BANI DA GATA Complete (0) - 1-1-1
BANI DA GATA Complete (0) - 1-1-1
( _Sai Allah_)
_Bismillahirrahmanirrahim_...
*1-5*
Ina daga quryar d'akin Innammu ina sauraron firarsu ita da gwaggwo Dije,dad'i ne yayi kamar
yakasheni irin yadda naji gwaggwo Dije na yaba kayan da aka siyomin,dukda basanon wanda za'a
auramin nake ba,zafi yayimin yawa sai had'a zufa nake amma kunya tahanani fita tsakar
gida,insha iska.
Maganar gwaggwo Dije najiyo tana fad'in ai ranar asibici za'a kawo kayan lefe,naji agari ana
fad'in lefen Maryama yayi kyau,dan andad'e a karkararnan ba'ayi lefe irinsa ba.
Gwaggwo Dije tasauya fuska daga fara'a zuwa damuwa tace"Asabe tsoro kuma?".
Innammu tace"ina tsoron kada sukawo kayansu masu tsada mu kuma bamuda wannnan halin da
zamu mayar masu,aje ayita magana cikin karkara".
Gwaggwo Dije tace"haba Asabe kamar dai bakisan halin mai gari ba,kuma zuri'ar gidan mai gari
ba,kinsan mutanan kirkine bazasuyi mana haka ba".
Innammu tace"nasan da haka Yaya Dije,amma dole hankalimmu yatashi,amma Malam yace idan
akwai abinda ake buqata game da kayan aure ayi masa magana".
Gwaggwo Dije tace"kayan Maryama ko a inda mukaje saye,mutane nata yabasu,dan haka bamuda
wani shakku,gado ne lambu wan,sai kabet madaidaici,tare da madubi sai kujeru guda ukku, gaba
d'aya set d'in dubu shirin da ukku,ga kuma kayan da zamu jera mata abisa kabet d'in,gaskiya
Malam yayi qoqari sosae Asabe".
Innammu taji dad'in maganar Gwaggwo Dije sosae dan haka hankalinta yad'an kwanta.
Kwanakin bikina nata matsowa gari yacika da magana anyimin lefe kwalla biyu.
Gidan mai garin *DONA*,wato qauyemmu kenan ko kuma nace rigarmu, mutanan kirkine dan
abokanan arziqi na mahaifina *Malam Mani* da mahaifiyata *Asabe* sunanta zomana barka tare
da fatan alkairi,dan ayadda suke fad'i wai nayi sa'a arayuwa,ni kuma abin baidame niba dan
bawani son Ashiru nake ba,kasancewar tinda nataso aruwata bansan ra'ayin kainaba sai wanda
mahaifina yaza6amin.
*Ashiru* yaron mai gari na ukku shine wanda iyayemmu suka yanke shawarar had'ani da
shi,dukda lokacin ina yar Shekara goma sha biyar amma nasan abinda nakeso arayuwata,saidai
babu yadda na'iya saboda banida wanda nakeso.
Bawani kantamin arai yayi ba,saboda lokuta da dama idan naje kiwo yana zuwa inda nake tare da
shanummu,yadameni da surutu amma bana kulasa,saidai nayi niyyar yima iyayena biyayya kamar
yadda nasaba.
Mahaifina irin mutanan nanne policy man, wato masu tsatstsauran ra'ayi duk abinda yafad'a baya
canzawa kowa yasanshi da wannan halin,muna tsoron mahaifimmu sosae ni da qanwata
*Aisha*,saboda ko dariya bai cika yimana ba,koda wani abu muke buqata saidai mufad'ima
Innammu,bamu zuwa talla da kasuwa saidai muna zuwa kiwo da makarantar allo akusa da
gidammu.
Munsamu tarbiya sosae wanda har kwatance akeyi da gidammu acikin karkara, shiyasa mai gari
ya'auko neman aurena gidammu kuma mahaifina yabada ni batare da an shawarce ni ba ko kuma
anji ra'ayina.
Mutane da dama suna fad'amin inada kyau sosae,duk da aqauye ba'a damu da wani kyau ba, amma
awa'annan zamani cikin yammata babu macen da takaini kyau da diri.
**************
Ana saura sati d'aya bikina,ina tafiya akan hanya nadawo daga gidan Baba Tanimu wato yayan
Babana,sauri nake sosae dan magriba takusa gashi Babana yahanamu fita gab da magriba.
Ina tafiya amma ji nake kamar ana bin bayana,sai tsoro yakamani dan nayi tinanin ko Ashiru ne
yabiyo ni kada Babana yaganni atsaye tare da shi dan zanji matuqar kunya.
Sallama aka yimin cikin siririyar murya,ban waigaba duk da mamaki yacika min zuciya dajin irin
wannan zazzaqar murya.
Saida yayi sallama qaro na ukku sannan ahankali nawaiga cike da son ganin mai wannan murya
haka.
Mamaki yaqara cikani jin yakira sunana nace"bawon Allah a ina kasan sunana?".
Yayi murmushi wanda yaqara fiddo masa da kyawunsa,sai naqara kid'imewa,da alama yafara
ganoni dan haka saina fara shiga taitayina.
Yace"zan fad'a maki Maryam,amma inaso nayi sallah ina ne gidanku dan inzo zuwa anjima?".
Nazaro daradaren idanuwana masu d'auke da gashin ido gazar gazar,duk da duhu yafara amma
saida naga yalunshe Idanuwanshi cikin wani salo wanda bamfahimci inda aka nufaba.
Yace"idan har bakiso nayi maku sata toh, saimun had'u zuwa anjima".
Maryam tace"mahaifina baya barina fita da daddare,yanzu da kaganni nan atsaye dan nasan yana
masallaci".
Yace"toh shikenan,yanzu bazan qara ganin wannan Kyakykyawar fuskar taki ba?, ki taimakamin
Wlhy idan banganinki ba,bazan iya bacci ba".
Gaban Maryam yaqara fad'uwa qaro na biyu,dan yafara bata tsoro,da sauri tafad'a gida,batare da
taqara sauraren abinda zaifad'a mata ba.
Yakalli gidan da tashiga yayi murmushi,aransa yace wato nan ne gidanku ko,yadad'e atsaye kafin
yatafi.
Inna takalleni fuskarta cike da tambaya tace"Lafiya kika shigo kamar wadda aka jefo daga sama?
".
Da harzan fad'a mata abinda yafaru saikuma nace"Inna nayi tinanin Baba yana gida ne".
