Matar Habibi Book Complete by Lubna Sufyan - 1.PDF by Sufi - Com.ng
Matar Habibi Book Complete by Lubna Sufyan - 1.PDF by Sufi - Com.ng
# ✨
#WomenOfWords
#09035723778
Littafin nan na kudine akan #1k kacal, zaizo a manhajar Telegram 10/12/2024 In Shaa Allaah,
bayan mun kammala shafukan dandano.
Duka littafin nan sadaukarwa ne ga Marubuciya Aisha Shafi'i, idan kunci karo da littafin nan, kun
nishadantu, kun karu ta kowacce irin fuska, ku rokawa mijinta Isma'il Rahmar Allaah, ku roka
mata sauki da juriyar rashin shi, ku rokawa yarinyarta rayuwa mai albarka. Nagode
MATAR HABIBI
(Free page)
Daya tashi zaune, saurarawa yayi, wai ko kunnuwanshi ne suke son yaudararshi, da gaske
sallame sallah ne yakeji
Ya furta yana janyo wayarshi, ya duba lokaci, karfe biyar da minti goma sha biyu, cikinshi yayi
karar daya tabbata ta yunwa ce tunda daren jiya ba wani abincin kirki yaci ba, sai kuma cikin
nashi ya sakeyin wani sauti, wannan karin na tashin hankali ne, ya kuwa diro daga kan gado
cikin hanzari yana bude kofar dakin shi ya nufi hanyar da zata sadashi da dakin Jamila, ko
tunanin ya zurfafa ba zai iya tuno ranar da Jamila ta makara ba, in ba don ita ba ai da ya
tabbata makota sun sakashi a jerin mazan da ba'a gani a masallaci sallar asuba
"Jamilaa..."
Ya kira bayan ya tura kofar dakin nata, a kwance ya ganta kan darduma, jikinta sanye da hijabi
ruwan toka, ta dunkule jikinta waje daya, alamar da tayi sallah bacci ya dauketa a wajen,
karasawa yayi yana dan bubbugata hadi da sake kiran sunanta
"Jamilaa"
Motsawa tayi da sunan Allaah a bakinta, tayi hamma tana kokarin mikewa
"Wallahi kuwa..."
"Kayya, baccin daya daukeni ne, kasan kuma ba alarm nake sakawa ba tunda na rigada na
saba tashi"
"Allaah Ya kyauta, amman akwai damuwa, saboda ba wani abin kirki naci ba jiya, ga aikin da
yake gabana a shago yau, ni anya ma na tabayin dorere a rayuwata?"
Sai taji zuciyarta tayi mata wani iri, tausayin shi yana neman danneta, sai kwakwalwarta ta
dawo mata da maganar shi
"Nifa ba karamin taimako na kikeyi ba tunda kike tashina, badan ke ba ai in ta matar nan ne sai
dai inyi dorere..."
"Ai shikenan haka Allaah Ya nufa, sai ka samu kaje kayi sallah, lokaci na tafiya, bari in shiga
bayi..."
Ta karasa maganar tana mikewa, tana jin yanda yake binta da kallo, sai bayan ta shiga bayin
kuma tukunna taji karar budewa da rufewar kofar dakin nata, alamar ya fita. Ta danyi mintina
biyu kafin ta fito, saita cire hijabinta ta koma kusa da Nana da take ta bacci, har yanzun kirjinta
yayi mata nauyi. Tun da ta auri Baffa, bai taba gajiyawa wajen nuna sha'awarshi ta auren mace
fiye da guda daya ba, shisa ma ta sakawa ranta salama, duk kuwa da yanda take da zafin kishi.
Wani lokacin bayan tayi masa addu'ar karin yalwar arziki sai taji kamar ta koma tace Allaah
karya bashi da yawa, iya wanda zai ishesu hidimarsu batare da sun takura ba, amman banda
na karin aure.
Wata rana sai taba kanta dariya, lokacin daya fara gini, haka ya daukota akan mashin dinshi
yazo ya nuna mata, ta dinga kallon yanayin tsarin gidan cike da sha'awa, musamman da yake
fada mata za'a dora bene, saboda yanason yayi part biyu
Taji dirar maganar har tsakiyar kanta, amman saita dake ta amsa shi da
"Sai ta zauna a kasan, ni kuma ina sama, ai dai naci arzikin kasancewa uwargida da akasha
gwagwarmaya da ita a bani zabin inda nake so ko?"
Dariyar dai Baffa ya karayi batare da yace mata komai ba. Kuma lokacin daya kammala ginin
kasan, aka fitar da kafar benen akayi dakin da komai, sai suka tashi suka dawo, watanni takwas
kenan, yace mata a nutse yake so saman ma suna ciki ana ginawa, da duk karsashin
dawowarsu sabon gida, harma da kujerun da ya sake mata duk ya rage saboda tana tunanin
kowanne lokaci zai iya rakito aure, amman da taga ko bulo ba'a shigo dashi ba saita fara sakin
jiki. Amman gab da azumi ta fara kula da canzawarshi, shi mutum ne da inya shigo gida to
yakan ajiye wayarshi ne ya zauna ya biyewa yara suyita shiririta.
Kuma itama din akan zauna da ita a taba hirar, amman lokaci daya inya dawo, to yana manne
da waya yana dannawa, sai kayi masa magana nawa baiji ba, hankalinshi yana kan wayar, da
bata damu ba, saida ya fara tashi yana barin dakin in tana nan aka kirashi, tasan yanayin aikin
shi, yana mu'amala da mutane kala-kala, kuma ciki harda mata, sau nawa suke kiranshi a
waya, wata rana ma ba amsawa kawai yakeyi a gabanta ba, a lasifika yake sakawa yayi
maganarshi a nutse. Saita kara ganin wayar bawai da daddare bane kawai, har da asuba. Baffa
da ana idar da sallah zai shigo gida danya koma bacci, amman sai gari ya fara haske ma wani
zubin kafin ya shigo, ko inya shigo din ya wuce dakin shi ya turo harya murza mukulli.
Shi yasa Jamila sanin cewa wata tayi mata kutse cikin rayuwar miji, da ta ganshi rike da wayar
sai taji zuciyarta nayi mata zafi, babu abinda yake dawo mata sai lokacin da yake neman
aurenta, kalamanshi, yanda yake riritata kamar kwai, saita hasaso irin wannan riritar wata take
samu, wani abu daya jima da mutuwa a tsakaninta dashi, amman taji dadi saboda a lokacin
azumi na karatowa, tasawa ranta zata tsaya ta kara kyautata duk ibadunta a cikin watan, sai
tayi addu'a sosai. Kuma hakan ne ya faru, har a sujjadarta rokon Allaah takeyi daya saka mata
salama idan har Baffa nada rabon zama da wata matar bayan ita. Sai gashi ta fara samun sauki
"Allaah Kasa kar mijina ya juyamun baya, Allaah Kasa kar in taba wulakanta a idanuwanshi,
Allaah Kasa kar mutuncina ya zube a idanuwanshi, Allaah Kasa kar matar da zai auro ta cutar
dani koni in cutar da ita, Allaah Ka rabani da kishin da zai zame mun fitina koya hanani zaman
lafiya"
Haka take jerowa tana sake maimaitawa duk sallah, duk wani motsi ma da zatayi, tasan Baffa,
ko tace ta dauka ta gama sanin shi, shekaru bakwai ko tace takwas in za'a hada da lokacin da
yake nemanta, ko kadan bata taba hasaso zai kasance cikin irin mazan nan masu kushe
matansu a wajen 'yan matan da suke nema ba, tana can gurfane kullum tana addu'ar karta
wulakanta a idanuwanshi, batayi tunanin hadawa da addu'ar kar ta wulakanta ta sanadinshi ba
sam, tunda akwai wani wulakanci daya wuce ace mijin daya kamata ya kare maka mutuncinka
shine yake zubar maka dashi? Abin yayi mata zafi matuka, kuma inda ma ya tsaya iya abinda
tayi din da zaifi mata, sai gashi kirikiri ya yanko karya a cikin wata mai girma irin Ramadan
"Hmm..."
Ta furta a fili ko yanzun dinma, farkon aurensu ta dauka shine zai dinga tashinsu sallah, da yake
ta saba gidansu har kananun yara ma sai an tashe su da asuba, mazan haka Baba zai tattarasu
su wuce masallaci, to da lokaci yayi take bude ido, ko da bata sallah kuwa saita farka, tun
tanayin luf da ita tana jiranshi harta gane in dai ta biyewa Baffa to zata daina yin sallar asuba a
cikin lokacinta, saita tashe shi shima. Amman wai yau dadin soyayya yasa shi rufe ido yana
zabgawa budurwa karyar cewa wai indan itace da sai dai ya dingayin dorere, budurwar da sai
bayan ta tashe shi, yana zaune ma yana sahur zataji vibration din wayar alamar ta kirashi, ko
taji ringing din wayar idan ya manta bai sata a silent ba.
Shisa ta daukarwa kanta alkawari har azumin ya kare ta daina tashin shi, zata barshi da
budurwar tashi, duk da ba karamin danne zuciyarta tayi ba kafin ta iya kin tayar dashi din, tunda
ita ba sahur takeyi ba, sai dai tasha ruwa, da daddare take cika cikinta. Shikuma Baffa in an kira
sallah ya sha ruwa ya tafi masallaci, koya dawo sai dai ya dan sha kayan ruwa, baya iya sakin
jiki yaci abinci sai ya dawo daga tarawih. To jiyama daya dawo ta hada masa komai, sai waya ta
dauke masa hankali, lokaci zuwa lokaci zaiyi murmushi mai sauti, tun tana danne zuciyarta har
tace masa
"Abincinka yana hucewa fa, daka hakura ka gama ci saika danna wayar"
"Kwashe kawai, ba yunwa nakeji ba yau, naci anjima idan Allaah Ya kaimu"
Haka ta kwashe komai tanajin kamar ta fisge wayar ta kwala da kasa, balle da aka fara jera
masa kira ya kalleta yana fadin
"Akwai gajiya sosai a tare dani, ga kaina na dan yimun ciwo, inaso in samu bacci sosai yau"
Tasan a fakaice so yakeyi yace mata ba sai taje dakinshi ba, tunda yanaso ya sake yayi wayar
shi da budurwa, da wannan takaicin ta kwanta, shine ma abinda ya kara mata karfin gwiwar
komawa daki abinta bayan tayi brush tasha ruwa. Haka tayi nafilarta, tayi addu'o'inta, ta zauna
zuciyarta nata bugawa, tana kuma kasa kunne ko zata juyo motsin Baffa, amman shiru, har aka
kira sallah, saida tayi, tana zaune tana azkar din safe ta juyo takun tafiyarshi, tayi maza ta
kwanta ta jirashi, tana kuma aiwatar da diramar data shirya zatayi.
Tun tana tunane-tunane har bacci ya kwasheta, rigimar Nana ce ta tasheta wajen karfe takwas
da rabi, saita mike gabaki daya, tayi mata wanka, ta shiryata, tukunna ta hada mata shayi ta
zuba mata a kofinta ta bata, ta kama hannunta zuwa dakinsu Asaad, ta lekasu, bacci sukeyi
daga shi har Arif din. Idan akwai abinda take kara godewa Allaah akai shine yanda in dai babu
makaranta sukeyin baccin safe, tana yawanjin iyayen yara na korafin yanda suke tashi da
sanyin safiya idan babu makaranta, amman ita dai Allaah Ya duba mata. Ta gyara musu labulen
dakin, taja hannun Nana suka nufi kitchen, saida ta zaunar da ita akan kujera irin ta katakon
nan a cikin kitchen din tukunna ta hada wanke-wanke.
