Akhdari
Akhdari
LITTAFIN AKHDARI
A HARSHEN HAUSA
GABATARWA
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI, TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA GA
FIYAYYEN HALITTA ANNABI MUHAMMAD {SAW} DA IYALENSA, DA SAHABBANSA DA
WAƊANDA SUKA BISU DA KYAUTATAWA ZUWA RANAN SAKAMAKO.
1
2
MATNUL AKHDARI
FASULLA SHAFI
1. HUƊUBAR MAWALLAFI - - - 3
2
3
MATNUL AKHDARI
HUƊUBAR MAWALLAFI
3
4
MATNUL AKHDARI
kuma yana wajaba a gareshi da ya kiyaye dokokin Allah, kuma ya tsaya inda {Allah}
ya umurce shi da inda ya hane shi, kuma ya tuba zuwa ga Allah tsarki ya tabbata a
gareshi, tun gabanin yayi fushi dashi.
kuma sharuɗɗan tuba : yin nadama bisa laifin daya aikata, da yin niyyan ba ze sake
komawa zuwa ga wannan zunubi ba, cikin ragowar rayuwansa, da barin aikata
wannan zunibin nan take, idan ya kasance mai cuɗanya da ita.
kuma bāya halatta gareshi da ya jinkirta tuba, kuma kada yace har sai Allah ya
shirye shi, domin wannan na daga alaman taɓewa da rashin rabo da shafewar
basirah.
kuma yana wajaba a gareshi da ya kiyaye harshensa daga alfasha da abun ƙi, da
mummunan magana, da rantsuwar saki, da tsawa ga musulmi, da wulaƙanta shi,
da zaginsa, da bashi tsoro ba tare da wani haƙƙi na shari'ah ba.
1
Alamomin balaga ga namiji sun ƙunshi fara gashin mara ko mafarki ko kaiwa shekaru goma sha biyar, ga mace kuma ukun da
suka gabata sannan da fara jinin haila.
2
Imani da Allah, da mala’ikunsa, da littafansa, da manzanninsa, da rana ta ƙarshe da imani da kaddara alherinsa da sharrinsa, sannan
da nisantan shirka.
4
5
MATNUL AKHDARI
kuma yana wajaba a gareshi da ya kiyaye ganinsa daga kallon haram, kuma baya
halatta gareshi da ya kalli wani musulmi, kallon da zata cutar dashi, sai fa idan ya
kasance fasiƙi ne, yana wajaba a ƙaurace masa.
kuma yana wajaba a gareshi daya kiyaye dukkan gaɓɓansa gwargwadon iko, kuma
yayi soyayya domin Allah, yayi ƙiyayya dominsa, kuma ya yarda domin Allah, yayi
fushi dominsa, kuma yayi umurni da kyakkyawan aiki, yayi hani ga mummuna.
kuma baya halatta ga musulmi da yayi abota da fasiƙi, ko tarayya dashi, ba tare da
wata lallura ba.
kuma kada ya nemi yardan halittu wajen saɓawa mahalicci, kamar yadda Allah
tsarki ya tabbata a gareshi yace " Allah da manzansa suka fi cancanta su nemi
yardansu in sun kasance muminai. (suratut-taubah 09:62)”
1
Aibanta mutum a gabansa
2
Aibanta wani a bayansa
5
6
MATNUL AKHDARI
Manzon Allah (SAW) yace “babu biyayya ga abin halitta wajen saɓawa mahalicci”.
kuma baya halatta gareshi da ya aikata wani aiki fashe ya san hukuncin Allah
cikinsa, kuma ya tambayi malamai, yayi koyi da masu bin sunnan annabinmu
muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi. Malaman dake shiryarwa
bisa ɗa’a ga Allah, kuma suna tsoratarwa daga bin shaiɗan.
kuma kada ya yardar wa kansa abun da fallasassu suka yardar wa kansu, waɗanda
ruyawansu ta ƙare cikin rashin ɗa’a ga Allah. kaicon bakin cikinsu, kaicon tsawon
kukansu ranan alƙiyamah.
Muna rokon Allah tsarki ya tabbata a gareshi, da ya datar damu ga bin sunnan
annabinmu kuma shugabanmu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a
gareshi.
6
7
MATNUL AKHDARI
FASALI CIKIN TSARKI
Tsarki kashi biyu ne ;
1. Tsarkin kari {hadasi}
2. Tsarkin dauɗa {khabasi}.
kuma dukkansu basu inganta saida ruwa mai tsarki mai tsarkakewa, kuma shine
wanda launinsa, ko ɗanɗanonsa ko ƙanshi sa bai sawya ba da abinda ke
nisantan sa a rinjaye, kamar mai, ko man dabbobi, ko romo, ko ƙazantar
dabbobi, ko sabulu, ko dauɗa da makamantansu.