Inna tace"hmmm,ai kinsan bayaso kuma kikaje kikayi zamanki kina ganin yadda rana tafad'i".
Da dare yayi bayan munci abinci ni da Aisha,muka tafi cikin bukkarmu muka kwanta.
Duk irin yadda muke fira ni da Aisha amma daren nan saida tayi bacci tabarni, zuciyata cike da
tinani akan wannan bawan Allah.
Dana rufe idanuwana sai naga kamar zanganshi,ina tino lokacin da yayimin wani murmushi
bansan lokacin dana tashi zaune ba.
Bansan meye yakeson samunaba,nakasa bacci saboda wani wanda bansani ba.
Bansan lokacin da aka fara kiran sallar asalatu ba, saidai naji Innammu tana tayar da mu.
Koda gari yawaye saida Innammu tace idanuwana sun kunbura ko bansamu bacci bane.
Nadai samu nayi mata qaryar idanuwana kemum ciwo.
Abu kamar wasa nakasa samun natsuwa banida walwala yau kwanana biyu kenan har amfara
tambayata abinda yake damuna,amma nace babu komai.
Babu abinda nake buqata sai kawai inga bawan Allah da nagani shekaran jiya.
Inaso infita amma nasan daqer ne za'a barni infita dan yanzu ko kiwon shanu Aisha take zuwa
saboda anhanani fita.
Saidai inshiga bukkarmu inyi tagumi Aisha ce,tafi kowa ganina cikin wannan halin,dan haka
taketa faman tambayana abinda yake faruwa,amma banfad'a mata ba.
Arana ta ukku ne,gwaggo Dije da Inna Sahura matar yayan Babana sukazo gidammu danyin
wanke wanken yakan aurena dan yau saura kwana bakwai daurin aurena.
Dan haka natafi gidan gwaggwo Dije dan a al'ada ranar da ake wannan wanke waken amarya
bazata zauna gidansu ba.
Ahankali nake tafiya kaina na qasa,cikin shigata ta cikakkun fulani,da ganina kaga kamilar mace
mai kamun kai.
Saida na'isa qofar gidan ina qoqarin bud'e qofar,naji sallama kamar irin na ranar farko.
Da sauri,najuya tare da kallon mai magana,gabana yaqara fad'uwa,saboda qarin kyau da zati daya
qaramin.
Yana rufe baki Maryam tafara tafiya,yana biye abayanta saida sukaje bayan gari inda babu mutane
sannan tatsaya cak.
Yace"Maryam ni sunana *Habibu*,tin ranar da nafara ganinki naji babu macen da nakeso aduniya
sai ke,amma inaso kizo muzauna dan kada natakura maki".
Haqiqa tinda taganshi tarasa samun natsuwa,amma kuma yau tinda taganshi taji tana cikin farin
ciki da walwala,shin ko itama tafara sonshi ne?.
Fuskarta araunane tace"kayi haquri bazamu iya zama anan ba,kuma yakamata nabar
wurinnan,saboda banaso wani yaganni".
Habibu yace"Maryam dan Allah kada kitafi kibarni,wlhy ina sonki,ina cikin damuwa,zuciyana ke
d'aya take buqata akusa da ni".......................
*5-10*
Gaban *Maryam* yaqara fad'uwa,wani saboda al'amari,ji tayi takasa tafiya daga inda take.
Habib yace"Maryam ina sonki,dan Allah kema kisoni kamar yadda nakeson ki".
Wahaye masu zafi suka fara zuba daga cikin idanuwanta,tana kukan rashin sanin yadda
zatayi,haqiqa taji tanason Habib har cikin rainta amma batasan yadda zatayi da mahaifinta ba
yasaurareta.
Gaba d'aya hankalinshi yatashi,ganin halin da take ciki,yarud'e yana tambayarta abinda yafaru.
Habib yace"Maryam me nayi maki kodai bakya sona ne,dan Allah kifad'amin gaskiya".
Ganin hawayen da tagani suna bin fuskarshi sai hankalinta yaqara tashi,dan batason ganin 6acin
ransa bare kuma hawayensa,zuciyarta tacika da tambayoyi da dama,shin me Habib yake yima
kuka?.
Bakinta na rawa tace"Habib ina sonka,amma saidai bansan yadda zanyi ba, dan mahaifina yabada
aure ga Ashiru d'an mai gari,bansan yadda zanyi ba".
Hankalinta yaqara tashi ganin yadda naga idanuwan Habib sun rine daga fari zuwa ja,jikinta
yafara rawa.
Ahankali takad'a kai alamar a'ah,sai sannan taga yad'an saki ranshi.
Da sauri tad'ago idanuwanta tana kallonshi tace"ya zamuyi?,kasan halin Babana kuwa?".
Habib yace"yanzu banaso asamu matsala,kitafi gidan da aka aikeki,da daddare bayan sallar isha'i
zamu had'u".
Maryam tazaro idanuwa tace"ina zamu had'u bayan ba'a barina fita?".
Habib yace"bayan sallar isha'i,zakiga bayan dannin gidanku ana haska fitila,ni ne,sai kiyi dibara
kifito batare da kowa yaganki ba".
Habib yace"haba Maryam ya zakiyi mana irin wannan fatar kodai baki sona ne?".
Maryam tace"inajin tsoro ne,idan mahaifina yasani akwai matsala".
Habib yace"idan wannan shawarar batayi makiba,kifad'a mani wata,wadda hankalinki zaikwanta
da ita".
Ganin yad'an 6ata ransa,sai tayi saurin yadda da maganarshi,tace"insha Allah bazamu samu
matsala ba.
Ganin wani mutum zai wuce tare da shanunshi yasa tayi saurin tafiya batare da tayi sallama da
shiba,shima kuma yafahinci hakan saidai yayi murmushi yatafi abinshi.
Babu inda tatsaya sai cikin gidan Gwaggo Dije,guri tasamu tazauna tana tinanin irin yadda takamu
da son Habib cikin lokaci kad'an,sai kace wani almara,ashe haka so yake?.
Amma wani sashe na zuciyarta yana tinanin irin yadda tayi saurin yadda da shawarar da Habib
yakawo akan fitar da zatayi da daddare,bayan kowa yayi bacci,tana ganin shareshi zatayi bazata
fitaba.
Damarece Gwaggo Dije tadawo daga gidammu nasan sungama wanke wankensu,dan haka tayi
saurin tafiya gida.
Koda takoma gida kasacin komai tayi,dan farin cikin da take ciki,yau dai taga mutum da rashin
ganinshi yahanata sukuni.