Ta gama tana goge wajen Baffa ya fito, ya shirya cikin kananun kaya, fuskarshi fayau, yayi kyau
kamar ko da yaushe, zuwa yanzun kuma ta tabbata bawai a idanuwanta bane kawai Baffan
yake da kyau, tunda gashi nan ya haska a idanuwan wata ma
"Sannu da aiki"
"Yawwa Babansu..."
"Mamin yara"
In yanajin nishadi, gaisuwar safen da basuyi ba dazun ita tayi masa ya amsa a sanyaye yana
dorawa da
A jikin doguwar rigarta dinkin bubu ta kara goge hannuwanta da suke da danshi tana fitowa
daga kitchen din
Ta fadi tana rakashi har wajen mashin dinshi, ita ta bude masa gate tunda ba maigadi ne dasu
ba, saida ya fita ta mayar da gate din ta rufe, ta koma ciki.
*
Karfe shida da kwata tagama komai tunda ba wani abu mai wahala tayi ba, doya fa kwai ta
soya, tayi zobo, tana da sauran dafaffen nama, tayi miyar ganye, dan wannan tun safe ma tayi
ta, saita tuka tuwon shinkafa dai-dai cikinsu, kuma ita da wuri take fara aikinta koma meye zata
dafa kuwa, bataso ana shan ruwa tana kitchen sai dai bacin rana, sai su Asaad da Nana da
suke binta, Asaad nata yi mata surutunshi kan abinda batajin ta fahimta gabaki daya, wani
tsohon labarine akan yanda littafinshi ya bace a Islamiyya
Tana kwasar komai zuwa falo, Arif yana nan zaune akan kafet yana kallon MBC3, Baffa kuma
yana kan doguwar kujera a kwance kamar gawa, ko mintina goma baiyi da shigowa ba, sannu
da zuwan da tayi masa ma da kai ya amsa, daga shi har mashin din kamar zasu tuntsire,
idanuwan nan sun shige ciki, yayi zuru-zuru, ko dasu Nana suka dinga masa oyoyo ma dan
rikesu yayi kadan batare da yace komai ba
"Barni a kwancen nan, ki dai cikamun jug da koma menene kikayi mana na sha dan Allaah, ki
matsomun dashi kusa, ki kuma zubamun abinci, yau inaga a gida zanyi Magriba"
Saida dariya ta kwace mata, tun asali daman Baffa bashi da jumurin yunwa, dan azumi daga
Ramadan, sitta shawwal sai kuma na arfa yakeyi, bayansu baya karayin wani azumi
Dakinta ta shige bayan tasa su Asaad da Nana sun zauna kusa da Arif, ta dauro alwala tukunna
ta fito, bata biyewa Baffa ba, ta samu kofi madaidaici, ta zuba masa zobo, sannan ta hada masa
doyar ma a plate. Ya kuwa tashi zaune yana karbar kofin
Kafin ta amsa sukaji kiran sallar kuwa, nan da nan ya kwankwade zobon hannun shi, jikinshi har
rawa yake lokacin daya sauke kofin ya dirarwa doyar
"Baba kaci a hankali, babu kyau cin abinci da sauri ko Mami?"
Asaad ya fadi
Dariyar dai suka sake bawa Jamila, ta tashi ta tafi dan ta gabatar da sallar magriba yanda zatayi
buda bakin cikin natsuwa. Sanda ta dawo a kwance ta samu Baffa
"Kwanciya ka sakeyi?"
"Cikina ke juyamun"
Wani abu na rashin jin dadi ya tsarga mata, cike da tausayawa take ta jera masa sannu, doyar
ma data dorawa buri saita kasa ci da yawa, ta dai zubawa yaran, zobo daman kowa na da robar
shi da take zuba musu saboda a kofi za'a iya zubarwa a sakata aiki. Itafa ba haka taso ba,
kawai dai taso ya dan sha wahala ne kadan, azumin ya gasa shi, bawai yayi ciwo ba. Sai gashi
sallar Magriba a gida yayita, ya samu ya lallaba Isha'i saboda Tarawih. Daya dawo yasa ta zuba
masa tuwo, saita tashi dansu Asaad da wuri suke kwanciya, kuma saita tsaya tana biya musu
addu'ar bacci suna maimaitawa duk da sun haddace, ta karayi musu wata tukunna, ta goya
Nana, dan itace take hirar dare wani lokacin
Sanda ta koma falon Baffa ta samu rike da wayarshi, da alama ranshi a bace yake, tana zama
yana mikewa ya nufi dakinshi, tana juyo yanda ya turo kofar garam kamar itace ta bata masa rai
"Allaah Ya kyauta..."
Jamila ta fadi, ta sauko Nana, ta janyo kulolin gabanta, a cikin kwanon da yaci tuwon ta zuba
itama, tana ci tana bawa Nana itama, suka gama ta sake goya Nana dan tanaso ta kimtsa
wajen kafin su kwanta. Kuma hasashenta ya zama gaskiya, ran Baffa a bace yake. Gabaki daya
yau tunda ya fita shago komai ya rincabe masa, ya samu yaran shagon nashi sunata aiki,
danma sun rufe karbar dinkin sallah tun saura sati biyu azumi, kuma shi yayiwa kanshi alkawari
tuntuni, duk runtsi ba zai dinga kwana a shago yana dinki ba. Suna cikin aikin aka dauke wuta,
tun jiya Gen dinsu yaketa wata qara, yau ma sai yaki tashi, daya kira Sani dan yazo ya duba
musu sai yace masa sunje wata gaisuwa baya ma cikin garin Kano, sai yammaci, zaizo ya duba
bayan shan ruwa, dan haka dole yayi abinda bayaso, aiki da keken dinki wanda bana wuta ba.
Zuwa la'asar duk ya zazzage dan abinda yayi saura a cikinshi, ga ciwon cinyoyi da yakeji duk
sun rike, kwata-kwata baima samu natsuwar danna waya ba, yama manta a silent ya sakata har
sai bayan ya dawo daha Tarawih din nan, sai abin ya fado masa, ya riga yasan dole zai sha
mita wajen Aziza. Yana duba wayar kuwa ya samu ta kirashi babu adadi, ga sakonni ta text da
WhatsApp ta bar masa har yana rasa ta inda zai fara karantasu, sai kawai ya fara da tura mata
da gajeran sako
"Ayimun hakuri Babe, yau abubuwane suka rincabemun a shago, wayar kuma tana silent. Nayi
missing dinki da yawa"
Saida ya tura ya fara bin nata sakonnin, sai kuma zuciyarshi ta buga daya tuna yau yayi mata
alkawarin zuwa yayi buda baki a wajenta, tun kwanaki biyar da suka wuce sukayi wannan
tsarin, ya tabbata ta shirya masa shagali, lokaci daya yaji ranshi ya baci, musamman ma da ta
dawo masa da sakon daya tura da
"Ka kusa? Inata jiranka tun dazun. Gashi har tara saura"
Yana shirin kiranta ne Jamila ta shigo, shisa ya tashi ya shiga dakinshi yana addu'ar Allaah
Yasa karta biyo bayanshi, yasan halinta da naci wani zubin
Yake fadi cikin magiya da kwantar da kai saboda yanda Aziza ta birkice masa, kamar ma kuka
takeyi
"Ni ba sai kaci anan ba, kazo ka dauka kawai dan bansan yanda zanyi da abubuwan nan dana
shirya maka ba"
"Na fada miki da zazzabi na dawo, yanzun haka ina cikin bargo a kwance, dan Allaah kiyi
hakuri, ki sakamun komai a firij, na miki alkawari gobe In Shaa Allaah zanzo da wuri ma"
"Hmmm..."
Gabaki daya a gajiye yake jinshi, bayajin ma yana da cikakke karfin fita da mashin din daya riga
ya shigo dashi, balle harya falla unguwarsu Aziza
"Ke kinsan babu yanda za'ayi haka kawai da gangan inyi missing din abubuwan da nasan kin
shiryamun, kinsan yaushe rabon da inji wani abu mai dadi a bakina?"
"Habibi saboda zuwanka fa nace yau 'yan gidama suci albarkacinka nayi tortilla da sauce din
kwai"
Duk da in za'a tsire shi baisan meye tortilla din ba, amman yanda ta fade shi tanayi kamar zata
taune harshenta yasa Baffa hasaso wani abu da yaji naman kaza a cikin kanshi, ga kuma kwai
data kira
Bai sauke wayar ba saida ya tabbata Aziza ta hakura, musamman daya fara dauko mata hirar
daya kula tafi faranta mata rai akan komai, hirar yanda in ta shigo gidanshi zata wanke masa
takaicin rashin iya girkin Jamila, za kuma ta zame masa fitilar daya jima yana nema, a takaice
dai, Baffa yace mata
"Kina saka inaji kamar sai yanzun zanyi aure Aziza, kamar banma san iya abubuwan da na rasa
ba sai yanzun da kika shigo rayuwata..."
✨
Kun shiryawa wannan tafiyar kuwa?
#LubnaSufyan
#WomenOfWords
#09035723778
Littafin nan na kudine akan #1k kacal, zaizo a manhajar Telegram 10/12/2024 In Shaa Allaah,
bayan mun kammala shafukan dandano.
9035723778
Opay
Lubabatu Sufyan
Saika turo shaidar biya ta lambar da take sama. Nagode da addu'a'inku, nagode kuma da
kwarin gwiwar da bakwa gajiya da bani
Duka littafin nan sadaukarwa ne ga Marubuciya Aisha Shafi'i, idan kunci karo da littafin nan, kun
nishadantu, kun karu ta kowacce irin fuska, ku rokawa mijinta Isma'il Rahmar Allaah, ku roka
mata sauki da juriyar rashin shi, ku rokawa yarinyarta rayuwa mai albarka. Nagode
MATAR HABIBI
2
(Free page)
"Nifa naji wani Malami na wa'azi in dai har sallar dare zatasa ka makara gara ka hakura da ita"
"Babansu ai ana maganar sallar asuba ne, yau kuma bamu makara ba yanzun ma ake shirin
tayarwa"
A hasale ya amsa ta da
"Amman ai mun makara sahur ko? Kinsan irin wahalar da na sha jiya kuwa Jamila? Gaskiya
kisa alarm a wayarki yau"
Kamar ba zai tafi ba sai kuma ya wuce, ta tabe baki, jiya bayan ta kwantar da Nana tayi mata
addu'a sosai, da batayi niyyar zuwa dakinshi bama, sai kuma ta sake kayan jikinta zuwa
doguwar rigar bacci da ta wuce har kwaurinta, ta kara goga humra, ta nemi hula ta saka a kanta
sannan ta tafi, a kwance ta sameshi yana danna waya, da yake wutar dakin a kunne take saita
kashe, tabi hasken wayarshi har zuwa kan gadon, kafin ma ta gyara kwanciyarta yace
Maganar tayi mata bambarakwai, a lokaci daya kuma wani abu yazo yayi mata tsaye a
makoshi, tasan shi din ba wani mabukaci bane ta wannan fannin, saboda kaso tamanin cikin
dari na lokutta itace take binshi, kuma tasan tana iya kokarinta wajen yin gyara, shi ba
ma'abocin bada kudi bane ba, sai ayi watanni kyautar kudi bata gifta a tsakaninsu ba, ko roka
tayi kuwa bako da yaushe yake bata ba, saima kaji yana mitar
"Kin cika kashe kudi Jamila, meye zaki siya da baki dashi a gida?"
