0% found this document useful (0 votes)
26 views123 pages

A Cikin Ido

The document is a narrative that explores the complexities of relationships, emotions, and societal expectations within a family setting. It highlights the struggles of characters dealing with love, jealousy, and the impact of illness on family dynamics. The dialogue-driven format reveals intimate moments and conflicts among the characters, particularly focusing on Marhaba and her interactions with others in her life.

Uploaded by

fannahsaad
Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as DOCX, PDF, TXT or read online on Scribd
0% found this document useful (0 votes)
26 views123 pages

A Cikin Ido

The document is a narrative that explores the complexities of relationships, emotions, and societal expectations within a family setting. It highlights the struggles of characters dealing with love, jealousy, and the impact of illness on family dynamics. The dialogue-driven format reveals intimate moments and conflicts among the characters, particularly focusing on Marhaba and her interactions with others in her life.

Uploaded by

fannahsaad
Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as DOCX, PDF, TXT or read online on Scribd
You are on page 1/ 123

[6/17, 12:40 PM] Ummulhair S Panisau: A CIKIN IDO...

Na

Ummulkhairi S Panisau.

(Khairat Up)

Karamci Writers association.

(Karamci shi ne tushen mu'amala tagari.)

paid book

freepg 1.

"Ku kam kuna bani sha'awa kamar ba auren haɗi aka yi muku ba duk kun kwantar da hankalinku ku haɗe
kanku kun burgeni fa kawata"

"Aisha baki san zafin ƙiyayya ba , da ace kin san zafin ƙiyayya da baki yi mamakin ganin na kwantar da
hankalina ba Wallahi Wallahi bana bin ki bashin rantsuwa ko ba da bana son Ya Alee ba zan nuna masa
ƙiyayya ba saboda na san zafinta." Tuni idanuwata suka cika da hawaye ƙiris suke jira su zubo ƙasa amma
ƙoƙarin hana su zubowan take ajiyar zuciya ta sauke ta miƙe tsaye tace mata.

"Ki zauna sosai Aisha bara na kawo miki abinci nasan kin ɗauko hanya."

Aisha ta riƙo hannunta hakan ya sa ta juyo da sauri tana jiran ƙarin bayani.
Marhaba na jima ina lura da wasu abubuwa a tattare dake ni na sani akwai abinda yake damunki akwai
lauje ciki naɗi dan girman Allah ina son sanin asalin damuwarki ina ji a jikina akwai darasin da zan tsinta
a cikin labarin rayuwarku.

Komawa nayi na zauna a kan kujera na saki kukan da nake riƙewa tun ɗazu bata hana ni ba nima bana
son a hana nin saboda ina da buƙatar hakan saidai hakan ba zai saka na fallasa ciwon da yake cikin
zuciyata ba wani irin ciwo ne wanda ya jima a lullube cikin ƙirjina labule ne wanda bana son na yaye shi
saboda banƙaɗo sirrin ma yana ƙara saka ni cikin tashin hankali bana mantawa da Abbana bare Ammin
mu irin......

"Kar ki damu Marhaba wata rana za ki bani labarin."

"Nagode da kika fahimata" na gaya mata.

Ɗazu baƙi kika yi ne na yo aike amma baki ji sai dawo min da sautun aka yi

Kayi haƙuri banji ba kuma ba ma baƙi bane ƙawata Aisha Sambo ce ta zo taga wuri kasan bata zo kawo
amarya ba.

Duk da haka kina saka ido kan lamarin gida da Allah duk sai na damu da ya dawo da sautun.

Kanta a ƙasa ta na murza yan yatsunta tace "In Sha Allah zan kiyaye."

"Yauwa."

Daga haka ya shige cikin ɗaƙin da ke gefe. Marhaba ko bin bayansa tayi da kallo kafin ta shiga madafi ta
ɗauƙo kayan abincin ta jera masa a ƙasa yadda ta saba kafin ta bishi ɗaƙin.
Yana cire riga ta shiga hakan ya saka tayi baya da sauri ta juya tana runtse idanuwanta gam kafin tace
"Kayi haƙuri ban san baka gama ba." Ta faɗa bakinta na karkarwa.

Bai damu ba ya taɓe bakinsa yace "Kar ki damu ya aka yi?"

Dama na shirya abincin ne shi ne nazo na kira ka.

To ina zuwa bara nayi alwala naga lokacin sallah ya kusa ki fito min da farar jallabiya ina zuwa.

"To" kawai tace.

Yana shiga ta sauke ajiyar zuciya ta buɗe wardrobe ta ɗauko masa rigar ta ajiye bayan ta fesa turare a jiki
harda short ta ɗauƙo masa ta fita da sauri jin yana ƙoƙarin fitowa.

Yan fitowa yaga gilmawarta murmushi yayi fili yace "Silly girl".

Tan fita ta zauna a kan kujera ta kunna tv amma sai ta jona karatun Qur'ani gashi tana san ta shiga bayi
saboda cikinta da ya murɗa amma dole sai ta gama zuba masa komai tukuna amma sarkin sai jimawa
wajan shiryawa. Cikin ranta ko cewa tayi "Mutum kamar mace sai iyayi." yadda take yi da fuskarta ya
saka ya gane cewa gungunai take yi masa a zuciya amma sai ya maze ya zauna yace "Bismillah" wato ta
zuba masa kenan.

Cike da nutsuwa take zuba masa abincin daidai saboda ta lura ba mai ci bane sosai.

Anjima Aminu zai zo da matarsa sai ki kasance cikin shiri in akwai abin da kike bukata na tarbarsu ki
gaya min sai na kawo miki.
Babu abin da nake buƙata.

Zanje masallaci na dawo.

A dawo lafiya.

Allah Ya sa.

Amin.

Yana fita ta tattare komai ta kai kicin da sauri ta shiga ɗaƙi ta afka banɗaki saboda bayan gida da ya
dameta.

Tana fitowa ta koma kicin ta dan ƙwaba fulawa ta yi samosa kaɗan ta dafa zubo da kayan ƙamshi ta juye
a jug ta sa a fridge.

Ta soya taliya ta juye a fridge ta soya nama tayi peppe meat ta ajiye kan dinning.

Kan ya dawo ta gama komai kuma bai dawo da wuri bama sai bayan magariba lokacin da ya dawo ma
tana banɗaki tana wanka.

Kai tsaye ya isa dinning din ya duba abin da tayi yako yi mamaki kuma ya ji dadin hakan. Wayarsa ce ta
kaste shi ya ɗauƙo yaga mai kiran nasa. A fili ya furta "Sabreen" ɗauka yayi ya gyara tsayuwarsa yana
goga yatsansa kan tsinin hancinsa.

"Dear na karfe nawa yanzu?"


agogo ya kalla yace "Ƙarfe nawa kika kirani ki tambaya?"

Cike da shagwaɓa tace dashi "Amma ka san yau tun safe da muka yi waya bamu kuma ba."

Kiyi haƙuri na ɗan shiga busy ne amma kina raina.

Kawai dai kayi amarya ka soma sauya hali amma dai ina daɗa yi maka tuni banda saɓa alkawari kar ka
manta da batun ƙauna.

Hum Sabreen kenan zan kira ki anjima ko yanzu Aminu ke kirana mun yi zai zo ne shi da Matarsa.

Kawai ka fito a mutum kace na dameka.

Matsalata dake kenan san hayaniya wani lokacin wane irin kin dameni ai kinsan waye ni ai in kin dameni
da tuni na ajiye wayar ko?

To kayi haƙuri sai anjima masoyina.

"Mu jima lafiya zan kiraki da kaina please?" Ya faɗa da alamun roƙo.

Daidai lokacin da Marhaba ta fito sai taji wani banbarakwai amma sai ta fuske ta ajiye mayafinta kan
kujera na abayar ta nufi ƙofa zata buɗe saboda bugawar da ake yi cikin taku biyu ya isa inda take ya riko
hannunta yana zare mata ido ya ajiye wayar cikin aljihunsa ya matse fuska yace "Shashanci ne zai sa ki
buɗe ƙofa ba tare da kin saka lulluɓi ba".

A sanyayye tace "Ka yi haƙuri na manta ne."


Da ido ya yi mata nu ni da ta ɗauki mayafin ta yafa shi kuma ya isa ya buɗe ƙofar.

Aminu dake ɗan tsokana ne ya miƙa masa hannu yace "Ya ALEE har zamu juya ashe kuna nan."

"Da kun juya ɗin ai." Ya faɗa yana basu hanya don su shiga ciki. Da fara'a ta karbesu tayi masu tayin
ruwa ta zauna suka kara gaisawa suna raha abin su Ya Alee jefi-jefi yake shiga hirar tasu yana danna
waya hira suke da Sabreen suna charting shi sa ma hankalinsa baya kansu sosai.

Yaya Aminu ku tashi muje ku ci abinci dan Allah.

Auntynmu ai bamu isa muki tayin matar yaya ba "Bismillah Babe" ya fada yana lauya hannusa na dama
alamar tayi gaba tana murmushi ta yi gaban ya bita ya ja mata kujerar kafin ya zauna shi ma snacks din
ta fara zuba musu da zobon ta zauna ita ma suna gamawa ta zuba musu taliyar a plate a plate daya suka
ci abincin sai suka burge Marhaba taji daman ita da Ya Aliyu ne

Hirarsu kawai suke yi matar ma ke jin kunyar abubuwan da Aminun keyi dan shi mutum ne me
buɗaɗɗan hali bashi da miskilanci irin na Ya Alee.

Sai da yaga sun gama ya tashi ya shiga ɗaƙi ya barsu. Ruwa ya kuma watsawa ya fito kenan ta kuma
shigowa wannan karan bayan tayi sallama ya bata izinin shiga.

Amma me tana shiga tayi kyakyawan gamo domin babu riga jikinsa ,sai ta kulle idonta shi ko ba kallonta
yake yi ba dama yace "Yaya?." Ya karasa saka singiletinsa.

"Dama ...dama zasu tafi wai".

"To ina zuwa."

Ta karasa ficewa daga ɗakin gaba ɗaya ta dafe kirji kafin a hankali tace "Wanan baya jin kunya."
Nata ɗakin ta shiga ta zuba mata kayan kwalliya ta ta fita.

Har ya fito yana sallama dasu itama sai tayi musu sallama ta bawa Husna ledar hade da yi mata godiya.

Aminu yaji dadi sosai shi ma ya bata dubu biyar yace sun gode tukuicin abinci ne ya yi dadi sosai.

Tayi masa godiya suka jera duk su hudun suna isa koma ya kalleta yayi mata alamar ta tsaya iya nan
tsayawar tayi tace "Ya Aminu Aunty Husna sai da safe mun gode da ziyara sai munzo."

Suka haɗa baki wajan cewa "Muna jiranki Matar Yaya."

[6/17, 12:40 PM] Ummulhair S Panisau: A CIKIN IDO....

Na

Ummulkhairi S Panisau.

(Khairat UP)

Karamci Writers Association.

(karamci shi ne tushen mu'amala tagari.)

2
"Mar'yam manyan yan rigima kenan." Abba ya faɗa a fili yana shafa sajensa yana murmushi in ya tuna
da wahalar soyayyar da ya sha da soyayyar Mar'yam wadda har yau yana shan wahalar soyayyar ta a
ƙirjinsa babu ya rasa yadda zai yi da ƙaunarta da ya huda masa duk wani sashi da loko na ƙirjinsa da ace
zai iya cire soyayyarta a zuciyarsa da tuni ya cire yayi wulli da ita amma ina son ya riga da yayi masa
bazata yayi masa kamun kazar kuku. Hawayen da ya saba zubarwa ya shafe daga fuskarsa a ko yaushe in
ya tuna rayuwarsa da uwargidansa Mar'yam baya kwana da lafiya komai ta sa masa na ciwo wanda ba
zai taɓa warkewa daga cikinsa ba ba zai yi mamaki ba yau in aka cewa Mar'yam ya mutu zata kasace
cikin farin ciki hamdala ta sha gaya masa "Mutuwarsa ita ce kaɗai ce ƴancinta a gidan duniya bata son
shi kuma ba zata taba son shi ba bare wani abu da ya dangance shi." Lebbansa ya lasa ya jiƙasu da yawun
bakinsa ya gyara kwanciyarsa lokaci guda yaji tuwon ma ya fitar masa daga rai.

Yau ina gama shirin tafiya makaranta shi zai kaita yana jiranta. Zani ta ɗaura da riga ta ɗaura ɗankwalinta
kafin ta ɗauko dogon hijabinta ta saka.

A falo ta same shi yana waya wayar da ta ma saba ganinsa yana yi kawai dai in ya ganta yana ajiye wayar
da wacca suke yin wayar tare.

Na gama.

Muje.

A mashin ya goyata ya umarceta da ta rike shi da kyau bai ɗauki mota ba sabada tayar ta lallace.

Ko da ya sauke ta ya gaya mata ta je gida zai zo da dare ya ɗaukota.

Da sauri tace "A'a dan Allah zan koma gida da kaina ba sai naje gida ba ."
Da mamaki ta kalleta sabida yadda yasan mata da san zuwa gida amma banda Marhaba a iya zaman da
suka yi bai taba jin tana son zuwa gida ba ko tace zata kira Amminsu amma bai taɓa ji ba. Ba tare da ya ja
ba yace "Aa ki je gidanku zan zo na ɗauke ki mun yi waya da Ahmad yace "Abba ba shi da lafiya ya faɗi
dazu da safe ciwon ƙirjinsa ya tashi."

Hankalinta ya tashi tuni ta soma kuka jikinta na rawa ta riko hannunsa da sauri tace"Kayi min rai ka kaini
gidan kawai ba zan tsinci komai ba in har banje naga lafiyar Abba ba."

A ranshi yace "Yarinya kamar mai juju" a fili kuwa yace "Shi yasa ban gaya miki ba tun muna gidan amma
muje."

"Nagode" ta faɗa bakinta na rawa.

Ahmad tsugune gaban Ammi yana goge hawayensa ya ce "Ammi dan Allah kiyi haƙuri."

Ba tare da ta kalle shi ba ta taɓe bakinta kawai ta cigaba da duba wayarta.

Ammi wacce iriyar ƙiyayya ce wanan kike yi mana.

A hankali ta ɗago ta kalle shi ta ja tsaki tace "Tashi ka bar min ɗaki tun ban ɓata maka rai ba shashasha
kun wani dame ni da zancen wancan mutumin kar ka soma shiga abin da ba ma a san za a haife ka a fara
shi ba "tashi ka bani gu" ta fada masa a tsawace.

Shi tayi wa tsawar amma Marhaba ce ta yi waje da gudu shigowarta kenan amma tayo nan ɓangaren
Ammin sai ta tarar da abin da ke faruwa tsakaninsta da Yaya Ahmad.

Ahmad jiki a sanyayye ya fita daga ɗakin.


Gaba ɗayansu a ɗakin Abban kuka suke yi an rasa mai hana wani hatta da Amaryar Abban ta kasa
tausarsu a yanayin da Abban yake ciki dole in ka gan shi ka tausaya masa amma wai Mar'yam ta kasa
russuna kuma sunji faɗan ma ya na da haɗi da Ammin shi ya saka Abban faɗuwa dan dama yana da
ciwon zuciya likita ya sha faɗa musu da su dinga kula da shi ko dan lafiyarsa zuciyarsa na dab da daina
aiki shi kuma ya kasa daina saka tunanin a cikin ransa.

"Kuyi haƙuri mana tayaya zai shi sauƙi a haka kun zo kun sa shi a gaba kuna kuka harda ku ma
Ahmad?"Ya Alee ya faɗa.

Alhaji Idris doko ya shigo ɗakin ya dinga yi musu faɗa ya tattarasu duka yace su fita daga ɗakin baya san
sakarci mazansu da matansu kuwa suka yi waje. Shi kan shi da ya ƙara kallon aminin nasa sai da jikinsa
yayi sanyi a hankali yace "Allah Ya baka lafiya Sufyan Doko taka jarabawar kenan son mace."

Fita shi ma ya yi daga ɗakin duk mazan ya sa su a gaba suka tafi masallaci.

"Wai dan Allah me yasa Ammi take yin haka ? Haba ko ba komai ai akwai zuciyar musulumci taya ma za
ayi ta iya yin wanan biris din da mutum miji ma kuma uban ƴa'ƴanta."

"Aunty Sajida kenan kamar ba a nan kika taso ba ko? Shi yasa kike kallon wanan a matsayin sabon abu."

"Mariya ki rabu da ita tana sane so take yi ta manta amma ba zamu bari ta manta ba."

"Amina wacce iriyar ƙiyayya ce wanan dan Allah." Sajida ta faɗa a sanyayye. Ita ko Marhaba bata iya
cewa komai to me zata ce? ita gani take yi ma kamar Ammin ta fi kowa tsanarta da su har Abban hawaye
kawai take sharewa lokaci bayan lokaci tana roƙon Allah Ya bawa Abbansu lafiya Ya rabashi da wanan
ciwon ya huta.

"Marhaba".
"Na'am" ta faɗa jiki na rawa.

Aunty Sajida ta ce "Zo ki zauna Marhaba ke har yau baki daina firgita ba ki dinga tunani anyhow so kike
yi kema wani abun ya same ki? kina kallo dai Abba sabda tunani da damuwa ya ɗorawa kansa wanan
ciwon akan wadda bata dace da ya damun a kanta ba ke ma haka kike son ki kasance ne?"

Kukan da take riƙewa ta saki gaba ɗaya ta kwanta a ƙasa aka rasa mai hanata kukan jikinta sai rawa yake
yi kawai suma sai suka sa kukan sun sani gwarasu a kan ta Ammi kan kula su jefi-jefi amma Marhaba sun
rasa me yasa bata san yarinyar nan ko kaɗan kamar ba ita ta haifesu ba.

Yaya Alee da tunda suka shigo yake bin falon da kallo yana jin shashekar kukanta amma bai ganta ba
kara shiga yayi ya ganota kwance a kan carpet tana kuka a hankali ya shiga tsakiyarsu ya riƙo hannunta
kawai suka fita daga falon.

Bai saketa ba sai a tsakar gidan ya tsayar da ita haɗe da ɗauko handkerchief ya bata ta goge fuskarta ya
kuma saka dan yatsan sa a kan lebansa alama tayi shiru kukan ya isa haka.

Daga bayansu Alhaji Idris yace "Aliyu maza ka maida ta gida gobe ta dawo dan wanan sai kuka ta iya."

"Shi yasa na ɗaukota Abba gidan zamu tafi Allah Ya bawa Abban lafiya sai anjima zan dawo."

"To ,to maza kuje Allah Ya muku albarka."

"Ameen."

Ya gyara mata mashin ya kwantar da shi ta hau sanan ya gƴagƴara mata rigarta sanan ya hau ya kunna
suka tafi. A baki gate ya ke masu Ahmad dariya yace "Sai kace mata wai kuka kuke yi a agan mata kunji
kunya Wallahi"
Basu kai ka kula shi ba ya burga mashin dinsa yayi gaba.

Alhaji Idris har yamma yana gidan amininsa yaran ko tuntuni duk ya sa su tafi gida musamman matan

Yana ɗakin Aminin nasa yana kallon sa yana kuma tuna ƙuruciyarsu da baƙar ranar da Doko yaga
Mar'yam ya faɗawa soyayyarta ya shafa kansa ya ce "Allah Ya yaye maka wahala Doko."

A hankali ya soma ƙoƙarin buɗe idanuwansa bakinsa na motsi amma ba a jin abin da yake faɗa.

Da sauri Alh.Idris ya tashi ya isa kusa da Sufyan Doko ya zauna yana masa sannu.

"Shege idi to ban mutu ba da raina har yau da ƙwarina."

Dariya suka yi duk su biyun daga bisani Idris Doko ya haɗe rai kamar ba shi ya gama dariya ba yanzu.

"Sufyan ka san dai yaran nan naka kai ne kadai gatansu sai Allah kai suke kallo suke samun sanyi amma
ka kasa haƙura da wanan yarinyar. Na san mutuwa ta Allah ce amma ai wanan kisan kai ne kake son yi da
kan ka baka tausayawa kan ka bare makusantanka in ka hallaka kan ka ai ba Mar'yam ce tayi asara ba
mu muk yi asara."

Da ƙyar yace "Doko ku cigaba da yi min addu'a amma ba zan iya daina son Mar'yam ba a raina da sonta
aka hallice ni ba zan iya daina son ta ba kawai dai ina roƙon Allah ko sau ɗaya ne Ya saka mata tausayina
a ranta."

Baƙin ciki da taƙaici suka yi ma Alh.Idris rufdugu yayi tsaki ya bar ɗakin.
Murmushin ƙarfin hali kawai Alh.Sufyan yayi.

[6/17, 12:40 PM] Ummulhair S Panisau: A CIKIN IDO....

NA

Ummulkhairi S Panisau

(Khairat UP)

Karamci Writers Association.

(Karamci shi ne tushen mu'amala tagari).

Amarya ta shigo ganin yanayin da Alhaji Idris ya fita sai hankalinta ya tashi ta ɗauka wani abun ne ye sa
mu mijin nasu sai ta ganshi garau a zaune ma amma hankalinsa yana wani wurin.

Alhaji yaya jikin naka da naga Yaya ya fita a birkice na ɗauka ko jikin ne.

Aa Habibato lafiya jiki Alhamdullilahi ai ya yi sauƙi.

To Alhamdullilahi ,Allah Ya kiyaye na gaba.

Ameen Ameen.
Me kake so ayi maka?.

Babu komai matata kawai dai ina son yin alwala ne na yi sallah.

To bara na sirka ruwa.

Nagode sosai Allah Ya yi miki albarka.

Ameen Alhaji.

Ta kai bakin ƙofar banɗakin ta ji ya tambayeta ko yaran sun shigo.

Ta gaya masa sun zo amma Yaya ya tarkatasu sun koma gidajensu saboda kukan da suke tayi.

Allah sarki bara nayi sallar sai na kikirasu ko hankalinsu zai kwanta shi yasa bana son ana kiransu ana
ɗaga musu hankali.

To ai dole su ji hakkinsu ne.

Haka ne.

Yana son ya ji ko Mar'yam ɗin ta zo duba shi amma ya kasa duk da ya san ba zata zo ɗin ba.

Alhaji na haɗa maka muje ko?

Je ki huta abin ki zan iya mijin na ki ai ba rago ba ne yana nan daram da ƙwarinsa.
Tayi dariya kawai ta rausayar da kanta ta fita daga ɗakin. Mugun tausayin mijin nata take yi sabo da
wahalar da yake sha kan matar da ba ƙaunarsa take yi ba yanzu duk wanan abu bai sassautar da
zuciyarta tazo ta duba shi ba saboda mugun hali tabbas Sabani a so bai yi ba.

Jiki a salube ta isa ɓangaren Mar'yam tayi mata sallama ta amsa mata kadaran kadaham kuma bata
daina abin da take yi ba.

Duk da haka Habiba bata saduda ba ta ce mata "Ammin yara Abban nasu ya farka ki zo ki duba shi dan
Allah. Sai kallon ƙofa yake ko bai faɗa ba na san ke yake biɗa."

A wulakance ta kalli Habiban da sai da taji ƙirjinta ya buga matar na da kwarjini musamman in ta ɗaure
fuskar nan kamar kunu ya taɓke.

"Da na san ma maganar da ki zo min da ita kenan da ba ki isa shigo min ɗaki ba amma babu komai yanzu
ma ba ta ƙure ba ki tashi ki bar min ɗaki ko?."

Tashi tayi jiki a sanyayye ta ce "Ki yi haƙuri ita rayuwar nan na wa take ma ban san asalin abinda ya
asassa wanan baƙar ƙiyayyar ba amma ina roƙon Allah Ya kashe miki gobarar da ta cika miki zuciya ko
kya samu sassaci kema."

Murmushin gefen baki tayi kan ta juya ta ce mata "kin san addu'ar da nake yi kullum a fili da baɗini?"

Da sauri ta gƴaɗa mata kai alamar aa.

Kullum sai na roƙi Allah da ya ɗauƙi raina ko na rabu da auren wancan mutumin ,ko ko ya ɗauki ransa na
daina ganinsa abin da ya tokare min ƙirji ba zai taɓa sauka ba har sai ran da na rabu da auren Sufyan
Doko.
Innallillahi wa inna illahir raj'un wai Ammi me ya yi miki da zafi haka da ba za ki yafe mai ba? Shin dama
so laifi ne?

Amarya kije kawai mijinki bai taɓa yi min laifin komai ba kawai son shi ne bana yi ko ince miki laifin shi
ɗaya aure na da ya yi shi ne kawai."

Amma ai koma meye ya'ya tara fa a tsakaninku ai ƙiyayaa ta kare.

Dariyar gefen baki tayi kawai tace "Ina son dan ALLAH ki fitar min daga ɗaki Wallahi bana son kina min
wanan maganar in dai wata maganar ce zan ji ki amma banda ta Doko.

Bata da zaɓin da ya wuce ta fita daga ɗakin tana hawayen tausayin Alh.Sufyan cikin ranta kuwa kullum
tunaninta shi ne wanan wane irin aure ne Alhaji ya ƙi haƙura da Mar'yam ya kafe ya dage.

Ya Alee ina son naje na ga jikin Abba.

Kallo ɗaya ya yi mata ya maida kan sa kan wayarsa ya cigaba da yin aikinsa bai ce mata komai ba.

Zaunawa tayi da ta gaji da jiran amsarsa ita ma ta ɗauko wayarta ta kunna ta jira ya gama booting kafin
ta kunna datar ta .

Saƙonni suna ta shigowa wayar amma hankalinta na kan Abbanta so take yi ta gan shi ko ya wartsake
duk da Abban ya kirasu da kan sa kuma ya gaggaya musu yaji garau kar su damu lafiya yake.

"Zan kai ki amma sai anjima da daddare bana so na kai ki ku haɗu da yayyunki kuyi ta wanan koke-
koken."

A bazata taji amsar sa sai dai bata ce masa komai ba hakan ya saka ya kalleta amma ba shi take kalla ba
sai ya basar shi ma duk da ya ji zafin ƙin amsa shin da ta yi.
A nan aka yi ta kiranta yayyunta suna jajjada mata Abba ya ji sauki kar ta damu.

Tashi ta yi ta shiga ɗora musu abincin rana. Kasa jura ya yi ya tashi ya bita kicin din.

"Na yi miki magana ba ki ba ni amsa ba ko ji na ne ba ki yi ba?"

A sukwane ta juyo ta kalle shi kafin ta juya kan pampo ta kashe.

"Na yi tsamanin ba ka ji ni bane shi ya saka nima na yi tunanin ba da ni kake ba tunda naga aiki kake a
waya."

Bakinsa ya buɗe yana kallonta sama da ƙasa ji wani latsi ko ma yace rainin hankali wai a waya.

Yana kallo ta cigaba da aikinta bata ko kara kallansa ba.

Juyawa ya yi koma falon ya zauna sai ga kiran Sabreen ɗin ya shigo da ke ya sauka daga kan watsaap din.

Sai ya kasa ɗauka ganin kamar ko wayar da yake yi da Sabreen ne ya bata haushi sai ya ki ɗauka.

Ita ma can sarai take jiran taji ya ɗauka kamar ko yaushe har leƙawa tayi amma sai ta ga bai ɗaga wayar
ba sai ta koma har wata yar ajiyar zuciya ta sauke na jindadin hakan da ya yi.

Da ta matsa masa da kira sai ya ɗauka ya fita waje amsa kiran.

Taɓe baki tayi tace "Oho dai Ya Alee ɗin nan ya fiya rainin hankali da yawa Wallahi."
Sabreen in ki ka kirani sau biyu uku ban ɗaga wayar ki ba hankalin ki ba zai baki bana kusa ba ne ko ina
wani aikin ne sai kiyi ta kira kamar makauniya?

Daga ɓangaren Sabreen kuwa ta ji haushi ta shaƙa amma bata nuna ba saboda kissarta so take ta ja
hankalinsa ta kuma lalaba ya aureta. "Ka san bana san kayi nesa dani shi yasa nake kiranka amma kayi
min afuwa zan rage."

Hum! Kina ji na ? zan na kiran ki kawai in ina free bana son kina kirana in ina cikin gida in dai bani na kira
ki da kaina ba.

Saboda kana tsoron matarka ko me?

Ba tsoro bane bana san cin fuska yarinyar nan tana haƙuri da ni da kuma wayoyin da muk.....

Wai son yarinyar ka fara ko me?

Na taɓa ce miki bana sonta ne dama?

