iskan yaro nan,ace don ka raina mutane saboda
wannan d'an laifin da bai taka kara....."
"Rilwanu ban hanaka magana bane?"
Alhaji yana huci ya koma ya zauna,Abba wanda ya gama
tunzura da wannan d'abi'un na Siyama ya dubi Jafar
"Amma jafar meya hana kazo ka sanarmin? Wannan ai
shiririta ne. Kana zaune da mace tana yin abunda taga
dama gareka amma ka kasa magana? Sai kace ta d'aure
maka bakinka?"
Abba yayi ta fada cikin tsananin bakin ciki,Jafar yasha jinin
jikinsa. Wannan inda ace Abba zaiji ainahin abunda ya
janyo sakin ya zaiji ne?
Karshe Abba ya umarci Jafar da tafiya,Alhaji yayi saurin
katseshi
"Bafa zai bar nan wurin ba sai ya mayarda matarsa."
Abba ya harareshi kafin ya k'ara kallon Jafar
"Tafi Jafar."
Sai bayan fitar Jafar, Abba suka tattauna magana da Alhaji
wanda yasa zuciyar alhajin yin sanyi.
*****
A fusace Abba ya shiga gidansa.
"Maimuna! Maimuna!! Siyama!!"
Da gudu gudu suka fito. Abba baiyi wata wata ba ya
kwashe Siyama da mari wanda tsananin gigita saida ta
zube k'asa. Zuwa yanzu hawayenta sun gaji da zuba sai
kukan zuci. Abba ya nuna Siyama
"Wannan yarinyar shaidaniyar kanta ce ashe ban sani ba?
Tarbiyyar dana baki kenan? Ashe zaki iya koyi da jahilan
mata a harkar aurenki? Tabbas Maimuna kin cuceni kwarai
da har kika bari na mik'a Siyama gidan aure bata iya komai
ba a fannin kula da miji. Yanzu da ace Jafar bare ne da tuni
auren nan ya jima da mutuwa. Toh wallahi sai na hukuntaki
daidai da laifinki."
Tun daga ranar Abba ya sallami mata yan aiki a cewarsa ya
basu hutun watanni uku. Hankalin Siyama ya tashi sa'ilin
da Abba ya sanar da ita rankatakaf aikin gidan nan ya koma
hannunta. Ya k'ara fa cewa
"Wallahi na iske kuskure daga ko'ina saina ci mutuncinki a
gidan nan!"
Fuu! Ya fice yana bar musu fuka fukin babbar rigarsa dake
tashi a sama.
*********
Jafar jin labarin mutuwar Bash a wajen Hajja ya kad'ashi.
Ya rike kai yana jinjina al'amarin,tabbas hatsarin ya afku
bayan barinsa daga gidansa. Lallai mutum ba komai bane
sai fatan cikawa da imani kawai.
"Ya dai na ganka haka?"
"Dole ki ganshi haka tunda ya aikata abunda yayi niyya bisa
son zuciyarsa."
Hajja ta dubi Alhaji wanda ya shigo cikin rashin fahimta
"Menene ya faru?"
Alhaji ya zayyane mata halin da ake ciki. Shiru tayi kafin
tayi salati.
"Babana ya akayi ka aikata wannan d'anyen aikin? Meyasa
baka sanarmin ba?"
Jafar dai shiru yayi,Alhaji yayi kwafa
"Ina zai sanar damu? Ai bamu isa dashi bane."
Jin haka Jafar ya soma basu hakuri har da durkusawa
k'asa.
"Ai baba na fad'a maka abunda zaisa na yafe maka kawai
shine ka janye sakin nan ba idan kuwa ba haka ba wallahi
babu ni...."
"Alhaji kayimin afuwa domin Allah,maida auren Siyama
tashin hankaline agareni. Ku fahimceni..."
"Toh shikenan! Naji,tunda ka zab'i rabuwarka dani kaje.
Kada na k'ara ganin keyarka a gidana!!"
Jafar da Hajja suka dubeshi a razane,shakka babu da
gaske yake. Wannan yasa Jafar ya daure yace
"Shikenan na janye sakin,na maidata. Allah Ya huci
zuciyarku."
Yana kaiwa nan ya fice da saurinsa yana jin tamkar ya
kashe kansa don bakin cikin mayarda Siyama da aka
sanyashi yayi.
Tun daga lokacin rayuwa ta chanjawa Jafar. Baida wani
babbar matsalar data sha kanshi irin na aurensa da Siyama
da Alhaji ke matsa mishi akan ta komo d'akinta. Saida Abba
ya bud'ewa Alhaji wuta yace ya barshi sai nan da wata uku
zata koma d'akinta sannan ne Alhaji ya daina cewa komai
akan maganar.
Yana tsaye yana sharce gashin kansa da (comb) yana
kallon matarsa ta madubi sai turo baki takeyi ita a lallai tana
fushi. Murmushi yayi ya ajiye ya karasa wajenta. Tayi
azamar kauda fuskarta. Ya sanya hannunsa a hab'anta ya
juyo da ita, tayi saurin rufe idonta ita ala dole bazata
kalleshi ba
Jafar yayi dariya
"Oh kallon nawa ma baza'ayi ba? Shikenan nayi niyyar nace
maki ki shirya muje na saukeki amma tunda hakane.."
Da sauri ta rukunkumeshi tana dariya
"A'a kayi hakuri Yaya j zan kalleka har ma abunda yafi
kallon zan aikata maka in har zanje kamun Basma."