Amman kyautar da 'yan uwanta suke mata lokaci zuwa lokaci tunda sun san ba sana'a takeyi
ba, a ciki take dauka tana siyan magungunan mata, maganin sanyi kam wannan baya yanke
mata sam ko dan yanda ake kara jaddada amfanin yawan shanshi ga mace ko da bata da aure
balle kuma mai aure. Da kanta a WhatsApp ta fice daga cikin groups da dama na matan aure
saboda yanda in an samu wata mai maganin matan, suka siya aka gwada za'azo ayita sharhi,
kaji wasu suna bada labarin yanda miji ya manne musu, wata ma zatace
"Nifa da niyyar kwana biyu yazo, amman kinganshi nan yana maganar ya kamata ace wannan
komawar dani ya koma"
To ita kuwa duk wani doki da rawar kai a wannan harkar Baffa yayi mata itane a cikin watanni
ukunsu na farkon aure kafin ta fara laulayin cikin Arif da yazo mata da zafi, daga baya kuma sai
taga kamar abin koya fita daga ranshine, yanayin wannan hirar da take gani tsakanin mata, ita
kuma inta siya tayi amfani dashi sai taga dai babu wani canji ta bangaren Baffa, saima ita da
wasu magungunan zata ga kyansu, wasu kuma inta sha idan sun cika bauri ta wuni cikinta na
murdawa. Sai kuma takeji kamar ta daina burgeshi yanzun, wannan soyayyar duk ta disashe.
Amman duk da haka kai tsaye bai taba bude baki ya fada mata magana mai zafin ta yau ba.
Idan ma gajiyar yayi to zai kyaleta ne ta shige jikinshi sosai ta kwanta.
Yanda gwiwoyinta sukayi mata sanyi yasa ta kasa tashi tabar masa dakin, zuciyarta ta dinga
mata zafi, musmaman ma data ga ya juya kwanciyar shi yana matsawa ya bada tazara a
tsakaninsu. Ta rufe idanuwanta da sukeyi mata yaji-yaji, bata kasance cikin mata masu saurin
kuka ba, asalima abinda zai saka hawayenta zuba ba karami bane ba, ta dinga jero duk wata
addu'a da tazo bakinta ko zata samu saukin zafin da kirjinta yakeyi, ashe bacci ne ya dauketa a
haka, bata sani ba sai data fitsari ya tasheta tunda ta daddaki zobon da tayi babu laifi. Bataga
alamar Baffa a kusa da ita ba, saita dauka ya shiga bayi, shisa ta nufi kofa ta bude da nufin
tafiya dakinta, kuma har zata wuce saita dinga juyo karar kiran wayarshi daga falo.
Da mamaki ta nufi falon, yana kwance kan doguwar kujera yana bacci, ga wayar nan a kasa da
alama subuce masa tayi bai sani ba, daman Baffa da bacci, sau nawa ko kiranshi akayi ita kiran
saiya tasheta shi yana baccinshi. Ta karasa ta dauki wayar, sai dai tana dauka kiran na
yankewa, zata ajiye masa a gefenshi sako ya shigo, kuma da yake ko a mukulli take zaka iya
karanta sakon ta saman inka dan taba, haka kawai taji tanaso ta karanta, anyi saving din
lambar da "AZ" kawai.
"Habibi bacci kayi ko? To bari in tashi inyi sallah in rokar mana Allaah Yasa next azumi kana
gefena zakayi baccin nan"
Wani duhu-duhu ya nemi rufe mata ido, musamman da wani sakon ya kara shigowa
"Ina sonka sosai. Allaah Ya kulamun da kai Habibi Na, sai anjima In Shaa Allaah dan yau gara
na kwana a zaune da in bari kayi dorere"
Daman haka kishin yake? Duk wanda take zato tanaji a baya karya ne, yanzun ne tasan yanda
yake. To taya mata suke iya danne shi? Ya suke kallon mijinsu ya ketare ya tafi dakin wata
matar batare da zuciyarsu ta kama da wuta ta kone ba? Ita gata, sako kawai tagani amman
zuciyarta kamar tana gab da zama toka saboda yanda takejin tana ci da wuta. Sai gashi tanajin
alamar hawaye suna neman zubo mata, ta ajiye masa wayarshi inda ta ganta a kasa, ta wuce
dakinta da kudiri daya. In Shaa Allaah har a karasa azumi nan da kwanaki bakwai ko takwas ta
gama tashin shi Sahur, ita AZ din saita tashe shi kafin azumi na gaba din da zasuyi tare saita
dora daga inda ta tsaya a wannan din.
Yau ko dar bataji bama, dan daya shigo dakinta bankan-bankan lokacin ma da hijabinta a hannu
"Kasan goman karshen nan, sallah jima inayi, sai na dan kishingida sai yanzun na tashi naji
anata kiraye-kirayen sallah, to alwala nayi ma yanzun nake shirin zuwa in tasheka"
Taji ranta yayi mata sanyi-sanyi ganin nashi ran a bace, a nutse tayi sallarta ta idar tana zaman
Azkar. Tana idarwa ta koma tayi kwanciyarta.
Wajen Azahar tana zaune tana firar dankali, Nana kuma ta gama kukan faduwar da tayi da
keken Arif ta buge bakinta har saida yayi jini, shine ta samu take baccin wahala, tayi mata
shimfida anan tsakar gidan. Da yake gidan inka shigo gate, akwai wata yar haraba da har mota
ma za'a iya parking dinta kuma a samu waje, sai ka kara shigowa wata kofa da zata hadaka da
cikin gidan, daka shigo kofar akwai dan filin tsakar gida da ba wani girma ne dashi ba, daga
gefe kitchen ne wadatacce anyi masa kanta mai kyau daga ciki, da yake itama ba wani tarkace
ne da ita ba sai tsarin kitchen din yayi kyau. Akwai karamin bandaki a tsakar gidan, sai kuma
wata kofa da inka shiga itace zata sadaka da falon Jamila, a cikin falon akwai daki daga hannun
dama, inda ta mayar dashi dakin yaran, sai kuma daga hannun haggu dan dogon corridor ne da
zai sadaka da dakuna guda biyu da suke kallon juna, daya na Jamila, dayan kuma na Baffa,
kowanne daki kuma da bayi a ciki.
Tsarin gidan yayi kyau, dai-dai na masu rufin asiri. Sai dai yanda Baffa yake gaya mata tsarin
saman ne yasa taji son wajen ya kara kamata, tunda yace a falon har wajen dining za'a fitar,
sannan kuma kitchen a ciki za'ayi shi shima, ba kamar na kasan da yake a waje ba. Irin dai
tsarin gidajen 'yan gayu. Abinda kawai take so da kasan shine tsakar gida, dan ita tanaso ta fito
taga sararin samaniya lokaci zuwa lokaci, bawai kullum kana cikin daki ba. Har mamakin irin
gidajen da basu da tsakar gida kwata-kwata takeyi.
Asaad ya fadi cike da kosawa, tayi 'yar dariya. Shi Arif in dai akwai kallo tofa bashi da lokacin
komai tunda yarone marar hayaniya, komai nashi da sanyi-sanyi yakeyi. Asaad kuwa irin yaran
nan ne masu kulafacin uwa. Baiki duk inda tasa kafarta ya mayar da tashi ba, gashi da son aiki,
shisa bata rasa abinda zata bashi ya tayata ko danma ya zauna waje daya
"Duka zaka tsince dan albarka, kayi maza kagama in baka ka dakamun maggi"
Aikuwa saiya kara maida hankali, dan yanason ta bashi dakan abu a karamin turminta,
kwankwasa gidan da akayi yasa ta ajiye firar dankalin taje ta bude, tun daga kofar suka fara
gaisawa da Rufaida. Wata mata guda daya da tun ranar da suka dawo unguwar suka fara
mutunci saboda kirkinta, itama tace basu fi shekara biyu da dawowa unguwar ba, tana da
yaranta hudu
"Dan Allaah ki taimako mun da flavor in kina da milk zansa a kunun aya, ragowar Intee ta
mungular mun dashi"
"Allaah Ya shirya mana yaran nan, gashi kai ba abin ka jibgi kudinka ba"
Daki Jamila ta shiga tana barin Rufaida da Asaad da yake gaishe da ita, tunda dan karamin firij
din nata a falo yake, data ajiye shi nan tsakar gida rana ta hanashi abin kirki, a kitchen kuma ya
cike mata waje, saita mayar dashi falo tayi masa waje tunda falon wadatacce ne. Data fito ta
kawo mata ne take ce mata
"Kinga wata gumba ce aka kawomun naji dadinta wallahi, kin aiko Arif ya karbar miki na manta
dana fito miki da ita"
"Wannan gumbar yanda kikasan kina shan madara da kantu haka zakijita, kefa mazan yanzun
saida gyara"
Yanayin fuskar Jamila dai inka gani kasan yau zancen bai zauna mata ba sam, saima yake tuno
mata da wulakancin da Baffa yayi mata jiya
"Allaah Ya shiryaki wallahi, to ke ina ruwanki da karo aurenshi? Daman ai bawai zaki gyara
bane dan karya karo aure, a'a taki mafitar zaki duba, ki gyara dan ki samu naki matsayin a
wajen shi, in kika tsaya wallahi 'yan matan nan na yanzun da suke da ido a tsakar kai sai su sa
kwabarki tayi ruwa"
Dan jim Jamila tayi tana tauna maganganun Rufaida din, wata irin shakuwa ce ta shiga
tsakaninsu kamar sunyi shekaru tare, dan Jamila zatace ita dai a yanzun bata da kawa kamar
Rufaida, kuma sukan tattauna matsalolin da ba'a rasa duk wata mace dashi, musamman ta
maza, su ba juna shawara
"Hmmm..."
Jamila ta iya fadi, kuma yanayinta yasa Rufaida ta fahimci cewa tana da damuwar da bataso ta
fito fili ta fadi
"Karki yarda ki bar mijinki a hannun wata, musamman ma yarinyar da duk wani feleqe da takeyi
kokarinta ta taddoki ne, kibari inta shigo sai kiyi lokacinta, amman yanzun kam ki kara rike
mijinki"
Haka Rufaida ta dinga bata shawarwari kala-kala har saida taga tana aminta da maganganunta,
ta kuma kira Arif tace ya bita ya karbo mata gumbar. Rufaida na fita bata jima ba, dan dawowar
Arif kenan shima ya ruga daki dan ya cigaba da kallon shi, taji wayarta na ringing, ta dauka
tunda tana nan ajiye a kusa da ita. Baffa ne, ta daga tasa a kunne hadi dayin sallama
"Mamin yara"
Ya fadi daga dayan bangaren yanasa tayi murmushi, kafin kuma ta amsa ya dora da
"Daman zanji ya kuka wuni ne? Ina yaran? Kinata aiki halan?"