Baka faɗa ba amma ai na ji ka gaya min Abbanku ne ya ɗaura auren ba tare da shawara da kai ba.

Shi ne me?

Sai kuma tayi shiru ta rasa me zata ce masa kawai sai ta yi masa sallama ta kashe wayar.

Ya bi wayar da kallo.Tsaki ya saki ya koma cikim gidan bai san ma ya ɓata lokacinsa da yawa ba sai yanzu
da ya shig ciki ya kalli agogo.
*

Gaba ɗaya ranta a jagule yake aikin take amma bakinta a zumbure yake kamar zai taɓo hancin ta saboda
bakin ciki. A yadda ta taso a gidansu taga wat iriyar bahaguwar rayuwa bata fatan ita ma ta kasance cikin
irin wanan rayuwar ,ko da Abban ya haɗa aurenta Ya Alee bata taɓa jin ƙin sa a ranta ba dama can yana
burgeta cikin ƴa'ƴan Abban ba shi da yawan kula mutane amma yana da faɗa ba wai irin na masifa ba aa
in kayi zai yi maka ,shi yasa ba kowa yake kulawa ba bare a taɓo shi ya yi da mutum ba ,ɗan gayu ne , ga
aji kamar mace yana da farin jinin ƴan'mata sosai dan ko a unguwarsu ta sha jin suna gulmarsa da kuma
son kasancewa da shi sai dai babu wacce yake kulawa......

"Tunanin me kike yi ne ana ta magana ba kya ji?"

Bakin nata ta ƙara yin sama da shi ta harare shi a fakaice tace "Ban ji ba ne."

Ƙwafa ya yi ya juya ya bar ɗakin kawai.

Bayan shi ta bi shi da kallo kawai ta koma ta zauna kan gado daɓas tuni ta ji hawaye na yi mata zarya a
ƙuncinta waye zai sota ita ma kamar saura? Ko dai bata da farin jini ne? Auren nata ma ba dan Abban ba
kila da ba zata yi ba dan babu wanda ya taɓa cewa yana sonta.

[6/17, 12:41 PM] Ummulhair S Panisau: A CIKIN IDO.....

NA

Ummulkhairi S Panisau.

(Khairat UP)

Karamci Writers Association.

[Karamci shi ne tushen mu'amala tagari].


4

Sai ya ji babu daɗi haka ya saka ya koma. Bisa gado ya ganta tana share hawaye sai ya ji tausayinta ya
kama shi sosai a hankali ya shiga ciki ya zauna a gefenta.

"Me aka yi miki kike kuka?"

"Babu komai."

"Babu komai kike kuka?"

"Eh kaina ne yake yin ciwo."

"Hum! Ciwon kai ne zai saka ki kuka Marhaba?"

Kai kawai ta gƴaɗa masa ta juya masa ƙeyarta.

Hannunshi ya saka ya juyo da ita fuskarta a ƙasa a hankali ya s hannunshi na dama ya ɗago da haɓarta
idanuwansu suka sarƙe da na juna na kusan sakan biyu kafin ta ɗauke kanta daga kallon da yake yi mata.

"Na san dai ban yi miki komai ba amma kar ki manta ke ɗin amanata ce amana ce da na ƙarɓa daga
wurin Abba kuma na yi alƙawarin riƙewa da hannu biyu-biyu dan Allah ki daure ki tayani cika wanan
alƙawarin.

Bai bata damar ƙara yin wata maganar ba ya rungomota jikin shi tsam yana shafa bayanta yana lallashin
ta har sai da ya ji ta daina kukan sannan ya cikata. "Ki kwanta ki huta sai da safe."Bai bata damar ƙara yin
magana ba ya fita daga ɗakin ya bar ta da mamakinsa. Ƙasan ranta sai ta ji wani irin dali kamar ma dai
butterflies na yi mata cakulkuli a cikinta. Murmushi tayi tana shafa rigar ta gaba ɗaya ƙamshinsa ya cika
mata hanci da baya ta koma ta kwanta haɗe da lumshe ido.
*

Banɗaki ya shiga ya sakarwa kansa ruwan sanyi idanuwansa a kulle yana tuna yanayin da suka shiga
yanzu mamakin kan sa yake yi ma da ya iya rungume yarinyar bai taɓa ba wanan ne karonsa na farko da
ya taɓa rungume mace sai ya ji abun sabo a wurinsa kuma ya ji daɗin hakan. Hannunta laushi ƙamshi mai
daɗi ke fita daga cikin jikinta. A ƙalla ya ɗauki mintuna goma a ƙasan shayar nan kan ya kashe ya ɗaura
tawul ya yi alwala.

Murmushi ne ya kuɓuce masa a bazata wanda bai san dalili ba shi ma , drowarsa ya buɗe ya ɗauko
jallabiya da short da singileti ya saka. Sallah ya tada ,bayan ya idar ya zauna kan sallayar yana jan carbi
hakan nan ya ji yau yana roƙon Allah da Ya bashi damar cika auren sa kamar na kowa ta kwanta masa a
rai haƙurinta da sanyinta uwa uba biyayyarta sune suka rinjaye shi ya ji ta yi masa kuma he's ready to
spend his life with her.

Wanke-Wanke take yi a kicin sauri take yi ta shirya ta tafi makaranta yau suna da gwaji (test).

Juyawar da zata yi ta ji ta yi karo da mutum dake ya fi ta tsayi sai ta bugu da ƙasan ƙirjinsa "Wash" ta
faɗa a fili tana sosa goshinta. Sunkuyawa ya yi ya hura mata iska a kunne yace"Am sorry ban san za ki
juyo ba."

Da sauri tayi baya jin maganarsa ba zato ba tsamani ta ji ya janyota da ƙarfi ta faɗa a kan ƙirjinsa.

Gaba ɗaya su biyun yanayin bugun zuciyarsu ya sauya bugu da sauri da sauri baya ma Marhaba da tayi
tsili-tsili da ido tana rarrabasu kamar wadda tayi wa sarki ƙarya.

Ba kya kallon ruwan ƙumfa a bayanki? so kike ki ji wa kan ki ciwo?.


Ban lura ba sauri nake yi Aisha tace min yau akawi gwajin da zamu yi nan da awa ɗaya shi ya sa nake son
hattamawa da wuri.

To me aka yi kenan sauri ya haifi nawa?

Bata iya ce masa komai ba ya gyara mata tsyauwarta da kyauya ce "Je ki shirya zan ƙarasa miki."

Idanuwa ta zaro masa cike da mamakinsa.

Tafin hannunsa ya saka ya ture mata fuska wuri guda yace "Go" ya ɗau sosan wanke-wanken ya cigaba
da wanke kwanukan.

"Wai ba ki tafi ba har yanzu? in kika makara kuma ki ce ni ne na jawo ko?"

Da saurita juya ta shiga ɗaki tayi wanka ta sa doguwar riga baƙa irin ta yadin nan ta ɗora hular chantly a
kai ta saka turare mai ƙaramin ƙarfi.Man leɓe kawai ta shafa ta kuma murza farar powder saboda tsane
gumi dan lokacin yanayi na zafi ne. Sai ta ji tana son ƙara kallon mudubi ko dan ta ga kyawun da ta yi
saboda mijinta dariya tayi tana kulle fuskarta da tafin hannunta tayi ɗan tsalle kaɗan.

"Sauran ki minti arba'in ki makara."

Da sauri ta juyo sai kuma ta ƙara juyawa ta ɗauki hijab ɗin ta saka.

Zata fita ya riƙo ƙugunta da hannunsa ya manna ta da jikin kofar ɗakin.

Abun yazo mata a bazata, ga mamakinsa sai ta waro idanuwanta kamar zasu faɗo ƙasa.

Iska ya hura mata a fuskar ta hakan ya sa ta dawo duniyar mamakin da ta shiga.


"Kin yi kyau matata ,wato cutata kike yi ko?"

Ba tare da ta sani ba ta yi saurin girgiza masa kanta alamar a'a ba haka bane amma a zahiri cewa tayi
"kayi haƙuri Yaya ban cuce ka ba Wallahi."

Dariya ma ta bashi ya dungure mata kai ya ja da baya yace "Muje kawai kar ki makara."

Sum-sum ta ɗauko jakarta ta yi waje.

Bayan fitar ta shi da kan shi mamakin kan sa yake yi wai kuwa shi ne? Ko Sabreen da suka ɗauki tsahon
shekaru biyar tare bai taɓa jin irin wanan yanayin a kan ta ba yana sonta ya sani amma ba irin yadda
yake ji a kan Marhaba ba.

Haka ya kai ta makarantar ya koma a hanya ma tunaninta kawa yake yi murmushi ya ya karya kwanar
gidansu yace "Easy Doko kar ka zama wawa a so mana."

[6/17, 12:42 PM] Ummulhair S Panisau: A CIKIN IDO....

NA

Ummulkhairi S Panisau

(KhairatUP)

Karamci Writers Association.

(Karamci shi ne tushen mu'amala tagari.)

5
Tun dare yamma take cikinta yake ciwo ta san al'adar ta ce ta zo amma sai ta sha baƙar wahala kafin ya
zo komai ta ci sai ta dawo da shi kamar mai laulayin ciki.

Yanzun ma so take ta samu farar ƙasa ta sha ko zuciyarta ta kwanta mata amma ta rasa ko a hanyar
makaranta da ta taho bata gani ba gashi bata da lambar wayar Ya Ali bare ta kira shi ya taho mata da
shi.Rashin samun mafita ya saka ta kwanta luff kamar mage a kan ƙaramar kujera mai zaman banza ko
girki bata iya yi ba gab take da ta fara kuka sabo da yadda cikinta ke murɗa mata.

Da sallama ya shigo ta amsa masa da ƙyar hannun ta kan mararta tana yamutsa fuska.

Ya yi mamakin ganinta a kwace dan ba al'adar ta ba ce ba kwanciya a irin wanan lokacin.

A hankali ya ƙarasa inda take ya tsuguna a gabanta ya shafi fuskarta da ya bushe da hawaye.

"Mene ne?"Ya tambaye ta cikin murya mai sanyi.

Kanta ta gyaɗa masa alamar babu komai.

Ya jijiga mata kansa hade da sauke mata harara yace " Tashi ki gaya min me aka miki"?

Bata san ma ta tashi sabo da yadda take jin tashin zuciya in har ta ce za ta bude bakinta tabbas zata yi
masa amai.

Zaunar da ita ya yi ya saka gwiwowinsa biyu a ƙasa ya tallafo fuskarta da tafin hannayen sa biyu ya na
jiran ƙarin bayani.
Ta buɗe baki kenan ta ji amai ya taho mata.Aliyu Doko bai san lokacin da ya sa hannyensa biyu a ƙasan
haɓarta ba.

Ba ita kaɗai ba shi kan shi mamakin kan sa ya ji . Ɗauke idanuwanta tayi daga kallonsa so take ta tashi
amma ya toshe mata hanyar bi ,lura ya yi da in ya cigaba da zama zai yi katoɓara ya saka ya tashi ya ja
hannunta suka shiga ɗaki tare ,banɗaki ya buɗe mata ta shiga babu musu.

Bayan shigarta ya lura da staining tayi amma ba ta sani ba. Murmushi ya yi ya shafa kansa yace "Silly girl
shi sa take kuka kenan"? ya taɓe bakinsa ya fita daga ɗakin ya koma na sa.

Ko da na shiga banɗakin na lura na ɓata kayana hakorana na haɗa da harshena na datsa tare da runtse
idanuwana cike da jin matsananciyar kunya "Na shiga uku ya gan ni kenan".

Haka na kimtsa a gurguje na gyara jikina na sauya kaya na fesa tuarare ni fa in baƙona na wata ya zo da
kai na ma ƙyanƙyamin kai na nake ji. Ban yarda na fita daga ɗakin ba na koma na kwanta a kan gado.

Shiru-shiru ya ga ba ta fito ba ga yunwa yana ji tashi ya yi dan tsokana yake ji ya shiga ɗakin na ta a
kwance ya tarar da ita, "Yau sarauta kike ji ne?"

A zabure ta juyo ta zuba masa kyawawan idanuwanta masu maiƙo ta sauke masa su.

Sai da ya ji ƙirjinsa ya harba masa hasalima kasa cewa komai ya yi a ƙalla sun kai daƙiƙa biyar suna kallon
juna. A hankali ta juyar da fuskarta tana runtse idanuwanta.

"Ki zo ki ba ni abinci, yunwa nake ji yau na ga kamar haushi na kike ji shi ya sa kike hora ni da yunwa."

Da sauri ta tashi tace "A'a ban jin daɗin jiki na ne kayi haƙuri muje na dafa maka indomie."
Bai ƙara ce wa komai ba ya fice ta bi bayan sa ktchen ta shiga kai-tsaye ta ɗora masa indomie ta haɗa
harda ƙwai.

Yana falon a zaune sai bin motsinta yake yi da kallo kawai duk da Sabreen na ta kiransa amma yau sa
ya ga rashin dacewar ɗaga kiran a cikin gidan haka ya sa ya tura mata da saƙon ta jira shi zai kirata yana
aiki ne.

Bayan ta gama ta zubo masa ta kawo masa ƙasan carpet ta ajiye masa ta koma ta ɗauko masa ruwa ta
ajiye mai ta tashi zata koma ya riƙo hannunta bata tashi ba kuma bata juya ba sai ta ji wani banbarakwai.

"Ki zauna mu ci abincin tare ban ga alamar kin yi girki ba yau." ya faɗa yana kallon bayanta kuma bai
saki hannun nata ba.

Komawa tayi ta zauna amma ta kasa sakin jikin ta a takure take gaba ɗaya ,cokalin ya ajiye mata a
gabanta yace "Bismillah".

Muryarta na karkarwa tace "Zan juye ruwan tea ne karya ƙone."

Sakin hannun nata ya yi ya bita da kallo har ta shiga ciki. Ajiyar zuciya ya sauke kawai yana jin wani irin
yanayi na saukar masa murmushi ya saki a karo na ba adadi mamakin kan sa yake da kan sa yarinyar
gaba ɗaya ta shiga ransa ya rasa ma a wane mataki zai saka ta acikin bargon zuciyarsa sai ya ji kamar ma
ba soyayya yayi ba a da sai yake gani kamar yanzu ne ye ma fara sanin ainihin meye soyayyar.

Marhaba kuwa tana komawa kicin din ta jingina da jikin bangon kicin din ƙirjinta na duka uku-uku hannu
ta saka ta dafe ƙirjin tana jin wani abu na sukar mata rai game da Ya Alee.

Ƙauri taji yana tashi da sauri ta kashe gas ɗin tana dungurin kant da kanta "Haba Marhaba kiyi a hankali
mana wanan ai sai ki bada mata."ta faɗawa kan ta da kan ta.

Haka ta sake dafa wani ta kai masa da cup da spon harda container din suger.
Tare suka ci abincin kan suka sha shayin suna hira duk da yawancin hirar ta karatu ce yake tambayarta
tana ba shi amsa.

Duk nacin kiran da Sabreen ke masa bai sa ya ɗaga ba kacokan ya maida hankalinsa kan Marhaba Doko
da ya jima yana tausayin ta sabo da gwagwarmayar da ta sha a rayuwa bai taɓa ganin tashin hankali irin
na gidan Alahaji.Sufyan Doko ba ganin abin yake kamar a labarin littafin Hausa ko kuma flim da ace ba a
gabansu wasu abubuwan suka faru ba zai ce ƙarya ne.

Sabreen da ke ta zagaye ɗakinta tana jin wani irin haushi da tsanar kanta bisa dagewarta akan Aliyu
wanda tunda ya yi auren nan ta daina gane kansa gaba ɗaya ya sauya mata kamar ba shi ba ta rasa
yadda zata yi ta cire shi daga ranta amma ta kasa mugun jin haushin kanta take yi akan sa taga ma kamar
iska ce take wahalar da mai kayan kara. Bata hango kamaluwar alaƙarsu da Aliyu nan kwana kusa ba
kamar dai so yake yi ya yi mata halin maza ita kuwa bata ga abin da zai raba ta da shi ba sai ta nuna masa
bai isa ba ita da shi mutu ka raba ne.

Yanayin na damina ne ,lokaci guda hadari ya haɗu ga iska mai sanyi na kaɗawa ta ko ina kowa hada-
hadar fakewa ya ke yi.

Daman Marhaba na son ruwa sosai tuni ta ji ranta ya yi mata fes bakinta ya kasa rufuwa dan tsantsar
farin cikin saukar ruwan da yayyafi ya fara sauka ga ƙamshin ƙasa na tashi tuni ta kunna gawayin nan mai
guda ɗaya ta saka turaren wuta. Doguwar riga ce a jikinta mai dogon hannu,yau tayi tsifa haka ya sa ta
ɗauko hula fara irin ta chantly din nan ta saka ta suri silifas tayi waje jin ana buga mata ƙofa.

Ko da ta buɗe sai taga baƙuwar fuska amma fara'ar da ke fuskarta bata gushe ba a hankali ta buɗe
labbanta tace "Sannu baiwar Allah ban gane ki ba".
Baƙuwar ta ƙare mata kallo tsab kafin ta yi dariya irin ta rainin hankali kafin tace mata "Ki yi haƙuri ki
bani dama na shigo ciki kinga ruwa ake yi."

Da sauri ta matsa tana murmushi tace "Afuwa,Bismillah shigo."

Wuri ta samu ta zauna tana bin ko ina na gidan da kallo tana murmushi cikin ranta kuwa ta yaba da falon
babu hayaniya a cikin jeren da aka yi na ƙawata shi so simple.

Kicin ta shiga ta kawo mata ruwa da leme sai cake ta ajiye mata a gabanta.

A hankali tace "Da baki wahalar da kan ki ba Marhaba ko?"ta faɗa tana dariyar ƙeta.

Duk da Marhaba ta ji wani banbarakwai hakan bai sa ta kasa bata amsa ba.

"Kin faɗa daidai Marhaba na ke sai dai ke ban gane ki ba ko za ki yi min bayanin kan ki?"

"Eh ba za ki san ni ba kam amma ni na san ki saboda kin ƙwace min wani sashi na rayuwata wanda ni aro
na baki ba wai ƙwacewar kika yi ba kamar yadda kike tsammani. Kawai ki kaddara na tashi daga baccin
da nake yi ne dan na amshi abin da dama can nawa ne ni kaɗai."

Zuwa yanzu matar mamaki ta fara bata sai dai ta kasa cewa komai amma tana san karin bayani.

Kar ki wahalar da ƙwaƙwalwar ki dan ba za ki iya ba wa kan ki amsar abin da kike kai-kawo wurin ganin
kin sani ba ni ce dai kawai zan iya yi miki bayanin in kin bani damar yin hakan.

A sanyaye tace "Baiwar Allah ki yi haƙuri ki sanar da ni abin da na ɗauka na ki ba tare da na sani ba,dan
kin sani a duhu Wallahi."
Dariyar dai ta ƙara yi kan tace da ita "Sunana Sabreen Kabir Mai taya ni budurwar mijinki ce wadda yake
so yake kuma fatan aura amma kika yi tsaye kika shiga tsakani amma ina so ki sani ba wurin zaman ki
bane nan wanan wurin zamana ne na zo ne na yi miki kashedi kan abin ƙaunata kar ki saki jiki ki ɗauka
kin samu wuri sam ba haka bane wa'adi ne na baki wanda ko wani irin lokaci za ki iy ganin ki a waje ni
kuma a ciki.

Tunda ta faɗi sunanta ta kuma alakanta kanta da budurwar Ya ALI ta ji kanta ya sara mata amma bata iya
bari karayarta ta fito fili ba sai tayi murmushin nan da ake kira yaƙe ya fi kuka ciwo.

"Ba zan musa miki ba kuma bana shakkar kuna soyayya da mijina sai dai ki zauna kiyi nazari mana da kan
ki ke yake so kike son sa amma ni ya aura ya killace a cikin gidan shi ni kuma nake amsa sunan matarsa a
ko ina kinga kenan matsayina ya ɗara naki nesa ba kusa ba. Zan so ki ƙara zage damtse dan samu abun
da kikr burin samun duk da ni ma ba kanwar lasa bace ba.

Tafi Sabreen tayi ta gyara zamanta haɗe da ɗauko lemon robar ta ƙurɓa ta ce "Matar da har yau bata iya
gyara gadon ta ba? matar da har yau ba a taba shiga ɗakinta ba dan sauke hakkin auren ta ba? ai ta
zama matar cushe in dai na tuna daidai haka ake kiran irin ku ko matar cushe?"

Tabbas Sabreen ta yi sara a kan gaɓa kuma ta yi harbi a daidai inda ya dace kuma ya soki ƙirjin Marhaba
a inda ya kamata sai dai bata yarda ta nuna karayarta ba a fili.

Tashi Sabreen tayi ta gyara zaman gyalen abayarta ta ɗauki mukulin motar ta haɗe da jakarta ƴar
ƙarama ta yi hanyar waje ta juyo tana murmushin samun nasara kan tace "Ko da yau kin samu Zaki
ragowata kika samu sanan ina son ki sani na shirya tsab dan ganin na raba ki da Zaki na domin nawa ne
ni kaɗai ban shirya raba shi da ko wace macce ba in nace kowacce mace ina nufin harda ke a ciki da kike
amsa sunan matarsa ko nace matar hoto.Kar na cika ki da surutu na bar ki lafiya ki isarwa Zakina na
kawo masa ziyara ba ya nan nagode da karramawa Matar cushe."Daga haka ta sa kai ta bar mata gidan.

Komawa tayi ta zauna kan kujera ba wani kuzari tuni hawaye suka soma yi mata sintiri a kan fuska tana
jin maƙogwaronta na kai komo wani abu mai ɗaci na damun harshenta kwantawa tayi da jikin kujerar
tana sauke numfashi gaba ɗaya ma walwalar da take ciki ta kau yanayin mai sanyi da daɗi da ya ratsa ko
ina na jikinta ya sauka komai ma baya yi mata daɗi ba abin da Sabreen tayi mata bane ya dame ta ba aa
sirrinta da Ya ALEE ya bankaɗa mata shi ya fi dagargaza ƙirjinta wai bai taba kwana da ita ba bai santa a
matsayin ƴa mace ba ba shi ita aka yi ita matar cushe ce? Wata zuciyar tace"Tabbas ke matar cushe ce
ko ki taɓa jin ya ce yana son ki? ko ya taɓa yarda da kaddarasa ya aminta ke matar shi ce ya sauke miki
hakkin ki? dama ai yana yin waya a ɓoye da ita yake yi ba san ki yake yi ba ke matar cushe ce kar ki yi wa
kan ki ƙarya kece kike son sa..." toshe kunnuwanta tayi ta saki wani irin kuka. Bata san adadin lokacin da
ta ɗauka tana kuka ba sai dai idanuwanta sun yi kozai-kozai sun yi ja sabo da kuka.

[6/17, 12:42 PM] Ummulhair S Panisau: A CIKIN IDO.....

NA

Ummulkhairi S Panisau.

(KhairatUP)

Karamci Writers Association.

(Karamci shi ne tushen mu'amala tagari)

Ranar Aliyu bai dawo da wuri ba sai da ya biya ta gida daga nan kuma suka zaga majalisa da Ahmad da
Faruk da suka haɗu sun jima basu yi irin wanan zaman ba tunda suka yi aure kowa unguwarsa daban.

Kan ya ankara sai ya ga goma saura ƴan mintuna yana gyara zaman hularsa ya miƙe yace "Guys lokaci ya
ja fa ni nayi hanyar garinmu."

Faruk yana dariya yace "Kai dai kana tsoro kar a rufe maka ƙofa yau."

"Baka yi ƙarya ba in ma hakan ne ,sai dai ba hakan bane dan Marhaba mar'atusaliha ce babu ruwanta da
fitinar duniya ban sani ba ko dai kai Nafisa za ta hana ka shiga ba ne in ka koma." Aliyu ya faɗa yana zura
takalminsa.
Suka tafa suna dariya gaba ɗaya sai kuma kowa ya nufi inda ya ajiye motarsa suka yi musabaha suka
rabu.

Sai da ya tsaya ya sai mata ice cream da cake dan ya ga mayyar cake ce ya haɗa da tsire na dubu biyu ya
ɗauki hanya.

Marhaba ta gama cika tayi fam ƙiris take jira kawai ta fashe amma haka ta daure ta kimtsa ko ina ta
kunna turaren wuta kayan abincin ma ta jera masa a inda yake ci tana tsaka da gayara taga ta ji tsayuwar
motarshi haushin shi ta ji ya ƙara kamata ta yi gum da baki ta buɗe masa sakatar tayi wuf ta shige
ɗakinta harda saka sakata ta kashe fitala tayi luf abin ta a cikin bargo tana hararar ƙofar.

Da salama ya shigo sai ya ji shiru ba a amsa masa ba bai damu ba ya shiga ciki ya ajiye ledojin a kan
dinning. Ba ji motsinta ba sai ya nufi ɗakinta amma yana murɗa hannun ƙofar ya ji a kulle ga ba haske a
ɗakin. Da mamaki ya buɗe bakin shi dan bata taɓa yi masa haka ba.ƙwanƙwasa ƙofar ya fara yi amma ba
amsa sai ya ji ba daɗi ya koma tunanin ko bacci ta yi ko kuma bata da lafiya amma ya ga ta yi girki komai
ta ajiye masa tsaki ya yi ya koma kan Dinning ɗin ya ɗauki ledojin ya saka a cikin firdge.

Cacakular abincin kawai ya yi ba wani abin kirki ya ci ba ya maida kicin haka kawai ya ji ba dadi da bai
gan ta ba.Haka ya yi wanka ya saka jallabiya ya kuma fita ya bubuga mata ƙofa amma ta ƙi buɗe masa.

ɗakinsa ya koma bayan ya kashe komai ya rufe ko ina ya kwanta cike da tunani fal a ƙirjinsa ba halinta
bane amma me ya faru? bacci dai ɓarawo ne ya sace shi.

Ita kanta uka ta kwana tana yi ba ji ba gani in ta tuna da matar cushen nan sai ta ji ranta ya kara baci
juye-juye ta dinga yi har ɓarawon ya sace ta.

Washe gari da sassafe ta tashi ta yi masa girki ta adana masa kan dinning ta koma ɗaki ta kulle.

Ko da ya tashi ya shirya ya fito ya ga abin kari ya saki baki yana kallon dining din tsaki ya saki kenan ma
abin iskanci ne ba rashin lafiya take yi ba raini ne kwafa ya yi ya saɓi jakarsa ya fice ko ruwa bai sha ba.
Sai da ta ji tashin motarsa ya fita daga cikin gidan sanan ta fito sai ta ga ma bai taɓa abincin ba sam sai ta
ƙara jin haushin sa ya kamata.

Ranar ma bai dawo da wuri ba ko da ya dawo ma bai neme ta ba abincin ma bai ci ba ya yi shigewarsa
ɗaki. Tuni Sabreen ta ƙara ƙaimi wurin shiga jikin Aliyu suka ƙara ɗinkewa da junansu suna soyewarsu.

Sati guda ana ƴar wasan ɓuya da Aliyu da Marhaba ko ta ina ta ƙuntacce kanta bata fitowa shi kuwa bai
ƙara neman ta ba jira yake ya ga gudun ruwanta.

Rashin lallabata da bai y ba ya ƙara hasala mata zuciya ta yarda da batun Sabreen daman ba son ta yake
yi ba.

Washe gari tana da lakca kuma ba kuɗi a hannunta ta gama yankewa ba zata ƙara tambayarsa komai
ba ta rasa yadda zata yi da rayuwarta kawai sai ta yanke gwara ta kira Yaya Ahamad ya turo mata kuɗi to
me zata ce masa ?

Ajiyar

Zuciya ta sauke ta tashi ta gyara gashinta tayi falo sai dai ta yi gamo dan yana zaune a falon yana dadana
wayarsa yana murmushi ta ko sakar masa harara ta yi wajan tv ta dauko wayarta.

Tunda ta fito yake kallonta ta wutsiyar ido yana mamakin yadda ta yi ƙiba wato shi kaɗai ke haukansa
kenan ta na juyowa bayan ta ɗauko wayarta ya yi maza ya tashi ya sha gabanta ya yi mata tsyae ƙerere
ya rungume hannayensa a ƙirjinsa ya sakar mata idanuwansa masu ladaftar da mai laifi.

Gefe ta yi za ta wuce ya kuma shan gabanta ta kuma yin gefe ya kuma shan gabanta karshe ma
hannayenta biyu ya haɗe gu guda ya ɗauke ta cak ya shige ɗakinsa da ita ya ajiyeta a kan gado.