Ya janyeta yayi mata wani irin kallo ta kauda kanta tana
murmushi
"A'a ban yarda ba,kince zaki iya kallona menene abun
d'auke kai? Kinsan ina burin ganin ranar da zakiyi ta kallona
har tsawon kamar minti uku ma."
Tayi kokarin mikewa ya janyota cinyarsa
"Ai ba haka mukayi dake ba yar budurwata. Saikin kalleni
ko kuma ki..."
"Nayi me? Ni inagaa shi zaifi min sauki fad'amin."
Ya tallafo fuskarta yayi mata rad'a a kunne. Tayi wuf ta hau
zille zille suna dariya
"Aa Yaya j,barni na saka kayana kaga lokaci fa yana
tafiya."
Dakyar Jafar ya bar Hadiyya. Ta shirya tsaf kai idan ja
ganta bakace tana dauke da d'an mutum a cikinta ba. Wani
ma sai yayi mata kallon wacce bata da aure. Ta yafa
mayafi wadatacce ta sanya komatsanta a 'yar jakar hannu
sannan ta fito ta kulle kofar. Anan d'an soron gidan ya
iskeshi yana goge mashin d'insa. Ko kallonta baiyi ba ya
cigaba wai a dole fushi yakeyi. Ta danne dariyar dake cinta.
Ta karasa ta rungumoshi ta baya, tana jin sanda ya sauke
ajiyar zuciya. Cikin lankwasar fa murya tace
"Haba mijina,mahad'in rayuwata kasan fa komai da nakeyi
duk saboda kai ne. Yanzu idan ba yau asabar ba sai lahadi
fa gareni na hutu. Kaima shaida ne tunda na koma karatuna
komai na rayuwa ya chanjamin amma haka nake kokari
saboda son da nake yiwa karatun. Bikin Basma fa?"
Ya juyo ya sumbaci goshinta yana murmushi
"Na huce ai deeyana. Saidai kwalliyar nan tayi yawa. Ina
fatan ba haka kike yinta ba kije makarantar?"
Tayi murmushi
"Ni kuma a suwa da zan tsallake umarnin mai house?"
Ya jinjina kai sannan ya fita da mashin d'in...
*****46
Wajen hud'u na yamma an soma sha'anin biki,Basma an
fito anyi shar. Hadiyya ma sai binta akeyi da kallo cike da
sha'awar yanda tayi kyau ta chanja. Suna zaune suna hira
da Mamanta inda mama ke tambayarta ko Siyama ta dawo.
Hadiyya tace batasan ma halin da suke ciki ba amma
kwarai har a zuciya tana son dawowarta. Mama ta jinjina
kanta
"Ai da tausayi. Allah Yasa ya maidota."
"Amin dai,na lura bayason nayi mishi maganar ma kwata
kwata."
Mama zatayi magana wata budurwa 'yar makociyarta tazo
"Maman Hadiyya wai kinyi bak'i daga nijar suna nan tsaye a
kofar gidanki tare da Kawu nuhu shine yace nazo..."
Kafin takai karshe Hadiyya da mama sun mike a razane. Da
azama mama ta zura takalmanta tayi gaba. Hadiyya wuf ta
fad'a d'aki ta dauki mayafinta jiki yana rawa tayi saurin bin
bayan mama wacce tayi mata nisa. Tana kaiwa daidai
kofar gidan,taga mamanta ta runtuma a guje ta fad'a jikin
wani mutum dogo fari tas kana ganinshi kasan bafulatani
ne. Kuka sosai ta sanya, shima kukan yakeyi yana fad'in
"Allah Sarki Inno ashe da rabon muga juna?"
Ita kanta Hadiyya kukan farin ciki takeyi tana k'are musu
kallo. Su hud'u ne,maza uku sai mace d'aya. Kana ganinsu
kasan jinin mamanta ne saboda dukkansu suna d'iban
kama da ita. Dakyar aka shiga ciki aka zauna. Nan aka
kara gaisawa. Mama ta rasa inda zata sanya ranta don
dadi. Sai bayan an nutsu,dogon nan da mama tayi kira da
Hamma ya soma magana.
"Munsha wuya sosai kafin mu gane inda kake Inno. Baffa
tana shan kwanshe ba lafiya ita ta tilasta akan lallai ko
nawa zamuyi asararsu sai mun nemo mata inda kake. Toh
da farko Surajo muka soma nemowa dakyar muka samu
kwatanshen gidanta. Ashe tayi k'aura daga birnin Tawa ta
koma Arlit da zama. Karka so kaga wuyar da munkashi
Inno. Karshe dai munka isa munyi sa'ar ganota. Ita ta bamu
labarin mutuwar Muntari munyi kuka aradun Allah. Karshe
ta bamu adireshin inda kake a nijeriya. Koda munkazo kano
munka bawa wata a tasha ya karanta mana abunda ita
Surajo ta rubuta mana a takarda sai ta gane unguwar itace
tayi mana alfarma daman direba ce ta kawomu har nan
gidan wanga dan uwan na muntari. Anan munka taho nan
gidanka."
Mama tana kukam farin ciki saida hankalinta ya tashi da
taji mahaifinta ba lafiya. Nan ta rikice tace su wuce
yanzu,Kawu nuhu ya dakatar da ita
"Tafiya yanzu bazai yiwu ba Hajiya,baki ganin sun kwaso
gajiya? A bari zuwa gobe sai ayi tafiyar. Bari zan wuce gida
zansa a kawo musu abinci."