1
Ruwan mai tsarki ne mai tsarkakewa.
7
8
MATNUL AKHDARI
FASALI CIKIN NAJASA
Idan najasa ta ayyana a fili, to ana wanke
mahallinta, amma idan ta fantsama, ana
wanke tufafin dukkanta.
kuma duk wanda ya tuna da najasa alhali yana sallah, to ya yanke sallar, saifa idan
yana tsoron fitan lokacinta.
Duk wanda yayi sallah da ita (tufafi mai najasa) sannan ya tuna bayan ya idar da
sallan, to ze maimaita sallan, matuƙar lokacinta bai fita bah.
8
9
MATNUL AKHDARI
FASALI CIKIN FARILLAN ALWALA
Duk wanda ya manta farilla cikin farillan alwala, to idan ya tuna da wuri, ze wanke
gaɓan da duk abunda ya biyo bayanta, amma idan akwai jinkiri, to ze wanke gaɓan
ita kaɗai, kuma ya maimaita duk sallan daya sallata da alwalan.
9
10
MATNUL AKHDARI
Amma idan ya bar sunnah, to ze aikata ta domin sallolin dake gabatowa, ba tare da
maimaita sallolin da suka wuce ba.
Kuma duk wanda ya manta da wani lum'ah, to ze wanke ta da niyya, kuma idan
yayi sallah kafin nan, ze maimaita sallansa.
Duk wanda ya tuna da kuskuran baki da shaƙa ruwa bayan ya fara wanke fuska, to
kada ya koma ya aikata su, sai ya kammala alwalansa.
kuma yana wajaba a tsefe yatsun hannu yayin alwala, kuma tsefe yatsun ƙafa
mustahabbi ne. Yana wajaba a tsefe gemu mara cika yayin alwala koma bayan
cikakkiya, kuma yana wajaba a tsefe gemu yayin wanka koda cikakkiya ce.
10
11
MATNUL AKHDARI
Sabubba sune : bacci mai nauyi, suma, māye, hauka, sunbanta, shafan mace idan
an nufaci jin daɗi ko an ji daɗin, da shafan azzakari da tafin hannu ko da tafin
yatsu.
Duk wanda yake kokwanto kan hadasi to alwala ta wajaba a gareshi, saifa idan ya
kasance mai yawan waswasi ne, to babu komai a gareshi.
kuma shi maziyyi wani ruwa ne mai fita yayin sha'awah ƙarama ta hanyar tunani ko
kallo ko waninsa.
11
12
MATNUL AKHDARI
FASALI CIKIN ABUBUWAN DA BASU HALATTA BA GA
MARA ALWALA
Kuma bāya halatta ba ga mara alwala da yayi:
1. Sallah.
2. Ɗawafi.
3. Shafan mushafin alƙur'ani da hannunsa ko da sanda ko makamantansu.
4. Shafan allon alƙur'ani saifa ga ɗalibi ko malamin da ze kyautata shi.
Hukuncin yaro wajen shafar Alƙur'ani kamar babba yake, Amma laifin yana ga
wanda ya miƙa masa alƙur'anin.
Kuma duk wanda yayi sallah batare da alwala ba, da gangan to kafiri ne, Muna
neman tsarin Allah daga haka.
12
13
MATNUL AKHDARI
Duk wanda yayi mafarkin yana jima'i amma ba abinda ya fita daga jikinsa, to babu
komai a gareshi.
Duk wanda yaga maniyyi bushesshe a tufafinsa, baisan sanda ya fitar dashi ba, to
sai yayi wanka ya maimaita sallolin daya sallata bayan baccinsa ta ƙarshe cikin
wannan tufafin.
13
14
MATNUL AKHDARI
14
15
MATNUL AKHDARI
Duk wanda ya manta da wata lum'ah ko gaɓa cikin wankansa, to ya gaggauta zuwa
ga wanke ta yayin da ya tuna, koda bayan wata ɗaya ne, kuma ya maimaita duk
sallolin daya sallata gabaninsa.
Idan gaɓa mai lum'an ta dace da gaɓan alwala kuma an wanke ta yayin alwala, to
hakan ya isar masa.
15
16
MATNUL AKHDARI
Bāya halatta ga mai janaba da ya shiga masallaci, ko yayi karatun alƙur'ani, sai dai
aya ɗaya ko makamancinta domin neman tsari ko makamancinsa.
kuma bāya halatta ga wanda baya iya wanka da ruwan sanyi, da yayi jima'i da
matansa, har sai ya tattali nā'uran tafasa ruwa, sai fa idan mafarki yayi, to babu
matsala a gare shi.
16
17
MATNUL AKHDARI
17
18
MATNUL AKHDARI
Abubuwa dake warware taymama ɗaya suke da abubuwan dake warware alwala.
Kuma ba'a sallatan farillai guda biyu da taymama ɗaya, amma ya halatta ayi sallolin
nafila masu yawa da taymama ɗaya.