Komawa ya yi ya rufe ɗakin da mukuli ya saka a aljihunsa ya janyo wata ƴar ƙaramar kujera ya zauna a
kai yana kallonta. Sun yi kusan minti biyar a haka kafin daga bisani ya ce "Ina jin ki me na yi miki?"
Shiru ta yi masa ta zumɓuri baki kamar zai haɗe da hancinta.

"Na rantse miki da Allah in ba ki gaya min ƙwaƙwaran dalilin da ya sa ki ke yin wanan shirmen ba sai na
zane miki jikin ki tsab kafin na kai maganar wurin Abban Doko ko kuma Mami".

Ambatar Mami kaɗai da ya yi ya sa ta ji hantar cikinta ta kaɗa tayi wani zillo ta koma da baya. Tsawa ya
daka mata ya ce ta dawo inda ya ajiyeta ko ya kwasheta da mari. Ga mamakinsa kawai sai ya ga tana
kuka bai ƙara ce mata komai ba ya tashi tsaye ya buɗe drowar sa ya zaro belt ya koma gabanta ya kafa
kunne yana jiran ƙarin bayani.

"Ko kiyi magana ko na lahira ya fi ki jin dadi."

Tuni jikinta ya fara rawata manta waye Ya ALEE take ta yi masa gardama da raini baki na ƙarƙarwa tace
"Ka yi haƙuri dan Allah, ba abin da ka yi min."

Iskanci ne ya saka kika kulle ƙofa,ki ka daina fitowa ,ki ka kuma daina yin girki? Raina ni kika yi dan yanzu
ina aurenki ko meye ne?

Ta soma haɗa hannyenta wuri guda tana mazari ya kuma sakar mata wata tsawar bata san lokacin da ta
soma bayani ba tana kuka.

Damaa....dama wata budurwarka ce ta zo ran nan da baka nan wai baka sona zata dawo gidan nan ni
kuma in fita wai ni matar cushe ce baka taɓa kwana a ɗakina shi ne ni kuma na ji haushi na daina fitowa
tunda ba son zama da ni ka ke ba shi sa ka ke ta fadar sirrinmu a gun budurwarka........

Bin ta kawai yake da kallo kafin yace da ita "Wacece ta zo gidan da bana nan?"

"Wata ce wai Sabreen kuma ai naji kuna waya da ita ."


Mamaki da takaici suka ishe shi ya dinga hararata kafin ya buɗe bakinsa ya yi magana "Da ta zo me ya sa
ba ki gaya min ba kika dinga yi min wanan wasan banzan?"

Bata ce masa komai ba tayi shiru.Tashi ya yi ya dafa ƙugunsa ya kalleta ya yi ƙwafa kan ya koma ya zauna
ya ɗauko wayarsa ya soma neman layin Sabreen.

Bugu biyu ta ɗaga wayar dake a amsa ƙuwa ya saka tana jin muryar Sabreen ta gane muryar yo yaushe
zata manta wanan muryar da ta nuna mata matsayinta.

"Zakina yau kuma an waiwayo ni an kira gaskiya ka kyauta dama tunaninka nake yi kamar ba yanzu muka
gama chat ba" ta karasa faɗa tana dariya.

An ce kin zo gidana me ya kawo ki ,kuma me ya sa kika zo ki ka haɗa min fitina da matata?

Ba Sabreen ba kaɗai hatta Marhaba sai da ƙirjinta ya buga na kiranta da matarsa da yayi kai tsaye.

Zakina laifi nayi dan na zo gidanka? ni fa son ka ne ya saka na kasa dannewa na je na ga matar da ka aura
na kuma gaya mata alakar da take tsakanina da kai ta shirya bani abun da na wa ne dan ni ba zan bada
aron kauna ba.

Sabreen ni da ke mun taɓa maganar cushen Marhaba aka ba ni ? na taɓa gaya miki bana kwana da ita?

Sai tayi sak ta kasa cewa komai kafin ta haɗe rai tace "Baka taɓa gaya min ba amma ni na sani cushenta
aka baka mana tunda ni kake so."

Ina son wanan ya zamo na farko kuma na ƙarshe da za ki kuma zuwa gidana ki ci zarafin matata ina ni ne
nake soyayar da ke ba ita ba ina son ta yadda nake son ki yanzu ita ce sirrina ni ma ni ne sirrinta bazan
so wani ya taɓa mata martabar ta ba ko da kuwa kece ina fata kin fahimci karatun. Sanan bana so kar ki
kuma taka kafar ki kizo min gida bana so.
Zakina ni kake gayawa wanan maganar saboda waccar yarinyar? Ni ka ke cewa kana son ta ni kuma me
kake yi min in ita kana son ta?

Matata ce kuma ina son ta.

Zak..... bai bata damar ƙarasawa ba ya katse wayar ya ajiye a gefe.

Sai kuma ta ji kunya ashe ma ba shi ya faɗa mata ba da ta sani tayi masa maganar a ranar da ta sani ta
yi...

"Daga yau kar ki ƙara yi min irin abin da kika yi." Yana gama faɗa ya tashi ya buɗe ɗakin ya fice ya bar ta.

[6/17, 12:42 PM] Ummulhair S Panisau: 7

Haka tana ji tana gani ya dinga nuna mata soyayya mara algus duk ta fita daga hayyacinta ta kasa hana
shi abin da ya yi niya , bata gane abun nayi ne ba sai da taji yana niyan shiga cikin babban birinta yakushi
da cizo kuwa Aliyu ya sha shi ya fi a kirga amma ko gezau ko a jikinsa wai an tsikari kakkausa.

Aliyu bai taɓa shiga wata duniya mai daɗin duniyar da Marhaba ta kai shi ba , ya kara gane cewa mata
ababen so ne kuma dole rayuwa sai da su. Albarka kawai yake sa mata saboda tukuicin kanta da
mutunta da rike da daraja yana alfahari da shi ne ya fara kasancewa tare da ita fara'arsa ta kasa ɓoyuwa
ko ƙanƙani. A hankali ya sauko daga kan gadon ya ƙara rufa mata zanin gadon ya fita falo kicin ya shiga
ya ɗora ruwan zafi a kettle ya zauna a falo bini-bini ya saki murmushi. Ruwan ko na tafasa ya shiga
banɗakin ya juye ya kuma komawa ya saka wani sai daga haɗa mata ruwa a wani bahon wanka ya saka
gishiri kaɗan ya koma ɗakin ya lallaba ya tashe ta aiko yana ɗaga ta ta yi saurin buɗe idanuwanta ta
ganta a hannunshi wata kunyarsa ta ƙara rufar mata tayi maza ta runtse idanuwanta ruf tana ji tana gani
ya sa ta a cikin ruwan tayi zillo ta miƙe ya maidata ya sunkuya daidai saitin kunnenta yace ma ta "ki yi
haƙuri ki zauna a ciki za ki ji daɗin jikin ki sosai hakan zai saka wurin ya daina yi miki zafi ko ba kya so ki
warke da wuri?"
Sai tayi luff cikin ruwan a hankali ta soma jindaɗin ruwan ganin ta nutsu sai ya fita ya koma kicin ya dawo
mata da wani ruwan ya juye ma ta a bokiti ya ce "in kin fito kiyi wanka ki yi sallah nagode Allah Ya yi miki
albarka in sha Allah zan zame miki garkuwa kuma abin alfahari ba za ki kama ni da laifin cin zarafi ki ba
na miki alkawarin riƙe ki da amana." Daga haka ya sa kai ya fita daga bayin.

Mamaki bai bar kan fuskar Marhaba ba ba ki buɗe ta bi bayan shi da kallo. A ƙasan ranta kuwa daɗi take
ji sosai na rike darajarta da ta yi ta kawo ɗakin mijinta ko a haka ma Alhamdullilahi tayi alkawarin
kyautata masa daidai gwargwado.

[6/17, 12:42 PM] Ummulhair S Panisau: A CIKIN IDO.....

NA

Ummulkhairi S Panisau.

(KhairatUp)

Karamci Writers Association.

(Karamci shi ne tushen mu'amala tagari)

Gaba ɗaya kunya suka saukar mata ta ma rasa me zata ce da shi haƙuri ya kamata ta ba shi ko zagin kan
ta ya kamata tayi?

"innallillahi me na yi ne wai ni Marhaba?"Bata da amsa haka ta tashi gwiwa a sage ta fita daga ɗakin har
wani leƙe ta dinga yi ko yana falon dan kunyarsa ma take ji Wallahi.

Fuskar shi a murtuke ya zauna ƙwam a falon yana kallon tv ran shi ya gama ɓaci da duk saboda mata
biyun Sabreen da Marhaba gaba ɗaya sun gama caja mai kai.

Bata da wani zaɓi da ya rage ta je ta ba shi haƙuri.


Tsugunawa ta yi a gaba shi ta na nuƙu-nuƙu ta na haɗa hannayenta biyu ta rasa ma ta ina za ta fara.

Yaya Alee dan Allah ka yafe min ka yi haƙuri na san ban kyauta ba amma ka samu wani wuri a cikin ranka
ka yafe min ba da gangan nayi ba..

Ya wuce kije.

Yadda ya amsa da bambamci da yanayin fuskar sa sai ta ji ba ta gamsu da haƙurin na sa ba.Ta yi rau-rau
da idanuwanta tana son ƙara yi masa magana amma ya yi saurin ɗaga mata hannu alamar ta rabu da shi.

Sum-sum ta miƙe ta yi hanyar ɗakinta jikinta a sanyayye. "Na ga ta kaina ni kam me na yi haka?"

Aliyu.

Bin bayan ta ya yi da kallo ya saki tsaki in ban da ma shirmammiya waye zai ɗauki maganar wadda ake
takarar soyayya da ita? wai matar cushe shi an gayaa mata in bai san abu ko za a kashe shi ba zai amsa
ba bare kuma mata fa matar da ake so ya haihu da ita.. mtsw Sabreen bata da hankali yau ya tabatar da
akwai abin da ya ke damun ta shi yasa take yi masa hakan. Gaba ɗaya na gama yanke hukuncin abin da
zai yi ya ga alama maganar rashin kwana a ɗakinta ya fi sosa mata rai kuma bai ga laifinta ba tunda dama
auren ya haɗa da hakan da wanan ya yanke kawo ƙarshen zaman da suke yi ko dan martabar ta ma da
ƙimarsa kila in ta ji nauyin sa bakinta ya buɗe in wata ta kuma zuwar mata da irin wanan maganar ta mai
da martani.

Misalin ƙarfe goma sha ɗaya na dare ya gama shiryawa ya isa ɗakinta ya yi mata izinin bin sa ɗakinsa.

Sai da ta yi ɗan jim kafin kafin ta tashi ta zura hijab ɗin da take yin sallah ta saka slifas ɗinta ta saka ta
nufi ɗakin nasa.

Salamu alaikum.
Wa'alaikum salam.

Yaya gani.

Bismillah oh kawo min tea tukuna ki zo. Da to ta amsa masa kafin ta fita daga ɗakin. Ba tare da tunanin
komai ba ta dafa masa shayin yadda yake so ta kai masa.

Sai da ya gama sha tas ya kuma umartar ta da ta mayar kicin ta kuma kashe komai ta dawo akwai
maganar da yake so su yi da juna tukuna.

Yadda ya ce hakan ta yi masa. Gefen shi ya nuna mata da hannunsa. Nan da nan jikinta ya soma ƙyarma
ta zauna gefenshi tana mazari. Ai numfashinta bai ɗauke ba sai da ta ji ya sa hannunsa ya riko ƙugun ta
gam ya haɗa da jikin sa ya sauke kan sa a kan ƙafaɗarta yana shinshina wuyanta kamar kare ya ga abin
ci.

Bata san lokacin da tace "La'ilaha illallahu Ya Aliyu me ye haka?"

Ciki-ciki ya ce "Kar ki hana ni so nake na maida ke matata yau ba gobe ba."

"Ya Aliyu ka yi haƙuri".

"Aa bazan iya ba dole na nunawa duniya ke matar so ce ba matar cushe ce ba."

Tana ji tana gani ya dinga nuna mata soyayya mara algus duk ta fita daga hayyacinta ta kasa hana shi
abin da ya yi niya , bata gane abun nayi ne ba sai da taji yana niyan shiga cikin babban birinta yakushi da
cizo kuwa Aliyu ya sha shi ya fi a kirga amma ko gezau ko a jikinsa wai an tsikari kakkausa.

Aliyu bai taɓa shiga wata duniya mai daɗin duniyar da Marhaba ta kai shi ba , ya kara gane cewa mata
ababen so ne kuma dole rayuwa sai da su. Albarka kawai yake sa mata saboda tukuicin kanta da
mutunta da rike da daraja yana alfahari da shi ne ya fara kasancewa tare da ita fara'arsa ta kasa ɓoyuwa
ko ƙanƙani. A hankali ya sauko daga kan gadon ya ƙara rufa mata zanin gadon ya fita falo kicin ya shiga
ya ɗora ruwan zafi a kettle ya zauna a falo bini-bini ya saki murmushi. Ruwan ko na tafasa ya shiga
banɗakin ya juye ya kuma komawa ya saka wani sai daga haɗa mata ruwa a wani bahon wanka ya saka
gishiri kaɗan ya koma ɗakin ya lallaba ya tashe ta aiko yana ɗaga ta ta yi saurin buɗe idanuwanta ta
ganta a hannunshi wata kunyarsa ta ƙara rufar mata tayi maza ta runtse idanuwanta ruf tana ji tana gani
ya sa ta a cikin ruwan tayi zillo ta miƙe ya maidata ya sunkuya daidai saitin kunnenta yace ma ta "ki yi
haƙuri ki zauna a ciki za ki ji daɗin jikin ki sosai hakan zai saka wurin ya daina yi miki zafi ko ba kya so ki
warke da wuri?"

Sai tayi luff cikin ruwan a hankali ta soma jindaɗin ruwan ganin ta nutsu sai ya fita ya koma kicin ya dawo
mata da wani ruwan ya juye ma ta a bokiti ya ce "in kin fito kiyi wanka ki yi sallah nagode Allah Ya yi miki
albarka in sha Allah zan zame miki garkuwa kuma abin alfahari ba za ki kama ni da laifin cin zarafi ki ba
na miki alkawarin riƙe ki da amana." Daga haka ya sa kai ya fita daga bayin.

Mamaki bai bar kan fuskar Marhaba ba ba ki buɗe ta bi bayan shi da kallo. A ƙasan ranta kuwa daɗi take
ji sosai na rike darajarta da ta yi ta kawo ɗakin mijinta ko a haka ma Alhamdullilahi tayi alkawarin
kyautata masa daidai gwargwado.

Alhaji Doko zaune a farfajiyar gidansu kan farar kujera gabasa flask din shayi ne da kofuna guda biyu.
Daga ɓangaren daman shi kuwa motocin gidan ne guda uku akwai fara akwai baƙa akwai kuma katuwar
jeep baƙa. Shukokin da ke kewayeda gidan suka ƙarawa farfajiyar gidan ado da kwalliya ko ina korayen
ganye ne. Agogonsa yake ta dubawa da alamu yana jiran wani ne. Shaddar jikinsa nayi wa kallo ɗaya na
san naira tayi kuka a wurin cikin aljihunsa ya zira hannunsa ya ɗauko wayarsa ya danna jim kaɗan ya kara
ta a kunnen shi yana jiran a amsa masa.

Ban ji abinda ya faɗa ba ya dai maida hankalinsa kan gate ɗin shigowa cikin sa'a kuwa yana juyawa ya
ga wanda yake jiran ya iso.

Wayar ya maida cikin aljihunsa ya kuma gyara zamansa yana murmushi.

Wani matashin saurayi ne ya shigo ƙananun kaya ne a jikinsa tsaf abin shi babu ƙazanta. Rissinawa yayi
ƙasa yana gaida Alhaji Doko.

"Sannu da zuwa Malam Junaidu ina ta jiran ka tuntuni nake son shiga kasuwa amma ka ɓatan lokaci"
ya faɗa da fara'a kan fuskarsa alamar wasa yake yi masa shi ma.
Kai ya ƙara saukewa ƙasa yace"Tuba nake Alhajin Allah ka yi haƙuri takardun ne ban samu sukunin
kamalawa ba sai ɗazu ayi mini afuwa."

"Na maka Junaidu." Suka yi dariya tare. Nan suka zauna suka cigaba da tattaunawa a tsakaninsu.

Hajiya Barira Doko zaune a gaban Mami tana yi mata wani irin kallo na takaici da baƙin-ciki gaba ɗaya
bata taɓa ganin mace ma kafiya da taurin zuciya irin ta Mami ba tsaki kuwa tayi shi cikin carbi amma ta
kasa daina mamakin hakan.

Aunty ki daina yi mini irin wanan kallon dan kin san zuciyata ba zata rissina ba sai lokacin da aka rabani
da wannan alakakai ɗin. Duk kun kasa fahimta ta ko a wancan lokacin yanzu ma haka ni babu wanda
yake tunani na ko halin da nake ciki....

Dakata haka malama shegiya mai mugun abuda taurin kai. Dan ubanki a wannan shekarun in aka sake ki
uban me za ki tsinta wace riba za ki samu? ina za ki kai hakkin mutumin nan ke hatta ƴa'ƴan da kika haifa
basu tsira daga uƙubar ki ba don me ke kaɗai kin hana kowa sukuni shekaru sun shuɗe kina nan jiya i yau
ni.....

Ba za ki gane ba Adda ba za ki ji irin raɗaɗi da bacin ran da nake ciki ba ,duk lokacin da na kalli mutumin
nan haushin kaina nake ji.

Yanzu ta daina ba wa kowa mamaki sai haushi da taƙaici. Tsakin dai ta kuma saki ta miƙe tace "Allah ne
kaɗai zai sassauta wanan zuciyar taki."kin ga tafiyata.

Riko hijabin Addar tayi tace "Adda a cikin ido...."

"Wanan ya wuce haka abun da yake damun ki gaba da haka ne ba zan daina gaya miki ba kin cuci kan ki
kuma kin shiga hakkin ƴa'ƴan da kika haifa a cikin ki ina roƙon Allah da ya sa ki gane ki dawo hayyacinki
don kuwa kin jima da ɓata wanda ya ɓata kuwa ƙoƙarin nemansa ake.
Kuka Mami ta saki ta saka hannunta kan bakinta ta danne sautin kukanta. Adda Barira kuwa fita tayi jiki
a sanyayye tana share ta ta ƙwallar na tausayin ƴar'uwarta.

Hajiya Barira na fita suka yi kiciɓis da Alhaji Doko zai shigo. Da baya ya koma yana murmushi yace "Hajiya
yau kin kawo mana ziyara ?"

"Wallahi kuwa Alhaji ya kasuwa?"

Kasuwa Alhamdullilahi ya yaran kwana biyu basu leƙo mu ba.

Suna nan lafiya ka san gidan naku yanzu babu yara shi yasa amma zasu zo su gaishe ka da yardar Allah.

Allah Ya kawo su.

Alhajiya na san kana haƙuri da Mar'yam ina so ka ƙara a wanda kake yi wata rana sai labari.

Murmushin ƙarfin hali yayi ya ce "Hajiya kenan wata ranar nan ba zata zo ba ko kin manta shekarun da
muka kwashe? kina gani fa ƴa'ƴanmu goma amma babu abinda ya sauya bare ya canja.

Kasa cewa komai Adda Barira tayi kawai sai tayi masa sallama ta yi gaba abin ta.

Kusan mintuna biyar ya ƙara kafin ya shige ciki cike da ciwo a ƙirjinsa.

Bai nufi ko ina ba sai ɗakin Mar'yam aiko ya dinga jiyo sautin kukant da sararrafa ya isa ɗakin nata jiki na
rawa ya tsuguna a gabanta.

Ƙamshin turatensa ya doki hancinta tuni ta ɗago idanuwanta ta sauke masa su hatta tsigar jikinsa sai da
ya tashi saboda kaifin idanuwanta a kansa. A zabure ta tashi daga kan kujerar tilo dake cikin ɗakin nata
ta nuna shida yatsa cike da tsiwa da rashin kunya take nuna shi.
"Ban gaya maka kada ka kuskura ka ƙara shigowa ɗakina ba? ban gaya maka ba. Wallahi bana son
ganin ka Alhaji Sufyan bana ƙaunar ganinka a inuwar da nake kayi wa Allah ka rabu dani ka rabani da
kowa ka shiga rayuwata a lokacin da ban buƙata ba ka janyo min abubuwa da dama a cikin rayuwata ka
sake ni mana na huta kai ma ka huta.

Mar'yam ba zan iya sakin ki ba koda kuwa naman jikina za ki saka wuƙa kina yayanka ba zan ƙi ki ba
soyayyar ki ce Allah Ya jarrabce ni da ita ba zan iya daina son ki ba kuma ba zan iya rabuwa da ke ba ba ki
san yadda nake ji ba....

Dariya tayi kamar tuburan fuskar nan shaɓe-shaɓe da hawaye ga bakin kwallin da ta shafa ya soma bin
hawayen fuskarta sai ta ɓaci da baƙin kwalli. Idanuwan nan sun yi jajir ta maka masa harara haɗe da
sakar masa tsaki ta yarfa hanunta tace "Dalla gafara can da anyi magana kace so so so son banza son
wofi wane irin so ne wannan bayan kan ka kawai kake so da ace kana sona da tuni ka so abinda nake so
ma'ana ka sauwake mini nay rayuwata yadda nake so kan ka kawai kake so mugu azzallumi....ta haɗiyi
zuciya ta share hawayen da ke bin fuskarta ta cigaba Wallahi bana son ka kuma ba zan taɓa son ka bana
ma son mai son ka bana son haɗa hanya da shi.

Yau abun ya waiwayo ta jima bata yi masa irin wannan tsiwar ba sai yau dama ya sanin shigowa ɗakin
nata yake yi zuwa yanzu.

Ya kamata na ci darajar ƴa'ƴan da ke tsakaninmu bai kamata ki dinga jifana da irin waƴanan munanan
kalaman ba ni fa mijinki ne uban ƴa'ƴanki.

Wani irin kallo ta watsa masa ta ja wani dogon tsaki ta sakar mai a fuska ta murguɗa baki tamkar wata
ƙaramar yarinya tace masa "Sufyan!Sufyan! na rantse da Allah ba zaka ci darajar kowa ba ,ban ma ɗauke
ka a matsayin mijin ba bare ka ci wanan darajar. Ban ma ɗauki yaran ka da wata tsiya ba bare ka ci
darajarsu a wurina yaran da in ta ni ce ba zan haifesu ba amma Allah Ya ƙaddara hakan kuma kai ka san
ta yadda ka samo su ba da son raina bane hasalima yaudarata kayi ka same su shi yasa na bar ka dasu
can ku ƙarata da gaske nake yi maka a shekarun baya yau ma na maimaita ba gudu ba ja da baya
wannan ƙiyayyar ba zata gushe ba har sai lokacin da ɗayanmu ya gushe.
Tuni labbanshi suka bushe yaji wani irin ciwon kai ya sara masa shi fa ba haushinta yake ji ba kawai
burinsa guda ne a duniyar nan Mar'yam ta ce tana son shi baya ganin laifinta ita ya cuta ita ce ba a yi wa
adalci ba amma ya zai yi? ba yin kansa bane Allah ne Ya ɗora masa.... bai gama tunanin ba ta saka masa
ihu ya fitar mata daga ɗaki idan kuma yana taƙama gidansa ne ya yi mata izini ta bar masa gidansa.

Sum-Sum ya ja da baya ya fice daga ɗakin hanunsa akan kirjinsa ya na masa wani irin dukan lugude.

Amaryar Alhaji Sufyan Doko ta share hawayenta tausayin Alhaji take ji da ma ƴa'ƴansa ta rasa dalilin
wana baƙar ƙiyayyar tabbas idan ka ce ba ka son abu to fa har a cikin ido yake maka tsawurya.

[6/17, 12:42 PM] Ummulhair S Panisau: A CIKIN IDO.....

NA

Ummulkhairi S Panisau.

(KhairatUP)

Karamaci Writers Association.

(Karamci shi ne tushen mu'amala tagari.)

Kafin Abban Doko ya ƙaraso Sajida da Mariya sun ji labari sun iso sai faɗa suke yi wa Ahmad da ba'a gaya
masu ba.

Abban Doko na isowa dakta.Faruk ya fito daga ɗakin da aka ajiye Abba.Gaba ɗaya suka nufi inda dakta
yake suna tambayarsa jikin Alhaji.
Cike da ɓacin rai ya kalle su kafin yace "Gaskiya ba kwa son bawan Allahn nan da kuna son shi da kuna
kiyaye lafiyarsa da kuma ka'idojin da aka ce ku bi. Mutumin da yake fama da ciwo irin na zuciya bai dace
a dinga ɓata masa rai ba ko kun san matakin da yake a halin yanzu? matakin dayake ciki ko wanne irin
lokaci zaku iya rasa shi saboda zuciyarsa dab take da ta daina aiki jikinsa ma ya daina ƙarbar magani
yadda ya dace.

Duk suka kasa cewa komai suka bi shi da kallo suna jiran karin bayani.

Za ayi masa aiki yanzu dai na yi abinda zan iya akwai yuwuwar a saka masa wani mashin a cikin zuciyarsa
wanda sai da shi zata dinga aiki yadda ya kamata nayi magana da likitan da na sani specialist ne a wanan
ɓangaren a can Egypt yake zai baku appointment sai kuje ya duba shi ya gaya muku abinda ya kamata ayi
amma kafin nan ku kula sosai kar a kuma ɓata masa rai domin kuwa komai ƙanƙantar ɓacin rai zai iya
sakawa ku rasa shi. Daga nan ya sa kai yayi gaba abin sa.

Kuka matan suka saki suna jin ciwon halin da mahaifinsu yake ciki silar mahaifiyarsu in har wannan shi ne
so to Abba bai iya zaɓen soyayya ba yayi zaɓen tumun dare.

Alhaji Idris da lokaci ɗaya ya zabge ya gyara zaman babbar rigarsa ya samu gu ya zauna ajiyar zuciya
kawai yake saukewa baya jin Doko amininsa zai sha saboda in dai a kan soyayyar Mar'yam ne ba zai
russina ba ko da kuwa dan lafiyarsa ce sonta da ƙaunarta a jininsa yake ba zai taɓa kankaruwa ba
muddin ba Mar'yam ce da kanta zata amsa tayin soyayyar sa ba to fa ba zai taɓa barin zuciyarsa tayi
sakat ba. Ba shi da sauran hope akan Sufyan Doko.

Cike da jimamin halin da Abba yake ciki suka koma gidajensu saboda likita yace su tafi yana bukatar hutu
ba zasu ba wa kowa damar ganinshi ba sai an kwana biyu yana under observation ne. Ahmad ne ma ya
so yayi gardama Abba ya taka amsa burki ya gaya masa akwai nas da likitoci zasu saka ido a kansa in sha
Allah zai tashi babu abinda zai same shi.

Marhaba kuwa bata san me yake faruwa ba ta gama komai da ta saba tayi wanka ta saka wata doguwar
riga baƙa mai adon duwatsu ta yafa mayafinta. Ba wata kwalliya tayi ba man leɓe kawai ta shafa ta saka
kwalli a idanuwanta suka ƙara haske sau biyu tana komawa ɗaki tana karewa kanta kallo a madubi
saboda ta burge mijinta.
Aliyu kamar yadda ya faɗa biyawa yayi ta gidan abinci ya siyo musu tuwon shinkafa miyar agushi da
nama a ciki. Ya tsaya ya sai mata fresh milk da tsire irin wanda take so sanan ya nufi gida.

Tun kan ya buga ƙofar ta buɗe masa da fara'a a kan fuskarsa duk da yana cikin yanayi mara daɗi hakan
bai hana ya rungumeta a jikinsa ba sai da ya sumbaci goshinta tukuna ya miƙa mata ledar hannuns ta
karɓa da sauri ta ce masa "Sannu da zuwa Sukooni."

Idanuwansa ya ƙarawa girma saboda mamakin sunan da ta kira shi da shi *Sukooni* dan ya daɗa
tabatarwa ya nuna kansa da yatsa alamar "ni"?ta gyada masa kanta tace "kai mana."

Janyota yayi jikin shi ya rungumeta ta gefe ya sumbaci goshinta a hankali yace "Nagode". Tare suka shiga
ciki ta kwashe abubuwan da yazo dasu tayi kicin ta zuba musu a plate ta kai falon ta koma ta ɗauko ruwa
ta kai ta taho da ƙananun kofuna saboda youghrt ɗin ta ajiye masa.