Mama tayi godiya bayan tafiyarsa suka juye yare zuwa
fillanci sai hirar yan uwa akeyi. Hadiyya kallon mamanta
takeyi tana mai jin wani dadi a ranta yau kukan dare ya
k'are tunda an samu biyan bukata sai godiyar Allah. Suna
hirarsi taga suna kallota. Mama tayi dariya tana gayamusu
diyarta ce ita kadai gareta tayi aure ma. Hamma ya mik'a
mata hannu
"Yakinan yarona."
Hadiyya na murmushi ta mika hannunta ta zauna a gefensa
tana gaishesu. Hamma ya dafa kanta
"Kayi hakuri kaji? Bakasanmu ba. Ka yafemuna."
Saiga hawaye a fuskarsa. Mama ta dakewa zuciyarta,
"Hadiyya,hamma shine babban yayana a wajen mamanmu.
Wannan da kike gani ta nuna d'an tsamurmurin bak'i,d'an
kanin baffa nane sunansa Haladu. Wancan kuma,(ta nuna
gajeran cikinsu) baffanmu d'aya dashi sunansa Saminou.
Itama wannan sunanta Amina muna ce mata Amindago.
D'iyar yayan Baffana ce. Hadiyya sai kallonsu takeyi cike da
kauna. Babu mai jin Hausa cikinsu sai Hamma da surajo.
Ganin suna hira itama hadiyya ta shiga daki ta kira Jafar ta
sanar dashi abunda ke faruwa. Yaji dadi sosai ya tayasu
murna yace zai biyo anjima. Kan kace me,yan uwan
mahaifin hadiyya sun cika gidan kowanne da d'an
kwanonsa na abinci. Basma ma bayan gama kamunta ta
kira Hadiyya taji tana ina sai take sanar mata nan da nan ta
suka taho da 'yan gidansu harma da wasu yan uwanta da
sukazo biki. Gidan Mama ya cika. Sarah sai hidimar aiki
takeyi ita kanta ta taya mama murna. Surajo sai binta
yakeyi da kallo har ya kasa hakura cikin fulatanci ya
tambayi mama ko wacece.
Nan tayi mishi bayani ai kuwa yace yaga matar aure a
Kano. Mamaki ya kama yan uwan saida suka gane da
gaske yakeyi sannan mama tayi murmushi cikin yaren
Hausa ta yiwa sarah maganar. Ta kara da cewa
"Na tabbata babu wanda zai barki ki tafi nijar aure."
"Haba me zai hana mama? Ai nikam bani da yan uwan da
suka fiku. Wallahi ina kaunarku fiye dasu tunda suka kasa
taimakona a halin da nake ciki. Ai babu inda bazan iya zuwa
ba saidai zanyi shawara da kakata naji abunda zatace."
"Yauwa Saratu,ko idan mun dawo ne ko kuma ta waya saiki
sanar dani."
Sarah taji dadi sosai don har fita tayi suka d'anyi hira.
Shima surajo matarsa sun rabu saboda takura masa da
takeyi. Tabarshi da 'ya'yansa shida.
Jafar kuwa harda iyayensa yazo,itama anti habiba jin da
tayi washegari zasu tafi tazo. Kowa ya taya mama farin ciki
karshe har hadiyya suka tattara suka tafi.
*******
Duk wanda zaiga Siyama sai ya tausayawa rayuwarta.
Gaba d'aya bazakace itace wannan Siyamar ba kyakkyawa
kodayaushe cikin wahala take a gidan. Tayi bak'i ta lalace
tamkar ba gidan ubanta ba. Ko yanzu ta kammala aiki Abba
ya dawo yaga sashensa bai gyaru ba yanzu zai kamata ya
lafta sannan ya sanyata ta k'ara yi. Hajiya bata magana
kasancewar sau d'aya ta gwada yin magana ya kusan
dukanta sannan ya tsawatar akan kada ta sake tasa mishi
baki a lamarinsa da d'iyarsa. Siyama bata damu sosai da
abunda Abba keyi mata ba. Sai lokacin ta soma fahimtar
kuskuren data tafka a gidan Jafar. Tausayi da matsanan
son mijinta ya shigeta. Tana ji inama ya maidata ta
gwammace tayi aikin da take kad'an da batason yi na
gyaran gidanta akan wannan na gidan. Ko babu komai acan
bata wanki. Amma anan gashi har nata dana hajiyarta da
faruk ita keda alhakin yinsa. A wata biyu tuni ya kware a
kowane aiki. Har ta saba,ga wani uban ladabi da ta koya
kullum ta tashi saita durkusa ta gaishe da hajiyarta abunda
koda wasa batayi a baya. Ga Abba kuwa,yafi kowa jin dadin
wannan chanji na Siyama. Kullum idan ta kammala zaka
tsinceta zaune tana karatun alkur'ani tana yi tana hawaye
da jin takaicin wannan sakin da Bash ya janyo mata. A gefe
daya ba wanda ta tsana yanzu kamar hajiyarta da rumaisa
wadanda sun bada nasu kwamashon wajen lalacewar
aurenta. Wata rana da yammaci anti rumaisa tazo saidai
bata iske hajiyarsu ba ta d'an fita. Kasancewar Lahadi
Abba yana gidan,ta zauna ta soma bawa Siyama labarin
abunda ke damunta akan mijinta wanda a yanzu ya juya
mata baya aure zaiyi bata ko kalleta ba balle ta tofa ta
cigaba da linke kayan shanyar data wanke,Faruk yana
gefenta yana wasa abunda. Har hakan ya bawa anti
rumaisa mamaki. Ta dubeta
"Siyama ni kika share haka?"