18
19
MATNUL AKHDARI
Duk wanda yayi taymama domin sallan farilla, ya halatta yayi sallan nafila da ita, da
taɓa alƙur'ani mai girma da ɗawafi, da karatun alƙur'ani idan yayi niyyan hakan
kuma ya sada ta da sallah kuma ya zanto lokacin sallan bai fita bah.
kuma ya halatta ya aikata duk abin da aka ambata a baya da taymaman sallan
nafila, amma banda sallan farilla.
Duk wanda ya sallaci sallan isha'i da taymama, ya halatta yayi sallan shafa'i da
wuturi da ita ba tare da wani jinkiri ba.
Wanda yayi taymama domin janaba to babu makawa sai yayi niyyanta.
19
20
MATNUL AKHDARI
Mātā dangane da jinin haila sun kasu gida uku, farrariya1, sababbiya2 da mai ciki.
Mafi tsawon al'adah ga fararriya kwanaki goma sha biyar ne, ga sabbabiya kuma
gwargwadon al-adanta, amma idan jinin ya cigaba da zuwa, sai ta ƙara kwanaki
uku, matuƙar bai wuce kwanaki goma sha biyar ba3.
Sannan ga mai ciki {mafi tsawon aladanta} bayan cikin yakai watanni uku, zatayi
jinin kwanaki goma sha biyar, bayan cikin yakai watanni shida zatayi jinin kwanaki
ishirin.
Idan jinin ya yayyanke, sai ta harhaɗa kwanakin har sai al'adanta ya cika.
Kuma sallah da azumi da ɗawafi basu halatta ba ga mai haila, da taɓa alƙur'ani mai
girma, da shiga masallaci, kuma zata rama azumi amma banda sallah. kuma ya
halatta ta karanta Alƙur'ani.
1
Wacca ta fara jinin haila
2
Wacca ta saba yin haila
3
Misali mai al’adar kwanaki biyar sai ta kara kwanaki uku yakai kwanaki takwas, idan ya wuce haka ya zama jinin ciwo, mai aladar
kwanaki goma sha uku sai ta kara kwanaki biyu.
20
21
MATNUL AKHDARI
Amma, Idan jinin ya ɗauke kafin hakan, koda a ranan haihuwa ne, zatayi wanka ta
fara sallah, sannan idan jinin ya dawo, kuma tazaransa da jinin farko yakai kwanaki
goma sha biyar, to sabon jinin haila ne, idan bai kai kwanaki goma shabiyar ba, to
zata haɗashi da jinin farko {jinin biki} domin cigabansa ne.
21
22
MATNUL AKHDARI
Lokaci mukhtari na sallan asubah na farawa daga ɓullowar alfijr zuwa bayyanan
haske maɗaukakiya, lalurinsa kuma zuwa ɓullowan rana.
Duk sallan da ba'a yita a lokacinta ba, kamar yadda ya gabata, to ta zama sallan
ramuwa.
Wanda ya jinkirta sallah har lokacinta ta fita to yana da zunubi mai girma, saifa
idan ya kasance bisa mantuwa ne ko bacci yayi.
1
Lokaci mukhtari shine lokacin farko daya dace ayi sallan farilla
2
Idan rana ta wuce tsakiyan sama
3
Lokaci laluri shine lokacin dake farawa bayan ƙarewan mukhtari, Jinkirta sallah zuwa lokaci laluri bai halatta ba, matukar babu uzuri
22
23
MATNUL AKHDARI
Ba'a yin sallan nafila bayan sallan asuba har sai rana ta ɗaukaka, haka bayan sallan
la'asar zuwa sallan magriba, da bayan ɓullowan alfijir saifa sallan nafilan dare ga
wanda bacci ta rinjaye shi.
kuma {ba’a nafila} daga lokacinda limami ya zauna kan mimbari ranan juma'a, da
bayan sallan juma'a har sai ya fita daga masallaci.
23
24
MATNUL AKHDARI
kuma makruhi1 ne yin sallah cikin dogon wando, face akwai wani {riga ko mayafi} a
samansa.
Duk wanda tufafinsa ta samu najasa, kuma bai samu wata tufan da zeyi sallah da
ita bah, kuma bai samu ruwan da ze wanke tufafin ba, ko baida tufafin da zesa
yayin wanke mai najasan, kuma yaji tsoron fitan lokaci, to yayi sallah da tufafi mai
najasan.
Kuma baya halatta a jinkirta sallah daga lokacinta saboda rashin tsarki, kuma duk
wanda ya aikata haka ya saɓawa mahaliccinsa.
1
Makruhi shine aikin da babu zunubi ga wanda ya aikata, amma akwai lada ga wanda bai aikata ba.