Sai taji wani sanyi ya ratsa zuciyarta, akace abubuwan da mata suke so daga wajen mazajensu
ba masu yawa bane ba, kulawa komin kankantarta na daga cikin wannan abubuwan, ta manta
rabon da haka kawai Baffa ya kirata a waya. In kuwa ya kira to sako zai bata, ayi masa wani
abin, ko ita ta kirashi suna bukatar wani abu, da takan kira inya tafi dan taji ya ya isa shagon sai
yace mata
"Daman shikenan abinda zaki fada? Kai kema dai kina da rigima, sai kace wanda zai bace a
hanya"
Irin wannan sage gwiwar da yakeyi mata kan abubuwa da yawa yasa ta hakura ta yakicewa
kanta yi masa su tunda basa burgeshi. Ko kuma ita dince ta daina burgeshi ba zata iya cewa ba
"Bama aikin da nakeyi, dankali ne nake ferewa"
"Akwai fa, kasan shi saurin lalacewa yakeyi, kuma azumin ma yazo gangara"
Tunda ita dankalinma baya cikin abubuwan da suke burgeta, saita soya shi sau nawa bataci ba
"To shikenan, kinga dinkunan nan da yawa, daman ince miki karki wahalar da kanki yau ba zan
dawo gida da wuri ba, mun nemi wani abin muci anan. Kiyi abinci mai sauki kawai na sahur"
Dariya yayi
Dariyar ya sakeyi
"Kafarki ce take kaikayi daman, Allaah Ya tsare, ki dauki dubu biyu a dakina inda nake ajiye
kudi saikiyi kudin mota..."
Ta jinjina kai, saida tasa hannu tana share wata yar kwallar farin ciki, yaushe rabon data jita
cikin nishadi haka? Yaushe rabon da Baffa ya biye mata suyi hira cike da kulawa irin wannan?
Harta manta, waya kuwa ko history ta duba na shekara daya basuyi wayar data wuce yan
sakanni ba dashi, tunda yana gama fadar abinda zai fada yake kashewa batare ma daya jira
tace wani abu ba, hira kuwa tunda ya gane mayi da 'yan matanshi inya dawo ta yanke a
tsakaninsu, saita kirga magana nawa take hadasu inya dawo gidan kafin su kwanta.
Tace tana tsame hannunta daga cikin dankalik ta tafi ta dibo cefane ta hau gyarawa, bayan ta
wankesu, ta dauko wani kwali da busashen kifi yake a ciki, Yayanta Kabiru ne ya kawo musu
tsarabar shi daga Jos inda yake aiki, da yawa ta diba ta zuba a wata tukunya ta yanka albasa ta
zuba citta da tafarnuwa, dan Allaah Yayita da jin karni matuqa, in zatayi amfani da kifin saita
fara tafasa shi haka ta zubar da ruwan, tukunna ta zauna ta gyara shi ta cire kan da kaya. Cikin
wani lokaci sai gashi ta gama miyarta mai yawa. Yau kam yanda ya faranta mata rai, itama saita
faranta mishi.
Zata bashi mamaki, kayan buda baki zataje ta kai masa har shago, yaran shagon nashi ma sai
bakinsu ya canza yau, ba zata bari yanda baiyi sahur ba, yayi buda baki a wahale. Shinkafa da
miyar kifin zatayi, ta soya dankalin da wainar kwai, sai ta hada musu lemon citta, ta sauko wasu
kulolinta da bata taba amfani dasu ba, a ciki zata shirya komai, haka wasu filet dinta masu kyau
ta dauraye, ta fiddo robobin da taketa boyo don irin haka, Rufaida ce ta bata su guda goma,
design dinsu yayi kyau matuka, shisa ma ta adana, yau ga ranar amfani dasu tazo,
shawarwarin Rufaida na dazun suka dinga mata shawagi
Haka kawai da zata biyewa zuciyarta da bakin kishi taje ta illata mijinta, a yanzun dai in wani
abin ya same shi ai ita da yaranta sune da asara ba AZ din ba
Sai dai a lokacin da Jamila take aikinta cike da nishadi da son farantawa Baffa
Haka a gefe daya Baffa yake cikin nishadi da dokin ganin Magriba tayi dan yaje yaga abinda
✨
Aziza take ta fadin ta tanadar masa...!
#LubnaSufyan
#WomenOfWords
#09035723778
Littafin nan na kudine akan #1k kacal, zaizo a manhajar Telegram 10/12/2024 In Shaa Allaah,
bayan mun kammala shafukan dandano.
9035723778
Opay
Lubabatu Sufyan
Saika turo shaidar biya ta lambar da take sama. Nagode da addu'a'inku, nagode kuma da
kwarin gwiwar da bakwa gajiya da bani
Duka littafin nan sadaukarwa ne ga Marubuciya Aisha Shafi'i, idan kunci karo da littafin nan, kun
nishadantu, kun karu ta kowacce irin fuska, ku rokawa mijinta Isma'il Rahmar Allaah, ku roka
mata sauki da juriyar rashin shi, ku rokawa yarinyarta rayuwa mai albarka. Nagode
********************** **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
************************* **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery,
Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko
kuma post.
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafinmu ku yi search na AI
HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
********************** **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** **************************
MATAR HABIBI
3
(Free page)
Wannan shagon na yanzun, guda biyu ne ya siya, da 'yar karamar plaza ce, akace mai ita ya
rasu, to cikin yaran bayan an raba gado sai wasu suka siyar da nasu kason, wajene mai kyau,
kuma a bakin hanya. Bayan ya siya a hankali saiya rushe katangar data raba shagunan, aiki
yayi masa sosai, kusan duk wani tari daya dingayi da nufin siyan mota a wajen gyaran shagon
suka tafi. Aka fadada shi, akayi musu dan karamin bandaki a ciki, saboda yaran shagon nashi
idan aiki ya kacame musu, sukan kwana, da yake Baffa mutum ne mai tsantsani, bayason
amfani da bandakunan plaza din sam.
Har yar doguwar kujera aka saka a cikin shagon daga gefe. Da shigar kananun kaya ya fito
daga gida, sai kawai cikin yaran shagon nashi, Isma'il da yanzun zaice ma yana neman finshi
kwarewa a harkar dinkin nasu na maza, gashi shi harda na mata ma yakeyi, ya dauko masa
yadin daya manta ya siye shi yana fadin
Ya karba, yadine ruwan toka mai duhu, irin masu laushin nan, ba wani abu akayi a jikin dinkin
ba, amman yayi kyau matuqa, hannun dogo mai links, sai maballai a jiki, yasha guga, sai
kamshin turaren sa Isma'il din yake amfani dasu a jikin duk wani kaya da zai dinka sukeyi, sai
yaji ai wannan kayan sune ma yakamata ace ya saka anjima in zaije wajen Aziza. Haka kuwa
akayi, yana ganin shida tayi ya shiga bandakin nan, yayi amfani da soso da sabulun da suke
dashi ya kara wanke kafafuwanshi da babu abinda sukayi, har fuska ya wanke, inda ace shi din
ba kumama bane ba wanka zai karayi, to komin zafin da akeyi saiya sirka ruwa yake iya wanka.
Haka ya dauki mai da yake ajiye a saman wata yar shelf din katako da akayi, ya murza a
hannuwanshi da kuma kafafuwa, sauran ya murza fuska, ya daura alwala, tukunna ya dauki
kayan ya saka a cikin bayin
Yana fitowa ana fara kiran sallar magriba, Usman ya mika masa ruwa mai sanyi da dabino, yayi
Bismillah ya fara cin dabinon tukunna yasha ruwan
"Oga Allaah dai yasa ba zance zakaje ba, irin wannan shan wanka da magribar nan"
"Da gaskiyarshi fa Oga, ba zamu bari a hada baki damu ayiwa Maman Arif haka ba, kai Isma'il
kaine kayi dinkin nan, kamar a kunnenta"
Dariya Isma'il yayi yana daga hannuwa sama alamar saranda
A tare suka hada baki suka amsa, ciki kuwa harda Abbati da bai cika magana ba, dan shi saida
ya dora da
"Nan Madam take shaqaro kuloli da abinci ana aiko mana, so kakeyi a janye mana tallafi?"
Suma sallar suka wuce bayan sun rufe shagon, da yake akwai masallaci a nan gefensu. Ana
idarwa Baffa ya fadawa Usman akwai inda zashi, in dai wani abin ya taso sai su kirashi a waya,
ya dauki mashin dinshi bayan ya turawa Aziza sakon cewa yana hanya, sai lokacin ma ya kula
da cajin wayarshi saura 2%. Tunda yaje shago da safe bai sakata a caji ba, daman kuma jiyama
haka bacci ya dauke shi da dare suna chatting da Aziza bayan wayar da suka sha, wayar da
itace ma tasa shi ya barowa Jamila dakin nashi ya dawo falo. Addu'a yakeyi kar wani ya kirashi
wayar ta mutu kafin ya karasa, dan bayason saiya nemi wanda zai aika a kira masa Aziza, gara
dai ya kirata a waya.
A ranshi ya dinga zabga tsaki, shifa abinda ya tsana da unguwar nan ta Rijiyar Lemo kenan,
musamman wannan layin 'yan chanan, kamar babu layin daya kaishi yawan kwatoci, jiyan nan
ya bada aka wanke masa mashin dinshi tas, wani lokacin har mamakin yanda za'ace yarinya
kamar Aziza tana irin wannan unguwar yakeyi. Ko a cikin layin nasu ma gidansu ne kadai mai
katoton gate. Sai dai bayan ya karasa, ya samu waje a gefe yayi parking din mashin dinshi yana
kara kallon unguwar tasu, cike da mutane anata hada-hada, ga masu awara nan da dankali
waje-waje, an zagaye su layi danqam. Baiyi mintina uku ba Aziza ta fito, kamshin da take
zabgawa ya wanke masa duk wani takaicin bata mashin dinshi da yayi.
Daya kalleta kuwa saida ya tsinci kanshi da rokon Allaah daya hore masa halin karasa gininshi
ko zai samu ya mallaki Aziza kafin wani yazo yayi masa shigar sauri, bakinta daya sha jambaki
ja ya kara fito masa da hasken fatarta tar da kwan lantarki ya haske masa kamar don shi aka
bar wuta
"Kinyi kyau"
Ya fadi yana mata murmushi, ta danyi far da ido kafin ta saukesu cikin kunya
Yanayin yanda tayi maganar yaji duk ya susuce, shifa wannan abubuwan, yanayin yanda take
lankwasa murya in zatayi magana, 'yar shagwabar da takeyi masa, kwarkwasar nan, sai yaita
kallon Jamila yana tunanin yanda akayi tun farko bai taba kula bata da wannan abubuwan ba,
ya dinga zurfafa tunani, daman ko lokacin kafin suyi aure haka take? Ko kuma daga bayane ta
canza tunda tanajin aita same shi bata bukatar ta dinga yi masa irin wannan abubuwan
Cewar Aziza, bai kuma yi mata musu ba, yau ma kamar duk zuwan da zaiyi, ya shiga tunanin
yanda za'ayi a shiga da mota gidan nasu Aziza. Inka shiga karamar kofar jikin gate din, baifi
kayi taku hudu ba zaka samu katanga data raba gate din da cikin gidan nasu, sai kuma wata
kofa da ba'a sakawa kyaure bama, nan zaka shiga, wani dan surkukin soro ne da su biyu ma in
suka tsaya shi da Aziza a ciki tsaf yan hisba zasu samu sabon case, sai dai suji ana tambayar
lambar wayar iyayensu, don da wahala jikinsu ba zai gogi na juna ba saboda kankantar shi, a
gefe kofa ce da take a rufe, bai taba ganinta a bude ba, sai kuma dayar kofar da zata sadaka da
wadataccen falon da suke zama suna zance a ciki.