Siyama ta dubeta tayi murmushin takaici
"Me zance anti rumaisa? Laifine idan Yaya nura yayi aure?
Ki godewa Allah tunda bai rabaki da gidansa ba kamar ya
da kuka janyomin mutuwar aure."
Idanunta suka cika da kwalla
"Kun cuceni anti. Ina zaune gidan mijina kun tayarmin da
hankali kun rabani da aurena mutuncina. Kuna tunanin Allah
bazaimin sakayya ba? Kuna zaton zaku cigaba da rayuwar
farin ciki bayan kun kassara nawa rayuwar?"
Siyama tayi murmushi mai ciwo kafin ta k'ara cewa komai
tuni Anti ta rufeta da duka. Bata damu data kare kanta
ba,saidai ganin da tayi ta samu Faruk ya runtuma ihu
wanda ya janyo hankalin Abba yasa Siyama mikewa ta
janye d'anta tana kuka. Abba ya shigo sosai fuskarsa daure
wannan yasa anti rumaisa nutsuwa. Ya dubi Siyama
"Menene ya had'aku?"
Daidai lokacin Hajiya wacce ta dawo daga unguwa ta
shigo,Siyama wacce ta gama kaiwa bango tana kuka mai
karfi tace
"Wallahi yau zan tona duk abunda ya faru. Abba inaso yau
ku bani damar magana. A kirawo Yaya jafar😝(
Sabon salo) yau sai kowa yaji warin rub'abb'an kwan nan.
Abba abunda Yaya jafar yace maka shine ya had'amu
wallahi ba shi bane ya janyo sakin wani lamarin ne daban
saidai bance wannan d'in ma bana aikatawa ba. (Kazanta).
Abba ka yafemin,don Allah ka bani damar magana."*****46
Wajen hud'u na yamma an soma sha'anin biki,Basma an
fito anyi shar. Hadiyya ma sai binta akeyi da kallo cike da
sha'awar yanda tayi kyau ta chanja. Suna zaune suna hira
da Mamanta inda mama ke tambayarta ko Siyama ta dawo.
Hadiyya tace batasan ma halin da suke ciki ba amma
kwarai har a zuciya tana son dawowarta. Mama ta jinjina
kanta
"Ai da tausayi. Allah Yasa ya maidota."
"Amin dai,na lura bayason nayi mishi maganar ma kwata
kwata."
Mama zatayi magana wata budurwa 'yar makociyarta tazo
"Maman Hadiyya wai kinyi bak'i daga nijar suna nan tsaye a
kofar gidanki tare da Kawu nuhu shine yace nazo..."
Kafin takai karshe Hadiyya da mama sun mike a razane. Da
azama mama ta zura takalmanta tayi gaba. Hadiyya wuf ta
fad'a d'aki ta dauki mayafinta jiki yana rawa tayi saurin bin
bayan mama wacce tayi mata nisa. Tana kaiwa daidai
kofar gidan,taga mamanta ta runtuma a guje ta fad'a jikin
wani mutum dogo fari tas kana ganinshi kasan bafulatani
ne. Kuka sosai ta sanya, shima kukan yakeyi yana fad'in
"Allah Sarki Inno ashe da rabon muga juna?"
Ita kanta Hadiyya kukan farin ciki takeyi tana k'are musu
kallo. Su hud'u ne,maza uku sai mace d'aya. Kana ganinsu
kasan jinin mamanta ne saboda dukkansu suna d'iban
kama da ita. Dakyar aka shiga ciki aka zauna. Nan aka
kara gaisawa. Mama ta rasa inda zata sanya ranta don
dadi. Sai bayan an nutsu,dogon nan da mama tayi kira da
Hamma ya soma magana.
"Munsha wuya sosai kafin mu gane inda kake Inno. Baffa
tana shan kwanshe ba lafiya ita ta tilasta akan lallai ko
nawa zamuyi asararsu sai mun nemo mata inda kake. Toh
da farko Surajo muka soma nemowa dakyar muka samu
kwatanshen gidanta. Ashe tayi k'aura daga birnin Tawa ta
koma Arlit da zama. Karka so kaga wuyar da munkashi
Inno. Karshe dai munka isa munyi sa'ar ganota. Ita ta bamu
labarin mutuwar Muntari munyi kuka aradun Allah. Karshe
ta bamu adireshin inda kake a nijeriya. Koda munkazo kano
munka bawa wata a tasha ya karanta mana abunda ita
Surajo ta rubuta mana a takarda sai ta gane unguwar itace
tayi mana alfarma daman direba ce ta kawomu har nan
gidan wanga dan uwan na muntari. Anan munka taho nan
gidanka."
Mama tana kukam farin ciki saida hankalinta ya tashi da
taji mahaifinta ba lafiya. Nan ta rikice tace su wuce
yanzu,Kawu nuhu ya dakatar da ita
"Tafiya yanzu bazai yiwu ba Hajiya,baki ganin sun kwaso
gajiya? A bari zuwa gobe sai ayi tafiyar. Bari zan wuce gida
zansa a kawo musu abinci."
Mama tayi godiya bayan tafiyarsa suka juye yare zuwa
fillanci sai hirar yan uwa akeyi. Hadiyya kallon mamanta
takeyi tana mai jin wani dadi a ranta yau kukan dare ya
k'are tunda an samu biyan bukata sai godiyar Allah. Suna
hirarsi taga suna kallota. Mama tayi dariya tana gayamusu
diyarta ce ita kadai gareta tayi aure ma. Hamma ya mik'a
mata hannu
"Yakinan yarona."
