0% found this document useful (0 votes)
65 views112 pages

Mumnunar Dabi'a by Asma Baffa

The document is a fictional narrative centered around the lives of characters Ali, Asmau, and their children, including twins Sohail and Sahil. It explores themes of family dynamics, cultural expectations, and personal struggles, particularly focusing on the challenges faced by Sohail, who exhibits unusual behavior. The story unfolds in a blend of humor and drama, highlighting the complexities of relationships and societal norms in a Nigerian context.
Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as TXT, PDF, TXT or read online on Scribd
0% found this document useful (0 votes)
65 views112 pages

Mumnunar Dabi'a by Asma Baffa

The document is a fictional narrative centered around the lives of characters Ali, Asmau, and their children, including twins Sohail and Sahil. It explores themes of family dynamics, cultural expectations, and personal struggles, particularly focusing on the challenges faced by Sohail, who exhibits unusual behavior. The story unfolds in a blend of humor and drama, highlighting the complexities of relationships and societal norms in a Nigerian context.
Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as TXT, PDF, TXT or read online on Scribd
You are on page 1/ 112

[7/17, 3:17 PM] Asmabaffa: https://www.arewabooks.com/chapter?

id=6683ec1256566fe605af16a3

🪸MUMMUNAR DABI'A🪸

1-5

Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA NE GA 'YATA TASNIM

Page naki ne
UMMEETAH MUHAMMAD

BISMILLAH

ALLAH YA KAWO MU FANS, ALLAH YASA MU FARA LAFIYA MU GAMA DA RAI DA LAFIYA.

INA KAUNAR KU MASOYANA INA KUMA GAISHE KU.

JAN KUNNE GA MASU AUDIO,DUK WANDA YA JUYA MIN LITTAFI YA KOMA AUDIO SAI YA SAUKE
SHI DAGA CHANNEL DINSA.

*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason
juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene
matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin
taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma
babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko
kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi
glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da
humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu
karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-
muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku
da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban
burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza.
Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka
tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin
kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da
kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*
Labari
England

Baturiya ce kyakyawar gaske ajin karshe ta zauna tare da zuba uban tagumi tana
hawaye da kuka,yara ne maza guda biyu da alama 'yan biyu ne, kyawawan gaske kana
ganin su kaga ruwa biyu,hasken su bai kai na turawa ba kuma ya wuce ace na yan
Africa ne,haka gashinsu ma da komai nasu gaba daya,zaune suke suna wasa.

Wayarta ce tayi kara" ai da sauri ta daga cikin harshen turancinta tace kazo
kasar? wanda ta kira ya tattabar mata cewar nazo yanzu zaki gani,murna tayi tace
mutum ya huta da wannan masifa ko na kaisu gidan marayu,yara sun hanani sakewa,ko
club bana zuwa dama ni a club ya tsince ni muka yi aure,yazo ya sake ni ya tafi da
yaransa Nigeria bazan iya ba.
Tana zaune taji Door bell,da gudu ta mike ta bude kofar ranta a bace,wani matashi
ne kyakyawa shima wankan tarwada me suffar kamala da alama musulmi ne,Sunansa ta
kira Ali ga yaranka na gaji ka sake ni irin sakin ku na musulmi,bazan iya ba,wannan
yaran na gaji da su,ka dinga kawo su hutu,Ali dama ya gaji da wulakancin da
baturiyar take masa tunda ta haihu yake fama,nan take ya sake ta, divorce paper ta
mika masa yayi signing nan take itama tayi,ya duka gaban yaransa 'yan biyu ya dauke
su daya a hannun hagu daya a na dama ya fice daga gidan.

Waye Ali

Ali dan asalin kauyen Jigawa ne wani gari na fulani,maraya ya taso wanda shi
kadai iyayensa suka haifa a hannun kakansa namiji ya taso ya girma kafin Allah ya
masa rasuwa shima sai yan uwa na kauye,Ali cikin ikon Allah Cirani ya taho birnin
kano ya fara kasa lemo a faranti yana bi makarantu makarantu na yara.

A haka ya samu ya shiga University kasancewar ya gama karatun secondary gashi da


ilimin muhammadiyya, cikin ikon Allah ya kammala degree dinsa,yana gama bautar kasa
wani abokinsa dan gidan gwamna ya bashi babban aiki a mininstry,daga nan Ali ya
auri matarsa ta farko uwar gida Asmau, tunda ya auri Asmau bata taba haihuwa
ba,sunje asibiti iri iri ance a ita ne baza ta taba haihuwa ba,sabo da wannan
dalili ya kara aure ya auri matarsa ta biyu Nadia, shekarar Nadia daya ta haifo
Danta namiji kato kyakyawa da shi,yaci suna Adnan,Asmau ba ruwanta ita ta fawwalawa
Allah murna take, mutuniyar arziki ce,ita kuwa Nadia tunda ta haihu sai bakaken
magana,bayan ta yaye Adnan ta sake haifo Danta Ibrahim sai yarta mace Amal, tun
daga sannan kuma bata sake haihuwa ba itama har aka kwashe shekaru uku.

Ali kuwa Business ya fara gwadawa yana hadawa da aikinsa na gomnati,kamar wasa
sai ga Ali ya zama hamshakin me arziki har ta kai bazai iya aikin gomnati ba kawai
ya bar aikin,bashi wannan kasa bashi waccen,ya koma hadaddiyar GRA a cikin garin
Kano.

Ya mallaki kadarori na gasken gaske,har gidajen mai ne da shi state state,Ali


Sa'ad ya shahara wanda duk Nigeria an sanshi,yayi fice sam har iyalan nasa basu
fiye zama a Nigeria ba sai dai suzo da yawo, ganin yaransa sun dan fara tasawa sun
isa a sasu a secondary school sai suka dawo Nigeria garin kano gaba daya.
Yayin da shi kuma yake fita kasashe a inda yaje club yawon bude idonsa ya hango
halley baturiya ce usul kuma ba musulma ba,suka fara soyayya cikin kankanin lokaci
aka daura musu aure,shekara daya Halley ta haifo masa yan biyunsa kyawawan gaske
suka ci suna Sohail da Sahil.

Sai dai an samu matsala bayan sun shekara sun fara tasawa sai aka gano daya a
ciki wato Sohail ba lafiyayye bane daya ne lafiyayye,daya kamar dan ruwa haka yake
abubuwansa,gasu bulbul da su kuma kusan kansu daya Sahil yafi tsayi da kadan amma
banda wannan basu da banbanci,ba kowa ke gane su ba ma.
Daya daga cikin Dabi'un Sohail kuwa shine idan aka bashi abinci baya ci sosai
sai wasa,sannan sai anga ya girma shima kansu daya da Sahil sai kawai a wayi gari
aga ya rage girma ya sake komawa yaro,ana sake tashi washe gari sai aga ya dawo ya
zama kai daya da Sahil,har suka fara cin abinci da kansu,idan aka zuba musu shi
Sohail sai ya dinga wasa da nashi ya juye a kasa yana wasa a haka sai ya zana zero
0 da abincin nasa.

Idan kuma ruwa zai sha sai ya samu wuri me rami ko dan kurmi sai ya juye nasa a
ciki ya kafa baki ya fara sha,wannan Dabi'ar ta Sohail yasa baturiya Halley ta gaji
ta bawa uban su yaransa baza ita iya ba ita kam.

Bayan sati biyu da yaransa Ali ya sauka a Nigeria Kano driver da escort suka dakko
shi motocin da suke take masa baya sunfi biyar har zuwa katafaren gidansa dage wata
sabuwar GRA,yaransa suna hannunsa su biyu har part din uwar gidansa Asmau ya
taka,cikin shigarta ta alfarma ta sha material me tsadar gaske ta harde kafa daya
kan daya tana kallon film,murmushi tayi ganin mijinta ya shigo ta mike tare da
karbar yaran su biyu tace yarana sun iso,murmushi Ali Sa'ad ya saki ganin Asmau
bata da matsala ko da yace zai karbo yaransa daga wajen baturiya ya bar mata tayi
na'am har da murna kamar ita haife su sai zumudi take itama tayi yara har yan biyu.

Wata Allah ya bata bata so sun ishe ta ga wata tana murna an bata kyauta wanda
ba ita haife su ba,Sohail ne yake ta faman rikida yana wani haske yana duhu
kuma,Asmau ta kalle shi sosai tace kai wannan sai kace Nepa ana wal-duf,Ali yace
wlh nifa wannan yaron ina tunanin daya dan ruwa ne,Asmau tace haba dai inshaallah
ba haka bane,tace bari naje na kula da yarana kaje ka huta yau Amarya ke da kai ni
nayi yara,Murmushi Ali yayi yafi so ace kwanan Asmau ne yafi zumudi sabo da Asmau
ta musamman ce.

Juyawa yayi ya nufi part dinsa,Asmau kuwa tuni ta wuce bedroom dinta da
yaranta 'yan biyu.
A ciki ta shirya abinta ta musu wanka dake sun san da zuwan su komai an tanada
har kayan wasa, cikin fararen kaya ta shirya su tsaf abinta sannan ta kawo madarar
yara ta hada ta fara basu suna sha,Sahil normal yake shan nasa amma Sohail hannu ya
sa ya fisge tasa da karfi,Hajiya Asmau taji kamar babba mutum ne ya kwace sabo da
yanda taji karfi sosai an fisga,kallon Sohail tayi tace sai kace Daddy dinku ne ya
kwace abu irin wannan karfi haka,tana mamaki a ranta, sai taga yaki sha sam yana ta
kalle kallen wurare a palon.

Rarrafe yayi ya wuce yaga babu wani waje me rami ko kwurmi a hankali ya dafa
jikin kujera ya mike yana tafiya da kyar ya fice daga palon yana fitowa ya hango
wani dan kwari inda akwai flower a wajen a nan ya juye madararsa ya kafa baki yana
sha,Haj Asmau tana binsa a baya tana kallo,abin ya fara bata tsoro kuma.

Abinda ya kara girgizata shine bayan wasu kwanaki katsam ta nemi Sohail ta
rasa,hankalinta ya tashi matuka ta shiga kitchen tana shiga ta iske shi a cikin
bowl din gasarar koko da ta tace yana ta wankansa a ciki,duk inda yaga laima ko
danshi sai ya tafi ciki ya zauna.

Kishiyarta Nadia ita kanta tsoron Sohail take gasu kyakyawan gaske,Yaranta
sune manya Adnan ya kusa gama Jss3 shi kuma Ibrahim yana Jss 1,Amal tana primary 4.
Gaba daya Adnan bakin hali ne da shi shine wanda gaba daya ya tsani Sahil da
Sohail,ko kulasu baya yi sannan ya hana 'yan uwansa su kula su ko da wasa,itama
Nadia amaryar Ali haushin yaran yan biyu take ji sabo da ta gama sakankancewa itace
kadai zata ci gado idan mijinsu ya mutu tunda Asmau bata haihuwa,ji take kamar ta
kashe yaran ta huta sabo da tsana,duk da haka wani dadi take ji da Allah yasa daya
dan ruwa ne ba lafiyayye bane,ita gani take yi Dan ruwa ne ma Sohail,shi yasa bata
kallonsa a mutum sam,idan ta kalle shi ma sai dai ta dinga tuntsira masa dariya
haka kawai.

Bayan wasu 'yan shekaru har Sohail da Sahil suka girma suna magana suna gudu
ko ina har suka kai matakin zuwa makaranta,ba karamin wahala Asmau take sha da
Sohail ba sabo da barna da wasa tare da lalata waje kamar aljani haka yake,
maimakon yana girma aga ya canja sai abin ma ya kara rikicewa inda ya fara dalalar
da yawu,kullum cikin dalalar da yawu yake, wannan yasa Mahaifinsu ya fara kaishi
neman magani wajen malamai amma ba a dace ba duk sun ce ba aljani bane mutum
ne,gaba daya Sahil ya fishi girma shi Sohail sai sun girma tare sosai kawai sai a
wayi gari aga ya dawo wani yaro shi kadai.

Yau ma haka ce ta kasance Asmau tana ta murna Sohail ya dawo kai daya da Sahil
komansu kai daya,kawai yau da sassafe sai gani tayi Sohail ya dawo yaro tafiyar ma
da kyar yake yi ,a haka suka hakura aka sasu a pre nursery, Sahil yana da basira da
ganewa shi kuwa Sohail kullum sai bacci yake yi har a gama karatu yana bacci,amma
da ance an tashi an kada kararrawa zai tashi a bacci bazai sake bacci ba.

Malaman dama an sanar musu haka suke kyale shi, tare ake kaisu school da su Adnan
a dakko su,kudin makaranta ma Adnan ake bawa a hannunsa ace ya raba musu su yaran
kasancewar shine Babba,Adnan idan ya tashi sai kawai ya bawa iya yan uwansa wanda
suke uwa daya uba daya ya hana twins nasu,haka zasu je school suna kallo ana ta
ciye ciye na kayan yara amma banda su sai dai su zauna a class,gashi shi Sahil baya
wasa wani silent ne baya kula kowa,Sohail shine sarkin wasa amma bacci baya barinsa
yayi wasan indai a makaranta ne.

Watarana 'yan biyu sun kara wayo suna primary 2 Sahil ya gaji ya samu Mama Asmau
ya fada mata yace Mama Yaya Adnan bai taba bamu kudin school ba muna kallo ana
siyen alawa mu bamu da kudi,Asmau tayi murmushi tace to kuyi hakuri kunji ta basu
hakuri,tun daga ranar take musu abinci suna tafiya da shi sannan a jakar su ta zuba
musu alawoyi da biscuits,amma Adnan yana ganewa sai ya dinga kwace jakar yana
kwashewa ya bawa kannensa.
Abincin ma ya kwace ya zubar ya basu flasks dinsu haka,nan ma Sahil ya gaji ya
fadawa Mama Asmau.
Ranta yayi mugun baci amma ta danne ta basu hakuri ta canja sai ta dinga bude
tsakiyar littafinsu tana sa musu kudi a ciki na break a haka suka tsira suke samu
suna siyen wani abin.

Gaba daya Adnan da Mahaifiyarsu Ummi Nadia sun sawa sauran yaran tsanar su Sahil
basa kaunar su ko kadan shi kanshi Daddyn nasu Ali Sa'ad bai damu da su Sohail
ba,ganin kamar ba mutane bane,ba ruwansa da su komai sai dai su Adnan.

Ana wannan har su Sahil suka isa aike sosai ana aiken su su siyo abu a kanti,duk
sanda aka aiki Sohail to baza aga dai dai ba,yau Asmau ta fito zata aiki Sahil ta
iske jikinsa yayi zafi yana zazzabi tace kai Sohail zo na aike ka,yaje ya karbi
kudin,tace kayan miya zaka siyo min,me nace? Yace kayan miya,tace good boy tattasai
tumatir da attaruhu na dari biyu saura naga ba dai dai ba sai na zaneka yau.
Har ya fita tana nanata masa kayan miya zaka siyo ya fita yana gudu,amma yana
fita bakin gate yaci birki ya fara tafiyar sangaya kamar bazai tafi ba yana wasa da
kudin,sai da ya kwashe 30mnt bai je ba,yazo kusa da masu kayan miyar sai ya hango
anyi ruwan sama ya kwanta a tsakiyar titi,cikin ruwan yaje ya shige yana ta
wanka,kowa in yazo da mota sai dai yayi dariya ya kauce da motar ya wuce a nan ma
ya shafe 1hr yana facaka da ruwa wanda duk jar kasa ne jajir da ruwan,sai da ya
gaji sannan ya fito ya tafi siyo abinda aka aike shi.

Ance ya siyo kayan miya amma sai ya tafi wajen me abarba da kankana yace a bani
kayan marmari,ai kuwa aka yanka masa kankana da yawa a leda aka hada masa da abarba
itama a yanke aka bashi ya juya ya nufi gida,a hakan ma a hanya sai da ya nemi
bishiya ya kwanta a wajen ga ledar kankana a gefe sai da ya sha sanyinsa sannan ya
tashi ya koma gida,lokacin Mama har ta gaji ma tayi shinkafa da wake abinta,sai
gashi ya dawo jikinsa jajir da ruwan kasa ga ledar kankana ce da abarba a
ciki,bakin ciki ya kama Mama,duk hakurinta sai da ta zane Sohail da tsinken
tsintsiya,ranar kuwa kwana suka yi basu yi bacci ba yana ta kuka yaki dainawa kamar
an kunna inji,har Alhaji Ali sai da yazo cikin dare yace Asmau ke da yaran naki ne?
tace wlh nayi danasanin dukan Sohail wannan masifa har ina kai Allah ya
shirya,Murmushi yayi haka suka kwana ba bacci,Sahil ne kawai yayi bacci sabo da
yaro ne.

Bayan su Sahil sun gama primary school abin mamaki ba abinda Sohail ya iya amma
a jarabawa shine yake zuwa na farko komai sai ya cinye tas sai dai Sahil yazo shi
na biyu duk kokarinsa,tun ana mamaki ma har andaina.
A haka suka shiga secondary school lokacin Adnan yana university a England can
aka kaishi,Ibrahim ma yana shirye shiryen Tafiya can,Amal kuma Alhaji Ali yace mace
ce kawai tayi karatunta a Nigeria ita da kasar waje sai da yawo.

Nadia Amaryar Ali idan taga Sohail kawai sai ta dinga sheka masa dariya haka
kawai,har baya so ma ya ganta yaron ganin yana dalalar da yawu da girmansa dan
secondary guda amma yana haka,gasu Iya kallonka baka taba hango muninsu sai dai
Sohail rikida yake yau sai a wayi gari aga yayi dan duhu ko aga ya koma kamar
bature sak ko watarana kawai aga ya dawo wani yaro sosai.

Sai da suka shiga ss1 yau suna aji malamai sun gaji da baccin Sohail gashi sai
ya dinga cinye jarabawa sai suka daina daga masa kafa da anzo ana koyar da su
kullum sai an masa tambaya an tashe shi komai baccin da yake amma ana masa tambaya
sai yace shi ai bai dade da shiga school din ba jiya jiya aka kawo shi.
Yau ma wani malami ya gaji yana zuwa ya tashi Sohail ya mike tsaye yana murza
ido,yace what is a Noun? Sohail yace ai sabon zuwa ne ni jiya aka kawo ni,malamin
ya fara masifa yace tun pre nursery kuke a makarantar nan kace jiya aka kawo ka?
yace ae ni wlh jiya aka kawo ni ya kwabe fuska zaiyi kuka,dole aka kyale shi.

A cikin class din kuma farin jini ne da su Sahil sabo da kyawun su ana mugun
kaunar su duk makarantar, akwai wata yarinya Zayna a class din ba wanda take so ita
sai Sohail a duniya,har tissue take zuwa da ita kullum ta gogewa Sohail yawun
bakinsa watarana idan yana dalala,Sahil kuwa bashi da sakin fuska ma gani yake yafi
uban kowa a duniya duk da yana da kyawawan dabiu haka Allah yayi shi sai ka rantse
girman kaine da shi.

Ana haka a ss1 Sohail ya tsiro da wani abu duk macen da ta fara irgen dangi ko
jinin Haila sai kawai aji a bakinsa ya tona asiri ya fada da karfi a class din sai
kowa ya sani, budurwarsa Zayna ita ba abinda ta fara na nuna alamun balaga a tare
da ita sai gashin hammata,yau tana zuwa aji kowa yayi shuru ana jiran shigowar
malam tazo ta zauna a kusa da kawarta,Sohail ne yayi magana da karfi kuma da Zayna
Isma'il ta fara gashin hammataaaaaa.....aji aka barke da dariya ana kallon
Zayna,kunya ta lullube Zayna ta fada kasan sit ta buya,Sahil yana jinsu ko magana
baiyi ba.

Malam ne ya shigo nan take Sohail ya fara baccinsa abinsa har aka tashi yana
bacci,sannan Sahil ya tashe shi suka wuce driver yazo daukan su,Amal yayar su tana
motar tana wani daure fuska suka shiga ciki driver ya ja suka tafi,Amal ta samu
Sohail ta talla masa mari haka kawai tace shegu yan iska kunki fitowa da wuri muna
ta jiran ku,Sahil kuwa ransa ya baci ba zato ya saukewa Amal mari a fuska,kumatu ta
dafe tace Sahil ni ka mara? Yace an mare ki so what? Who do you think you are? ko
yaushe sai dai ku zage mu ku dake mu,me muka yi muku,idan kin yiwa Sohail ya kyale
ki ni bazan kyale ki ba,Sohail yana kallon su yace ku chasu arna ku chasu,shi da
ake tare masa amma ko a jikinsa.

Suna Isa gida Amal ta fito ta samu saurayinta na university dinsu yazo wajenta
shima dan gidan me kudi ne,suna fita wajensa ta wuce,Sohail yana zuwa zai wuce su
yace saurayin Aunty Amal ai Auntyn m Jinin haila take yi yau ya wuce abinsa,Amal
ranta ya baci kuma da gaske Sohail yake tace wlh idan na dawo ciki sai na lahira ya
fika jin dadi,ciki suka wuce aka barta nan saurayin yana murmushi ya zaci lafiyayye
ne Sohail yace ashe kina off,ya aka yi yaro ya gani,kwana nawa kike yi? Amal duk
taji kunya ta share zancen.

Ai kuwa tana gama sallamar bako part din Mama Asmau ta nufa a fusace,Mama ta
kalleta suna palo tare da yaranta tana biya musu karatun Qur'ani gobe suna da
hadda,lafiya ke Amal ko sallama babu? Zuwa nayi naci uban yaran naki ta furta da
tsiwa tana fisgo Sohail,Mama ta janye Sohail tace wlh kina taba min yaro saina
kwashe ki da mari tunda baki da kunya.

Ae bani da ita ai bake kika haife su ba juya ....karaf a kunnen Alhaji Ali
Daddy me shirin shigowa yana jin haka ya karaso ya cafke Amal babu bata lokaci ya
hau jibgarta sai da ya mata lilis babu wanda ya kwace ta,yace idan uwarki ce zaki
fada mata haka? Matata ita ba uwar ku bace? Amal tana kuka tana bada hakuri, da
kyar ya hakura ya kyaleta ta fice da gudu kuwa.
Matarsa Asmau ya bawa hakuri,tayi murmushi tace ba komai fa Allah dai ya shirye
su,duk Adnan ne ya koya musu.

Bayan shekaru biyu Su Sahil suka gama Secondary school dinsu,sun wani tasa sun
girma sun kara kyau,lokacin kuma Sohail Allah ya yaye masa dalalar yawu tuni,ya
daina abubuwa da yawa duk ya daina ya zama cikakken mutum amma fa akwai shirme,kana
ganin yanda yake abubuwansa kasan kansa yana fisga, sai dai an daina wasu abubuwan
manya wanda hakan ba karamin dadi yayiwa Asmau da Ali ba, idan yana abubuwa a
rikice zaka san lallai fa wani abu na damunsa,a hankali shima Sahil kawai rana
tsaka kansa ya fara tabuwa irin na Sohail,yanda Sohail ke shirmen shima haka yake
yi, iri daya suke shiriritar su da Sohail,Asmau ta damu sosai tayi tayi Alhaji Ali
ya tsaya a nema musu magani sosai amma yaki sam,ganin ma a haka basu da kokari basu
san komai na duniya ba sai dai result kawai a school me kyau sune suke daukan na
daya,amma idan ka tambaye su abu daya baza su iya fada maka ba,har shi Sahil din
duk kokarinsa yanzu babu ya gudu bai san komai ba,shi yasa sam Alhaji Ali
mahaifinsu bai damu da su ba.

Yana ganin ba abinda zasu iya tsinanawa a rayuwa kawai dai a basu ci da
sha,ganinsu yake kamar ma ba mutane ba,komai baya sawa da su sai dai yaran Nadia
sune mutane,ya dauki su Sohail ba wasu mutane ba,Asmau tun tana fada masa gaskiya
har ta gaji,zai basu sutura ci da sha shike nan,su Ibrahim kuwa har kasuwan ci yasa
ake koya musu suna gama school zai basu company guda shi da Adnan.
ita kuwa Nadia dan dalalar yawun ma da Sohail ya daina sai bacin rai take da
Sohail ya samu lafiya,duk shirmen da suke bugawa shi da Sahil a haka cewa take
lafiya suke.

Yau ma Mama gani tayi sun sha wankan kana nan kaya abinsu abinka da kuruciya,sun
sha kyau kamar a sace su,tace ina zuwa kuma? Sohail yana daura agogo shi a dole
shege yace filin ball zamu kalli wani match yana yarfe hannu,Sahil kuwa turare ya
fesa yana wani jiji da kai,Mama dariya tayi kawai tace to a dawo lafiya manyan
yara,suka amsa da Ameen,tace banda driving driver ya kaiku please,suka ce to sannan
Sohail harda yiwa Mama kiss a kumatu ta make shi suka fita suna dariya,amma yanda
suke kalle kalle da wuri wuri kasan ba lafiya kansu da tabi.

Driver ne ya kaisu har gidan su Zaynah suma katafaren gida a hadaddiyar


unguwa,tasan da zuwansu ta sha gayunta,yanzu tunda sun gama secondary ana barinta
tana zance,fitowa tayi sanye cikin doguwar rigar material,har ga Allah bata gane
waye Sohail ba waye Sahil ba yau ta kasa ganewa sai taje ta rike hannun
Sahil,Sohail yayi murmushi yace ke kin ganni nan tunda kema bakya iya
ganewa,Murmushi Sahil yayi tare da fisge hannunsa,Zayna dafe goshinta tayi tare da
furta oups I'm sorry,Sohail yace sai kace kin rike wani bare he is my blood tare
zamu aure ki fa mu biyu,Sahil yace InshaAllah ki kwantar da hankalinki matar 'yan
biyu ce ke,Zayna ta zaro ido tasan kansu da motsi shi yasa dariya suka yi sannan
suka shiga cikin gidan,Sahil ya koma mota ya zauna yana danna waya abinsa,yana
jiran Sohail,Sohail lekowa yayi yace kazo ka kama min,bazan iya zancen ba sai kace
ni kadai zan aure ta ai har da kai a ciki,driver yana jinsu yana ta dariya,yace au
dama wai zance kuka zo nan? Kuma mace daya zaku aura ku biyu? Sahil yace ta ishe mu
rayuwar duniya ya bude mota ya fice ya bar driver yana ta dariya.

Sohail suka shiga palo Zayna suna hirar school din su,Sahil yace I love you
Zayna, Zayna ta zaro ido tace kaga saurayina fa,Sohail ya bata rai yace shima yana
sonki ai tare muke son ki idan bakya sonsa nima bakya so na to shike nan na daina
kulaki,Zayna tace sai kace akuya ce ni ta ya zan so maza biyu ni bazan iya ba,to
shike nan nima na daina sonki wlh,Sahil a fusace ya mike kamar zai mare ta ya daki
table sai da ta tsorata,yace da Sohail muje,Sohail ya mike yace kinwa kanki ki
rasa mu karki sake kula mu.

Zayna tace to sai me aikin banza mahaukata da ku ma,nan a makaranta kake dalalar
da yawu,dama dan kana da kyau nake kulaka amma me zanci da mahaukata,Sahil ne ya
dawo ya rike Zayna ya kwashe ta da mari,ya fara dukanta sai da ya mata lilis tana
ihu yan gidan su suka fito da gudu,Sohail ya jawo Sahil.

Maman zayna tace amma ku dai kunyi asara ai zaku aikata mahaukatan banza,kowa ya
fito yana tambaya lafiya sai ace ai mahaukatan nan ne sai ace ohhh Allah sarki ai
mahaukata ne a kyale su,su Sahil ko a jikin su dan ance musu mahaukata suka yi
tafiyar su.

Sai dare suka koma gida , Mama suka iske Fada ta fara tace dan iskanci sai yanzu
zaku dawo,Sahil yace wai Mama a koma bamu nono mana kawai a huta ace muna maza zamu
fara university ba inda zamu je muyi dare sai kace mata,Sohail yana jinsu ya saka
Earpiece dinsa zai toshe kunne,Mama ta rike kunnen sa tare da murdewa dariya ya hau
yi dake yafi Sahil fara'a shi,bana so ne a samu matsala ku lalace,karatu zaku fara
fa, kafadar Mama Sahil ya dafa kamar wata sa'arsa yace ba abinda zai faru, Mama
tace Allah yasa,Abinci fa? Mun koshi mun ci burger dazu,tace to Good night ayi
adduar bacci kar a manta.
Sam su Sohail basu taba tambayar ina maman su ba,ko wacece ba ruwan su ko zancen
basu taba yi ba.

Bayan wasu watanni Sohail da Sihil aka kai su private University dake Germany
suna can suna karatunsu amma dai sai dai result me kyau basu san komai na karatun
ba har yanzu
Har suka shiga level 2 sannan suka zo hutu gida.

Suna zuwa hutu suka samu anyiwa Amal aure ta auri wani hamshakin me kudi dattijo
ne gidanta daban,Adnan ma yayi aure an masa aure,ko fada musu ba ayi ba sabo da ana
ganin basu da muhimmanci,basu da amfani a duniya haka mahaifinsu da sauran yan uwa
ke gani,basu ma ce me yasa ba a fada musu ba sai murna ma da suka yi Adnan yayi
aure da Amal,Mama Asmau itace komai dinsu a gidan sabo da ita ne ba a iya taka su.

Hajiya Asmau yau shiri suka yi ita da kishiyarta Nadia zasu je Kaduna bikin 'yan
uwan Nadia a danginta dake ita yar kaduna ce,Asmau Kara zata yi mata,su biyu driver
ya tuka a mota suka tafi cikin ikon Allah a hanya motar su tayi hatsari bayan tayi
dugu dugu motar nan take ta kama da wuta,da kyar aka samu ma aka kashe wutar,babu
wanda ya tsira a motar gaba daya sun mutu da Nadia da Asmau har driver,Alhaji Ali
sai mummunan labari yaji,nan take ya fadi a sume aka kaishi asibiti.

Su Adnan kuka kamar ba gobe,su 'yan biyu ma basu san me ake yi ba suna daki
suna game tunda Mama ta tafi basu fito ba,mutuwar ma sabo da iskanci ba wanda ya
kula su Sohail bare a fada musu kawai ba mutane bane,Alhaji ya farfado da shi aka
hada matan nasa wanda duk sun kone kurmus,sai sassan jikin su kadan,hayaniya da
kuka ne yayi yawa Sohail ya mike sanye daga shi sai gajeren wando ya fito yana
lekowa yaga mutane dankam mata sun cika ko ina na gidan.
Dawowa yayi ya saka jallabiya yace kai Sahil gida fa ana ta kuka an cika gida
ko menene oho,Sahil yana ji yace kar fa abar nan ce tazo gidan nan yau,ai kuwa ina
jin ma itace tazo din cewar Sohail,yace tabbas ta karaso bari muji wa tazo ta
dauke,Allah yasa Umma Nadia ce,Sahil yace 3qtr ma zan saka dan iskan zaman makoki
zanyi naji a jikina Umma Nadia ce,3qtr ya sha me tsada da tshirts dinsa wata
grey,shi kuwa Sohail jallabiya ce fara a jikinsa,a jikin Mirror suka tsaya suna
taje sumar su ,Sahil ya shafa man lebensu na maza me kyau,Sohail ya hau fesa turare
sai da suka gama suka bude kofa tare da fitowa wai zaman Makokin Nadia zasu yi.

Mata aka zuba musu ido yuuuuuuuu kamar za a cinye su sabo tsananin kyawunsu,suna
zuwa Main palo suka ga yan uwan Mama Asmau da yawa suna ta kuka,wani palon kuma yan
uwan Nadia ne,Amal tana ta rusa uban ihu a cikin su,Sohail yace cikin rada da alama
Umma Nadia ce,Sahil yace akwai rawar bungalo yau da galala,suka dawo ta parlon da
yan uwan Mama suke domin sun fi sanin su,Sohail ne yaji ana cewa Allah sarki sune
yaran Asmau wanda ta raina,Allah sarki sunyi rashi,Allah kaji kan Asmau, mutuniyar
arziki,Sohail yaci wani wawan birki yace wa naji kuna cewa? Sai lokacin ya tuna ai
tare suka tafi unguwa da Nadis, Yanda yayi maganar cikin tsawa da karaji sai da
suka firgita,Sahil yaje ya rike wata tsohuwa cikin dangin Asmau yace wacece ta
mutu? Dattijuwar tana hawaye tace Nadia ce da Asmau duka matan mahaifinku sunyi
hadarin mota Allah ya musu rasuwa gasu can ana sallatar su.

Sohail yace wai Maman mu har da ita ta rasu? Suka ce ae,sumarsa ya hargitsa ba
tare da ya sani bama,ya fara kokarin cire rigarsa da ya fesa mata turare yana
hawaye nan take idonsa yayi jajir, Sahil kuka yake wiwi sosai yake kuka,ana ta basu
hakuri,Dattijuwar tace sai hakuri,Sahil cikin karaji yace baza muyi hakurin
ba,wallahi bazan hakura ba sai munyi kukan.

Da kyar da lallashi suka tashi suka nufi wajen makokin,Alwala suka yi suka bi
sawu aka sallaci gawar Mama da Umma da su,ana sallar suna ta sharbar kuka sam basu
iya sallar ba sai kace mata.

Sohail anzo daukar gawar babu kara sohail da Sahil suka ce a tsaya dan Allah
suyiwa maman su addua amma baza mu yiwa Umma Nadia ba wlh suna hawaye ana jinsu
suna cewa baza mu yiwa Umma Nadia ba,kowa yayiwa iya uwarsa,haka aka jira,suka
tsuguna a saitin kanta sun dade suna hawaye suna yiwa Mama addua sannan suna gamawa
su biyu kacal suka daga makarar Mama kowa yayi mamaki duk nauyin mamaci da
makara,haka mutane suka kama amma basa jin nauyin sam su Sohail sun dauke nauyin
amma kamar basu dauki komai ba,suna tafiya suna hawaye sai uban sauri kuma suke yi
mutane sai da gudu gudu sauri sauri ake binsu,Nadia kuwa tana can karshen baya ana
kiri kiri da ita,ana kaita bakin kabarin Sohail yayi sauri ya shige kabarin ya
kwanta wai sai ya ji inda Mama zata kwanta,aka fito da shi da kyar yana cewa ni a
barni na dana yana kuka abin tausayi, Sahil shima ya shige ya kwanta,da kyar shima
aka fito da shi yana faman tirje tirje yana cewa sai na Dandana nima, ana musu
fada,aka zo za a sa Asmau a makwancinta suka hana,suka rike aka yi aka yi suka hana
har aka binne Nadia sun hana a saka Asmau,Sai da Alhaji Ali ya musu magana ya kira
su sannan aka samu aka fara sata,Sahil da sauri yaje ya saka rigarsa da ya cire ya
dukunkune ta ya saka a saitin kan Asmau yace ayi mata pillow taji dadin
kwanciya,kwace rigar aka yi sannan aka samu aka kammala komai.
Sohail kuka sosai ya durkushe a kasa kuka yake ba ji ba gani,an gama komai amma
Sohail yace mu baza mu tafi ba a nan zamu kwana sai munyi gadin Mama.

Daga ranar babu wanda ya kara ganin su Sohail suna dakinsu suna ta kuka da
jimami suna tuna maman su Asmau da irin rayuwarsu da suka yi,girki da kansu suke wa
kansu dama sun iya sosai suna taya Mama duk ta koya musu,bayan akwai masu aiki a
gidan amma Adnan ya hana a basu su yan biyun abinci,za dai a zuba komai a store su
dafa da kansu.

Bayan anyi kwana arba'in Mama komai nata anyi rabon gadonsa 'yan biyu ko
handkerchief ba wanda ya basu,itama Nadia anyi nata yaranta duk an fiddawa kowa
hakkinsa duk da ba wani abu suka tara ba,Alhaji Ali ko kadan baya saurarar su
Sohail haka kowa na gidan,gasu sun zama manyan samari sosai.
Hutunsu yana karewa suka samu Daddy a part dinsa,tare da Adnan da Ibrahim suka
iske su suna ta rubuce rubuce suka shiga da sallama,Adnan da Ibrahim suka wani
daure fuska,Alhaji Ali yace ya akayi twins? Sahil yace hutun mu ya kare muna so mu
koma school Daddy.