Innammu tace"Maryama bakici abinci ba,wai me saya kwanakinnan bakison cikin abinci,duk
kinfad'a?".
Aisha tace"Innammu ai tind'azu nake lura da Yayata sai fara'a take,lokuta da dama sai inga takalli
wuri d'aya tana murmushi,da alama tana cikin farin ciki bakamar kwana biyu da suka wuce ba".
Aisha tace"hamma Ashiru yana jiranki a d'akin Baba dan tinkina sallah yazo".
Ji tayi kamar an aiko mata da mutuwa dan haka tad'aure fuska,kamar zatayi kuka.
Maryam tafara gunguni tana fad'in bayan sallar magriba ko wane namiji yana masallaci yanason
yasamu lada amma shi wannan marar gurin yana nan,salon yadameni da surutun tsiya.
Innammu tace"eyye Maryama rashin kunya ko,toh bari idan Malam yadawo saiki fad'a masa,kuma
zama cikin masallacin bayan sallar magriba zuwa insha'i ba niyya bane?,kuma aiba farilla bane.
Jin amfad'i sunan Malam yasa bata qara fad'in komai ba,saidai tadauki zanin da zata yafa tanufi
hanyar zaure anan d'akin Babammu yake.
Sallama kawai nayi na'afka ciki,ba tare da gaisuwa ko wani magana ba,nasamu wuri nazauna
fuskata babu walwala,babu fara'a.
Ashiru yace"Maryam kenan,dan Allah me yasa baki sakin jikinki da ni,ai yakamata ace kinsaba da
ni,amma gashi ko magana bana samu daga gareki,ko saina biyane?".
Maryam tace"idan kagama abinda yakeyi,kafad'amin ni zankoma ciki,saboda ina cikin lazimina
kataso da ni".
Ashiru yayi murmushi yace"ina son nayita kallon wannan kyakykyawar fuskartaki Maryam,ina
matuqar sonki,haqiqa iyayemmu sunga dacewarmu shiyasa suka had'amu,kuma nayi farin ciki
sosae,akullum ina godia ga Allah,babban gurina shine naga an d'aura mana aure".
Maryam dai batace komai ba,Aisha ce tashigo tare da sallama hannunta d'auke da kofin silver cike
da ruwa mai sanyi nacikin tulu.
Aisha tace"na'iyalu".
Ashiru yakalli Maryam da tin zuwan Aisha batace komai ba,yayi murmushi yace"Aisha na kama
da ke Maryam,saidai kinfita haske sosae,nayaba da hankalinta sosae,amma fa bance tafiki ba".
Batare da tajira abinda zaifad'a mataba tayi cikin gida,tanata turo baki.
Tambayar kanshi yake,wai Maryam kunyarsa takeji ko kuwa bata sonshi ne?.
Wani 6angare na zuciyarsa yace"idan kunyarka takeji nan da kwanaki kad'an zata bari,idan kuma
sonka ne batayi toh nan da d'an lokaci zaka koya mata sonka,kayi mata duk abinda takeso sannan
kakula da ita kamar kwai".
**********
Maryam tana komawa cikin gida tatarar da su Inna na sallah,itama taje tad'auro alwala tafara
gabatar da sallah.
Ina gama sallah Aisha takawomin tuwo da miya agabana tace"Yayata ga abinci kici,dan duk yau
banga kinci abinci ba".
Inna dake cikin d'aki tace"Aisha kinaji da wannan Yayar taki,ai kinga batasan takaima baqonaku
ruwa ba bare kuma abinci".
Bance da su komai ba,haka nad'an ci tuwon kad'an saboda tinani yadame ni,abu kamar wasa,da
nayi niyyar nabar maganar Habib inqi fita,sai gashi naqosa lokaci yayi infita dan inhad'u da shi.
Bayan sallar isha'i,Baba yadawo tare da tsarabar fanke da qosai,nad'anci qosai kad'an,mukad'anyi
fira,sannan muka tafi muka kwanta dama abinda nakeso kenan.
Muna kwance bisa yar qaramar tabarmarmu,Aisha tace"Yayata wai me hamma Ashiru yayi maki
ne?".
Aisha tace"baki sakar masa fuska,ina lura sauda dama ko maganarshi bakiso ayi maki,amma shi
yana matuqar sonki".
Maryam tace"da dai baccinki kikayi da yafiye maki,ni yanzu bacci nakeji saida safe".
Aisha talura batason maganar shiyasa tayi shiru bata qara yin magana ba.
Maryam batayi bacci ba tana hangen tsakar gida kozata hangi hasken fitila.
Can dare yatsala kimanin qarfe daya na dare,dukda basuda agogo amma tasan dare yayi sosae.
Hasken fitila irin wanda battery yafara sanyi tahango,ranta yabata Habib ne.
Ahankali tatashi bata d'auki komai ba sai kallabi dan kada Aisha tafarka taga tad'auki
mayafi,tatambayeta ina zatatafi.
Ahankali take tafiya cikin sand'a har ta'isa tsakar gida,ta'isa bakin qofa saida taduba taga babu
komai babu wanda yake kallonta,sannan tabi ahankali tabude gida tafita.
Abayan gidansu tatarar da shi atsaye,yana ganinta yakashe touch light d'in dake hannunshi,suka
yima junansu murmushi cike da qauna,duk da garin babu haske sosae amma suna ganin juna.
Batayi masa musu ba,tabishi suka tafi sai da suka d'anyi nisa sannan yakama hannunta suka zauna
kusada wata bishiyar bedi.
Ji tayi wani abu yana bimata jijiyon jikinta,kamar shocking gaba d'aya jikinta yafara rawa,da sauri
tafara qoqarin qwace hannunta daga nashi.
Yad'an kalleta fuskarshi kamar zaiyi kuka yace"haba Maryam ba dole raina ya6aciba,ina ganin
kamar baki yadda da ni ba,dan nakama hannunki sai me,ai dan ina sonshi shine yakawo haka,idan
baki sona kifad'amin".
Cikin sanyin murya tace"Habib ya zakace bana sonka?,kuma da ban yarda da kaiba bazan fito
daga gidammu ba cikin wannan dare,kasani babu namijin da nata6a fad'ama kalmar so saikai".
Yayi murmushi yace"da gaske ko Ashiru baki ta6a fad'a masa cewa kina sonshi ba?".
Maryam tace"da gaske mana,nifa dama ba wani sonsa nakeyi ba,amma a ina kasan sunansa?".