Aziza ce a gaba yana biye da ita, tun daga bakin kofar kamshin turaren wuta yayi masa sallama
kamar ya shiga Maiduguri. Yaji wani sanyi na ratsa shi, kasala da gajiya duk suka rufar masa,
suna kara tuna masa da ya kamata shima yasa AC a gidanshi, ko da iya dakinshi ne kuwa. Ya
zauna a daya daga cikin kujerun dakin da sallama a bakinshi yana ba Aziza dariya duk da ta
amsa, ta dora da
Ya sauke numfashi yana amsawa, hankalin shi yana kan kwanonin da aka shirya a tsakar dakin,
bawai abinda ke ciki yake hasashe ba, kwanonin ne sukayi masa kyau matuka, dan bai taba
ganin irinsu ba. Aziza ta sauko ta fara budewa, kamshi ya cika hancin shi, saida ta mike ta
dauko wata darduma mai kyau, tukunna ta shimfida masa tana fadin
Saukowar yayi ya zauna, yana kallon fararen yatsunta da jan lalle a jikin faratan, yayi saurin
maida idanuwanshi kan farantin yana jan Istigfari saboda tunanin da yake neman kutso masa
cikin kai
"Kice mun ba wahalar da kanki kikayi ba kika sake shirya wani abin, ai nace jiya ki sakamun a
firij"
Saboda shifa wannan tortilla din data kirane a ranshi har yanzun, so yake kawai yaga daga inda
zata bullo
"Ya zanyi dakai tunda baka zo ba? Kuma kasan Mummy ma zatayi mun fada tace ya za'ayi in
baka abincin jiya"
Ta fara mika masa wani dan karamin kwano da wani abu a cikin narkakke da dan barbadin wani
ganye-ganye a ciki. Ya karba yana kura masa ido na dan sakanni kafin ya duba sauran tarkacen
da take ta kiciniyar dibar masa, shi dai baiga biredi ba, abinda yake hannun shi kuma yayi masa
kama da butter
"Nasanka da son dankali, gashi anci maiko tunda azumi ne shine nace gara inyi maka
mashed..."
Yaji kalmar, kuma yasan turanci ne, a dan abinda yakeji dai ya kasa fassara shi balle hadinshi
da abinda yake hannunshi, ya dai karbi cokalin da ta mika masa ya dibo yana kaiwa bakinshi da
Bismillah, ba don korar shaidan ba, don neman sa'a kar bakinshi ya kunyata shi yaki karbar
wannan abin. Hakan kuwa ya faru, shi dai yaji galmi-galmi, amman baiyi masa yanayi da abinda
zai iya ci ba. A yunwar da yakeji ai gara ma ta bashi kunu akan wannan mashed abin. Gudun
karya bada kanshi ya dinga turawa yana hadiyewa yana rokon Allaah Ya kiyaye shi da bacin
ciki, saboda cikinshi bai cika son bakon abu ba. Har wani numfashi ya sauke lokacin daya ajiye
dan kwanon ta bashi filet
Cewar Aziza tana tashi, yaji dadin bashi wajen da tayi, tana ficewa kan tsiren da yake ciki ya
fara, yayi masa dadi sosai, yaso ace shine yafi komai yawa, sai kuma yaci samosa da spring
rolls, shima sunyi masa fiye ma da tsiren, kamar ya bude sauran kwanonin ya kara haka yakeji,
ya dauki lemon data tsiyaya masa ya kurba, akwai sanyi, amman dai bai gane ma dandanon
lemon ba, yayi masa wani daci-daci saiya ajiye
"Sufa 'yan gayu harshensu ma kamar daban yake dana sauran mutane"
Ya raya ma ranshi, yanata barin abinda yake tunanin yamballs ne daga karshe saboda soyayyar
da take tsakaninsu, idan Jamila tayi wuni yake yana ci, ya kudurce a ranshi zai siyi doya gobe
tunda ta fada masa sauranta ne ta soya musu jiya, ya dan ajiye filet din yana, daya dauka dai
sai yaji shi sakat a hannunshi, gashi da girma, amman baiyi masa nauyi kamar yanda ya sani
ba. Sannan daya kalla da kyau ma, bayan abin kamar ba kwai bane ba, yadai yi kyan suya, sai
kawai ya jefa shi a baki duka yana taunawa. Sai yaji kamar kubewa ce a tsakiyar, gabaki daya
komai da yaci ya nemi dawo masa, ba arziki ya fito dashi daga bakinshi, sai kuma tunanin inda
zai saka shi ya dinga masa yawo, cikin hanzari ya mike kamar zai kifa yana ficewa ya tura
kyauren gidan ya jefa shi ya dawo ya zauna, lemon daya ajiye ya dauka ya kwankwade saboda
zuciyarshi da taketa hargitsawa
Gabaki daya ba haka ya hango yau din ba, sai yakejin inama jiyan yazo, ya tabbata abinda ta
shirya masa jiya yafi na yau nesa ba kusa ba, kawai dai ita din da kuma kwalliyarta ne suka
danne masa rabin disappointment din, sai gata ta dawo dakin da sallamarta tana dorawa da
"Afuwan Habibi, kasan Matar Officer na gidan, yau nan tayi buda baki, nasan yanzun mijinta
zaizo daukarta, akwai ajiyarta a wajena"
Matar Officer kamar yanda Aziza take kiran Yayarta Jalila dashi, daga Jalilar sai ita, tazarar
shekaru biyu ce a tsakaninsu, sai dai Jalilar tayi aure da wuri, dan yanzun haka ma yaranta uku.
Kuma daga yanda Aziza take yawan maganarta, akwai shakuwa mai karfi a tsakaninsu
"Haba ni da kin gama cikamun cikina, ga aiki na baro a shago, anya ma zan iya asham yau?"
Sai tayi dariya ta karasa cikin dakin sosai tana zama a gefenshi
"Baka cinye ba, ga cheese balls dinma baka cinye ba, kuma saboda kai nayi"
Baiyi musu ba, wannan ai mai sauki ne saiya cillar dashi a hanya koya samu wani almajiri ya
bashi. Koma wanne abu dai, hira suka dingayi cikin nishadi. Ana fara kiran sallah yace mata
"An kiramu"
Ta turo baki
Murmushi yayi
"Ni akace na gaji da ganinki ne? Gashi da wahala in sake samun damar zuwa kafin sallah idan
Allaah Ya kaimu"
Aikuwa tayi kwal-kwal da idanuwa har yana hango kyallin hawaye a cikinsu, duk yaji ya susuce
"Wanne video call? Abinda daka shiga gida baka yarda muyi saboda matarka, bayan nima
yanzun ina da hakki akanka tunda ai aurena zakayi..."
Da sauri yace
"Inji wa ya gaya miki saboda ita ne? Nifa na isa da gidana, abinda nake so shi zanyi"
"To me yasa idan na kiraka baka dagawa? Aiko ba zakayi magana ba saika daga in ganka"
Ya jinjina kai
"Zan dauka, shikenan? Dan Allaah ki share hawayen nan bana sonsu"
Duk da haka saida ya kara bata lokaci yana lallashinta da yi mata alkawura kala-kala duk da
yaji an tayar da sallah. Ya ajiye mata dubu goma cifa, sababbin yan dubu-dubu. Yaji dadin
yanda ta manta da hadashi da wannan cheese ball din. Daya fito ne ma sukayi kicibis da Jalila
tana tsaye, bayanta goye da karamin Jawad, sai Jabir da Jafar da suke gefenta, ga wata
katuwar leda data ajiye a gabanta, zuciyar Aziza ta tsinke, kar dai har yanzun Balarabe baizo ya
daukesu ba
Cewar Aziza cikin karfin hali ganin idanuwan Baffa akansu ya fara sauka, ta kalli Jalilan tana
fadin
Duk da Baffa yasan ya girmeta haka ya dan rage tsaho yana gaishe da ita, ta amsa shi fuska a
sake
"Kinga kila ma ciki zan koma, yanzun Officer ya kirani wai kaman ya taka abune tayarshi tayi
faci"
Jalila ta fadi
Jabir ya fadi yana kallonta cikin maganarshi da bakowa bane yake ganewa, Aziza tayi saurin
kallon Baffa da alama baiji abinda akace bama, dan hankalinshi naga masallaci da har anyi
raka'ar farko, tunda da alwalarshi yacewa Aziza
"Bari kiga inyi sallah kafin in wuce, lafiya kalau mashin dina idan na barshi anan?"
Kai ta daga masa da sauri, dan unguwarsu tana da tsaro sosai duk kuwa da yawansu, akwai
karancin sace-sace musamman irin wannan lokacin ma da jama'a suke hada-hada. Baffa na
shigewa tana juyo karar mashin din Balarabe tun daga kan kwanar layinsu kamar babu salansa
a jiki, suka hada ido ita da Jalila cike da takaicin da har yau basu daina shakarshi akan wannan
mashin din nashi ba. Saikuwa gashi nan ya karyo kwanar, kana hango sabon uniform dinshi
shar
Baffa ya taba tambayarta da tace masa tana gidan Jalila din tana kiranta da Matar Officer,
farko-farkon haduwarsu, babu shiri ta katse hirar da fadin
Ta kashe wayar, tunda ai ba zata sharo masa karya ba, idan aurenta zaiyi dole wannan likon zai
cire, ta ina zata fara ce masa Balarabe dan karota ne?. Ko gaisawa bata tsaya sunyi ba, dan
kafin ya karaso ta cewa Jalila
Ta shige gida abinta. Baffa kuwa ana sallar nan kamar an kara zazzage masa hanji haka yakeji,
gashi limamin nan kamar ya zabi yayi tilawa ne a sallar asham din, kafafuwan Baffa har sanyi
sukeyi kafin ayi ruku'u. So kawai yakeyi a idar ya karasa gida ya dirarwa koma menene Jamila
ta tanadar masa, Allaah Yasa tayi zobo, dan yau jinshi yakeyi kamar baisha abinda ya kai masa
✨
inda ya kamata ba.
#LubnaSufyan
#WomenOfWords
#09035723778
Littafin nan na kudine akan #1k kacal, zaizo a manhajar Telegram 10/12/2024 In Shaa Allaah,
bayan mun kammala shafukan dandano.