Adnan da Ibrahim suka kwashe da wata mahaukaciyar dariya,Ibrahim ya kalle su


shekeke yace wai school sai kace suna ganewa,Adnan yace babu me biya muku har
Germany ku dinga yiwa mutane asarar kudi,me kuka sani,Alhaji Ali ne yayi magana
yace ya isa,kai Sahil naga ma kafi dan hankali company na dake Abuja na damkawa
Adnan da Ibrahim zasu dinga kula da shi suna aiki,kun san a cikin companies dina
wannan na Abuja yafi ko wanne sabo da haka duk wani Business su zasu dinga
juyawa,sabo da ina matukar kaunar Adnan,duk gidan nan ba wanda nake so sama da
Adnan sai Ibrahim,Su Sohail harda murna Daddy yana son Adnan da Ibrahim su yaya ana
kaunar ku cewar Sohail,Sahil yace mu kuwa bamu da kowa,Sohail yace kai muna da
Allah mu ya ishe mu harda tafa hannaye,Sahil yace fam fam magana ta kare mune muke
da Allah ya daga yatsa sama sannan yasa yatsan a baki yana tsotsa.

Adnan ya karbe zancen yace kai karku dame mu da shirme, da ku zamu tafi can kuna
taimaka mana da aikin gida,gaku ai bai kamata mu dauki yan aiki ba,sai ku dinga
wanke mana mota,shara da goge da girki komai dai kuma zamu dinga biyanku kudin
kashewa haka sannan sutura baza ta gagare ku ba kowa zai sa wacce yake so,wajen
kwana ma me kyau za a baku part komai,batun wata makaranta ba ganewa kuke yi ba ku
hakura ku fara shiri jibi zamu tafi, Ibrahim yace wannan shine daidai Daddy
shawarar da yaya Adnan ya bayar basa ganewa mene amfanin asarar kudi.

Sohail da Sahil basu ce komai ba kuma ko alama ransu bai baci ba hasalima ma da
sauri suka ce to zamu shirya,Ibrahim yana harararsu yace kuje dan Allah aiki
muke,suka juya suka bar wajen.
Suna komawa bedroom kuma suka fara shirin hada kayansu ko a jikinsu murna ma suke
yi su.

Wacece Zayna

Zayna 'ya ce ga Alhaji Shehu asalinsu babur ne,babanta Alhaji Shehu yana da
kanne mata da maza kasancewar shine babba sannan yan uwansa gaba daya suna
kasuwanci ya zaunar da shi a Kano,shima daga zuwa cirani Allah ya azurta shi tun
yana matashi har ya hadu da matarsa daya tilo yar fulani Hajiya Furera ita ya aura,
Allah ya basu yara hudu,Imran shine babba,Saif sai Zayna ta uku da autar su Arfat
suna kiranta da Baby.
Iyayensu mutanen kirki ne ga hakuri ga kyauta ga sanin yakamata,su Zayna sun
taso cikin kulawa da tarbiyya kamar ba yaran me kudi ba haka suke,sun san me suke
yi,nutsatsu da su sai dai suna da son me kudi.

Zayna kyakyawa ce ba laifi dai, ita ba fara ce ba tana da haske dai dai
mashaallah, 'yar lukuta ce Zayna, bayan su Sohail sun daina kulata Allah ya hadata
da yayansu Adnan taje shopping suka hadu,ta san shi yayan su Sohail ne amma ganin
da kudinsa daga nan suka fara soyayya har ta aure shi wanda har yau su Sohail basu
san Adnan Zayna ya aura ba.
Abuja din ma da zasu koma bada Zayna zasu tafi ba ita tana katafaren gidan
mijinta sai dai ya dinga zuwa weekend ko watarana ta dinga zuwa can haka suka
tsara,su Sahil sunce zasu je ganin amarya amma yace kar su je masa gida,haka Amal
ma ta nuna bata kauna suje gidanta shi yasa suka hakura kawai.

Bayan kwana biyu Adnan da Ibrahim su a jirgi suka tafi amma su Sahil sai suka
ce driver ya kawo su Abuja a mota,haka aka kaisu a mota .
Free page

1&2
500 ne.

0175487861
Asmau Garba Muhammad
Gtbank

Niger
+22790795939

AsmaBaffa
08061929616
[7/17, 3:17 PM] Asmabaffa: https://www.arewabooks.com/chapter?
id=6683ec1256566fe605af16a3

🪸MUMMUNAR DABI'A🪸

6-10

Official

By
AsmaBaffa

Sadaukarwa ne ga 'Yata Tasnim

Pagae naki ne
Ummu Khinal

GARGADI GA MASU AUDIO BAN YARDA A SACI LITTAFINA A JUYA ZUWA AUDIO BA.

*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason
juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene
matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin
taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma
babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko
kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi
glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da
humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu
karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-
muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku
da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban
burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza.
Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka
tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin
kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da
kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*

Su Sohail suna karasawa har asokoro wani mahaukacin gidane na alfarma


gida ne na musamman wanda komai nasa ba karamin dukiya aka narkar ba wajen gina
gidan ba,komai akwai na more rayuwa,Adnan suka gani yana hutawa zaune a wasu kujeru
na hutawa masu kyau ya dora kafa daya kan daya yana latsa waya sannan yana kora
ruwan lemo me inganci da kara lafiya a jikin dan Adam, kallon su yayi wani haushi
ya kama Adnan sun fisu kyau da cikar zati da komai ma,baki ya tabe tare da
mikewa,akwatunan su suka dakko tare da kallonsa "how far bro" suka furta.

A hasale yace kunga respect your self ni ba sa'anku bane kar ku sake kirana da
wani bro,who is your brother? Dalla ku wuce muje ya ja wani tsaki tare da wucewa
ciki suka bi bayansa suna murmushi ko a jikinsu,hirarsu ma suka fara yi,a fusace ya
sake juyowa yace kai kun cika min kunne,shuru suka yi kawai suka haura sama ya nuna
musu dakinsu hadadden gaske me dauke da makeken bed da toilet komai a kwai
ciki,suna ajiye Jakar su bai bari sun huta ba yace ku fito na nuna muku gidan
sannan na zana muku aikin ku,suka biyo shi kamar 'yan aiki.

Sai da ya nuna musu ko ina na gidan sannan suka koma palo,Sohail yace wash na
gaji,Ibrahim ne ya shigo yana magana yace ai ba hutu ne ya kawo ku ba,kai bari kuji
aikinku a gidan nan
Gyara gidan nan ku share ko ina ku goge,sannan kuyi mana wanki da guga, kuyi
girki,ku wanke mana motoci kullum,bude gate da kullewa,komai da kuka sani na gyara
gida da kula da shi kune zaku yi shi kunji,su Sahil suka ce sun ji,su kansu ganin
basu san komai ba sun hakura da rayuwar, tunda ana kiransu da mahaukata gani suke
basu da amfani a duniya,gani suke ba abinda zasu iya tabukawa a duniya,shi yasa
suka hakura kawai tunda sunga kowa baya daukan su a mutane,kuma suma abinda suke yi
da abinda suke ganin suna yi sai yasa suke ganin lallai ba daidai suke da kowa
ba,suka riki aikinsu hannu bibiyu,sun zama 'yan aiki ta karfi, sun fara musu bauta
ba ji ba gani har sun kai matakin samari na gaske ya isa ace sun kammala degree din
su amma sun kare a bautar yan uwan su, sun kwashe shekaru biyu suna bauta musu.

Su Sohail sun girma sosai dan sunfi ma su adnan girman jiki da tsayi,kai in ba
fada maka aka yi ba baka isa ka gane wane Sahil wane Sohail ba sai wanda ya mugun
saninsu zai iya tantancewa shima ba ko yaushe ba,kansu daya,tsayinsu daya
cif,kibarsu da jikinsu komai irinsu daya kai daya babu banbanci,sun ajiye saje da
gemu madaidaici,gasu jajir da su,ga tsayi gasu su ba ramammu ba sannan baza ace
suna da kiba ba,idanuwansu masu kyau farare tas,gasu da yalwar gashin gira da sumar
kansu me kyau da baki sai sheki suke yi kawai,kana ganinsu kasan ba wahala a tare
da su,sai dai suna bautuwa sosai, ko waye ya kalle su bazai so ya dauke idonsa a
kansu ba,gasu da kwarjini da cikar zati,gasu da tsafta ta gaske ga daukan wanka
tunda ana basu sutura da cima me kyau,komai iri daya suke yinsa,kawai banbancinsu
Sahil yana da wushirya yar kadan shi kuwa Sohail baida ita banda wannan basu da
banbancin da za a gane waye Sahil waye Sohail,halayyar su ma tazo kusan daya,Sohail
yafi fara'a,Sahil baida wata fara'a sai dai in suna tare da Sohail kawai zaka ga
yana dariya, 'yan mata kuwa basa tunanin ma sun kai mutanen da har zasu iya son
mace bare su aure ta wannan yasa ma su ba ruwansu da mata basa harkar su.

Ci gaban labari

Ibrahim ne ya shiga kwalawa Sahil kira "Sahil" "Sahil" kamar zai fasa
gidan,Sahil ya fito da gudu a gigice,dake su ba wahala sun gigice sun rude,sanye
yake cikin gajeren wando da riga armless maroon,Ibrahim yana wani gadara ya sha
wata azababbiyar shadda fara yana shining yace baka da hankali,jakin ina ne kai
kalli takalmin da koge min,brown nace ka goge? Na fada maka meeting zanje black
nace ka goge min amma ka goge min brown useless,karbi ka goge wannan,kuma idan
15mnt tayi baka goge ba wlh sai ka gane kurenka stupid,Jikin Sahil yana rawa ya
karba yace kana nufin a goge wannan? a'a goshin uwarka zaka goge min,Sahil yace
uwata ai bata nan ina zan ganta na goge maka goshinta? Dan Allah ka taimake ni ina
zanga Mummy na goge maka goshinta? Kuma kasan Mama ta rasu,dama Mama tana raye wlh
sai naje Kano na goge maka goshin nata,cike da mamaki Ibrahim ya tsaya sololo yana
kallon Sahil,yau ya tabbatar Sahil basu da hankali,tsaki yaja yace "Sahil" yace
na'am ka goge min takalmi zan fita, a goge dai ko kace? Sahil ya sake
tambaya,Ibrahim ya hasala sosai ya sake dakawa Sahil tsawa ya juya ya tafi gogewa.

Adnan kuwa cikin shirinsa ya fito zai fita ya samu motarsa da yace zai hau da
alama ba a wanke ta ba,Sohail ya dinga kwalawa kira,Sohail ya fito, yana zuwa Adnan
ya fara bala'i kai dan uwarka wacce motar nace ka wanke? yace bakar na wanke,haka
nace? ae cewa kayi na wanke maka fara kawai ni kuma na wanke bakar tafi kyau, Adnan
ya zaro ido yace are you mad? Ni in saka abu ka canja min zabi,ba komai ai zaka
aikata ai kafi kowa hauka da ciwon aka haife ka dalla bani key ya fisge key dinsa
ya wuce ya shiga motarsa ya tafi,Sohail ya juya ya wuce kitchen ya duba ba abubuwa
da yawa wanda yana bukata yayi amfani da su wajen girkin da zasu yi, yana shirin
fita ya siyo kawai Ibrahim ya dawo ya kulle kitchen din yace tunda baku da hankali
sai kunyi kwana bakwai baku ci abinci a gidan nan ba,sai dai ku siya da kudinku
useless ya juya ya tafi,Sahil ya kalli Sohail suka yi shuru basu ce kala ba.

Yau haka suka yini basu ci komai ba a gidan gashi su Ibrahim a waje zasu ci
hadadde abinsu,su kuwa basu ma da kudin ko sisi sabo da kawai komai sai dai su gani
an siya musu har sutura ba a basu kudin su siya an maida su kamar yara,idan ma
sunce a basu kudi baya wuce 1k, Sahil dazu kace zaka je shopping ina kudin? Sohail
yace ai kasan kayan abincin dama idan munje su suke transfer da kansu sai dai kawai
mu karbo a shagon,Sahil yace na tuna kuma gashi har yamma tayi likis wlh yunwa nake
ji, fita zamu yi ko zamu samu wani abu,Sahil yace nifa na gaji da wannan rayuwar
bro gidan nan zan bari na gudu kawai,Idan ka tafi ina zaka je? Wa kake da shi?
Sohail ya tambaya,Kazo mu gudu kawai,Sohail yace ba inda zanje ni,ina zani bamu da
hankali ance waye zai zauna damu a haka,Sahil yace to zan tafi na barka ni domin
gwara naje na bautawa wasu wlh,Sohail yace a dawo lafiya ma dinga waya.

Tafiya suke yi kawai a titi har sai da suka bar layinsu suka bar unguwar ma
baki daya,sai da suka shiga wata unguwar suka samu wani shago karami da shi kamar
container ce ma har sun wuce Sohail yace muje kaga wata a ciki kamar zamu samu wani
abu,dawowa suka yi da baya wata budurwa ce kyakyawa ajin karshe ta saka face mask
tana zaune a ciki,tana danna waya,ganinta da suffar musulmi suka furta salamu
alaykum cewar Sohail,Sahil kuwa ya hade rai yana gefe a tsaye.

Amsawa tayi sannan tace me za a baka? Sohail bai kulata ba, wani botikin gyada
fari me murfi dake gabanta ya fara yin kida da hannu biyu yana kida da bokitin,ta
tsaya tana kallon ikon Allah!

Dariya yayi ya tsaya yace to ya aka yi? Ya ake ciki? mene da ke na ci?

tace ga gyada,akwai biscuits,bread,cake etc gasu nan dai,Sohail ya kalleta suka


hada ido"
dariya tayi yanda yake leke leke a wajen yana kalle kalle yana sosa gashinsa,"
yace bamu da kudi ne magana ta Allah bamu ci komai ba,ki taimaka ki bamu bashi in
na samu zan kawo miki.
budurwar ta kare musu kallo tace guys kamar ku ace baku ci komai ba?
ke karki kara ce mana gayu mu ba gayu bane cewar Sahil yana hade hade rai, Sohail
yace bama gane komai ki bamu please
Budurwar ta lula tunanin oganta idan ta bada bashi,haka tayi shahada tace me zan
baku a ciki? Sahil yace Cake da lemo da gyada,Sohail yace da bread dinma da wani
abubuwan har da biscuits duk zamu ci,Mikewa tayi,amma Sohail har ya bude botikin ya
kwaso gyadar da yawan gaske ko irgawa baiyi ba,tace hey dan tsaya mana please.

Leda ta dakko ta dakko bread ya sa hannu zai fisge ta doke masa hannu ya janye
hannunsa da sauri ya harare ta, ta zuba musu cake manya biyu,ta zuba musu gyada
guda hudu ta dari biyar biyar ta saka musu bread kato slize bread,sai lemo
biyu,Sahil yace a kara da yogurt ta saka musu biyu ,sai da ta hada duk abinda suka
ce sannan tace da Sohail miko min wayarka"
wayar ya mika mata ta dakko littafi tayi rubutu tace sa hannu a nan,ya karbi biro
ya sa hannu tace kuje idan kun kawo kudi sai na baka wayarka.

Ran Sahil ya baci sarkin zuciya yace bata kayanta,Sohail yace kyaleta lets
go,suka juya suka tafi abinsu, har sunyi nisa Sahil ya dawo yace da budurwar marar
mutunci tare da sa yatsa ya dungure mata kai, ya juya ya tafi abinsa,dariya
budurwar tayi kawai tana cewa ikon Allah.

Kayan da suka karba a hannunta sai da suka yi kwana biyu bata ga keyar su ba shi
suke ci,sai da ya kare Sohail yace bari naje na karbo mana bashi,Sahil yana gida
Sohail ya tafi shi daya,budurwar yau tazo kenan da abincinta a flask cikin wata
leda Viva,taga Sohail tace kaine yau? yace ae bashi na dawo ki bani na bar miki
wayar tawa ki dinga bani abinci,kallonsa tayi tace wai kai ya sunanka ma? Yace
Sohail,tace ina dayan? Yayi mamaki data gane su,yace ta ya kika gane mu? dayan ai
yana da wushirya sannan bai son wasa baya fara'a,yace lallai kina da kwakwalwa,amma
ta daya kike zuwa a ajinku? dariya tayi,ya sunanki ke? No barshi na sani sunanki
Maheera,
A ina ka san sunana? ta furta tana kallonsa,yace bani alawa to na sha,robar alawar
ta bude ta bashi daya kyauta,ledar Viva ta mika masa tace dauki kaje gobe ka kawo
min flask dina,me zan baka bashi? Sai da yayi tunani sosai sannan yace Yogurt,ya
sake lulawa tunani yace cakes,yawwa ehmmm na tuna da lemo,sai da ta gama zubawa
yace da biscuits,cike da gajiyawa ta zuba ta bashi ya tafi.

Yana tafiya ta zauna tana mamakin anya kalau suke kuwa? Abinda suke yi sam
baiyi kama da na mutane normal ba a shekarun su,sunansa ta nanata "Sohail da Sahil"
uhm nice name ta jawo wayarta tana dannawa.

Sohail yana komawa abincin da Maheera ta basu a flask suka bude tuwon shinkafa
ne miyar egusi da nama yanka hudu a ciki,gashi tuwon da yawa zai ishe su ma,fara ci
suka yi da sauri da sauri yanda suka saba cin abinci basa amfani da spoon
yawanci,Sohail yace babar su ta iya girki,da alama makarantar koyon girki
tayi,Sahil yace ei ga dadin tsiya ba.

Adnan suna mamaki yanda suka kulle kitchen amma suke ganin su Sahil kalau da
su,takaici ya sa suka bude kitchen din ma,Sahil a zaune ya iske Adnan da Ibrahim a
dining suna duba files na aikin su,yana inda inda yana magana da kyar yace
Adnan...za...zan...tafi...unguwa..Ibrahim yaci magani yana masa wani irin kallo
cikin hargagi yace ina zaka je? Sahil yace kawai duniya zan shiga zan nemi kudi
nima....kafin ya rufe baki sun kece da wata mahaukaciyar dariya suna ta faman sheka
dariya,ya tsaya yana kallon su har suka gama dariyar,Adnan ya kalle shi sama da
kasa yace so a haka zaka nemi kudi? Dama kana da kwakwalwa? Ina kaga kwakwalwar
neman kudi?...suka sake kecewa da dariya,dama zaka iya tunani haka? Cewar
Ibrahim,dariya suka sake saki suna tafa hannu,Sahil gaba daya sai yaji gwiwoyinsa
sunyi sanyi,sai yaji ya sare gaba daya,ya tsaya kamar gunki,idanuwansa suka cika
taf da kwalla yanda suka sashi gaba suna ta dariya.

Adnan ne ya dakatar da Ibrahim ganin zai fara masifa,yace wait Ibrahim,kai Sahil
kudin mota za a baka? Sahil da kyar ya iya magana yace ae,Adnan yace wow Sahil you
get heart wooo,nan take ya zaro 20k yace gashi ya isheka kayi manage har ka samu
dai ka samu aikin yi,idan wahala tasa ka gaji zaka iya dawowa Abuja ga gida baka da
damuwa.

Ibrahim yace yanzu duniya zaka shiga kenan Sahil? Sai kuwa suka sake barkewa da
dariya,Adnan yace dan Allah jeka dariya zata kashe ni,Sahil ya juya jiki ba karfi
ya tafi.

Dakin su ya wuce direct yana shiga ciki ya fada saman bed yana kuka wiwi,Sohail
ne ya shigo ya same shi a haka,Shima bai ji dalili ba ya kwanta a gefensa ya fashe
da kuka har yafi Sahil dinma kuka,Sahil a hankali ya dago da kansa yana kallon
Sohail,Sohail yana kuka yace kar mu daina muci gaba dan uwana,Sahil ya daga kai
sama alamar suci gaba din,suka ci gaba da kukan su,sai da aka dade suna abu daya
sannan Sahil ya furta kai na gaji ya goge hawayensa ya jawo akwatinsa ya hada komai
nasa,Sohail yace yanzu tafiya zaka yi? Yace mene amfanin zama ni tafiya zanyi na
shiga duniya,gwara naje koma mene zai same ni ya same ni,to muje na rakaka.

Tare suka fito da Sohail suka shiga mota har tasha Sahil yace Lagos zan tafi
naje nayi ta kwana a kasan gada a haka idan abubuwa suka warware sai na maka waya
ka taho kaima kaji ko,Sohail yace to ba damuwa,har tasha suka je amma Sahil baida
kudin hawa mota me kyau dole ya shiga trailer wacce ake zuba yan cirani a ciki ruwa
da iska ya kare a kansu a hanya cikin kudi kadan.
Kudi ya biya aka rubuta sunansa da komai,yazo hawa trailer ya kasa,Sohail ya
tsuguna a kasa Sahil ya hau dokin wuyansa ya mike sannan Sahil ya kama motar ya hau
ya fada ciki,yana fadawa ya fada kan wata yar budurwa,yarinyar kuka take yi ta ture
shi gefe tace malam mene haka,sorry ya furta ya dago ya kalleta,gabansa ne fadi ya
ganta kyakyawar gaske yar fulani da ita,Jakarsa ya dauka tare da gyara zamansa a
gefen yarinyar ga kafadarsa ga tata,gashi motar wani kan wani ake hawa ba wani
Space dole a haka ake zuwa.

Sohail ne daga kasa a tasha ya kwalawa Sahil kira,Sahil ya mike tsaye ya daga
masa hannu suna dariya,yace karka manta in kaje ka kirani, inshaallah bro,ka kula
da kanka,Sahil ya daga masa kai,mutane suna ta hawa motar kamar kasa,Sahil mamaki
ya kamashi,gaba daya ba space a motar,wani akan wani haka ake a ciki,ko shanu baza
a saka haka ba,jikinsu har yayi futu futu da kura,ga wasu gaba daya wari suke yi,ya
rasa inda zai saka kansa a motar.

Wari ya isheshi,budurwar dake gefensa ya kalla ta toshe hancinta itama an


matse ta da kyar take shakar numfashi a haka motar bayan ta dame da mutane babu
kalar yaren da babu a ciki ta tashi ta hau kwalta suka fara tafiya.

Budurwar ce ta kwala ihu wani ya danno kanta tace wayyo zai kashe ni...zan
mutu.....tana jan numfashi da kyar, Sahil ne ya dagata tana daga zaune ya dawo da
ita saman cinyarsa,tace kai malam dan iska sauke ni,haka kawai ka dorani bisa
cinyarka,suka fara kokawa da Sahil yace dole ki zauna ai nan yafi Safe,kina safe
waje za'a kashe ki a nan wlh a banza,kina yar yarinya har kin san iskanci ne dalla
rufe mana baki ko na kwada miki mari,budurwar ta zaro ido,wanda suke kusa da su sai
dariya da ihu,wani dattijon banza yace wallahi kun dace kuma sai ace ma kanwarka ce
kuna kama,Sahil yace na fita kyau ai,Budurwar tace Allah karya ne inji wa ka fini
kyau?

Jifa taji anyi da ita a motar,wanda ta fada kan mutane sai da taji rauni,sabo
da bata san Sahil ba shi a tabin nasa zafi ne da shi,mutane suka sake
hankadota,kuka ta saki taji wuya,da kyar ta samu ta dawo wajen zamanta,Sahil shi
kanshi motar ta ishe shi ya rasa inda zai sa kansa,ya gaji da tsaiwa ya gaji da
zama.

Tausayi ya bawa budurwar tana satar kallonsa duk ya gigice kamar kansa da
motsi,ana haka ruwa ya tsuge da iska me karfi,jakarsa tayi sauri ta jawo ta saka
masa a cikin katuwar ledar da ta taho da ita yanda ruwa bazai taba ta ba,Suna
tafiya ruwa na zane su a hanyar lagos,sai da suka kwashe lokaci me tsawo ruwan ya
tsaya,mura da zazzabi suka kama Sahil,sai rawar sanyi yake,budurwar ta kalle shi
tace ka canja ko rigar jikinka ce,bata jira amsarsa ba ta zuge ta zaro riga me
kauri ta bashi,ya karba da kyar ya cire rigar jikinsa matan dake motar suka zubawa
surarsa Ido suna kallon cikar sura da zallar kyau na halittar Allah,rigar ya
canja,ta karbi wacce ya cire ta ajiye a gefe,dake ita da ledoji tazo manya ana ruwa
ta saka abinta,ruwa bai jikata ba sam.

Gyangyadi ya fara bai sani ba ya dora kansa a saman kafadar budurwar ,da sauri
ta juyo ta kalle shi zata yi magana ya dagata sai taga bacci yake sai kawai ta
hakura ta kyale shi,kowa ya zaci tare suke ma mata da miji ne,basu san kowa
tafiyarsa daban ba,wata mace dattijuwa tace gaskiya kinyi dacen miji 'yar nan gashi
kamar yaro shagwababbe da shi ba ruwanki,dariya ta kusa kwacewar budurwar sai dai
ta fuske tace uhm kawai, suna tafiya duhu yayi ba sallah ba salati ga uban duhu
suna tafiya a daji,Sahil baccinsa yake kawai shi,zamewa yayi a hankali cikin bacci
ya dawo da kansa kirjin Budurwar,tana jinsa gashi ko bra babu a jikinta, fuskarsa
ya dinga turawa cikin kirjinta kamar zai sha nonon uwarsa,duka ta dirka masa a
bayansa ya farka a hankali ya bude idonsa,sai lokacin ya tuna fa a mota yake.

Muryarta yaji me dadin saurare tace ka tasar min a jikina, tashi yayi a hankali
yace ruwa....dariya ya bata tace lallai ma wannan wai sai kace yaro mutum da gemu
kato da shi amma ni ina karama yake min haka, sai ka bari ai aje inda za a tsaya
sai ka siya ka sha,wai kamar ba namiji ba kai,shuru ya mata yana zaune a gefenta ya
sake komawa baccinsa.

Motar su ce ta lalace a dajin kowa tsoron hanyar yake,ana ta salati masu addua
suna yi amma Sahil shi baccinsa yake ma,sun dade a wajen kafin ta tashi suci gaba
da tafiya,sai cikin dare suka samu aka tsaya a garin yarabawa tasha suka firfito
kowa ya tafi neman abinda zai ci da masu sallah,budurwar ce kadai ta kasa fitowa
kafarta daya waje daya a ciki,Sahil yayi dariya sannan yasa hannu ya dakkota kamar
ya dauki tsinke ya direta a kasa.

Kunya ta kamata ta diririce, Masallaci ya nema yaje yayi sallolinsa itama haka
sannan yana fitowa ya siyi Apples,ya siyi ayaba,ya siyo naman kaza,sai ya siyo
yogurt da lemo ga ruwa da wuri ya dawo cikin motar sabo da kar a fara
turereniya,Ita kuwa budurwa bata da ko sisi na siyen komai kawai motar ta koma sabo
da itama bata so a dinga ture ture da ita wajen shiga,shi kadai ta samu a ciki ya
hau saman jakarsa ya zauna.

Kallonta yayi yace ya baki siyo komai ba? murmushi tayi tare da zama tace
banda kudi ni,yace tab rayuwa sai da cin abinci,ki dinga cin abin kanki,shi yasa
bakya ci gaba kullum jiya i yau gaki nan tsiya tsiya sai son kudin tsiya, kici a
jikinki baza kici ba sai shegen asusunki a boye,Ido budurwar ta zaro duk abinda ya
fada gaskiya ne,bata kashe kudi,indai abu ne wai tasa kudi ta siya sabo da ta ci to
baza ta siya ba kuwa sai dai ta tara kudin a asusunta.

Abinda ya siyo ya mika mata gaba daya yace gashi ki cinye,baki ta bude tace kai
fa? Yace kici kawai in kin rage ni na ci,tace no ai baza ayi haka ba to muci tare,
a hasale yace kici dalla ko na kwashe na zubar,mamaki ya kamata,ita wannan wanne
iri ne,haka ta fara ci duk abinda take sai da taci da yawa tace na koshi alhalin
bata koshi ba.
Yace baki koshi ba kici karya kike,"hmm" kawai tace taci gaba da cin abinta
sannan tace ya sunanka wai? Yace "Sahil",tace ni kuwa...katseta yayi yace sunanki
Islaha,baki ta bude tace a ranta ko ba mutum bane wai,amsa taji ya bata yace mutum
ne mana.

Tsoro taji yace ki daina tsoro mutum ne,ido ta zaro ta kasa cewa komai,yace zan
iya fada miki asalinki gaba daya da tarihinki tsaf, tace to fada min naji.
Asalinki ku ba hausawa bane wani yare ne ku can yankin Taraba State wanda kamar
fulani kuke da shanunku da komai amma ku ba fulani bane kuma,iyayenki yan Taraba
ne,Babanki mahaifi sunansa Sule mamanki sunanta Halisa ana kiranta Nany,kuma ke
kadai suka haifa sannan sun rasu, a hannun kanwar Mamanki kika taso a taraba,karshe
itama mijinta ya rasu ta fara tuwo tuwo,daga nan ita da yaranta data haifa mata su
uku namiji daya gaba daya da yaran nata karuwanci suke yi.

Cikin yaranta babbar yarta Shema'u ta zama me kudi sabo da karuwanci,ita kanta
kanwar mamanki da sauran yaranta sun zama masu kudi sun koma lagos da zama a nan
suke rayuwa ba ruwan su da sa ido na hausawa da dangi,kece anyi anyi a fara koya
miki kema ki fara kinki yarda,shine ta maida ki yar aikinta wanda yar aiki ma ta
fiki daraja a wajen su,azaba suke gana miki,yanzu ma aikenki tayi kauyen ku kika
kai sako shine zaki koma,sannan shekarunki ashirin da biyar 25, sannan abinda yasa
suke so kema ki fara sabo da kina da kyau matuka gaki da diri me kyau komai naki
yayi,duk wani namiji zai so ace ya mallake ki.
Kina son white color,kina son sakwara da miyar egusi,kina son wankan
shadda,sannan period 4days kike yi....kuma....Islaha taji tonon sililin yayi yawa
komai ya fada ba karya a ciki,ta dakatar da shi tace naji to,yace sannan kin gama
secondary kin shiga NCE sai suka daina biya miki dole kika hakura da karatu.

Mukus tayi duk abinda ya fada ba karya ciki,abincin ta mika masa tace na
koshi,lokacin ya karba ya fara cin abinsa,ido Islaha ta tsura masa tana kallonsa
kamar mayya,na miki kyau ne? ta tsinci muryarsa ya furta ba tare da ya kalle ta
ba,da sauri ta dauke kanta ta fara wasa da yatsunta tana yarfe hannu,dariya yayi ba
shiri tare da kamo hannunta yace mu gani ciwo yake,a hankali cike da kunya ta zame
hannunta,tambaya ya jefo mata ke baki da kayan wasa ne muyi wasa? Cike da mamaki
tace wanne irin wasa? A gidan ku ba a siya miki doll Baby su Teddy,murmushi tayi
tace da girman nawa? baki ya turo,jajayen lips dinsa suka birge ta,kanta ta sadda
kasa sabo da kunya,sun dade a haka kafin mutanen motar su dawo suka ci gaba da
tafiya abin su.

Sai washe gari da safe suka isa lagos,Islaha bayan sun sauka,ta tambayi Sahil
ina zaka kai? yace gari mana ya juya dauke da jakarsa yayi tafiyarsa ko waigowa
bai sake yi ba,baki ta tabe tayi tafiyarta itama.

Gidansu ta nufa a taxi tana zuwa Kanwar Mamanta da suke kira da Aunty ta ga ta
shigo da safe,ranta a bace tace uban me kika tsaya yi Islaha baki dawo da wuri
ba,aikin gidan nan uban wa zai miki? Islaha cikin tsoro tace kiyi hakuri kin san
motar da kika ce na shiga bata da sauri ga tsaye tsaye shi yasa,ke dalla rufe mana
baki cewar Khairat yar Aunty ta cikinta,a kalla zata kai 30yrs,kanwarta Khalisat ce
tace wannan fa sam bata da saiti,Islaha tayi shuru dai ita,Aunty tace ai kuwa ga
aiki nan ya taru sai ki fara,a gajiye Islaha take amma haka ta fara aikin gidan.

Gidane me kyau cikin estate duk gidajen layin iri daya ne,gidan yana da kyau a
me rufin asiri dai a lagos duk da unguwar ta masu karamin karfi ce amma tayi
kyau,Islaha sai da ta gyara gidan tsaf ta gama komai tazo ta dora girkin
dare,Khairat tace wankin namu fa sai yaushe? Zanyi gobe inshaallah,da sauran rana a
gari madam ki wanke mana kaya,Khalisat ce ta kawo mata kaya ta jibge,Islaha haka
tana girki tana wankin sai da ta gama tas,Allah yasa ma kayan ba dirty,sai da ta
gama komai sannan ta samu tayi wanka ta canja kaya cikin riga da wandonta yan
gwanjo amma sun mata kyau sosai abinka da me kyau,abincin ta ebo taci ta koshi,tana
palo Yaseer ya shigo babban dan gidan Aunty,Aunty tace Yaseer bana son wannan
yarinya r da kace zaka aura Rukayya take ko,Yaseer ya kalli Mahaifiyar su ya furta
amma kin san an sa rana fa!

Aunty tace ai baza ka aure ta ba gaskiya na tambayi malamai na sunce sam ba


Alkhairi a auren ku sannan indai ka aureta sunce kai da arziki sai dai kaga ana
yi,nasan tun tana karama kuke soyayya hasalima ta samu mazajen aure amma ta makale
sai kai ta dinga jiranka tun bamu da kudi gashi muna da rufin asiri amma baza ka
aure ta ba,malamai sunce babu alkhairi.

Islaha tana jinsu tace amma ai ba wanda ya isa ya hana wani arziki a
duniya,Allah shike bayarwa shike hanawa,Aunty rankwashi ta zubawa Islaha tace wlh
idan ina magana kina sa min baki sai naci ubanki, shuru Islaha tayi tana jinsu har
Yaseer dinma katon jahili ya yarda da abinda uwarsa ta furta,yace to Aunty ai kuwa
sai dai kije wajen Malamai a cirewa Rukayya so na a ranta,idan ba haka ba ta ya zan
iya cewa na fasa? karka damu wannan me sauki ne za a sa taji bata sonka da kanta
tace ta fasa,ya furta to shike nan tunda ba alkhairi me zanyi da ita yanda nake so
nayi kudi ido rufe.

Sahil machine ya hau yace kasuwar 'yan tumatir zaka kaini,me machine kuwa ya
kaishi babbar kasuwar tumatir dake Lagos,hausawa da yare ne damkam ana ta hada
hada,Sahil ya tsaya rataye da jakarsa yana kallon abinda akeyi,gashi su baza su iya
aikin karfi ba,wani ne a ciki ya kalli Sahil ya ganshi ya dade a tsaye,ya zaci wani
shahararren me kudi ne yazo daga kasar waje zai siyi tumatir,da sauri ya karaso
gabansa yace

Good day sir, Hausa Sahil yayi yace sannu da aiki,ashe kana jin hausa ai na zaci
daga Tunisia ka sauka,Sahil yace no,okay kaya zaka siya ne? Mota nawa kake so?
Sahil ya kalle shi yace aiki nazo nema ni dan gidan malam shehu ne,mutumin ya
kalli Sahil sama da kasa yace aiki? Irin wanda muke yi na karfi na sauke tumatir
daga mota?
Sahil ya amsa da ae mana shi,ai gidanmu ma sabo da bani da kudi idan aka ga hadari
ya taso har danyar daddawa ake kaimin dakina na kwana sabo da kasan life no balance
at all,yanzu idan baka da shi a gidanku sai uwarka ta mutu baka sani ba.