24
25
MATNUL AKHDARI
Duk wanda bai samu tufafin da ze suturce alauran sa ba, to yayi sallan tsirara,
kuma duk wanda yayi kuskuren alƙiblah, to ze maimaita sallan idan lokacinta bai
gushe ba.
kuma dukkan hukuncin da zesa a maimaita sallah cikin lokaci, to hukuncin baya sa
a maimaita sallan ramuwa da ta nafila.
25
26
MATNUL AKHDARI
1
Daidaita a tsaye bayan ɗagowa daga ruku’u da daidaita a zaune bayan ɗagowa daga sujada
26
27
MATNUL AKHDARI
1. Tada Iƙaamah
2. Karatun surah
3. Tsayuwa dominta
4. Asirtawa inda ake asirtawa
5. Bayyanawa inda ake bayyanawa
6. Cewa sami'allahu liman hamida
7. Dukkan kabbara sunnah ce face kabbaran harama
8. Tahiyyu biyu
9. Zama dominsu
10. Gabatarda karatun fatiha kafin surah
11. Sallama ta biyu da ta uku ga mamu,
12. Kuma bayyana sallama wajibi ne
13. Salati ga Manzon Allah (SAW) a tahiyan ƙarshe.
14. Sujada bisa hanci da tafukan hannaye da gwiwoyi da yatsun dugadugai.
15. Da sanya shamaki ga liman da mai sallah shi kaɗai, kuma mafi ƙarancin
shamakin ta zanto mai kaurin sandan mashi, tsawonta kuma zira'i ɗaya, sannan ta
zanto mai tsarki, tabbatacciya ba mai kawo waswasi a rai ba.
27
28
MATNUL AKHDARI
1
Māmu shine mai bin liman sallah
28
29
MATNUL AKHDARI
MAKRUHAN SALLAH
1
Khushu’i ya ƙunshi ƙanƙan da kai da tsoron allah da natsuwa da maida hankali a sallah.
29
30
MATNUL AKHDARI
30
31
MATNUL AKHDARI
FASALI CIKIN HALAYEN SALLOLIN FARILLA
Sallan farilla tana da halaye bakwai ababen jerantawa wanda ake aikatawa cikinsu,
huɗu cikinsu wajibi ne {jerantasu}, uku kuma mustahabbi ne, halaye huɗun daya
wajaba a jerantasu :
Jerantawa tsakanin waɗannan halaye huɗu wajibi ne, idan mai sallah nada ikon
sallah a wani hali sannan yayi sallar a wani hali na daban, to sallansa ta ɓaci.
Halaye ukun da mustahabbi ne jerantasu, shine duk wanda bai iya sallah a halaye
huɗun da suka gabata yayin sallan yana kwance a ɓangaren jikinsa ta dama,
sannan a ɓangaren hagu, sannan a gadon bayansa.
Idan ya sassaɓa cikin halaye ukun nan, sallansa bata ɓaci bah.
Kuma dogaron dake lalata sallah shine dogaron da masallaci ze faɗi idan an cire
madogaran, amma idan baze faɗi ba, to wannan dogaron makruhi ne.
31
32
MATNUL AKHDARI
Amma gameda sallan nafila, ya hallatta mai ikon tsayuwa ya sallaceta a zaune,
saidai yanada rabin ladan wanda yayi a tsaye, kuma ya hallata ya fara sallan a
zaune sannan ya miƙe, ko ya fara a tsaye sannan ya zauna, saifa idan ya shigeta da
niyyan tsayuwa, a wannan halin zama baya halatta.
32
33
MATNUL AKHDARI
Kuma baya halatta ayi sakaci wajen ramawa, duk wanda a duk rana yake rama
sallan kwanaki biyar1 to ba mai sakaci bane.
kuma ze rama sallan ne bisa ga halin data kuɓuce masa, idan ta kasance sallan
zaman gida, ze ramata a matsayin sallan zaman gida, idan ta kasance sallan halin
tafiya ce, ze ramata a matsayin sallan halin tafiya, duk ɗaya ne mazaunin gida yake
ko matafiyi yayin rama sallan.
Kuma jerantawa tsakanin hādirai {sallar wannan lokacin} da rama salloli kaɗan
wajibi ne, kuma salloli kaɗan sune salloli huɗu ko ƙasa da haka.
Saboda haka duk wanda ze rama salloli huɗu kaɗai ko ƙasa da haka, wajibi ne ya
fara rama sallolin kafin aikata sallan wannan lokacin, koda lokacin sallan ze fita.
Kuma rama sallah ta halatta a dukkan lokuta na rana da yini, da yayin ɓullowar
rana, da lokacin faɗuwanta.
1
Salloli ashirin da biyar
33
34
MATNUL AKHDARI
Kuma wanda ze rama sallah baze yi sallan nafilah ba, haka sallan walha, da sallan
dare a ramadan.