9035723778
Opay
Lubabatu Sufyan
Saika turo shaidar biya ta lambar da take sama. Nagode da addu'a'inku, nagode kuma da
kwarin gwiwar da bakwa gajiya da bani
*
Duka littafin nan sadaukarwa ne ga Marubuciya Aisha Shafi'i, idan kunci karo da littafin nan, kun
nishadantu, kun karu ta kowacce irin fuska, ku rokawa mijinta Isma'il Rahmar Allaah, ku roka
mata sauki da juriyar rashin shi, ku rokawa yarinyarta rayuwa mai albarka. Nagode
MATAR HABIBI
(Free page)
Adai-daita na ajiyeta, ta dauki katon kwandon data hada komai a ciki, don da taga almajiri ma
shi zata ba ya dauka ya tsallakar mata dashi saita bashi ko Naira dari ne sadaka. Kwandon yayi
mata nauyi, haka ta kinkima saboda wani mai mota daya gansu a tsaye, mata su wajen biyar
saiya daga musu kafa suka samu suka tsallaka, sai nishi takeyi, ta ajiye kwandon a kasa dan ta
numfasa. Ta godewa Allaah da tabarwa Rufaida har Nana. Da yake ba kwiya gareta ba, su
Asaad na dauke mata hankali ta samu ta silalo, ai da taji a jikinta da daukar wannan kwandon.
Yanda Baffa yace ba zai dawo da wurin nan ba, sai kaga har goma ta wuce ma kafin ya shiga
gida, tasan yana son shan ruwan shayi wani zubin, saita hada masa shi yasha kayan kamshi.
Shisa kwandon ya kara nauyi.
Kamar ance ta juya, ta hangi Baffa yana daukar mashin dinshi, sai dai ba kayan daya fita dasu
bane a jikin nashi, yadi ne yanzun, kuma daga inda take taga yayi kyau duk kuwa da bai saka
hula ba. Babu yanda za'ayi ta ware baki ta kwala masa kira, bata kuma fito da wayarta ba.
Hakan yasa ta dauki kwandon, nauyin shi na hanata sauri yanda ya kamata, sai dai kafin ma ta
karasa Baffan ya haye mashin dinshi yayi gaba, tunda baya ya bata ya fice ta dayan bangaren
shisa bai ganta ba
Wata zuciyar ta raya mata, sai tayi tunanin ta karasa shagon taji. Haka kuwa akayi, Abbati ne ya
fara ganinta tunda yana bakin kofar shagon a tsaye da kankana a hannunshi
"Maman Asaad"
"Naganshi ya fita ma yanzun, kar dai gida ya koma, yace mun zaku dade yau a shago saboda
akwai ayyuka"
Sai Baffa ya juya yana kallon Isma'il cikin neman dauki, dan shi karya bata cikin dabi'unshi, ko
da kuwa ta kare kaice, kalamai ma gabaki daya basa yawaita a bakinshi.
Cewar Isma'il shima sarkin maganar yau da alama ya rasa ta cewa, kuma hakan nada nasaba
da yanda Jamila takeyi musu kwarjini. Macece da nagartarta take shimfide akan fuskarta.
Yanayinsu, da kuma yadin jikin Baffa ta hada waje daya a cikin kanta, kwakwalwarta ta dai-daita
mata lissafin. Shisa ya kirata yau kenan? Shisa yayi mata kirki? Saboda zaije zance wajen AZ
dinshi kenan, acan zaiyi buda baki kome? Ita tana can tana kitimillin hada masa, banda ruwa da
dabino bata saka komai a cikinta ba tanata sauri ta fito, ashe tana da rabon ta cika cikin nata taf
da bakin ciki.
"Na bar yara a makota, ga kayan buda baki nan, bari in wuce"
Saboda jikinsu a sanyaye yake su duka, kamar sune suka saka Baffa tafiya zance a ranar yau,
sai suka kasa wani yunkuri har Jamila ta juya, ta tare napep, zuciyarta na wani irin tafasa.
Numfashi kawai take maidawa har suka isa, dari biyar din data bashi ma ca tayi ya rike canjin ta
wuce ta shiga gidan Rufaida, taji dadin samunta ta tayar da sallah dan kwata-kwata bata son
wani dogon surutu, ta sabi Nana tana riketa a hannu ta cewa su Asaad
Bata san ko muryarta bace ko yanayin fuskarta yasa duk suka shiga hankalinsu. Tana zuwa
kofar gida kuwa ta samu Yayarta Yasmin da take tsaye tana danna waya
Yasmin din tayi dariya. Tun haihuwar Yasmin ta biyu, ta kwallafa rai akan idan namiji ne za'a
saka sunan mahaifinta Abubakar, har shafa cikin take tana fadin Assadiqu kamar yanda take da
niyyar kiranshi, ta shiga watan haihuwarta, Kanin mijinta ya rasu, kawai tana haihuwa da yayi
masa huduba, bata kawowa ranta ba Abubakar din ya saka ba, sai ranar suna taji ana
Ta tabbata da ba'a zaune take ba sai jiri ya tikata da kasa, ita tun yana da rai ma ba shiri sukeyi
ba, duk da ance babu kyau tado da halayen mamaci musamman wanda ba nagartattu ba, shi
kam mutum ne mai tsugudidi, sannan ya saka mata ido ainun, duk wani husumi da zai taso
tsakaninta da dangin mijin nata in aka bibiya shi ya kitsa zancen. Kamar mace haka yake da
gutsiri tsoma. Da yake kuwa ranar Juma'a ne ta haihu, saita fara kiran yaron da Danjuma, wani
suna da mijin nata da dangin shi suka tsana saboda sunce akan meye zata boye sunan yaro,
shima mijin da yayi magana sai tace masa
"Ni da nayi dakon wata shida, nayi nishin nakuda ai ayi mun alfarmar kiran yaro da sunan daya
kwantamun ko? Tunda ban hana kowa ya kirashi da sunan da aka rada masa ba"
Haka dole ya hakura ya kyaleta, tunda yasan hali, jan maganar kamar neman zunguro sama da
kara ne tunda har batace masa ta tafasa ba akan sauyin sunan da aka samu. Tun daga lokacin
ta tashi daga Adda Yamin a wajen kannenta ta koma Maman Danjuma, tun suna kiran sunan da
zolaya har yanzun kusan kowa ma haka yake kiranta dashi. Gidan Jamila ta bude suka shiga,
su Arif suka gaishe da ita
"Keni ba zama zanyi ba, Yaya Babangida ne ya hadani da aiki, ga sakonki nan"
Cewar Yasmin tana mika mata ledar data shigo da ita, kafin ta fara kokarin sauke jakar
kafadarta, sai ga wuta sun kawo, daman fitilar caji ce da take dorawa sama, ita ta haske tsakar
gida, saita wuce daki da yara ta kunna musu tv ta dawo, Nana ce kawai ta makale taki sauka.
Kudi ne Yasmin ta mika mata, tasa hannu ta karba
Haka kawai sai taji hawaye ya balle mata, wani irin rauni ya mamaye ta
Da sauri tasa hannu ta goge hawayen, kawai tana hasaso tarin kauna da hadin kan da suke
dashi, yanda ta fahimci ba sai iyayenka nada kudi bane kake kasancewa dangata, ita kam 'yar
gata ce, sun taso cikin tarin kulawa, yanzun gashi aure ya rabota da gidan nasu, ya kuma
sakata yunwar wannan kulawar. Tunda in ba yunwarta da takeyi ba, wayar kasa da mintina biyu
da sukayi da Baffa itace fa tasa ta son faranta masa
Yasmin tayi maganar cikin fada, amman zaka iya tsintar damuwa a kasan muryarta. Saboda
tasan halin Jamila, abinda zaisaka hawayenta zuba ba karami bane ba, akwai kujerun roba
guda hudu, wata cikin wata daga can gefe, Yasmin ta karasa ta dauko guda daya, duk da batayi
niyyar zama ba
"Baffa ne"
"Zance ya tafi"
"Shine kike shararar hawaye sai kace wanda ya nakadawa duka, to in ba daukar kafa ba ke ina
ruwanki da zancen shi?"
"Adda bafa dan ya tafi zancen bane ba, kayan buda baki na shirya masa na tafi na kai saboda
yace mun zai dade bai dawo ba, na samu ya tafi wajenta"
"Da yace miki zai dade sai yace kiyi abinci ki kwashi kafa ki kai masa?"
Ta girgiza kai
Tayi shiru
"Ke yanzun waye yace miki anayi wa maza wannan kankanbar? Ai kina budurwa ne kafin ya
sameki, shine zaki burgeshi da irin wannan iyayin, amman yanzun tunda ba sakaki yayi ba gara
ki rufawa kanki asiri, in ba kina neman ciwon zuciya bane ba"
Fada sosai Yasmin tayi mata kafin ta dora da lallami, ta nuna mata duk taji, ta kuma lallasu,
haka sukayi sallama, ta rakata tana dawowa. Ta duba ledar, lace ne mai kyan gaske sai atamfa
kala biyu, sai kuma shadda da tasan ta Baffa ce. Da yake Yaya Babangidan yanzun kasuwa
nayi dashi, kuma shi din mutum ne mai son hidimtawa dangi, babu ruwanshi da kana dashi,
inya tashi zaiyi maka, su matan har mazajensu yake hadawa. Ta tattara duka ta shige dakinta
dasu ta adana. Kamar yanda Yasmin ta fada mata ne, ita ta kai kanta, babu wanda ya aiketa.
Amman ta kasa daina jin takaicin wai saboda yana so yaje zance ne yau yayi mata kirki.
Tana da hakuri, amman tasan idan bata rama wannan abin da Baffa yayi mata ba, zata jima
dashi a rai. Ta samu tayi sallar isha'i da asham, ta dan zuba abinci kadan taci, tazo ta dauki su
Asaad da sukayi bacci a falo ta kaisu dakinsu, tana tashin kowanne yayi fitsari, tukunna tayi
musu addu'a, Nana da take goye a bayanta itama tayi bacci, taje ta kwantar da ita. Taji ana
kwankwasa gida, wani abu ya taso mata, haka ta sauka taje ta bude masa, ta kuma danne
zuciyarta tayi masa sannu da zuwa
"Kece da sannu ai Mamin yara, ya naji gidan tsit, ko har sunyi bacci"
Data kalle shi, yanda yadin yayi masa kyau bai hanata ganin bakin shi ba, sai takejin kamar
dariyar da yakeyi mata dinma duk ta yaudara ce yau. Shikuma ganin irin kallon da takeyi masa
yasa shi saurin cewa
"Kinganni da yadi ko? Hmm, kwata na fada, Allaah Ya taimaka Isma'il ya dinka mun wannan
yadin, na samu na canza, kayan na can ma shago na manta dasu"
"A'a fa"
Ya fada da sauri
Sai wani guntun murmushin takaici mai sauti ya kwace mata hadi da mamakin yanzun ne Baffa
ya koyi shararo karya haka, ko kuma tunda can ne itace dai bata maida hankali ba.
Ta furta tana wucewa ta shige daki, bata kuma tsaya ko ina ba sai dakinta, ta haye gado, tana
shirin kwanciya ne Baffa ya turo kofa, ta daga kai ta kalle shi
Zuciyarta tayi wani tsallen murna a cikin kirjinta, ta danyi 'yar dariya
"Yau kuma zolayar taka ce ta motsa, wanne abincin kuma Babansu? Banda wanda nasan yau
har makotanku a shago sai sun samu rabonsu"
Ya dan diririce yana juya maganarta, yana juya maganarta, sai yayi dariya shima duk da kuwa
bai gane me take nufi ba
"Ni dai a dawomun da robobin dana zuba zobo dan Allaah"
Jamila ta fadi, zuciyar Baffa ta buga, kar dai abinci ta aika musu dashi shago?