Wanda suke magana me suna Aminu dariya ya dinga yi yace gaye kamarka sabo da
talauci sai a kai daddawa dakinka na kwana?
Sahil yace sai dai in hadari bai taso ba amma yana tasowa za a kawota a faranti.
Mutumin yace au baka da ko sisi a haka?kalli fa kayan jikinka sai me kudi ke sa
irinsu"
Sahil ya furta ae nema dai zanyi,dariya mutumin yayi sosai yace kalli kalarka fa
zaka iya kuwa? Zan iya mana,mutumin yace sunana Aminu to kaifa? Sahil nake,yace
indai aikin wahala ne baya wahala zaka samu,ka sauke duk kwando daya 50 Naira.

Sahil yace zanyi haka,Sahil suna da karfi wanda bana mutane ba ma amma na aikin
banza da anzo wanda mutum zai amfani kansa da shi sai lalaci yazo ya lullube su
karfin bazai zo ba sam,haka ya ajiye jakarsa ya ratsa ta cikin kwandunan
tumatir,Aminu yace waccen motar zamu je,suna karasawa Sahil ya shige cikin katuwar
trailer a dole ya fito neman kudi,kwandon tumatir ya duka zai daga amma yayi yayi
amma ya kasa,matasa dake wajen suka dinga ihu da dariya.

Sahil zuciya ya sake yi ya yunkura zai dauka amma yin duniya ya kasa yana matsawa
kansa ma sai ya fada saman sauran kwandunan,mutane wannan ya ja hankalinsu aka taru
ana kallonsa yana ta faman nishi da haki,mutane suna ta tunanin hutu ne ya masa
yawa kawai duba da kalar jikinsa ana gani an san ajebo ne,masifa suka fara masa ya
sakko musu daga mota,haka ya sakko kawai jikinsa a sanyaye.

Wajen masu abinci ya nufa sabo da tun a mota bai ci komai ba,ya samu ya siyi
jullof din shinkafa da yankan namansa biyu ya zauna yaci ya sha pure water sannan
ya mike ya mike ya koma cikin kasuwar.

Aminu ya kira ya tambaye shi dan Allah a ina kuke kwana? Aminu yayi dariya tare
da nuna masa wasu dakuna na langa langa yace kaga wannan dakunan a haka duk shekara
kasan nawa muke hadawa muna biya? Sahil ya tambaya nawa? Yace dubu dari biyu kalli
dai dakine kamar container,a haka ma munfi mu ashirin a ciki wani kusan a kan wani
yake kwana,sannan ka jira kaga wasu a inda suke kwana.
Sahil yayi mamaki ya koma gefe ya zauna,ga hadari ya hado sosai,yana zaune aka
fara yayyafi sai yaga duk wasu suna saka rigar ruwa ga dare yayi wasu a cikin kurar
ruwa da suke turawa ta eban kaya a ciki yaga sun saka kwali sun kwanta,wasu yan
achaba a saman machinan su suka hau da rigar ruwa suka kwanta ruwa na dukan su,abin
babu kyan gani yanda wasu a hausawan mu da gatansu da komai amma suke tafiya suna
zubarwa da arewa mutunci,baza ka taba ganin yare a haka a wulakance a arewa ba da
sunan neman kudi amma yan arewa duk inda kaskanci yake suna can,kana magana ace
neman kudi ne,neman kudi sai mutum ya jefa rayuwarsa a hadari bayana a arewa ma
wani yana da jarin da yafi zamansa a can.

Sahil dare yayi yana wata yar runfa a tsaye ya fake ga mutane sunyi yawa,wasu
yan shaye shaye ne suka zo da gudu suka hankado Sahil cikin ruwan suka tsaya a
rumfar babu inda Sahil zai fake gashi dare yayi ga ruwa ana tsinkawa kamar da bakin
kwarya,waige waige ya fara cikin ruwan amma ba inda zai shiga,gani yayi babu
amfanin tsaiwarsa kawai yabi ta cikin ruwan yana tafiya wanda bai san inda ya dosa
ba,ruwa na dukansa yana ji wayarsa tana ringing yasan Sohail ne ke kiransa yaji ya
sauka lafiya ba damar daga waya.

Yana ta tafiya cikin ruwan har ya bar layin ya shiga wani layin me kyau wanda
bai san a ina yake ba,dai dai wani katafaren hotel yazo zai dan fake a jikin
katangarsu, cikin tsararen hotel din ya kalla ya samu ya rakube ya fake a jikin
wajen ya tsuguna! a haka yayi baccinsa har rana ta fito bai sani ba,karar mota ce
tasa ya bude idonsa,kafafunsa har kumbura suka yi sosai,da kyar ya iya mikewa tsaye
ya sake kallon cikin hotel din kenan

Ido ya zaro yana kallon Islaha wacce suka zauna a mota budurwa tsaleliya cikin
damammun kaya, bum short ne a jikinta da guntuwar riga gaba daya ta kudundune
jikinta sai kakkare jikinta take yi tana jin kunya wanda da kyar take tafiya da
alama bata saba ba,ga duwawu kaya guda komai ya ji,a gigice ta fito ta fice da
sauri bata iya kallon kowa ta tare taxi ta fada ciki suka tafi,Sahil yana tsaye
yana mamaki

Ya furta wonder shall never end,so duk mata haka suke wannan wato mummunar
dabiarta ce ashe amma a haka kamar ta kirki,tsaki ya ja yana mamaki yace ahhh amma
na dorata a cinyata harda wani ita ba haka take ba,shi yasa ni fa dama can jinina
bai hadu da mata ba,indai akace mata ne to ba ruwana da su,Allah yasa nidai bana
jin sha'awa,mata suje da abin su gwara da Allah yayi ni haka Dagger din bata aiki
thank God ya juya zai tafi kenan sai Khalisat yar uwar Islaha ta fito cikin
tsaleliyar motarta fara kal"

Sahil ta kalla ta furta wow kaga wani handsome,harshenta ta zaro ta lashi


labbanta tace wannan idan na mallake shi aurensa ma zanyi,zan iya cinye wannan
danye wow,da gani dan me kudi ne ba karya,anya ma kuwa yasan hausa,Sahil kuwa waya
yake da Sohail bai ma san me take yi ba sai ji yayi an masa horn,bai ko juyo ba sai
da ya gama wayarsa ya juya zai tafi Khalisat ta sauke glass kasa tana murmushi,ba
karya ta zuba kyau doguwar rigar silk material ce a jikinta kusan tsirara tsirara
haka take komai ana gani,Tunaninta zata birge Sahil sai taga ko a jikinsa kamar
namiji ya kalla.

Murmushin da tasan yana kara mata kyau tayi cikin yanga da salon lankwasa murya
ta furta zan iya dropping naka? Sahil da sauri ya furta no,please ta sake cewa tana
wani shagwaba, gashi yana ta tunanin ko aljanun nasa zasu fada masa wace ita amma
shuru,haka Islaha ya kasa gane gaskiya wanda a aikin banza kawai sai dai suji an
fada musu abu amma wannan karon shuru ba labari.

Motar ya bude a fusace ya shiga baya yace muje,tace gaba zaka dawo sai kace ka
shiga taxi
Yace haka nake so idan baza ki iya ba sauke ni,shuru tayi ta ja motar ta hau
titi tana tambaya ina zan saukeka? Kafin ta rufe baki yace kasan gada,baki ta bude
tace wacce gadar? Ya furta inda mutane suke kwana, Khalisat tayi mamaki sannan

Tace wai baka da gidan zama? Ya furta ae neman kudi nazo cirani,Wani dadi taji
itakam tayi tsuntuwa,tace no ai baka samu aikin ba ko? Yace yeah, Alright muje
gidanmu zan baka daki ka zauna har na wani lokacin da Allah zai sa ka samu wajen
zama? Ko godiya Sahil baiyi ba ya furta Okay da fatan dai ba karuwanci zanyi ba?
Domin kudin karuwanci da za a biyani bazai dauke ni ba,yana wani fisfisga shi kadai
yana muzurai,dariya khalisat tayi kawai itama kyakyawa ce mashaallah komai na birge
maza tana da shi.

Gidansu me kyau ta nufa da Sahil ba wani shayi ko dar dar, suna zuwa tayi
parking ya fito ya kalli gidan yace gidan ba laifi,Khalisat tana murmushin jin
dadi,ciki suka shiga tare.

FREE PAGE

400 NE

0175487861
Asmau Garba Muhammad
Gtbank

'Yan Niger
+22790795939

AsmaBaffa
08061929616
[7/17, 3:17 PM] Asmabaffa: https://www.arewabooks.com/chapter?
id=6687e323e3651b348bbd12f6

🪸MUMMUNAR DABI'A 🪸

11-15

Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA NE GA 'YATA TASNIM

Page naki ne
Mrs Chief

MASU AUDIO BAN YARDA A SATAR MIN NOVEL A JUYA BA,DUK WANDA YA DORA A CHANNEL SAI AN
SAUKE.
Gidan nasu yana da kyau sosai Sahil har palo Khalisat ta shigar da shi
wanda palon ya gaji da kyau da tsaruwa, murmushi tayi tace sit,zama yayi ta shiga
kwalawa Mum kira tana cewa Aunty dake duk ta hanasu kiranta da Mama ko Mum kawai
Aunty ce kar su kara cewa ita ta haife su,Aunty ce ta fito tare da Khairat,suka
zubawa Sahil ido suna kallonsa,Aunty ta hadiyi yawu dama ace saurayinta ne,itama
Khairat haka,Aunty tana yiwa Sahil kallon duniyanci tace wannan fa? Khalisat tace
he is my friend zai dan zauna damu for a while kafin ya samu gidan zama,ai dakin
nan a gyare yake? Aunty ta saki murmushi tace a ranta da alama akwai kudi a
hannunsa.

A fili ta furta ba damuwa a gyare yake ai ki kaishi sai a kawo masa abinci da
ruwa, yaje yayi wanka ya huta,Khalisat tana murna ta riko hannun Sahil tace lets
go,hannunsa ya fisge tare da hade rai ya mike ya bita har bedroom lafiyayye me
dauke da gado da sip da mudubi tare da toilet dakin yayi kyau,ac ta kunna masa tace
kayi wanka bari naje nima zanyi wanka sai na sa yar aiki ta kawo maka abinci,Sahil
dai yana kallonta da mamaki abinda suke masa ba tare da sun san shi waye ba.

Bayan ta fita yace karfa ko yan mafia ne ban sani ba,no..no..kaina yafi karfinsu
baza su iya dani ba,Allah bazai basu iko a kaina ba,wani tunanin ya sake ya furta
kaiiii....karfa naji na bace kar a siyar da kaina,su din banza nafi karfinsu yace
sannan ya shiga toilet abinsa,wanka yayi ya fito ya saka kayansa kanana riga da
wando,Navy color ya sha uban kyau sosai, gefen rigarsa ma da yar laimar ruwan jiya
da ya zane shi.

Knocking yaji anyi,yace come in,a hankali aka turo kofar tare da shugowa dauke
da sallama a bakinta,Sai yaji kamar yasan muryar,Islaha ce ta shugo dauke da tire a
hannunta na abinci da ruwa,sanye take da Hijab har kasa tana wani dari dari,a
hankali ta dago kanta suka yi ido biyu,yace you.....yana nunata da yatsa,kanta ta
sadda kasa fuskarta dauke da murmushi ta dago a hankali

Fuska taga ya daure kamar bai taba saninta ba a duniya,mamaki ya kamata


matuka,ransa a bace yana mata wani mugun kallo yace kalle ki kamar ta kirki a
haka,munafukar banza,ido ta zaro tana kallonsa,yace ban san me ke damunku ba matan
wannan zamanin masu fuska biyu,a fili kuna nuna ku na Allah ne a badini ashe kuna
da wata mummunar Dabia da ba san da ita ba,daga yau karki nuna kin sanni a
duniya,kuma duk wani abu nawa karki sake kice zaki taba,avoid me duk inda kika
ganni karki sake ki kulani kuma karki taba min abu,abincinki dauki ki kara gaba
bana bukata.

Islaha tsoro da mamaki ya kamata,ita tasan bata masa komai ba ita,a tsorace ta
juya! Ya ja mata wani wawan tsaki tare da furta stupid,yana uban huci ya kwanta a
saman bed din,tuni Islaha ta fita ta bar masa dakin tana mamaki me ta masa sannan
me ya kawo shi gidansu a ina yasan Khalisat,jajayen lips dinta ta turo gaba tace
koma mene zan gani wlh Allah yasa ace dan iska ne me neman mata wallahi sai ya hadu
da rashin mutunci na sai na fito da sabuwar bad character dina a gidan Nan,kowa sai
yasan Islaha bata da mutunci,kowa sai yasan ni ba a gaban uwata na taso ba,kuma sai
an san ni yar tuwo tuwo ce ta raini ni,badai suna bada gabansu ba maza suna
ishiriniya abinsu,mace kawai ki bada jiki namiji ya dinga ishiriniya a kanki zan
gani ta ja kwafa.

Khalisat ce ta shigo dakin Sahil cikin wata gown guntuwa maroon wacce da kadan
ta rufe duwawunta,Sahil dai kamar yaga namiji again,tace ya an kawo maka abincin?
Yana kakkafe idanuwa yana masifa kamar ubanta yace wata banzar yarinya ce ta kawo
bana so ta sake kawo min abinci,Khalisat tace Islaha ce yar kauye,ai wannan
yarinyar dabba ce gaba daya,Sahil nan take yace a'a fa Allah ya gani dai mutum
ce,Khalisat zata sake magana yace ba ruwana da ita ni kawai kiyi shuru,sam baya so
a zageta,Khalisat tace yar iskar yarinya.....kafin ta rufe baki ya fara waka dan
kar ma yaji yana kida da bakinsa gijib... gijijib...tsayawa Khalisat tayi tana
jinsa tana dariya wakar tasa ta hausa ce yake yin abarsa,Juyawa tayi tace bari na
kawo maka abincin da kaina ta fice.

Dauke da abincinsa ta dawo a plate jullof rice ce ta sha hadi da naman kaza ga
ruwa da lemo,zama yayi ya fara ci Khalisat ta zauna a gefensa tare da dafa
kafadarsa,ya zame a hankali yana cewa hannunki nauyi,kasar da aka halicce ki da ita
wajen nauyi aka ebo,,kyale shi tayi tare da furta sorry tana lasar labba,yace ko ci
zaki yi ne? da sauri ta furta a'a,sai bayan ya koshi sannan ta mike ya gabatar da
sallolin da ake binsa har ya idar,Khalisat tana zaune a gefen bed din tana
jiransa,juyowa yayi ya kalleta tare da furta zanyi bacci,Khalisat ba kunya tace zan
iya taya ka kwanciya? idanuwa ya zaro sai da ta tsorata tun kafin yayi magana a
fusace ya mike ya jawo jakarsa yace ki tayani kwanciya a wanne dalili raping dina
zaki yi? Mikewa tayi tana bashi hakuri I'm sorry kwanta akan yar wannan maganar
zaka tafi? Kayi hakuri kwanta abinka,ta fice da sauri sannan ya kwanta abinsa.

Sohail....Adnan ya kwalawa kira....Sohail...ji wannan banzan yaron ina


kiransa,Sohail ne ya fito daga kitchen da sauri,fada Adnan ya hau yi yace sabo da
hauka kana ji ina kiranka,Sohail kansa ya nuna yace oh dama kirana kake yi? Uwarka
nake yi cewar Adnan.
Sohail yace ai ta mutu Maman,
Ba wannan ba ai ba ita ta haife ku ba,uwarku arniya ita nake nufi, Sohail yana
tsaye sanye da jean black da riga arsh color yace kai ka santa ma ashe?
Dama muna da uwa? Kuna da ita arniya ba Adnan ya bashi amsa.
Arniya ce? Taji dadinta ba ruwanta da kishirwar azumi,ta tsula tsiyarta kawai ba
komai.
Adnan ido ya zaro yace uwar taku? Sohail yace kai mu bamu da uwa.

Yaya Adnan nayi sabuwar kawa me kirki,Adnan ransa ya baci nan take da kyar ya
danne yace wace?
Wata ce sunanta Maheera kyakyawa ce sosai.
A ina take? A gaban layin nan take,Adnan yace lallai ya kamata na ganta mu gaisa
Sohail yace ba damuwa zan rakaka Sahil ma ya santa shima kawarsa ce mu kasan mace
daya muke bukata,Adnan yayi dariya yace gaskiya ne mazaje yan biyu masu mace
daya,Sohail yace ae mun sasanta kanmu ni da Sahil ko mace ta rungume shi nima sai
tayi min nawa,Adnan yace nifa? Sohail yace direct yace a'a banda kai wlh ka kula
mana mata sai gawarka.
Adnan ya jinjina kai yace matata zata zo anjima kayi girki me dadi,ba damuwa na
kusa gamawa ma cewar Sohail"
Adnan yana takama ya juya ya haura sama abinsa.

Zuwa yamma Zayna ta sauka a jirgi,Adnan da kansa yaje ya dakko ta,tayi kiba ta
kara kyau ga wanka yabi jiki,Sohail yana shirya dining ya gansu Adnan ya rungumo
kugunta sun shigo,Sohail ya kura mata ido yaga Zayna ce,mamaki ya kamashi da alama
itace matar Adnan din.

Nunawa tayi bata san ma Sohail ba,juyawa tayi ta kalli Adnan tace Baby wannan fa
na tuna ashe fa kaninka ne,Sohail ko a jikinsa yayi murmushi yace yaya dama ita ka
aura?
Adnan kiss ya mannawa Zayna a kumatu yace ita ce,Sohail yace sannu Aunty ya juya ya
wuce part dinsa cike da mamaki,wai Adnan ya auri budurwar su shi da Sahil,baki ya
tabe yace suji dadinsu ni ina ruwana da Allah zai sa ma ni kuka yazo min ai kwana
zanyi ina yi naji dadin jikina,ai kuka wani Exercise ne daban,kuka duniya ne,dama
shi Sohail haka kawai ma in kan ya motsa kuka yake shi kadai haka kawai.

Bayan Zayna ta huta dining suka zauna,Ibrahim,adnan da Zayna suna kwasar girkin
Sohail suna hira abin su,Sohail ne ya fito ya wuce su da sauri,Zayna ta masa banzan
kallo ta ja tsaki,bai ma san tana yi ba tuni yayi gaba,yana tafiya da uban sauri
kamar zai tashi sama,wasu a layin sun sanshi sosai suna mutunci,sai magana suke
masa amma sai dai ya daga musu hannu,ka rantse wani mummunan abu ne ya faru,bai
tsaya ba sai da yaje shagon Maheera har ciki sannan yaci birki,ta dora kanta a
table tana danna waya ya daki botiki da karfi ta tashi a firgice,dariya yayi yace
nine,tace Oh Sohail ko sallama,kujera ya ja ya zauna yana so ya bata labari,yace
bari na baki labari kinga ni gidanmu....gidanmu ..uhmmmm....katseshi tayi tace dan
Allah ka kyale ni da surutun nan bana ganewa damuwa ta min yawa ka rabu dani,yace
abu zan fada miki,tace no...ni kyaleni bazan ji ba kai labari ma kafin ka bawa
mutum sai ya tsaya wahalar saurare.

Shuru yayi,wasu suka shugo siyayya ya mike ya fara basu amma duk ya rage kudin
abin dari biyar sai yace ku bada dari biyu an muku ragi dole mu kawo canji a kasar
nan mu da araha zamu siyar,Maheera ta mike da sauri ta fisge ledar kayan tace ke
kudinki ba haka ba ta lissafa kudin da kanta,matar tace me shago ya mana kyauta ki
hana yar bakin ciki,Maheera tace ba shagon sa bane malama ta karbi kudinta ta basu
kaya suka fice suna Allah wadai da Maheera me kudi yayi kyauta ta hana.

Sohail ya kalli Maheera yana murmushi ya ja hancinta yace to bani alawa,kara


maheera ta saki ta bige masa hannu tana shagwaba tace da zafi fa,Alawar ta ebo tace
yau biyar zan baka ta mika masa ya zuba a aljihu tare da bare daya ya sa a bakinsa
yace na gode na tafi gida.

Sunansa ta kira tace "Sohail"


Amsawa yayi ya dawo ya zauna tace ina cikin damuwa yau,na rasa wanda zan fadawa
naga munfi kusa da kai, sai ya nutsu kuwa yace ae ina jinki tell me.
Tace mamana tana da lalura tana Sule ja a gida ina da kanne biyu mace da namiji
nice nake kula da karatunsu,Mamana ciwon sugar ne da ita ina shan wahala ta kashe
kudin magani,gashi aikin nan da na samu oga ya sani a shago baya biyana akan lokaci
gashi babu abin kirki a salary din,ga kula da kaina ga yan gidanmu,ubanmu tun muna
yara ya rasu,yanzu aiki nake nema wanda ya dan fi wannan ko wanke wanke da shara ne
indai yafi wannan albashi zanyi,Sohail ya nutsu yanzu.

Ya dafa kafadarta yace akan wannan kike damuwa? Ki kwantar da hankalinki indai
aiki ne zaki samu,zan nemo miki,kinyi karatu? Tace na fara university amma kasan
bani da kudi dole na hakura yanzu ni kannena nake biyawa kudin makaranta,Sohail
yace to za a samu wani karki damu kinji ke da kike da Allah,wannan ba matsala bace
ki kwanta kiyi bacci in ta kama ma kina shan giya ki sha abarki aiki zaki samu
Inshaallah.

Dariya Maheera tayi sosai da sosai,tace na gode to,aljihunsa ya duba ya ciro 4k


yace suke nan gareni ragowar kudine da naje kasuwa siyo nama ungo ya mika mata,ta
saki baki tana kallonsa yace karbi kyauta na baki kawarmu ce ke,
ta karba tana ta godiya kamar yasan bata da ko sisi sannan idan kana wajen wani a
zaune dole ka dinga yiwa kanka wani abin, tace Sohail na gode,ya sake duba
aljihunsa ya ciro naira ashirin yace ah sorry ungo wannan ma hada da ita.
Ta karba tana dariya tace na gode.
wajen shagon taga ya leka ya dawo da leda baka a hannunsa ya ajiye mata a table.
Mene kuma? Ta tambaya
Yace duba ki gani yana tsotsar alawa me tsinke,dubawa tayi taga naman kaza soyayye
da yawa a ledar zai kai kaji biyu,ta zaro ido tace amma tun dazu baka bani ba kuma
me yasa ka ajiye a waje jikin kofa?

Yace ai bana so ki gani surprise zan miki kuma na manta badan kin tuna min ba da
tuni na tafi na barshi a wajen,tace kai ka soya? Yace ae,na gode sosai,yace bani
daya a ciki naci karki ce na saka miki wani abu"
Maheera harararsa take tace ai nawa ne bazan baka ba,Murmushi ya fice fit ko
sallama bai mata ba.
Tayi dariya kawai ta fara cin naman.

Yana komawa gida ya iske Zayna tana masifa a palo tace da Adnan ni gaskiya a
kawo min mace yar aiki wacce zata dinga yi min girki da wanki da sauran hidima
ta,shi Sohail ya muku naku,ni bazan iya cin girkin namiji ba,Adnan yana rawar jiki
yace za a nemo yar aikin tunda haka kike bukata,Sohail yana ji yace yaya akwai wata
ta iya girki sosai indai za a biyata albashi me kyau a kawo ta.

Zayna tace karka kawo mana mahaukaciya irinka fa,Sohail yaji zafin maganar amma
bai ko nuna ba yace ta iya fa, ina fada muku zan kawo ta nan ta fara yi muku na
gwaji,idan kuka gwadata in yayi shike nan,Adnan yace ba damuwa tunda haka kace a
kawo ta gobe tayi muji,yace an gama.

Zuwa yamma likis Sohail ya koma shagon da Maheera take da sauri, Maheera tana
zaune tana shan lemo da da naman da ya kawo mata, Sohail ya fado ciki yana sosa
sumarsa wacce taji aski irin na kwallayen shegun gari,gashinsu kamar na mata
daurewa suke da ribbon amma sun kwashe gefe da gefe an rubuta sunansu a gefe daya
an saka Sohail daya barin Sahil,shima Sahil yaka yayi,Daddy yayi yayi su gyara
sunki amma ba karamin kyau ya musu ba sai dai a al'adar mu ta malam bahaushe za ace
ba tarbiyya.

Maheera ta kalle shi tace Sohail ya ka dawo?


Yana murmushi yace albishirinki
Goro ta furta tana kallonsa"
Yace kin samu aiki amma sai dai ba irin na classy girls bane irinku,girki ne zaki
dinga yi,matar Yaya tace baza taci girkin namiji ba,shine nace akwai wata zata
yi,kin san nawa zasu biyaki duk wata? Maheera tace nawa?
Yace dubu dari,idan kina aiki me kyau zasu iya kara miki ma.
Zumbur Maheera ta mike tana tsalle da murna kamar yarinya,tace wannan fa dubu
ashirin yake bani duk wata!
Yes zanyi zanyi ba matsala,wayyo dadi Alhmdllh Allah na gode maka,tana murna tace
Alhmdllh.
Gaskiya Sohail kai mutumin kirki ne na gode.

Sohail yace na fada miki ai ko kina shan giya ki sha abarki kiyi bacci aiki zaki
samu,gobe zamu je zaki musu abinci da yamma zasu yi miki test in kinci shike nan an
dauke ki,kuma nasan ma kin iya girki!

Na iya girki sosai Inshaallah zanyi kokari zan dage Sohail.


Sohail ya furta aha Sahil yace a gaida ki,kin san da za a haifo mu a tare muka fito
duniya ba wanda ya riga wani zuwa,Maheera ta iya bi da Sohail ta kalle shi tana
dariya tace Allah? Aradu ya furta yana daukan alawa

Dariya ta sake saki tace amma yau naji dadi come ba zato Sohail yaji anyi hugging
nasa,ido ya zaro da sauri ya janye jikinsa tare da ja baya yace mene haka? Sahil fa
baya nan,to wlh shima sai kin masa na rantse.

Ido Maheera ta zaro tana murmushi tace Sahil din? Sohail yace ke ba a wasa damu
na fada miki sai kin masa shima ya hade rai,Maheera tace to never mind zan masa
shima amma ai kaine abokina Sohail ka gane?
Ni bazan gane ba kawai malama zamu yi fada,Sorry to zan masa shike nan?
You promise? ya sake tambaya,tace yeah,yatsa ya mika mata yace mu kulla,ta kawo
nata suka kulla ta furta shima sai an yiwa Sahil? yace kamar da kasa.

Juyawa yayi zai tafi ta ruko shi tace na sallameka ne? Ban gane ba sai ma kin
sallame ni? Ke mace fa ni baza ta juya ni ba in fada miki gaskiya 'yar nan, Maheera
tayi dariya tace to fa,har ya tafi ya dawo yace na fasa tafiya zo muyi game?
tace wacce iri ba kayan game a nan.
Wasan yar buya buya zamuyi,okay ka bari sai gobe idan naje test sai muzo muyi kaga
ko Oga ya kama mu kawai korata zaiyi shike nan.
Sohail yace no ba a haka kuyi rabuwar mutunci basai munyi ba tunda baya so.
Okay tace kawai,kallo ya fara kare mata yace wai mene wannan a kirjin ku?
Sam Maheera bata gane ba,yace gashi nan tulu tulu ana gani.
Maheera fuskewa tayi duk da taji kunya tace shi kuka sha kuka girma,yace Allah
sarki na Mama yana kabari yanzu ina tunosa ke ya akayi naki chakare chakare ita
kuwa Umma Nadia nata kamar na tsohuwar saniya wacce yunwa ta kamata.
Maheer ta dinga dariya ba shiri tace Umman taku guda?

Sohail yace ke bafa ita ta haife mu ba Na Mama yana Kabari nata me kyau ne Daddy
ma ya dinga ta yashe baki idan tana wajensa ya dinga ta dariyar dole hahahaha ranar
girkin Mama,Allah ko ni sai na iya Auren Mamata.

Dariya ta sake kama Maheera tace ashe ta hadu dai?


Yace tab ke kin isa ma kice shekarunta 47, Mamanmu ta iya sa kaya ko wanne wanka
kyau yake mata ga kamshi,gata da mutunci ke Mama fa duniya ce,akwai uwar data kai
tamu ma,Maheera tace Mamata fa? Sohail ya bata rai yace ko uwarki bata kai Maman mu
ba.
Da sauri Maheera ta kalle shi tace zagina kayi fa Sohail,yace to ba uwarki bace?
Uwarki mana nace bata kai tawa ba,nifa in kika takura min zan iya miki dukan tsiya.
Maheera tace ni din?
Kwalla ce ta cika masa ido tab da ya tuno da Mama Asmau.
Maheera tace sorry mene abin kuka? Yace baza ki gane bane... baza ki gane ba ina ta
so na baki labarin damuwa ta sai kice baza kiji ba labari na akwai jira kafin a
saurara,tsaki ya ja ya fice yayi tafiyarsa .

Maheera ta tsaya kamar gunki tana mamaki.


Bata yi tunanin zata ganshi ba washe gari ba
Sai gashi da yamma ya sha farar shadda tana shining ba karamin kyau yayi ba ka
rantse wani me kudin gaske ne,ga kyau,ita kanta Maheera tsayawa tayi tana ta faman
kallonsa,hannu daya a aljihu ya shugo yace ya garin me shago? Tace lafiya lau tana
murmushi.
Hannunta ya riko yace zo mu tafi.
hararsa tayi tace bazan je ba shine jiya kayi fushi?
Yace ni din? Yana nuna kansa da yatsa yace me nayi jiyan?
Au ka manta? Yace na manta kuma har ga Allah har ya manta ma,sai da ta tuna masa
yace Oh ya share zancen kamar ba shi ba.
Mikewa tayi suka fito,zata rufe shagon ya karbe key din yana cewa kawo kamar
namiji mace tana wahala haka Mama bata irin haka,ai ana taba ki kice wash zan
mutu.....harda gwadawa! dariya Maheera ta fara yi ba shiri har ya gama rufe shagon
yace muje
Juyawa tayi tana rataya handbag dinta,yace kawo handbag din na rike miki ki daina
wahala zaki yi muscles kamar na maza ki bubbude.
Jakar ya karba ya rike a hannunsa suna tafiya suna hira,yayi hauka yayi hankali a
haka har suka je gidan su.

Maheera kanta ya kusa bugawa ganin irin unguwar da suke da layin da suke balle
uwa uba gidan nasu tamfatsetse na gani na nunawa sa'a,tace a nan kake zaune? duk
bata kawo gidan uban Sahil da Sohail bane,tunaninta ma yaran riko ne ko 'yan uwa.
Sanda suka shiga Maheera tana ta kalle kalle ya kalleta yayi dariya yace kinga gida
me kamala ko? Yana dariya yace ai kamilallen gida ne wannan ba ballagazin gida ba
irin naku,nasan gidanku ballagazin gida ne.
Maheera tayi dariya tace kaima ai ba naku bane,bai ce mata komai ba,yace muje na
nuna miki kitchen din,In kin gama girkin ki shirya a dining sai na kira su masu
gidan su dandana.
Haka ya fisgi hannunta ya jata ko ina na gidan sai da ta dinga hakkin sosai yanda
yake fisgarta sai hakki take da nishi, da sauri yana nuna mata ko ina har katafaren
kitchen din katon gaske komai akwai ciki,ya nuna mata komai da kayan sarrafawa,kin
gane? tace ae naga komai da nake bukata akwai,yace yawwa to fara girkin ni bari
naje na gyara dakin Adnan da na Ibrahim kafin nan kin gama,ta furta ba damuwa,ya
juya ya tafi.
Farfesu ta fara yi na naman rago sannan ta tsara fried rice lafiyayya taji hadi
da su hantar rago da naman kaza,sannan ta hada couslow da lemo ingantacce ta shirya
a Dining, har da potatoe ball tayi da kwai da nama a tsakiya.
Tana gama shiryawa a dining ta zauna a palo tana kallon tv,sai taji karar takalmi
me tsini ana sakkowa daga sama ,Kamshi na mamaki ya mamaye palon.

Zayna ce take sakkowa ta sha wata material gown ready made abinta golden ta
tsula kyau,kana gani kasan taji hutu da kudi ba karya,Maheera tsabar tsananin
kyawunta yasa duk inda mace takai bata isa ta fita ba sai dai daiku tunda a duniya
baka rasa wanda ya fika dole ne wannan.

Zayna wani kallo ta bi Maheera da shi sama da kasa ta ganta sanye cikin material
silk black me adon flower pink sai dan mayafi siriri data dora a kanta,takalminta
normal dai na talaka me dan kyau gashi nan dai,sai dai kyawun Maheera ya tsoratata
amma ganin mijinta yana da class kuma sannan yana sonta gashi ma shi sai me kudi
yake kulawa sai kawai ta fuske a ranta tasan itama me kyauce komai da namiji ke
nema wajen mace tana da shi.

Maheera mikewa tayi tsaye da sauri tace good day Ma,Zayna ta wuce Dining kawai
ta zauna ba tare da ta wani amsawar kirki ba,Ibrahim ne ya fito yayi arba da
Maheera ya bita da uban kallo ya dauke kai ya wuce Dining ya zauna,shima tace Good
day Sir, har tana risinawa,hannu kawai ya daga mata,Adnan ne ya fito shima yana
zuba kamshi ya hade cikin kana nan kaya masu tsada blue, ko kallo Maheera bata
isheshi ba ya zauna a Dining,sai ga Sohail shima ya fito sanye cikin gajeren wando
da riga singlet da bocket da mopper a ciki ya hada uban zufa.

Hannunsa ya goge da karamin towel ya karaso wajen Maheera yana murmushi yace
kiyi serving nasu cikin rada yayi maganar.
Maheera ta karasa da sauri tana cewa kuyi hakuri" nan take ta fara serving nasu har
ta gama,suka ga girki sharr tun a ido ga kamshi.
Ibrahim ne ya riko hannun Maheera zata juya yace zo ki canja min Spoon 'yar kauye.
Tsoro Maheera taji akan idon Sohail aka yi,daga haka Sohail kawai idonsa ya canja
ya nufi Ibrahim gadan gadan ya sa baki a saitin keyarsa ta baya ya gartsa masa
cizo sai da wajen ya fashe,Ibrahim ya saki kara da ihu ya mike zasu yi kokawa da
Sohail!
Adnan yayi sauri ya rike Ibrahim yasan yana hada jiki da Sohail sai buzunsa
karfinsu ba na mutane bane,yace kyale shi kai zaka biyewa mahaukaci,abin kullum
karfi yake fa sun fara duka da cizo nan gaba sai tsince tsince a bola suna bin yara
da gudu.
Zayna ta tabe baki tace yo ni da suka ce zasu aure ni su biyu ma.
Sohail yace in Allah ya yarda baza ki haihu ba,mahaifarki ta mutu a haka zaki gama
aurenki,Adnan yace ameen da sauri kayi addua me kyau dama ni bana son haihuwa,
Zayna kamar zata yi kuka tace da Sohail mahaukaci karya kake,Maheera tana ta kallo
ta gaji ta janye Sohail tace relax mana ta jashi suka koma gefe suka zauna,Sohail
yace da Sahil ne ya rikeki da sauki bazan damu ba ai wannan ba yi bane,kawai a rike
mutum idan kika masa ciki fa,Maheera ta danne dariyarta,tace au ba ma shine zai min
cikin ba nice zan masa? Ina ka taba ganin namiji ya haihu?
Sohail yace ke wancen kwarto ne tsaf zai iya haihuwa,tayi murmushi kawai tana boye
dariyarta.
Kallonta yayi yace ki dinga rufe wannan chakare din naki ni bana son ganinsa duk
sai gani ake ta yi Mama fa Hijab take sawa idan zata fita ba a ganin nata,badan ma
mama ce ba ai sai nace miki bata da Chakare din nan.
Amma ke kowa sai gani akeyi haba Allah za a daina ce miki Classy girl me shago
kawai yafi dacewa dake,Maheera ta rufe bakinta sabo da dariya.