Duk {sallolin nafila} basu halatta gareshi ba face shafa’i da wuturi, da sallan idi
biyu, da sallan kisfewar rana, da sallan neman ruwa.
Kuma ya halatta ga masu rama sallah dasu rama cikin jam’i, idan halin sallolinsu ya
zanto irin ɗaya.
Idan mai rama sallah ya manta adadin sallolin da ake binsa, to zeyi ta ramawa
adadi mai yawa har ya zanto baida kokwanto {cewa wanda ya sallata sunfi wanda
ake binsa yawa}.
34
35
MATNUL AKHDARI
Ga duk ƙarin da akayi a sallah, za’ayi sujjadu biyu bayan sallama, sai a sake tahiya,
sannan ayi wata sallaman. {sujjadan ba’adi}
Kuma duk wanda yayi ragi kuma yayi ƙari a sallah, to zeyi sujjadan ƙabli.
Kuma duk wanda ya manta da sujjadan ƙabli har yayi sallama, to sai yayi sujjadun
bayan sallama idan babu jinkiri, amma idan an daɗe ko ya fita daga masallaci, to
sujjadan ta lalace, kuma sallan ma ta lalace matuƙar sunnoni uku ko sama da haka
ya rage, idan ba haka ba, to sallan bata lalace ba.
Duk wanda ya manta da sujjadan ba’adi, to ze aikata ta {duk sadda ya tuna} koda
an shekara.
Duk wanda ya rage farilla a sallansa, to sujjadan rafkanuwa bata wadatarwa, kuma
duk wanda ya rage mustahabbi to babu sujjadan rafkanuwa a gareshi.
1
Sujjadar rafkanuwa itace sujjadar ƙabli ko ba’adi
35
36
MATNUL AKHDARI
Ba’a aikata sujjadan ƙabli sai an rage sunnoni biyu ko sama da haka, amma sunnah
ɗaya ba’a mata sujjadar ƙabli, saifa wajen asirta karatu da bayyanawa.
Duk wanda ya asirta karatu inda ake bayyanawa to zeyi sujjadan ƙabli, duk wanda
ya bayyana inda ake asirtawa, ze yi sujjadan ba’adi.
Kuma duk wanda yayi magana a sallah da rafkanuwa to zeyi sujjadan ba’adi.
Duk wanda yayi sallama yayin da yayi raka’o’i biyu bisa rafkanuwa, to zeyi sujjadan
ba’adi {bayan ya cike sallansa}.
Duk wanda ya ƙara raka’a ɗaya ko biyu a sallansa {da rafkanuwa} zeyi sujjadan
ba’adi, duk wanda ya ƙara raka’o’i a salla adadi tamkar raka’o’in sallan, to sallansa
ta lalace.
Duk wanda yayi kokwanton cikan sallansa, to yazo da abinda yake kokwanto a
cikinta.
Kuma duk kokwanto gameda ragi a salla kaman tabbatar dashi ne, saboda haka
duk wanda yayi kokwanto kan rage raka’ah ko sujjada, to ze aikata ta sannan yayi
sujjadan ba’adi.
36
37
MATNUL AKHDARI
Duk wanda yayi kokwanto kan sallama, to yayi sallaman {yayin daya tuna} kuma
babu sujjada a gareshi idan babu jinkiri, amma idan an daɗe to sallan ta lalace.
Kuma mai yawan waswasi a sallah zeyi watsi da waswasinsa, kuma baze aikata
abinda yake waswasi kansa ba, amma zeyi sujjadan ba’adi, duk ɗaya ne yayi
kokwanto ne kan ƙari ko ragi.
Duk wanda ya bayyana ƙunūtu babu sujjada a gareshi, saidai yin haka da gangan
makruhi ne.
Kuma wanda ya karanta sura a raka’o’i biyun ƙarshe babu komai a gareshi.
Kuma duk wanda ya saurari ambaton annabi muhammad (SAW) alhali yana sallah
sannan yayi masa salati, to babu komai a gareshi koda yayi hakan ne da gangan ko
da mantuwa, ko a tsaye yake, ko a zaune.
Kuma duk wanda ya karanta surori biyu ko sama da haka a raka’a ɗaya, ko ya fita
daga wata surah zuwa wata, ko yayi ruku’u kafin kammala karatun surah to babu
komai a gareshi cikin dukkan halayen.
Duk wanda yayi nuni da yatsa ko kansa alhali yana sallah to babu komai a gareshi.
37
38
MATNUL AKHDARI
Kuma duk wanda ya maimaita fatiha da rafkanuwa, to zeyi sujjadan ba’adi, idan
kuma da gangan ne to sallansa ta ɓaci ga zance mafi rinjaye.