Yace mata yana ficewa daga dakin, zuwa yayi yasa wayar tashi a caji, ya kunnata, ya dan
zauna a wajen yana jira ta gama kawowa, sai ga sakonni, na Aziza, sai kuma Isma'il, da hanzari
ya fara bude na Isma'il din
"Inata kiran wayarka a kashe, yanzun Madam tabar shagon nan, ta kawo mana kayan buda
baki, amman dai munce mata kaje ka dawo"
A fili ya furta
Bayan ya karanta sakon, a yanda yasan Jamila, ya tabbata abinci ne niqi-niqi takai, kuma anan
gida din wanda zata bari ba mai yawa bane ba, tunanin karyar da zaiyi mata ya samu ko da
taliya ce ta dafa masa yakeyi, saboda da gaske yunwa yakeji. Haka ya bar wayar batare daya
ko bude sakonnin Aziza ba, ya sake komawa dakin Jamila ya ganta tana duba drawer din gefen
gado
Ya danyi jim
"Sannu, kuma da zuwa nayi ince a zubamun abinda aka rage, kinsan yan shagon nan,
musamman Isma'il, shiya fita da plate yan shagon Rahusa suka ganshi, nan suka tattaro suka
zo, dan abinda nacin ba mai yawa bane ba, anayi asham duk ya zazzage"
"Aikuwa babu wani abu sai abincin Sahur dinka, shisa na zuba muku shi da yawa daman, ko da
baku kadai zakuci ba, kuma da yake banma zaci yanzun zaka dawo ba"
Ta jinjina masa kai, tana mikewa, acan kitchen din ta zuba masa a filet, ta samu dan karamin
kwano ta zuba masa miyar, tana dan saka masa kifin kadan, duk kuwa da yawan da yake dashi
a cikin miyar, ta daukar masa pure water da kofi, a falo ta same shi zaune, ta ajiye masa komai
a gabanshi
Ya kalli shinkafar
"Bari inje in samu maganin nan in sha in kwanta ko zan samu bacci"
Ta jinjina masa kai kawai tana wucewa batare data amsa ba, haka ya tashi da shinkafar tas,
miyar tayi masa dadi, ya dinga cancana dan kifin da yake ciki kamar karya kare. Ya sha ruwan
yaje ya kwanta, sai lokacin ya dauki wayar shi yana kiran Aziza. Hira sukayi sosai, harda video
call din da yayi mata alkawari, duk da bai bari video call din yayi nisa ba, ko dan dare ne, gashi
ba hijabi ta saka ba, duk da baya ganin komai banda wuyanta sai kuma gashin kanta da yake
kwance luf har akan goshinta,hular data saka ta dan zame baya. Gashi duk ta narke sai
shagwaba takeyi masa, yaji ya fara susucewa, kuma tunda watan azumi ne, yasan bashi da
halin labewa bayan shaidan.
Haka yayi mata sallama yace zai kwanta, kuma kwanciyar yayi, amman cikinshi daya murda ne
ya saka shi tashi babu shiri yayi bandaki, wasa-wasa kafin karfe biyun dare ya shiga bayi yafi
sau takwas, danma Allaah Ya taimake shi cikinshi bai fara ciwo ba, da yazo ya kwanta dai sai
yaji jikinshi yayi laushi matuka, kamar duk yinin ranar baici komai ba, yasan dole ya lallaba
Jamila anjima ko indomie ce ta dafa masa ta soya masa kwai kamar guda biyar yayi sahur
dashi, dakyar ya samu bacci yanata mafarkin abinci
✨
Abinda Baffa bai sani ba shine Jamila bata kwanta da niyyar tashin shi ba...
#LubnaSufyan
#WomenOfWords
#09035723778
Littafin nan na kudine akan #1k kacal, zaizo a manhajar Telegram 10/12/2024 In Shaa Allaah,
bayan mun kammala shafukan dandano.
9035723778
Opay
Lubabatu Sufyan
Saika turo shaidar biya ta lambar da take sama. Nagode da addu'a'inku, nagode kuma da
kwarin gwiwar da bakwa gajiya da bani
Duka littafin nan sadaukarwa ne ga Marubuciya Aisha Shafi'i, idan kunci karo da littafin nan, kun
nishadantu, kun karu ta kowacce irin fuska, ku rokawa mijinta Isma'il Rahmar Allaah, ku roka
mata sauki da juriyar rashin shi, ku rokawa yarinyarta rayuwa mai albarka. Nagode
MATAR HABIBI
Kudin da Baffa ya bata ta kirga bayan tafiyarshi, saita tabe baki, saboda ta raina dubu goma,
kamar yanda ta raina kayan sallar da yayi mata, musamman lace din. Ko Mummy da ta ganshi
saida tace
"Wannan lace din ai karami ne Aziza, ba zai wuce dubu sha biyar ba"
Aikuwa dansu tabbatar haka ta dauki hoton shi ta turawa kawarta da take siyar da kaya tana
tambayarta, ita a wajenta ma dubu sha uku da dari biyar ne
"Inya baki wasu kudin a hankali saiki tarasu ki hada ki dauki babban shi"
Haka Mummy ta bata shawara. Jaka da takalmin dai sunyi mata kyau sosai. Taji sanyi da ba da
Baffa kadai ta dogara ba, sauran samarinta sunyi mata hidima kamar yanda suka saba. Kawai
matsalar zuciyarta ce, itace ta narke akan Baffa, saboda tana tunanin fata da kuma bakin
Mummy ne yake binta, ita take yawan fadar
"Kefa ba matar kananan yara bace ba, In Shaa Allaahu ke din matar babban mutum ce"
Manyan mutanen ne suke binta kuwa, masu kudi, dattijai da suka kusan haifarta dama wanda
suka haifi kamarta sau babu adadi. Tana son rayuwar hutu da jin dadi, amman fa auren tsoho
bai taba burgeta ba komin kudinshi. Duk kuwa yanda take ganin jin dadi shimfide a fuskar
Mummy din idan sun hidimta mata, wani zubin ko don Mummy ta huta sai taji kamar ta duba
wanda suka fi dama-dama a cikin maneman nata, a lokacin ne kuma ta gane da yawansu ba
auren bane ya kawosu. Alhaji Sadisu ne kawai yayi mata maganar aure da kanshi, shikuwa
matanshi uku a yanda ya fada mata, uwargidanshi ta rasu, da ita yake so ya cike ta hudu.
Shikuwa ko bai fada ba ta tabbata ya ba saba'in baya. Ba tajin tarin dukiyar shi zasu lullube
mata shekarun shi. Samarin kuma da suke tareta bata ma bata lokacinta akansu, tunda ta
tabbata ba aurenta zasuyi ba. Baffa shine namiji na farko da yazo wajenta taji ya kwanta mata
har cikin ranta, duk kuwa da taso ace yafi haka kudi, saboda Mummy da ta tabbata Baffan ba
zaiyi mata ba, ya aka kare ma lokacin auren Jalila da Balarabe. Shisa Mummy ta tattara burinta
da fatanta kacokan akanta.
Aziza itace 'ya ta hudu a wajen Marigayi Malam Ayuba da matarshi Rahanatu. Shi din
Bafullatani ne dan asalin garin Adamawa. Neman kudi ya shigo da iyayensu garin Kano, da
kuma rabon suma din arzikinsu yana nan Kanon. Rahanatu kuma 'yar Dawakin tofa ce ta asalin
garin Kano. Haka iyayenta duka 'yan Kano ne. Ta taso cikin gidan yawa, mata hudu, su kuwa
yaran gidan sun bawa talatin baya. Haihuwa ake a gidansu da ta zama gasa, duk da mahaifinsu
ba mai karfi bane ba. Dan 'yana aiki ne a gidan sarki, da yana cikin masu gadi, da yake mutum
ne shi mai shisshigi da tusa kai, haka ya dinga shiga da fice har saida aka maidashi bangaren
kula da dawakai. Sannan wannan shisshigin nashi yasa yake samun alkhairi babu laifi tunda
gwani ne kwarai wajen koda duk wani ahali na gidan Sarkin.
Kusan a cikin yaran gidan, Rahanatu itace tafi kowa haske da manyan idanuwa, hakan yasa
mutane suke cewa tafi kowa kyau, da yake za'a iya cewa ta biyo halin mahaifinta, saita kara da
iyayi da kuma son ace wata ce, da ta kafa rigima da naci saida aka sakata a makarantar bokon
da har mazan gidan ba damuwa sukayi da ita ba. Ta kuwa rungumi fadin rai ta dorawa kanta,
duk inda zata zauna saita san yanda tayi ta fadi cewa ita jinin sarauta ce. Yaran unguwa da aka
taso tare kullum cikin gulmar wannan karya ta Rahane suke tunda mafadaciya ce ta gaske ba'a
isa ayi a gabanta ba. Ko Rahanen ma ta hana a kirata dashi sai Rahanatu.
Tana aji uku a sakandire ta hadu da Ayuba, dan gaye dai-dai da zamanin shi. Yana da shagon
saida kayan masarufi. Gashi Bafullatanin usul, fari sol dashi. Cikin kankanin lokaci akayi
bikinsu, yana kuma yi mata hidima har ya zarta karfinshi wani lokacin saboda yanda take da
son harkar karya. Dai-dai gwargwado tsaye yake kansu. Data nemi komawa makaranta bai
tauyeta ba, dakyar dai ta hada takardun sakandire, dole ta hakura, sabodq hidimar gida data
yara. Tana da cikinta na biyar ya rasu, bayan gajeriyar jinya. Wannan rasuwa ta kidima
Rahanatu, gashi daga shagon nan sai gidan daya bar musu. Yara kanana, tunda a lokacin
Khalifa ne kawai yake da shekaru goma, Anwar takwas, Jalila shida, sai Aziza uku, dan ta samu
tazarar shekaru 3 ne a wannan karin. Bayan ta haihu ta samu namiji sai aka mayar masa da
suna Ayuba suna kiranshi da Nur.
Sai ga takardun sunyi mata rana, shige-shigen mahaifinta da mutanen daya sani, sai gashi an
samar mata aikin rubuta kati a Asibitin Aminu Kano. Kuma bata zauna haka da aikin ba, duk
wata sana'a da zata kawo mata karin kudi bata sanya da ita. So take yaranta su haska sufi na
kowa a unguwar tasu, su samu ilimi tunda ita dai taga ranarshi. Rayuwar karyar dai data
dorawa kanta, Malam Ayuba kan nuna mata rashin jin dadin shi akan irin rayuwar lokacin da
yake da rai, tunda yanayi mata komai, bayason yanda dai idonta yake kan wasu a cikin
kawayenta, tana so ta taddosu ko ta zartasu. Yanzun da kasa ta rufe masa ido, ga aikin data
samu, sai abinda yayi gaba.