Can gefe kuma su Zayna sai kwasar girki suke yi me shegen dadi suna ta ci,Adnan
cikin santi ya kira Maheera da hannu,ta karasa a nutse yace aikinki yayi kyau na
daukeki aiki,zan dinga biyanki dubu dari,tana murna tayi ta godiya abinta yace gobe
ki dawo nan da zama ki fara aikinki,ga Sohail nan zai nuna miki room dinki,tace na
gode Sir na gode ta juya ta fice.
Ibrahim sai duri yake ko kala bai ce ba,itama Zayna haka.

Maheera ta fice daga gidan tana ta murna,Sohail ya biyo bayanta yace dama na
fada miki zaki samu baki yarda dani ba gashi kuma,tace na yarda ai yanzu na gode
sosai Sohail,yace ki daina gode min ni,muje to ka rakani,yace a'a na gaji ni bacci
zanyi,tace to bye,ya juya abinsa ya tafi itama ta wuce gidan da take kwana gidan
wata kawar Maman su,matar tana auren me rufin asiri a Abuja,itace ma ta samowa
Maheera aiki ganin halin da suke ciki a suleja ta kawota gidanta Abuja ta samo mata
aiki,matar yaranta uku yare ce kuma na Igala,tana da kirki ga tausayi.

Gida Maheera ta koma tana murna ta samu wacce suke kira da maman Rahmat a
palo,maman Rahmat tace yau ya naga yarinya ta tana murna?
Maheera ta bata labarin samun sabon aikinta da salary dinta,ta bata labarin
Sohail,Maman Rahmat tace Alhmdllh sai dai zanyi missing zaki barni na daina cin
girki me dadi amma na tayaki murna Allah ya taimaka ya bada sa'a,a kula sosai a
tsare mutunci,sai kiyi waya ki sanar da yan uwanki da Mamanki ko?
Maheera tace ae anjima da dare zan kira su,kema ki kira Oga fadlu ki sanar masa ya
nemi wani ko wata,Maman Rahmat tace yanzu kuwa zan sanar masa inshaallah,Yaran
Maman ma suna tayata murna" tashi tayi ta shige bedroom tana cewa thanks.

Washe gari da safe da wuri Maheera ta hada wasu kayanta a akwati me kyau ta tafi
gidan su Sohail,har kofar gida me taxi ya sauke ta,knocking tayi dake Sohail ne ke
bude gate basu da me gadi,shuru ba a bude ba sai da ta gaji ta turo karamar kofar
ta jikin gate sai taga ta bude kawai ta shugo.
A compound ta hango Sohail yana zaune a kujera ya harde kafa daya kan daya yana
ji ana knocking bai kula gate din ba,tana shugowa ya bude idonsa da yake a lumshe
ya kalle ta kawai,ta karaso inda yake tace Hey,Hey shima yace sannan ya wani tafi
dogon tunani sai da ya jima a haka tana tsaye tana kallonsa sannan yayi zumbur ya
mike yace oh wai kece?

Akwatin ya fisge a hannunta yace idan an hanaki daukan heavy abu bakya jin
magana kawo muje ciki,ta bishi tana murmushi suka shiga ciki ya nuna mata bedroom
hadadde kamar dakin amarya yace ga room dinki,tace na gode Sohail,ya hade rai tare
da furta ki daina min godiya ki godewa Allah,tace ai ina gode masa yace wannan ke
ta shafa,kije ki ma matar gidan girki kafin 5pm suma su Adnan kiyi musu
nasu,Maheera tace to ta mike ta wuce kitchen.

Tana tsaka da girkin Sohail ya shugo sanye da jallabiya wata fara dangalalliya
duk kaurinsa a waje fari kal me dauke da kwantaccen gashi me kyau yace yana kallon
Maheera ya aikin? Murmushi tayi tace Alhmdllh
Yana murmushi yana sosa gashinsa ya furta ko na tayaki?
tace a'a na gode,zai kara magana tace jeka kawai karka jawo min a koreni a aikin
nan suce wani abu muke yi ka rufa min asiri,Okay....okay...ya furta yana kallonta
ya juya ya fita ya barta tana aikinta, kamshin girkinta ya cika gidan,tana gamawa
ta shirya dining Sohail yana can yana wanke mota.

Maheera sai da ta tambayi Zayna ko za a miki wani abu Hajiya? Zayna tace no sai
anjima ki dora abincin Ogana, okay tace,taje kitchen ta kwashe ragowar a plate da
Spoon ta fito har inda Sohail ke wanke mota,tace ga abincin naka,yace harda ni?
tace ae mana,yace ki daina dafawa dani kar su gani suji haushina ke 'yar aikin su
ce ba 'yar aikina ba,to yanzu dan kaci abinci sai ya zama matsala? Yace hmm
kawai......Adnan ne ya shigo da motarsa wata benz me shegen tsada,a idonsa yaga
Maheera tana mikawa Sohail abinci,mantuwa yayi ya dawo gidan shima.

Fitowa yayi a nutse cikin suits me tsada yana danna waya,yana zuwa inda suke
tsaye ya dakawa Maheera tsawa sai da ta firgita,yace ke waye ya dafa abincin da
kike bashi? jikinta ya hau mazari tace ni..ni...nice na dafawa Hajiyanka shine da
ya ragu na bashi.
hannu Adnan ya sa ya fatalar da plate din a hannun Maheera,abincin ya watse a wajen
a kasa ya furta look daga yau ke ba yar aikinsa bace,ni na daukeki aiki ni kadai
zaki yiwa aiki tare da matata da kanina,idan ba haka ba zan koreki a aikin,idan
yana son yaci abinci ga kitchen ya dafa da kansa.

Juyawa yayi ya kalli Sohail yace ka dakko abin shara ka share nan kayi clearing
komai ya ja tsaki ya juya abinsa ya wuce ciki.
Maheera tace ikon Allah haka kake shan wahala? Murmushi Sohail yayi yace rayuwa
kenan ya za ayi ko a jikinsa ma taga ya dakko abin shara ya share wajen tas ya
tattara plate din ya maida kitchen.

Maheera tana ta kallonsa cike da tausayinsa,yace kina ta kallona zan dafawa


kaina karki damu.
Jikinta a sanyaye ta koma ciki gaba daya tausayin Sohail ya kamata duk tunaninta
dan aiki ne suka dauke shi a gidan.

Daddy Ali ne ya kira Adnan ya sanar masa cewar zaizo Abuja wani aiki zai kawo shi
amma a ranar zai koma kano ba zama zaiyi ba,Sohai ma bai sani ba washe gari Zayna a
kitchen ta samu Maheera tace ke Maheera kike ko wa? kiyi abinci lafiyayye da wuri
before 2pm surikina zai shigo,Maheera tace Alright ma.
Ta fara girke girkenta Sohail ya sameta yace yau girki da wuri? Wai surukin Madam
ne zaizo,Sohail baki ya tabe yace na sani ai,sun fada maka ne? Yace sai sun fada
min ma,ko sunanki ai ji kika yi na fada miki to ko basu fada min ba na sani yana
hanya yanzu ma.

Maheera bata karyata shi ba,kira Sohail yaji Ibrahim yana kwala masa kamar zai
fasa gidan,Maheera tace jeka ana kiranka,fitowa yayi da sauri,Ibrahim yace kawo min
glass of juice,Sohail ya koma ya kawo masa lemo glass cup,yana karba yace jeka
dakina zaka ga wani note book green ka dakko min shi sauri.
Sohail ya wuce sama da sauri har hadadden dakin Ibrahim yana dubawa ya hango
notebooks guda uku daya green,daya blue,daya grey color,Sohail ya dauki daya ya
duba yace wanne ne green din a haka ya daga sama yana karewa ko wanne kallo,blue
din ciki ya dauka yace yesss....wannan shine green ya fito ya kawo.

Ibrahim takaici ya kamashi yace wannan yayi kama da green? shine green din? Sohail
yace idonka baya gani wannan ai shine green,wannan color din itace ta dace da green
haba Yaya kalli ko idon naka computer ta fara kashe shi,uwarka ce computer din ai.
Sohail ya furta ai kuwa da mun huta sai muyi ta danna ta ba ruwanmu muyi game muyi
kallo,computer uwar mu guda ai sai game kawai,tsaki Ibrahim ya ja cike da takaici
ya fisge littafin ya tafi da kansa ya dakko abinsa.

Sohail ya bi littafin da kallo yace wannan ne green? blue fa ka dakko,Ibrahim


yace Sohail dan Allah tafi ka bani waje just go....
Sohail ya nuna hanya yace na tafi kake nufi?
Ibrahim bakar magana ya fada yace a'a ka zauna nace,Sohail ya dawo palo ya zauna
tare da harde kafafu yace na gode Yaya yana dagawa Ibrahim gira kamar dan
iska,Ibrahim yace kai Sohail karuwa ka gani a nan a zaune? kana wani daga min gira
kamar dan iska yaga karuwa.

Sohail ya sake kashewa Ibrahim ido yace ai mu idan iskanci zamu yi karyar karuwa
ta kama kafar mu,dariya Ibrahim yayi ba shiri,yace gaskiya haukarku shahararriya
ce, Sohail yana jinsa yace Yaya Ibrahim jiya Allah kaje kayi iskanci da wata mace
sunanta Bilkisu,mamaki ya kusa kashe Ibrahim,yace a gidan uwarka?
Sohail yayi murmushi yace Allah kayi Sex da wata kuma shine na farkonka ta
rinjayeka,ka cuci kanka tunda kakai wannan shekarun baka taba yin iskanci ba sai
jiya,duk shekarun da ka kwashe kana hakuri sun tashi a banza fa.

Ibrahim ya hade rai yana muzurai yace kai karka min sharri zanci ubanka,in nayi
ma ina ruwanka? Ku aljanun naku ma munafukai ne,Sohail yace shike nan dama
tambayarka zanyi...Adnan ne ya shigo palon,Sohail yace Yaya Jiya Ibrahim yayi
zina,dubu dari ya bawa karuwar,budurwarsa ce ta kaishi ta baro.

Adnan ko a jikinsa yace to ina ruwanka munafuki yayi din rayuwarsa ce bazai huta
ba,idan ku baku da lafiya shi kalau yake,mu da lafiyar mu,Sohail yace ba a dai kuri
da lafiya,mu ko zazzabi ai bama yi sam.
Tashi yayi ya bar wajen nasu,Suka ci gaba da hirarsu shi da dan uwansa.

Ali ne ya karaso da escort dinsa motocinsa da securities dinsa,Sohail ne ya


karasa jikin motar Daddy dinsu ya bude masa kofa,Alhaji Ali ya fito ya sha farar
shadda,kana gani kasan akwai kudi,Sohail yace Daddy ina kwana barka da zuwa,Daddy
yayi dan murmushi bai ma amsa gaisuwar ba kawai tambaya yayi ina Adnan? Sohail yace
Adnan kafi kowa? Daddy yace wanne sunane haka sabon nick name ya samu? Sohail yabi
Daddy suna tafiya yace to ai kai kace kafi sonsa kaga ai yafi kowa ka sa masa kafi
su kawai.

Shuru Daddy yayi suka shiga ciki,Sohail sama ya haura yana kwalawa Adnan kira
Yaya ka fisu kazo ga ubanku yazo,da Adnan yazo Sohail ya kara furta ka fisu kaje
ubanku ya zo,kai fa banda kai? Adnan ya tambaya.
Sohail yace to gashi nan wa ya sani uban mu ne ko ba shi bane Allah ne ya
sani,Adnan ya ja tsaki ya wuce abinsa.

Zama suka yi suka gaisa da Daddy suka fara hirar aiki da harkokin kamfani da
yanda kudade suke shigowa,Zayna tana cikinsu a zaune suna ta hira abinsu,Sohail
kuwa yana dakinsa sai da ya gaji ya fito ya wuce kitchen ya samu Maheera tana fitar
musu da abinci,tayata yayi suka shirya abincin a dining,Daddy Ali yana kallo ko a
jikinsa sai ma murmushi da yayi yace Sohail akwai aiki wai ina Sahil? Sohail yace
yana Lagos,Ali bai ma san dansa ya tafi Lagos ba,Ali yace amma baku fada min ba?
Wanda kafi so din naka basu fada maka ba?
Ali ba kunya yace wallahi basu fada min ba, Kai Adnan me yasa banji labari ba?

Adnan yace wata harka ta samun kudi Sahil ya samu wacce zai tsaya da
kafafunsa,aiki ne me tsoka kuma shi yasa muka amince ya tafi,duk wani kudi da komai
mun bashi yana can ya fara aikinsa ba matsala yana samun kudi,Daddy ba bincike yace
to ai hakan yayi amma Sahil zai iya tsinana wani abu kuwa a duniya? Kar ya zubar
min da mutunci ina so zan fito takarar gomna next year, Adnan yace to wa ya sani ne
zanje na bincike shi naji.
Daddy yace kayi gaggawar hakan bana son abinda zai taba min siyasa ta.

Maheera dai tana jinsu Daddy ta gaisar sannan ta koma kitchen tana tsaye ta
lula tunanin abinda akewa Sohail wai dama baban su ne? Mamaki ya cika ta,Sohail ne
ya shigo da fara'arsa ya manta sam yace ki kaiwa Daddy tissue,tace wai da gaske
babanku ne? Sohail yayi murmushi yace ae mana ai babanmu ne nida Sahil shine ya
haife mu,ba ina ta cewa zan baki tarihina zan fada miki matsalata sai ki nuna bakya
son jin labarin.

Amma baban mu ne mahaifi, Maheera ta tuna sanda yake zuwa shagonta yace zan baki
tarihina,zan fada miki wata magana,sai ta dauka shirmensa ne kawai zai mata sai
tace baza taji ba ita ya kyaketa.

Idonta ne ya ciko da hawaye tace kayi hakuri ban sani ba wlh,yanzu ina Mamanku
ko itace ta mutu? Sohail yace ni ban sani ba tunda ni ban taba jin labarinta ba
amma dai ance tana England sannan arniya ce itace tace bata son mu shine Daddy ya
kawo mu wajen Mama Asmau itace ta raine mu har muka shiga University sai ta rasu
bayan ta rasu kuma shine aka cire mu daga makaranta muka dawo nan da su yaya muna
musu aiki,suna dan bamu 1k 2k,Daddy kuma shike daukan nauyin cinmu da shan mu sai
sutura ana siya mana sai dai muga an kawo mana,ba a bamu ko sisi mu siyi abu da
kanmu,sabo da mu bamu da amfani ance.
Maheera tana ta hawayen tausayi tace wlh kuna da amfani kuna da kyawun hali da
hankali kawai su basu gani ne amma ni na gani kuma na sani na yarda da kai
Sohail,Sahil ma haka you are the same kuna da hankali wlh,kunfi su Adnan hankali da
kyan hali,Sohail yace Allah? Ke kin yarda muna da hankali? Maheera tace sosai ma
Sohail na yarda da kai.
Kin yarda dani? Ba wanda ya taba cewa muna da hankali sai mama Asmau sai ke,kin
yarda da mu? Maheera tace ae.
Zamuyi magana bari na gama aikina,yace to ya juya ya fita sai murna yake da farin
ciki yau an samu wacce tace suna da hankali.

Sahil kuwa bacci ya sha sai yamma ya fito palon su Khalisat ya same su gaba daya
a palo suna kallon film, Dukkansu suka zuba masa ido kamar mayu ko wacce tana
sha'awar su har uwar tasu,Islaha dai tana kitchen tana aiki sai gata ta fito tana
shirya Dining,Sahil ya kalleta da muguwar tsana suka hada ido,jikin Islaha ya hau
rawa,tsoronsa take ji sosai,kanta ta dauke ta shirya dining,Khalisat tana ta jan
Sahil da hira yana sharewa.
Islaha ce ta shiga kitchen,yace kitchen ne can? Aunty ta karbe zancen tana
kwarkwasa tace ae kitchen ne zaka iya zuwa ka dauki abinda kake so,feel free ka
zama dan gida.

Mikewa yayi ya shiga kitchen din,ba zato Islaha ta ganshi tsoro ya kamata ta
fara rawar jiki,Sahil yace kyayi rawar jiki ai, wajen maza kuma kin iya cire pant a
sauke shi kasa,Munafuka me fuska biyu na tsane ki.

Islaha muryarta na rawa tace wlh ni ba yar iska bace ban taba iskanci da namiji
ba,tsawa ya buga mata enough....a mota muna tafiya haka kika ce ke ba yar iska bace
harda cewa cinyata ba safe waje bane,har na miki gata na zame miki uwa da uba na
doraki a precious cinyata safe waje irin wannan,harda ce min dan iska to gashi an
tsinci iskanci a wajenki,na rainaki ma wlh,akan kudi a tafi a bankadewa maza
Taskira shame on you, Allah yasa Sohail yayi mana kawar mu Maheera ta ishe mu
useless girl.

Islaha ta fara kuka da hawaye ita bata san me tayi masa ba ya tsaneta,ya juya
zai tafi tace wlh ban taba zina b....kafin ta karasa yace rufe min baki makaryaciya
na ganki da idona to,Allah ya nuna min gaskiya anje an bankade taskira,ke kuwa nawa
za a baki haka?

Islaha tace wlh idan ka kula su Khalisat wallahi a gidan nan sai anyi yaki ai
dai nice nan na fara saninka,lalataka zasu yi,
Indai ina gidan nan babu wacce ta isa ta lalataka Sahil yace au fashi da makami na
zaki yi? Tace ae? Baza su tsinci komai a jikinka ba face wahala,sai na fito da bad
character dina da nake dannewa a gidan nan,za a ga bad character, sai nayi fashi da
makami,Khalisat ce ta samo ka to sai nayi fashinka,yace to nidai abar nan tawa daya
ce ina kuke so na sata,kai ku tsaya sai na fadawa Sohail ya fada muku gaskiya ni ba
dan iska bane,wannan iskancin da zinace zinace na zamani bama yi,bamu iya bude
taskirar mata ba.

Daga fadan da yake yi kuma sai ya koma hira yace da na sauka ruwa ya zaneni ranar
da muka zo,Islaha tayi dariya tace sannu ai na tambayeka tun farko ina zaka je kaki
kulani,kasa kasa yayi da murya yace ya kike fama da aiki a gidan nan tace uhm ba a
magana ina shan wahala a rayuwa.
Sahil yace ai wahala yanzu kika soma gani tunda kike bada Taskira ana saka mazari
a ciki kin gama yawo,ke da albarka har abada a haka zaki kare,karshen ki bazai kyau
ba,bayan sun gama hira kuma ya koma masifarsa.
Ki daina kulani na fada miki na tsaneki ya bata rai ya fice yana huci.
Su Aunty duk tunaninsu Sahil me hankali ne murna suke ganin ya tsani Islaha gaba
daya,yana fitowa yace wannan wacce mahaukaciyar me aiki kuka samo ne? Na tsaneta
bana sonta,Aunty tace uhm yar gidan yar uwata ce ta ishe mu muma,tsaki ya ja ya
sake mikewa yace bari na koma wajenta sai na mata rashin mutunci ni zata raina,Su
Khalisat har wani dadi suke ji Islaha duk kyawunta baza ta kwace musu Sahil ba.

Kitchen din Sahil ya koma,ya kalli Islaha yace kina da saurayi wai? Mutumin da
yace yar iska ce ita tana kula maza tana Zina amma yanzu kuma yana tambayar
saurayi,Islaha ita kanta mamakinsa ya isheta,tace a'a bani da shi,yace yafi miki
mutunci mu maza da kike gani ba 'yan goyo bane mu,ko an goya mu sai an sauke
mu,Islaha tana dariya kasa kasa tace harda kai yace ae mana harda ni da Sohail
karki sake ki goya mu,Islaha tace wai wanne aiki kazo yi nan? Kujera ya ja ya zauna
yace bariki nazo yi,zobo me sanyi Islaha ta zuba a cup ta mika masa,yace mu a baki
ake bamu bama cin abu da kanmu,har yaushe aka haife mu yara ne mu fa,Islaha duk
wasa ta dauka yana yi shi kuwa da gaske yake fadar komai,tace to bari na baka a
baki.

Su Khalisat suna palo shuru shuru sun ga Sahil shuru yaki fitowa tsoro ya kama
su,Khairat tace bari na leka ta mike sadaf sadaf tace dole abi sahu bako ne ba a
san halinsa ba,Islaha tana ta bashi zobo a baki yana shanye abinsa sai da ya kusa
gamawa ya tankade cup din ya fadi kasa ya tarwatse yace da girmana,nifa ba dan iska
bane irinki me neman maza yaja tsaki ya juya sai suka yi karo da Khairat.

Khairat ta matsa da sauri taga Islaha tayi zugum ga cup a tarwatse bata sani ba
Sahil aljaninsu fada musu abu suke yi iya tsiyarka watarana baza ka iya kure su
ba,kafin kazo sun sani,Khairat ta harari Islaha tace stay away from him yafi
karfinki,gashi nan kin jawa kanki sai ki gyara wajen.

Sohail yana komawa wajen su Khalisat kamar munafukin miji yace yawwa ni gaskiya
indai itace kar ta dafa min abinci a gidan nan,kar ta yi min komai,Aunty tace karka
damu girkin ma da hannunmu zamu dinga yi maka har wanki da komai,yace yafi
muku,Khalisat tace bari nazo mu fita a mota na kaika yawo,Aunty tace da kin bari
tunda zan fita na fita tare da shi,Khalisat taji haushi da kishi tace ai na
shirya,Khairat tana jinsu tace ni na kaishi next week.
Sahil yace ayi haka? Kunki sharar masallaci zaku yi ta kasuwa,ko girki bakwa yi
ga me yi can bakwa wanki duk yi muku akeyi yanzu da kanku zaku yi min nawa? Aunty
tace laaa ba komai ai bakonka annabinka,Sahil yana kallonsu dai dai yace alright ku
kuka ga zaku iya ai! ya furta kai tsaye ba ko darrr.

Free page
400 ne

0175487861
Asmau Garba Muhammad
Gtbank

'Yan Niger
+22790795939

AsmaBaffa
08061929616
[7/17, 3:17 PM] Asmabaffa: 🪸MUMMUNAR DABI'A 🪸

16-20

Official
By
AsmaBaffa

SADAUKARWA NE GA 'YATA TASNIM

Page naki ne
Baby Ak

MASU AUDIO BAN YARDA A SATAR MIN NOVEL BA A JUYA BA,DUK WANDA YA DORA A CHANNEL
DINSA SAI YA SAUKE.

*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason
juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene
matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin
taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma
babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko
kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi
glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da
humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu
karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-
muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku
da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban
burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza.
Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka
tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin
kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da
kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*

Zuwa yamma Khalisat tace Sahil ya shirya su fita,Islaha ta fito lokacin ido
ta kyafta masa tana makale kafada wai yace yaki bazai je ba,Sahil ya kalli Khalisat
yace ni bazan je ba Islaha tace kar naje,baki Islaha ta rufe tare da sauri tace ba
ruwana ni nace kar kaje? Sahil yace ido ta kyafta min tana min nuni nace wai bazan
je ba.
Khalisat tace to Allah ya kamaki,Islaha ta wuce bedroom dinta da sauri,Sahil kuwa
tashi yayi yace ke Khalisat kike ko wa kilishi bazan je ba,ni ba sahoramin namiji
bane da zan bi mace ta fita dani yawo,ai idan ban fita da mace ba to kuwa mace bata
isa ta fita da dan uwan Sohail ba,duk gidan nan baku isa ba ko uwar ku ce bazan je
ba.

Haka kawai kun kawo ni gida an ajiye ni neman kudi fa nazo ba zan zauna gidan
yan iska ba,Babarku ma jiya sai da tayi kawalci,ta hada kawarta da wani me kudi ya
biyata kudi kuma anyi.
Itama Khairat dazu dazu ta gama waya zata samu wani a hotel senator ne kuma
arnene sunansa Michiel,bazan iya ba,ga yayarku can Shema'u a gidan ta ajiye yaro
matashi tana kashe masa kudi yana biya mata bukata ina zaku kai wannan zunubin?
Dakinsa ya wuce sai gashi dauke da jakarsa yana zarewa Khalisat ido yace akan ki
fita dani wani yawon shakatawa gwara na bar muku gidanku ni dama bance a kawo ni
ba,indai sai an kaini yawon shakatawa ne gwara na bar gidan.
Abincinku kuma kuyi kudinsa na biya ku mutanen banza,ni dan iska ne ance muku?.

Khairat da Aunty ne suka fito jin Hayaniya Sahil ya nuna su da yatsa yace duk
iskancinku sai kun kyale min abu dita bata iya hasala komai,mata kun sani a gaba
sai lashe lashen harshe kuke yi,bazan iya ba kuje ku zuba min magani a lemo na a
rabani da mazantaka ta.

Aunty tace kai ka iya bakinka wlh gidanmu kazo,butulu an taimakeka kazo kana
mana wulakanci,Sahil yana ji yace ni nace a taimake ni? Kuma badan Allah tayi
ba,Baba ki iya bakinki.
Khalisat ta zaro ido tace uwar tamu? Uwar taku kuwa wata ta kirki ce,Islaha ce
ta fito ta tsaya a gefen Sahil tace kuma ai ba fin wasu matan kuka yi ba asiri kuke
yiwa maza ana baku kudi amma ai baku fi kowacce mace ba.

Sahil yace kuma Taskirar ma duk Infection ne a ciki,gasu nan kullum a shan
magani,matukar baku tuba ba baza ku warke ba,ai dama Khairat watanta Uku bata yi
period ba ai Sanyi ne da ita,inji uban wa? Aunty ta furta amma kai Aljan ne idan ba
Aljan ba a gidan uban wa ka sani.
Sahil yace ai mijinki sai kunyi sharia da shi a Lahira dama kina da aure kina
bin maza bai sani ba,Aunty ta zaro ido nan take ta fara hada zufa,tana kame
kame,Sahil yace kuma Yaseer ba dan mijinki bane Sale me maganin yan bori shine ya
miki ciki,Aunty ta shiga tsoro tace amma kai aikoka aka yi kaci zarafin mu fita ka
bar mana gida.

Sahil yayi tafiyarsa ya bar gidan,Islaha suka kama suka rufe ta da duka ta musu
rashin kunya sai da suka mata lilis sannan suka kyaleta yashe a kasa tana
kuka,Aunty daki ta shiga ta fara watso kayan Islaha dama kadan suke jira,tana
masifa tace dauki ki bar mana gida kusan inda dare ya miki,Islaha ta mike da kyar
ta tattara kayanta tana cewa dan Allah Aunty kiyi hakuri wlh bazan kara ba.

Aunty tana masifa tace wlh sai kin bar gidan nan dama kin ishe mu,Yaseer ne ya
shigo ya iske abinda ke faruwa yana gidan yayar su Shemau,shine ke tukata a motarta
duk wani iskanci da zata je Yaseer kaninta shi ke kaita sannan kullum suna tare a
gidanta ko hotel,kudi take kashe masa sabo da yanda komai shi take aike, shine
kamar yaronta kuma kaninta uwa daya uba daya.

Yaseer yace ke Aunty ki kyaleta 'yar gidan yar uwarki guda jini daya,wa take da
shi bayan ke? Aunty tace tana da su tunda ta iya yi min rashin kunya ta bar min
gida na gaji,taje ta bi bako Sahil ya bata uwar da zai bata,Islaha ta mike tana
dingishi ta zuge jakarta me dauke da tsumman kayanta zata fita"
Yaseer ya rike ta tare da furta dan Allah kuyi hakuri Aunty, Aunty da kyar ta
hakura ta kyale Islaha tace ta zauna badan halinta ba.

Sahil kuwa machine ya tare ya hau abinsa yace kaini Banana Island ko Lekki,Me
machine yace ai nan yankin bama shiga da machine wani wajen amma zan kaika kusa da
Banana sai na ajiyeka ka shiga mota,Alright muje.

Me machine dai wuta yake kawai a titi ta wajen wata katuwar gada suka zo wucewa
mutane 'yan cirani gasu nan fululu,Sahil yace sauke ni a nan ga gidanmu,Me machine
yayi dariya ya tsaya yace nan ne gidan ku? Kace Banana Island ko Lekki,
Na fasa zuwa can to ko zaka min dole ne? Sahil ya furta ransa a bace.
Me machine yace ni a wa! bani kudi na kawai,Sahil ya bashi kudinsa ya wuce shi kuma
ya nufi kasan gada.
Mata da maza ne a wajen ga karuwai nan iri iri wasu a nan suke badalar su idan
Allah ya taimaki mace ta tara kudi ko ta hadu da me kudi sai ta kama gida a wata
unguwar ta koma shike nan taci gaba ita.

Sai faman kallon Sahil suke yi,ga maza nan wasu duk sun bar kayansu a wajen sun
tafi neman kudi,Sahil ya tsaya yana ta kallon wajen in banda kazanta da wari babu
komai a wajen,kamar zaiyi amai ga kudaje na dole wanda kazanta ta kawo su ta dole.

Sahil gajiya yayi da tsaiwa ya tsallaka gefen wasu flowers yayi fitsari,ashe ba
a fitsari a wajen sai gani yayi 'yan sanda sun zo sun kama shi,daya a ciki da
rashin mutunci yazo yana kiransa da Aboki zai mari Sahil hannun dan sanda baras ya
balle ihu ya saki ya tsuguna a wajen,Sauran su tunaninsu kuskure ne yasa Oga ya
karye,suka fincike jakar Sahil a jikinsa,duk yana kallon su bai ce kala ba,cikin
yan sandan su biyar daya a ciki ya rataya jakar a kafadarsa ya cakumi kugun Sahil
yace muje Office suna masifa ya jawo Ogansu ya karye,Sahil ya kalle su yace ku jani
ku kaini Office din,Suka fisgo Sahil amma suka ji gam gam kamar sun taba jikin
katanga,sai da suka hadu su hudu ko zasu iya daukan Sahil amma gam gam a tsaye,kuma
yana motsa jikinsa yana komai amma sun kasa,tsorata suka yi,wanda ya rataya jakar
Sahil ya fara kokarin cire jakar zai bashi abarsa amma jaka taki ciruwa.

Yayi yayi ya cire jakar ya kasa,sauran suka tayashi amma taki ciruwa,Sahil suka
dawo suna roka Oga please....hannu Sahil ya daga musu yace na yafe muku kuje
kawai,wanda jaka taki ciruwa a kafadarsa ya kwabe fuska zaiyi kuka yace
Sir....Sir....please....yana nunawa Sahil jakar ya fara sheshekar kuka,Sahil ya
barsu a cikin rana ya juya zai tafi ai binsa suka yi da gudu,me jaka yana faman
tiri tiri da ita ya rike Sahil tare da durkusawa a kasa yana bashi hakuri yana
rokonsa, wanda ya karye kuwa yana yashe a kasa rike da hannunsa yana ta ihu da
danasani.

Sahil hannu yasa ya janye jakarsa a kafadar dan sanda sai gashi dansanda ya
mike yana murna suna godewa Sahil,Sahil yayi tafiyarsa ya barsu.
A haka ya dinga garari a gari idan ya gaji ya samu waje ko jikin bishiya ya zauna
ya huta,ga ruwan sama ko yaushe sai dai ya nemi wajen fakewa.

Bashi da inda zai kwana gashi ruwa zai iya tsinkewa komai dare,tafiya ya dinga
yi har ya samu sabon gini kango ne an rufa shi kofa da window ba a sa ba,ciki ya
shiga ya ajiye jakarsa a nan sai da ya huta sosai sannan ya samu ya fita ya nemi
abinci ya siya ya dawo ya zauna ya cinye abinsa ya sha ruwa pure water,a nan ya
kwanta bacci ya kwashe shi wurin duk yashi da siminti.

Islaha ce kwance tana ta tunani ko Ina zai je oho,mikewa tayi tana kwance ta
zuba tagumi a hankali ta mike ta dauki wasu kudi ta saka rigar ruwanta a saman
doguwar rigar atamfarta wata maroon ta fito.

Tana ta duba Sahil unguwa unguwa bata ganshi ba,ta nufi kasan gada inda marasa
galibu suke tafiya taje ta duba ko ina babu shi,ta sake hawa machine tayi ciki ta
kangon da Sahil ke kwance ta wajen ta wuce haka ta gaji da nemansa ta koma gida
cikin dare.

Washe gari ma da wuri ta tashi ta gama ayyukanta ta sake fita nemansa duk inda
tasan yan cirani na zama sai da taje bata ga Sahil ba,har sai da ta kwashe 5days
kullum sai ta fita nemansa,shi kuma yana cikin kangon sai dai ya fito ya siyi
abinci ya koma.

Kudinsa ya kare bashi da ko sisi babu kudin siyen abinci,Sahil sai da ya kwana
ya yini bai ci komai ba ruwa ma a wani pampo ya samu ya sha,zama yayi a cikin
kangon yace gwara na koma gida kawai wannan ciranin bazai yuwu ba babu riba a
cikinsa,gwara na kira Sahil ya turo min kudi na koma naci gaba da bauta bazan iya
ba.
Please call me ya yiwa Sohail nan take Sohail ya kira shi,yace ya lagos din ko ta
samu ne? Sahil yace Allah ya tsinewa lagos wlh gwara arewa mutum yana cikin mutunci
da sutura,ni dawowa zanyi gida ka nemo kudin mota ka turo min,Sohail yace da wuri
haka? Yace ai gwara ka dawo gashi me shago ta zama kawar mu,Sahil yace nemo kudi ka
turo min jira nake yau na kwana na yini ba uwar da naci kaje ka roki Adnan a bani
kudi dan Allah yunwa zata kashe ni.

Sohail wayar ya kashe ya nufi bedroom din Adnan yayi knocking Adnan sai da ya
gama yangarsa ya bude kofa sanye cikin gajeren wando,yana ganin Sohail ya bata
rai,Sohail yace dama dan Allah kudi za a turawa Sahil zai dawo gida,Adnan ya kece
da dariya ba shiri ya dinga dariyar mugunta harda shakewa yace yaji wuya,ina neman
kudin? shi a dole me zuciya,ai ba abinda zai samu dama na fada muku ku hakura da
rayuwa ku zauna ku dinga bautar mu kunki ji,baku da gata amma ku kunki yarda shi a
dole zaiyi kudi to sai yayi kudin mu gani idan yana da kwakwalwar tara kudi.

Sohail yace arziki dai na Allah ne,Adnan yace au nasiha zaka min? Kai ka isa
kayi min fada kana talaka? Me yasa baka yiwa kanka fadan ba ka zama me kudi,kayi
tunani me kyau akanka ka zama me kudi in ka isa,amma ina me kudi ai kuwa nine nake
da hankali da tunani,talaka ai bashi da hankali tunda ya kasa yin hankalin yin
kudi.

Sohail yana jinsa yace hmm bani kudin na tura masa to,Adnan yace sai nan da
2weeks,bashi da kudin abinci fa Yaya dan Allah ka bani na tura masa dan
Allah.....Adnan yace wlh na rantse sai nan da 2weeks kuma ko ka kira Daddy bazai
bayarba sabo da komai naku yana hannunmu an dawo da rikon ku hannun mu.
Sohail juyawa yayi ya tafi kawai ya wuce bedroom dinsa yana rufe kofar ya jingina
da jikin kofar ya zame ya zauna a kasa hawaye ya fara zubarwa sosai yana kuka,ya
daga hannaye sama yana rokon Allah yace Allah kaga halin da muke ciki Allah ka
fitar damu Allah ka bani kudin da zan turawa Sahil,ya zauna yana addua yana kuka,ya
dade a haka ya wanke fuskarsa sanna ya fito.
Maheera ya gani tana Gyara kujeru ta kalle shi taga alamar kuka yayi.

Murmushin karfin hali yayi ya zauna kawai ya zuba tagumi,Maheera zama tayi a
kujera daya suna Facing juna tace Sohail lafiya? Me suka yi maka? Sohail ya kwashe
labari ya fadawa Maheera yace kuma Sahil yana can ya kwana baici komai ba a kango
yake kwana,Maheera tace to kwantar da hankalinka jiya Zayna ta bani dubu talatin
tace na siyi kayan sawa ta gaji da ganina cikin tsumma wai kyankyamina take yi a
haka,Sohail yace a hakan kika yi kalar kyankyami? Maheera ta daga masa kai tare da
furta haka tace.