ƊaKi ya shiga ya wanke bakinsa da hannaynsa biyun ya goge da tawul ya koma falon tare suka ci abincin
suna hira, daga bisani ta kunna masa tibi saboda ƙa'idarsa ce sai ya kalli maimaicin wani shiri yake
kwantawa.

Da kin kashe ma Hayati bacci zanyi bana jin daɗi na gaji kaina ciwo yake yi min.

Cike da damuwa ta kashe ta koma kicin ta ɗauko akwatin first aid ɗinsu ta nemo masa PCM ta kai masa
da ruwa yana sha tana yi masa sannu. Ɗaki ya wuce saboda da gasken a gajiye yake kuma yana cikin
damuwa tunda ya ga halin da Abban Doko yake ciki ga takurar Sabreen....

*Sukooni* ko akwai abinda kake so na kawo maka kuma?

Aa ba komai ki zo ki kwata ki huta.

To ka kwanta ni sai nayi sallah ka sani.


Aa ki kwanta zan tashe ki ƙarfe biyu ko uku sai muyi tare.

"To." Kawai tace da shi ta shige banɗaki.

Tausayinta yake ji sosai dan jikin Abban Doko ya sa jikinsa yayi sanyi sosai.

Da ta gama shirinta ya mannata da jikinsa kamar za a ƙwace masa ita suka yi baccinsu.

Wani abu ne mai nauyi taji yana yi mata kai kom o daga makogwaronta zuwa ƙirjinta. Ji take yi kamar ta
fasa ihu ta juya ta kalli ƙawarta Amira ta yi tsaki tace "Wallahi Amira ba zan bar Aliyu ya tafi a haka ba
dole sai nayi maganinsa."

Amira ta gyara zamanta tace "Haba Sab ya kamata ki zubar da makamanki akan wannan Aliyun ni duk
haushi kike bani mutumin da yayi aurensa ya bar ki har wani tunaninsa ma kike yi? Ki manta da shi
malama ki samu wani amma kafin nan ungo wannan ki rageta" ta miƙa mata wata ƴar ƙaramar ƙwalba ta
maganin nan tramol.

Amira me wannan?.

Maganin damuwarki ne ki sha ki yi fanka kawai ki huta ki manta da wani Aliyu da tsiyar soyayyarsa.
Malama in kika kasance da ni zaki anfanu nan kinga wannan ta ɗauko kudi ƴan dubu-dubu ta watsa
mata su a kan cinyarta tana taunar cingum irin na ƴan duniya ji kake ƙas ,ƙas ,ƙas tana jijiga ƙafafu.

Sabreen ta ƙarbi ƙwalbar maganin ta dinga jujuyawa bata son sha amma Amira ƙara ƙwaɗaita mata abin
take yi. Ba tare da wani dogon nazari ba ta kafa kai a kan bakin ƙwalbar ta shanye tas.

Amira tayi wani malalacin murmushi tace "Ko kefa ƙawata barkanki da shigowa cikin da'ira."
Sabreen kuwa magani ya fara ɗaukarta bata gane me Amira take cewa tayi luu ta kifa ta kwanta a kan
katifar da ke tsakiyar ɗakin.

Saida ta tattaɓe ko ina na jikin Sabreen taji bata motsi kafin ta kuma sakin dariya ta sa shewa ta faɗa
kanta.

Kwanaki biyu aka yi ana jinyar Abba ba a bari kowa ya gan shi don yana buƙatar ya huta sosai. Babu
ranar da Abba Idris Doko baya zuwa a asibiti sai dare yake komawa zaku yi mamakin har lokacin Mami
bata je asibitin ba bare ta tambayi wani yaya jikin Abban harkarta kawai take yi. Da yawa daga cikin
yayyunta sun fawalawa Allah komai kullum addu'a suke yi mata Allah Ya ganar da ita ya sanyayya mata
zuciya.

Dole suka nemi appointment da Daktan da aka haɗasu da shi a can Egypt. Nan da sati biyu zasu tafi sun
gama biyan komai da Ahmad da aunty amarya da Abba Idris za ayi tafiyar duk da Amina ta so a tafi da ita
Abban Doko ya hana kuma ya ƙara gargaɗinsu da kada su kuskura su faɗawa Marhaba halin da ake ciki
da jikin Abban.

Kowa ka gani a ahalin Alhaji Sufyan babu walwala bare annuri a tare dasu. Ita kuwa Marhaba bata ma
san me ake ciki ba amma jikinta yana bata akwai wani abu sau uku tana tambayar Yaya Aliyu izinin zuwa
gida ganin Abba ya hanata haka sai yace zai kai ta ba yau ba ba gobe ba.

Suna bacci ta tashi a firgice tana salati sai gumi take yi duk da sanyin Ac ɗin da ke tashi a ɗakin.

Fitilar ya kunna ya riƙo hannayenta biyu yace "Lafiya Hayati me nene?"

"Ya SUKOONI mafarki nayi mara kyau Wallahi akwai matsala me ya samu Abbana bana samun shi a waya
kai kuma ka hanani zuwa na gan shi wayyo Allah Abbana dan Allha ku kai ni wurin Abbana."
"ki nutsu mafarki ne kawai babu abinda ya samu Abbanmu yana nan cikin ƙoshin lafiya ɗazu ma mun yi
waya sun yi tafiya ne da Abban." Ya samu kansa da gilla mata ƙarya.

Bata yarda da shi ba amma babu yadda ta iya sai dai ta gama yankewa da safe zata kira Aunty Sajida taji
ko lafiya.

Haka ya lallabata ta kwanta a kan ƙirjinsa yana shafa bayanta kamar wata ƴar ƙanƙanuwar yarinya.

Hajiya Hauwa ce zaune ta kama haɓarta tana jimamin abinda yake afkuwa cike da ƙwafa ta juya ta kalli
Barira da Aishatu tace "Yanzu wannan yarinyar dama bata sauya hali ba lullubin biri tayi mana ta sauya
taku? Ina nan ina murna shiru an jima ba a ji wani tashin hankali ko hayaniya ba ashe ashe da sauranta?
wai me take nufi ne da rayuwa wanan wacce iriyar ƙiyayya ce abu sai kace babu ilimi kai wannan yarinya
Allah Ya wadai da halinta. Goronta ta ɓantaro ta saka a baki ta kuma gyara zama tace "Ku kai ni gidan
nata dan ubanta na tasa ta a gaba taje asibitin nan sai kace mai kafirar zuciya miji wasa ne kai Allah Ya
jikan marigayi amma ya tafi ya bar baya da ƙura." (Hajiya Hauwa ƙanwar mahaifin Mami ce,uwarsu ɗaya
ubansu ɗaya.) Tun ƙuruciya ake yin wannan tataɓurzar har girma kai ina dalilin wannan kaddara.

Hajiya Barira tace "Wallahi Hajiya na rasa yadda zan yi da Mar'yam da anyi magana ta saka kuka tace an
riga da an cuce ta ba a san me take ji ba."

"Don ubanta mu da aka aurar damu uban me ya same mu ? ba gamu ba Alhamdullilahi mun yi biyayya
kuma mun ga ribar biyayya sai ita mai kunnen ƙashi?."

Aishatu tace "Wallahi Mar'yam ta wuce duk lissafinku kuma bazata ji ba har gara ma Hajiya ke in kika
tursassata zata je ta duba mutumin nan kina gani fa yaran da ta haifa ma ba barinsu tayi ba ni ban taɓa
ganin irin wannan abu ba Wallahi."

"Uh'uh wannan wane irin tashin hankali ne haka ni Hauwa?"


Haka suka tafi gidan Alhaji Doko a falo suka tarar da yaran da Amarya suna zaune sun yi jigum maida
maganar ma suke yi.

Sallamarsu Hajiya Barira ce ta dawo dasu cikin hayyacinsu.

Nan-da-nan Amarya ta kawowa Hajiya Hauwa ruwa mai sanyi da abinci a fulas.

Bar ni ƴar nan bar ni yaya jikin mijin naku?

Da sauki Hajiya Alhamdullilahi.

To Allah sa kaffara. Naji ance waje zaku tafi ko?

Eh aiki za ayi masa.

Inallillahi wa inna illahir rajun kai Sufyan Allah Ya haɗa ka da muguwar kaddara yo kaddara mana
wannan mata sai kace dutse sam babu Allah a ranta sai kafiya? Sajida tashi ki kirawo mini ita nan.

Sajida ta waro idanuwanta waje sosai ta rike ƙirji.

Aiko Hajiya ta hau salati tana sanar da ubangiji ta dafe ƙirji sannan tace "Yau naga abinda ya ishe ni ,wai
mala'ikar mutuwa ce ita da ake tsoronta? to dan ubanta ni nan daidai nake da ita mu muka haifeta ba ita
ta haifemu ba ubanta na sakin nono na kama.

Babu wanda ya hanata magana bare ya bata haƙuri abin na Mami sai addu'a kamar mai shafar jinnu
haka take.
Aisha tashi ke ki kira mini ita shashashar yarinya kawai.

[6/17, 12:42 PM] Ummulhair S Panisau: A CIKIN IDO.....

NA

Ummulkhairi S Panisau.

(KhairatUP)

Karamci Writers Association.

(karamci shi ne tushen mu'amala tagari.)

10

Ci kan ki babu wanda ya tankawa Hajiya Hauwa sai binbinin faɗa take yi ta kasa yin shiru bare haƙurin
Mami ta fito tamkar dai sune suka yi laifin ba Mamin ba.

Mami zaune kan kujera tilo da ke a cikin ɗakinta. Abun duniya duk ya ishe ta ba mamaki in za a auna
jininta ba ƙaramin hawa yayi ba. Amma babu wanda yake gane damuwarta duk a wurinsu ita ce mai
laifi ,babu wanda ya saka kansa a takalminta kowa laifinta yake gani tun shekarun baya har zuwa yanzu
bata ganin akwai wanda zai fahimci ciwon da take ji sama da wadda aka yi wa irin auren da aka yi mata.
Hawayen da suke bin fuskarta ta share ƙoƙarin tashi take yi ta ji alamar za a shigo mata ɗaki idanuwanta
ƙyam akan ƙofar bata yi ko da kuskuren ɗauke su ba.

Aishatu kaɗai da ta gani sai da taji gabata ya faɗi roƙon Allah ta fara yi a zuciyarta Allah Ya sa ba Hajiya
ce ta zo ba dan ba zata iya zuwa wurin wannan mutumin ba.

"Kin kafe ni da idanuwanki kamar wadda na ci miki bashi. Marar mutunci sai ki tashi ki zo Hajiya na
nemanki a falo." Daga haka ta sa kai ta koma.
Yawu ta haɗiya mai ɗaci kafin ta miƙe ta fita daga ɗakin. Ba zaka taɓa samunta a falo ba koda yaushe
tana ɗakinta nan ne wurin zaman ta kuma nan ne wurin baccinta a ciki kawai take yin rayuwarta don ma
kar ta haɗu da yan gidan musammn ma maigidan.

Tun daga nesa ta hango Hajiya da yaran da in za a yanka ta zai yi wuya ta canki sunayensu dai-dai
haihuwarsu kawai tayi amma rainonsu ubansu ne yayi.

Hajiya kuwa ta taɓe baki kafin ta gyara zamanta a ƙasa kasancewar bata son zaman kan kujera saboda
ƙafa.

ƙasa take ƙoƙarin tsugunawa Hajiya tayi maza tace "kul tabbatacciya marar kunya ba sai kin yi haka ba za
ki nuna baki da mutunci ba yau ke ko kunya ba kya ji ? ke koda mutumin nan wani mugun abu yayi maki
ai kya tausaya masa saboda zaman tare ni wai mene ne laifin Sufyan ne? ...."

Bata barta ta ƙarasa ba tana hawaye tace "Laifinsa ɗaya aure na da yayi da bai aure ni ba da ƙila ina can
ina tawa rayuwar mai daɗi da ƴanci kamar kowacce mace , da ƙila ina rayuwa da ƴa'ƴana ciki farin ciki da
kulawa gaskiya ba a kyauta mini ba da aka kashe mini rayuwa."

"Na jima ina mamakin anya kuwa jininmu ce ke? Saboda baƙar zuciyar ki tayi yawa Mar'yam. To duk naji
tashi ki ɗauko mayafinki muje ki duba Sufyan."

"Kiyi haƙuri Hajiya ba zan je ba Allah Ya bashi lafiya amma ina roƙonku da ku gaya masa ya sauwaƙe mini
ba zan so nayi masa takaba ba."

Gaba ɗaya yaran suka saki gunjin kuka ji kake wiwi-wiwi ta ko ina kuka suke suna daɗa kowa ga kewar
mahaifinsu ga ƙiyayyar mahaifiyarsu yaya take so su yi ne wai?

Salallami Hajiya ta saka daga bisani kuma ta saki kuka irin kukan nan na taƙaici da baƙin ciki gaba ɗaya
yarinyar ta daina bata tsoro mamaki take bata kawai.
Adda Aisha ta sa hannu ta sauke mata shi a fuskarta a ɓarin dama ta ƙara mata a ɓarim hagu baƙin ciki
da taƙaici ya saka ta rufar mata da duka tana zaginta tamkar dai a gwawarmayarsu ta da.

Ko da za ku zare numfashina daga jikina ba zan fasa ba kuma ba zan janye ba da zaku yi min adalci ma da
kun yi min dukan da zan daina numfashi a doron duniya.

"Aa Aishatu bar ta bar ta ki ƙyaleta ai yanzu ta wuce duka sai nasiha kuma bata ji ku bar ta da halinta.
Nagode Mar'yam da kika nuna min ba ni ce uwarki ba kuma ba ni ce ubanki ba ban isa da ke ba to kije na
cire hannuna daga lamarinki ki ɗauka muddin yau ba ki je kin duba Sufyan ba babu ni babu ke a duniya
har lahira sakarya kawai wadda bata san annabi ya faku ba.

Su Amina basu taɓa ganin irin wannan tashin hankalin ba ko da Mami bata son su ai su mahaifiyarsu ce
suna sonta.

Tashi tayi ta nufi hanyar da zata sada ta da ɗakinta bata jima ba ta ɗauko hijabi da takunkumin nan na
fuska (facemask) ta saka bata ce musu komai ba tayi waje.

Haka jiki a sanyayye suka bi bayanta. Amina ce ta tuƙa su yayin da Bala ya ɗauki sauran suka tafi asibitin.

Sabreen da ta dawo cikin hayyacinta sai taji kanta yayi mata nauyi bata gani sosai. Hannunta ta saka ta
dafa kanta da yayi mata wan gingiringin tana yamutsa fuska.

"Amira me kika bani haka nake jina ba a hayyacina ba?"

Dariya taji wadda ba iya ta Amiran bace haka ya saka ta ɗaga kanta ta bi ɗakin da su kansu da kallo su
biyu ne ta dai san Amira amma bata san ɗayar ba sai kanta ya ɗaure.

Amira na dariyar shaƙiyanci tace "Ya kika ji ki ƙawata?"


"Ban gane ba ya ko zan ji ni kin cuce ni me kika bani na sh...."

Ashe dai muryarta ma da zaƙi kamar yadda ƙasanta yake da zaƙin." ɗayar ta faɗa suka tafa suna ihu.

Wata iriyar zabura Sabreen tayi ta fara ji kanta yana dawowa daidai innallillahi wa inna illahir raju'un ta
dinga faɗa tace "Dan Allah Amira me kuka yi min? meye haka ina kayana? na shiga uku wayyo Allah na
me kuka yi min?"

Su kuwa dariya suka dinga yi mata tare da matsawa jikinta sosai suka saka ta a tsaƙiya suna shashafa
mata jiki cike da iyawa da karuwanci.

Ƙawata na jima da ƙwaɗaita da ke sai dai sanin ba kya wannan layin ya saka ban taɓa nuna miki
zalamata ba sai wannan karon na samu nasara cikin sauki. Ke wa ya damu da wani namiji yanzu bada ya
loda miki kayan baƙin ciki da taƙaici , ki saki jikinki kawai a gara harkar nan da ke dan za ki yi arziƙi kuma
za ki ji daɗin hakan.

Amma Amira Allah Ya isa tsakanina da ke muguwa azalluma maciya amana.

"Wayyo Allah kiyi haƙuri kar bakin ki ya kamani" ta faɗa tana fashewa da dariyar ita da ƙawarta cike da
shaƙiyanci.

"Kina ji na? ki saki jikinki kawai mai afkuwa ta riga da ta afku ni nan nake gaya miki za ki dawo da kan ki
mu ma ba so muke ba amma haka aka koya mana harƙar ta ƙarfi kuma ba zamu dulmiya mu kaɗai ba sai
da abokan tafiya shi sa muka ɗan kara ki ayi dake na san idan kina cikin hayyacinki ba za ki bada goyon
baya ba shi yasa na biyo miki ta ƙarƙashin ƙasa."

Sai na gayawa ƴan'sanda ba zan bar maganar nan haka ba sai na kai ƙarar ku ta kett a min haddina da
kuka yi sai na kai ƙararku.
Ƙawar Amira tace "Ki je sis sai kin dawo amma kafin ki kai ƙarar mu ina so ki duba wannan bidiyo ɗin
kamar kece a ciki kina jidaɗin rayuwarki da mu ga kayan maye kinga shi kenan in muka ɗora babu wanda
zai ƙara kallonki da ƙima da mutunci , Aliyun ma duka zai miki wata ƙila ma a ƙi aurar ki ko iyayenki ma
su fitar dake daga gidansu. Wayyo har na tausaya miki. " ta ƙarasa faɗa da fuskar tausayi kamar gaske
tana jujuya kai da wayar.

Ragwaf ta koma da garu ta haɗe kai da guiwa ta saki kuka na jin haushin kanta da ta kasa tawakal ta
kawo kanta wurin muguwar ƙawa yanzu wa gari ya waya? ba wan ba ƙanin.

Kije kiyi shawara mun baki kwana biyu ki gama tsarawa kan ki mafita ko shigowa tawagarmu ko kuma
mu baza wannan ɗaukar duniya ta gani.

(Wata sabuwa Sabreen kin ga ta kan ki).

[6/17, 12:42 PM] Ummulhair S Panisau: A CIKIN IDO....

NA

Ummulkhairi S Panisau.

(Khairatup)

Karamci Writers Association.

(Karamci shi ne tushen mu'amala tagari.)

11

Su Naseer na hango shigowarsu Mami ya taɓo ƴan'uwansa ya nuna musu hanya.

Ahmad da Imran suka miƙe tsaye. Hajiya aka riƙe saboda tsufa ƙarfin hali kawai take ta fito.
Ƙasa suka tsuguna suka gaishe su Hajiya dasu Adda Barira suka amsa masa suna tambayar mai jiki.

Da sauƙi Ahmad ya faɗa yana kallon ɓarin da Mami take a tsaye yana son yayi mata magana yana
shakkarta don a cikinsu shi da Marhaba sune suke da ƙullafucin uwa.

Bata ce musu komai ba ta tsaya kawai ƙiƙam tana kallonsu ɗai-ɗai amma cikin ranta baƙi-ƙirin gaba
ɗayan ƴan wajan haushinsu take ji duk an wani takura mata wai ta duba wannan mutumin.

Ahmad ya ce dasu "Bismillah ku shigo amma bacci yake yi ma."

Allah sarki Sufyan Allah dai Ya bashi lafiya ya yaye masa wannan larurar.

Amin! Amin ! suka amsa mata.

Tare suka shiga ɗakin dukaninsu. A kwance yake kan gadon asibitin hannunshi na dama a kan saman
cikinsa ana masa ƙarin ruwa ga life supporting machine a gefensa yana aikinsa sai ƙara yake yi di!di!di!di.
Lokaci ɗaya kuwa ya zabge ya rame har wani duhu yayi kai baka ce yana numfashi ba abin tausayi.

Hajiya ta tausaya masa matuƙa ta dinga kwarara masa addu'ar samun lafiya suna amsawa da ameen.

Tunda suka shigo ɗakin tayi masa kallo ɗaya ta ɗauke kai bata ƙara koda marmarin ƙallon ɓarin da yake
ba. Ji tayi ma kamar ana azalzalar mata zuciya kamar an cinna mata wuta haka take ji da gasken-gaske
bata son Alhaji Sufyan kuma bata jin akwai lokacin da zata ji tana son sa wata iriyar wutar ƙiyayyarsa ce
take nuƙurƙusarta a ƙoƙon ranta.

Alhaji Doko kuwa a jikinsa yaji Mami na ɗakin da ƙyar ya buɗe idanuwansa yana laluben ta inda zai ganta
amma ta ƙi bashi damar hakan.

Cikin magana irin ta marasa lafiya masu jin jiki yace "Mar'yam kamar ƙamshin turaren ki nake ji ,da
gaske zuwa kika yi ko kawai gizo kike yi min yadda na saba ji?"
Hajiya tace "Ba gizo bane Sufyan ga Mar'yam nan tazo duba ka kayi shiru ka daina magana."

Alhamdullilahi! Allah nagode maka niko yau da wacce iriyar sa'a na tashi Ahmad ,Imran ga babarku nan
ta zo ta duba ni ku taya ni godiya.

Tausayinshi ya gama kama su wai dama ana samun irin wannan makahon son?

Adda Aishatu ta ja hannun Mamin ta kai ta gaban Alh.Sufyan ɗin.

Da ƙyar ta haɗa kalmomin "Yaya jikin naka?" Ta faɗa fuska a turbune babu annuri kamar anyi mata dole
koda yake dolen aka yi mata daman don ko magana ma bata son ya haɗa ta da shi.

Da Sauki Mar'yam ,da sauki naji sauki ai tunda kin zo yanzu naji sauki jiki yayi kyau sosai Alhamdullilahi
sune daman suka ki bani sallama suna maganr kai ni waje a duba lafiyata gani suke yi ni rago ne wai
ɓacin rai kaɗan zuciayata zata daina aiki..... bata ma tsaya ƙarasa jin zantantukan nasa ba tayi hanyar
ƙofa tana tsaki.

Sai yayi shiru kawai yana jin wani iri amma ba ƙaramin daɗi yaji ba da zuwan nata sai yaji kaso tamanin
daga cikin raɗaɗin da yake ji ya kau daga jikinsa.

Sai jikunan sauran yan ɗakin ya ƙara yin sanyi.

Mami na buɗe ɗaki suka yi kiciɓus da Alhaji Idris. Kallon-kallo suka soma yi wa junansu kamar wasu
zakaru a filin yaƙi. Mugun haushin ta Alhaji Idris yake ji da ace yana da dama da tuni yayi maganinta
amma in ba zai iya ba saboda Sufyan. Ita ma ɗin haushin sa take ji matuƙa musamman da yake bin bayan
abokinsa tsaki ta ja mai tsayi ta ce masa "Malam ka bani hanya na wuce ka wani yi min tsaye a gabana."

Bai ce mata komai ba ya matsa mata ta fita fuuu kamar wata kabubuwa.
"Doko ka ganta ko? ai na gaya muku zata zo ta duba ni fa gashi tazo kuma dan Allah ku dinga haƙuri da
ita ba a kyauta mata bane ku daina jin haushinta dan Allah ni na ma warke ko yanzu mu tafi gida tunda
naga gwanata.

Wallahi Sufyan kai ne babban misalin nan da ake cewa "Iska na wahalar da mai kayan kara" na rasa
wacce iriyar zuciya kake da ita ba ? ba a son ka amma kana ƙara kai kan ka wai baka tausayinmu ne? mu
baka duba son da muke yi maka sai ka kashe kan ka a kan mace zaka ji daɗi?

Al'amarin Abba da Mami mamaki yake ba wa kowa na wurin dole ka ƙara girmama soyayya da kuma
tsorata da lamarinta Alhaji Doko da Mami kaɗai misalin wahalar so ne. Jikin ƴa'ƴan ya ƙara yin sanyi.
Tabbas so masifa ne.

Yau dai a gaba ta saka shi tana kuka sai ya kai ta gidansu taga Abba da Mami tayi mafarki yau ma
gaskiaya sai taje.

har farfajiyar gidan ta bi shi tana kuka.

Babu yadda ya iya da ita dole ya daka mata tsawar da sai da ta gwamance bata biyo shi wajen ba da
gudu ta koma ciki ta shige ɗaki.

Kan sa ya kifa aka sitiyarin ɗin motar yana sauke ajiyar zuciya kan shi ciwo yake yi masa abubuwan sun
yi masa yawa ga nata kukan me zai ce mata Abban ba shi da lafiya yana asibiti za ayi masa aiki ko gaya
mata zai yi Maminta ce sila shi fa baya raba ɗayan biyu ko yau aka ce Abban Doko ya rasu Mami ce
sanadi ita ce silar komai dan gaba ɗaya bata da tausayi ko imani a ranta. Sai da ya fara zuwa kasuwa ya
duba abubuwan kafin ya tafi asibitin.

Yana shiga yaga ana hira da Abba. Ga Abbansa a gefen amininsa yana ɓare masa lemon ɓawo suna hira
ana dariya. Ba ƙaramin sha'awa abotar Abbansu ke ba shi ba.
Gaskiya Abban kana firgita mu gwara dai ka tashi ka gyagije ka koma gida mu gan ka kana tsalle da su
Mahaboob ka wani lafke a gado.

Aka sa dariya. Abbansa ya yi masa umbola "ungo naka" abokin nawa kake yi wa haka?

Aa rabu da shi Doko ai ya saba gani yake ina kan gado ba zan iya yin komai ba ku gaya masa yau da na ga
Mar'yam sai naji ina jin ƙarfi daidai da naku ko zamu gwada naushi ne?

Ah! Abban nan ka fi romeo da alama kace masoyiya ce ta zo shi yasa ka ji ka zama gwarzo.

Eh yau kam daidai nake daku.

Haka suka yi ta raha. Aliyu kuwa mamakin Abban yake yi yadda yake mutuwar son Mami zuwanta kawai
ya saka yaji wani karsashi da ƙwari a jikinsa gaskiya an samu sauyi a jikin Abban.

Likitan da yazo ya duba shi ya auna jininsa yaga ya sauka , komai ya koma normal cike da tsokana yace
"Tabbas zuwan Madam yayi rana Allah Ya bar soyayya. Zan baku sallama amma ku kasance cikin shiri
nan da zuwa litinin zaku tafi an gama komai.

Da murna suka fara harhaɗa kayansu suna kai wa mota.

Aliyu ya gayawa Abba zai kai ta gida ta duba Abban a can yau da rigima ta tashi sai ta je wurin Abba.

Ba komai ka kai ta ai jikin nasa da sauƙi sosai.

Da haka suka rabu ya tafi gida su ma suka tafi da Abban.


*

Ya san yau yayi laifi haka ya saka ya shiga gidan sum-sum yana kallon ɓarin da kicin yake ya duba bai
gan ta ba ya duba ma wurin dinning nan ma ba komai sarai ya san zata iya ƙin cin abinci saboda fushi.

Ɗakinta ya shiga a kan gado ya ganta a kwance alamu dai bacci tayi amma baccin ba daɗi ba ga
busasshen hawaye a fuskar. Murmushi yayi yace "Rigima ba kaya ba oh wannan yarinyar." gyara mata
kwanciya yayi ya fita daga ɗakin.

Kicin ɗin ya nufa ya kunna gas ya ɗauraye tukunya ya ɗora ruwan zafi ya ɗauko gayen tea ya saka ya
kuma ɗauko sirrin shayin Marhaba wato Jaysaar tea spice. (Ina masu son shayi ? ga wata dama kun
samu wannan haɗaɗɗan kayan shayin mai sanyayya maƙoshi da daɗin ƙamshi a farshi mai rahusa ga mai
buƙata zasu iya tuntuɓar wannan layin 09065856251) ya zuba tuni ƙamshinsa ya ziyarci hancinsa.Sai da
ya gama tsaf ya juye a fulas ɗin shayin. Dankali ya ɗebo ya feraye ya soma suya harda ƙwai sai da ya
gama komai ya kai falo sanan ya koma ɗakin Marhaba.

Motsinta yaji a banɗaki ga ƙarar saukar ruwa zaunawa yayi kan kujerar mudubi yana kallon ƙasa wani
tunanin ya tafi na daban bai ma ji fitowarta ba.

Ko da ta fito ta gan shi a ɗakin ta zumbura bakinta gaba ta kawar da kanta. Wardrobe ɗinta ta buɗe ta
ɗauko doguwar Egyptian gown ta juya zata koma banɗaki yayi wuff ya kamo ƙugunta ya mannata da
jikinsa ya sunkuyar da kan shi saitin wuyanta yana sinsinarta.