Habib yace"zanfad'a maki komai amma saina tabbatar da kina sona fiye da shi".
Yaqara kamo hannunta qaro na biyu awannan lokacin batayi yunqurin anshewa ba,saboda tanajin
tsoron kada ya6ata ranshi.
Yafara wasa da yatsun hannunta,nan fa jikinta yafara rawa harsaida yafahimta,amma dukda haka
bai sakar mata hannuba.
Yakira sunanta ahankali yace"Maryam ina so kisaba dani kafin muyi aure,kinga damunyi aure
munsaba da juna".
Habib yasa hannunshi na dama yashafi fuskarta sannan yace"zamuyi aure insha Allah,saidai inajin
tsoron yadda zanyi da mahaifinki domin naji ana fad'in yanada tsatstsauran ra'ayi".
Fuskarta kamar wadda zatayi kuka tace"haqiqa haka halin mahaifina yake nima bansan yadda
zamuyi ba".
Yana kallon bakinta alokacin da take magana,yanayin lips d'inta suna matuqar tayar masa da
hankali,baisan lokacin da yalumshe idanuwanshi ba.
Maryam tace"Habib yakamata natafi gida kada Aisha tatashi taga bana nan".tatashi tsaye sai
lokacin yasakar mata hannu.
Shima tashi yayi tsaye,yana kallon cikin idanuwanta yace"Maryam ko kingaji da ganina ne?,nifa
bangaji da jin muryarki ba da ganin kyakykyawar fuskarki,Maryam komai naki yana matuqar
d'aukar hankalina,wlhy idan narasaki bansan yadda zanyi da rayuwata ba".
Tausayinsa ne yakatama dan tasan zaiyi wuya mahaifinta yayarda da shi dan yariga yagama
magana.
Tana cikin tinani ji tayi yamannata akan qirjinshi,yakai bakinshi saitin kunnanta,ahankali yake
fad'in tinanin me kike?.
Ganin yaqi sakinta yasa tafara kokowar qwatar jikinta daga nashi.
Tasamu taqwace kanta tana maida numfashi cikin sauri,shima hakance takasance daga gareshi.
Wannan lokacin bai nuna 6acin ransa ba,yace"Maryam nifa ne wanda zai aureki dan narungumeki
ajikina ba wani abu bane?".
Baice mata komaiba kawai yajuya yafara tafiya,hankalin Maryam yatashi dan tanaji kamar bata
kyautaba abinda tayi mashi,tayi tinanin yanzu idan yayi fushi yatafi ina zaki qara ganinshi,yafara
yimata nisa gashi kuma darene bare taqwalla masa kira.
Kawai saita ruga ta'isa gabanshi tana maida numfashi da sauri,tace"kayi haquri bazan qaraba".
Yayi murmushi hannuwanshi guda biyu yabud'e mata alamar ta taho,batasan lokacin data fad'a
aqirjinsa ba.
Ahankali yake shafa bayanta da hannunshi na dama kamar yana kallashin wani baby,sunkai
10mins ahaka,sannan suka saki juna.
Suna mayarda ajiyar zuciya,wani sabon sonshine yake qara shigarta,ji take duk duniya babu
namjin da takeso kamarsa,fatanta Allah yasa Baba ya yadda da shi amatsayin wanda takeso kuma
yayadda suyi aure.
Iska yahura mata cikin idanuwanta,jinhakan yasa tadawo cikin hankalinta sukayima junansu
murmushi.
Yace"muje narakaki,amma ina fatan gobema zaki qara temakamin kifito ko?".
Tad'an saci kallonshi tayi murmushi sannan tace"insha Allah zan fito".
Harkusa da qofar gida yarakata saida yaga shigarta gida sannan yajuya tatafi.
Kamar yadda tayi sand'a tafita haka tayi tadawo gida,cikin sa'a babu wanda yaganta hartashige
bukkarsu.
Aisha tace"Yaya mafarki nayi babu kowa cikin kubbarnan saini d'aya,ina kikaje?".
Washe gari da marece aka kai kayan lefe gidan Yayan Babana wato Baba Tanimu,biki nata matso
saura kwana hud'u soyayya na qara qarfi atsakanin *Maryam da Habib*.
Anata shirye shiryen biki,dan Malam cewa yayi ayi komai awadace har Sa d'insa yaqara kaiwa
kasuwa domin ayimin duk abinda akasan ina buqata,babban gurinshi shine ad'aura aure yaga
munzauna lafiya,dan anyaba da halin Ashiru nima kuma ana yabona sosae.
Yau saura kwana ukku bikina dan harjeren kayana anje anyi,a cikin gidan mai gari aka yankarma
Ashiru wani sashe,ayadda naji Aisha nafad'i wai daki dayane ciki da falo sai kewaye da kitchen,sai
murna akeyi wai ni d'ayace aka fara yima kitchen acikin karkarar kuma kayana sunyi kyau da
wurin,ban dai kulasu ba,illa takaici da suke bani,bande nunama kowa komai ba.
Tin ranar da nafara fita muna had'uwa da Habib,babu ranar da bata fita,tasaba da shi sosae tare da
kalamunsa masu dad'i,kuma kullun da irin salon soyayyar da yake nuna mata.
Koda dare yayi kamar yadda tasaba fita,haka tayi sand'a nafita abinta.
A inda suka saba had'uwa anan suka had'u,kamar yadda yasaba mata da had'uwarsu zasu rungume
junansu sai sunyi kamar 15mins sannan surabu.
Guri suka samu suka zauna kusa da wata bishiya,yakama hannunta yahad'a tare da nashi
yarintse,suka kalli juna sukayi murmushi kasancewar garin akwai hasken farin wata.
Habib yace"Maryam nifa yau hada tsaraba nayo mana,amma duk saboda kene".
Maryam tace"saboda ni kuma?".
Maryam tayi murmushi tace"nima ina sonka fiye da komai,fatana shine Baba yayadda da
kai,amma gashi haryau saura kwana ukku bikina,babu wani abu da zamuyu".
Jikinsu yayi sanyi,yamatso daf da ita yana kallon lips d'inta,itama kallonshi take,ji tayi yahad'a
bakinshi da nata yafara tsotsa,bata hanashi ba dan jikinta yamutu,saida yagaji dan kansa sannan
yasaketa.
Yace"Maryam wannan shine bature ke kira da kiss,idan kikaga bature yayima mace haka to
sunyadda zasuyi aure".