Aljihun doguwar rigarta ta duba tace gashi sai nayi mata karya nace tela bai
dinka min kayan ba,dama dubu talatin a zamanin nan wanne kaya zata siya min na
kirki kuma a garin Abuja sai dai atamfa karama da gwanjo. Sohail ya karbi kudin
yace na gode Maheera,tace to ba gashi Allah ya rufa asiri ba ai dai ko a trailer ya
dawo kamar yanda ya tafi.

Murmushi yayi sai yanzu hankalin Sohail ya kwanta ya fice da sauri ya nemi POS
ya turawa Sahil kudin,ya kira shi a waya ya sanar masa,Sahil ya mike yana murna
cikinsa ba komai ya fito daga kangon zai nemi me POS ya cire kudin,yana fitowa
Islaha tana zuwa wajen a kafa tana ta dube dube tana nemansa,ido biyu suka yi ta
ganshi ya rame sosai yayi busu busu da siminti ,Murnar ganinsa tayi tace ina ka
shiga dan Allah Sahil yau nafi kwana shida ina nemanka

Sahil ya kalle ta yace ina nan wajen ai yanzu ma fita zanyi kika zo ina zan samu
me POS? Kudi zan cire na siyo abinci,Islaha tace zo mu tafi,bayan ya cire kudin
suka wuce wajen cin abinci, a nan suka zauna yace ke me zaki ci? Islaha zuciyar
Sahil na birgeta yanda yake kula da mace,tace a koshe nake,ai daga gida nake
fa,yace to lemo fa? tace zan sha to ta dauki nasa ta sha,yana cin abincin yana
kallonta yace kika sa min baki a lemo na bazan sha ba,sai kace kazama ta dauke tace
to siyi wani bari na shanye wannan din,lemonsa ya kwace yasa aka kawo mata wani.

Wani matashi ne ya zauna in banda kallon Islaha ba abinda yake,Sahil ya kalli


matashin yace kai dauke idonka,Saurayin yace ai da gani budurwa ce baka da ikon
hanani kallonta,Sahil ya kalli Islaha a fusace yace ke kika bashi dama ya kalle ki?
Islaha tace ni kaga nace ya kalle ni.
Idan kin san na iskanci kike nema kiyi magana tunda sana'arki ce,Islaha tana zaune
ta share zancen tace nifa da zan samu wani aikin a wani gidan barin gidan Aunty
zanyi.

Sahil ya kalleta kawai ya gama cin abincinsa ya mike tare da furta nifa Abuja
zan koma gidanmu na fasa neman kudin bazan iya ba,Islaha tace da wuri haka dan
Allah karka tafi,.
Ke da Sohail aka haifo ni bada ke ba.
A ina gidan naku yake a Abuja? Address ya fada mata,tace number waya please wlh
kana da hankali kai nutsatse ne,dariya Sahil yayi yace tab ni din? dan baki san
yanda ake cewa bani da hankali bane,ai har mahaukata ake fada mana,amma ai ni na
sani me hankali ne,ya bata number wayarsa daga wajen ya mata sallama ya wuce Tasha
a kafa yake tafiya.

Yana cikin tafiya a titi wata mota me bala'in tsada ta gaske ta fara wala wala a
titi kamar zata yi hatsari Allah yasa ya ganganre kasa a hankali yayi parking a
gaban Sahil.
Wani dattijo ne fari da alama bahaushe ne sabo da yana ta waya da hausa sannan
kayan jikinsa shadda ce me tsadar gaske,agogonsa da takalmi duk masu tsada ne
sosai,gaban motar ya bude yana tunanin kiran me gyara sai Sahil ya tambaye shi yace
Baba gyara motar ta samu ne? Yayi murmushi ya kalli Sahil sannan ya furta yaro kana
gani karambani yasa nayi tuki da kaina amma bana driving sabo da ido na baya gani
sosai ma.

Sahil yace bude motar na duba maka to,Dattijon yace thank you ya bude gaban mota
yace ka iya gyara ne? Sahil yace a'a zan gwada dai ko zan samu sa'a,Dattijon yace
to Alhmdllh gwada mu gani gaba daya taki tashi ma mutuwa take a hanya.
Sahil yayi tabe tabensa ya gama yace shiga ka kunna mu gani,Dattijon ya shiga ya
kunna ta tashi normal,yaji dadi yace ta dawo dai dai amma da har wani kuka take
yi,Sahil yace ta warke ai baza ta kara yin komai ba,amma ka dinga kiran Engineer
suna mata service akan lokaci.

Dattijon yace na gode ya zaro kudi da yawa yan dubu dubu ya mikawa Sahil,Sahil
yace ka barshi akan dan wannan sai ka bani kudi bana bukata,Dattijon dai yayi ta
godiya yace sunana Alhaji Isah Danjuma,Sahil yayi murmushi kawai ya juya zai
tafi,Dattijon Alhaji Isa yace zo na rage maka hanya mana ina zaka je?

Sahil yace aini bako ne ma zan koma gida da kaina,Alhaji Isa yace ko kana cikin
masu zuwa cirani? Sahil yace kamar ka sani.
Okay Okay da alamarka kayi karatu?
Na dai fara University aka cire mu sabo da bamu da kokari bama ganewa mu dakikai
ne.
Dariya Alhaji Isa yayi yace kana da kokari mana gashi ka gyara min mota ai kasan me
kake yi tabbas,karka damu muje gidana ni ka kwanta min a rai zan taimaka maka karka
yi rayuwar da wasu suke zuwa suna zubar mana da mutunci hausawa.

Sahil cewa yayi na gode Alhaji a wajen Allah nake nema,Alhaji Isa yace ka taba
ganin anyi ruwan kudi a duniya duk adduar ka? Sahil yace idan Allah yaga dama fa ni
yayi min ruwan kudin? Ni Inshaallah Allahruwan kudi za ayi min daga sama!
Alhaji yace ba a ja da ikon Allah amma duk da haka na gode,Sahil ya juya yayi
tafiyarsa yana cewa haka kawai ka cuce ni za ayi min ruwan kudi.
Tasha ya wuce ya shiga wata trailer din zuwa Abuja,rana tsaka sai ganin Sahil
suka yi ya dawo a rame yayi duhu yayi futu futu,Adnan da Ibrahim suna palo suka
dinga sheka dariya harda buga kafa,Zayna ce ta sakko itama daga sama ta hau dariya
tace masu zuciyar neman kudi.

Sohail ne ya fito tare da janye Sahil suka wuce bedroom dinsu,Sohail yace duk
ka rame sai da na fada maka karka tafi,ya fita yaje kitchen ya kawowa Sahil
girki,Sahil ya zauna yaci ya koshi yace Alhmdllh Allah ka raba mu da cirani.
Sohail yayi dariya,Sahil ya shiga toilet ya dinga wanka sai da ya dade yana abu
daya haka ma brush duk da yana yi kullum amma na yau na musamman ne.
Yana fitowa sai gashi fes da shi ya canja kaya masu kyau,jakarsa kuwa gaba daya
kayan ciki ya zuba a washing machine ya sake wanke su,jakar ma ya wanke ta du ya
shanya sannan yayi sallar Azahar.

Sohail yace tashi muje kaga Baby Maheera kawar mu,kwanaki ta rungume ni sai ta
maka kaima dama nace sai ta dauki Alkawari.
Sahil yace Good hakan yayi muje,fitowa suka yi gidan ba kowa da Alama mutanen
gidan sun fita,a kitchen suka iske Maheera cikin riga da skert yan kanti,Maheera
tace barka da zuwa Sahil tana murmushi,Sohail yana gefe,tace ya hanya? barka da
dawowa,kaci abinci kuwa? Ta tambaya tana murmushin birgewa,Sohail kawai sai yaji ai
bai kamata ace Sahil ta yiwa haka ba,amma sabo da kar Sahil yaji haushi sai ya
wayance yace kin fiye dariya da yawa da murmushi,saukinta ma Sahil kika yiwa amma
wannan surutun da kike ba birgewa a ciki,kin fini son dan uwa nane da zaki zauna
kina surutu? Ki tsaya a matsayinki,abinci dai yaci na kula da abina karki kawo mana
iyayi kice ke zaki kula da shi.

Maheera tace kuka ce ni kawar ku ce duka na ma tuna da alkwarin Hugging da muka


ajiye yau ga Sahil yazo shima ayi masa,Sohail yace ba yau ba sai ya huta ya gaji
yanzu,Sahil yace da Islaha ce ma tayi mana nata zai fi dadi,Sohail yace wace
Islaha?

Sabuwar kawace nima na yo mana ita Allah ta hadu tafi wannan ma Maheera
din,Sohail yace kai anya kuwa zata kai wannan? Ta kai wannan hankali? Sahil yace
tab Islaha dai bata da hankali ita can na tsinceta tana duniyanci,yarinyar nan ta
dinga nuna min barikanci,ni Sahil zata yiwa bariki Allah ya kamata ai,Yanzu ma da
zan taho harda kuka,Sohail yace ubanta ne kai to da zata yi kuka,ga Maheeran mu.

Maheera tana jinsu tana ta dariya tace ayi maka hugging dinka ko? Sohail yace
ance sai gobe ba yanzu ba,muje dan uwa kyaleta tayi aikinta,ka daina kulata sosai
sabo da kar a koreta a aiki,Sahil yayi dariya dan shi bai gane nufin Sohail ba yace
to ni dama ai ban fiye magana ba.

Fitowa suka yi Islaha anya ta kai wannan kuwa Sohail ya sake tambaya dan abin ya
tsaya masa ance zata fi Maheera,Sahil yace sai ka ganta kawai za dai suyi kai daya
da wannan din sai dai kamar Islaha din ta fita cola shape,Sohail yace ji karya kai
yunwar lagos ta kashe ma ido.

Sahil yace fatar Islaha zam flour suluf suluf,Sohail yace uhm ita wannan din
ance maka garin masara ce fatarta? Libis take itama,Sahil yayi dariya yace naga
rayuwa a kira Maheera na bata labarin Lagos,Sohail yace ni yafi cancanta ka bawa
domin nine jininka,fafur Sohail yaki yarda.

Zuwa dare Maheera ta fito kallo palo ta samu sai Sahil da Sohail kawai,Sohail ya
ganta cikin kayan bacci doguwar riga har kasa me dogon hannu,yace me kika fito yi?
Tace kallo mana,Koma daki kiyi baccinki,ba a so mace ta dinga kaiwa tsakiyar dare
har 10 ta wuce tana kallon aikin banza shedanu zasu shigeta koma ciki.

Maheera tace kallon bazan yi ba haba Sohail fuska ya bata ya kalleta ransa a
bace juyawa tayi ba shiri ta koma ciki,Sahil yace mace sai da muzurai ka birge ni.
gobe zamu je ka rakani muyi sabon aski cewar Sahil"
Sohail yana kallo yasan askin Sahil ya lalace amma sai yace ai askin ka fes yake
bro,ba sai kayi ba,ni ya kamata nayi sabo kalli nawa fa duk ya lalace kai kuwa fess
kake kana taba gashinka zai lalace.

Sahil yace baka isa ba sai naje ya zaka barni na dawo kazami,bakin ciki zaka
fara min? Sohail yace Allah ya kiyaye ni nayi maka bakin ciki Sahil im sorry muje
taren.

Washe gari suka yo askin su iri daya gashi yaji gyara,Sohail Allah Allah yake kar
Maheera taga Sahil,sai kuwa suka sameta a palo tace kaiiii mashaallah kunyi kyau
yan biyu na rasa wa yafi kyau ma,Sahil ya harareta dan me zaki yabe ni ke mama ce?
Maheera baki ta bude tace daga abin arziki? Sahil yace ae bana so a yabe ni,Sohail
yace yawwa a kyale mu yana hararar Maheera suka wuce.

Maheera tace uhm ai kan yana kubucewa dole sai anyi hakuri da ku,Sai da suka yi
wanka Sahil ya kwanta bacci Sohail ya fito wajen Maheera tana kitchen tana musu
girki,yace kika ce kin rasa wanda yafi wani kyau a cikinmu? Maheera ta manta ma ta
fada,tace ai kamar ku daya amma kace baka da kamarsa zaka iya bar masa ni ma,Sohail
yace ae zan iya mana ance miki damuwa nayi dake ko sonki nake?
Maheera tayi shuru ya ja tsaki ya fice.

Sai bayan Sahil ya tafi da kwana daya Aunty ganin ba kowa a gidan ta kori
Islaha tace tafi kisan inda dare ya miki,kije duk inda zaki a duniya na gaji da ke
tunda baki da wani amfani a rayuwa,sabo da bakin hali anyi anyi a hadaki da mazan
arziki kinki,ashe abinda kika yiwa Alhaji Umaru kenan? Na tura ki har hotel ki
tayashi kwana ashe da maganin bacci kika tafi kika zuba masa a lemo sai da yayi
sati bai farfado ba yana bacci,kin kusa kashe bawan Allah,sai yau ya kirani a waya
ya fada min sai da aka kwantar da shi a asibiti.

Islaha tace to kawai ni sai naje yayi iskanci dani ni kuwa na zuba masa maganin
bacci a lemo ya sheka bacci,nayi kwanciya ta na sha bacci na da safe na fito.
Aunty tace kinwa kanki hada kayanki ki kara gaba,Islaha ta dauki jakarta tace a
bude taskira lafiya,watarana mazan zasu daina yayin ku duk tsafinku,Aunty da gudu
ta bi Islaha har Islaha ta fice da gudu daga gidan.

Tasha ta wuce ta shiga motar Abuja da kudin asusunta da ta tara sunfi dubu
hamsim,dake karamar mota ce zuwa dare sun sauka bayan sallar Isha,Direct gidan da
Sahil ya bata address ta nufa ruwan sama ake tsulawa kamar da bakin kwarya haka me
mota ya sauketa ta fito,tuni ta jike sharkaf sai rawar sanyi take,tanaturo karamar
kofar gate din taji ta bude ai kuwa ta fado gidan.

A ranta tace gaskiya batan kai nayi ta ya Sahil zai kasance a irin wannan
gida,duk da cewar komai kalarsa ta me kudi ce amma yanda taga yana fama da talauci
ta ya za ace nan ne gidan,har kofa ta nufa tayi knocking ruwa na zaneta,Sahil ne a
palo shi kadai yayi zugum ya zuba tagumi kasancewar yau yaci uban aikin da Ibrahim
ya sa shi me wahala duka motocin su sai da ya wanke,ya share compound ko ina,ya
gyara fulawowin da suke gidan ko ina har garden.

Tashi yayi cike da gajiya ya bude kofar, tsayawa yayi kamar gawa sabo da
tsoro,idanuwansa ya murza sosai ya bude ya ga dai ita ce,kumatunsa ya buga yace ba
ita bace Sahil dawo hayyacinka,ya ga dai tana nan,hannu ya mika a hankali tare da
rike hannunta a tsorace yaji dai mutum ce,yace ah'ah lafiya?
Nice fa Islaha ai Aunty ce ta kore ni shine na taho nan.

Kuma ki rasa wajen wanda zaki taho sai wajena,Kizo ayi miki ciki ko wata
matsala ta faru ace nine,Islaha tana rawar sanyi tace dan Allah ai da mace a
gidan,Sahil matsawa yayi daga kofar yace wuce ciki,ta shige da sauri ya kulle
kofar, Ibrahim ne ya fito ya bi Islaha da kallo yana gadara,yace ke me ya kawo ki
nan? Sahil yace na santa kawata ce hanya ta biyo da ita zata tafi soon.

Sabo da mugunta Ibrahim a ransa yace Allah yasa kayi mata ciki tunda baku da
hankali masifa ta afka muku a ja ku can a kulle a prison kowa ya huta da jaraba
Allah yasa,Mamaki ya tsaya yi ina suke samo yan mata haka ne full option shi kuwa
duk baya samu duk kudinsa da motar da yake hawa,a fili ya kalli Sahil yace kuke nan
kawo mata gida wannan tazo wannan tazo bakwa gajiya da zinace zinace ne sabo da
Allah yayi muku kyau sai ku dinga lalata yaran mutane an muku fada kunki ji,kuje
duniya ce zata yi muku karatu da kanta,wai dan ya bata Sahil a gaban Islaha.

Zayna ce ta fito cikin kana nan kaya riga da wando 3qtr farare ta sha kyau sun
mata kyau amma ba ruwanta da kannen miji na kallon surar ta haka take fitowa
cikinsu suna kallo,

Tana zuwa ta kalli Islaha,ran Zayna ya kara baci tace a ranta a barni naji da
wannan yar aikin Maheera ita kadai ga wata an kara kawo ta na rasa wacce tafi kyau
ma a cikinsu.

Zayna a fili tace wannan fa? Sahil yace sabuwar yar aiki ce aka kawo miki zata
dinga miki wanki da guga,Zayna tace kuma me yasa ake kawo min mata irin wannan
munana,Maheera da kyar na karbe ta ga wata me kiba a duwawu duk sai jika mana palo
take da ruwan jikinta dan Allah jata can kuje ta furta tana yatsina.

Islaha kuwa Ibrahim da Zayna ta gasawa harara suna kallonta tabi Sahil suka
tafi,dakin Maheera ya kaita,ya samu Maheera tana linke kayanta yace ga bakuwa anyi
wata ce sabuwar yar aiki me wankin Zayna,Murmushi Maheera tayi tace to bismillah
amma kinci dukan ruwa shugo.

Islaha ta shugo jakarta a cikin leda yanda ruwa bazai sameta ba,Maheera tace ga
toilet shiga kiyi wanka,room din yaji gyara yana ta kamshi ta shige toilet tana
cewa na gode,Wanka tayi sannan ta gabatar da Sallah Maheera ta kawo mata lafiyayyen
abinci,taci ta koshi,Maheera ta kalleta tace ya sunanki ne? "Islaha" sunana,
mashaallah sunana Maheera ni,Nice to meet you,nice to meet you too.

Kwanciya suka yi a bed dinsu suna hira sama sama cikin kankanin lokaci suka
saba,Sahil kuwa a bedroom ya samu Sohail yace Islaha fa tazo,ban gane ba? Yace
wannan kawar tawa bata gari ba,ni wlh bana so tazo ba ta gari bace,Sohail yace ba
komai muyi musaya na baka ta garin Maheera ka bani wannan zan ji da ita ni zan sa
ta dawo ta gari,Sahil yace to sai dai haka muyi musaya kawai ni da Maheera kai da
Islaha,Sohail yace congratulations ka samu ta gari.

Washe gari Islaha ce ta taya Maheera suka yi girkin tare,Islaha tace muje mu
gyara gidan,Maheera tace karki fara ma idan ba so kike masu gidan su ci mutuncinmu
su kore mu ba,su Sahil ne suke yi aikinsu ne kuma baka isa ka taya su ba,Islaha
tace ni na isa,naga alama tsoro su kike ji.

Sohail ne ya fito Islaha ma bata banbance su ba tace Sahil ina kwana? Sohail
yace ba shi bane,Sahil ne ya fito ta shiga kallon su shima tace ina kwana Sahil
yace ni yanzu ba naki bane munyi musaya nida dan uwana,Islaha zata yi magana
Maheera ta dan taba ta alamar ta amince,Nan take tace to.

Sahil baki ya cuno gaba tare da bare alawa me tsinke ya sa a baki yana tsotsa kamar
yaro
kitchen ya shiga ya iske Zayna tana girki,yace yau da kanki kike girki Yaya ta
palo? Sunan nawa ne Yaya ta palo ka maida ni tsohuwa ka shiga hankalinka wlh, ae
karka dameni bana son munafurci naman kai nake dafawa ogana da hannuna zan tsara
shi yanda zai yi dadi,Sahil yace hmm ai kuwa baza ta dahu ba yau,inji uban wa? Na
dai fada miki baza ta dahu ba yau,tsaki Zayna taja taci gaba da girkinta shi kuma
ya fita,tun 9pm Zayna take dafa naman kai yaki dahuwa har 2am na dare yanda ta zuba
a tukunya haka yake ko ruwan romon bai canja kala ba,Zayna ta ja tsaki ta zauna a
kujera tare da kifa kanta a jikin Sink bacci ya kwasheta nama yana ta tafa a
banza,sai da Adnan ya gaji da jira yazo kitchen din ya tashe ta,tana murza ido tare
hamma tace yaki dahuwa Sahil ne dan iska yace bazai dahu ba yayi min kwari.

Adnan gas din ya kashe yace muje haka na hakura,suka fito suka bar nama,washe
gari da safe sabo da masifa Zayna ta dawo ta kunna gas ta maida naman kai taci gaba
da dafawa,Su Maheera suna ta aikinsu naman kai yaki dahuwa tun tana yi a dadin rai
har ta fara tsaki,Islaha tana satar kallonta tana dariya a boye,tace girki sai ai
sai mu,na godewa Allah duk da bani da iyaye wacce ta raine ni tayi kokari nasan
darajar dan Adam,Zayna ta ja tsaki ta kwashe naman kan tas a leda ta zuba a
dustbin,ruwan ta zubar yabi ruwa tayi fatali da tukunyar tare da furta ku gyara min
kitchen,ta fice daga kitchen din.

Kasancewar weekend yau da yamma Ibrahim ya fita shakatawa Zayna da Adnan sun
fita su ma zasu shakata,sai Twins sai Islaha da Maheera,Sohail yace kar Maheera ta
sake kula shi yanzu ta Sahil ce ita,Fitowa suka yi tare da Islaha,Maheera ta zauna
a kusa da Sahil,Islaha ta zauna a gefen Sohail,Sahil haushi yaji amma ya danne sabo
da Sohail,Shima Sohail haka sai kallon Maheera yake,suna tv game amma hankalinsa na
kan Maheera sai cinye shi ake yi,Islaha tace karka damu Sohail ina bayanka i will
support you, Sahil da sauri ya Kalli Islaha yana zare ido sai kuma yayi
shuru,gajiya yayi ya shiga hararar ta,Islaha ta boye dariyarta tare da kara matsawa
kusa da Sohail,tsaki Sahil ya ja ya tashi ya bar palon tare da haurawa sama.

Sohail ya kalli Islaha da narkankun idanuwansa,kansa ya sadda kasa ya lula


tunani sai kawai ganin hawaye suka yi yana digowa daga idon Sohail zuwa kasa
dis ..dis...dis,Maheera tace lafiya Sohail cike da kulawa,Sohail yana shesheka yana
nuna kansa yace kamar ni....ni....kamar ni da Sahil ace abokan mu sai aure suke yi
amma mu ko auren kare yawa baza mu samu ba,Auren kare yawa dai ai ko shi ma yi,jiya
muka je gidan da Sahil muka ga abokin mu mudassir da matarsa wacce shekarar su daya
da aure suna ta fada,muka samu suna ta fada abinsu,dan Allah wannan ba abin sha'awa
bane? Ni da Sahil sha'awar fadan nan ya kama mu ace mune amma bazai samu ba.

Maheera da Islaha suna kallon Ikon Allah duk da cewa Maheera ta fadawa Islaha
suna da matsalar aljanu ta dinga binsu a haka,Islaha tace kai dan Allah amma sun
birge ni.

Sohail yace baku gani ba ya zage ta itama ta rama,sai naji sha'awar aure...saura
kadan dariya su Islaha suyi dariya,Islaha tace na zaci ma soyayya kaga ana yi irin
ya rungume matarsa suna kiss,Sohail baki ya bude yace Allah ya kiyaye bana fatan
wannan baya birgeni sam,har kin sa raina ya baci ya mike zai tafi Maheera ta rike
shi da sauri tace zauna muyi magana.
Islaha tashi tayi ta haura sama ta kira Sahil suka zauna a compound kamar samari
sunzo zance,Maheera tace Sohail ka tsaya kaji ka saurare ni,yace to ya zuba mata
ido ya nutsu.

Tace har yaushe zaku zauna a cikin wannan rayuwar? Kuna da hankali kuna da ilimi
kuna da basira,taya zaku tsaya su maida ku yan aikin su kuna abu daya,kuna yan uwan
su,wannan fa abin ba me karewa bane Sohail,hannunsa ta rike tace ba sai kun nemi
abu ta hannunsu ba Sohail,Allah ya baku lafiya ku nemi aikin yi da kanku ko karami
ne,kuyi tunanin zaku yi aure ku haifi yara ku zama iyaye kuma,so kuke rayuwarku ta
kare a haka shekara da shekaru kuna bauta musu.

Kuna so kuyi aure ku haihu ku dauki nayin yaranku da matar ku,idan kun tsaya a
haka ta ya hakan zai faru,Sohail ku zauna kuyi tunani ku nemi mafita.
Ni wlh na yarda da ku zaku iya Sohail kuna da hali me kyau kuna da tunani kuma na
yarda.

Sohail yace kuma ina so na dinga siyawa matata leshi,tace to ka gani ko ai dole
ku mike tsaye ku nemi kudi,Sohail yace kin tabbata zamu iya? Maheera tace na
tabbatar,yace na gode Maheera da kokarinki Inshaallah zamu gwada,tace to haka nake
son ji.
Kirjinta ya kafe da kallo yace wai wannan mene amfaninsa ne? Maheera tace ina
ruwanka wai da shi,to sai a dinga budewa ba a saka hijab,dariya tayi cike da kunya
tace dan Allah ka daina kallo na,ni nace ki bude ina ruwana kalla zanyi ya furta
tare da sake matsawa jikinta.

Yanda Maheera tayiwa Sohail bayanin su fara neman na kansu haka itama Islaha ta
cewa Sahil sabo da baki suka hada,Sahil yace zamu yi shawara,tace yawwa Baby ta
furta da tsokana,Sahil yatsa ya sa a baki yana tsotsa da shagwaba daga ance Baby,
ya dora kansa a kafadarta yana kukan shagwaba Uhum...uhmmm....
Dariya kamar cikin Islaha zaiyi ciwo.

Bayan su Sohail sun koma bedroom ko shirin bacci kasa yi suka yi kowannen su ya
zauna a bakin gado yayi shuru ya lula tunanin rayuwa akan maganar su Maheera,kowa
da abinda yake sakawa a ransa.
Sahil ne yayi magana yace Islaha ta fada min maganar da ban taba tunaninta ba sai
yau,Sohail yace ashe fa ana yin aure a haihu ai na tuna kuma dole sai da kudi,Sahil
yace kawai mu fadawa su yaya zamu fara neman aiki ko karami ne a garin nan,Sohail
ya furta nima haka nake tunani kawai ayi hakan,suka gama tattaunawa sannan Sohail
akan da safe zasu sanar da su Adnan kawai.

AsmaBaffa
[7/17, 3:17 PM] Asmabaffa: 🪸MUMMUNAR DABI'A
🪸

21-25

Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA NE GA 'YATA TASNIM

Page naki ne
Sadiya Muhammad

https://chat.whatsapp.com/CShgPK2Dsi8GIrvd5njOML

Gaskiyar hausawa da suka ce wata miyar sai a makota🥳💃idan kina bukatar shan wannan
miya kuma zaki sha ta mai yawa ma💃🥳Zance ne ake na *R&U EXCLUSIVE KITCHEN AND MORE*
Indai kayan kicin ne a kan farashin sari🙌 sadakallahul Azim an gama zance, kayan
daki, bedsheets, takalma jaka kayan sakawa maƙura kenan, *R&U EXCLUSIVE KITCHEN
AND MORE* nan nake kira da kasuwar ki a hannun ki😘maza masu hada kayan lefe duka
*R&U EXCLUSIVE KITCHEN AND MORE* suna maraba. Domin neman karin bayani 07034559202
domin gani da ido taba link ki shiga domin siyayyar kayayyaki a farashi mai rahusa
😘
Ko wanka basu yi ba haka bacci ya kwashe su da wannan tunanin.
Washe gari da safe bayan sun gama aikin gidan da suka saba,Sohail sanye yake da
jallabiya fara shi kuwa Sahil shadda ce a jikinsa milk color, a zaune suka samu
Ibrahim da Adnan a garden sun baje laptop da takardu ga lemo a gefe suna korawa
suna ta aikin Office,tun kafin su Sohail su karaso Suka hade fuska ba mutunci,bayan
sun karaso suna daga tsaye Ibrahim yace "what"? Sohail ne yace dama Yaya mun yanke
shawara ne muma muna son mu fara aiki,Adnan da wani bala'i ya dago da lemo a
hannunsa ya watsa musu a jikinsu yace me kuke nufi? To wallahi wannan kamfanin ba
gadonku a ciki,babu aikin da za a baku kuyi a ciki ku din banz.....kafin ya rufe
baki Sahil yana goge rigarsa da ya jika masa da lemo yace relax mu ba a wajen ku
muke nema ba,a duniya zamu nema wajen bare da yardar Allah,kawai fada muku muka
yi,Adnan dariya ta kwace masa,Ibrahim ma dariya ya saki yace Allah ya bada sa'a aje
a nemo aiki mu gani.

Sohail da Sahil suka juya abinsu tare da tafiya dakinsu suka hada takardun su
har wanda suka fara a kasar waje,Wanda bashi da amfani sai in zaka ci gaba da
school ka kai makaranta,Sahil zama yayi da biro a hannunsa ya fara rubuta takardar
neman aiki.
Yana ta rubutunsa harda furta i can do it Sir.....yes....zan iya mana zan iya ,ci
gaba yayi da rubutu i have power, Sohail yana ji yace kai turanci bai hau ba Man
power zaka saka kace i have man power, Sahil ya rubuta i have Man power, Yanzu kayi
turanci cewar Sohail,suna ta rubutunsu suka gama tare da zuba takardu a cikin
folder sabuwa.

Wanka suka sha kowannen su farar suits yasa tare da gyara gashinsu ba karamin
kyau suka yi ba sai ka rantse masu hankali ne,suna kamshi suka fito lokacin Islaha
da Maheera suna gyara palo,Islaha tace sune zasu yi aikin kuma ko an kore su baza
su tafi ba su kam sunga gidan zama.

Tsayawa suka yi galala suna kallon twins sun watso kyau,Zayna ce ta fito tana
shan tea a hannunta,ita kanta sun tafi da ita ta tsaya tana ta kallon su a sace a
ranta tace ina ma daya ne a ciki mijina,tunowa tayi basu da kudi sai ta tabe baki
tare da jan tsaki ta juya inda ta fito.

Islaha tace ban taba ganinku kunyi shiga haka ba kunyi kyau mashaallah,Sohail ne
yace mun gode kin tabbatar munyi kyau? Islaha tace sosai ma yau mata sai....Sahil
ne ya katse ta karki dami mutane,Maheera kallon Sohail tayi taji kamar kar ya fita
ma yayi ta zama a gida,Haushi taji ta bata rai,Sohail yace baki ce komai ba tace me
zance sai kun dawo Allah ya bada sa'a a samu aikin suka ce Ameen,wucewa zasu yi
Sohail ya ja hancin Maheera yace kefa kika ce a nemi aiki kuma sai kiji haushi sabo
da zan fita ko so na kike yi ne? Maheera da sauri tace ni haka nace ina sonka?
Allah ya kiyaye aljanun karya suke yi da suka fada maka,Sohail dariya yayi yace
shike nan dama ni Islaha nake so ba ke ba,Maheera ta dauke kai,Sahil yana jinsu yau
yan maganar basa kansa ko uban waye in baiga dama ba bazai kula su ba ko me zaka
ce,Haka suka fita Maheera ta zauna a saman kujera ranta a bace.

Islaha ta sheke da dariya tace lallai Maheera kina da aiki kuwa wlh,idan kika ce
kar su fita ma ai bakya kaunar su aiki fa zasu nemo,Maheera ta mike bata ce komai
ba suka gyara ko ina na gidan komai sai da suka yi.
Ibrahim ne ya fito sai faman kallon Islaha yake kamar maye,Islaha tana sane da shi
ta kalle shi suka hada ido ya sakar mata murmushi tare da cewa kawo min tea,Wucewa
tayi kitchen Maheera tana daki ta shiga wanka,Tea ta kawo masa yanda ya
bukata,kallonta yayi yace zauna mana,da mamaki tace a nan din mu ai yan aiki ne,ni
nace ki zauna ai.

Haka ta zauna a hankali sai kallonta yake yana murmushi,yace 'yar wanne state ce
ke? Islaha tace taraba state Maheera kuma yar Adamawa ce asalinsu amma a sule ja
suke da zama,Ibrahim yace ai ke wayayya ce naga alama,Islaha tace uhm bari naje
zanyi aiki"
ba a son ransa ba yace okay kar na takura ki, mikewa tayi da sauri ta bar wajen ta
wuce bangaren su,Ibrahim ya bita da kallo yana murmushi.

Sohail kuwa shigar da suka yi kamata yayi a gansu a mota amma a kafa suka
fito,suka tsaya tare da zubawa hanya ido Sahil yace kabi hanyar dama ni nabi hanyar
hagu kasan ba kowa zai dauke mu aiki har mu biyu ba a waje daya,Sohail yace ka kawo
shawara kawai yabi hannun dama Sahil yabi hagu yana cewa duk wanda ya riga gamawa
kawai ya wuce gida,mu hadu a gida.
Yanda suka fita neman aikin duk wani kamfani ko masana'anta sai sun shiga ciki
suce aiki suke nema,Wani wajen ayi musu rashin mutunci,wani wajen kuma a rabu
lafiya wani wajen kuma a kulle ko securitues su hana shiga.

Sohail ya gaji da tafiya da yawo tun sassafe suke abu daya har yamma tayi 4pm ma
ta wuce domin idan lokacin sallah yayi masallaci suke shiga na kusa suyi sallah su
dora daga inda suka tsaya.
Suit din ma duk sun cire ta saman sabo da wahala,har necktie din sun warware
shi a haka kowannen su ke tafiya,last kamfani Sohail ya gani yace daga wannan gida
zan koma sai kuma gobe idan Allah ya kaimu,Sohail ya iske kofar a kulle alamar ba
mutane ya bubbuga shuru,yaci gaba da dukan kofa har ya gaji ga rana ya hada gumi,a
bakin wajen ya zauna da folder a hannunsa ya zuba tagumi,mikewa yayi a hankali
kamar zaiyi kuka ya shiga taxi ya nufi gida,Sahil kuwa har after 5 yana zaune a
jikin bishiya yana ta bacci a haka ya jefar da folder a gefe,daga dan zama zai huta
sai bacci,sai wurin 6pm ya farka ya tashi shima da kyar yake daga kafa ya shiga
mota sai gida.

Maheera suna zaune suna kallo sai ga Sohail ya fado cikin dakin ransa a bace
yana tafiya da kyar ya dafe kugu da hannu,bai ko kula kowa ba ya wuce tare da
haurawa sama,suka bishi da kallo sun san ba nasara ba a dace ba shuru suka yi
kawai,yana shiga bedroom ya zauna a kasa ya kwanta a kasan tile yana kallon sama
hawaye suna ta faman sintiri daga idanuwan Sohail,ba a dade ba Sahil shima haka ya
shigo yana nishin gajiya ya wuce bai ma kula da mutane a palon ba,Ya fada dakin su
ya shiga,saman bed ya fada shi yana wash....

Islaha ce ta shirya abinci a tire ta nufi dakin zata kai musu,Adnan ya fito yace
ke idan ba aiki ba me yake kawo ku sama? Sabo da kuyi mana sata ko? Uban me zakuyi?
Islaha ba tsoro tace Oga ba wajenka zanzo ba gida dai ai ba kune kadai masu shi
ba,twins ma suna da hakki domin gidan uban su ne suma,kun zauna ba tausayi ba imani
sai azaftar da bayin Allah kuke yi,a tunanina ku masu nemo musu aikin yi ne don
ganin rayuwar su ta inganta,ku tuna wallahi akwai Allah wannan zaluncin yayi yawa
ku ko tausayi baku da shi, har matarka me wuya kamar na zabuwa ka bata dama tana
fada musu abinda taga dama.