Cikin yaran nata biyar kuwa, Khalifa ne ya fita zakka. Ya samu karatu zuwa NCE, yana aikin
koyarwa, yanzun haka yana da mata da yaro daya. Ko kadan Khalifa bayason irin rayuwar da
Mummy kamar yanda suke kiranta takeyi, ta kuma dora kannenshi akai. Ga Anwar nan, yana
BUK a yanzun haka, saboda shi yace daman ba zai iya FCE ba, kusan yafi kowa jin kai a
cikinsu, saboda shine sak ya biyo mahaifinsu, yana daga cikin matasan da suka rungumi mining
din Pi lokacin da yazo, dan gani kasheni ne akan Pi, dan zaku iya raba jaha dashi idan kayi
kokarin rage masa burinshi akan Pi. Haka yayi sa'a yana cikin wanda aka budewa yin kyc da
wuri, saboda haka lokacin da aka fara bumburutun Pi saiya zamana ya samu kudin da bai taba
rike irinsu ba.
Khalifa ya bashi shawara ya samu sana'ar da zai dingayi, suka zauna sukayi magana sosai,
kuma Anwar ya nuna masa ya dauki shawarar, yana komawa gida, suka zauna da Mummy ya
fada mata kudurinshi na da yayi niyyar yayi musu gyara ne a gidan, sai ta rushe duk wani tsari
da Khalifa ya dorashi akai, sai gani yayi an dauko gyaran gida, gini ne na zamanin da, na kasa,
sai akayi masa shafen suminti, dan haka katanga akaja bayan an ware daki daya akayi masa
gyara na gaske, sai katangar ta raba wannan dakin da sauran gidan ba'a gyara ba, ya siyo
wannan katon gate din aka kakaba a gidan.
Sauran Pi din yace ba zai siyar ba zai jira a shiga kasuwa dashi ne, dan abinda yayi saura ya
fara saro gilasai, hulunan hana sallah da zobunan azurfa, daman yana dan taba siyar da
takalma, yana samun rufin asiri dai-dai gwargwado dan kuwa Anwar ya iya kasuwanci, karya ce
kawai takeyi masa cikas, tunda kudin maimakon yayi abinda ya kamata dasu sai a siyi turaruka
ko takalma designers. A wajen Anwar dama Jalila a yanzun, da aji kunya gara an kwana da
yunwa. Kawai wani hali da suke dashi su dukansu, suna son farin cikin Mummy, duk wani fata
nasu na yanda zasu gatanta ne, ko Jalila tayi niyyar yin auren kudi yanda Mummy take so, sai
ga Balarabe da suka fara wata irin soyayya mai tsayawa a rai duk kuwa da tarin talaucin shi.
Haka Mummy naji tana gani ta hakura akayi auren.
Shikuwa Auta Nur yanda duk akayi dashi haka yake binsu. Jalila a yanzun haka ta gama
diploma dinta anan Kano Poly, amman ita data samu mijin daya kwanta mata sam ba zatayi
wani karatu ba. Aure take so, tunda ta tasa tasan ma'anarshi, ko yaushe cike take da mafarkin
auren nan. Balle data kara samun babbar waya, tana cikin group din matan sirri na Facebook,
tana bibiyar manyan bloggers a manhajar Instagram, sai ta karajin tanason auren, babu kuma
abinda yafi burgeta irin ace yau ta mallaki kitchen dinta na kanta, tana dafa ma mijinta
abubuwan burgewa itama ta dauki hotonsu ta shiga wannan trend din da ake yayi na 'ga abinda
nake ciyar da mijina'.
Shisa duk shiriritarta, tunda Mummy tayi musu tsaye a bangaren boko dama Islamiyya, itace dai
sai taga dama take zuwa Islamiyar lokacin, bata wasa da addu'a akan aurenta. Dan bata
dagowa daga sujjada bata roki Allaah daya bata miji nagari ba, kuma tana da yakinin rokonta
Allaah Ya amsa ya jeho mata Baffa. Duk da karsashinta ya rage lokacin da taji yana da aure
harda yara uku, amman shi da kanshi Baffan ne ya kara mata karfin gwiwa, a bakinshi takejin
shi da Jamila aure ne akayi musu na hadi, yanzun a tare da son da takeyi masa, akwai tausayi
mai yawan gaske da yake bata. Ace matashi dan kwalisa kamarshi, ga rufin asiri yana dashi
dai-dai gwargwado amman baiyi sa'ar mata ba.
A goman karshen nan batayi wasa ba wajen addu'a, harda Mummy take hadawa idan Baffa
shine mijin nata, to abin ya kwantawa Mummy a rai. Tasan duk yanda zasu so juna da Baffa, in
dai Mummy bata karbe shi da budaddiyar zuciya ba, ba zataji dadin zaman yanda ya kamata
ba. Ai tana gani akan Jalila, duk wani abu da Balarabe zaiyiwa Jalila sai ta kushe, ko ita kuwa
ya bada aka kawowa haka zata karba tana kushe abin da Balaraben ma gabaki daya. Wani
zubin ma da kuka Jalila take barin gidan saboda kwarzabar Mummy akan auren nata. Shisa ba
zata taba wasa da addu'a ba ita kam, tunda tasan babu wanda zai tausaya mata sama da
Ubangijinta, to kuwa gara ta gurfana a gabanShi ta kai kukanta.
Yanzun a cikin kawayenta su shida, Aisha da Hassana duk sunyi aure, saura su hudu, ita, Mimi,
Nabila da kuma Maryam. Sunfi dasawa da Mimi saboda yanayin rayuwarsu yazo daya, suna da
son asan dasu a waje, gayu, dama karya, duk da ita Mimi suna da kudi, amman kudin nasu bai
kai yanda ita take zuzutawa ba. Maryam yanzun haka ansa ranarta, Nabila ma anyi gaisuwa,
shiya karawa Aziza jin kamar ta janyo Baffa yazo ayi magana tasan cewa da gaske yakeyi, yau
ma sunyi zasu hadu a gidan Hassana,ita, Mimi da kuma Nabila, tunda duk Hassana dince
takeyi musu dinki. Ta kware sosai, haka kuwa akayi, suna cikin hira ne, Mimi take basu labarin
saurayin da tayi Nawaf
"Nifa bawai baiyi mun bane ba, yanda yake isata da hirar matarshi da yaranshi shine abinda
yasa duk ya fice a raina, to tunda yana son matar tashi uwarme ya kawo shi wajena?"
"Ke dai Allaah Ya shiryeki, ai wannan alama ce mai kyau, ba wai hirar matar tashi ba da yakeyi
miki, yanda yake nuna miki iyalanshi ma da muhimmanci a wajenshi, kema sai kiyi fatan idan
abin ya tabbata Allaah Yasa kiyi muhimmancin nan"
"Koma menene, karka kawomun maganar matarka, babu ruwana da ita, kazo muyi hira kan
abinda ya shafemu, nifa shisa sam bana son ma in kwasowa kaina mijin wata, duk yanda zakiyi
dashi sai an samu damuwa, wannan makirar matar tashi saita kawowa soyayyar taku wani
cikas din"
Aziza da take jinsu ce tace
"Bafa kowacce ba, wata ma bata da wannan muhimmancin a wajenshi, kinga kaman Habibi na,
wallahi har tausayi yake bani, saboda dama can shi ba auren soyayya sukayi ba, wata dusa ce
aka hadashi da ita, hakuri kawai yakeyi, shisa nake ta shiri, dan na tabbata kwace shi a
hannunta ba wahala zaiyi mun ba"
"Wato zama yayi yana shirya miki drama ke kuma kika hau? Auren hadin shekara mai zuwa ma
kina iya ganinta da lodin shagamu, in babu kenan, ya mika mata ta karbe da hannu biyu, yazo
yana shirgaki"
Wannan karin su duka sukayi dariya banda Aziza da maganar ta bata mata rai sosai
Mimi tace
"Ciki mana, ba haka suke zuwa suna samun su Aziza suna shirga musu karya ba, yanzun daya
shiga gida zakiga ba zai sake waya dake ba sai gobe idan ya fito, makirin"
"To ni ba waya ba, wallahi har video call munyi dashi jiya da daddare, yana gidan nashi kuma
balle wata waya"
"Nace miki fa wata dusa ce yake aure, tana can tana baccin asara mana"
Aziza ta bata amsa sunayin dariya tare da Nabila, amman banda Hassana da fuskarta ke kara
hadewa waje daya
"Amman kinsan daga ke harshi baku kyauta mata ba, saboda abune da idan akayi miki shi ke
ba zakiji dadi ba"
"Babu wani rashin jin dadi, aina dauka shirga mun kawa yakeyi, in har yana video call da ita a
gida to da gaske waccen batama san ciwon kanta ba balle har tayi muhimmancin a wajen miji,
idan irin wannan wawayen matan ne to fa kwace miji a hannunsu ba zaiyi wuya ba, ke dai kawai
ki shiga da shirinki"
Ganin kome zata fada ba zasu taba fahimtarta ba,sai tayi shiru, amman ita tayi samari masu
mata, bama guda daya ba. Ita asalima bataso ka kwaso mata maganar matarka, sannan in dai
ka shiga gida, tasan lokacin komawarka gida yayi, koya zaka kirata ba zata amsa maka ba, da
yake da anyi isha'i in ba wani abu zatayi ba, kwanciya takeyi tai bacci, ba'a wannan chatting din
daren da ita sam. Tana kokarin kiyaye kin yin duk wani abu da ba zataso ayi mata ba a
matsayinta na mace to kar tayiwa wata macen.
Sai ta cigaba da fere doyar da takeyi tunda daman suna tsakar gidane
"Duk dani dai in ba kaddara ba auren mijin watan nan bai kwanta mun ba"
"Nifa na kasa gane wannan maganar ta mijin wata, waishi namijin inace don mace hudu aka
halicce shi? Sai wata ta kwakume tace ita kadai zata rayu dashi, ni wallahi babu wani mijin
wata, mijinmu dai"
Nan fa musu ya kaure tsakanin Mima da Aziza da kowa yaki fahimtar dan uwanshi, ganin abin
na neman zama rigima Nabila ta katse su da fadin
"Kuna da fadin, yanzun fa akayi azahar, kuna nema ku karar da dan energy din naku akan
gardamar da banga amfaninta ba, kowa ba sai ya auri wanda yayi masa ba"
"Ni iskancin kawo mun dinki a kurarren lokaci ma nake so ku duka ku bari, nayi muku magana
kunqi jiko, to zaku sha mamaki wannan karin"
Su duka sai suka koma lallashinta, dan sun san Hassana, tsaf zata iya kin dinkawa ko da kuwa
tana da lokaci, gashi sun kasa sake wani wajen dinkin, bayan kwarewar da tayi, suna samun
rangwame saboda kawancen da yake tsakaninsu. Duk da haka Aziza da Nabila saida suka
sake zantawa akan Baffa da suka tashi tafiya tunda hanyar su daya ce, acan ma suka bar Mima
da yake ita bata da nisa da gidan Hassana din, unguwa dayace, layi biyu ne ya rabasu
A lokacin da Nabila take karawa Aziza kwarin gwiwar shiga gidan Baffa, da kuma karin dabarun
da zatayi amfani dasu ta kamashi a hannu, wasu dabaru da take hadawa da fatan bawai ta
kama Baffa kawai ba, a'a ta jijjige Jamila daga gidan gabaki daya ta rayu ita dashi su kadai.
Shikuma yana can shago ulcer din da bashi da ita na neman duk wata hanya da zasu kulla
zumunta...
********************** **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
************************* **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery,
Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko
kuma post.
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafinmu ku yi search na AI
HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
********************** **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** **************************