Habib yayi murmushi tare da shafa gefen fuskarta yace"zan fad'a maki,amma sai bayan munyi
aure,kin yadda?".
Maryam tasa tafikan hannunta ta rufe fuskarta,bakinsa yad'ura bisa bayan hannunta yayi kissing
nasu.
Maryam tabud'e fuskarta,nama ne balangu tare da yaji da alama zaiyi dad'i sosae.
Habib tad'auko guda d'aya zaisaka mata abaki amma taqi ansa,wai taqoshi.
Yayi fama da ita taqi ansa,saida taga yabata ransa sannan taci,atare sukaci sukacinye,kwanciya
yayi qasa yad'aura kanshi bisa ciyarta sannan sukaci gaba da firarsu.
Maryam tace"a'ah".
Habib yace"kije kisamesa kifad'a masa gaskiyar cewa ni kikeso,ba Ashiru ba".
Saida taji gabanta yafad'i hankalinta yatashi,tini tafara hawaye tace"wlhy kashe ni zayayi Habib".
Shima Habib hankalinshi yatashi ganin yadda cikin seconds dukta kid'ime tarasa samun natsuwa.
Habib yace"toh yi haquri,yaqara rungumeta sosae,yanzu abar maganar zamusan yadda zamuyi
kafin ranar bikin".
Maryam taqara rungumeshi tana kuka dan gani take kamar rabasu za'ayi,ji take idan ba shiba
bazata ta6a iya zama da kowane d'a namiji ba arayuwarta.
Kamar kullun lokaci nayi yarakata har qofar gidansu,saida yaga shigarta sannan yatafi,zuciyarshi
cike da tinanin yadda zaya 6ulloma wannan matsalar.
Yan uwa sunzo daga aauyika da dama,antaru gidan Baba Tanimu gobe d'aurin aure,Maryam da
Habib sunata tinanin yadda zasuyi su qulla wancan su kwance wannan.
Asubar yau da Baba zai bude gida,yaga anrufe gidan ba kamar yadda yarufe ba,dama cikin
kwanakinnan idan zaitafi masallaci da asuba saiyaga ba kamar yadda yarufe gidan ba,babu wanda
yafad'i mawa,amma yad'auri niyyar saiyaga mai bud'e gidan.
Biki yakankama sai shagulgula ake,anata farin ciki, *Inna Rahine* aminiyar Innammu itace
tayimin kitso da kunshi,babu wani farin ciki azuciyata,dan ni naqosa dare yayi musan abinyi ni da
Habib.
Yau mu hud'u ne muka kwanta a bukkarmu,Amina d'iyar Inna Sahura matar Baba Tanimu,gidansu
yacika da mutane shine tadawo gidammu takwanta,sai Zulai d'iyar Baaba Rahane da sukazo daga
FAGON RABGAU.
Haka muka kwanta,inajinsu suna fira,amma ban saka masu bakiba dan so nake suyi bacci amma
sunqiyin shiru bare kuma suyi bacci.
Yau namakara sosae,dan sai kimanin 12:45 sannan naji sunyi bacci.
Kamar kullum muna had'uwa muka rungume juna cikin jin dad'i saidai yau kuka nake sosae,dan
ina ganin gobe da rana za'a d'auramin aure da Ashiru ba Habib d'inda nakeso ba.
Namfa yashiga kallashina kamar zai had'iyeni,kiss tako ina,baki,wuya,hannuna, yau dai har
kallabin dake kanta saida yacire yayita yaba irin kyau da naqara masa,ni kuma kuka nake masa
yafad'a mani yadda zamuyi.
Daqer yasamu nayi masa shiru,yace"idan bazaki iya fad'ima mahaifinki ni kikesoba saidai mu
gudu muje wani wuri muyi aure,wlhy ina sonki Maryam".
*10-15*
Hankalin kowa yaqara tashi gaba d'aya mutanan dake wurin suka saka salati.
Amma duk tashin hankalinnan da aka shiga,abin mamaki banda Babammu acikin masu kawo
mani d'auki.
Baba yaharari inda Maryam take yashe aqasa yace"hmm,ai tsabar rashin kunyane,da iskanci
kubarni da ita,idan jikinta yafad'a mata halin da ake ciki,yanzu zakuga tatashi garas".
Baba yafara qoqarin tashi tsare yana nad'e babbar riga da niyyar fara luguda Maryam.
Mai gari cikin 6acin rai yace"wai ke Malam Liman wane irin mutun ne kai?,me yasa cikin lokaci
kad'an kasauya halinka,wai baka yadda da qaddara bane?".
Sannan Mai gari yakalli inda Kamilu(yaron Mai gari) yake yace"kai Kamilu jeka zaure kad'auko
buta nanan".
Babu 6ata lokaci aka kawo buta tare da ruwa aciki,Baba Tanimu ne yayayyafa mata ruwa,saida
tad'auki lokaci sannan tafarfad'o,tare da ajiyar zuciya da sauri da sauri,alamar taci kuka tagaji.
Mai gari yace"Malam Tanimu katafi da Maryama gidanka tad'an huta saboda halin da take ciki".
Yakalli inda Habib yake durqushe yace"kai kuma katsaya zamuyi magana da kai".
Baba yace"ranka ya dad'e,Mai gari idan yarinyar nan batabar garin nan yau ba,wlhy saina tsine
mata kuma sannan ni nabarmata garin ita tazauna,amma kuma kamar yadda nafad'a abaya wlhy
saina dawo nakasheta".
Cikin dishashshiyar murya tare da kuka Maryam tafara magana tace"Babana dan Allah,dan hasken
alqur'ani kayimin haquri,kada katsinemin wlhy zantafi nabar garin nan,amma kayafe min.......".
Kukan da yaci qarfinta yasa tayi shiru badan ranta yaso ba.
Baba Tanimu da hawaye suka fara zubar masa yace"dan Allah Liman,kabari ad'aurama yarannan
aure kafin subar garin nan,kuma kabamu lokaci iyayen yaron nan suzo ayi maganar aurensu".
Baba yace"ina ruwammu da maganar iyayen yaro,kuma banida hurumi da aurensu,babu abinda
yahad'ani da su".
Mai gari yakira sunan Habib yace"Habib a ina iyayenka suke?,kuma meye sana'arka?".
Habib yashare hawayenshi yace"ranka ya dad'e,iyayena suna garin Kebbi ne,kuma sana'ata shine
koyarwa a makarantar primary qaramar hukumar Argungun,kuma sannan dama iyayena sundad'e
suna son nayi aure amma bansamu matar da tayimin ba,sai Maryam".