Hadiyya na murmushi ta mika hannunta ta zauna a gefensa
tana gaishesu. Hamma ya dafa kanta
"Kayi hakuri kaji? Bakasanmu ba. Ka yafemuna."
Saiga hawaye a fuskarsa. Mama ta dakewa zuciyarta,
"Hadiyya,hamma shine babban yayana a wajen mamanmu.
Wannan da kike gani ta nuna d'an tsamurmurin bak'i,d'an
kanin baffa nane sunansa Haladu. Wancan kuma,(ta nuna
gajeran cikinsu) baffanmu d'aya dashi sunansa Saminou.
Itama wannan sunanta Amina muna ce mata Amindago.
D'iyar yayan Baffana ce. Hadiyya sai kallonsu takeyi cike da
kauna. Babu mai jin Hausa cikinsu sai Hamma da surajo.
Ganin suna hira itama hadiyya ta shiga daki ta kira Jafar ta
sanar dashi abunda ke faruwa. Yaji dadi sosai ya tayasu
murna yace zai biyo anjima. Kan kace me,yan uwan
mahaifin hadiyya sun cika gidan kowanne da d'an
kwanonsa na abinci. Basma ma bayan gama kamunta ta
kira Hadiyya taji tana ina sai take sanar mata nan da nan ta
suka taho da 'yan gidansu harma da wasu yan uwanta da
sukazo biki. Gidan Mama ya cika. Sarah sai hidimar aiki
takeyi ita kanta ta taya mama murna. Surajo sai binta
yakeyi da kallo har ya kasa hakura cikin fulatanci ya
tambayi mama ko wacece.
Nan tayi mishi bayani ai kuwa yace yaga matar aure a
Kano. Mamaki ya kama yan uwan saida suka gane da
gaske yakeyi sannan mama tayi murmushi cikin yaren
Hausa ta yiwa sarah maganar. Ta kara da cewa
"Na tabbata babu wanda zai barki ki tafi nijar aure."
"Haba me zai hana mama? Ai nikam bani da yan uwan da
suka fiku. Wallahi ina kaunarku fiye dasu tunda suka kasa
taimakona a halin da nake ciki. Ai babu inda bazan iya zuwa
ba saidai zanyi shawara da kakata naji abunda zatace."
"Yauwa Saratu,ko idan mun dawo ne ko kuma ta waya saiki
sanar dani."
Sarah taji dadi sosai don har fita tayi suka d'anyi hira.
Shima surajo matarsa sun rabu saboda takura masa da
takeyi. Tabarshi da 'ya'yansa shida.
Jafar kuwa harda iyayensa yazo,itama anti habiba jin da
tayi washegari zasu tafi tazo. Kowa ya taya mama farin ciki
karshe har hadiyya suka tattara suka tafi.
*******
Duk wanda zaiga Siyama sai ya tausayawa rayuwarta.
Gaba d'aya bazakace itace wannan Siyamar ba kyakkyawa
kodayaushe cikin wahala take a gidan. Tayi bak'i ta lalace
tamkar ba gidan ubanta ba. Ko yanzu ta kammala aiki Abba
ya dawo yaga sashensa bai gyaru ba yanzu zai kamata ya
lafta sannan ya sanyata ta k'ara yi. Hajiya bata magana
kasancewar sau d'aya ta gwada yin magana ya kusan
dukanta sannan ya tsawatar akan kada ta sake tasa mishi
baki a lamarinsa da d'iyarsa. Siyama bata damu sosai da
abunda Abba keyi mata ba. Sai lokacin ta soma fahimtar
kuskuren data tafka a gidan Jafar. Tausayi da matsanan
son mijinta ya shigeta. Tana ji inama ya maidata ta
gwammace tayi aikin da take kad'an da batason yi na
gyaran gidanta akan wannan na gidan. Ko babu komai acan
bata wanki. Amma anan gashi har nata dana hajiyarta da
faruk ita keda alhakin yinsa. A wata biyu tuni ya kware a
kowane aiki. Har ta saba,ga wani uban ladabi da ta koya
kullum ta tashi saita durkusa ta gaishe da hajiyarta abunda
koda wasa batayi a baya. Ga Abba kuwa,yafi kowa jin dadin
wannan chanji na Siyama. Kullum idan ta kammala zaka
tsinceta zaune tana karatun alkur'ani tana yi tana hawaye
da jin takaicin wannan sakin da Bash ya janyo mata. A gefe
daya ba wanda ta tsana yanzu kamar hajiyarta da rumaisa
wadanda sun bada nasu kwamashon wajen lalacewar
aurenta. Wata rana da yammaci anti rumaisa tazo saidai
bata iske hajiyarsu ba ta d'an fita. Kasancewar Lahadi
Abba yana gidan,ta zauna ta soma bawa Siyama labarin
abunda ke damunta akan mijinta wanda a yanzu ya juya
mata baya aure zaiyi bata ko kalleta ba balle ta tofa ta
cigaba da linke kayan shanyar data wanke,Faruk yana
gefenta yana wasa abunda. Har hakan ya bawa anti
rumaisa mamaki. Ta dubeta
"Siyama ni kika share haka?"
Siyama ta dubeta tayi murmushin takaici
"Me zance anti rumaisa? Laifine idan Yaya nura yayi aure?
Ki godewa Allah tunda bai rabaki da gidansa ba kamar ya
da kuka janyomin mutuwar aure."