Duk wanda ya tuna da karatun surah bayan ya durƙusa zuwa ruku’u, to kada ya
koma yin karatun, {ya cigaba da sallansa}
Kuma duk wanda yayi kuskuren asirtawa ko bayyanawa {sannan ya tuna} kafin
ruku’u, to idan hakan ta kasance ga surah ce kaɗai sai ya maimaita karatun suran,
kuma babu sujjada a gareshi, amma idan ya kasance da karatun fatiha to ze
maimaita sannan yayi sujjadan ba’adi.
Idan kuma yayi ruku’u to {ya cigaba da sallansa} sai yayi sujjadan ƙabli idan
asirtawa yayi wajen bayyanawa, ko sujjadan ba’adi idan bayyanawa yayi wajen
asirtawa, koda ko surace kaɗai ko fatiha.
Kuma duk wanda yayi dariya a sallah to sallansa ta ɓaci, duk ɗaya ne da gangan
yayi koda rafkanuwa, kuma babu mai dariya a sallah face rafkananne, mai wasa,
Shi mumini idan ya himmatu da yin sallah, yana nisantar da zuciyansa daga komai
koma bayan Allah, kuma yana barin tunanin duniya da abunda ke cikinta, ya
halarto da zuciyansa ga buwayan Allah, da girmansa, kuma ya raurawar da
zuciyansa, ya tsoratar da kansa kan girman Allah, wanda girmansa ya ɗaukaka,
wannan itace sallan masu taƙawah {tsoron Allah}!.
38
39
MATNUL AKHDARI
Kuma babu laifi ga wanda yayi murmushi, kuma kukan mai tsoron Allah abun
gafartawa ne, kuma duk wanda yayi sauraro kaɗan ga mai magana yayin sallah to
babu komai a gareshi.
Duk wanda ya miƙe a raka’ah ta biyu {maimakon zaman tahiya} to idan ya tuna
kafin hannayensa da gwiwoyinsa subar ƙasa, to sai ya zauna kuma babu sujjada a
gareshi.
Duk wanda yayi busa cikin salla da rafkanuwa, zeyi sujjadar ba’adi. Idan kuma da
gangan ne to sallansa ta ɓaci.
Duk wadda yayi atishawa a sallah to kada ya shagaltu da faɗin Alhamdulillah, kuma
kada ya maida ma wanda ya gaida shi {wanda yace masa Yarhamakallahu}. Amma
idan yace Alhamdulillah, babu matsala a gareshi.
Kuma duk wanda yayi hamma cikin sallah to ya rufe bakinsa, kuma kada yayi tofi
sai a tufafinsa kuma ba tare da fidda sautin harafi ba.
39
40
MATNUL AKHDARI
Duk wanda yake kokwanton hadasi ko najasa yayin sallah; sannan yayi tunani na
lokaci ƙanƙani sai ya tabbatar da tsarkinsa, to babu matsala a gareshi.
Kuma duk wanda yayi waiwaye a sallah da rafkanuwa to babu matsala a gareshi,
amma yin haka da gangan makruhi ne, idan kuma ya juya wa alƙibla baya to ze
maimaita sallan {domin ta lalace}.
Duk wanda yayi sallah da tufafin alhariri, ko da zoben zinari, ko yayi sata yayin
salla, ko yayi kallo zuwa ga haram, to shi mai saɓo ne, amma sallansa tayi.
Kuma duk wanda yayi kuskuren karanta alƙur’ani, da kalman da bata cikin ƙur’ani,
to zeyi sujjadan ba’adi, idan akwai kalman a ƙur’ani to babu sujjada a gareshi saifa
idan ya sawya lafazin kalmar ko ya lalata ma’ananta, sai yayi sujjadan ba’adi.
Duk wanda yayi gyangyaɗi yayin sallah, to babu sujjada a gareshi, amma idan
baccinsa tayi nauyi to ze maimaita alwala da sallan.
Kuma nishin mara lafiya a sallah abun yafewa ne, kuma gyaran murya domin
lallura abun yafewa ne, idan kuma domin fahimtarwa ne to makruhi ne, amma
bata lalata sallah.
Duk wanda aka ƙwala masa kira sai yace subhanallah, to haka makruhi ne, amma
sallansa ta inganta.
40
41
MATNUL AKHDARI
Kuma duk wanda ya tsaya cikin wata ayah, kuma babu wanda ya tuna masa, to ya
barta ya shiga ayah ta gaba, idan ya kasa karanta ayan dake gaba, to yayi ruku’u
amma kada ya buɗe mushafin alƙur’ani ya duba, saifa idan hakan ta kasance cikin
suratul fatiha domin babu makawa sai an karanceta, da mushafin alƙur’ani ko
waninta.
Idan ya bar ayah {a suratul fatiha} da mantuwa, zeyi sujjadar ƙabli, idan kuma ya
bar sama da ayah, to sallansa ta lalace.
Kuma duk wanda yayi tunanin duniya kaɗan cikin sallah, to ladansa ta ragu amma
sallansa bata ɓaci ba.