Mai gari yace"Habib yanzu kaga halin da ake ciki,kace nason Maryama,tsakani da Allah wato son
aure,ina fatan zaka riqe Maryama cikin aminci da kulawa?".
Habib yace"insha Allah ranka ya dad'e,kuma iyayena zasuyi farin cikin ganin Maryam amatsayin
mata agareni".
Mai gari yace"kamar yadda Malam Liman yayi alqawarin halakar da Maryama acikin daren
nan,shine nake ganin d'aura mata aure ita da Habib shine yadace,idan yatafi da ita kunga muma
hankalimmu zaifi kwanciya akan hukuncin daya yanke na d'aukar ranta".
Mai gari yakalli inda Baba Mande yake zaune yace"Malam Mande naga tinda kazo bakayi magana
ba,amma me kake gani akan maganata?".
Baba Mande cikin tausayawa yace"wlhy ranka ya dad'e lamarin ne yad'auremin kai,gani nake
kamar a mafarki,abinda Malam Liman yake aikatawa,amma nima ina ganin hakan shine
yafi,ad'aura masu auren,inyaso saisu tafi da aurensu".
Kowa ya'amince da wannan shawarar,babu 6ata lokaci aka d'aura masu aure agaban jama'a,Mai
gari shine wakilin Habib.
Baba Tanimu ne wakilina,koda Baba yaga ana niyyar d'aura auren,tashi yayi yasaka takalminshi
yatafi.
Anyi mana nasiha tare da hud'uba sosae tare da fad'a akan rayuwa.
Mutane da dama saida suka zubar ma Maryam da hawaye,mai d'ari biyu,mai d'ari hudu harda mai
d'ari biyar haka aka riqa had'a mata kud'i,sannan aka d'aukar mata kayanta da Baba yayi mata
wurgi da su(kayan sawarta)tare da yimasu rakiya har qarshen gari.
Tana tafiya tana kuka,haka Maryama tabar mahaifarta tabi Habib wanda ayanzu yake amatsayin
mijinta.
Gari gaba d'aya maganar akeyi kowa da abinda yake fad'a agari.
Masu tausaya mata,da masu yi mata kuka,hada masu Allah yaqara mata,wasuma cewa suke
mahaifinta yakamata tana zina da wannan saurayin d'an birni.
Mai gari shine yakashe maganar,yace duk wanda aka qarajin wannan maganar a bakinshi,sai anyi
masa bulala talatin tare da tarar buhun farin wake biyu da naira dubu ukku.
Saida mutane suka fara ganin ambuga misali akan Malam Ya'u da matarsa Salamatu sannan kowa
yashiga taitayinsa.
Koda yan biki sukaji abinda yafaru,haka suka d'au hanya suna tafe suna kuka har gidan
Babammu,tare da fad'ima Innammu duk abinda yafaru.
Shikuwa Baba babu abinda yadameshi,Dangi babu wanda yanufoshi domin bada haquri dan
sunriga da sunsan halinsa.
Akabarsu Innammu cikin damuwa da tinani dan ko abinci basuci sosae,kullum ana cikin tashin
hankali,hartafara rashin lafiya.
Itama Gwaggo Sahura haka abin yadameta,tasha kuka har tagode Allah,amma babu yadda suka
iya sai haquri.
Baba Tanimu da Baba Mande basu qarabi takan Babammu ba dan abinda yayima Maryam yayi
masu zafi sosae.
********************
Harsuka shiga motar da zata kaisu Katsina Maryam batabar kuka ba,duk irin lallashin da Habib
yake mata.
Bayan sun isa Katsina sai aka kaisu tasha suka shiga motar Kebbi State.
Duk abinda yasaya yabata taci bataci ko ruwa bata shaba,harsuka isa,lokacin da suka isa Argungun
dare yayi sosae,haka aka saukesu daga cikin mota.
Aqasa suka taka harsuka isa gidan da zasu sauka dayake babu tafiya sosae,Maryam taqara rud'ewa
saboda kukan karnikan da suke binsu abaya.
Habib ne yabud'e gidan suka shiga,sannan yamaida yarufe.
Suna shiga cikin gidan yabude wani d'aki sannan yakama hannunta suka shiga,cikin rashin sa'a
garin babu wuta,saidai yakunta masu touch light.
Katifa ce atsakar d'akin tare da bed sheet,tare da sauran abubuwan da bata kula da su ba.
Yakalli cikin idanuwanta tausayinta yaqara kamashi,yace"Maryam ko akwai abinda kike buqata
yanzu?".
Habib yace "toh shikenan",fita waje yayi bayan mintina kad'an sai gashi yadawo.
Tatashi tafita,shima fita yayi ban d'aki yashiga da niyyar yin wanka.
Bayan tayi alwala tashiga d'aki tasamu wuri lafiyayye tafara jero salloli,tare da roqon Allah da
yakawo mata mafita,yasa mahaifinta yayafe mata,Allah yabasu zama lafiya tsakaninta da
Habib,Allah yaba mahsiyarta da yan uwanta haqurin rashinta.
Habib yafito wanka yatarar da tagama sallah,takoma bisa katifa tayi tagumi.
Da sauri ya'isa inda take,ya durqusa yafara lallashinta sannan yace"yazuba mata ruwan wanka
yana ban d'aki".
Bata wani d'auki lokaci sosae ba tafito sanye da kayan jikinta,takoma gefen katifa tazauna.
Yana gama sallah bayan yayi addu'a ,yakallo inda take,yayi mata murmushi.
Yataso yazo inda take,ledar nama da rubar Fanta da yasaya masu amota itace yajanyo,yabud'e
masu,babu irin faman da baiyi da itama amma taqici saida taga ya6ata ransa,sannan tafara ci shine
yake bata abaki shima yanaci har saida suka cinye.
Sannan yagyara masu shifid'a suka kwanta,can anjima zafi yadameshi yatashi yacire rigar jikinsa
yatsaya da boxer sannan yaji sauqi.
Yafara lalubar inda Maryam take kwance banda had'a gumi babu abinda takeyi.
Habib yakira sunan,yace"Maryam zafi yayi maki yawa tashi kicire wannan kayan".
Maryam tatashi tafara qoqarin cire rigar jikinta,bayan tacire dama bawani breastwear ne Jikinta
ba,kuma babu Vest,tana matuqar jin kunya hakanan tayi d'aurin gaba takwanta,saukinta d'akin
babu haske.