Idanunta suka cika da kwalla
"Kun cuceni anti. Ina zaune gidan mijina kun tayarmin da
hankali kun rabani da aurena mutuncina. Kuna tunanin Allah
bazaimin sakayya ba? Kuna zaton zaku cigaba da rayuwar
farin ciki bayan kun kassara nawa rayuwar?"
Siyama tayi murmushi mai ciwo kafin ta k'ara cewa komai
tuni Anti ta rufeta da duka. Bata damu data kare kanta
ba,saidai ganin da tayi ta samu Faruk ya runtuma ihu
wanda ya janyo hankalin Abba yasa Siyama mikewa ta
janye d'anta tana kuka. Abba ya shigo sosai fuskarsa daure
wannan yasa anti rumaisa nutsuwa. Ya dubi Siyama
"Menene ya had'aku?"
Daidai lokacin Hajiya wacce ta dawo daga unguwa ta
shigo,Siyama wacce ta gama kaiwa bango tana kuka mai
karfi tace
"Wallahi yau zan tona duk abunda ya faru. Abba inaso yau
ku bani damar magana. A kirawo Yaya jafar😝(
Sabon salo) yau sai kowa yaji warin rub'abb'an kwan nan.
Abba abunda Yaya jafar yace maka shine ya had'amu
wallahi ba shi bane ya janyo sakin wani lamarin ne daban
saidai bance wannan d'in ma bana aikatawa ba. (Kazanta).
Abba ka yafemin,don Allah ka bani damar magana."
Kazamar Gida*****47
Hajiya ta yarda jakar hannunta hankalinta ya tashi ta zaro
ido tana gumi tana duban Siyama. Rumaisa ji tayi kamar ta
saki fitsari a tsaye,cikinta sai kad'awa yakeyi
Abba cike da mamaki yake duban Siyama,tsananin
tausayinta ya kamashi ya d'agota tsaye
"Tashi Siyama,na baki dama. Bayan magriba zamu had'u
kowa da kowa ayi maganar. Ke kuma ki zauna kada kibar
gidan nan sai an gama."
Rumaisa ta hau rawar murya
"Abba baice nakai dare ba ai
"
Ya watsa mata wani kallo kafin ya jinjina kanshi
"Shikenan zanyi kiran Nuran na gayamishi ni nace ki zauna
zamuyi magana."
Hajiya ta dafe kirji
"Yar iskar yarinya me kike nufi?"
Jin wannan furucin yasa suka san ta shigo. Siyama
hankalinta ya tashi,ta sanarwa Abba bazata iya zama
wajensu ba. Yace ta dauki yaronta ta yafo mayafi ta
biyoshi. Yana tsaye ta dauko mayafi ta ciccibi yaronta suka
fita,jajayen idanun Hajiya yana kanta tamkar ta shak'ota
takeji. Gidansu Jafar ya kaita wajen Hajja sannan ya nufi
sashen Alhaji ya sanar dashi anjima bayan magrib yanason
ganinsu. Daga nan ya bugawa jafar yace yazo shima da
iyalinsa..
Hajiya ta kasa zaune ta kasa tsaye,ta dubi Rumaisa
"Siyama yar kutumar uba ce,(sry) me take nufi? Asiri zata
tonamin? Na shiga uku ni Maimuna."
Kawai sai tayi zaman yan bori a kasa ta rushe da kuka. Anti
rumaisa ma kukan takeyi na danasanin abunda ta aikata,ta
mike da sauri
"Wallahi bazan zauna ba tafiya zanyi."
Daga haka tayi hanyar fita saidai me? Abba ya kulle kofar
gidansa gam saboda yasan halinsu. Dole ta koma ciki tana
fad'a
"Duk kece Ummul aba'isin shigarmu wannan masifa Hajiya.
Da ace munyi hakuri da lamarin auren nan na Siyama an
nema mata maganin mallaka da duk haka bata faru ba
yanzu gashinan ba tsuntsu ba tarko."
Hajiya ta soma balbaleta da fad'a
"Kyace haka mana tunda kin gama lashe kud'ad'en da
yaron nan ya aika maki. Abun kunyar ai bani kadai ya shafa
ba."
Haka sukayita maganganu wannan ta yab'awa
wannan,wannan ta maida martani babu zancen ganin
girma.
*****
Jafar yayi mamakin jin kiran da Abba keyi mishi. Duk da
haka dai yayi kiran Hadiyya yace ta shirya gashinan tafe
zasu fita. Itama dai cikin mamakin ta shirya tana jiransa
koda yazo kawai wucewa sukayi.
*******
MISALIN BAKWAI NA DARE......
"Ke muke sauraro Siyama."
Wannan yasa Jafar satar kallon inda take cike da mamakin
yanda ta kod'e ta chanja. Tabbas alhakin abunda tayimishi
ne ya maisheta haka. Hadiyya ta tausayawa Siyama
matuka ganin yanda gaba daya tayi duhu ta rame sai kace
wacce ba gaban iyayenta take ba koda dai gidan miji yafi
amma lalacewarta tamkar wacce ke a hannun kishiyar uwa.
Ta k'ara rungumar Faruk wanda tun zuwanta ya mak'ale
mata ita kanta tayi kewar yaron. Kowa ya baza kunne yana
sauraron abunda Siyama zata fad'a. Hajiya da rumaisa
gumi suke had'awa,Yaya hanif ma yana zaune cike da
mamaki domin shi d'in baisan dalilin taron ba yazo ne
domin gaida Abbansa akace shima ya samu wuri ya zauna.