"Ka rabu dani ni ka rabu dani ka kyalle ni." Ta faɗa a taɓare kamar zata yi kuka.

"Yi haƙuri ƴar matata ba da gayya nayi ba kece kika kasa fahimta ta."

"Kawai dan nace zanje gidanmu shi ne kake yi min ihu da tsawa me nayi maka laifin me nayi maka?"

"Am sorry! Ba zan kuma ba ki yafe wa ɗan saurayinki."


Juyo da ita yayi ya rungumeta sosai ya ƙara bata haƙuri. Shi ya taya ta har ta shirya suka nufi falo.

Idanuwanta ta waro waje ganin fulasai a falo a jere ga cups da plates.

Sukooni girki kayi mana?

Eh naga za ki kashe kan ki ne kuma ni ki bar ni da wa? Bana son zama da yunwa ki kiyaye.

In Sha Allahu na daina.

To ko ke fa.

Tare suka karya a kwano ɗaya suna hira sai da ta ƙoshi tukuna ya gaya mata da safe zasu je gidan nasu
amma bai gaya mata Abban ba shi da lafiya ba saboda kar hankalinta ya tashi ciwonta ya tashi.

Ta ko ji daɗin hakan. Cike da ɗoki da zumuɗi tayi bacci ranar.

[6/17, 12:42 PM] Ummulhair S Panisau: A CIKIN IDO.....

NA

Ummulkhairi S Panisau

(khairatup)

karamci writers association.

(Karamci shi ne tushen mu'amala tagari.)


12

Yanzu kai kana yi wa kan ka adalci Sufyanu? gaba ɗaya ka kalle ka ka kuma kalli rayuwar da kake ciki ko
nace ka ɗorawa kan ka ? me kake nema a duniyar nan? kuɗi ? , ƴa'ƴa? Aboki?, ɗan'uwa? Surukai? ko
jikoki? wannene baka da shi a ciki fisabilillahi? baka tausayin yaran nan? kullum a koke suke kullum cikin
ɓacin rai da tashin hankali suke. Tun ƙuruciya aka abu ɗaya amma har yau baka bari zuciyarka ta huta ba
ka hana ta sakat ka kasa yarda da kaddarar ka. Ka saki yarinyar nan da ba ƙaunar ka take yi ba ka rabu da
ita kila ta fara ganin ka da ƙima ko nace da idon rahama tunda haka kake so bana jindaɗin ganinka a
haka tun ranar da ka haɗu da wannan yarinyar rayuwarka bata kuma yin daɗi ba haka kawai ka ɗorawa
kan ka wannan lalurar.

Murmushin gefen baki Sufyan Doko yayi ya ɗan muskuta kaɗan ya kalli abokinsa kuma ɗan'uwansa
kallonsa yake yi kamar zai ga zanen wani abu akan fuskarsa.

Babu abinda na rasa a cikin abubuwan da ka lissafa ba sai Soyayyar Mar'yam soyayyarta kaɗai na rasa
kuma ba zan samu maye gurbinta ba ku gane bani ni ne na ɗorawa kaina ba Allah ne y ɗora min
ƙaunarta a ko wanne ɓargo na jikina ba zan iya daina son ta ba kuma ban taɓa riƙe ta ba ku daina ganin
laifinta dan Allah!.. Maganar saki kuma ba zan sake ta ba har gaban abada bazan sake ta ba nayi wa
mahaifinta alƙawarin haƙuri da ita da halayenta nayi masa alƙawarin kareta daga dukanin wani sharri
kuma nayi alƙawarin kasancewa da ita ko wuya ko daɗi bata yi min komai ba ko ma yaya halin Mar'yam
yake ni ina sonta kuma ina ƙaunarta kuma ba zan fasa son ta ba daman ai ba hallayenta nake so ba ita
nake so komai nata nake so da kyau ko ba kyau ko a iya ƴa'ƴan nan da ta haifa min ai ya isa ya nuna
muku tana sona.....

Dalla yi mini shiru wasu ƴa'ƴan? da ni da kai mun san a yadda rabon ƴa'ƴan ya zo.

Kuma rabon ne ya saka aka yi aurena da na Mar'yam ba ƴa'ƴa goma ai maganar ƙiyayya ta ƙare.

Fahimta ce baka so kayi ko kuma ka fahimtar amma kake wahalar da kan ka. Bara kaji mace in bata
sonka da sauƙi zaka iya siye zuciyarta wata rana amma ba zaka taba rusa ƙiyayyar mace a kan ka ba haka
ce tsakanin ka da Mar'yam rashin son da take yi maka ce ta riƙiɗa ta koma baƙar ƙiyayya a ƙirjinta.

Ko k manta sanadin ciwon Marhaba?


Ka manta dalilin da ya saka na aurawa Aliyu Marhaba?

Ka manta sanadin toyewar fatar Marhaba?

Kai Sufyan ka farga mana.

Murmushin dai ya kuma yi yace "Babu abinda na manta abokina komai yana zaune a cikin kaina da
ƙirjina amma na karɓi kaddarata.

Ni dai ina roƙonka da ka haɗa min kan iyalina ka kula min dasu ko bayan raina kar ka bambamta mini
Mar'yam da Habiba dukaninsu matana ne. Kowacce matsayinta daban amma duniya ta sani matsayin
Mar'yam ya fi na kowa a raina bayan Umma da Abba.

"You are insane Doko." Alhaji Idris ya faɗa yana rungumar abokinsa a ɓoye ya share hawayen da suka
zubo masa a fuska baya son ya karaya baya son ya nuna masa shi ma tausayinsa yake ji.

"In Allah ya yarda lafiya za ayi aikin ku dawo lafiya ka zo ka cigaba da zama da wannan monster wife ɗin
taka dan ni in zaka bani amanarta ma ka cuce ni mata ba zuciyar imani a ƙirjinta ko fa irin ɗan tausayin
nan bata da shi fa haba da Allah she's just hard like a rock.

Dariya suka saka ya kuma ce masa ka ƙara haƙuri da Mar'yam. Ko ka daki dutse da hannunka ko dutsen
ya daki hannunka zafin dai hannun naka ne zai ji to haka yake a guna kace zaka rabani da son Mar'yam
don zuciyata ta rage raɗaɗin rashin soyayyarta a guna ba zai yuwu ba ku ɗauka kawai don ita aka yi ni.

"Mun ɗauka Doko."

*
Be shiga cikin gidan ba a bakin gate ma ya sauketa saboda ana jiran shi a kasuwa wasu sabbin kaya ne
aka sauke zai je ayi lissafinsu a gabansa. Yana ƙoƙarin ƙarya kwana ya ga kiran babban wan su ya shigo
masa waya.

Da yake Yaya Muba bai fiya kiransa ba sai ya ɗan rage gudu ya ɗaga kiran ya saka a amsa kuwa
(handsfree).

Salamu alaikum Yaya

Waalaikumussalam kana ina ne haka?

Ina hanyar kasuwa lafiya dai ko?

Eh to lafiya amma in ka gama abinda kake yi ka biya ta gida Dada na son ganin ka kuma da gaggawa.

Sai da yayi ɗan jim sai kuma yace "To bara na je na gani kaya ne aka kawo in bana nan ba zan gane
lissafin ba ka san mutane ba a yarda dasu ɗari bisa ɗari.

Haka ne sai anjima.

Mu jima lafiya.

Allah Ya sa daga haka suka ajiye waya su biyun.

Kasuwar ya nufa amma cike da tunanin dalili neman da Dada take yi masa da gaggawa Allah sa ba batun
Marhaba bane.
*

Tana shiga falon ta soma jin hayaniyar yayyunta da sauri ta ƙarasa ciki tace "Cin amana duk kuna nan
amma ka rasa mai gaya min za ayi meeting a gida ba saboda ni ba a sona?"

Adda Sajida ta jawo hannunta tace "Kiyi haƙuri autar Abba daga ke fa aka kulle ƙofa kowa ya sani Abba
da ke yake ji a cikin gidan nan su fa sauran duk daga bayanki suke a ƙirjin Abban."

Kaji wani daɗin baki ni za ayi wa dabara?

Adda Amina tace "Kamar an koro ki da sassafe me ya kawo ki?

Abinda ya kawo ku zuwa nayi na ga Abba na kwana biyu ban gan shi ba wayar shi ma bata shiga shi sa
naga gwara dai nazo naga lafiyarsa.

Gwara da kika zo kam kije kiyi masa sannu kwanansa biyar a asibiti zancen da nake yi miki ma wani satin
zasu tafi Egypt aiki za ayi masa.

Sak tayi tana kallon bakin Yayarta kamar dai bata fahimtar abinda take faɗa ko bata ganewa haka ta
zuba mata na mujiyarta.

Saida Mariya ta dafa ta tukunna ta dawo hayyacinta. "Yanzu an kyauta min kenan a kasa gaya min Abban
ba shi da lafiya me yasa za a ɓoye min wannan lamarin ai ina da haƙƙi a kai ko?

Abban Doko ne yayi gargaɗin kada kowa ya gaya miki saboda ciwon ki kar ya tashi kiyi haƙuri.

Mami ce ko?
Babu wanda ya bata amsa kawa ta sabi jakarta ta nufi hanyar ɗakin Abban nasu.

[6/17, 12:42 PM] Ummulhair S Panisau: A CIKIN IDO....

NA

UMMULKHAIRI SANI PANISAU

(KHAIRATUP)

Karamci Writers Association.

(Karamci shi ne tushen mu'amala tagari).

Paid book

13.

_________________________

Tun daga bakin kofa kawai ta tsaya ta karewa Abban kallo tuni hawaye suka taru a cikin idanuwanta
gaba daya ya zabge ya rame lokaci guda kamar ba Alhaji Sufyan ba. A hankali kamar marar gaskiya cikin
sanda ta shiga cikin dakin so take tayi kuka amma bata son ta tada masa hankali.

A hankali ta zauna a gefen gadon ta zauna hannunsa ta kamo ta rike tuni hawayen da take rikewa suka
kwace.

Cikin bacci yaji saukar hawaye akan hannunsa a hankali ya bude idanuwansa ya juya dan ganin waye.
Murmushi ya saki yace "Marahaba ta waya gaya miki dan Allah?"
Abba jikina ne ya bani baka da lafiya. Nayi ta mafarki da kai Abba me yasa kuka sa a boye min ni ba yar
ka bace kamar sauran?

Murmushin dai ya kara sakar mata yace "Kiyi hakuri na san ki da kuka wanan ne baban dalilin da ya saka
na kasa gaya maki ga ciwonki kar lalurarki ta tashi ba dan sun fi ki ba ke da kike uwar masu gida.

Murmushi tayi tace dashi "Allah Ya baka lafiya Abbana , Allah Ya sa kaffara dan Allah ka daina damuwa a
ranka komai yayi farko zai yi karshe."

In Sha Allahu Marhaba ta ina godiya da addu'a Allah Ya yi muku albarka gaba dayanku.

Amin.

Ta jima a zaune a dakin har sauran ma suka zo suka riske ta a dakin suna taya shi hira.

Hakan ko ba karamin faranta masa yayi ba duk inda ya juya yaransa da Mar'yam ta haifa masa ne yake
gani kowannensu nan-nan yake dashi duk farin cikinsa suke so basa son su ga ran shi ya baci kwallar da
ta zubo masa ya dauke a wayance ta gefe yana yi musu wani irin kallo shi kadai ya san abun da yake ji a
zuciyarsa tausayinsu yake ji daga su har shi ababen tausayi ne Allah shi ne Ya san daidai da kuma dalilin
komai.

Yana gama abinda ya shigar da shi kasuwar ya nufi gidan nasu duk da yana jin faɗuwar gaba amma bai
sare ba tun daga babban tsakar gidan nasu ya ke haɗuwa da ƙannen shi da yayyunshi suka dinga
gaisawa.

Sai da ya bi ɗakunan matan Abban na shi tukuna ya shiga ɓangaren Maman.


Gefe ya zauna saboda ya tarar tana addu'a sai da ta gama ta shafa kafin ya gyara zamansa da kyau ya
gaishe ta. Amsawa tayi ciki-ciki ba wata walwala a kan fuskarta.

Mama naga duk ranki a ɓace lafiya ? ko ance miki nayi wani abun ne?

Wani irin kallo tayi masa kafin ta juyar da kanta gefe. Asiya ce ta fito daga ɗakin Mama cikin doguwar
riga zata wuce.

Mama tayi gyaran murya tace"Asiya baki ga yayan naku bane?"

"Lah! Mama ban gan shi ba Wallahi,sannu da zuwa Yaya Aliyu."

(Asiya ƴar wan Mama ce da suke uwa ɗaya uba ɗaya ta jima tana son a haɗa auren sa da Aliyu Alhaji yayi
mata saurin shiga yanzu kuma take son ta tada maganar shi yasa ma ta kirawo Asiyar shi ma ta kirawo
don su sassanta dan sam bata son Marhaba saboda uwarta.)

Lafiya ƙalau Asiya. Ya kike ya gidan da kawun?

Duk kowa lafiya Wallahi.

Ma Sha Allah.

Daga haka bai ƙara cewa komai ba ya maida kansa ƙasa yana kallon carpet ɗin Mama kallo.

Da ido tayi mata nuni da ta je.

Bayan fitar Asiya ta kira Aliyu cike da tausasawa a muryarta.


"Babana!".

"Na'am Mama." Ya amsa a sanyayye.

Naga kayi shiru ne bayan ka san da cewa ina jiran ka zo min da batun aurenka da Asiya amma kayi biris
dani in ka shigo gidan ma sai ka maƙale a wurin Abbanku saboda kar nayi maka maganar aurenku. To
saurareni da kyau kaji ni ba gudu ba ja da baya ban san yadda zaka yi da Abban ka ba amma ina son ka
same shi da kanka ka gaya masa batun auren ka da Asiya.

Mama ina sane amma ba kya ganin yanzu yayi kusa? bafa mu rufe shekara ba ma kuma ga Abban Doko
ba shi da lafiya aiki ma za a kai shi can Egypt amma.....

Sannu isasshe yo Sufyan ɗin meye na shi a batun auren nan ? Bana son wani zancen shashanci kana ji na
ko? to ka kiyaye ni da kyau ka kuma karkaɗa kunnuwanka aure babu fashi na gama magana da yayyanku
dama shi yasa na saka ya kira ka. Bana son wanan yarinyar auren ƴa'ƴan Mar'yam ai tashin hankali ne yo
me zaka ɗauka a gun ƴarta ta tsotsi baƙin halin da taurin kai a nono waye bai san irin mugun halin matar
nan ba amma aka wani haɗa mini kai da ƴarta salon a kashe min kai da baƙar ƙiyayya.

Hum!Mama ban miki musu ba kuma ba zan ki bin umarninki ba. Amma lafiya lau muke zaune da
Marhaba bata da matsala ba wata ƙiyayya da take nuna min sai biyayya da haƙuri. Mama a gabanki ta
taso kuma kin ga irin ƙalubalen da ta fuskanta....

Dalla gafara can matsa can ana nuna maka hanya kana kaucewa ni zaka gayawa bata da matsala wato ta
gama da kai ko? Ka...

Da sauri ya tashi yace "Mama kiyi haƙuri in aka dawo daga can ƙasar lafiya sai muyi magana da Abban in
sha Allahu yadda kike so haka za ayi."

Ta karkace kai ta kalli gefe tace "Ya fi maka ,Allah Ya ba shi lafiya."
"Ameen."

Yana fita ta hau mita wato an ware masa an bashi ya san daɗin abun shi ne zai min wani kinibibi wai tana
da kirki na bi kirki da gudu na take da takalmi yaran nan ya zama mara kunya .Har ni za a gayawa
Mar'yam me ban sani ba na baiwwar Allahn nan ba? mata ba imani ba tausayi kwata-kwata shi kuma
Sufya naci da rashin zuciya ai maganinsa ma bai san mai son san ba ya biyewa kyau da kyal-kyal banza
gashi nan ta bar masa ciwo.

Bayan isha'i ya koma ya ɗauki matarsa suka tafi gida. Tana komawa kaya kawai ta cire ta shige bayi tayi
wanka ta fito. Sama-sama ta shirya ta saka wata doguwar riga marar hannu ta saka hular nan ta chantly.
A falo ta tarar da shi ko ciki bai shiga ba bare ya sauya kayansa kansa na kallon cilin ɗin falon yayi shiru.
Sai ta ji duk ba daɗi ba mamaki a kasuwa aka ɓata masa rai.

Dafa shi tayi ta baya. A hankali ya juyo ya kalleta sai ya sakar mata murmushin ƙarfin hali.

Ya Rooh lafiya wani abun aka yi maka?

Me kika gani? ba abinda aka yi min.

Aa ba haka na saba ganin ka ba ka gaya min me ya faru?

Babu komai ki ɗan sama min abinci na ci ki dafa min tea yunwa nake ji.

Ba don ta gamsu da jawabinsa ba ta amsa ta nufi kicin ɗin.


Indomie ta dafa masa da ƙwai ta dafa mai tea din tayi masa sandwich da ragowar biredinsu na safe cikin
ƙanƙanin lokaci ta gama komai ta kai masa.

Kafin nan ma ya sauya kayan jikinsa jallabiya ya saka fara. Haka ya dinga jan ta da hira don ta saki jiki ta
manta da damuwarsa. Shi kuwa tashin hankalinsa Ammi tace sai ya auri Aseeya ko da can bata yi masa
ba bare yanzu da idonta ya ƙara buɗewa.

Bayan sun gama suka yi kallo suna hira daga nan suka shiga don su kwanta. Rungumeta yayi a ƙirjinsa
kawai ya bata peack a goshi sannan yayi musu addu'a ya tofa musu suka kwanta.

Sabreen kuwa kallo ɗaya zaka yi mata ka san tana cikin damuwa ta fige ta rame cikin kwana biyu banda
ciwon kai babu abinda ke damunta gaba ɗaya a tsorace take ko ƙarar waya taji sai ta firgita jikinta ya hau
rawa idanuwanta sun koma ciki sun yi rami ko baccin kirki bata yi.

Yanzun ma wayar ake yi mata amma ta kasa ɗagawa duk da ta san Amira ce ta tsani yarinyar sosai yanzu
gashi sai barazana suke yi mata kan bidiyo ɗinta da ke cikin wayarsu kuka ta saki ta haɗa hannayenta
biyu ta rufe fuskarta. Gaba ɗaya haushin kanta ma take ji da kuma da na sanin zuwa wurin Amira tun
asali ,da na sanin taurin kanta take yi na kan dole sai ta mallaki Aliyu ,ji take ina ma ta mutu ta huta da
wannan tashin hankalin ,wa zata tunkara ya taimaki rayuwarta ya raba ta da Amira da ƙawarta take
zuciyarta tace mata "Aliyu" ki nemi Aliyu ki masa bayani kila ya samar miki da mafita. Haka ta yanke
hukuncin da safe zata kira Aliyu duk da bai zama lallai ya ɗaga kiran ta ba amma zata gwada ya
taimaketa ta rabu da wayanan makiran matan biyu.

"Matar nan taki ɗaga wayarmu gashi na amshi kuɗin Hajiya Lailat ban san ma ta inda zan fara ba gashi na
kira Malam bai ɗaga ba ni kuma garin nan na shi nisa yake yi min kinga da samun kan yar banza ba wuya
zai yi mana ba.

Haka ne amma ni ina ganin ki tura mata da saƙon hotonta da muka ɗauka kiyi mata barazanar ta ɗaga
wayar ki ko ki tura a tiktok ko watsapp ko instagram.
Kina ganin zata kira?

Zata kira ki gwada.

Haka ta samu hoton da ya fi ko wanne muni tayi dogon rubutu akai mai cike da barazana da firgitarwa ta
tura mata.

Sabreen na kwantawa taji karar shigowar saƙo haka ya saka ta duba saƙon na farko ta hau kan watsapp.

Ba tare da ta gane nambar wayar ba ta hau kan watsapp. Tana buɗewa ta ci karo da hotonta wayar ta
saki a kasa ta saki ihun firgici daɓas ta koma ta zauna ta dinga kurma ihu. Ba jimawa taji ana buga ƙofar
ɗakin ta san Mama ce.

"Sabreen me ya faru ba kya ji na buɗe min ƙofar nan me ya faru kike ihu haka waye a ciki kina jina ki
buɗe mini." Maman ke ta tambayar Sabreen ihun ya shiga har tsakar kanta ta shiga cikin tashin hankali
sosai.

Da ƙyar ta tattaro nutsuwa ta share hawayenta ta buɗe ƙofar.

Mama tace "Me ya same ki me haka?"

Mama yi haƙuri ba komai kawai abu na gani kamar ɓera shi ne na tsorata na yi ihu ban san ma za ki tashi
saboda hakan ba.

Amma baki da kirki Sabreen wanne irin shashanci ne Wannan? Haba da Allah.

Kiyi haƙuri na yi laifi.


Tsaki kawai ta ja ta koma. Da sauri ta kulle ƙofar hannu na rawa ta bi layin da kira saida ta kira sau biyar
kafin Amira ta ɗaga tana dariya tace "Kika ce da ba kya ji?"

Amira don girman Allah don son da kike yi wa iyayenki kiyi min rai ki goge abin nan ki rabu dani me nayi
miki ni kam daga ƙawace sai ki bi ki ruguza min farin cikin rayuwa.

Dariya sosai Amira tayi tace "Bana bin ki bashin rantsuwa Sab sai na dulmiyar dake zan turo miki
adirishin da za ki zo gobe ki same ni da yamma bayan magariba da irin shigar da za ki yi kuma ki tabbatar
kin sanya niqab ko facemask kar ki kuskura kice za ki min musu na biyu kuma kar ki sake ki faɗawa wani
abinda ke faruwa in ba haka ba yadda na tura miki hoton nan haka zan yaɗa shi kowa ya gani kin kuma
san ƙarshen abin.

Zanyi duk abin da kike so amma kar ki saka hotona a ko ina zan zo Wallahi zan zo .

Ko ke fa (hhhh) yanzu kika koma ainihin Sabreen ɗin da na sani ba fa wani abu bane morar dukiya zamu
yi abin da ake yayi kenan za ki bari kan ki ya ƙulle haba kamar ba wayayya ba in kika nutsu kika bada kai
bori ya hau waye ma ya san me kike yi ni yanzu kin taɓa sanin ina yi ba don na jawo ki ciki ba. Ki saki
jikinki kawai hajiyata arziki da daɗi ke kiranki kina guduwa.

Sabreen bata taɓa sanin bata da baki ba sai yau duk sai ta ji ta muzanta taji ma ta tsani kanta tana
shasheƙar kuka ta kwanta can kuma ta zabura ta miƙe ba tare da ta kalli lokaci ba ta nemo layin Aliyu
tayi ta kira amma yaƙi ɗaga kiranta dama ta san zai yi wuya ya ɗaga amma bata sare ba ta sake kira ta
tura masa saƙo *HELP* ta cigaba da kiransa kuma.

Da yake ma yana cikin damuwa baccin ma don ya samu tayi ne ya saka ya kwanta. Wayar shi ya hango
tana haske ya duba agogo yayi tsaki.

"Waye wannan yake min irin wannan kiran."


Sunan Sabreen ya gani ga saƙo ta tura masa da sauri ya tashi ya fita daga ɗakin ya bi kiran be sani ba ko
tana cikin matsala ne ko ba komai sun yi zaman mutunci da soyayya.

Ko gama ringing bata yi ba ta ɗaga wayar tana kuka tana shiɗewa tace "Aliyu ka taimaka mini ka ceto
min mutunci na da martaba ta ,zasu ga bayana ban musu komai ba."

Shhhhhhh! calm down ya isa haka ki nutsu ki daina kukan ki gaya min abinda yake faruwa kin ji?

Ajiyar zuciya ta saki ta soma masa bayanin komai.

A tsaye yake amma komawa yayi ya zauna a kan kujera ba wai yau ya fara jin irin wannan ba amma ba
taɓa kawowa na kusan sa ba...

Hello Aliyu ba ka ji na?

Kiyi shiru Sab kar ki damu ki yi yadda suka ce miki.

Eh! Nayi yadda suke so kuma?

Eh kije ki tura min adireshin in sun tura miki da details ɗin komai in sha Allahu ƙarshen su ne ya zo sai na
saka an ɗauresu an ƙwato miki hakkinki da suka ci suka kuma taka miki martaba daga kan ki sun daina
iskanci.

Hawayen da ke ta kwaranya ta share da bayan hannunta tana ajiyar zuciya tace"Nagode! Aliyu ka yafe
min."

Ba komai kije ki kwanta sai da safe sauran ki kwana kina kuka.

Ba zan yi ba in sha Allahu na daina.


Yauwa kije ki kwanta.

Sai da safe.

Yana juyawa suka yi ido huɗu da Marhaba. Tuni tayi fici-fici da idanuwanta kawai sai ta juya ta koma
ɗaki.

Duk da yaji babu daɗi haka ya bi bayanta amma ba shi da wani kalaman kare kansa ta riga da taji yana
waya da sabreen.

Gefenta ya kwanta ya ɗan matsa jikinta sai dai bata motsa ba bare ta nuna masa alamun ta ji zuwan
nasa.

Bai ja da nisa ba ya matsa ya koma baccinsa.

Marhaba tana motsawa ta shafa gefenta bata ji shi ba haka ya sa ta buɗe idanuwanta tarwai dan ta gani
ko baya nan. Ta yi kusan minti biyu a zaune bata gan shi ba kuma bata ji ƙarar ruwa ba kenan baya
banɗaki. Ji tayi kamar ana magana ƙasa-ƙasa daga falo tashi tayi ta fita daga ɗakin ya juyawa ɗakin baya
tunda taji ya ruɗe yana ta ambaton sunan Sabreen ta yi sak ta kasa motsi tana kallon bayansa duk
abinda yake faɗa tana jin sa sarai.

Yana gama waya ya juyo ya ganta.

Wani irin tuƙuƙi take ji a cikin zuciyarta wato wanda kake so tun asali ba zaka manta da shi ba sai taji ma
ashe ba sonta yake ba ƙila ma jikinta yake mora kawai kishi ya cika mata zuciya gaba ɗaya hawaye kawai
take sharewa kar ya gani ko ya jita.
Daren dai ba wani mai daɗi bane a garesu duk su biyun yana son ya lallabata baya son kuma ta raina shi
ta ce zata dinga tuhumarsa akan abubuwan da basu shafe ta ba.

Ita kuma haushin kin kulatan ya ƙara ƙular da ita.

Asuba ta gari masoya.

[6/17, 12:42 PM] Ummulhair S Panisau: 14

Washe gari tana da lakcar safe da wuri ta tashi ta kimtsa ko ina tayi musu abin kari. Bata damu da ta
tashe shi ba. Saida ta gama shiryawa tsaf ta koma ɗakinsa ta ƙwanƙwasa haɗe da yin sallama ta shiga
cikin ɗakin.

Yana saka links a hannun rigarsa ta ƙarasa ta taimaka masa ya gama shiryawa ciki-ciki ta gaishe shi fuska
ba annuri. Shi ma bai ce mata komai ba ta juya zata fita yayi maza ya janyota ta dawo da baya jikinsu na
gugar na juna ya rungumeta, kan shi ya ranƙwafa kan wuyanta ya sakar mata sumba a gefen wuya yace
"Laifi me nayi ne gimbiyar mata ake yi mini irin wannan hukuncin? "

Zumburar bakinta tayi gaba tamkar bakin zai haɗe da hancinta. Babu komai.

Aa ba haka bane kishin ƴan'mata ne ya tashi kawai ake horani.

Kan me zan hora ka? kawai na baka space ne kayi yadda kake so da ƴan'matan ka.

Dariya ta bashi kuma sai da ya dara ya juyo da ita suna fuskantar juna ya sa hannayensa biyu ya tallafo
fuskarta so yake ta kalli cikin idanuwansa amma ta ƙi bashi haɗin kan hakan.

Marhaba kar ki ɗauka wata alaƙa ce a tsakanina da Sabreen na soayayya ba haka bane da ne amma
yanzu ke ce a cikin raina sonki ne yake gudana a cikin jinin jikina. Mun yi zaman da ba zan iya ƙin
taimakonta ba tana cikin matsala bata da wanda zata nemi taimakonsa sai ni shi sa ta kirani ni kuma ina
da damar da zan taimaka mata in Allah Ya yarda kar ki saka hakan a ranki ki maida shi wani abun ina
sonki ba wani ne ya saka ni son ki ba kyawawan ɗabi'unki sune suka ja ni na ji ina son kasancewa dake
kar ki ɗauko halin da ba naki ba Marhaba. In zan yi aure dole zan gaya miki kuma ba za ki hana ni ba
Allah ne ya bani damar hakan kuma ban taɓa ce miki ba zan yi aure ba ko ke kaɗai zan zauna da ita ba
kinsani ai a gidnmu mata uku ne a gidanku mata biyu ne nima ina da wannan ra'ayin ko yaushe zan iya
zuwar miki da maganar auren.