Kuma duk wanda ya ture mai wucewa ta gabansa, ko yayi sujjada a ɓangaren
goshinsa, ko yayi sujjada a naɗi ɗaya ko biyu na rawaninsa, to babu matsala a
gareshi.
41
42
MATNUL AKHDARI
Kuma Liman na ɗauke rafkanuwan mᾱmu1, saifa idan {rafkanuwan) ta kasance kan
farillah.
Idan mᾱmu ya rafkana baiyi ruku’u bah, ko an matse shi, ko yana gyangyaɗi
{angaje} sanda akayi, kuma hakan ya kasance ba’a raka’an farko ba, to idan ya
tsammaci rizƙan liman kafin ɗagowansa daga sujjada ta biyu, yayi ruku’u ya cigaba
da sallan.2
Amma idan bai tsammaci rizƙan limamin bah, to yayi watsi da raka’an, ya cigaba da
bin limaminsa, saiya rama raka’ah ɗaya bayan sallaman limamin a maimakonta.
Kuma idan ya rafkana baiyi sujjada ba, ko yayi gyangyaɗi ko an matse shi, har liman
ya miƙe ga sabuwar raka’a, to sai yayi sujjadan idan ya tsammaci rizƙan limamin
kafin yayi ruku’u, amma idan bai tsammaci hakan ba, to yayi watsi wa wannan
raka’an ya miƙe ya cigaba da bin limaminsa, sannan ya rama raka’ah ɗaya bayan
sallaman limamin.
Kuma cikin halayen da suka gabata {inda mᾱmu ze rama raka’ah ɗaya}, to babu
sujjadan rafkanuwa a gareshi, saifa idan ya kasance kokwanto yayi kan ruku’un ko
sujjadan, to zeyi sujjadan ba’adi.
1
Mᾱmu shine mai bin liman sallah.
2
Idan haka ta faru a raka’an farko to sallan ta lalace, sai mamun ya sake kabbaran harama yabi limaminsa.
42
43
MATNUL AKHDARI
Kuma duk wanda maciji ko kunama sukazo masa alhali yana sallah, saiya kashe, to
babu matsala a gareshi, saifa idan ya ɗauki lokaci mai tsawo ko ya juya baya ga
alƙiblah, to ze yanke sallah {domin ta lalace}.
Kuma duk wanda ke kokwanto shin yana sallan wuturi ne ko raka’a ta biyun
shafa’i, to ya maidata raka’a ta biyun shafa’i, kuma zeyi sujjadan ba’adi sannan yayi
wuturi.
Kuma duk wanda yayi magana tsakanin shafa’i da wuturi da mantuwa to babu
matsala a gareshi, amma yin haka da gangan makruhi ne.
Kuma ga masbuƙi1, idan bai samu raka’a ko ɗaya ba tare da liman, to kada yayi
sujjadan ƙabli ko ba’adi tare dashi, Idan kuma yayi sujjadan to sallansa ta lalace.
Idan kuma ya samu raka’ah cikakka ko sama da haka {tare da liman}, to zeyi
sujjadan ƙabli tare dashi, sannan ya jinkirta ba’adi har sai ya ramo raka’o’in daya
rasa, sannan yayi sujjadan bayan sallama. Idan yayi sujjadan ba’adi kafin cike
sallansa da gangan, to sallan ta lalace.
Idan masbuƙi yayi rafkanuwa bayan sallaman limami to hukuncinsa ɗaya yake da
mai sallah shi kaɗai.
1
Mᾱmun daya rasa wasu raka’o’i a sallah.
43
44
MATNUL AKHDARI
Kuma idan masbuƙi ya samu sujjadan ba’adi ta janibin limaminsa, sannan sujjadan
ƙabli daga wajensa, to sujjadan ƙablin ta wadatar.
Kuma duk wanda ya manta da ruku’u sannan ya tuna yayin sujjada, to ze miƙe
tsaye, sannan anso ya maimaita karatun ƙur’ani, sannan yayi ruku’u ya cigaba da
sallansa, sai yayi sujjadan ba’adi.
Kuma duk wanda ya manta da sujada ɗaya, sannan ya tuna bayan miƙewa {ga
sabuwar raka’ah}, to sai ya koma a zaune yayi sujjadan, saifa idan ya kasance yayi
zama kafin miƙewansa, to baze sake zaman ba.
Idan ya tuna da sujjada bayan ya ɗago kansa daga ruku’un raka’an dake gaba da
ita, to ya cigaba da sallansa, kada yayi sujjadan, sannan yayi watsi da wannan
raka’an ya ƙara raka’ah ɗaya, yana mai gini kan abinda ya sallata, Kuma zeyi
sujjadan ƙabli idan mantuwan ta kasance ne cikin raka’o’i biyun farko bayan ƙulla
raka’ah ta uku.