Abinci ne zan kai musu kuma wallahi ba wanda ya isa ya hanani na kai musu babu
shi a duniya,Adnan baki bude yace Iyyeeeeeee.... fantastic,wato an kawo ki an
taimakeki an baki aikin yi shine kike ganin kin isa,Islaha tace ni baku taimakeni
ba,zaman Sahil nake yi wajensa nazo,karuwarsa ce ke? Islaha tace ae karuwarsa ce ni
sai me? Ta ja tsaki ta juya zata wuce Adnan ya fisgota tare da kifa mata mari yayi
ball da tire din abincin ya watse,ya zazzaro mata ido yace yan biyu na tsane su
bana kaunar ganinsu.

Islaha tace wallahi Allah ya isa kuma sai na kai abinci sai na kuma hado wani na
kai musu,Adnan yace ke ga me taurin kai ko zanyi maganinki a gidan nan zaki raina
kanki ya sauka kasa,tace kai din banza zaman lagos fa nayi wallahi karr nake duk
sai nayi maganinku a gidan nan kuma bazan bar gidan ba,nazo kenan.

Ta koma kitchen ta hado wani abincin ta haura sama har bedroom din su Sohail
tayi knocking,Sohail yana daga kwance a kasa yace come in,a hankali ta tura kofar
ta shiga ta gansu a haka bata ji dadi ba ta ajiye musu tace,rayuwa sai hakuri kowa
da kaddararsa kuyi hakuri, inshaallah zaku samu aikin yi tana fadar haka ta fita ta
basu waje.
Tana fita tazo ta gyara inda Adnan ya zubar mata da abinci.
Yan biyu sai dare suka yi tashi suka ci abincin sannan suka yi wanka ko fitowa basu
sake yi ba suka zauna kawai suka fara baccinsu.

Maheera tana zaune ta mike itama ta nufi dakin su Sahil,Zayna ta dawo daga
unguwa ta shigo tana karkada key din mota,Maheera ta kalleta kawai zata wuce Zayna
tace ke ina zaki je wannan part din masu gida ne idan ba aiki ba waye ya aikeki?
Maheera juyowa tayi zata dawo Islaha tace dalla jeki mu ba wanda zamu kyale, gidane
baza mu fita ba wallahi bana tsoron kowa rayuwar lagos nayi iskanci ne kawai bana
yi amma indai da baki za ayi magana ba wanda ya isa naji tsoronsa.
Zayna ta juyo a fusace da matukar mamaki tace ke......a gidan mijina? Gidan aure
na kizo kina daga min murya an dauke ki aiki amma kizo ni kina daga min murya?
Islaha tace miji manya muma zaman wasu muke duk da ba a daura ba zaman su
muke,Zayna tace to kuwa sai nasa kin bar gidan nan bari Adnan din ya shugo,Islaha
tace shima adnan din naci ubansa ai ta kansa na fara baki sani ba,inci uban mijin
inci na matar duk na gama da ku,Maheera tace Islaha kiyi shuru,Islaha tace ke kike
jin tsoron su wlh.

Zayna sama ta wuce tana huci.


Maheera bedroom ta koma tana yiwa Islaha fada gidansu fa muka zo cin arziki
muke,kuma kin san biyana akeyi ina da matsala a gidanmu nima indai rashin kunya ce
na iya amma sabo da Iyayena da yan uwana nake hakura ina biyayya.
Amma ni duk layinmu ma tsoro na ake ji amma rayuwa da yanayi yasa na sakko,ki
dain jansu da fada ki bari mu cimma buri sai mu fara bude musu munanan halayen
mu,dariya Islaha tayi tace ina da hot temper bazan iya shuru ba kiyi hakuri amma
zan fara mugunta a gidan nan,zaki ga tsiyar da zan dinga yi musu inda kika ga bera
haka zan dawo

Wayar Maheera ce tayi kara ta duba taga kanwarta ce Juwairiyya ta daga tace yan
university ya aka yi? Juwairiyya tayi dariya tace Alhmdllh Aunty kayan abincina ya
kare sannan akwai wani kudi zamu biya 15k na escortion zamu je wani kamfani,Maheera
tace kin san wata yayi nisa Juwairiyya bani da ki sisi wlh yanzu gashi jiya kudin
hannuna na turawa Ammar ya siyowa Mama magungunanta su ma abincin su ya kusa
karewa sai an siyi wani, Juwairiyya tace Aunty kina kokari ma an gode Allah ya buda
bari mu jira mu gani me Allah zaiyi,nima zan duba idan na samu zaki ga Alert cewar
Maheera,to Aunty na gode cewar Juwairiyya ta kashe wayar.

Islaha ta tambaya kudi za a bata? wai haka tace ni yanzu ma ban san ya zanyi
ba,Islaha tace ga 20k cikin kudin asusuna ki tura mata tunda kinga ni ba abinda zan
siya,Idan na karbe miki kudi ke kuma fa?
Islaha tace ba komai ai mun zama daya,rayuwa ce fa ni nasan wataran wa zai taimake
ni? Kema kina taimako duk me taimako Allah baya hanashi sabo da haka karbi kawai.
Maheera karba tayi tana ta godiya tana jin dadi.

Washe gari Adnan ya samu Ibrahim yana masa magana akan Islaha lallai ya koreta
ta bar musu gida taci mutuncinsa taci mutuncin matata.
Ibrahim yace Islaha kuma? Ae itace,
Gaskiya ba halinta bane kuma ma ai yarinya ce baka ganin bata da wayo kawai kayi
hakuri zuwa wani lokaci su Sohail ne suke ziga ta,Adnan yace yarinyar nan bata da
hankali fa,Ka dai dan kara hakuri tukun,fafur Ibrahim ya hana a kore ta shi baya
ganin laifin Islaha sabo da sonta yake tsakani da Allah kuma burin aurenta yake.
Twins ma yau haka suka sha wanka suka fita neman aiki basu samo ba,wasa wasa
sai da suka kwashe sati kullum suna garari da takardu amma ba labari,hakan yasa
suka ce sun hakura baza su samu komai a duniya ba suka daina fita ma gaba daya
kullum suna gida tare da su Maheera.

Zayna ce ta aiki Maheera kasuwa ta siyo abinda babu na kitchen,tana hanyar


tafiya a kafa,sanye take cikin t-shirts brown da wando ta saka hijab daidai gwiwa
tana tafiya a nutse,Wani mutum ne shi ba tsoho ba kuma baza a kirashi da yaro ba
yayi parking da motarsa cikin sauri ya bude motar ya fito da kansa waje yana ta
faman tari yana shidewa yana jan numfashi da kyar, yana ta daga hannu alamar a
taimake shi,kasa ya fado daga cikin motar,Maheera ta lura da hakan da sauri ta
karasa inda yake tana tambaya lafiya? Da me zan taimake shi,gaban motarsa yake
nuna mata da yatsa,ta duba da sauri ta ga Inhaler wacce masu Athsma suke amfani da
ita,da sauri ta sa masa a baki,a hankali ya fara dawowa hayyacinsa har ya gama
dawowa dai dai.

Kallon Maheera yayi yace na gode kin taimakeni idan ba damuwa dan Allah ki bani
number dinki za mu gaisa,ba musu ta bashi number dinta ta kara gaba,yana ta roko ta
tsaya ya rage mata hanya amma taki yarda.

Bayan ta koma gida da kwana uku ta manta ma anyi wannan sai ga kiran
mutumin,dagawa tayi ganin bakuwar number gaishe da shi tayi ya amsa sannan yace
sunana Alhaji Saminu wanda kika taimaka lokacin da Asthma dina ta tashi,tace oh ya
gida ya aiki,yace lafiya Alhmdllh,ina sake godiya fa Maheera,tace ba komai wlh ya
wuce ai,yace ni sunana Alhaji Saminu Shehu kamar yanda na fada miki,nine me
kamfanin J&S nigeria,ina da branch a lagos da Rivers sai kuma nan Abuja,Banyi
niyyar sanar dake ba amma da kika ganni fitowa nayi daga gida zan je wajen
abokina,Maheera tace mashaallah.
Ci gaba yayi da magana dalilin da yasa na miki magana naji dadi kin taimakeni,so
ina da matata da yarana uku,ina so a matsayina da kika ji ki fada min abinda kike
so ni kuma inshaallah zan miki.

Maheera taji dadi tace wlh bana bukatar komai na gode amma akwai saurayina da
dan uwansa mun dade muna neman aiki kuma an kusa bikinmu Sir amma basu samu aikin
ba,'yan biyu ne kuma dan Allah ka taimaka ka bawa ko mutum daya ne aikinyi,amma a
takaice idan ba dama zamu iya haduwa na baka labarin su ko zaka tausaya,Jamilu yace
ba damuwa bari na baki address din Office dina,ta dinga godiya tana murna.

Suna gama waya ya tura mata address yace tazo yanzu yana Office dinsa ma.
Shiryawa tayi a gurguje cikin fitted gown ta leshi blackblue ta yafa mayafi me kyau
ta saka takalmi kalar mayafin da jaka ta fice da sauri,A palo ta samu Sohail,Sahil
da Islaha suna kallo,tace zanje unguwa yanzu zan dawo,Sohail ya kalleta yace kuma
sai da kika yi kwalliya kice kawai party zaki je,party da safe 11am fa,to baza ki
fita ba,Maheera tace hmm mamata zan turawa kudi,karya kike Sohail ya bata
amsa,Sahil yace yanzu suka yi waya da wani Saminu,Sohail yace
Saminuuuuuu....Maheera juyawa tayi kawai zata tafi abinta Sohail yace in kika fita
kin gama yawo na fada miki.

Maheera kofa ta bude tayi ficewarta,Sohail yace za ayi jaraba....yau a gidan


nan,Sahil ya fara dariya yana kallonsa yace wai ko sonta kake ne? Sohail yace so?
na so wannan? Maheera ce fa ita zan so kawata ce fa? Ka kyaleta taje to,yace ai yau
wannan fadan da jarabar duniya sai an yita a gidan nan,Islaha tana ta dariya tace
wlh da nice kai Sohail auren Maheera zanyi.
Sohail ya nuna kansa ni na aure ta inyi me da ita? tsaki ya ja ya kalli Sahil yace
kai ko haushi ma baka ji ba kana kallo ta fita,Sahil yace to ina zan iya da ita.
Sohail yana ta jira ko aljanu zasu haska masa inda taje shuru ba labari,takaici ya
kama shi, Islaha sai jinsa tayi yana cewa ba wani bayani? Kamar wani boka,yana cewa
ba rahoto? Mene ne rahoto a kanta? a bani bayani shuru bai ji komai ba.
Sahil ya tambaya yace kai fa? An baka bayani? Sahil yace shuru ba labari.
Sohail mikewa yayi tsaye sanye cikin jallabiyya yana sintiri a palo ya kasa
zama.

Maheera kuwa har katafaren building din Saminu ta nufa,har tanfatsetsen Office
dinsa aka kaishi wanda ya gaji da tsaruwa,kujera ya nuna mata yace Zauna
bismillah,Zama tayi a nutse sannan suka gaisa,yace I'm busy bani labari a gurguje
ina da meeting,Maheera ta kalli Saminu sanye yake cikin wani yadi wanda bai da wani
tsada in ka ganshi sai ka rantse da Allah ba shine me kudi haka ba,sam kudin babu
kama a jikinsa.
Labarin su Sohail ta bashi a takaice,yace amma na tausaya musu wannan wanne irin
azzaluman dangi ne amma laifin iyayen ne da uwarsu da uban sune masu laifi babba.
Bamu neman ma'aikata yanzu babu wajen daukan yan aiki sam amma zan iya daukan
mutum daya a ciki,zan sa a koya masa aiki,idan naga kwazonsa zan bashi babban
matsayi sannan sai ya koma karatu in ya gama sai ya kawo min takardunsa,kije ki
tuntube su" su zabi daya a ciki sai na bashi aiki,amma nayi ne sabo da ke, jin
kince shi zaki aura,Maheera tace na gode tana ta godiya suka yi sallama ta fito.
Tana zuwa gida Sohail kawai ta samu a palo ransa a bace yana ta zirga zirga
tasan hali,da kuka ta shugo tare da dingishi da kafa,rudewa yayi ganin ta dawo da
kuka sai ya manta da fadan da zaiyi,ya karaso da sauri ya riketa yana tambayarta
menene? Lafiya?

Maheera tace faduwa nayi mota ce ta taho kamar zata kade ni garin gudu na
fadi,Sohail yace sannu to muje asibiti? tace no ina jin sauki,yace okay to tana
dingishi sai ya dauketa cak,taso tayi dariya,sai ta fuske ya kaita har
dakinsu,Islaha tana kwance a gefen bed yace matsa ke,Islaha ta matsa can baya ya
kwantar da Maheera sannan ya cire mata takalman kafarta ya adana su har jakar a
inda take ajiyewa ya sa mata,mayafin ya cire mata a hankali ya ajiye gefe ya kalli
Islaha yace Jinya zanyi ki sauka kwanciya zanyi,Ba shiri Maheera ta mike zaune
tace naji sauki wlh dama kadan ne,Sohail yace idan kinga banyi jinyar nan ba to na
mutu,Islaha tana ta dariya ganin yanda Maheera take ta zare idanu.

Sohail Saman bed din ya haura ta mike zata gudu ya jawota ta fado kansa,tace dan
Allah ka bari ba kyau,yace duk masu jinya haka suke da raki, Islaha kawo min ruwan
zafi a bowl,Maheera tace na shiga uku dan Allah Sohail na yafe ka kyaleni,tsaki
yaja tana rike gam gam a jikinsa,sai da Islaha ta kawo ruwan a bowl da towel karami
tana ta yiwa Maheera dariya,Sohail duk ya shaketa a jikinsa,kokawa suka shiga yi
shi Ita,hakan sai ya masa dadi kamar wasa suke yi,ba shiri tace iya kafa ne gata ka
gasata ta miko masa kafar,sai haki suke faman yi,kafarta me kyau fara ya jawo tare
da dorata a cinyarsa ya matse towel din yana dannawa a kafarta,ruwan yayi zafi fa
Sohail ka rage zan kone,ko kulata baiyi ba sai da ya gama gashinsa sannan ya mike
ya fita.

Islaha tana dakin bayan ya fita Maheera tace to dariyar me kike kuma? Islaha
tace wlh duk ya taba miki duwawu da kirji kamar ya kama namiji,Maheera tace ina ji
ai,dadi kika ji kenan? dariya tayi tace uwar dadi naji,ki zauna na baki labari amma
to be sincere jikinsa wlh dadi kamar kar a daina ta furta tare da rufe fuskarta da
tafin hannayen ta, Islaha tayi dariya tace yau kwana zakiyi kina tunaninsa kenan?
Hmm kawai tace.

Zama tayi Sannan Maheera ta bata labarin Alhaji Saminu da haduwar su da kuma yau
abinda yace,Islaha sai murna tace Alhmdllh,yanzu su biyun zaki samu kiwa bayani
daya sai ya barwa daya.

Zuwa dare ganin su Adnan suna palo sai Maheera ta kirasu a sirrince suka koma
garden har Islaha,Zama suka yi Maheera ta basu labarin komai akan aikin,Farin ciki
ya kama Sohail da Sahil suna ta murna,Sohail yace na barwa Sahil yaje yayi
aikin,Sahil yace a'a kai zaka yi ni na fika zafin nema.
Suna haka Islaha tace ga takarda mun rubuta daya yes daya no wanda ya dauke yes
shine zaiyi aikin wanda ya dauki no sai yayi hakuri sai nan gaba rabonsa in ya
zo,Takarda ta watsa guda biyu a nanade,Sohail ya zaba Sohail ma ya dauka ko wanne
ya bude,Sohail shine ya dauki Yes Sahil kuma no? Sahil yayi dariya yace Allah yayi
zabinsa.
Maheera tace to sai ka tattara iya takardun da kake dasu gobe kaje ka same shi a
Office,ga address zan baka,Sohail yace na gode taho Islaha na rungume ki,Islaha da
wasa ta tafi kamar gaske,Sahil ya riketa yace ba kyau fa babu aure,Maheera har ta
sandare a zaune sai taga Islaha tana mata dariya a sace.

Sohail a wajen suna hira amma shi ya dauki tsinke sai faman zana zero 0
yake,Maheera tace dan Allah karka je ka zana musu Zero a takardu ka kula sosai kayi
aiki me kyau,Sahil yace ai mun sha wahala kafin a samu Inshaallah zaiyi kokari ko?
Sohail yace Allah ne masani yaci gaba da zana Zero,Sun dade kafin su koma ciki.

Washe gari Sohail Ya dau wanka kace shine me kamfanin yana kamshi ya fice da
sauri yana gyara agogo,Adnan da Ibrahim suka bishi da kallo sun ganshi da
takardu,Ko kulasu baiyi ba bai ma nuna ya gansu ba ya wuce,dariya suka yi Ibrahim
yace ana asarar wanka a hanya,Adnan yace wallahi dariya suke bani.
Sohail kuwa sai da yaje aka masa iso ciki wajen Ogan,yana shiga yaga yar yarinyar
Oga Saminu kyakyawa da ita tana wasa a Office din,shi ai ya samu abin so sai ya
dauketa yana dariya yace taho muyi wasa,yana ta mata wasa,Saminu a duniya yana so
yaga me son yaransa,ai sai yaji kaunar Sohail,Yace kaine wanda Maheera tace? Yace
ae nine ya mika masa hannu suka gaisa,daya hannun kuma yana dauke da yar
Saminu,yace kaine wanda zata aura kenan mashaallah kamar ba dan kasar ba,Sohail
yayi dariya yace haka ma dan uwana yake baza ka gane mu ba,zama yayi ya nutsu
yarinyar tana cinyarsa,Oga Saminu sai wani washe baki yake an dauki yarsa,yace
sauketa muyi magana to,Sohail ya ajiyeta yace Maheera tace nayi kokari na nutsu shi
yasa zan ajiye wannan yarinyar kuma yanda tace sai na dage sosai kamfaninka sai
yaci gaba a duniya,Alhaji Saminu yace Alhmdllh na yaba da kwazonka wlh,ka kwanta
min a rai kuma naci alwashin baka duk wata gudunmuwa,Sohail yace na gode.

Takardunsa ya duba ya kalli yanda duk A1 ne da shi,yace ga kokari kuma,Nan take


ya kira wani yaronsa yace Idris ga wannan kaje da shi office dinka ka fara masa
training ka koya masa komai yanda muke tafiyar da company din nan sannan ka nuna
masa yanda zai dinga tsara aikin a computer da abinda zai dinga yi,yace Okay Sir a
wanne fannin za a ajiye shi,ka fara nuna masa wannan matakin zan tura maka me zaka
nuna masa idan ya iya nan da 3days zan dawo da shi Office dina nan ma sai naga
kwazonsa to ni nasan matsayin da zan bashi,yace an gama Sir, ya ja Sohail suka
tafi,inda aka ci sa'a aikin daga wanda za ayi a computer sai takardu,Sohail ga
Aljanu kafin azo a koya masa waje ma ya iya,Idris mamaki ya kamashi yace wai ka
taba aiki irin wannan ne? Sohail yace kai dai muci gaba kawai,Idris yaga abin
mamaki yau,idan ya bashi aiki kafin wani dan lokaci ya gama aikin,Aikin Idris da
sai yayi wata yana abu daya sai yaga Sohail cikin lokaci kadan wai ya gama shi,ya
duba kuma babu gyara ko tangarda.

Suka dawo fannin takardu duk paper daya ko a cike take da rubutu kallo daya ya
gama da ita ya jawo wata mamaki ya kama Idris,kallo daya ya karanta ya fadi komai
da ake nufi,Aikin da aka ce sai 5pm za a gamawa Sohail 12pm an gama shi,Idris ya
saci jiki ya tafi Office din Alhaji Saminu ya dinga bashi labarin abinda ya
gani,Saminu yasan wani labarin nasu yaji dadi,a ransa yace in hakane wannan kamfani
zai ci gaba aiki da me aljanu irin wannan akwai dadi,nan gaba in naga yanda abin
yake babban matsayi zan bashi kai har manager zan bashi na duka kamfanunuwa na su
koma hannunsa indai yana da amana.

Sohail aka dawo da shi Office din oga Saminu kawai ya bashi System ya dinga
zuba aiki,Office Office aka dinga kai Sohail sai gama musu aiki yake kamar inji ko
inji bazai haka ba,Oga murna kawai yake,kuma idan suna shawara yanda kamfani zaici
gaba sai aji ya kawo shawara me amfani wacce tafi ta kowa,Yau Oga yinin farin ciki
yayi a Office.
2pm nayi sai ga Maheera dauke da Flask na abinci lafiyayye ta shiryo shi ta
kawowa Sohail,bata shiga Building din ba daga bakin gate ta tsaya ta kirashi a
waya.

Fitowa yayi ya wani soke biro a bayan kunnensa shi ga ma'aikaci,Maheera tayi
tayi dariya ta more,yana zuwa yace sabo da na soke biro a bayan kunne kike min
dariya,me kika zo yi? Abinci na kawo maka,murmushi yayi tare da shafa gefen
fuskarta yace na gode wai so na kike ne? Maheera tace a'a kawai kaunarka
nake,Kauna? Ni bana son Kauna kawai so nake so ya furta yana turo jajayan lips
dinsa,ni zan tafi ko ka ci abincin ka bani na koma da shi gida,Haba ki sha wahala
ki kawo kuma na cinye na kuma baki ki tafi dashi ai idan nayi haka na zama Adnan
marar Imani,kije zan taho da su,please karka manta,bazan manta ba Hajjaju kin kusa
zama Hajiya,a makka za a daura mana aure,Dariya Maheera tayi tace hmm,yace Allah da
gaske nake da ni da Sahil da Islaha dake zamu tafi a daura mana,Sahil ne waliyyi
na,ki fada a gidanku,Maheera tace ba ruwana sai kace aljanu ne zasu daura,yace to
shike nan,ina siyan mota zaki ganni na daukeki munje gidanku naga danginki,ranar
Mamanki ta shiga uku ta lalace da kudi,kudi dai kudi dai,ke har wani kudin zan bata
nace ungo wannan ki zubar da su me rabo ya tsinta,Maheera tana ta dariya.

Flask din ya ajiye ya matsa jikinta sosai kamar zasu manne da juna,rungumeta yayi
yace na gode,jikinta ta kwace ta karfi ta matsa baya tace ana kallon mu fa,kuma ni
ba matarka bace,Sohail yace ke da a kauye kika girma ba a san me zakiyi ba mene
haka? Dariya tayi ba shiri wai Sohail ke fadar haka,juyawa tayi ta fara tafiya zuwa
yayi ya dauketa cak ya tafi da ita a haka tana cewa ka sauke ni wai mene haka
iskanci ne fa wannan,Sai da yayi nisa ya sauketa yace na rage miki hanya,karki ta
wahala,murmushi ta saki ta juyo tare da tsura masa kyawawan idanuwanta,juyawa yayi
yace bye ya koma ciki da sauri.

Abincin da ta kai masa sai da yaje Office din Oga Saminu ya bashi yace ko zaici
yace na gode na fita lunch yanzu, wajen Idris yaje yace suci tare,tare suka ci
abincin na Maheera,Idris sai santi yake.

Sai 4pm suka tashi,Oga Saminu yace Sohail muje na saukeka a gida naji ma unguwar
mu daya ashe,ya sake furta Sohail tabbas babu tantama zan baka aiki sannan nan gaba
ma zan canja maka matsayi inshaallah indai muna raye,Sohail yayi ta godiya suka
fito,Driver ne ya bude musu mota suka shiga katuwar motar Saminu ta gani ta nunawa
sa'a suka wuce gida.

Suna tafiya Sohail yace gaskiya Sir baka nuna kai me kudi ne,magana ta gaskiya ka
dinga cin kudinka,a yanda kake da kudi ya kamata a dinga ganinka da securities da
motoci na binka ko uku ne,sannan sutura ma gaskiya ka godewa Allah ka dinga saka me
tsada,kalle ni fa bani da sana'a siya mana akeyi amma takalmi na kadai sai ya siyi
yadin jikinka,Alhaji Saminu yayi dariya yace kullum fadan da mukeyi da matata kenan
wallahi,ita dole sai na canja ni kuma haka nake ban damu ba,Gaskiya ka canja ai
shine godiyar Allah din aga banbanci,Alhaji Saminu yayi dariya yace amma a haka ake
ce muku baku da hankali gashi muna magana ta nutsuwa,Sohail yace to da aka daukeni
aikin za a bani mota wai?

Alhaji Saminu yace za a baka mota me tsada ta gaske sannan za a baka gida a
estate me kyau,Sohail sai murna yace dama mun iya mota tun muna yara kawai dan kara
gogewa zamuyi, mashaallah cewar Alhaji Saminu,ya sauke Sohail a bakin gate dinsu ya
wuce gida, Sohail ma ya shiga gida dauke da takardu a hannunsa da aka ce ya karanta
a gida ya cike su.

Yana shugowa ya samu Adnan da Ibrahim a zaune a palo suna ta aiki a System sun
saka Sahil Mopping yana ta mopping haka kawai akan Zayna tace su Islaha ne suka yi
Mopping shine suka ce wallahi sai ya sake yin sabo.

Sohail yana shugowa ya karbe Mopper din yayi jifa da ita yace muje dan
Allah,Adnan ya zaro ido yace Sohail nine na sashi da tsawa yayi maganar, Sohail
tsawar yayi shima kamar wani zaki yace bazai yi ba na hanashi,ai mun fada muku mun
daina aiki a gidan nan aikin kudi muke nema sabo da haka baza muyi ba muma aikin da
zai amfane mu muke nema,Ibrahim yace a tunaninku zaku samu aiki a haka? Sohail yace
zauna ka sa wasa sai na zana muku Zero wallahi,Sifili ba saina zana muku shi ya
furta tare da jan hannun Sahil suka haura sama,Suna shiga daki Sahil yace ya aikin?

Alhmdllh suka zauna a bakin gado ya bashi labarin aikin,Sahil ya dinga murna
yace har mota za a baka da gida? Sohail yace me tsada ma ina fada maka amma muyi
shuru kar mu fada su, Maheera kawai zamu fadawa ko Daddy bazai ji ba sai dai a
ganmu da abinmu,Sahil yace mun faso gari muma,ai kana aikin nan ina ta
kallonka,Sohail yayi dariya domin yawanci ana nuna musu aljanun,shege ai na ganka
har Oga sai da ya baka kujerarsa ka hau kayi masa aiki,tafawa suka yi kamar
abokai,yace bari nayi wanka nazo,kaga takardun da zan cike,duba ka karanta ka cike
min,Sahil ma kallo daya kamar Aljani ya dauki biro duk yayi sai kace yasan kan
aikin kuma daidai yayi shima.

Islaha ce ta shiga bedroom ta samu Maheera tana bacci tace ki tashi sweetynki
ya dawo daga Office,ido ta bude kadan tace bana son iskanci waye Sweetyna yayi ta
dawowa mana,abinci ne ai yasan inda yake ko kije ki kai masa,baya ta juya tare da
komawa baccinta.

Sahil yana fitowa yaga Amal tazo gidan itama yau ta kawowa yan uwanta ziyara,ta
sha Shadda fara,Zayna ya shiga kira Yaya ta palo.....Yaya ta Palo....Zayna...ki
fito kinyi bakuwa kanwar miji tazo azo a nemi shiga,kin san dangin miji masifa ne
dole sai ana yin shishigi da neman taskirar zama wai bazai ce gindin zama ba.

Amal tana wani kallon up and down tana tabe baki tace wace kuma Yaya ta palo?
Sahil yace Zayna ce, to mece idan ba Yaya ta palo ba matar da mate dinmu ce,sa'ar
mu ce fa duk mace akace shekarun mu daya da ita ai ta zama Yaya ta palo kuma.

Amal tace lallai Ibrahim kun bari yaran nan suna shanawa shi yasa suka raina
kowa,wallahi da ina nan azabar da zasu sha sai sun kwammace ba a haifo su ba yan
iska mahaukata marasa kwakwalwa,ba ilimi ba komai sai jahilci da hauka.

Sahil yace hmmm ke nan tunani kike kinfi kowa ko sabo da kin auri me suffar
kwadi,Aunty Amal wai ina kike saka timbin me gidanki ne? Sabo da kudinsa ke tumbin
nasa ma bakya gani,Ibrahim dariya ta kusa kulle masa ciki kawai dannewa yake,Sabo
da Sahil bai fiye magana ba amma duk randa yaga dama to fa za aji tone tone.

Sahil yace wallahi Aunty Amal hakuri kike yi kawai sabo da kudi,ai kuwa ba wani
sonki yake ba wlh uwar gidansa itace komai dinsa ki daina hura hanci,rannan ma haka
yace duk duniya ba kamarta ita yake so,sannan baki sani ba wallahi bana ya biya
mata Umrah ita da yaranta kaf ke kuma yace miki kiyi hakuri wannan shekarar bashi
da kudi,to uwar gida next week zasu tafi,daga nan yace su wuce dubai zasu siyo
kayan sawa ita da yaranta.
Ai dan baki sani bane idan uwar gida tana da hankali tana da biyayya duk wata
Amarya ko balarabiya ce ko dangin uwar mu ce baturiya bata isa ta kwace fada a
wajen uwargida ba,ya aure ki kawai sabo da ya samu sabon jini kullum ki bashi
taskira uwar gida kuma ita ce da shi.
Ki daina jiji da kai Aunty Amal bakya gabansa kuma yanzu so kike ki haihu baki
samu ciki ba sabo da gado kin damu sai kin haihu to ciki ne dake ammaAllah ne yasan
abinda zaki haifa,idan baki yarda ba kije ayi miki test, dama ke mayyar sex ce da
zaki taho ma sai dai me tunbi yazo kuka yi na ban kwana,yace babu kamarki a ransa,
kika taho kina murna karya yake wlh.

Amal gwiwar ta ce tayi sanyi jin abinda Sahil ya fada tasan basa karya,tace amma
wlh idan na koma sai anyi tashin hankali,yanzu Alhaji Rabiu haka zai min,Sahil yace
katon kwado kina ce masa Baby, Kuma dan yayi miki ke din ba har wajen malami
kawarki ta rakaki ba wai zaki mallake shi,Islaha tace kinga Zayna muje ciki wannan
yaron munafuki ne,Aljanunsa kaf munafukai ne,Ibrahim yana ta dariya abinsa yasan
halin su Sohail shi yasa yayi shuru kar su tona masa asiri.

Sohail ne ya fito yana duba Maheera bata nan ya duba kitchen Islaha ce kadai
ciki tana girki yace girki kike? Tace yanzu na fara Aunty Zayna ce tace farfesu
zamu yi musu da white rice and stew wai Aunty Amal tazo sannan wai na dafa mata kan
rago ka ganshi an kawo yanzu fresh da shi,Sohail yace yau babu wanda zaici abinci a
gidan nan sai dai su fita waje suci mu kadai ne zamu ci mu koshi ni,ke,Sahil da
Maheera, suna kallo zamuyi party sai dai su bar gidan nan suci abinci a waje,nidai
zan dafa musu ko dan aikin Maheera kar ya kubuce,Sohail yace bazai dafu ba abincin
yau ko me za a dafa indai a gidan nan ne bazai dafu ba,Islaha bata yarda ba yana
fita ta fara girki,ruwan ma yaki tafasa bare a zuba shinkafa wuta ci take ci take a
gas amma idan aka taba ruwan sanyi karara,Islaha ta dinga dariya ita kadai a
kitchen,komai ta dora bazai yi ba sai dai a taba aji sanyi,har ta kwashe awanni ta
gaji ta maida komai fridge ta fito.

Tana fitowa taga Sahil da Sohail sun shugo da ledoji niki niki,Sahil yace kowa
yaje yayi wanka yau akwai party, suka shiga wanka,Maheera ta hade cikin wani
material dinta na sallah me kyau,Islaha ta sa riga da skert yan kanti sunyi mata
kyau kamar ba gobe,Sohail kuwa da Sahil kana nan kaya suka sha masu kyau wando jean
fari riga ruwan toka me rubutu blue a gaba,palo suka fito kawai suka samu
Ibrahim,Amal,Adnan da Zayna a dining suna jiran abinci daga wajen su Islaha.

Ido suka bude ganin Su Sohail da su Islaha duk sun sha wanka sun fito da abinci
a leda sun dora a center table,Sahil ya bude ya fito da su hot
pizza,shawarma,burger, kaza ta sha gashi katuwa a bankare gashin amarya,ga kuma
wata kalar shinkafa ta larabawa da katon kifi yaji hadi,ga hadin salat a gefe da
lemon tsami,ga ruwa ga lemuka da fruits salat abin ba sauki.

Suka baje komai a center table,Amal har tana dariya irin taga mahaukata ta
dakawa Islaha tsawa ke yarinyar nan dalla kawo mana abincin mu,Islaha tace yarinya
tana bayan uwarta,Adnan a fusace suka yo kan Islaha,Ibrahim yace dan Allah ku
kyaleta su Sohail ne suke zuga su,ai su Sohail zaku ci uba da waccen bakar
munafukar Maheera sune suke zigata,ai ita yarinya ce me hankali.

Adnan yace ko sonta kake yi ne? In kana sonta kayi magana ta karfi kudi zai
siyar maka ita ai,Amal tace ko dan su Sohail ma sai na so ya aureta naga ta
tsiya,bari mu kyaleta zasu ga tsiya kudi zaiyi aiki ai talakawa ne iyayenta zasu ji
yaren kudi.

Amal ta sake cewa kawo mana abinci,Su dai sunga suna kuskus basu san me suke cewa
ba,suma su Sohail aljanun basu fada musu ba,Islaha tace yanzu kika yi magana da
kika bini a sannu,to abinci wlh yaki dafuwa na dade ina abu daya ko me na dora ko
zafi bayayi bare ya tafasa,Sohail yace kuma nine nace yau mu kadaine zamu ci abinci
a gidan nan ba abinda zai dafu.

Zayna tace na yarda wlh ni na gani rannan,Amal ta mike ta shiga kitchen din da
kanta ta dora tukunya ta dade a haka ruwan sanyi ta sauke ta fito ta zubawa Sohail
rankwashi tace dan iska marar mutunci,kunyi asarar halinku,shuru suka mata tace
kuzo muje eatery muci,suka mike,Maheera ta kunna kida ta ware uban volume wai party
zasu yi Sohail ya samu aiki.
Sahil yace wata ta zauna cinyata safe waje ne.

Kida na tashi suna ta ciye ciyensu abin dariya ko wacce makale kusa da
daya,hauka tana motsawa Sohail yace ayi musayar kawa,Maheera ta koma kusa da
Sahil,Islaha ta koma gefen Sohail,Sohail kuma sai kishi,yaga Maheera sai kallon
Sahil take tana murmushi me kayatarwa kuma tana sani tayi tunda shi yace ayi
musaya.
Sohail idonsa na kanta ya saki baki yana kallonta haushi ya kama shi yace a
ransa ai kuwa sai na baki haushi yau,ya ballo kaza yace da Islaha ungo kici,Islaha
ta bude baki ta yagi nama tana taunawa ta kwabe fuska kamar zata yi kuka wai duk
cikin dadi ne,tace Aunty babar Khalisat ina nan dadi zai kashe ni ta furta da sigar
kuka ka rantse kuka take sharba harda yarfe hannu.

Maheera wani bakin kishi ya kulleta a rai,Islaha tana ta mata inkiya da nuni ta
fahimta ba da gaske bane amma haushin Sohail ya kashe Maheera tace a ranta ai hauka
ma tana iske hali,halinsa ne wlh sai na rama ta dakko Shawarma itama ta fara bawa
Sahil a baki yana ci,Sohail ya kame ya zama gunki da lemo a hannunsa,ransa ya
baci,Islaha ta mika masa a baki shima yana ta ci amma wuri daya ya tsurawa ido yana
bacin rai,duk da yana kokarin dannewa sabo da Sahil ne.
Sahil kuma yana ta nunawa Islaha ta daina taki ji,Har ya gaji ya kura mata ido
yana cewa uhm uhm...uhm...uhm wai ta daina ga kida kamar zai fasa gida suna ta
dumurmusar abinci suna cusawa juna haushi kowa yana ta ramuwar gayya ba ga mazan ba
ga matan sun biye su,ana party amma kowa haushin kowa yake ji anyi musayar mata.