Bata son tana mugun son Aliyu ba sai yanzu da yake gaya mata cewa zai iya ƙara aure ko yaushe
innallillahi wa inna illahir raj'un take ta ambata a cikin ranta jikinta duk yayi sanyi babu wani kuzari a
tattare da ita.

A hankali ta iya furta masa "In Sha ALLAH zan yi biyayya ba zaka same ni da ɓata maka ba."

Daɗin abinda ta faɗa ya saka ya rungumeta a jikinsa tsam kamar zai maida ta ciki yace "Ina sonki Allah Ya
miki albarka matata."

"Ameen."

Falon suka koma su ci abinci.sai da suka gama ya sauke ta a makaranta ya bata kuɗin mota ta koma gida
saboda zai biya ta wani wuri kar ta jira shi.

Amira kuwa ta gama tsara komai ta tura mata da adireshi da lokaci.

Tayi masa fowrding din saƙon. Yace ta tafi zai same ta a can.

Alhaji Idris da Ahmad sun gama tsara yadda tafiyar zata yuwu. Bayan sun gama tattaunawa Ahmad ya
tafi ,Alhaji ya shiga cikin gida.
A babban falon gidan ya zauna a kan kujera one sitter ya cire hularsa ya kwanta jikin kujerar gaba ɗaya a
gajiye yake musamman ma yanzu da girma yazo masa amma dole ya ƙwarara na sa jikin ko dan amininsa
in ya nuna gajiyawarsa yaran kuma ya zasu yi?

Assalamu Alaikum Alhaji ashe ka shigo?

A hankali ya ɗago kansa ya sauke kanta yace "Wa'allaikumussalam Hajiya Ƙarama."

Zaunawa tayi kan kujera tana kallon mijin nasu.

Kin kafa min ido a lalla sai kin hango tsufana ko?

Murmushi tayi tace "Haba dai ai kai binu ne baka tsufa ji ka fa har yau jiya iyau ai kai ka san ba a saka a
sahun tsofaffi ba.

Baki da dama Aminatu.

Suka yi dariya su biyun.

Alhaji yaya jikin Yaya Sufyan?

Uhm! jiki da sauki Alhamdullilahi jibi muke saka ran tafiya amma ban san me yasa ba jikina yana bani
akwai wani abun bana son rasa Doko.

Hajiya Ƙarama tace "Alhaji kar ka shiga hurumin ubangiji cuta ai ba mutuwa bace da yardar Allah zai
warke zai tashi ya koma kamar da. Mutuwa ai rigar kowa ce kowa jiran lokaci yake yi duk wanda ya tafi
bai yi sauri ba mu kuma bamu yi nawa ba dukaninmu zamu je can ina iyayenmu?ina magabatanmu ai
duk babu ƙasa ta lullube musu idanuwansu kuma sanin gawar fari sai Allah.
Haka ne, Allah Ya bawa Doko lafiya.

Amin Amin.

suka cigaba da hirarsu ta mata da miji.

A gidan Alh.Sufyan Doko kuwa Aunty Amarya ke kula dashi komai tana kaf-kaf dashi bata son ya nemi
abu ya rasa. Kodayaushe ƙoƙarinta guda ne ta ga Alh. Da Mar'yam sun daidaita kansu.

Yanzu ma ayaba ta ɓare masa tana bashi a bakinsa suna hira abinsu sai shi mata albarka yake yi yana
kuma jajjada mata girma da nauyin amana.

Wai Alhaji me yasa kake son yin irin wannan maganganun ne? Da an zauna kayi ta bada amana kenan
ina ji jiya ma Sajida nayi maka maganar hakan Imran mada safe wai ya kake so ayi maka ne don Allah?

Murmushi yayi kawai ya kawar da kai gefe bai ce mata komai ba.

Sai nayi magana sai ka kawar da kai gefe baka son a taɓa maka yar mai ko?

Wallahi ban san kina da irin wanan halin ba sai yau. Duk kun bi kun ki yarda da kaddara. Ku kuna ganin
Mar'yam ta isa ta saka min ciwo ne? duk abinda Allah Ya yi sai ya faru babu makawa babu wayo bare
dabara.

"Haka ne" kawai ta faɗa ta tsuke bakinta.


*

Tana sauka dai-dai bakin gate ɗin otel ɗin da suka gaya mata ta zaro niqbinta ta saka akan fuskarta.
Wayarta ta zaro ta kira layin da Amira ta bata.

"Ina waje" tace da ita.

A ɓangaren Amira kuwa amsawa tayi da "To ki shigo ki hawo sama kawai daga hannun damanki akwai
ɗakuna biyar ɗakin ƙarshe wato na biyar ɗin za ki shigo kai tsaye ba tare da kin yi hayaniya ko ƙwanƙwsa
ƙofa ba kawai ki shigo ciki."

Da to ta amsa mata kawai. Yadda suka yi ta turawa Aliyu ya kirata ya gaya mata karta damu ta tabbatar
wayar na kan recording zasu shigo bayan minti biyar tayi duk yadda zata yi Amira ta faɗi abinda ta aikata
mata. Da wannan ƙwarin gwuiwar ta shiga cikin otel ɗin yadda ta kwatanta mata hakan ta yi da adduo'i a
bakinta ta shiga ɗakin.

Tana shiga taci karo da kujeru kanana guda biyu masu zaman banza. Ta bi ɗakin da kallo sai ƙamshi yake
yi ga sanyin Ac da tv a maƙale a bangon ɗakin. Tana ƙara shiga ciki ta yi tozali dasu Amira su uku da
Amira da ƙawarta sai wata mata babba ce kuma kyakyawa.

"Ya kika tsaya kuma ki ƙaraso mana". ƙawar Amira ta faɗa.

"Malama ki cire wannan niqab ɗin ai kin riga da kin shigo."

Hannunta na rawa ta sauke niqan ɗin daga fusƙarta.


Tashi tsaye wannan matar tayi ta kasa ɓoye jindaɗinta. "Tabarakallah Amira ai hoto ɓoye zahirin
kyawunta yayi gaskiya zan yi miki ƙari akan wancan farashin don kuwa yaba kyauta tuƙuici ne na yaba
kuma na gamsu.

Dariya suka saki suka tafa suna shewa irin ta ƴan duniya.

Sabreen ta tsokano Amira "Kiji tsoron Allah kar kiyi sanadin ruguza min rayuwata kin sani wanan ba
harkata bace hasalima yaudarata kika yi kika yi mini abinda bai dace ba amma shi ne kike cinikina da
wasu kuma meye ribarki Amira ki fa tuna na yarda dake.....

Yi mini shiru kinga fitata na duba yanzun ma in za ki bamu matsala zan yi miki allura tsab ki rasa
hankalinki kamar wancan karon ke mu da muke da ƙwayoyi iri-iri ,shegiya arziƙi na ƙwanƙwasa miki ƙofa
kina guje mata kin san ko nawa Hajiya ta bayar a baki?

Na fi son rahamar Allah a kan kuɗin da zasu ƙare a gidan duniya. Na fi son mutunci na a kan wayanan
kuɗaɗen da kike tunkaho dasu.

Hajiya tace "Kinga beauty ba fa wani abun bane ba wanda zai san kin yi...."

Katseta tayi tace "Allah Yana ji yana kuma gani."

Mtswwwww ƙawar Amira ta ja dogon tsaki kan tace "Baiwar Allah kina ɓata mana lokaci ba wa'azi muka
zo ji ba in wa'azi kike son yi ki jira mu gama sai ki tafi massalaci kiyi."

Gaya mata dai ƙawata. Ko wanne ɗan koyo da rarrafe ya fara da kin saba shi kenan miƙewa za kiyi.

Ganin zata ɓata musu lokaci ya sa suka tashi su biyun suka nufeta gadan-gadan jiki na rawa zasu yi aikin
sa kai don mugunta.
Amira ce ta kama hannayen Sabreen tana ƙoƙarin ɗaure mata hannu ta baya yayin da ƙawar ta ɗauko
wata allura ta haɗa ta jijiga ta nufesu da sauri. Damtsen hannun Sabreen ta kamo zata soka mata allurar
suka ji an banko ƙofar ɗakin da ƙarfi.

Gaba ɗaya sai kallo ya koma sama.

ƴan sanda guda uku suka shigo sanye da kakinsu.

"Kowa ya tsaya a inda yake duk wadda ta motsa sai na harbe mata ƙafa a wurin."

Da sauri Amira ta saki hannun Sabreen, ita kuma ta yarda Allura tuni Hajiya ta soma ƙoƙarin saka face
mask amma jikinta sai rawa yake yi ta kasa sawa bata son kuma a ganta don mijinta wani babban ƙusa
ne a gari,babban ɗan siyasa ne.

"Lah yallabai lafiya?" Amira ta tambaya cike da ƙarfin hali da dakiya.

"An shigar da ƙararku na yiwa wannan baiwar Allahn barazana haɗe da fyaɗe wato cin zarafinta."

Amira ta soma tafi tace "Haba yallabai fyaɗe ko daɗin ji babu. Dama mata na yiwa mata fyaɗe ne?
gaskiya baku ji daidai ba nan daka gan mu shooting muke yi na fim." Ta zabga ƙarya.

Wani daga ciki ya daka mata tsawa"kar ki maida mu bamu san komai ba mana. Mun ji komai kuma muna
da hujja. Ku wuce mu tafi in kika ƙara cewa tak sai na kifa miki mari."

Ta ja da baya ta tsuke bakinta.

Aka tarkata su suka yi waje.


A bakin gate ɗin suka yi tozali da Aliyu. Sabreen ta wuce wurinsa.

Amira kuma tayi ƙwafa haɗe da yi mata kallon za ki gane kurenki.

Dan sandan yace da su "Oga muje ko."

"ok kuyi gaba zan taho da ita a mota."

[6/17, 12:42 PM] Ummulhair S Panisau: TUN A KARON FARKO....

NA

Ummulkhairi S Panisau (KhairtUP)

Karamci Writers Association.

(Karamci shi ne tushen mu'amala tagari)

16

Ahmad meke faruwa me nake ji ne haka ina Abban?

Ahmad ya kasa magana sai hawaye da yake sharewa akai-akai kawai.

A hasale Aliyu ya miƙe ya nufi wurin likitan da ke duba Abban Doko sai rawa jikinsa yake yi saboda tashin
hankali.
Ofishin likitan ya shiga tsabar tashin hankalin da yake ciki bai ma lura da marasa lafiyan da suke wurin
da kuma wanda likita yake dubawa.

"Likita wai Abban ya rasu? kowa sai cewa yake yi ya rasu meye gaskiyar magana?"

likita ya kalli Aliyu da kyau ya gane ba a cikin hayyacinsa yake ba.a hankali yace dashi ; Aliyu calm down
dawo cikin hayyacinka waye yace ya rasu? Bai rasu bafa amma yana cikin coma.

Ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauke sai a lokacin hawayen da suka maƙale masa a cikin idanuwansa suka
samu nasarar zubowa. Wani sanyi yaji ya ratsa shi sai yanzu yaji iska na shigar shi gaba ɗaya ya shiga
cikin damuwa sai a lokacin ma Abban shi ya faɗo masa a rai shin yana ina?

"Nagode" kawai ya faɗa ya fita da gudu bai tsaya ba sai a gaban Ahmad ya ko dage ya takarkare ya fyalla
masa mari ganin sai kuka yake da sambatu kamar mace yana mai magana amma baya fahimtar komai
kamar dai yadda Marhaba tayi masa.

"Ka dawo cikin hayacin ka Ahmad Abban bai rasu ba,coma ya shiga waya ce maka rasuwa yayi kuma ina
sauran?"

Na'am Abba bai rasu ba? Da gaske Aliyu?

Daga wurin likitan nake yace bai rasu ba shi bai ce muku ya rasu ba a ina ka samo wannan information
ɗin?

Mun ga Abban Doko ya fito yana kuka bai ce mana komai ba ya fita hakan ya saka jikinmu ya mutu muka
ɗauka rasuwa Abban yayi.

Mtsw gaba ɗaya kun gama dani Wallahi yanzu da za a auna jinina tabbas za a ga ya hau fiye da ƙima ga
can Marhaba ma an saka mata oxygen saboda wannan abun da kuka sanar mata a bazata.
Innalllilahi muje na ganta tana ina?

Suka nufi ward ɗin da take.

Alhaji Idris Doko banda ciwo babu abinda kan sa yake yi mai bai kula kowacce daga cikin matansa ba ya
shige ɗakinsa ya kulle ta ciki. Babbar rigarsa ya cire ya ɗora a kan gado ya ajiye hular ma a kan gado ya
koma kan sofa ɗin dake cikin ɗakin ya zauna ya yi jigum hannu a kan haɓa. Wannan karo bai yi yunkurin
shar hawayensa ba barinsu yayi su sauka su zuba yadda ya kamata ya jima bai shiga cikin matsanancin
hali ba irin na yau, gaba ɗaya ya gama cire tsammani da samun abokinsa kawai yana yi masa addu'ar
samun dace da wucewa lafiya.

Har cikin kansa ya ke jin bugun ƙofar kuma ya san babu wacce zata yi masa irin wannan bugun sai
Amminsu Aliyu.

Tashi yayi don ya buɗe mata don ya san nacinta muddin bai buɗe mata ba ba zata taɓa barinsa ba.

Yana buɗewa ta afka cikin ɗakin da sauri kamar an jefota ko an ingizata kamar zata doke shi ta ture shi
gefe ta kulle ƙofar ɗakin ta juya tana kallonsa.

"Ina roƙon Allah da ya nuna mini ranar da za ki yi hankali Zuhurriya."

Harara ta fara aika masa da ita kafin ta sakar masa tsaki.

"Ban taɓa ganin wahalalle irin ka ba Idrisu baka da zuciya ko kaɗan na rantse da Allah babu ruwana da
wancan mutumin ni buƙatata na sani ko ayi abinda nake so ko kuma kowa ya rasa in taƙamarka Aliyu
ɗanka ne nima ina da haƙƙi a kansa tunda ni na ɗauki cikin shi wata tara a cikina na kuma shayar da shi
na raine shi."

Zuhurriya huh! ban san cewa har yanzu rashin ilimi bai sake ki ba ,da ace kina da ilimin da baki yi
waɗanan abubuwan ba. Ki bar ni na ji da rashin lafiyar ɗan'uwana ba surutan banzan ki nake so ba
nutsuwa nake so.

In kaga an zauna lafiya a gidan nan to tabbas anyi abinda nake so ne.

Me kike so ayi miki?

Auren Aliyu da Asiya nake so ayi.

Aure! Aure! wane irin aure ana zaune ƙalau duka-duka yaushe aka yi auren da zai kuma yin wani? a
wannan lokacin ma da ake cikin wannan tashin hankalin wanne aure za ayi masa? kina jin abinda kike
faɗa kuwa da bakinki?

Sarai kuma ras nake jina ni na fi ka sanin me nake faɗa tunda ni nan da kaina ni Zuhra nake faɗa Aliyu dai
ɗana ne kuma na isa da shi ko a bi maganata ko kuma a biyani nono na da ya sha ehe.

Ya salamu Allah ! Alhamdullilahi!. Zuhura duk abinda kike nufi na sani kuma ba zan hana Aliyu bin
umarninki ba sai dai ki sani ba yanzu za ayi ba in ma shi ya sa kika ɗauko musu ƴa ne tun yanzu to ki
koma ki gaya musu ba yanzu ba ne auren sai abokina ya samu lafiya shi ne uban Aliyu shi zai masa aure
bani ba.

Ta soma shewa tana tsalle tana masa ihu ahayye nannaye wasa ma kennan to ban san wannan
tatsuniyar ba ban san wannan ba Wallahi aure sai anyi.
Zan gani Zuhura ni ne sama dake ko kece sama dani,fitar min daga ɗaki malama bana son na furta miki
abinda zamu dawo mun da na sani ni da ke kar ki sa raina ya ɓaci kin ishe ni haka da me zan ji? ko an
gaya miki ban san dalilin gabar da kika ɗauka da aminiyar ki ba ? in tuna miki ko kuma in bar ki a haka?

Shiru tayi ta koma da baya baki a sake a mamakance tace "Dama ka sani? yaya aka yi ka sani?"

Na san komai.

Babu sauran masifa ta sa kai ta bar masa ɗakin.

Kan shi dake barazanar yi masa ciwo ya dafa ya koma ya zauna shi kan shi kokawa yake yi da
numfashinsa da a ce za a duba shi tabbas jininsa ya hau kuma sai an bashi gado. Ya Allah ga bawan ka ;ka
duba lamuransa ka ba shi lafiya da nisan kwana amin.

Marhaba bayan wasu mintuna ta dawo cikin hayyacinta da kuka ta tashi tana neman ƴan'uwanta su
gaya mata ƙarya suke yi babu abinda ya samu Abbansu gatansu masoyinsu.

Daidai lokacin da Aliyu da Ahmad suka shigo ɗakin. Ƙoƙarin saukowa take yi daga kan gadon Aliyu yayi
sauri ya isa gabanta.

Me haka kuma, ina za ki je?

Wurinku zani ina Abbana ku ka ce ya mutu ai wasa ne ko? Abbana yana nan yana gida cikin ƙoshin lafiya
ko? was...

Rungumeta yayi a ƙirjinsa yana shafa bayanta rarrashinta yake yi sosai. Sai da ya tabbatar da ta yi shiru
ta nutsu tukunna ya sa hannayensa biyu ya tallafo fuskarta bai damu da wanzuwar Ahmad a wurin ba ya
sumbaci goshinta yace da ita "Ya isa kiyi shiru basu sani ba ,kuskuren fahimta aka samu shi ya saka su
tunanin cewa Abba ya rasu ba rasuwa yayi ba amma tabbas yana buƙatar addu'o'inmu yana da buƙatar
mu a kusa da shi tada hankalinmu shi ne zai saka ya kara ƙaraya don Allah ku kiyaye ku kuma ƙwarara wa
junanku guiwa. In sha Allahu gobe zamu tafi Egypt ɗin.

Rungumesa ta kuma ji a jikinta tana kuka a hankali Allah Ya sani ba zata yafewa Mami ba.

Bayan gama cuku-cukun komai washegari aka tafi filin jirgi ba tare da hayyacin Abba ba ,Har a lokacin
kuma Mami bata taɓa leƙawa wurin Abba ba ko da aike bata yi masa ya jiki ba.

Babu wanda Mami bata ƙure haƙurinsa ba da wannan halin ko in kulan da ta yi ma Abban ba ko babu
komai ai rashin lafiya ce bata sani ba zai dawo ko ba zai dawo ba. Tambayoyi ne fal a cikin zuciyoyinsu
mene ne laifin Abban?

Sun jima suna ji da ganin labaran soyayya amma basu taba cin karo da irin labarin Mami da Abba ba. A
lokuta da dama su kan yi tunanin yadda aka yi aka samesu da wannan ƙiyayyar ta Mami ga mahaifinsu
ƙiyayyar da aka ce TUN A KARON FARKO ake kafta ta har yau babu sassauci a ƙirjin Mami iyaye sun
shuɗe ƙanne da yayyu sun ja bakunansu sun yi jigum sun gaji da lallashi da nasiha amma duk da haka
Mami bata girgiza ba.A soyayya ta uwa da ɗa Mami bata taɓa jin zata rissina don su ba duk da anyi zaton
in ta haihu zata haƙura ta zauna ko dan darajar su amma ina aka ce abin da baka so fa ba zaka taɓa son
shi ba.

Akwai tambayoyi cike fal a ƙirjinansu, akwai ayoyin tambaya ga ala'ƙar Mami da Abba. Ya kamata su
waiwaya baya su gano ainihin matsalar me ya jawo wannan ƙiyayyar TUN A KARON FARKO!.

Muje zuwa amsoshin ku na nan a gaba.

[6/17, 12:42 PM] Ummulhair S Panisau: TUN A KARON FARKO....

NA
Ummulkhairi S Panisau (KhairtUP)

Karamci Writers Association.

(Karamci shi ne tushen mu'amala tagari)

Pg 17

Tun barinta ɗakin Abba gabanta ya tsananta yi mata bugu yawu ma ya ƙi tafiya yadda ya kamata a
wurinta. Zaunawa tayi tana tambayar kanta yadda aka yi Abba ya son abinda ya faru a wancan lokacin na
ƙuruciya kenan ma kallon sauna yake yi mata tana yi masa kallon biri yana yi mata na ayaba. Kamar an
mintsine ta haka ta miƙe da ƙarfinta taji wani irin abu na taso mata a ƙirjinta da gaske fa bata son
cigaban Mar'yam kuma ba zata taɓa so ba sai dai ba ta so wani abu ya samu Sufyan ba don ko haushinsa
da take ji duk na ɓacin rai ne. Hannu ɗaya ta dunƙule ta buga a tafin hannunta ɗayan a fili ta furta "Ba
zata saɓu ba bindiga a ruwa dole ayi yadda take so kuma dole a bi ta."

Asiya ce ta shigo cikin ɗakin tana zuzuɓur baki kamar zai taɓo mata hancinta.

A sukwane Ammi ta juya tace "Lafiya Asiya?"

"Ammi ni na haƙura da auran nan na Yaya Aliyu ni fa daman ba wani so nake yi ba ku ne kuka dage ni
daman da akwai wanda nake so a can Doko." Ta faɗa cike da sakalci da rashin kunya tana jujuya kai hagu
da dama.

Daman Ammi a ƙufule take aiko ta sauke masifarta a kan yarinyar ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba.

"Don ubanki ni kike gayawa haka? to ki kom can Dokon mana ana son ayi miki gata kina kaucewa an
gaya miki wata tsiyar ce a can Dokon? ana nuna miki annabi kina ga kafiri to ki saurareni nan da kyau
baki haifu ba nace baki haifu ba. Har yau wuyanki bai yi isan da zame ce ga yadda za ayi kice ba haka ba
ƙarya kike yi Asiya sai anyi kuma da ranku za ayi. Marar kunyar banza marar kunyar wofi."
Asiya ta ji Ammi ta hau sai ta lallaɓa ta sauko.

"Ba fa haka nake nufi ba, dama Yayan ne ko na kirasa baya ɗaga wayata bai fa taɓa zuwa wurina ba
amma kuna son ku cusa masa ni gasiya a duba lamarin nan."

Babu ruwanki da zancen Aliyu ni na san maganinsa ban son zubda aji kuma kar ki ƙara kiransa da kan shi
zai zo inda kike wa'adi na bashi na cin sharafinsa yadda yake so kuma wa'adi ya kusan cika ni kuma zan
murza nawa kambun.

Asiya bata sake cewa komai ba ta juya ta bar ɗakin.

Aka bar Ammi da mita da ƙananun soki burutsue ita kaɗai.

Ya sani sarai duk wani hura wutar ƙiyayar Sufyan Doko a cikin zuciyar Mar'yam Zuhurriya ce umul'abaisil
ɗin faruwarsa..... baya ma son ya tuna abinda ya ji ya kuma gani da idanuwansa dalilai da dama suka
hana shi ɗaukar mataki a kan Zuhurriya. Wayarsa da ke ƙara ya ɗauko ya duba nan ya ga kiran na Aliyu
ne.

"Salamu alaikum!".

"Wa'alaikumssalam Abba kana ina?".

"Aliyu kada ku damu dukanku ina nan lafiya gida na zo na huta naji kaina yana yi min barazanar ciwo ne
kamar zai faɗo ƙasa ne."
"To Abba na ji daɗi ka huta anjima zan shigo bayan mun dawo daga filin jirgi mun gama magana kawai
gobe zamu tashi da safe."

Hakan ya kamata ayi dama Allah Yay muku albarka dukanku.

Ameen Abba sai anjima....

Arh! Aliyu tsaya kun yi magana da Amminku ne a game da Asiya?

Eh Abba daman ina son muyi maganar na bari ne sai Abban Doko ya samu sauƙi ne shi yasa na yi shiru.

To shi kenan bana buƙatar ganin ka a gidan nan har sai na ɗauki mataki ko da yake zaku tafi tare dasu ne
ka dinga kiranta a waya kuna gaisawa kawai.

To Abba Allah Ya ƙara girma da nisan kwana.

Amin Aliyuna Allah ya yi maka albarka kaima ya baka masu yi maka biyayya yadda kake yi mana.

Amin Abbana nagode matuƙa tare da addu'arka babu wani mahaluƙi da ya isa ya ga bayana da izinin
Allah.

Murmushin manya Abban yayi kawai ya kashe wayar.

Marhaba a daren bata yarda ta koma gidanta ba sai ta yanke gwara ta koma gidansu ta ga tafiyar Abba
kamar yadda aka shaida musu zasu tafi da safe.
Aliyu ya shigo ainihin ɗakin da aka bata ya zauna a gefenta kallonta yake yi amma taƙi yarda su haɗa
idanu da juna.

Wai matar nan me nayi miki ne na ga sai wani ɗaɗauke min kai kike yi me nayi miki?

Babu!.

A yadda ta amsa masa ma sai yaji wani banbarakwai ya kuma gane cewa tabbas fushi take yi da shi.

Wai me yasa kike yin haka ne ni fa ba yaro bane da zan yi ta bin ki ina baki haƙuri kamar wasu yan fim na
fi so in laifi nayi miki kaitsaye ki gaya min ba wai kiyi ta kumbure-kumbure ba kina gaya min magana ko
amsa min a duk yadda kike so bana so na gaya miki bana so sabo da haka ki kiyaye.

Tuni hawaye sun tarar mata a cikin idanuwa ta gama karaya da lamarin Yaya AIiyu. Share hawaye take yi
kar ya gani shi kuma basar da ita yayi da gayya don baya son raini yaga alama so take ta maida shi wani
ƙaramin yaro yayi ta bin ta yana rarrashi tana basarwa shi ba zai ɗauki wannan halin ba gwara ma ya
gwada mata shi namiji ne.

Wayarsa ya cigaba da dannawa kusan minti biyar tana ta sharɓe yaga zai biye mata kawai ya miƙe tsaye
ya sa wayar a aljihun wandonsa yace da ita "Zan tafi Imran zai zo ku tafi gida tare kafin mu tafi zamu biyo
muyi muku sallama. Allah Ya sauwake. ya juya yayi ficewarsa.

Ita kuwa ta kwanta yaraf ta koma ta cusa kanta a cikin fillo ta saki kuka haɗe da toshe bakinta. Wato
bata da wani muhmmanci a wurinsa ba zai ma lallabata ba ko don ya samu matar da yake so zai aura shi
yasa ya fara nuna mata ainihin kalar shi? Turƙashi ta yarda yau tana son Yaya Aliyu da ta ɗauka shaƙuwa
ce kawai da burgewa saidai bayan abinda ya faru tsakaninsu sai taji duk duniya ita shi take so yana da
abubuwan da kowacce mace zata so ace mijinta na da shi ga ilimi,ya iya tarairaya,ya iya ado,ya iya
magana,yana da aji,yana da biyayya ,yana da kulawa to ya bazata yi kishinsa ba? Bata son su rabu yana
fushi da ita . Fushi bai ganta ba dole ta sauke kai ta maida hankali kan mijinta ta kula dashi ta kuma dasa
masa soyyarta mai girma a cikin ranta da ace zuciyarta tayi watsewar tangaran bisa kwalta gwara ta
sauke kai ta samu mijinta a hannu.
Jim kaɗan Yaya Imran ya shigo ya tsaya ta gama kimtsawa suka tafi. Gidansu ya kai ta kaitsaye ɗakinsu ta
shiga tayi wanka kafin ta koma kan gado ta zauna tayi jigum gaba ɗaya zuciyarta babu daɗi wayarta ta
janyo ta lalaubo nambar wayarshi sai kuma ta kasa kiransa kawai sai ta yanke hukuncin aika masa da
saƙon ba haƙuri.

Shi kan shi zuciyarsa babu daɗi ya zame kujerar motarsa ya kwanta ya sa hannun shi na dama wurin dafa
saman goshinsa hannunsa a lumshe duk baya jindaɗin komai.