Shikuma Habib yakasa bacci sai faman juyi yake,daya rufe idanuwansa sai hango lokacin da suka
rungume junansu irin yadda yaji aransa.
Rantse idanuwanshi yayi yafara lalubar inda Maryam take akusa da shi,ita kuma batasan abinda
yake faruwa ba dan baccinta yayi nisa dama kuma tadad'e batayi baccin ba.
Jawota yayi ajikinshi,yafara qoqarin zare zanin da ke jikinta tare da d'aurata bisa jikinshi.
Ji yayi jikinta zafi rau kamar wuta,hankalinshi yatashi yadafa goshinta namma babu sauqi saiga
Allah.
Yatashi yahaska touch light sannan yafita waje domin yasamo ruwa.
Yadda yadawo yana haska inda take kwance,yaga tafarka sai rawar sanyi take.
Vest d'inshi fara yad'auko yafara tsomata cikin ruwa,sannan yafara yimata moping d'in jikinta har
zuwa fuskarta.
Ana cikin haka sai aka dawoda wuta,gaba d'aya d'akin yagauraye da haske.
Fuskarta da gashin kanta yatsaya kallo,dukda idanuwanta arufe suke amma zaka iya tabbatar da
manyan idanuwa gareta,masu d'auke da eye lashes,eye brow d'inta yayi daidai da fuskarta,tanada
dongon hanci tare da qaramin baki mai d'auke da pink d'in lips,gashin kanta wanda yaji kitso
madaidaita,wanda harya sauka bisa qirjinta.
Baisan lokacin da yahad'iye yawuba,ganin tsawon gashin kanta,ahankali yakai idanuwanshi inda
gashin kanta yatsaya,hankalinshi yaqara tashi ganin yadda qirjinta suke,yarinyace qarama amma
Allah yabata nasu na fulani.
Hannunshi yasa yafara d'auke gashinta da yazubo gaba,yafara qoqarin mayar da shi bayanta.
Baisan lokacin da yafara shafa mata suba,haryafara fita hayyacinsa,dasauri Maryam tabud'e
idanuwanta,tafara masa sabon kuka............................
*20-25*
Watarana da marece suna zaune a tsakar gida sunshinfid'a tabarma ita da Habib suna fira cikin jin
dad'i.
Maryam takalli Habib tace"ni kuwa ranka ya dad'e,ina son nafara zuwa wurin Aunty koyon
d'inki,dan tasha ceman idan inaso natambaye ka sai nafara zuwa zata koyamin".
Habib yace"haba Maryam me zakiyi da koyon wani d'inki,ni fa banaso naga matana tana wahala".
Maryam tayi murmushi tace"ai wannan ba wahala bace, amma tinda bakaso shine".
Habib yace"shikenan idan nayi tinani zan fad'a maki, shawarar da nayanke".
Maryam tace"wlhy Aunty tanada kirki dan ta'iya zama da murane sosae, gashi kuma bata qyamar
kowa, inason irin wannan halin sosae".
Habib yace"eh mutane na fad'in tanada kirki sosae, dan tinda nake agunguwar nan banta6ajin ance
gashi tayi sa'insa da kowaba, bare kuma mijinta".
Haka sukaci gaba da hirarsu, tanaso tayima Habib zancen iyayensa amma tanajin tsoro kada ranshi
ya6aci.
Haka sukaci gaba da zamansu har tsawon wata hud'u,amma abinda yake bata mamaki haryanzu
shine rashin fitarshi wajen aiki gashi yanzu bai cika sayen kayan abinci kamar da ba,sai yace baida
kud'i.
Ahaka harsuka share shekara d'aya,Maryam babu ciki batayi ko 6ari ba,halin Habib yafara
chanzawa sosae, abin mamaki yanzu baya sakar mata fuska kamar da ga kuma rashin isashshen
abinci da kulawa.
Cikin wata d'aya Maryam tafara ramewa duk wanda yasanta lokacin baya yasan tacanza sosae.
Watarana yadawo da daddare lokacin tana kwance bisa katifa,tatashi zaune tare da yimasa sannu
da zuwa.
Yanata qoqarin sake kaya ya'ansa,Maryam tatsaya tana kallonshi cike da mamaki, ita tarasa laifin
da ta'aikata masa.
Habib yad'aure fuska yace"Allah yasa lafiya, yanzu dai kinsan wanka zanshiga".
Haka tayita jiranshi haryafi wanka wajen karfe 11pm,yayi shirin bacci sannan yakwanta.
Haushi yakama Maryam amma bata nuna masa ba, tace"ranka ya dad'e kaifa naketa jira tind'azu".
Maryam tace"Inaso kafad'amin laifin da na'aikata maka, kwana biyu bakason kulani,baka
sakarmin fuska kamar lokacin baya, dan Allah kafad'amin laifin dana aikata mata,wlhy bansan
nayiba".
Maryam tace"akwai abinda nadad'e inaso natambayeka, amma bansan yadda zaka fahimci
tambayar ba".
Habib yayi murmushin qarfin hali tare da kallon inda take zaune gefen katifa yace"iyayena da
dangina kikeson tambaya ko, na dad'e da sanin hakan Maryam kuma zanfad'a maki".
Yagyara zama sannan yafara magana, Ni dan qasar Agadaz ma'ana buzajene mu,iyayena tare da
yan uwana muna zaune cikin kulawa da qaunar juna,ina cikin karatuna ajami'a har nakai mataki na
ukku yaqi yatayar da mu daga qasar Agadaz,muka koma Ghana da zama,yanzu munyi asarar
komai namu duk dukiyar mahaifina yanzu babu komai amma muna godema Allah dayasa bamuyi
asarar rammu ba.
Yanzu haka iyayena da 'yan uwana guda biyu wa'anda muke uwa d'aya uba d'aya da su suna qasar
Ghana da zama.
Ina tare da su, kasancewar rashin aikinyi yayi mani yawa kuma ni daya ne d'a namiji awurin
iyayena shine yasa nafad'o Nigeria da zama tare da neman aikinyi.
Cikin rashin sa'a bansamu aikinyi ba kasancewar banida takaddun makaranta,gashi kuma banida
da kud'in da zanfara wani karatu, hakane nafara share share asibiti,Alhaji Nura mijin Maman
Abdul shine yasamarmin wannan aikin(clearner),dayake likitane a asibitin.
Bawani biyammu akeyi wa yawaba sai tarin wahala shine yasa nabar aikin, nakoma inayin aikin
Painting sannan nafarajin sauqin rayuwa.