Free page
400 ne

0175487861
Asmau Garba Muhammad
Gtbank

'Yan Niger
+22790795939

AsmaBaffa
08061929616
[7/17, 3:17 PM] Asmabaffa: 🪸MUMMUNAR DABI'A 🪸

26-30

Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA NE GA 'YATA TASNIM.

Page naki ne
Umu Afrah

Follow this link to join my WhatsApp group:


https://chat.whatsapp.com/HYpizDjKAkJB4QClSeLTvw
Sai dare Maheera ta mike tace zanje na kwanta bacci nake ji gobe gidanmu
zanje ganin gida har yanzu ban samu naje ba,Sohail yace Allah ya kaimu,Islaha ta
mike suka wuce ciki,bayan sun shige bangaren su Sahil ya kalli Sohail yace ya
kamata Islaha fa ta koma wajen danginta ko yaya suke bai kamata kawai ta bar can ta
yo nan ba,mata fa idan aka biye musu basu da hankali,dole sai ana sara ana duba
bakin gatari,bai kamata tazo nan ta zauna ba kaga su Yaya su ba kaunar mu suke
ba,Daddy kuma ba damuwa yayi damu ba bare yasan me muke yi,gwara Maheera tana da
hujjar zama aiki suka dauke ta,Islaha kuwa sam ma Zayna bata bata wani aikin yi
bare su biya ta, su fa ba damuwar su bace koma me zamu yi muyi kawai a duniya,uwar
mu Mahaifiya har yau bata neme mu ba ma shima Daddy ko zancenta baya yi mana, indai
da hali kawai ta tafi indai dan ni tazo ba ruwana ni dai.

Sohail yace hakane kuma amma yanzu ya za ayi da ita? bari na kira su kawai ayi
a gaban kowa,kamar masu hankali yau haka suka yi magana.
Sohail ne ya mike ya musu knocking a kofar su Maheera.

Budewa tayi yace dan Allah ku dan zo zamu yi magana,Fitowa suka yi palo tare da
zama.
Sahil yace abinda yasa na kiraku,Islaha akanki ne,duk duniya dan Adam baya rasa
dangi ko ya suke,Islaha tace ae,yace yawwa ku mata watarana tunaninku gajere ne,
Maheera ke aiki kike yi kina da dalilin zuwa nan,Islaha nayi tunanin za a bata
aikin ma hakan bai samu ba sai dai amma tana tayaki na gida tunda ita basu biya ta
ko sisi ba.

Magana ta gaskiya ni ba korarki zanyi ba Islaha nasan kina da dangi ko da baki


da iyaye Wacce ta rike ki ta kore ki bai kamata ki taho wajena ba,kamata yayi ki
koma Taraba wajen danginki,ni bana so ace zamana kike yi ni ba iskancin nan nake
ba,gwara ma da yi nake sai a zargeni da hujja,ya kamata ki koma danginki shine
darajarki, nima kinga babu me zargina,idan Daddy yazo su Yaya zasu iya hada mana
sharri,ki koma danginki ba korarki nayi ba kawai ji nayi ba tsari haka sam,ba wani
dan uwa da zaiji kina nan yaji dadi indai suna kaunar ki.

Sohail yace wannan haka yake maganarsa gaskiya ce tare muka yi shawara,nima na ziga
shi mun tantance gaskiya.

Islaha murmushi tayi tace ba komai na fahimce ku,karku damu ina da dangi kuma
Inshaallah zan tafi,Sahil ya kalleta yace sai naji tausayinki kuma Allah
sarki,shuru tayi tace shike nan? suka ce ae tace to baku da damuwa indai nice.
Sahil ya kalli Islaha da tausayawa yace tausayi nidai.
Maheera ce tayi magana tace gaskiya bai kamata ba ina laifin ku bari mu kaita
gidansu da kanmu,Islaha tace sai kace yarinya kema dai Maheera karku damu dan
Allah.

Su Sohail kamar ba su suka yi maganar ba kawai sun ma ci gaba da uzuri suna


duba waya suna dariya,Maheera ta mike suka wuce bedroom,Islaha tana shiga ta fara
hada kayanta,Maheera tace ke yanzu maganar Twins zaki biyewa shirmen su ne fa.

Islaha tace abinda suka fada gaskiya ne Maheera,Sahil yana tubanin ni Karuwa ce
wanda ba haka bane,nasan ranar da yake zargin ya ganni shine ranar da Aunty ta bani
kaya na rashin mutunci tace sai na saka nabi Khalisat hotel ko ta koreni daga
gidanta,babu yanda zanyi haka na shirya na bita,kuma ba abinda na aikata maganin
bacci na saka masa a lemo ya sha da safe na fito na koma gida,nidai na tabbata a
nan Sahil ya ganni, Abinda ya faru kenan ko Sahil ya ganni bazai wuce wannan ranar
ba,kuma banga laifinsa ba domin duk wanda ya ganni a lokacin zai yarda ni karuwa ce
sabo da shigar da take jikina.

Maheera tace to kuma sai kice zaki tafi haba Islaha,Islaha tace a daren nan kuwa
zaki ga na tafi,Jakarta ta dauka Maheera ta riketa tace haba Islaha mene haka da
daren nan zaki tafi.

Fisge jikinta Islaha tayi ta fice,Maheera ta biyota amma Islaha ta arce ma da


gudu,ba kowa a palo ko compound haka ta fice abinta.
Ranar Maheera ko baccin kirki bata yi ba sabo da tafiyar Islaha.

Washe gari da safe ta fito tayi aikinta tana shirya dining Sahil ya fito,Maheera
ta kalle shi tace Islaha ta tafi tun jiya da dare,dammm ya danyi a tsaye,yace ta
tafi? tace ae a daren ta tafi,Sahil shuru yayi zama yayi a hankali a saman kujera.
Hankalinsa ya gama tashi gashi aljanun nasu yawanci abin da ba a damu da shi ba
shi suke fada musu.

Tagumi ya zuba Maheera tayi tafiyarta tare da ci gaba da aikinta,Sohail ne ya


fito zai tafi wajen aiki ya samu Sahil yayi tagumi,tambayarsa yayi yace me ya faru?
Maheera fitowa tayi da plate dauke a hannunta ta furta Islaha ta tafi tun jiya da
dare,kuma yanzu ba a sani ba gida ta tafi ko ba gidan ta tafi ba,a wanne halin take
oho,tunda ba san can garin nasu mene ya hanata zuwa ba.
Sohail yayi shuru shima yace gaskiya ne bamu kyauta ba sai yanzu na ga illar hakan
mun gode da tunatarwa Maheera.

Sahil ya mike tare da zama ya zuba tagumi yace sabo da zuciya shine ta tafi cikin
dare idan aka sace ta fa,Sohail ya furta har na fara tunanin kudin fansar Islaha da
zamu kai gashi ban fara aikin ba ina zamu samu kudin?
Sahil ya furta ai da Maheera kin fada min sanda ta tafi a daren zan bita da bulala
me kyau zan rako har ta gida,Sohail ya furta
lallai bamu kyauta ba na wuce Office.

Maheera takaici ya kamata tace wlh badan aikin nan nawa ba sai nayi tafiya ta nima
wannan ai ba daidai bane, na gaji da halinku
Sohail ya kusa kofa ya juyo sosai ya kalleta yace Allah ya baki hakuri,juyawa tayi
ranta a bace.

Sahil baice komai ba har Sohail ya fita yana tunani,Amal ta fito da shirin
komawa gidan mijinta dauke da akwatinta Adnan ya fito zai rakasu airport" tare da
Ibrahim zasu tafi suka samu Sahil yayi tagumi ya zurawa waje daya ido baya ko
motsi.

Kallonsa suka yi kawai suka tabe baki tare da wucewa abinsu.


Sai da ya gaji a haka sannan ya kwanta a saman kujera ya zubawa sama ido ba ci ba
sha,har lokacin sallar azahar yayi bai san yayi ba,shi kadai a gida Maheera har ta
shirya ta sanar da Zayna ta fito da kayanta tayi tafiyarta ko kulashi bata yi ba.

Da kyar ya mike ya dauro Alwala tare da gabatar da Sallah ya roki Allah ya


bayyana Islaha sai da ya gama adduar ya koma saman kujera ya kwanta, a haka Sohail
ya dawo ya iske shi,yayi sallamar duniya shuru shuru,sai da ya shugo yaga inda ya
bar Sahil a nan ya same shi kuma ba bacci yake ba,Yana tsotsar Alawa me tsinke

Yace lafiya? gaba daya abinda muka yi bai dace ba,yanzu wa yasan inda take,ko an
sace ta ma jiya da da dare wa sani,Sohail yace kasa ina tsoron kudin fansa Sahil

Sahil yace yau ko ruwa ban sha ba bare na iya cin wani abu,wannan abin ya tsaya
min ba wai ni wai sonta nake ba ka gane,ni da bakina da nace ta tafi shine ya
dameni,Sohail tashi yayi yace kuma gaskiya bamu kyauta ba gashi yanzu Maheera fushi
take yi itama.
Kitchen ya shiga ya ebowa Sahil snacks da lemo ya kawo masa yace muci wannan
Maheera fushi take yi bata ajiye mana abinci ba yau ina zan sa kaina.

Sahil kadan yaci ya koma ya kwanta ya dora da tunaninsa,gani yayi kwanciya baza
ta kaishi ba ya mike tare da cewa bari naje na nemo ta a gari, ya fita kofar gida
bakin gate ya tsaya yana kallon hanya a haka neman Islaha ya fita iya bakin
gate,sai da aka yi kiran sallar Magrib sannan ya koma gida.

Islaha kuwa a tasha ta kusa kwana da asuba suna yin sallah ta shiga motar
Taraba garinsu suka tafi tana motar tana ta tunani wai Sahil ya iya cewa ta
tafi,Farcenta tasa a baki tana ci tana tunanin kawai a haka har suka isa Taraba.

Sauka tayi ta shiga motar kauyen su me suna Sharbe inda ba abinda ake kiwo sai
dabbobi iri iri,kauyen ma kafin aje aiki ne,Allah yasa Aunty tana aikenta tana
kaiwa dangi sakon kudi da kayan abinci,duk iskancin Aunty akwai taimakon dangi,duk
yanda dan adam ya kai ga lalacewa baya rasa halin kwarai.
Wani sakarkarin gida Islaha ta sauka wanda duk garin daga ginin kasa sai Gidan
kara da bukkoki irin na fulani,babu wani ginin bulon siminti ko guda daya a garin.

Islaha ta saba da birni bata kaunar ma ace ta dawo garin da zama kuma ko waye
haka zaiji,ace ka taso a birni ka dawo irin wannan kauyen,gashi yan uwan nasu kawai
su dai a basu kudi,wanda ya basu shine mutum,basa iya rike dan wani dangin su
Islaha yawanci haka suke.

Gidan wata wacce suke kira da Lalai kanwar kakar su Islaha ce itace ta rage
tana da rai a cikin dattijai dangi sauran duk da kwarinsu kuma ta fisu dama
dama,duk ciki babu wanda zai iya rike Islaha.

Lalai ita kanta ta zaci Aunty ce ta aiko Islaha ta kawo musu kayan abinci da
kudi,tana ganin Islaha hannu bibiyu ta tarbe ta tana murna tace marhabin ja'ira yau
ma kinzo,Islaha ta shiga dan karamin dakin Lalai wanda sai gadonta karami sai
kayanta irin na tsofaffi,gida kuma gidan kara ne gaba dayansa, Lalai ce kawai a
cikinsa.

Bayan sun zauna ta kawowa Islaha tuwon masara da miyar kuka amma fa miyar da
nama a ciki,Islaha taci ta koshi tayi wanka tayi sallah sannan ta zauna tana
hutawa.

Lalai tana ta jira taji ance ga sako daga Aunty amma shuru,Lalai ta gaza hakuri
Islaha tana mata hira tace Auntyn taku ce ta aiko ki? Islaha tace a'a Lalai,ta kore
ni daga gidanta tace baza ta iya ba na tafi,ina zanje bani da kowa sai ku dole nan
zan dawo ku rike ni.

Kirji Lalai ta dafe tace sabo da Allah a dora min nauyi ina tsohuwa ta,nima fa
Abdulrazaqu shine yake ci dani,ba kudi ne dani ba,Allah ya gani fama nake da
kaina,ga dangi nan da yawa su Gali,su shamsu duk su Allah ya hore musu suna da shi
'yan uwan uwarki ne na kusa ba na nesa ba ai sai kije can yafi.

Islaha tace kema fa kin san su Baffa Gali Lalai baza su min ba kuma ma ko sun
yarda ai matansu basu da mutunci,sannan da dangin uwata dana ubana duk daya suke
yan uwane gaba daya auren zumunci kuka hada,ke yanzu Lalai ba me rike ni bace? Kun
fi so na shiga duniya,wallahi dole ku rike ni tunda nazo a yar uwarku ya zaku yi
dani ba inda zanje.

Lalai tace inda rayuwa ta canja sabo da Allah gishiri ma yanzu ya zama masifa
ni azo a zauna min nima fa yar Allah bani muci ce,Islaha tace nima itace ke dama ai
bakya son mutane bakya so wani ya rabeki bare ya amfana dake.
Zan shiga duniya ne ya zanyi,Lalai tana ji tace to gaskiya bazan lamunci
gandandan dake ba ki zauna irin yanda kuke yi a birni,da miji ya fito ki fitar kiyi
aure a kaiki dakin mijinki ko da katifa ne,ga samari nan da yawa a dangi duk kaunar
ki suke yi idan sunzo ki zabi daya,ba hauka ake ba da zaki zauna a gabana kin fini
girma nono duk sun cika miki kirji bazan iya ba,kullum ina bude ido ina ganinki a
haka bazan iya ba,wannan maguzancin bada ni ba baza kizo ki jawo min hawan jini ba.
Islaha tace naji zanyi kokari na fitar dan Allah ki kyaleni na huta da kudi na
kawo miki ko kayan abinci ai da yanzu kin rasa inda zaki sa kanki dani sabo da
murna.
Lalai ta furta nidai na fada miki ki fidda miji.

Islaha zata hau gadon Lalai ta kwanta kamar yanda ta saba idan Aunty ta aiko ta
Lalai tace karki hau min gado ko ni ba kwana nake a kai ba sosai, kiyi shimfida ga
tabarmar kaba can,Islaha bata ce komai ba ta dauki tabarmar ta shimfida tana cewa
indai aka ce iyayenka sun rasu a wannan zamani ka shiga uku babu me iya rikeka sai
daidai ku,haka ta sa rigar bacci ta kwanta.

Sahil sai dare ya tuna da waya ana kiran mutum a ciki,cikin dare ya dinga kiran
Islaha ko dagawa bata yi ba,da ta gaji ma kashe wayar tayi gaba daya,Sahil kwana
yayi yana gwada kira sai bacci barawo da asuba ya dauke shi.
Gaba daya gidan baya musu dadi sam Sahil ya rasa sukuni hakan sai ya damu Sohail
shima ga Maheera tana jin haushin su duk Sohail ya damu kansa,tunda ta tafi ganin
gida bata kira shi ba.

Wayar Sohail ce tayi kara ya duba,yana dubawa yaga Email ne aka turo
sako,dubawa yayi sai ya ga an dauke shi aiki a kamfani personal assistant na
matemakin manager aka bashi,ga Alert na kudi,sannan gobe yaje ya karbi motarsa da
takardun gidansa
Sahil yana daki yanda yanzu yake zama baya so ma a kulashi,Sohail ne ya nuna
masa,murna ya tayashi sosai,Ya fito ya turawa Maheera text ya sanar mata,tayi
murmushi tace mashaallah.

Message ta turo masa congratulations! sai ka dage nan gaba ka zama manager din
da kansa.
Karantawa yayi ya tura mata yaushe zaki dawo?
Reply ta masa da Jibi Inshaallah,ya furta Allah ya kaimu da baki kawai ya maida
wayarsa Aljihu shi a dole ya bata amsa yace Allah ya kaimu,shuru taga ba reply nasa
ta zubawa wayar Ido tana jira,shi kuwa ya riga ya fada da baki.

Maman su Maheera wacce take katuwa da ita me kiba kyakyawa ta kalli Maheera tayi
murmushi tace Maheera wannan Sohail din da kike min zancensa ko da shi za ayi ne?
Murmushi tayi,Mama tace wlh naji dadi da kika canja hali Maheera amma da kullum
baki da aiki sai tsokana sai fada,Maheera tace hmm yanzu ai wannan aikin da nake
samu ina yi kinga Mama dole nayi ladabin dole kar a samu matsala a kore ni,daga
haka ban san sanda na canja hali ba gaba daya,yanzu ko kudi kika bani bazan yi
abinda nayi da ba,nayi hankali, a baya ma ai da kuruciya.

Juwairiyya tace lallai Aunty Maheera Allah dai yasa kin daina kar kije ki samu
miji kice zaki yi masa wannan mulkin kama karyar kice dole ke sai an miki yanda
kike so,sai kin samu yanda kike so nasan hali,Ammar yace wlh kamar kin sani nima
abinda nake so nace kenan,dariya suka yi Maheera ta mike ta bar dan karamin palon
nasu dake gidan nasu gaba daya 2 bedrooms ne sai palo sai kitchen da toilet,daya
bedroom din na Ammar daya Juwairiyya, Mama da Maheera,gidan daidai talaka.

Adnan ne ya kwalawa Sahil kira,Sahil ya fito yana tafiya da kyar kasancewar


baya cin abinci sosai sabo da tafiyar Islaha,yana kallo Amal ta tafi gidan mijinta
ko magana,Zayna ko me zasu yi kanzil baya cewa.
Adnan yace ka wanke min motar? har ya gama maganar Sahil bai jin ma me yace ya
tafi tunani,Hello....Adnan ya furta sannan a hankali ya dago kansa ya kalle
shi,yace munce mun daina aiki muma aikin yi muke nema ku dauki ma'aikatan ku ya
juya baya abinsa yana cewa ina cikin tunanina kawai ka dameni.

Adnan cike da masifa yace kaje ka wanke min mota tun wuri na fada maka,ko
kulashi Sahil baiyi ba ya koma ya kwanta abinsa.
Ran Adnan ya baci sosai yau Daddy ya kira a waya ya daga bayan sun gaisa Adnan yace
Daddy karar Twins na kawo maka yanzu kwata kwata sun raina mu baka isa kace suyi
ba,babu abinda suke yi sai rashin mutunci,aikensu idan kayi zasu ce baza suyi ba
direct,Daddy murmushi yayi yace to baka ganin ba kalau suke ba,Aljanun ne suka
canja su,ai Daddy ba komai Aljanu zasu sasu suyi ba naga dai Aljanun sai lokaci
lokaci suke zuwa kansu watarana ma sai ka rantse kalau suke,ko yanzu yanda suka
koma kenan da lafiyar su.

Daddy yace aiki yayi min yawa Adnan na kusa zuwa garin akwai wani meeting da
zamu yi da me gidana zanga me suke yi,Adnan yace shike nan,Na bawa Ibrahim kyautar
gida shima ya kamata yayi aure,Adnan yaji dadi,cikin Daddy ya buga yace twins fa?
Daddy yace su nake tunani gaskiya babu wata mace da zata so twins a haka bare ma
suyi aure,ai baza su iya rike aure ba sabo da rashin lafiyar su,Adnan yaji dadi
yace gaskiya dai,sai da suka gama hirar kamfani suka kashe wayar.

Sohail yau an bashi sabuwar Motarsa da takardun gidansa sannan ga Alert na kudi
masu nauyi,Murna tasa yau da wuri ya shiga motar ya dawo gida,Adnan yana shirin
fita yaga mota baka kirar Marcedes baka me kyau sabuwa ta shugo gidan anyi parking.
Sohail ne ya fito daga ciki da takardunsa a hannu,Adnan ya saki baki yana kallonsa
ina ya samo mota ne,yanda bai kulashi ba shima Sohail bai masa magana ba ya wuce ta
gabansa ya shige ciki.

Sahil ya samu yana kallo a palo,yace wai Sahil baza kayi hakuri ba akan yarinya
ta tafi fa, please kaci gaba da rayuwarka,kaga Allah ban zanci zan iya komai a
duniya ba duba da yanda a makaranta gaba daya bani da kokari ba abinda na sani sai
dai a jarabawa,amma yanzu kuma komai sai naga kamar ba yi nake yi ba da kaina kamar
yi min akeyi,ta ya zan san wannan uban turancin Sohail,amma sai naga na karanta sai
naga na iya computer,amma a school bamu iya komai ba muyi ta jin kunya,ni dai
mamaki nake yi da nake iya aikin nan sai mu kasa abu watarana kuma mu iya
shi,turanci fa ka duba watarana sai muji munyi watarana sai mu kasa ko sentence
daya.

Sahil yace rayuwa ce kawai ni ta Islaha nake yi,na gaji kada Allah yasa ta dawo
tayi ta tafiya na gaji da halin yarinyar nan,bata da kunya dama badan haka ba daga
yar magana sai ta tafi cikin dare ita ga me zuciya,tana dagula min lisaafi.

Sohail ya nuna masa key din mota da takardun gida ya nuna masa Alert yace to
wahala ta kare gobe zan fara aiki.
Sahil wannan murnar tasa ya share zancen Islaha sunyi kudi yanzu.

Sohai ya furta Yanzu Oga yace Business na kayan da suke shigowa da shi za a koya
min sosai nafi dacewa da wajen sabo da ko wanda bai boko ba zai iya wannan bangaren
na shige da ficen kaya ta kamfanin yace shine daidai ni,tunda na fada masa watarana
zata iya kwabewa na kasa karanta komai ko computer din ma ta gagareni,shine yace to
wannan bangaren shine daidai ni ko ba boko zan iya.

Bari a nunawa Maheera Sahil yace kai baka da hankali ka nuna mata gida da mota
amma kudi ba a nunawa mace samu baka ji maza suna fada ba,Sohail yace ahhh gaskiya
a nuna mata na farko shike nan ai,ita ta iya bata yi kyashi ba ta samo aikin sai
mune zamu ce baza mu nuna mata ba"
kai nuna mata karka ishe ni,ko ni yanzu baka so na irin Maheera,komai ita komai ita
cewar Sahil.
Dariya Sohail yayi yace nima na rasa dalili ba a son raina ba ban san ina yi
ba,abin yana damuna ka tayani da addua,Sahil ya furta Allah ya yaye maka to.

Sohail Maheera ya samu a kitchen lokacin ta dawo daga gida tana girki a
hankali ya tsaya a bayanta,kamshinsa ta ji ta juyo da sauri,dariya yayi yace kin
fiye tsoro,matsawa tayi daga yanda suke tsaye gaf da juna,Maheera ta kalle shi tace
any Good news naga kana wani murna kai kadai,wayarsa Samsung ya mika mata yace
gashi ki kalla,Maheera ta duba ta gani ta rufe baki da tafin hannu tana murna,Key
din mota ya karkada mata a saitin fuska,ta karba ta gani tace wow,sai takardun
gida, Alhmdllh gaskiya na muku murna sosai Allah sanya Alkhairi.

Yace to aikinki ya kare kuma ki shirya ki koma gida,Maheera tace a'a ni ka


kyale min aikina gwara na dogara da kaina,au ke bada Allah kika dogara bama da
kanki kika dogara? Karki shirka dai.
dariya tayi tace wai kudin nake nufi, badai albashi ne ba ni zan dinga biyanki
abinda suke baki,maganin Mama da sauran matsala ta kannenki duk zan dinga yi.

Maheera tace idan ka daina yi fa? ku maza wani dorar da alkawari kuke yi wannan
ba yuwuwa zaiyi ba, haushi Sohail yaji yace kice kawai karya nake yafi miki,wanne
irin abu ne haka ana fada miki bakya ji,kinfi so ki zauna kiyi ta girki,Maheera
tace gida kake so na koma? Na barku kuci gaba da wani abin ba daidai ba nasan me
zaku aikata gaba.

Da ke kika raine mu ba haka kika tsince mu ba Allah ne yake tafiyar da


komai,Kice dole sai kin samu a hanya,ke zaki shiryar damu? badan muna ganin
mutuncinki ba 'yar tatsitsiya dake har ke zaki ce kato kamata nayi abu nayi,Kalle
ki fa kalle ni baki wuce na goyaki na zagaye Abuja da ke ba gaba daya ko hutawa
bazanyi ba.

Maheera dariya take tace Sohail ni kwana biyu naga kamar hankali kuke yi sai
kuyi ta magana ta normal mutane,kallonta yayi kawai tare da shafa gemunsa yace
girma ne yazo kalli fa gemuna ya furta yana shafa gemunsa.
Sahil ne ya shigo ya kalli farfesun da Maheera tayi yace mota ta dawo min da
hankali na yanzu yunwa nake ji,nama daya ya dauka ya cinye ya karbi key din motar
yaje ya shiga ya tafi dani shima wanda da akwai karambani Sun iya mama Asmau ke
hanasu hawa sabo da matsalar kwakwalwarsu.

Maheera suna ta hira da Sohail basu saba rike kudi ba sabo da ba a basu kudi
sam,yace yanzu ya za ayi da kudin nan ne? Sun isheni a accnt dina ni na rasa abin
siya,Maheera tace ance maka kashewa zaka yi lokaci guda? Matsalar data dame ku
zakuyi,Sohail ya lula tunani yace matsala mu bamu da wata matsala muna ci muna
koshi muna da sutura to mene za muyi?

Kuje kuyi tunani mana matsalar taku,Sohail yace yawwa kika ce muna bukatar aiki
mu samu kudi muyi aure mu haifi yara ko? Maheera tace ae mana to ai a fara ta
kansa,dariya tayi tace kuma daga samun kudin sai auren kana da budurwar ne?

Sohail yace ba gaki ba,ka taba ce min you love me ne da zaka kace nice....to I
love you Sohail ya furta da sauri kafin ta rufe baki,Sahil dinfa ko kaine zaka yi
auren ka rigashi sabo da kai kayi kudi? to ba Allah ne yace ayi ba tunda bashi da
budurwa a kasa ba shike nan ba,a'a a daura dai auren tare ku aure ni ku biyu kawai
ai kunce na ishe ku ko?
Kaga sai a raba muku kwana yau kai kazo mu kwana tare gobe Sahil yazo,Sohail yace
ai kuwa da an rataye Sahil anyi hanging dinsa kawai an huta, yarinya na sani to
namiji daya shi yake auren mata hudu mace namiji daya tal take aura.

To yanzu mata hudun zaka yi kenan? Sohail yace to a Office tv dina naji wa'azin
Allah ne yace malam yace a taimaki mata sunyi yawa a gari idan da hali mutum yayi
ta karawa har su kai hudu,kinga kece uwargida zan miki wannan alfarmar na aureki a
farko daga baya sai a karo miki ta biyu a haka har na cike hudu na,Yan mata hudu
rigis ni kadai gaskiya mun muku wayo mu.

Maheera tace wanne malami ne yayi wannan wa'azin? ban sanshi ba channel din a
tv din Office dina take,Maheera a ranta tace dole na kira Alhaji Saminu a tsinke
wannan Channel,ina so ya dinga jin wa'azi amma banda na kishiya,inda baida kai ai
sai yace sai yayi, sai ya aure su.

Maheera tace Sohail ba haka malamin yake nufi ba,nufinsa idan mutum zai iya
adalci kuma yana da kudi sosai,Sai zai iya adalci aka ce idan bazai iya ba yayi
zamansa da guda dayarsa,Sohail yace aya da hadisi ya kawo to Hajiya.

Maheera tace uhmm ai shike nan yace ae ga kuma Hurul ayni yace na lahira suna
can a lahira suna jirana gaskiya mun gama da ku mata kuyi hakuri 10-0 kawai.
Dariya ya bawa Maheera tace ashe kai mayen mata ne ban sani ba,daga kaga ka fara
kudi shine ka fara zancen mata,Adnan shi da matarsa daya ta ishe shi abinsa gwanin
sha'awa kai da mamanku take baturiya baka gaji halin turawa ba mace daya danginku
suke yi,Sohail yace ni nasan wata mama ne ina ruwana da su.

Yaushe zaki tafi gidanku? Maheera tace ina nan bazan tafi ba,aikina
zanyi,Sohail yace shike nan ki ta zama tunda ke bakya son ci gaba,tace ae naji
mutumin da zaiyi mata hudu waye zai dogara da shi jeka can da matanka bada Maheera
ba.

Maman su Maheera aka kwantar a asibiti ciwonta ya tashi,kannen Maheera ne suka


kaita asibiti sai da suka kwana kudinsu ya kare sannan suka kira Maheera,tare da
sanar mata.
Sohail kuma ya rigata sanin ma an kai Mama asibiti yau aljanun sun waiwayo,Zuwa
yayi har asibitin ya dubata su Juwairiyya basu sanshi ba sai kallonsa suke yi,ya
tambayi kudin nawa zasu biya? Suka ce dubu dari biyu da hamsim mun biya dubu
hamsim,dubu hamsim dinsu ya basu yaje ya biya kudin komai da komai da duk wani
magunguna da ake bukata masu tsada ya siya mata da yawa aka siya wanda zai dade bai
kare ba.

Abincin masu ciwon sugar daban haka yasa aka masa list duk ya siyowa Mama,komai
naci sai da ya siyo har na kannen Maheera abinda zasu ci lemuka da fruits da kayan
shayi etc sai kudi ya basu yace ga wannan ku rike idan zaku siyi abinci,Suka ce mun
gode.
Ammar yace dan Allah waye kai? Sohail yace sunana Sohail idan Maheera tazo ku fada
mata ta sanni,suka ce to an gode.

Yana tafiya Maheera taje asibitin ko zama bata yi ba tace ya jikin maman? Bacci
take tun rana,me suka ce za a biya?
Wani yazo ya biya komai kalli abinda ya siyo yace sunansa Sohail,kawai ganinsa muka
yi yazo, Juwairiyya tace Aunty wani kyakyawa ne wlh,Sahil ne ya shigo kamar ana
fada musu,Ammar yace yawwa gashi ma ya dawo,basu gane ba Sohail bane,ita kanta
Maheera sai da yayi magana taga wushiyarsa yar karama ta gane Sahil ne.
Tace dan uwansa ne fa ba shi bane wannan Sahil ne waccen Sohail,Su Ammar suka ce
ikon Allah basu da banbanci,Sahil zuwa yayi ya ja kujera ya zauna ya tambaya ya
jikin Maman? tace da sauki,Su Ammar suka gaida shi yayi musu ya me jiki.
Sahil harda cewa kaiii Mama tana jin jiki wannan kibar tata bata Allah bace ciwon
ne ya hura ta karku dauka jin dadi ne yasa tayi kiba haka, suka ce ae haka likita
yace,Allah ya bata lafiya ya furta,20k ya basu yace sa suyi wani abun,suka ce kaima
sai ka bamu?

Yace ya zanyi Sohail yace na baku ba yin kaina bane Sohail ne ya min dole yace
lallai na baku,ba wani kudi ne da mu ba rufin asirin Allah ne,Maheera ta boye
dariyarta tace to mun gode ka gaida gida,yace a'a sai kace mahaukaci zance gida
ance ana gaisheka gida ba mutum ba ba komai ba kice na gaishe shi bazan yi ba ya
fice yana cewa Mama Allah ya baki lafiya kiba haka kamar ta jin dadi kai ciwo da
wuya yake,sai kace kibar sihiri kafafu tutum tutum haka.

England
Wata dattijuwa ce zaune a garden din gidanta tare da wani tsohon bature Halley
Maman su Sohail,Mijinta ta kalla Ivan,cikin harshen turanci tace ina so zanje
Nigeria zuwa nan da wata uku,tun daga yarana dana bada su na zaci idan nayi aure
zan sake haihuwa ban sake haihuwa ba tunda na aure ka wanda a baya ina da kuruciya
bani da aiki sai club da holewa na sa a gaba,yaro na daya bashi da lafiya suka
dameni na bawa ubansu shi ya sake ni,yanzu ni nasan nayi kuskure suna can sun zama
musulmai,bana so kuma su kasance musulmai gaskiya,bana son musulunci,bayan haka
yanzu basu sanni ba ina bukatar yarana su sanni na jasu a jiki.

Na nemi ubansu rannan da kyar na samu number dinsa wajen abokinsa Harry na kira
yana ji nice ya kashe wayarsa,yanzu Nigeria zan tafi na ja yarana a jikina su san
wace ni tunda ban haifi wasu ba.
Mijinta Ivan yace kinyi ganganci kuma baki yi daidai ba,yanzu baza su saurare ki
ba,baza ki iya canja musu addini ba,indai hakane Halley har yanzu to baki hankali
ba,na zaci ma zaki ce bari kije ki basu hakuri su karbe ki a matsayin uwa amma ke
ta addini kike yi,sannan kuma tunda baki haifi wasu ba shine zaki neme su,yaran
naki kisan da marar lafiya baki tausaya musu ba,baki da hankali Ivan ya mike ya
wuce ciki ya barta iskar lambu na fifita mata sisirin dogon wuyanta ,Halley tace
zan je dai naga yarana ya suka koma yanzu,murmushi tayi tana tunano su.

Online ta hau ta shiga searching sunansu ko zata gansu,har cikin friends din
mahaifin su Sohail ta shiga ko zata gansu bata san uban ma bata su yake ba,shi dai
kawai ya basu ci da sutura shine kawai,text ta turawa Alhaji Ali ya turo mata pics
din yaranta yana ganin haka yayi blocking number dinta gaba daya ya shiga harkarsa.

Islaha kuwa kwananta daya da asuba Lalai ta tasheta tace maza kiyi sallah kije
ki cika gidan nan da ruwa,Islaha tace Abdulrazaqu fa ai shi naga yana ebo miki
tunda shine namiji a gidan nan kuma danki ne na cikinki sai yau zaki ce ni, Lalai
tace to ke naga dama zan dafa na baki kici a kwance ne,Islaha brush tayi tayi
alwala da sallah ta zauna azkhar dinma Lalai damunta tayi ta tashi haka,da kuturin
iyayi mu zaki nunawa addini zaki zauna kina mismis da baki.

Tashi Islaha tayi ta dauki botiki duk garin babu budurwa me girmanta da
shekarunta sai kallonta akeyi,gashi kasan ba yar garin bace kana ganinta yar birni
ce,rijiyar da suke iban ruwan ta karasa,kowa da gugansa yake zuwa.

Ruwan ta jawo ta cika botiki duk maza ne a wajen sun fito iban ruwa kafin su
tafi gona wasu su tafi kiwo,Islaha tana gama Iba ta dauka ta kai gida haka ta dinga
jidon ruwa sai da ta cika ko ina na gidan sannan Lalai ta bata dumamen tuwo da wani
dan koko a kofi kamar na yaron yaye tace gashi nan.

Islaha tace kaddara kenan in ba kaddara ba me zai sa naci wannan tuwon,Lalai


ce ma zata yi wani girki ta bani naci,Lalai tana ji tace uban wa ya kawo ki
gidan,ji nake ke kika kawo kanki kinibabbiyya.
Islaha haka tana kushewa ta cinye tuwo ta shanye koko tace dan dai kawai na rayu
ne wlh da bazan ci ba,Lalai ta fito tana masifa sai kije kiyi wanke wanke ko a
banza zan zauna ina dafawa ina baki kina ci.

Islaha taje tayi wanke wankenta tayi shara ta gyara gidan,Lalai tace saura
daka, mu kin san a nan sai munyi sissika,surfe ma da hannu muke yi a turmi sai ki
fito ai,Islaha ta dauki tabarya ta tsaya a jikin katon turmi,Lalai ta zuba dawa
tace bismillah mu fara wannan dai zan tayaki,kyazo kici a kwance ne,sabo da Allah
sai dai a baki kici ki koshi, sa jiki yi da jiki maza saka tabarya,Islaha ta saka
tabarya daya chakwal chakwal sam bata iya ba,Lalai ta sa tata tace yar bibiyu zamu
yi muje zuwa a hankali zaki goge.