Zeyi sujjadar ba’adi idan bata kasance cikin raka’o’in biyun farko bah, ko ta kasance
cikinsu amma ya tuna kafin ƙulla raka’ah ta uku domin karatun fatiha da surah
basu kuɓuce ba.
44
45
MATNUL AKHDARI
Kuma duk wanda yayi sallama alhali yana kokwanton cikan sallansa, to sallan ta
ɓaci.
kuma rafkanuwa a sallan ramako ɗaya yake da rafkanuwa a sallan cikin lokaci.
Rafkanuwa cikin sallan farilla daya yake da rafkanuwa cikin sallan nafila, saifa a
wurare shida
1. Karatun fatiha
2. Karatun surah
3. Bayyana karatu wajen asirtawa
4. Asirta karatu wajen bayyanawa
5. ƙarin raka’ah
6. Mantawa da wasu rukannan sallah
Ga duk wanda ya manta karatun fatiha a sallan nafila sannan ya tuna bayan
ɗagowa daga ruku’u to ya cigaba da sallansa, sannan yayi sujjadan ƙabli, saɓanin
sallan farilla inda zeyi watsi da wannan raka’an ya kawo wata maimakonta, kuma
sujjadan rafkanuwansa ze kasance kamar yadda muka ambata a mas’alan wanda
ya manta da sujjada.
45
46
MATNUL AKHDARI
Kuma duk wanda ya miƙe ga raka’ah ta uku a sallan nafila, idan ya tuna kafin yin
ruku’u, to ya zauna ya sallame sannan yayi sujjadan ba’adi.
Idan bai tuna ba har yayi ruku’u to ya ƙara raka’ah ta huɗu sannan yayi sujjadan
ƙabli {domin ya rage sallaman raka’o’i biyun farko}.
Saɓanin sallar farilla, inda ze zauna duk lokacin daya tuna, yayi sallama, sannan
yayi sujjadan ba’adi.
Kuma duk wanda ya manta da wani rukuni cikin sallan nafila, kaman ruku’u ko
sujjada, kuma bai tuna ba har yayi sallama da lokaci mai tsawo, to baze maimaita
sallan ba, saɓanin sallan farilla inda ze maimaita komin tsawon lokaci.
Kuma duk wanda ya yanke sallan nafila da gangan, ko ya bar raka’ah ko sujjada da
gangan, to ze maimaita ta komin tsawon lokaci.
Kuma duk wanda yayi ajiyan zuciya a sallah, to babu matsala gareshi, saifa idan
yayi furuci da wani harafi {sai yayi sujjadan ba’adi idan da rafkanuwa ne}.
46
47
MATNUL AKHDARI
Idan limaminka ya miƙe bayan yin sujjada ɗaya, to kace subhanallah kada ka miƙe
tare dashi, saifa idan kaji tsoron ze ƙulla raka’ah, {ze ɗago daga ruku’u}, to sai ka
miƙe ka bishi, {raka’anku ta farko wacca ba’ayi mata sujada ba ta baci, saboda haka
ta biyun ta zama ta farko} sannan kada ka zauna tare dashi cikin raka’ansa ta biyu
{raka’ar da limamin ya tsammace ta ta biyu wanda a haƙiƙani itace ta farko} ko na
huɗunsa {raka’ar da limamin ya tsammace ta ta huɗu amma a haƙiƙani itace ta
uku}. Idan yayi sallama to ka ƙara raka’ah ɗaya maimakon raka’ar da kayi watsi da
ita, sannan kayi sujjadan ƙabli.
Amma idan kun kasance cikin jam’i to abinda akafi so shine ku gabatarda ɗaya
daga cikinku ya limance ku wajen cike sallan.
Idan limami zeyi sujjada ta uku to kace subhanallah, kada kayi sujjadar tare dashi,
kuma idan limami ya miƙe ga raka’ah ta biyar, to wajibi ne ga duk wanda yake da
yaƙini ko kokwanton hakan daya bishi, wanda kuma yakeda yaƙinin ƙari ce to
wajibi ne ya zauna. Idan wanda ya wajaba ya miƙe ya zauna, ko wanda ya wajaba
ya zauna ya miƙe, to sallansa ta lalace.
Kuma idan limami yayi sallama kafin cike sallansa, waɗanda ke bayansu sai suce
subhanallah!, idan limamin ya gamsu dasu to sai ya cike sallan, idan kuma yana
kokwanto sai ya tambayi aadilai biyu, kuma ya halatta suyi magana.
Idan limamin nada yaƙinin cikan sallan, to yayi watsi da hukuncin aadilan ya
sallame sallan, saifa idan mutane {masu ganin sallar bai cika ba} suna da yawa, to
sai yayi watsi da yaƙininsa, ya koma zuwaga fahimtansu.
47
48
MATNUL AKHDARI
المصادر و المراجع
Email : [email protected]
48