Duk inda Alhaji Nura yaji anason painting yanayimin magana, kuma yayimin hanya,munayima
asibitoci fenti, da gidaje da masallatai da shaguna da dai sauransu,da hakane natara kud'i nasayi
wannan gidan da muke zaune.
Abinda kuwa yakaini rigarku har naganki, wani dan qaramin clinic da aka gina maku, Alhaji Nura
ne yayimin hanya naje yin fenti rigar dan abokinsa ne akaba kwangilar aikin wirin shine yafad'a
masa yanada mai yin fenti sosae, shike aka bani address d'in Charanchi har nasamu rigar, aranar
da naje aranarne nafara gaininki.
Amma babu wani aikin gwannati da nakeyi, nafad'i hakan ne domin iyayenki su yadda da ni kuma
su auramin ke Maryam.
Wannan shine taqaitaccen labarina amma duk ranar da Allah yahuremin zamuje Ghana kiga
iyayena tare da yan uwana.
Maryam tayi ajiyar zuciya tace"haqiqa natausaya maku halin da kuka shiga ko kuma nace halin
da kuke cikin,Allah yatsare gaba".
Haka Maryam takwana cikin tinani ,abin duniya yadameta, yanzu yaushe zasuje wani Ghana
dukda ba sanin wurin tayi ba, amma daji tasan akwai nisa kuma banan bane.
Cikin wannan lokacin Habib da Maryam sunkoma kamae yadda suke da.
Bayan wata d'aya Habib yadawo da sabon halinshi, tinda yaga Aunty ta'aiko mata da shinkafa da
miya da nama, shikenan saiya fara fushi da ita wai taje tana fad'in baya bata abinci.
Daga lokacin Habib yabar tanka mata dama kuma baya bata abinci tare sabulun wanka da wanki,
baya kwana ad'akin da take saidai yatafi d'ayan d'akin yakwana.
Gaba daya Maryam batajin dad'in zama da shi, idan yafita tinda safe baya dawowa sai sha biyu na
dare, ga yunwa tadameta duk da Aunty batasan abinda yake faruwa ba, amma kullum saita
aikomin da abincin rana.
Nayi sati ukku banshiga gidan Aunty ba, saboda hankalinta ba kwance yakeba,tabi tarame tayi
baqi, gashin kanta yafara zubewa.
Batada sabulun wanki bare wanka wani lokacin ma ruwan da zatayi amfani da shi gagararta
yakeyi.
Sai idan yatashi amfanin kanshi yake sayen ruwa, idan yayi amfani da sabulunsa ya6oye sauran.
Wataranar asabar da daddare, tinani yayi mata rabon da tace takwanta tayi bacci harta manta.
Bayan yashiga d'akin da yake bacci yanzu yakwanta,Maryam tatashi tashiga cikin d'akin ziciyarta
cike da tsoron abinda zai biyo baya.
Tayi masa sallama amma bai ansa ba, dukda tasan ba bacci yakeyi ba, Maryam tasamu gefe guda
tazauna gabanta na fad'uwa tafara magana ahankali.
Hawaye ne ke fitowa daga cikin idanuwanta tace"dan Allah kayi haquri mukawo qarshen wannan
zaman da mukeyi,akullum hankalina yana qara tashi,idan natina aure soyayya mukayi, kasani
*BANI DA GATA* ( _Sαi Allah_)😭,narabu da iyayena da mahaifata duk dan nakasance tare da
kai, amma me yasa kakeyimin irin haka?,kafad'amin laifin da nayi maka, wlhy nayi alqawarin zan
baka haquri tare da yimaka alqawarin bazan qarayin laifin ba..........".
Kukane yaci qarfinta dan dole tayi shiru taci gaba da kukanta mai ban tausayi.
Amma abin mamaki Habib ko kallon inda take bayiba bare yayi mata magana, yayi lamo kamar
yayi bacci.
Haka Maryam tagaji da jiran ansa, tayi 2hrs atsugunne a d'akin amma baiyi mata magana
ba,jikinta babu qarfi tatashi takoma d'akinta taci gaba da kuka, yadda taga dare haka taga rana.
Da asuba lokacin da tatashi haryafita daga cikin gidan,tayi alwala tare da sallah bayan tagama
takwanta da niyyar samun bacci amma kuma baccin yagagareta dan yunwa da takeji kamar batada
kayan ciki.
Dole tatashi dukda jikinta babu qarfi tayi sharar tsakar gida, abin haushi ga kayan wanke wanke
amma babu klin din wankesu.
Tatara kayan wanke wanken gefe d'aya sannan tashiga d'akin da yake kwana yanzu
tagyara,tagyara d'akin da take kwana, sannan takyara kitchen,Allah yasa sunada ruwa tawanke
toilet sannan tadawo gaban wanke wanke tayi tagumi ga yunwa da damunta.
Tana gaban kayan harrana tafito,Ji tayi andafata,afirgice tatashi tsaye tana kollon wanda yadafata.
Aunty ce fuskarta cike da damuwa tare da tashin hankali,Maryam tafara qoqarin share hawayen
dake bin fuskarta tace"Aunty sannu da zuwa,ina kwana? ".
Aunty tace"Maryam dan Allah me ke damunki?, yanzu bakida lafiya kuma baki fad'amin ba".
Tabatasan lokacin da tafashe da kuka ba, ganin haka sai hankalin Aunty yaqara tashi sosae, taja
hannun Maryam suka shiga d'aki.
Aunty tana kuka tace"Maryam dan Allah kiyi haquri kifad'amin abinda yake damunki, wlhy
hankalina yatashi sosae ganin ki haka,Maryam wlhy Allah ne sheda na ad'auke ki amatsayin
qanwata uwa d'aya uba d'aya,wlhy duk abinda yasameki yasameni dan nima agarin nan banida
kowa sai mijina sai ya'ya sai ke da kuma sauran abokanan arziqi".
Maryam saida taci kuka mai isarta sannan tafara bata labarinta tindaga qauyensu har had'uwarta da
Habib da aurensu da kuma abinda yarabo da ita daga gida da irin abinda yafad'a mata game da
iyayenshi sannan tafad'a mata irin zaman da take ciki ahalin yanzu, bata 6oye mata komai dan
awannan lokacin batada kamarta acikin garin Argungun.............
*Masu karatu ko kunga laifin Maryam da tafad'a ma Aunty labarin rayuwarta da halin da take
ciki😭?.*