Yana tsaka da tunani ne yaji shigowar saƙo. Sunanta ya gani hararar wayar ya fara yi kafin ya maida ta ya
ajiye a gefe ko duban abinda saƙon ya ƙunsa bai bi ta kai ba ta ba shi haushi sosai yaga alama kishi ne da
ita in idanuwanta suka rufe ba a abin arziƙi da ita ,sai tace zata raina shi ba zai ɗauki ta juya shi ba gwara
ya nuna mata shi namiji ne ba zai bata ƙofar da zata maida shi sakarai ba in ta gane lagonsa shi da kan
shi ya san cewa akwai matsala baya son tarihi ya maimaita kansa.

Ganin shiru bai amsa mata ba sai jikinta ya ƙara yin sanyi ta kwanta lamo a kan gado ta shiga cikin bargo.
Gidan ko da can ba daɗi yake yi mata ba don kowa ya fita jindaɗi izayar da ta sha a wurin Mami Allah ne
kawai ya san shi kawai don tayi kama da Abban ita fa mamakinta ma yadda aka yi aka haifesu auren
shekara ashirin da tara amma babu shaƙuwa babu soyayya in ta ga wasu iyayensu musamman ma uwa
da uba suna nan-nan da ƴa'ƴansu sai taji abun na bata sha'awa abin burgewa su kuwa a gidansu basu ga
hakan ba.... huh!ta sauke ajiyar zuciya ta kuma tura masa da saƙon ban haƙuri don bata son ta zamto
tamkar Mami a hallayen kula da miji.

Asiya a bayan gidan tana leƙe-leƙe kar a ganta ta ɗauko wayarta ta nemo wata namba ta saka a kunne
tana juye-juye kar a ganta hannunta har rawa yake yi don fargaba.

"Hello Hajiya ba zan iya ba don Allah ku bar maganar nan ni gaba ɗaya a tsorace nake kar a kama ni."

Daga ɗaya ɓangaren aka bata amsa "Ke dallah ki nutsu ki saurara min haka bana son wannan haukan
naki ke kullum baki da basira kamar ba mace ba, to saurara kiji ni da kyau irin Ammin ba a haka ake
kayar da ita ƙasa ba sai da wayo da dabara da saita nutsuwa wuri guda kina ji ki nutsu kiyi abinda na saka
ki."

"Hajiya! Abin nan fa ba zai yuwu ba Yaya Aliyun ma fa ba kula ni yake yi ba bama zuwa gidan nan yake yi
ba bare na sa abinda kika bani har yaji zai kasance da ni gaskiya ki bar maganar nan na dawo gida kin san
Ibro nake so kuma jirana yake yi."

"Wallahi zan ci kut.....ki idan kika kuma yi mini zancen wannan yaron Wallahi sai ranki ya ɓaci ana nuna
miki Annabi kina runtse ido. Ki saurare ni da kyau sai kin yi abin da na saka ki in ba haka ba sai kin biyani
nonona da kika sha."

Shiru Asiya tayi ta kasa cewa komai sai kawai tace "Shi kenan Allah Ya saka ya zo kafin ya tafi."

"Gwaran miki dai shashasha mara basira kawai."

Shiru Asiya tayi waya a hannu tana kallon ƙasa gaba ɗaya bata son wannan haɗin da Hajiyarta ke son ta
haɗa gaba ɗaya Ammin tsoro take bata hatsabibiyar mata ce Ammi duk gidan tsoronta suke da bala'in ta
kwata-kwata bata tsoron Allah ko a can tana jin yadda ake faɗar masifar matar tun suna ƴan'mata ma ta
fara jin labarin ƴanmatancinsu a can Doko duk-da Mamin ba mai magana bace aka ce an ce dai tana da
miskilanci da halin-ko-in-kula da yawan samari ma shakkarta suke kwarjini take yi musu sam ba mace
bace mai fara'a....

"Me kike yi a nan Asy?"

Saboda tsoron da taji sai da ta saki wayarta a ƙasa.

"Lah yi haƙuri na tsorata ki na fita har na dawo na ganki a nan lafiya?"

"Lafiya network ne babu a ciki na fito nan yin waya."


"To muje ko"

Tare suka nufi cikin gidan. Tsakar gidan ƴan ƙananun suna ta hada-hada gida ya kacame da sowa da
hayaniyar yara.

[6/17, 12:42 PM] Ummulhair S Panisau: TUN A KARON FARKO....

NA

Ummulkhairi S Panisau (KhairatUP)

Karamci Writers Association.

(Karamci shi ne tushen mu'amala tagari)

Pg 18.

Washegari Abba Idris Doko ya gama haɗa kayansa tsaf cikin ƙaramin akwati. Duk ɗakunan matansa sai
da ya bi ya dubasu daman al'adarsa ce hakan ko baya gari zai kira ko wacce a wayar salularta.

Kowacce sun yi sallama mai kyau. Ammi kuwa kasa ma haɗa idanuwana tayi da shi a cikin fargaba take
bata son mai zai biyo baya ba.

"Kiyi ƙoƙarin gyara ɗabi'unki Zuhura kiji tsoron Allah in ma kina da sa hannu fiye da haka ki wanke kanki
ko in ce ki warware ƙullin da kika ƙulla. Har kullum Allah Yana tare da masu gaskiya da amana Mar'yam
dai ƙawarki ce tun ta yarinta kusan ma tare muka sonku duk abinda kika aikata sunan shi cin
amana ,zambo cikin aminci."

"Wai ni Idris me kake nufi ne? wanne ƙulli kuma? wane abu nayi wa Mar'yam ni na yi mata ko ita tayi
min kowa ita kowa ita kenan ma bani da wani muhimmanci a duniyar zuwa nayi kawai nayi mata fadanci
ko me?" Ta faɗa a hasale.
Murmushin gefen baki yayi yace "Me hali dai baya fasa halinsa Allah Ya shirye ki."

"Ameen." ta faɗa a hasale.

Yana fita ta saki tsaki kamar bakinta zai tsinke. Dama can tsiwa gareta ga neman magana bata shayin
kowa.

A farfajiyar gidan ya gama sallama da yaranshi duk.Aliyu Da Hashimu ne suka raka shi duk da tare da shi
za ayi tafiyar Hashimu kuma zai dawo da mota amma yanzu gidan Abban Doko zasu fara zuwa.

Cikin tafiyar mintuna kaɗan suka isa gidan. Ba ma su kai ga shiga ciki ba suka tarar da kaf ƴa'ƴan Alhaji a
farfajiyar gidan sun yi jigum ga ambulance nan sun zagaye ta suna kuka.

Alhaji Ya waiga ya hanga bai ci karo da Mar'yam ba daman ya son ba zai sameta ba a wurin.

Amarya ya kalla lokaci guda duk ta fige ta rame kamar ba ita ba har baƙi yaga tayi masa a ido. Alhini ya
na ta dukanta.Ya kuma juyawa ya ga yaran ma kukan suke yi an riƙe Marhaba da take ta shiɗewa tsabar
kuka daman ya sani sai abun ya fi dukanta fiye da kowa saboda kusancinta da mahaifinta.

Wani abu mai ɗaci yaji ya wuce masa ta makogwaronsa da ƙyar yake cilla ƙafa ya shiga cikin ainihin
gidan . Ɓangaren Mar'yam ya nufa ɗakinta ya ƙwanƙwasa sannan yayi mata sallama.

Duk da tana jin faɗuwar gaba haka bai hana ta maze ta ari dauriya da haɗe rai ta buɗe ƙofar ɗakin.

"Mar'yam.." ya ma kasa ce mata komai ji yake yi kamar zai yi kuka saboda tausayin amininsa kenan ma
sadauka...."
"Alhaji Idiris Aliyu Doko yau kuma bayan shekarun da suka gabata?"

"Mar'yam a karo na biyu ina son ki yi mini wata alfamar."

"Hh!Alfarma kuma Idris ? kuma ni kake son nayi maka alfarmar? ai babu wannan a tsakaninmu wadda
nayi maka a baya ma har yau ina kokawa."

"Don Allah ba don ni ba ,ba don Sufyan ba ki duba Allah ki duba manzonsa ki zo kuyi sallama da Sufyan
bamu sani ba ko zai dawo ko ba zai dawo ba...."kasa ƙarasawa yayi yaji hawaye na son zubo masa haka
ya saka ya juya da sauri.

Kallon bayansa ta dinga yi tana jin wani irin abu na taso mata a ƙirji, baya take tunowa ina-ma-ina-ma
ina-ma zata iya goge wannan daga baƙin allon ƙirjinta.

"A karo na biyu Sufyan Doko ya ƙara cin darajar ka."

"Nagode Mar'yam."

Hijab ta sako ta bi shi a baya fuskar nan babu haiba ba fara'a.

A karo na farko taji wani abu ya ɗarsar mata a zuciya na tausayi irin tausayin da ake kira tausayin uwa ga
ƴa'ƴanta bata taɓa jin hakan a cikin ranta ba sai yau a fuzge ta bisu da kallo dukaninsu sai taga duk sun
rame sun fice daga hayyacinsu bata san yadda aka yi ba ta dai ji wani abu ya taɓa ta a game dasu. A
hankali ta nufi motar ambulance ɗin ta shiga ciki.

Ahmad ne a gefensa.
Shi kuma yana kwance kan gado ga oxygen a hancinsa, yayi baƙi sosai ya zabge ya koma wai ɗan tsrut
saboda ciwo bata ji komai amma taji wani abu ta dai zama confused ta rasa ma me zata yi tunani ko me
take ji a lokacin.

Ahmad ne ya ɗago kansa jin Abban ya taɓo shi. Da sauri ya tsuguna wurin bakin Abban nasa don yaji
abinda yake faɗa.

Harshensa a kakarye ya haɗa masa jimlar "Mar'yam ina sonki."

A sukwane ba tare da ya kalli Mamin ba yace mata "Yana yi miki magana."

Tashi yayi ya fita daga motar ya kulle.

Duk suka biyo shi suka ce masa "Lafiya ? ya na ga ka fito ka barsu tare? kar ta cutar da shi fa." Kowa da
abinda yake tambayarsa.

"Aa babu komai magana zasu yi."

"Daman Abban na iya magana?" Inji Amina.

Abun ya bani mamaki har hannuna ya kama kuma yayi magana Mami na shiga ya iya yin magana ke ni
soyayyar da Abban ke yi wa Mami ma tsoro take bani kamar aikin asiri.

Murmushi Sajida tayi kawai.

Shi kuma Imran yace "Babu wani asiri shi so ai gamon jini ne wannan soyayyar da kuke ji da gani daga
Allah take kuma ita ce ƙaddarar Abba rashin jituwarsu wani abun ne na daban daga Allah ba kowanne
bane dole sai ya ƙare da farinciki ba akwai alaƙar da bata da ƙarshe ko da kuwa ɗayan baya so.
"Amma dai Allah Ya wadai da irin wannan muguwar soyayyar me amfanin son da ba a sonka?" Inji
Amina.

Abba Idris Doko ya gyara zaman rigars yace "Ku shiga mota mu wuce lokaci na tafiya."

Ahmad ya amsa kuma yana son ya shiga ambulance ɗin amma Ababn ya tsaida shi ka shiga gaba kawai
ka ƙyale su.

"Amma Abba Mami fa..."

"A'a bana son gardama tsahon shekaru ashirin da tara bata cutar dashi ba yau ma ba zata cutar da shi
ba."

Jin hakan ya saka ya zagaya ya shiga gidan gaba.

Yana shiga Mami na leƙowa ta kalli Alhaji Idris tace da shi "Ka zo."

Ya kalli sauran yaran ya ce su wuce kawai zasu taho tare.

Mar'yam.... ku san sakanni biyar yayi kafin ya iya ƙara cewa komai.

Na son kin yi biyayya kuma kin haƙura da dukannin wani buri da kika tanada wa kan ki na gidan aure da
soyayya... na sani na rusa miki dukanin wani tanadi na shiga cikin rayuwarki a lokacin da ba kya buƙatar
hakan...na san akwai abinda ya faru a shekarun baya kuma na san sadaukarwar aka yi mini......
Duk su biyun ɗaga kai suka yi suka kalle shi.

Murmushi yayi yace "Ban rike kowa ba kuma ban sa hakan a raina ba. Roƙo na ɗaya ne Mar'yam a
gareki. Don Allah kiyi haƙuri ki duba ƴa'ƴana ki kula min da su cuta ba mutuwa bace kuma nayi imani da
Allah da ranar lahira ,na kuma son mutuwa rigar kowa ce ina ji jikina kamar sallama nake yi da ku,ina ji
kamar ba zan dawo ba don Allah ki kula dasu musanmman Marhaba."

"Doko don Allah kayi shiru hakan nan waya gaya maka cuta mutuwa ce? In sha Allahu zaka tashi, zaka
dawo da ƙafafuwanka ras har mu buga ball kamar baya na jima ban tsokane ka ba Doko i need you by
my side zan iya yin komai domin ka , nayi kewar mu da rayuwarmu don ALLAH fight Doko fight."

Hannun amininsa kum ɗan'uwansa ya kama gam a cikin hannunsa guntuwar ƙwalla suka zubo masa.

Ƙirjinsa ya ji ya tsananta bugu hannunsa ya saka ya dafe saitin da zuciyarsa take yana jin wani iri.

Idris Doko ya dafa shi "Relax Doko ya isa kayi shiru don Allah ka kwanta ka huta kaji ko ba komai mun
fahimci komai zata kula maka dasu tare zaku cigaba da kula dasu da yardar Allah.

Sai taji wani abu ya tsarga mata tausayin Sufyan Doko take ji yau fa ita ke tausayin Doko A KARON
FARKO na rayuwarsu tare.

Jini ke fitowa ta bakinsa Idiris Doko ke share masa da hankicinsa yana share hawayen tausayin amininsa.

Gaba ɗaya rayuwarsu take taryowa daga can har zuwa yau babu inda Doko bai yi don ya faranta mata rai
ba.Babu lallaɓatan da bai yi bad on ya samu kanta. Bata taɓa ganin mutum mai haƙurin Sufyan Doko ba
ga ɗauke kai ga sauƙin kai da sanin ya kamata in ta ce ma bata wahalar da bawan Allahn nan ba ma tayi
ƙarya bata san ya aka yi ba kawai taji bakinta ya furta "Sufyan Doko ka yafe min."

Ba iya su ba ita kanta data faɗi kalmar haƙurin sai da taji bambarakwai.
Wallahi ban taɓa riƙe ki a raina ba indai nine Sufyan na yafe miki ni miki yafe min.

Daga haka motar tayi shiru babu wanda ya ƙara cewa komai. Sai tashin ƙarar mashin kawai kake ji ɗin
ɗin ɗin.

A iyafot suka rabu da kowa Abban Doko da Aliyu da Ahmad Da Imran suka tafi da Abban sauran kuma
suka koma gida.

Tunda ta shiga ɗaki bata kuma leqowa ba.

Amarya ma bata kuma cewa komai ba.

[6/17, 12:42 PM] Ummulhair S Panisau: A CIKIN IDO...

NA

Ummulkhairi S Panisau (KhairatUP).

Karamci Writers Association.

(Karamci shi ne tushen mu'amala tagari)

Pg 19

________________________

Fuskar Sufyan Doko take gani da ta kulle idanuwanta mamakin hakan take ji bata son a yanayin da take
ciki ba amma tabbas yau taji tausayinsa kaɗan anya na kaɗan gashi tana ta tunaninsa. Yaranta suka gifta
mata a tunaninta to ta ina ma zata fara jan su a jikinta? musamman ma wadda ya faɗa Marhaba ajiyar
zuciya ta sauke a hankali tashi tayi daga zaunen ta koma kan gadonta ta kwanta a kan filo ta miƙe
ƙafufuwanta sambal farare tas dasu kamar jini zai fito in ka zurma hannayenka a cikinsu.

Wani abu taji ya taso mata a ƙirjinta da tuna da wani abu tuni hawaye suka soma kwaranya daga cikin
idanuwanta zuciyarta taƙi yi mata daɗi tun ranar da Sufyan Da Idiris suka shigo cikin rayuwarsu komai ya
dagule musu aminiyarta ta zamo babbar maƙiyarta da ba haka suke ba rayuwarsu abar so ce abar
kwatance amma kalmar SO ta rusa musu komai na fariciki da walwala a cikin duniyarsu tun lokacin da ta
auri Sufyan zuciyarta bata yi mata sanyi ba kullum a cikin baƙinciki take da fushi in za a yanka ta bata
zata ce ga abinda Sufyan yayi mata ba amma bata son shi ta kasa son shi kuma bata jin zata ƙaunace
shin.

Ajiyar zuciya ta sauke ta ɗau ɗankwalinta da ya kwance ta ɗaura. Abubuwan da Sufyan ya gaya mata yau
sun sanyaya mata jiki karon farko ta ji tana son tayi masa addu'ar samun lafiya ko don ya cigaba da zama
da yaransa da yake mugun so.

WAIWAYE.

_____________________

1990's

Jigawa State.

KƘARAMAR HUKUMAR DOKO.

_______________

Alhaji Ahmad Ibrahim Doko manomi ne kuma ɗan boko ne. Mutum ne kamili bafulatani mai jin ƙan na
ƙasa da shi. Duk wanda yake ƙarƙashin Alahaji Ibrahim ya san sauƙin kansa. Yana da dukiya yana kuma
da mata biyu da ƴa'ƴa goma sha ɗaya maza takwas mata uku. Al'adar gidan Alahaji.Doko bai yarda da
soyayya ba ko ɓata lokaci da ake yi wurin zance in dai ka zo da batun kana son ɗansa ko ƴarsa zai bada
ga koma waye in har ya yarda da kamala da darajar gidanku.
Yana da yayyu maza amma duk suna mabmbanta garuruwa biyu kuma na zaune cikin garin Kano. A can
ma ƴar autar shi take Mar'yam tun wani hutu da ya zo ya tafi da ita kasancewar tana da sunan Hajiyar su
da ta rasu sai suka ɗauki son duniya suka ɗora mata dan hatta kamannin Hajiyarsu sai da ta kwaso su. Shi
yasa ma Mar'yam ba tashin Doko bace da su kan zo amma da ta fara makaranta bata wani fiya zuwa ba
in ma tazo sai dai tayi kwana biyu zuwa uku.

Maƙocin Alhaji Ahmad shi ne Alhaji Mudasir Shehu mahaifi ne ga Zuhuriya Mudan ƙawa kuma ga
Mar'yam a lokacin da suke gari ɗaya an san su tare suke komai makarantar bokon ma tare aka saka su ta
kwana nan Girls secondary ta Garki.

Da mahaifin Zuhura da Mar'yam tare suka yi neman ilimi da rayuwa tare ma suka yi aure kuma gidajensu
na jikin juna.

In magariba tayi zasu fito daga sallah ba zasu koma cikii ba sai sun yi hira kuma an fito da abinci su ci su
tattauna kan cigabansu dana garinsu da mutanen ciki. Wajan ƙarfe tara kuma su koma gida haka ma yara
duk mazan zasu koma ƙarfe tara kafin a kulle gida ba su yarda da yawon banza ba ko fita haka kawai
kuma sun ɗora su kan noma da kiwo har ma kasuwanci kuma basu barsu a haka ba sai da suka sa suka
nemi ilimi daga na arabi har na boko saboda haka babu rashin wayewa ko ilimi a garin Doko akwai ƴan
boko sosai.

Cikin gidan Alh.Ibrahim yana da girma kuma yana ɗauke da ɓangare biyu kowacce a ɓangarenta akwai
ɗakuna uku da banɗakuna a ciki sai guda ɗaya a waje musamman saboda baƙi maza.

Akwai madafi a ciki don wata larura ta dare sai kuma wani babba wanda ake girkin gidan gaba ɗaya a ciki
kuma bai yarda masu aiki su yi masa girki ba matan ke yin masa girki da ƴa'ƴansu mata.

Gidan akwai tsafta da tarbiya.

Haka ma gidan Alh Mudan.

Akwai Mal.Ahmad Doko da Mal.Aminu Abubakar Doko sun kasance maƙotan juna kuma manoma su
ma , malaman addini ne suna da tsangayar da ake ɗaukar masu karatu.
Duk dai abokan juna suke su huɗun duk da arzikinsu ba ɗaya bane ba hakan bai saka an ware ko ana
nuna musu ƙyama ba kansu a haɗe yake gaba ɗayansu ana kwatance da amintarsu a garin kuma ana
ganin girmansu.

Haka ma ƴa'ƴasu ma suna da tarbiya da biyayya daga mata har maza in aka yi musu zaɓi babu wanda ya
isa ya musa haka za ayi kuma a zauna lafiya ko kana so ko baka so sai anyi in yaso ku fara soyayyar a
gidan auren can su ƙarata.

Zuhuriya Mudansir Shehu Doko aminiya ga Mar'yam Ibrahim Ahmad Doko tare suke makaranta duk da
ba gari ɗaya suke ba amma suna son juna da fahimtar junansu.Duk wanda ya san su ya son amintarsu
tun daga makaranta har garinsu duk da kuwa suna da hallaye mabambamta wanda zaka iya cewa basu
dace da kasancewa tare ba saboda bambamcin halayensu.

Mar'yam yarinya ce duk inda ka kai ga ganin fara'arta zai yi matuƙar wahala ka gani saboda miskilanci da
nunƙufarcinta wannan ma ya saka bata da wata shaƙiƙiya sai iya Zuhuriya. Ita kaɗai ce take kulawa kuma
zaka ga suna hira suna harkokinsu tare.

Mar'yam na da ƙoƙari ga kuma gayu tana da tsafta ko da suke ƴan makaranta bata zama da ƙazanta
kuma ba zaka ji wari a jikinta ba fara ce tas kuma tana da tsayi amma ba can ba tana da jiki mai kyau ba
za a saka ta a fannin sirara fitik ba hancinta dogo ne idanuwanta farare tas bakinta ɗan ƙarami haƙoranta
farare tas dasu saboda yadda take kula dasu. Tana da ƙoƙari sosai daga na arabin har na bokon. Mar'yam
bata son raini kuma in tace bata son abu to fa bata so kuma babu yadda za ayi ta so shi ko da kuwa za a
kashe ta da duka.

Zuhura kuwa tana da surutu da kuma shishigi ga shegen sa idon tsiya da hangen abin wani gata da
bakicikin ka samu abu bata samu ba yanzun nan hankalinta zai tashi ga faɗa da gulma muguwa ce wadda
kowa ya sani don in kayi mata abu ma sai ta rama ramuwa ma irin ta izaya. Bata da wani ƙoƙari sosai don
ba wani maida kai take yi ba wajen ɗaukar karatun ba kawai tana zuwa ne don Babansu ya saka ta. Tana
mugun jin haushin Mar'yam amma bata nunawa a fili baƙincikinta Mar'yam ta fita kyau da farin jinin
mutane duk da rashin maganarta da saukin fara'arta kuwa ga farin jinin samari in dai zasu fita a gansu to
zata yi kasuwa wannan na mugun baƙanta mata rai da ruhi amma bata taɓa nuna hassadarta a fili ba sai
dai ta ƙudurta a cikin ranta ba zata barta tayi rawar gaban hantsi ba sai ta san yadda zata tarwatsa
tauraruwarta.

Bakinta yayi tsini tsabar rigima da take cin ta sam wannan karon bata son zuwa Doko hakan nan take jin
bata son zuwa duk da kafin zuwan yau ɗin tana ta ɗokin tafiyar.

Hajiya Mama ta gyara zamanta da kyau tana dariya tace cike da tsokana. "Wallahi Mar'yam kina da
rigima nan kika saka Abbanku a gaba za ki Doko ya yarda ya shirya miki tafiyar yau kuma ki wani zo kice
kin fasa bayan an gayawa Baban da haj. Innar za ki je kin kyauta kenan?"

Ta kuma zumburar bakinta gaba idanuwanta sun yi rau-rau ƙiris take jira ta fashe da kuka. "Hajiya Mama
ni fa kawai ji nayi bana son zuwa kuma gaba ɗaya raina bai son tafiayar don Allah ki saka Abba ya haƙuri
naje wani hutun".

Hajiya Mamar ta kama haɓarta ta miƙe tsaye ta kwashe kayan da ta ninke ta zuba acikin dirowar
kayansu tace "Kin san dai Abban baya son irin wannan abin sai da yace miki ki haƙura in anyi hutun
islamiya kya tafi kika dage kuma an sawa Inna rai tana ta yo waya ta telephone kuma sai kice wai kin fasa
? ai baki kyauta ba mu ma naga wani satin zamu taho ba sai mu dawo tare ba? Ki je ki tayasu da shirin
bikin kin ga ai Aishatun nan za a kawo ta na rasa irin ki Wallahi ba kya son makaranta ko kaɗan kamar
ana gutsirar naman jikin ki."

Kawai sai ta saki kuka gaba ɗaya ta kwanta ta botsarewa Hajiya Mama. Hajiyar kuwa ta saki dariya sosai
tana jinjina irin rigima ta Mar'yam.

"To tashi Hajiyar masu gida yi wankanki ki kimtsa zan lallaba Abban naji ko zai haƙura ki tafi wani satin
tare damu."

"To Allah sa ma ya yarda."

Amin.
Hajiya Mama kuwa ta faɗi hakan ne don ta lallaba ta tayi wankan ta shirya don ta son Abban ba zai yarda
ba.

Abban yana zaune cikin ɗakin da yake nazarin littatafansa dake professa ne a jami'a. Hajiya Mama na
shiga cikin ɗakin ya ajiye littafin ya saki murmushi yace "Hajiyar Mar'yam kun shirya ne?"

Ga can uwar masu gida tana aikin rigimar tata wai ta fasa tafiyar kaji fa wata rigima nan ta cika mana
gida da ɓaɓatun sai ta tafi ayi komai a kan idonta yanzu kuma wai ta fasa duk ta rikita min lissafi yanzu
ma lallaɓa ta nayi ta yi wanka kafin Yayansu ya shigo su wuce.

Murmushi yayi yace "Gidan rigima da kanta ba uwar masu gida ba ai na son za a rina amma dai zanje in ji
dalilin rigimar."

Bayan ta fito daga wankan ta shafa mai ta shafa farar powder ta ja jagira yadda ta saba ta zagaye ɗan
ƙaramin bakinta da baƙar jagira sannan ta shafa jambakin nan kan ta kile. Kwalli ta zizara ta ɗiga a
goshinta ɗan ɗis t kalli mudubi taga tayi kyau sosai. Turare ta fesa ta yi ɗaurin nan nan ture kaga tsiya ta
ɗauki mayafi ta yafa akan kafaɗarta. Awawaro ta ɗauko ta saka biyu a hagu biyu a dama ta sanya zobe
guda biyu . Ɗinkin ta na ƙarewa kallo ɗinki mai kyau ta saka doguwar riga hagu da dama anyi tsagun da
bai kai ciki ba irin yankan gefe da gefe ta ɗaura zani hannun rigar dogo daidai guiwar sahu na hannunta.

Tana fita falo suka zubo mata ido gabaɗaya don kwalliyarta tayi kyau abar burgrwa babu wani rashin
ɗa'a a shigarta.

Ma Sha Allah!uwar masu gida tabarkallah gaskiya kin yi kyau anya kuwa jama'ar Doko kuwa zasu iya
gane ki kuwa?

Hararsa tayi ta kuma sakar masa tsaki.

Shi kuwa dariya yayi ya miƙe yace "Bani na kar zomon ba rataya aka bani."
Harar dai ta kuma sakar masa ta isa kusa da Hajiya Mama ta rugumeta tayi mata sallama.

Ɗakin baban ta shiga tayi masa sallama ya yi mata kyakyawan sallama.

Yaya Faruk ya saita masu hanya suka nufi Doko.

Da yake ya san halin kayarsa ba mai magana bace shi ma bai takaleta da hira ba radio kawai ya kunna ta
zame masa abokiyar tafiya.

Taga kawai take kallo suna wuce garuruwa da shaguna da bishiyu.Ƙarshe ma kwantawa tayi ta kulle
idanuwanta.

Ƙare mata kallo yayi yace da ita "Mar'yam ina tausayawa wanda za ki aura saboda miskilancin ki
gabaɗaya baki da hali."

Hum kawai tace bata kula shi ba.

Kya maidani soko mana ina magana kin min banza.

To Yaya me zance maka? ni wanda zai aure ni kawai ya aure ni da halina a yadda nake ni bani ma da
wani lokacin soyayya ni kam kawai a dinga ɓata lokaci ana surutai na ƙarya da wofi wai soyayya.

Yo ke da babu soyayyar a haife ki?

To ni dai daɗinta bani nace a hafenin ba.

Murɗaɗiya kawai.
Yayan murɗaɗiya ba.

Dariya yayi cike da mamakin ta ya kuma maida hankalinsa kan tuƙinsa.