Siyama ta soma magana cikin ruwan hawaye. Tiryan tiryan
ta basu labarin abunda ya faru tun daga kiran da Bash yayi
mata da kuma kud'i da uzzurawar dasu Hajiya suka yiwa
rayuwarta akan lallai saita kashe aurenta ta auri Bash
saboda yana da kud'i. Bata boye komai ba ciki kuwa harda
motar Bash data shiga bisa larura.
Salati kawai kakeji da kuka. Abba jikinsa har rawa yakeyi.
Jafar saida yaji hankalinsa ya tashi,ya kad'u sosai da jin
gaskiyar abunda ya faru. Nadama mai tsanani na abunda ya
aikatawa Siyama ya rufeshi,inama yabi shawarar Haris da
Hadiyya yayi bincike a baya. Tsananin tausayin Siyama ya
kamashi. Abba ya kaiwa Rumaisa duka a hanci sai ga jini
yana fitowa. Hajiya tana ihun kuka tace
"Oh ni Maimuna yau Allah Ya hadani da shegiyar yarinya.
Wannan sharrin ki rasa wacce zakiyiwa sai ni?"
Siyama na hawaye bata saurareta ba ta ciro wayarta ta
mik'awa Abbanta.
"Abba ga sakonnin da muke musayarsu ciki kuwa harda na
kud'in da hajiya ta aikomin tace daga Bash ne."
Ta juya ga Hajiya
"Hajiya ke uwata ce, ina sonki. Ina iyakar kokari wajen yin
biyayya agareki saidai baki taba bani shawara na gari ba a
komai na rayuwata. Kodayaushe burinki ki rabani da farin
cikina. Gashi a yanzu kinyi nasara,saidai hajiya ki sani
alhakina bazai barki ki runtsa ba. Allah zai sakamin abunda
kika aikata ga rayuwata. Yaya jafar ka gafarceni,wallahi
ban taba sha'awar aikata zina ba. Ni ba mazinaciya bace,
kaddara ce ta afkamin. Don Allah ku gafartamin."
Siyama ke maganar tana kuka sosai,ta bawa kowa tausayi
musamman ma Jafar wanda boyayyen soyayyar nan nata
dake boye a k'asan zuciyarsa ya dawo sabo fil. Ji yakeyi
inama yana da damar da zai rungumeta ya rarrasheta.
Abba ya dubeta
"Baki da laifi Siyama,saidai kinyi kuskure da tun a farkon
lamarin baki sanar da ko mijinki ba idan mu bazaki iya
sanar damu ba. Na tabbata da abun baikai ga haka ba,koda
dai haka Allah Ya kaddara zai faru toh dole ya kasance."
Ya maida dubansa ga Hajiya
"Hajiya Maimuna ya mukayi dake a baya akan auren Jafar
da Siyama? Inace na fadamaki muddin kikayi nasarar raba
aurensu kema a bakacin aurenki ko? Toh ni Alhaji Mustapha
na sakeki ki tattara komai naki ki barmin gidana. Mugun
halinki nikam bazan iya dashi ba."
Siyama ta runtse ido,har cikin ranta bataso ba. Uwa uwa ce
duk lalacewarta kafiso ka budi ido ka ganta tare da
mahaifinka. Hawaye masu zafi suka zubo mata. Hanif
kuwa baiji ko d'ar da hukuncin Abba ba,saboda shi kanshi
yaji bakin cikin abunda ta aikata. Ai kuwa hajiya ta mike
tana zage zage babu wanda ya kulata karshe ta fice daga
gidan tana tsine tsine.
Abba ya dubi Rumaisa
"Ke kuwa na rabaki da gidana..."
"Haba Yaya,abun yayi yawa. Don Allah kada ka yiwa
yaranka mugun baki. Kaifa mahaifi ne."
Cewar Alhaji. Wannan yasa Abba yiwa anti rumaisa tsawa
"Tashi ki wuce gidan mijinki,aure ne Nura sai yayi babu
fashi. Don uwarki saikin gasu a gidan."
Ta mike tana goge hancinta da mayafi,sum sum ta fita.
Hadiyya dai tana gefe tana hawayen tausayi ganin lamarin
takeyi kamar a fim.
Abba yayi dogon nasiha,karshe Alhaji yayiwa Siyama
albishir akan tun washegarin ranar da sakin ya afku Jafar
ya maidata saidai Abba da yak'i komen. Amma ta shirya
gobe mijinta zaizo su tafi. Ta gefe ta saci kallon Jafar taga
ko yayi na'am da hakan. Illai kuwa haka dinne,murmushi
Jafar yake sakar mata tayi azamar sunkuyar da kanta.
Hawayen farin ciki suka kwaranyo mata.
*******48
Bayan kowa ya watse,Siyama ta rako hadiyya da jafar zasu
koma gida. Hadiyya ta dubeta tana dariya
"Toh antina,sai kuma munzo daukar abarmu ko?"
Siyama tayi dariya ta rungumeta cikin farin ciki. Jafar yana
kallonsu yana jin dadi a ransa. Hadiyya tayi azamar fita
tana cewa
"Bari na shiga na yiwa Hajja sallama."
Abunda Jafar ke jira kenan,ai kuwa da hanzari ya rungume
Siyama jikinsa yana rawa ga wani irin sanyi da yaji a ransa.
Ya dago fuskarta ya hau sumbatar bakinta bata musa mishi
ba har saida ya kammala don kanshi ya saketa. Suka dubi
juna cikin so da kaunar juna,murmushi ya sakar mata ya
shafi gefen kumatunta
"Ki yafemin.."