Ita kuma ta koma da baya bacci ya ɗauketa.

[6/17, 12:42 PM] Ummulhair S Panisau: A CIKIN IDO...

NA

Ummulkhairi S Panisau (KhairatUP)

Karamci Writers Association.

(Karamci shi ne tushen mu'amala tagari)

20

Tunda suka isa yara ke bin motar da gudu ana ta ihu irin dai yadda yaran ke yi.

A daidai ƙofar gidan suka tsaya lokacin ma samarin gidan sun daddawo daga gonaki.

Baban ma ya dawo aka hau yi musu lale-lele maraba da zuwa.

Nan-da-nan aka yi musu iso cikin gida aka hau shigar musu da kayansu ciki da tsabar Kano da Abban ya
aiko dasu na biki.
A tsakar gida Hajiya Inna ta shimfiɗa ƙatuwar tabarma suka za-zauna.

A cikin kanon sha aka zubo musu ruwan sanyi daga cikin randa aka kawo ma Faruk da tuwo a cikin
samira ga soyayyan nama a cikin ƴar ƙaramar samira an barbaɗa masa yajin daddawa.

Suka dinga hirar Kano da yaushe rabo ana ta yin haba-haba da shi. Mutanen Doko suna da karamci da
iya saukar baƙi in dai yazo sai ya tafi da farincikin karamcin da ake nuna musu kamar dai wasu daban a
cikin al'umma.

Yana gamawa aka kai shi ɗakinsu Badamasi ya huta gajiya.

Ita ma ɗakin Hajiya Inna ta shige cikin ƙuryar ɗaki ta haye kan gadon tayi kwancaiyarta.

Tana tsaka da bacci ne taji saukar duka a bayanta ta bata ɗal aiko a zabure ta miƙe tana sosa bayanta
saboda zafin da taji na dukan.

"Amma ke dai baki da mutunci Zuhura wannan ai wulaƙanci ne me nayi miki azzaluma"?

Zaunawa tayi a kan gadon tace "Azzaluma ko dai ƙawar azzaluma shegiya ki shigo garin ki kasa shigowa
ki sanar min isowarki ƴar duniya".

Harararta tayi kawai kafin tace mata "Kar ki fasa don ubanki anƙi a shigo cikin gidan in ma za ni ba
wurinki za ni ba wurinsu Gwagwon za ni kai gaisuwa ai ke ya kamata ki zo ki mini sannu da zuwa taki
kalar sannu da zuwan kenan?"

Ta kama baki tace "uh'uh Allah ƴar gari to sannu da zuwa Hajiya Mar'yam sannu yaya hanya?"

Tsaki ta saki ta sauko daga kan gadon ta gyara ɗaurin ɗankwalinta tayi hanyar banɗakin Inna don ta
kama ruwa.
Sai da ta fito ta kalli ƙawarta tace "Na ji kin yi shiru lafiya duk na gan ki wani iri?"

"Uhm ƙawata labari ne a bakina fa shi yasa ma na kasa yarda ki shigo gwara nazo na gaya miki ko akwai
shawarar da za ki bani."

"Shawarar me kenan?"

Wallahi nake gaya miki ƙawata zuciyar nan ce ta afka akwatin sirrin wani bawan Allah ni fa duk na susuce
ko baccin kirki bana iya yi ina can ina tunaninsa."

Allah Ya wadai naka ya lallace kin shiga uku soyayya wata abar yi ce ma kuma ma don rashin aji kece kika
gani kina so sai ki je ki gaya masa kawai.

Kamar ya na gaya masa haba ba aji kenan.

Da kika faɗa soyayyar shi baki ji ajin naki ya sauka ba sai don za ki gaya masa?

Eh ai soyayyar da ke kamuwa ake yi da ita bani na sawa kaina ba Allah ne ya ɗora min kuma nima ina ji a
jikina yana son nawa kawai ya kasa gaya min ne.

Sai kiyi tayi ai ni matsa min na huta.

Don Allah ki zo ki rubuta min wasiƙar lobbaya na aika masa a ɓoye kin ɗan rubuta masa i lobiyu i need
you.

Na rantse da Allah ba zan rubuta miki ba kuma in kika kuma gaya min wannan maganar sai na fasa miki
baki na miki ɗan banzan duka.
Dariya Zuhuiriya ta saka ta kwanta a kan gadon tana ɓaɓaka dariya kamar zararriya har Inna ma ta shigo
ɗakin ta soma yi musu faɗan irin dariyar da suke yi har tsakar gida ana jinsu san kuma bata da amfani a
addini sai kace ba mata ba . Gum suka yi da bakinsu saboda kar a kuma yi musu faɗa.

Tashi-Tashi ki shirya mu fita don Allah akwai wani wasa da za ayi a bayan layi.

Ke ni ƙyale ni kin son bana son wannan yawon iskar ai kije ki dawo ni a a gajiye nake Wallahi.

Wani zubin kamar mai kwankwamai haka kike ko don kin ga ina son zuwa wurinki ne shi yas kike
wulaƙanta ni yadda kike so kar kije ɗin.

Kallonta tayi sai kuma tace "Kin saba yi min daɗin baki ko kuma kiyi min kalar tausayi kamar bana son ki
ko na fi ƙarfinki sai kije ki shirya nima zan ci abinci tukuna sai na sauya shiga mu tafi."

Rungumeta tayi ta baya cike da farinciki ta fita daga ɗakin.

Kai kawai ta girgiza ta shige banɗaki.

Tana fitowa daga wankan tayi shafa ta kuma yin wata kwalliyar har tafi wadda ta taho da ita daga
Kano.Atampa mai tsada ta ɗauko cikin wadda Abba ya ɗinka musu waccar sallar babba. Falon Ina ta fito
tana saka awarwaro mai guda shidda a hannu ɗaya .

Inna ta kalleta tana murmushi haɗe da cewa "Tabarkallah Uwar masu gida kin yi kyau sai ina kuma?"
Yaƙe tayi tace da ita "Wallahi Inna a gajiye nake hasalima bana son zuwa wurin wasan nan don dai
Zuhura ta matsa ne kin son bana son hayaniya Wallahi." Yadda take maganar ma ya isa ya saka ka gane
tabbas bata son fitar.

Inna ta ajiye shinkafar da take gyarawa za a jiƙa da safe waina za a soya. Ban da abinki ai za ki ji daɗi in
kin zauna kawai a gidan me za ki tsinta kije ki ga gari daman kin jima baki ga wasan dandali ba.

Shikennan Inna sai mun dawo.

Allah Ya sa a kula kuma banda rawar kai duk da na san baki da matsala ta nan.

In Sha Allahu Inna.

Tana fita ta shige gidansu Zuhura a tsakar gida ta same su dukanninsu kowa a zaune ita kuma
hamshakiyar sai masifa take yi da ƙaninta Isiya.

"Allah dai Ya kyauta miki Zuhura baki da hali wani bin ki rasa da wa za ki dinga faɗa har ana jiyo muryarki
daga waje sai ƙanin bayanki.Ki gyara hali Wallahi."

Hararta tayi sannan tace "kin san me ya yi mi ne? Za ki wani shiga sabgar da babu ruwanki".

Hannu ta ɗaga sama ta tsuguna tana gaida matan gidan suna mata barka da zuwa.

"Malama kiyi sauri mu tafi don ni ba jimawa zan yi ba hasalima don ke zan je."

Haka suka tafi Zuhura na mita da bambanin faɗa a hanya suka haɗu da Atika sun sha kwalliya jambakin
nan radam an shafa a baki ga shi an ɗiɗiga a saman fuska riga daban zani daban ɗankwali ma daban.
Bata dai ce musu komai ba suka ɗauki hanyar wurin wasa suna tafe suna hira ƙasa-ƙasa.

Mar'yam kuwa bakinta gum bata cewa um bare um'um.

Bakin bishiyar tsamiya suke zaune tun da suka gama noman jikinsu yayi la'asar sun yi futuk dasu saboda
aiki baya ma Sufyan da mafi yawan aikin shi yayi.

Idiris ya ɗauki fatanyarsa ya kalli amininsa yace da shi "Wai ba zaka taso mu tafi ba?"

"Wallahi Doko na gaji kamar an min duka haka nake jina ji yadda hannuna yayi kanta yau kawai."

"Shegen son jikinka dai tashi da Allah mu wuce ko ka manta yau akawai wasa ka sani ko mu haɗu da
firities (preeties)"

Bushewa Sufyan yayi da dariya sannan yace "Da ka faɗi wannan maganar sai ka tuna min da mafarkina
na jiya. Wato Allah da girma yake in dai na samu wannan yarinyar na more mata alquran."

Tsaki Idris yayi yace "To ɗan malam jikan malam ka san dai bamu da komai ko? aljihumu fus mu ɗalibai
ne kar ma ka fara rakito mana zancen auren nan ka sa wani yaji har ya kai kunnen Malam dama sarai ka
san yadda suka matsa mana akan batun aure."

Kai ni Wallahi in dai zan ga wannan yarinyar sai n nemi aurenta ko da bata sona zan jure.

Duka ya ɗala masa a bayansa da ƙarfi . Sufyan ko ya saki ƙara ya tashi da zafinsa yace "Wallahi sai na
rama ba zan yarda ba sai na rama." Suka fara kokaye-kokaye kamar wasu yara ƙananu daga nesa ya
hangosu su uku ta tsakiyar ce ta ɗauke masa hankali sosai gabaɗaya kwalliyarta ta tafi da imanin shi
gabaɗaya.
"Tabarakalla Ma Sha Allah" Ya ambata a fili yana sakin wuyan rigar Idris ya yi gaba abinsa.

Idiris kuwa ya bi bayan Sufyan da kallo ya maida hankalinsa kan inda ya dosa ƴan'mata uku ya hango
cikin shigar burgewa sai dai shigar ta tsakiyar tafi burge shi da kwalliyarta take yaji wani abu kamar
mashi ya soki ƙirjinsa da ƙarfi har yana lumshe ido.

Tunda suka ƙaryo ƙwana ta hangi samarin biyu suna faɗa kamar yara sai ta yamutsa fuskarta suna ƙara
kusantosu sai taji kamar tayi amai ta ƙyabe fuska musamman da taga Sufyan wanda kayan jikinsa ma sun
yi dama-dama da ruwa da jar ƙasa sai kawai ta kawar da kanta gefe.

Sufyan da Idiris basu bar nufar su ba cikin sakan biyar suka isa garesu suma suka tsaya.

Zuhura tace "Yayi Hamimai don ku kam kun wuce ace muku aminai saboda kusanci da amincinku
SufyanIdirisDoko."

Dariya Sufyan yayi don jin sunan da ta kirasu da shi wai "Hamimai"

"Meye kuma Hamimai?" Idiris ya tambayeta yana kallon ƙeyar Mar'yam don juyar da kai tayi gefe guda.

Zuhura ta ƙara iyayinta haɗe da ƙarya muryarta tace "Hala daga gona kuke nagan ku futuk musanman
Sufyanu."

Tunda Mar'yam taji muryar Idiris taji gabanta ya buga mata ras take ta ji tana son juyawa ta gan shi da
kyau amma ina miskilanci ya shiga tsakani.

Sufyan yace "Zuhuriya wacce wannan naga tayi shiru kamar bata magana?"
Wai Mar'yam?

Ita fa.

Ƙawarmu ce tazo daga birnin Kano hutu amma fa ƴar garinmu ce ƙanwarsu Badamasi ce ƴar wajen
Hajiya Inna matar Alhaji Ahmad.

Au! Au kice sister ce.

Ƙwarai ma kuwa.

Kwalliyarta ya ƙara bi da kallo babu hayaniya babu gidadanci g nutsuwa da aji gabaɗaya ta gama birge
shi.

Mar'yam kuwa hakan nan taji ma Sufyan ya bata haushi ya fiya dariya kamar wani shashasha ko sha-ka-
tafi.

A hankali tace "Zamu wuce ko in koma kin dai son na gaji ko?"

"Yi haƙuri muje."Zuhura ta faɗa tana dariya.

Sufyan da Idiris kuwa suka yi musu sallama suka ce dasu zasu bi yo bayansu wanka daman zasu je suyi.

Da haka suka rabu.

Atika kuwa da suka yi gaba tace "Mar'yam a dinga sakin fuska dai gashi ma kamar Sufyan ya kware miki
ke ki godewa Allah Sufyan yadda ƴan'mata ke rububin shi....."
"Dallah can bari me haka wannan ƙazamin za ki haɗani da shi to bana so kar ki kuma wannan ai raini ne."
Ta katse ta da sauri haɗe da jan tsaki tayi gaba ta barsu a baya.

[6/17, 12:42 PM] Ummulhair S Panisau: A Cikin ido....

NA

Ummulkhairi S Panisau (khairatUP)

Karamci writer's Association.

(Karamci shi ne tushen mu'amala tagari)

15.

Babu abinda ke tashi a cikin motar sai koken Sabreen gaba ɗaya ta muzanta kenan yau da ba don Aliyu
ba sai sun yi mata raga-raga tunanin hakan kawai da tayi sai taji wani irin tsoro ya shigeta ta kuma
antayawa kogin tashin hankali. Hawaye ne kawai suke yin fareti a kan fuskarta.

Tun yana ƙoƙarin sharewa har ya ga ya kasa ɗauke kai a hankali ya buɗe ƙaramin bakinsa yace "Ya isa
mana Sab kukan me zai miki? kawai ki sani wanan ya zame miki izina d ishara akan irin ƙawayen da za ki
dinga mu'amala dasu. Ba laifinki bane kaddara ce kuma ba mamaki silarki su ma su daina ki daina kuka
please."

Har harɗewa maganarta take yi wurin maida masa amsa. "Na so na rusa maka rayuwarka amma Allah
bai bani iko ba na so na raba kan ka da matarka Allah bai so ba sai ya maido mini sharrina kaina. Ka yafe
min Alee ka yafe min nayi nadama ina ma kan yin ta da ace nayi tawakalli na kuma yarda da hukuncin
Allah da wata ƙila ina nan cikin nutsuwa da farinciki ban taɓa tunanin zan kasance cikin muzanta irin
wadda na riska a yau ba ko bacci bana iya yi da ace ban gaya maka ba da tuni sun ƙara dulmiyar dani sun
lallata min rayuwata da suna a idon duniya bani da wata sauran mamora Alee babu wanda zai aure ni...
ta saki kukan gaba ɗaya ta sa kanta tsakanin cinyoyinta biyu tana kuka ko ina a jikinta rawa yake yi
kawai.
Tausayinta ya kama shi abin ka da tsohuwar zuma sai yayi kamar zai dafa ta sai kuma ya fasa bai kuma ce
mata komai ba har suka isa station.

Kafin su fito daga mota ya zaro hanky ya miƙa mata. "Gwara ki zamo mai ƙarfin zuciya Sabreen babu
wanda zai iya yi miki faɗa a kodayaushe sai ke a kan kan ki ke ce kawai za ki daukar wa kan ki matakin
ƴanci da bin hakkin kai so kuka ba naki bani akwai ƙalubale kala-kala da zasu iya riskarki a kowanne
mataki na rayuwa ina fatan kin fahimce ni ? kar wanan abun ya zame miki dodo kamata yayi ki yi amfani
da shi ki ƙarfafawa kanki guiwa da kan ki.

"In sha Allah" ta furta a hankali tana goge hawayen ga idanuwanta jajir don kuka baƙin gilashinta ta
ɗauko daga ciki jaka ta saka.

Tare suka jera suka shiga cikin station ɗin.

Suna shiga suka ga su Amira a kan kujera a zaune wanan Hajiar sai kare fuskarta take yi da hannu.

Idanuwan Amira kamar zasu faɗo ƙasa don harara.

Zaunawa suka yi kusan mintuna bakwai tsakani aka yi musu iso wurin DPO dama tuni an ƙwace
wayoyinsu duk su ukun.

Bayan duk sun zauna DPO ya soma magana.

"Amira Amiru ko"?

Cike da rashin kunya tace "na'am."


Ya kuma kallon ƙawar Ameeran yace "Haulat Sabi'u amma ana kiranki da Baby"

Ita kuwa ɗankwalinta tay gaba da shi alamar ture ka ga tsiya ɗin nan ta kawar da kai gefe.

Aikuwa ƴar sandar wurin bata yi wata-wata ba ta ɗauke mata fuska da mari hagu da dama tuni taga
taurari da tsakar rana suna yawo a gabanta.

"Bar ta a haka ma Ispeto."

Ta kuwa koma da baya ta haɗe hannayenta wuri guda.

Ba sai mun yi dogon surutu da ku ba kun san akan abin da ake tuhumar ku da shi na san kun san ni kuma
nima na san ku na jima ina gaya muku cewa wata rana tulunku zai fashe yau yayi fashewar da ba zai
gyaru ba dama ƙiris nake jira gashi yau dubunku ta cika.

"Yallabai ƙarya take yi ba haka bane da yardarta hakan ya faru babu wani fin ƙarfi da aka yi mata da
yardarta ne....." Haulat Baby ta faɗa tana zoɓaro baki.

Teburin gabanshi ya buga da ƙarfi ya daka musu tsawa yace "An jima ana kawo ƙararku rashi hujja ya
saka ake sakin ku. Sabon ku ne kuyi ta haikewa ƴa'ƴan mutane ko ta ƙarfi ko ta asiri ko ma ku siyar da
yara ko ku ɗorasu akan turbar fanɗarewa iyayensu ta hanyar shiga harkar karuwanci ga safarar ƙananun
yara da kuke yi wa mata manyan ƙusoshi a ciki da wajen garin nan to yau ƙarshen ku ya zo babu wata
doguwar magana da zamu yi da ku kotu zamu kai ku."

Tuni Hajiya ta sauƙo ƙasa tace "Yallabai kayi wa Allah kar ka haɗani da sabgarsu bana son mijina yaji
wanan abun da yake faruwa aurena mutuwa zai yi ƴa'ƴana daina ganin girmana zasu yi iyayena da
ƴan'uwana basu karɓe ni ba."

Hajiya kiyi mana shiru ki koma baya. Ba halinki bane aka kama ku da su? ba kya irin harkarsu muka ganki
a inda bai kamata ba?
Yallabai ba haka bane ko da nake yin haka kaddara ce ba da sona ba ne ba halina bane Wallahi ,Yallabai
mijina babban attajiri ne ɗan siyasa ne ba ya zama dani ni kuma na kasa jurewa mata suna burgeni suna
bani sha'awa haka ma maza sai dai nafi son jinsina ban san barazana suke yi mata ba ni kawai suna kawo
min ƴan'mata ne ina biyansu kuma da yardarsu nake komai ban san ita wanan haka bane sai yanzun
gasu nan ku tambayesu.

Amira tace "Haka ne yallabai babu ruwanta bata sani ba."

Haka aka amshi wayoyinsu duka suka buɗe aka shiga aka goge kaf vedios da hotuna ɗin wayoyinsu duka
aka yi formating dai-dai da emails da chart duk sai da aka bankaɗa aka goge sanan aka saka wayoyin a
cikin evidence bag aka ajiye a loka.

Aka yi gaba dasu,Hajiya kuma ta kira ƙawarta tayi belinta.

Bayan dogon jawabi aka yi musu tsakani da Sabreen.

Aliyu da kan shi ya maida Sabreen gida.

Ko da ya duba agogo ya ga dare yayi sosai wajen ƙarfe goma ma na dare.

Wayarsa ya ɗauko yaga kiran Marhaba har sau biyar da message. Kan shi ya dafa ya kunna mota ya fita
daga gidansu Sabreen.

Kai tsaye gida ya nufa ko kayan ƙwalam ɗin ma bai tsaya ya siya musu ba.

Yana shiga falon ya ganta a ƙasa a zaune sai kuka take yi ga waya a hannunta jikinta ko ina rawa yake yi
tana gaba tana baya da jikinta.
Da sauri cike da mamaki ya isa kusa da ita ya tsuguna a gabanta yace "Me ya faru lafiya na gan ki a
haka?"

Bata ce masa komai ba kuma bata fasa rawar jikin ba ,kukan da take yi ma babu sauti sai hawaye kawai
ki zirara goshinta ya dafa zafi rau ganin sai magana yake yi mata ta kasa bashi amsa ya saka ya sa
hannayensa biyu ya jijigata da ƙarfin gaske ya kira sunanta "Hauwa'u" . Sai a lokacin ta dawo hayyacinta
sai kuma ta rungume shi ta saki kukan sosai cukuikuye shi take yi har yana jin zafin sukar farcenta a
bayansa.

Menene ya faru kike irin wanan kukan?

Cike da rashin nutsuwa take ce masa "Kowa baya sona Mami bata sona ,Ammi bata sona,kai ma baka
sona Abba da....nak...e tunanin yana sona...shi ma ya daina sona zai tafi ya barni ni kaɗai a cikin mutanen
da basa sona...me nayi muku? Baƙin jinina har ya kai haka?......

"Ke" ya faɗa da ƙarfi ya doke mata bakinta ya zauna da kyau ya gyara mata zama ita ma ya fuskanceta da
kyau.

"Ki gaya min me aka miki?"

Yaya Aliyu Aure zaka yi?

Abba yana kwance a gadon asibiti rai a hannun Allah . Ina ta kiran ka don kayi min izinin zuwa ganin shi
ka ƙi ɗaga wayata saboda kana wurin budurwarka sakkayar da zaka min kenan? daman tun a KARON
FARKO ba sona kake yi ba tayin aurena aka yi maka ...

Ganin kamar ba a hayyacinta take ba ya saka ya tashi da sauri ya buɗe drower ɗin falon ya ɗauko
inhealer ɗinta ya koma zuwa lokacin numfashinta ya fara sama da ƙasa ta kwanta tana tari ga amai tana
ji tuni idanuwanta suka juye daga asalin kalarsu zuwa ja shaƙa mata ya dinga yi amma kamar babu
abinda yake yi mata ma. Mukulin motarsa ya ɗauka ya ɗauketa ya sa a bayan mota ya nufi asibiti da ita
ƙarshenta sai an saka mata oxygen ko kuma a yi mata allurar nan ta jijiya.
*

Alhaji Idris ko ina na jikinsa rawa yake yi gaba ɗaya zuciyarsa ta gama karaya ya gama saddakarwa
amininsa yau tafiya zai yi ya barsu.

Kwance yake marabarsa da gawa kaɗan ne numfashin ma sama-sama yake fita in ba ido ka saka sosai
bama bama ba zaka yarda akawai ragowar numfashi a tare da shi ba. Hannunsa ya saka a cikin hannun
aminin nasa shi ma nasa hannun rawa yake saboda tashin hankalin da yake ciki.

Hawayen da suka jima a maƙale cikin ƙwayar idanuwansa ne suka yi nasarar zubowa.

"Allah Ya duba maka Doko ,Allah Ya tashi kafaɗunka aminina don Allah kada ka karaya in ka karaya zamu
rasa ka kar ka bari soyayya tayi ajalinka Doko ka tuna muna nan muna jiranka,mu na nan muna kuka
saboda kai don Allah Do...." bai iya ƙarasawa ba ya juyar da kan sa gefe daga bisani ma ya fice daga ward
ɗin.

A yanayin da suka ga Alh. Idris Doko ya fito yana karkarwa ga hawaye a saman fuskarsa sai su ma
suka saki kukan gaba ɗaya suna daɗa gasgata cewa Abban nasu ya rasu.

Kallon tausayi ya bisu da shi kafin ya fice da sauri bai iya ma tsayawa rarrashin su kamar sauran
lokutan baya ba.

Wanan ya saka suka kira Marhaba ta taho gida Abba ya rasu.

Shi ne dalilin da ya sa Aliyu ya sameta a wanan yanayin.

Yana tafe yana kallon kujerar baya,ya ɗauko wayarsa ya kira Ahmad ya saka a handsfree.
"Ahmad me yake faruwa? me ya samu Abban Doko?"

"Mun rasa Abba Aliyu mun rasa shi.."

innallillahi wa inna illahir rajun waye ya gaya muku Abban ya rasu? ku tabbata ya rasu kai gani nan ina
hanya ba haka bane ban yarda ba.

Motar ya ƙarawa gudu sosai a ɗari uku da sittin ya ja su ya ma manta da halin da Marhaba take ciki.

Kayanta da aka kawo mata daga wurin wanki take dubawa ,kwashewa take yi tana sawa a cikin kwabet
ɗinta amma daka kalli fuskarta a zahiri za ka san babu wani annuri a tare da ita.

Buɗe ƙofar ɗakin aka yi aka shigo a hankali ta juya ta kalli ƙofar kallo ɗaya tayi musu ta juya ta cigaba da
abin da take yi.

A hankali-a hankali suka shigo cikin ɗakin suna rabe-rabe kamar marasa gaskiya ko wanda suka yi wa
sarki ƙarya.

Bata kula su ba su kuma basu saba yi mata magana ba basa hira ma bare suyi sabon da zasu saki ji da
ita.

Wanan ya taɓa wanan haka waccar ta taɓa waccar haka suka dinga yi daga bisani dai Amina tace ;
"Mami nasan kina mamakin zuwan mu cikin ɗakin ki mun ƙarya miki dokar ki ta zuwa inda kike... mun zo
ne muyi miki albishir da abin da kika daɗe kina roƙa.."ta kasa ƙarasawa saboda kuka da ya sarƙe ta.

Mami mace ce mai taurin zuciya da halin ko in kula ba kasafai aka fiya gane yanayin ta ba tun bayan da
aka haɗa aurenta da Sufyan bata ƙara yin ko da dariya ba a da ba haka take ba duk da tana da miskilanci
amma mace ce mai faram-faram amma daga ranar da Sufyan Doko ya shigo cikin rayuwarta komai ya
sauya mata tamkar ƙiftawar ido.... ajiyar zuciya ta sauke a hankali kafin ta kalle su ta kuma kalli ƙofar
ɗakin tace dasu "Ta inda kuka shigo nake so ku juya ku fita ba sai kun yi min rashin kunya ba zan san ku
ɗin ƴa'ƴan Sufyan ne."

A ƙufule Sajida tace "Anya kuwa akwai zuciya a ƙirjinki Mami? anya kuwa kin tausayinmu? ke kika haife
mu kuwa ko dai baki mu kawai aka yi riƙo. Abba bai cancanci wanan izayar ba gaba ɗaya rayuwarsa ya
ƙareta sabo da soyayyar ki ne why Mami why?"

Murmushin gefen baki tayu tace "Ban yi mamakin waɗanan kalmomin daga gareki ba kuma ban ga
laifinki ba ban kuma ji haushinki ba kawai dai bana son hayaniya a kaina zaku iya tafiya sanan ni nan na
umarce ku da kirana da sunana Mar'yam zan fi son hakan."

Sun kasa cewa komai zuwa yanzu kuma sun daina mamakin Mami ji suka yi kamar babu ƙafafuwa a
jikinsu sabo da sanyin da jikinsu yayi.

"Wacce iriyar ƙiyayya ce haka Mami."

"Ba zaku gane ba wanan ƙiyayyar TUN A KARON FARKO ta ginu ba yanzu ta ginu ba kuje ba maganarku
bace ba."

Sajida tace "Mami maganar mu ce Abba mahaifinmu ne..."

Rigar hannunta ta ajiye tace "Akwai wadda Sufyan yayi wa auren dole a cikinku?"

Suka yi shiru hakan ya sa ta cigaba.

"Akwai wadda a cikinku Sufyan ya raba da mafarkinta? akwai wadda bata son mijinta a cikinku? Wanan
shirun da kuka yi ya nuna min cewa dukaninku auren so kuka yi, auren jindadi da farinciki kuka yi
kowacce kuma tana son mijinta kuma tana zaune lafiya da mijinta. Ba zan iya ce muku komai ba amma
kuyi min wanan alfarmar a matsayinku na ƴa'ƴan Sufyan ku roƙa min shi ya sauwaƙe min aurensa yayi
min fin ƙarfi na zauna da aurensa a kaina tsahon wanan shekarun ,yayi min alƙawarin sakina in na haifa
masa ƴa'ƴa amma bai cika ba,ya rabani da ƴan'uwana ya kuma raba ni da ƴa'ƴana uwa uba ya saka
mahaifina yayi min baki akan aurensa....idan zan zauna ina lissafa muku ba ɗin da Sufyan yayi min zaku
ƙara tsanata ne bana son nayi masa takaba bana so kuma bana fata nayi masa kuje ku saka ya sauwaƙe
min aurensa hakan zai faranta mini raina sosai.

Basu ƙara cewa komai b suka juya sum-sum suka fita daga ɗakin.

You might also like