Da sauri ta rufe bakinshi
"A'a Yaya jafar,ni keda laifi don Allah ka yafemin bazan kara
boye maka komai ba."
Yayi murmushi
"Na yafe maki siyama,komai ya wuce."
Farin ciki ya cika mata zuciya. Ta sauke numfashi. Haka
sukayi sallama cikin kewar juna.
********
Washegari da yamma saida ya kammala komai a kasuwa
sannan ya nufi wajen Haris. Nan ma haris yaji mamakin
yanda lamarin ya faru karshe ya kara nusar dashi
muhimmancin yin bincike kafin yankewa mutum hukunci
gudun shiga hakki. A gurguje yayi mishi godiya da sallama
ya tafi dauko Siyama har Haris yana mishi dariya.
Hadiyya ta gyarawa siyama komai na dakinta da falo. Hatta
bandakunan ta wankesu sunyi kyal dasu. Girki lafiyayye ta
shirya musu ta jera a tsakar falon Siyama. Sai kamshin
turaren wuta ke tashi. Saida ta kammala tayi wankanta tsaf
itama tayi kwalliya. Jim kadan taji shigowar mashin d'in
Jafar tayi azamar bud'e musu gidan ta rungume Siyama ta
amshi Faruk.
Siyama taji dadi matuka ganin irin gyaran da Hadiyya ta
yiwa sashenta.
Bata kara gaskata cewar Hadiyya tana kaunarta ba saida
tayi kwanaki a gidan,anti sama anti k'asa take kiranta
dashi. Ga kula da Faruk duk da itama d'in tana fama da
nata cikin. Wannan yasa Siyama wancakali da kishi ta riki
Hadiyya yar uwa. Yanzu yan jafar suna yawan zuwa
gidan,Hajja na kaunar surukanta kamar me.
Jafar kodayaushe Siyama cikin shayar dashi mamaki
takeyi. Bai taba dauka KAZAMAR GIDA zata koma
TSAFTATACCIYAR GUDA ba. Ba shakka Allahu mai hikima
ne,Mai chanja bayinSa ne. Sai gashi kodayaushe Siyama
cikin aiki take. A wata guda ta murje tayi kyau abinta.
Hadiyya kuwa dakyar Jafar ya barta suka shirya zuwa nijar
wajen yan uwan mamanta da Maman nata. Ganin haka
itama Siyama tace baza'a barta a baya ba. Tare sukaje
abinsu don mota guda Jafar yayi musu haya,daga su sai
direban. Mama tayi mamaki kwarai na ganin Siyama tare
dasu. Taji dadin hakan kwarai. Sunga sarah tayi kyau
abinta da mijinta Surajo. Yaranta suna hannun kakarta tana
kula dasu.
Komai na rayuwa ya chanja. Hajiya dakyar Abba ya
maidota bayan bin da yan uwanta suka dungayi karshe tayi
alkawarin zata gyara halinta. Abun zai baka mamaki idan
kaga Hajiya a falon Hajjah ana hira da dariya.
Lamarin Allah kenan!!
******
Hadiyya zaune tana koyawa Faruk homework,yan biyunta
Na'im da Na'ima suka shigo a guje suka fada jikin Siyama.
Hadiyya ta daka musu tsawa
"Kuyi a hankali mana,baku ganin cikin dake jikinta?"
Siyama dake zaune da tulelan ciki haihuwa yau ko gobe tayi
dariya
"Barsu malama,idan basu zo wajen uwarsu ba wajen wa
zasuje?"
Hadiyya tayi murmushi tana kallon Siyama
"Allah anti ke kike sangarta yaran nan. Basajin magana."
"Kul,karki kara cewa yarana basuji zamu sa k'afar wando
d'aya."
Ta maida dubanta garesu
"Me kuke so?"
Na'ima sarkin surutu tace
"Anti alawa mukeso."
Tayi murmushi ta kama hannunsu suka shiga d'aki
"Ku muje ai akwai sauran wanda na siya maku jiya."
Da murna suka bita d'akin. Hadiyya ta girgiza kanta,ta lura
Siyama bazata daina shagwab'a yaran nan ba.
Da daddare suna zaune suna kallo a falo,Jafar ya dawo.
Yaran suka tafi wajenshi da gudu suna murnar ganinsa. Ya
daukesu daya bayan daya ya cilla sama kamar yanda yake
musu. Sannan ya amsa sannu da zuwan da matansa keyi
mishi.
"Maman twins ya nauyin jiki?"
"Alhamdulilllah baban twins."
Siyama ta amsa,ya dubesu
"Akwai albishir da zan maku amma kowacce saita fad'i
abunda zata bani."
Siyama da Hadiyya suka dubi juna kafin su dubeshi,Siyama
tayi magana
"Kada ka damu,zaka samu abunda yafi kud'i."
Yayi dariya sannan ya ciro takarda ya mik'a musu
"Alhamdulillah,yau na samu aiki a First bank. Sai ku tayani
addu'a Allah Ya dafamin."
Cikin murna matsananci suka rungumeshi a tare suna
hamdala,yaran ma ganin haka suma suka rungume
abbansu ta baya......!
Karshen KAZAMAR GIDA kenan
..inda nayi kuskure pls ayimin gyara kuma a yafemin...d'an
Adam ajizi ne
.wanda duk na b'atawa shima yayi hakuri...
Rufaida Omar Ibraheem!

You might also like