Islaha ta dinga yi suna yi a haka da Lalai kaikayi yana tashi zuwa jikinsu,
Abdulrazaqu ne ya shigo sai faman zagasu yake yana karewa Islaha kallo yana
sannunku da aiki,Islaha ashe kin dawo nan da zama yana wage baki,da wata hularsa
bokoko.
Lalai tace tayi aure taki ka ganta nan kalar bazawara, Abdulrazaqu yace ai
watakil rabon na gida ne shi yasa Allah ya dawo da ita,yin Allah
ne,Islaha..Islaha...kaga Islaha sarkin aiki cewar Abdulrazaqu,Islaha haushin
Abdulraqu ya gama kamata da irin kallon da yake mata.

A cikin gidan ya nemi jikin bishiya ya zauna sai faman kallonta yake yana
murmushi baki a bude,Islaha ta gaji amma sai da aka gama daka da ita,sannan Lalai
ta kwaso danyen rogon da Abdulrazaqu ya kawo ta mikawa Islaha wuka tace maza mu
fere shi za a dafa yau aci da kuli.

Islaha ta karba bata ce komai ba haka suka fere rogon nan tas Lalai ta wanke ta
dora a murhu ta fara dafawa,tace share wajen,Islaha ta sake share ko ina taje tayi
wanka,tana yin wanka Lalai tace kinyi asarar sabulu ai zamuyi surfen dawa,Tazo ta
zuba dawa a turmi da dan ruwa tace sa tabarya muje,Islaha tana daka tana kuka tace
wlh ni ban iya irin wannan aikin ba,ban saba da yi ba,kashe ni zakiyi haka,
Abdulrazaqu ya fita amma bai dade ba sabo da Islaha ya sake dawowa.

Ya ganta tana kuka yace ji banza raguwa mu anan yarinya karama ba sai ta daka
dawa kwano biyar ba amma ke dan wannan aikin kike wa kuka karki bada ni mana,Islaha
tayi banza da shi tana hawaye, sai da suka gama tas sannan Lalai tace ai bamu bushe
an wanke dawar ba,dakko faranti da faifai,Islaha taje ta dakko haka suka bushe tass
tace dauki ki wanke,Islaha taje ta wanke ta shanya a wani karamin tempol.

Tashi na aikeki ki siyo kuli,Islaha ta mike da kyar take tafiya,haka ta karbi


kudin tace gidan su Baffa Gali zaki je matarsa tana siyarwa,Hijab ta saka ta fice.
Tana shiga gidan Baffa Gali kowa ya fara murna tunaninsu Aunty ce ta sake aiko
Islaha da kudi ko wani abu,Sai lale ake yiwa Islaha,Baffa Gali yace ashe kinzo
garin gidan Lalai kika sauka ne? Islaha tace ae,yace Ja'ira gari duk danginki amma
mu baza ki dinga sauka a wajen mu ba,mufa yan uwanki ne na kusa ba na nesa
ba,Islaha tace ai na dawo nan da zama gaba daya ba Aunty ce ta aiko ni ba.

Gali yace toooo....fada kuka yi? Islaha tace itace tace ta gaji dani,Gali yace
kece kika mata rashin kunya Islaha,laifinki ne,ba ruwan Auntynku mutuniyar arziki
ce,ku yaran yanzu baku iya samun waje ba,yar banza kina zare ido kamar na uwarki,
Gwara ma da kika sauka gidan Lalai din ni nan baza mu shirya ba,kuma ki fidda miji
kinji na fada miki.

Islaha tace a bani kuli inji Lalai,Matar Gali ta karbi kudin a wulakance ta
kawo kulin ta bata tace ki gaida Lalai,Islaha ta juya tayi tafiyarta,a ranta tace
nina jawowa kaina da ban lallaba Aunty ba da tuni ina Lagos abina,ashe Aunty dai
duk da haka tayi kokari ta iya rike ni,inci insha duk da itama irin lalai ce sai
naci aiki ake bani ga zagi ga gori amma da dama aikin nasu ba irin na kauye ba,idan
nayi sati ina wannan aikin sunan na tashi a aiki na zama tsohuwar karfi da yaji
bazan iya ba idan na gaji guduwa zanyi wlh.

A haka ta dawo gidan Itace ta daka kulin Lalai ta kwashe rogo shi suka ci suka
koshi sannan ma ta samu tayi sallah.

Maheera tana can suna jinyar Mama kullum su Sohail sai sunje asibitin dubiya
har Mama ta samu sauki aka sallame su,amma Zayna da su Adnan an fada musu ko ya me
jiki basu ce ba,Ibrahim kuwa ya tafi kano gida wurin Daddy har yanzu bai dawo ba
tunda suka tafi tare da Amal bai ma san Islaha bata gidan ba sai yau da ya dawo da
yamma,ya gaji ya tambayi Maheera tace ai ta tafi garinsu,yace ina ne? Tace Taraba
kauye,wanne kauyen? Tace ban sani ba,yace baki da hankali duk zaman da kuke yi baki
tambayi address dinsu ba ya ja tsaki ya fara gwada kiran Islaha number bata shiga.

Bai gaji ba yace amma indai ta taba kunna layin a garin da take ai masu
tracking number zasu gano zanje na bincika har kauyen da take zanje.
Sohail dai yana ta zuwa aikinsa gwanin sha'awa Alhaji Saminu ana ta samun ci
gaba a kamfani mugun kaunar Sohail yake yi sun saba sosai,bangaren da Sohail yake
basai me karatun boko me zurfi ba,sannan akwai wani a kusa ko da haukar zata motsa.

Gidan an zuba furniture da komai na bukata flat house ne me kyau,dauke yake da 3


bedrooms sai parlo,ga katon kitchen da Dining area daban,gaba daya estate din irin
ginin kala daya ne komai kai daya kowa da wajen parking da komai, ko ina yaji
fulawoyi kamar a turai,basu bar gidan su Adnan ba amma kullum sai sunje sabon gidan
kuma watarana su kwana acan watarana su yini su dawo gidan su Adnan su kwana haka
suke sintiri.

Motar ma kusan Sahil yafi Sohail hawa,Kayan abinci da duk wani nauyi Sohail ya
daukewa Maheera na gidansu bata musu komai yanzu,gashi bai taba zuwa gidan ba,sai
daga baya tunda yasan gidan ya dame su da zuwa, Mama ce ta kira Maheera a
waya,bayan sun gaisa tace Maheera nifa yaron nan da yake ta mana hidima ya kamata
ace idan soyayya kuke kin fitar da shi tunda yana da aikin yi,kuma yana da hankali
ni na yaba da shi gaskiya,indai kin san soyayya kuke yi banga amfanin zaman haka
ba,Maheera tace to ni dai mutunci muke yi da shi Mama,ban tabbatar da so na yake
ba.

Mama tace shike nan tunda haka kika ce amma ni bazan so ace yana kashe mana
kudi a haka ba gaskiya kawai kisan yanda zaki ko ki dakatar da shi ko ki tsaida shi
a mijin aure kawai,Maheera tace to,Mama tana kashe waya sai ga Sohail yayi parking
motarsa sanye yake cikin sky shadda ya zuba kyau,gidan ya shiga kai tsaye,Mama ta
amsa sallamarsa tace Sohail kaine kazo? Sohail ya sosa gashinsa daga bakin kofa
yaki shiga kuma yana daga tsaye ya leko da kansa yace Mama Ina yini? Baza ka shigo
ba kuma yau? Ai ka zama dan gida,Sohail yace kunyarki nake ji kunyar surukai nake
yi,Ammar yayi dariya kamar me,Yace dan Allah ka shigo? Sohail yace wallahi Allah
bazan shugo ba yau kullum sai nazo na shigo, nazo ina raina sirikata,Mama dariya ta
kamata,tace yau naji shashan yaro kai kuwa kalau kake?

Sohail yace ki fadawa Maheera Mama ta dawo gida nayi nayi taki ta dawo ai ba
mutunci bane ta zauna cikinmu,gwara zayna ita tana da miji,Amma mu maza mu hudu ne
a gidan ita budurwa ta hakura da aikin nan zan mata komai ni kadai kudina ya
isa,amma taki sai Iyayi take min wani ita ai kaza kaza ya gwada yanda Maheera take
magana,Mama tana daga palo yana daga bakin gate a haka suke zancen,Mama tace to ka
turo iyayenka indai sonta kake suje dangin ubanta a nema maka aurenta na gaji da
wannan soyayyar in ka tabbatar sonta kake kayi magana,Sohail yace zan dai tabbatar,
zan tafi,yau Mama bazan baki kudi ba Ammar zan bawa,Mama tace to ai abin naka yayi
yawa ni kyautar ma taka ta ishe ni,Sohail yaji dadi ya kira Ammar ya bashi kudi ya
juya ya tafi yana murna yace yawwa dama nace Mama sai ta shiga uku da kudi gashi
tace kyautar har ta isheta,sai nan gaba ma, ya shiga motarsa ya tafi.
Shi da Sahil kaya iri daya yake musu komai iri daya,kasancewar ma basu saba rike
kudi ba sai suyi ta shawarar me zasu yi da kudin.

Washe gari Sohail ya kwanta ya bawa Sahil Amt dinsa da key din mota yace kaje
ka kai Maheera shopping duk abinda take so ta siya,Sahil yace ka isa ka aikeni wato
kayi kudi ni zaka aika ko? Kaje ka dauke ta ka kaita ni karka dameni tunanin Islaha
nake yi na kasa dainawa,ban san a halin da take ciki ba,nayi kuskure,Sohail yace
bani naje na kaita marar mutunci akan nace zan huta ka kaita duk kudin ba mu dai
nake nemowa ba,Sahil yace jeka dai bazan je ba Islaha ta tafi ita yarinyar nan
Allah bai yita da yar karamar sanwa ba,Duwunta kadai tallaja guda ne inji larabawa
suka ce Tallaja,aba ba kadan ba yanzu ta kama hanya ta tafi duk wanda ya ganta ya
kenan,Sohail yace Allah ya kiyaye kar tayi aure ma,Wanda ya sameta kuwa zai sha
kallo,Sahil ransa ya baci yace bani key din naje na kai Maheera din ina dan dubawa
gari ko zan dace na ganta.
Ba musu ya bashi key din ya fita.

Ibrahim kuwa tracking aka dinga masa yana biyan kudi sai da aka gano inda take
har gidan da take,ya cika da farin ciki washe gari a .mota ya tafi ma da kansa sabo
da shiga kauyen,ya dinga sharara tafiya yana bin location har garin da Islaha take.

400 ne 1&2 gaba daya

0175487861
Asmau Garba Muhammad
Gtbank

Yan Niger
+22790795939

AsmaBaffa
08061929616
[7/17, 3:17 PM] Asmabaffa: 🪸MUMMUNAR DABI'A 🪸
31-35

Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA NE GA 'YATA TASNIM

Page naki ne
Bestynbeelat

Ibrahim yana tafiya a motarsa yace chaiiii wannan kauye haka wanne iri ne,dama
har yanzu da irin wannan kauyukan a kasar nan,wannan kauye kaddara ce ta kawo ni
ace kamar ni Ibrahim ina son yar wannan garin zuciyata baki kyauta min ba, 'yar
wannan garin kamar ni za ace ina son yar nan kauyen Allah ya kiyaye ba mayu bane ma
duk tabi ta lashe mana kurwa sai dai aga muna ramewa a rasa dalili.
Amsa ya bawa kansa yace ko ma mayyar ce haka zan aura duk su Sahil ta lashe min
su.

Wasu yara suna ta faman wasa da kasa Ibrahim yana dan tsayawa kusa da yaran da
niyyar tambayar su suka watse gaba daya da gudu suna cewa barayi barayi ne...sabo
da sunga mota, a kauyen ana musu huduba in sunga mota su gudu barayi ne,Ibrahim ya
dinga mamaki yana daga cikin mota.

Abdulrazaqu ne ya dawo daga gona da ganyen zogale da yawan gaske zai kai
gida,Ibrahim ya fito daga mota tare da yi masa sallama,Hannu Ibrahim ya mika
masa,Abdulrazaqu yaki bayarwa yace kawai na baka hannu mu bace tare mu gaisa daga
baya baya.

Ibrahim yayi murmushi shaddarsa tana sheki tana daukan ido arsh ga jiki ya ji hutu
dole Abdulrazaqu su firgita,Ibrahim yace dan Allah gidan su Islaha nake nema,
Abdulrazaqu yace yayanta ne ni ma da kake gani na,Amma kai na ganka baki bakwa
kama,gaskiya da kamarka tayi sai dai a auri Islaha a garin nan.

Abdulrazaqu yaji haushi yace amma kai baka da ilimi sam kazo garinmu ka tare ni
kana min tambaya sai ka dinga chaba min magana ko ance maka so shi a kyau yake? Duk
ga ba munana nan ba sunfi auruwa sunfi samun mazaje na gari kuma kyawawan maza suke
aura,sai kayi mamaki kace me ya gani a jikinta shi gashi kyakyawa,kuma kyakyawa
mace kaga tana ta fadawa hannun mazaje munana,kaga mace hadaddiya mijinta ficika
baza a siye shi ba,shi so da aure ai ba ruwansa da kyau malam ka gyara
kalamanka,daka ganni bakin ba Allah ne yayi ni ba,a gidanku aka kirkireni? Ko kai
farin ne gaka nan wankan tarwada kai a wankan tarwadar ma da alama kanti ka shiga
ka dawo haka dama ai munji labari yan birni mayuka suke shafawa har mazan,mu kuwa
mun tsaya yanda Allah yayi mu,ka ganni nan ko vaseline sai na shekara ban shafa
ba,watarana ma mangyada nake shafawa da sanyi amma gani dakaukau dani aikin da nake
baka isa kayi shi ba.

Ibrahim yayi dariya yace shi yasa ai gaka nan kamar an tonoka daga rami abokina
maida wukar ka kira min Islaha idan tana nan,idan na sameta na maka alkawarin jari
me tsoka ka fara kasuwanci zan maka gida me kyau a kauyen nan da babu kamarsa.
Abdulrazaqu yana jin haka yace da ina son Islaha nima amma na bar maka ita zan
tsaya tsayin daka ko da tsiya sai ka aure ta ka kaddara ka sameta an gama.

Ibrahim yaji dadi yace na gode jeka zan bika a baya da mota,Ibrahim maimakon
yace Abdulrazaqu ya shiga mota su tafi baya so ya shigar masa mota kar kamshin ta
ya canja ya bata masa mota,a haka suka tafi shi yana daga cikin mota Abdulrazaqu
yana tafiya a kafa har kofar gidan Lalai.
Ibrahim yana parking a gindin bishiya ya fito yace ai a nan gidan Islaha take?
Abdulrazaqu yace ae a nan take,yace cab,Shigo ciki gidan tsohuwa ce ba wani abu ta
riga ta tashi a aiki, shigo ko a wanne hali ka kalleta ba komai,Ibrahim yayi
murmushi suka shiga kai tsaye gidan,Lalai tana jikin katangar kara tana leken mota
a kofar gidanta riga daban zani daban.
Islaha tana zaune a gindin murhu tana ta faman iza wutar tuwo ta hada zufa
idonta yayi ja sabo da hayaki.

Mamaki ya kamata ganin Ibrahim a tsakar gidan su yazo, Abdulrazaqu yace Islaha
kinyi bako daga birni ai kin sanshi ko? Lalai tace sannu da zuwa maraba, ta fada
daki ta dakko tabarma sabuwa ta shimfida masa a kasan bishiyar mangoro dake
gidan,Ibrahim ya cire takalminsa me kyau ya zauna,tare da gaishe da Lalai,Islaha
haushinsa taji da yazo amma bata nuna masa ba tunda gidansu yazo kuma dan ita
yazo,mikewa tayi sanye cikin riga fitted gown ta atamfa green,komai ya fito
chass,Ibrahim ya kare mata kallo irin na wayayyun yan birni kamar ba kallonta yake
ba,karasowa tayi tace sannu da zuwa ina yini,kazo lafiya,ya hanya? Ta furta a jere.
ya amsa lfy Alhmdllh,shine kika taho ba sanarwa,murmushi tayi,yace ba sallama ba
komai ko dan zaman tare ai kya yi mana sallama,Islaha tace ai wanda naje dominsa
yasan na taho.

Kishi ne ya cika zuciyar Ibrahim yace ai shi bai damu dake ba,da ya damu dake ai
da yazo,ko ya zo ne? Twins basa soyayya ba masu lafiya bane baza su iya inganta
rayuwar kansu bama bare su inganta ta wani,gagararrun Aljanu ne da su, bakaken
aljanu kuma masu gulma ma su suka hau kansu,da cutar aka haife su,kinga wanda aka
haifa da cuta ai baya warkewa,tsoro ma muke ji kar nan gaba su fara duka ko su fara
tsince tsince a bola.

Islaha tace Allah baya sa ba inshaallah zasu warke baza su taba zama hakan
ba,kaima idan kun san farkon ku ai baku san karshen ku ba,Ibrahim yace Allah ne ya
dora musu ba ni ba,mu bar wannan maganar muyi abinda ya kawo ni, Lalai ce ta fito
da ruwa da abinci ta kawo har da hado fura ta kawo masa, Islaha tana kallon ikon
Allah yanda Abdulrazaqu da Lalai suke wani nan nan da Ibrahim kamar zasu cinye shi.
Lalai ce ta kalli Islaha ta gasa mata harara tace ki zauna mana kuyi hira
wajenki yazo kin wani tsaya masa kerere a ka,Islaha ta zauna tana jin haushi a
ranta,Ibrahim ko ruwan su bai sha ba,bare yaci wani abu nasu ma.
Islaha ya kalla yace kina shan wahala a nan kizo mu koma gida dan Allah wannan
garin bai dace da irinki ba,ke ba kalarsu bace,idan ma baza ki koma gidanmu ba muje
zan kama miki hayar gida idan ma so kike zan siya miki gida naki na kanki sannan
zan baki jari na bude miki wani abun na Business ki dinga yin abinki,idan ta kama
har Dubai zan nuna miki yanda ake shugo da kaya ki dinga samun kudi,Islaha a ranta
tace gwara a bani Sahil na kare a talauci na,a fili tace na gode ni nan yafi min
idan kaga na bar nan to nayi aure.

Ai me sauki ne sai na turo manya a nemar min aurenki,Islaha tace ban shirya
aure ba yanzu ni soyayya ma gaba daya bata gabana,murmushi Ibrahim yayi yace a
ransa a hankali zaki shigo hannu ne yarinya,a fili kuma yace ba komai zan jiraki
ni,ya dan dade yana hira tana amsawa sama sama sannan yace Alhmdllh tunda na san
inda kike yanzu hankalina ya kwanta zan tafi,tace a yau zaka koma Abuja? Yace a
cikin gari zan kwana a hotel gobe sai na wuce,tace yafi dai,mikewa yayi zai tafi
tace ka gaida gida.

Lalai ta tsomo baki au baza ki raka shi ba? Mayafinta ta yafa tabi shi suka
fita,Ibrahim sai dadi yake ji shi gani yake ma ya samu Islaha an gama,50k ya
ajiyewa Lalai sabo da ya siyeta da kudi, Abdulrazaqu ma haka ya bashi 20k,sai murna
suke yi,Ibrahim yace idan na dawo za a rakani gidajen yan uwan Islaha na gaishe
su,Lalai ta yashe baki tace Allah ya kaimu dan nan kaji,an gode Allah ya tabbatar
da alkhairi gashi kayi dace dama bata da saurayi bata kula kowa a sadaka zaka
sameta,Ibrahim yace na sani ai ya wuce abinsa.

Suna zuwa jikin mota ya bude motarsa ya dakko ruwan roba ya balle ya sha
abinsa,wato bazai sha na gidan ba,Islaha tace shine mu kaki shan ruwanmu ka dakko
naka ai ba so bane wannan,Ya kalleta yace Typoid masifa ce sabo da ina son budurwa
kawai sai na cuci kaina Typoid ta kamani ko na sha tsutsa a cikina ta hayayyafa ta
cika min ciki, Typoid bata jin maga ni.

wato mu ta kashe mu kenan?cewar Islaha,Ibrahim yace ku ai kun saba ta saba da


jininku ta sanku,baki ta tabe ya shiga mota sannan ya sauke glass ya miko 50k itama
yace gashi kya samu ki dinga siyen wani abin,Islaha tace ina da kudi na ance maka
bana ci ina koshi ne..
Nasan kina koshi mana amma garau garau gashi nan naga kin kara cikowa ma,Karki wa
kanki ki karba karki koma gida kina cizon yatsa,Islaha taki karba fafur tace ina so
na fada maka karka dawo wajena ni dai da Sahil nake soyayya sabo da haka bazan kula
yaya na kula kani ba.

Ya kalleta cike da kishi yace Sahil baya sonki ki daina batawa kanki lokaci bai
san ma kina yi ba harkarsa yake ya manta da ke ma,Islaha tace na ji duk da haka,kai
fa bai ma dace ko da wasa ka kulani ba sabo da kaninka tunda tare ka ganmu,Ibrahim
yace idan kika ga na hakura to kice an daura miki aure,Ba ruwana da wani Sahil
kanina ne yazo muyi takara wanda ya samu shike nan ba abinda ya dameni,Islaha ta
gaji tace to ka gaida gida na gode ta juya ta shige gida ko sisinsa bata karba ba.

Islaha tana komawa gida Lalai ta fara masifa tace ina lekenku kina fada masa
magana,har ya baki kika karba to ubanwa kike so yaro kyakyawa da shi ga kudi dan
birni,Islaha tace to ni bana sonsa kaninsa nake so karki dameni,Lalai tace to kuwa
matukar baza kiso wannan ba sai dai ki bar min gida wlh,yaro dan mutunci ga
kyauta,Islaha tace ae naji zan tafi bazan taba sonsa ba wlh ni bana sonsa,sabo da
ya baku kudi ni zaku cuceni.

Lalai ta fara ruwan bala'i kizo gidana in ciyar dake amma nace kiyi abu kice a'a
ai kuwa baki isa ba kici ki sha kice zaki rainani,Islaha tace iya na aikin wahala
ta naci kyauta kika bani ba aiki nayi ba sannan aka bani,tuwon da rogo sai dambu ko
danwake shine ake ta min gori sabo da ni bazan baki abin duniya ba,nidai na fada
miki bana sonsa gwara na bar gidan kuma da bana gidan ai da baku samu kudin ba,zan
iya danne ki na kwace kudin nayi tafiya ta gwara ki kyale ni kaka Lalai,ni talaka
na nake so kaninsa,ba wanda yake bani ci da sha a dangi babu wanda zai fada min
naji kaf garin nan,bani da mafadi sai a bari ace an dauki nauyina sannan sai a fada
min naji,kullum in yini ina aiki a bani dan tuwo shike nan a dameni ace za a bani
Umarni a haka zanbi umarnin? Ba a dauke ni a matsayin 'ya ba,ko Baffa Ghali
dukkansu basu isa dani ba,daurin aure kuma ko a masallaci al'ummar annabi zasu
daura min.

Lalai tace zaki ci ubanki da ni kike zance,duk wannan abin da kike yi kyaleki
ake yi,ai dai a gabana kike to kamar kin so Ibrahima,Wallahi bazan aure shi ba
cewar Islaha,shuru Lalai tayi mata suka ci gaba da aikin girki,Lalai ta kawo maggi
dunkule biyu rak wai shi za a sa a miya ya isa,ga miyar da yawa,Islaha ta mike ta
dakko farin maginta data siyo a boye ta faki idon Lalai ta watsa a miya sannan ta
kara dunkulen biyu a ciki,haka take yiwa Lalai kullum,sai aji miya zakwai zakwai
Lalai ta zaci tsabar gogewa ce da girki irin na yan birni yasa Idan Islaha tayi
miya zaki kamar kar miya ta kare,sai Abdulrazaqu ma yace a dinga bawa Islaha miya
tana yi gaskiya tafi dadi.

Bayan an gama girki sunyi sallar magriba,Lalai ta zubo tuwo tana ci tace kaji
miyar yan bariki,miya sai bariki,amma mutane ace dunkule baya zakin miya,bayan ma
farin magin nan cuta yake sawa amma wasu a dinga gabza shi a miya,Lalai tana wulla
loma tace ai ni sam bana cin farin maggi duk inda naje indai an sa farin maggi a
miya sai na gane,kana ci zaka ji zaki har kai,yana wani bauri kamar ruwan teku.

Islaha tana jinta tana dariya a ranta tace ace dunkule biyu rak miya kamar zan
mutu idan ina ci sabo da rashin dadi,ai gwara da na siyo farin maggi na a boye na
ajiye su,kullum da anzo girki zan faki ido na zuba.
Lalai tana yin sallar Isha ta mike ta dauki mayafinta tace na tafi gidan Baffanki
Shamsu,Islaha tace a dawo lafiya.

Lalai tana tafiya ta dinga bin gidajen yan uwa tana basu labarin Ibrahim da
irin kudinsa da kuma yanda Islaha tace ita bata sonsa talaka take so kaninsa.
Baffa Shamsu yana ji yace haba karya take wane ita, ita din banza,me akayi aka yi
Islaha,Lalai tace to yace kuma zaizo ya gaishe ku zaku sha kudi ku mike tsaye so
take tayi mana asara,Shamsu yace ai baza mu barta haka ba da malamai zamu hada ta
dole ta so shi ta aure shi,gaba daya ki lallabata kiji sunan waccen wanda take so
din ki fada min zamu bi ta wata hanyar kawai sai dai taji ta tsane shi ta fada son
wannan Ibrahim kika ce ko? Lalai tace kwarai kuwa shi yasa nace bari nazo wajen ku
ni tafi karfi na,baku ga yanda take min ba kamar zata dake ni har girgiza take idan
tana min masifa,Shamsu yace jeki karki sake tsokanarta karki nuna komai ki nuna
zabinta shine namu muma da haka zamu yaudare ta.
Lalai tace yawwa shike nan ai yanzu lallabata zanyi,bari na koma sai ka jini ina
jin sunansa zan dawo na sanar maka.

Bayan Lalai ta dawo ta samu Islaha ta kunna wayarta tana game a ciki,amma ta
sata a flymode, ta zauna da fara'a tace ku dai idan kuna wannan abin bakwa jin
sallama,Ai na amsa cewar Islaha,Lalai tace Islaha wato dai bakya son wannan Ibrahim
din? Zaki mana asarar kudi,arziki yazo mana har gida,Islaha ta turo baki tace ni
bana son zancensa,Lalai tace ai muma zabinki muke so tunda kinki yarda ya zamu yi
baza mu yi miki dole ba,Shi wanda kike so din iceko na kirki ne? Islaha tace ae
sosai,ya sunansa ne shi wai?

Islaha dariya tayi a ranta tace haba Lalai da wayona da hankalina ba a banza na
zauna a birni ba kuma ina aiki da ilimina,ni zaki rainawa hankali wallahi nafi
karfinku nafi karfin tunaninku,a fili kuma tace Sunansa Tijjani,Lalai tace ya mori
suna Allah yasa ya gaji me sunansa shehu ibrahim Tijjani Inyasi,dariya Islaha tayi
tace hmm shi dai sunansa ne haka ba wani gado.
Lalai tace to Allah ya nuna mana Allah ya kawo shi na ganshi waye wannan me
sa'ar.

Islaha tace Lalai amma yanzu tunda zanyi auren ai zan daina daka da sissika?
Lalai tace inji uban wa ko gomna zaki aura sai kinyi sai in kin bar gidan nan,
kawai sai na dafa na baki kici a huce hauka ake a ci dake sannan aikin ma baza kiyi
ba sai dai kici a kwance sannu Sa'ida sunan wata bishiya,kece shafaffiya da mai da
za a nemo da wahala sannan ayi aikin wahalar duk a baki kici a kwance sabo da kece
Gimbiya hakima ishashiya,gwana yar hutu,Islaha tace to naji ni ki kyale ni.

Washe gari da safe da Abdulrazaqu ya shigo sakamakon dakinsa a waje yake daban na
bukka, Lalai ta ja Shi gefe tana fada masa yanda suka yi da Baffa shamsu ta inda za
a bullowa Islaha, Islaha tana can tana aikinta na gyara zogale yau dambu zasu yi
kuma.

Lalai yau ma da dare ta koma gidan Baffa Shamsu ta fada masa sunansa
Tijjani,Baffa Shamsu yace zaici ubansa ko waye wannan Tijjanin da take so,ga
Ibrahim ai yafi.
Ya mike yace muje gidan Malam Ishu da shi kadai na yarda a garin nan.
Tare da Lalai suka je har can,suka zubewa Malam Ishu bayani da abinda ya kawo su
ayi musu,Malam Ishu ya buga kasar dake gabansa, Malam Ishu sai da ya buga sau uku
yace gaskiya babu wani me suna Tijjani da take alaka da shi,karya ta muku,amma ba
sai ta fadi sunansa ba ku kyaleta aikin ba wahala ma an raba su aikin me sauki
ne,amma zaku yanka zakara kuma ita za a bawa ta ci indai ta ci naman to shike nan
zata fada son Ibrahim ta gigice da gaggawa zata matsu a yi bikin,Sai shi wannan za
a raba su wani rubutu zan baku ku tabbatar kun zuba mata a ruwa ta sha indai ta sha
ko yaya ko ba tijjani ba ko uban waye ma a ranta sai ta daina kaunarsa kawai sai
Ibrahim,kullum sai tayi kuka akan Ibrahim,da kanta zata nemo shi yazo ayi biki.

Dari biyar suka bashi sadaka a haka sai murna yake ya sha kudi,yace gobe Lalai
ta dawo ya karanta manta yanda zata aikata aikin, Islaha bata san me suke yi
ba,washe gari Lalai ta koma ya bata wani rubutu a leda yace shi zaki juye mata a
ruwan sha idan zata sha ruwa ko yaya ki zuba indai ta sha an gama,ya dakko wata
laya ya bata yace wannan idan kin yanka zakara an gyarashi kisa layar a cikinsa ki
samu zare da allura ki dinke cikin zakaran tsab ki dafa shi yaji hadi,idan ya dahu
sai ki farke dinkin ki cire layar ki haka rami a binne ta sai ki bata taci,ko ya
taci shima an gama,kuma zaku iya ci kuma iya abin ita zai shafa,Lalai tace an gama
tayi godiya ta tafi direct gidan Baffa Shamsu.

A can Baffa shamsu ya bada katon zakaransa tace a nan gidan zan dafa kawai na
kai can sabo da a can zata iya ganina,Yace haka za ayi,Lalai da matar Baffa Shamsu
suka gyara zakara aka wanke tas suka saka laya tare da sa zare da katuwar allura ta
dinkin buhu suka dinke da kyar yanda dai layar baza ta fito ba suka lallaba suka yi
farfesu me kyau lafiyayye,Lalai ta binne laya amma tunda Malam yace zasu iya cin
naman duk sai da suka ci aka barwa Islaha wani dan kadan a kwano iya wanda zata
ci,dama yace ko yaya indai taci shike nan dama dan ita aka yi ita kadai zai shafa.

Lalai da kwano tazo a rufe da bargajejen hakarkarin zakara a kwano,ta samu


Islaha har ta gama dafa musu dankalin Hausa tayi yar miyar jajjage,Lalai tace har
kin gama sannu,tace yawwa,daga gidan Baffanki nake Shamsu zakaransa ya kasa zai
mutu aka yanka shi shine suka dafa naci nima a can kinga naki na taho miki da shi
maza kici abinki.

Islaha karba tayi ta duba tunani yazo mata haka kawai zasu bata wani nama kuma
har haka da girmansa,ga wani mutunci da Lalai take yi mata yanzu,Islaha a ranta
tace nafi karfinku wlh,Lalai tace bari nayi wanka maza ki cinye a wanke kwanon zasu
zo karba,Islaha ta washe dan karamin bakinta tana murmushi tace na gade bari yanzu
zan cinye abina,kai amma na gode ashe dai Baffa Shamsu suna so na,Lalai ta cika
baho da ruwa tana cewa ai hannunka bai rubewa ka yanke ya yar,Islaha tace bari na
baje naci abina yau akwai harka,Lalai tasan dole ma sai Islaha taci gashi taga sai
murna take yi,sai ta shige wankanta,Islaha tana ganin haka ta dauke naman ta jefa
cikin bakar leda ta kulle ta boye a cikin jakar kayanta,dan romon kuma ta dan
jagwalgwala har gefen kwano alamar anci har romon an sha,ta fito hannunta duk maiko
da romon nama,Lalai ta fito a wanka sai murna take Islaha ta cinye nama,Islaha tace
bani Sabulu,Lalai ta mika mata ta wanke hannunta tas,abincinta ma da zata ci ko da
hannunta bata ci ba da cokali taci dankalin .

Ta fita zata kai kwano kitchen kiri kiri taga Lalai ta bude randarta ta daki da
sauri ta juye wani bakin abu a randar kamar rubutu ta mayar da murfi ta rufe,bata
san Islaha ta juyo zata shigo ta gani ba,fuskewa tayi kamar bata gani ba.

Tana zuwa Islaha ta sake fita tace na manta bari na dakko kofi na sha ruwa,ta
dakko kofi tare da bude randa ta cika kofi da ruwa ta fice waje ta juya ta kai
kofin bakinta kamar sha take tana zagawa ta watsa ruwan a jikin katangar karan ta
dauraye kofin ta maida ta kife ta dawo,Lalai sai murna take an gama aiki sun samu
nasara.

Islaha tsoron Lalai ta shiga yi tun daga ranar bata kara cin abin hannun Lalai
ba,sannan ruwan gidan bata sha fita take ta sha a can inda suke ebowa,abinci ma
indai ba ita ta dafa ba to kwana take da yunwa.

Bayan sati biyu ko nisa Ibrahim bai gani ba ganin baya samun wayarta ya sake
dawowa,Islaha tana ji ance ance shine ta dauki buta tace bari nayi fitsari ta shige
bayi taki fitowa,har ya shigo gidan suka gaji da jiranta taki fitowa,Lalai tun daga
nan tasan aiki bai ci ba,haka ta raka Ibrahim gidan dangi gida gida ai kuwa sunga
ruwan Naira duk ya siye su da kudi sun haukace sai shi.
Lalai yau ma dubu hamsim, Abdulrazaqu ma ya sha nasa kudin,yaran gari ma duk
wanda yazo dubu daya dari biyar biyar haka ya dinga rabawa yaran garin,dattijai da
matasan kauyen daga me 2k sai me 3k haka ya dinga rabo,duk inda ka zaga zancen
Ibrahim me ruwan Nairori ake yi,har an sa masa suna me ruwan Nairori Na Islaha.

Islaha sai da ta gaji ta fito,Lalai ta fisgo hannunta ta zuba mata rankwashi dan
ubanki kije yar iska marar mutunci,ta jawo Islaha har gaban motar Ibrahim inda yake
tsaye yana latsa waya.
Islaha tace na fada maka gaskiya kaki ji na fada maka ka kyale ni wallahi asarar
kudinka kake ji,Ibrahim yace Baffa Ghali yace ya bani,Akan Sahil kike wannan
shirmen ai na fada musu komai na su Sahil din da kike hauka a kansa ya ja tsaki ya
shiga mota yace karki sa na aureki ta karfi gwara ma ki yarda ta salama.
Juyawa tayi ta tafi abinta,yaja mota ya wuce,tana shiga gidan Abdulrazaqu harda
kifawa Islaha mari shegiya yar iska ina ji kika ce bakya sonsa wallahi sai kin aure
shi,Islaha kumatunta suka tasa suka yi jajir, tana dagowa ta shammace shi ba zato
ta yarfawa Abdulrazaqu mari itama tace ka isa ka mareni ba abinda na maka bazan
aure shi ba, Abdulrazaqu dafe kumatu yayi yace ni kika iya mari? Ya jawo bulala
Lalai ce ta rike shi tace kyaleta a hankali ake bi zata so shi ne sai a hankali.

Islaha tace ka dakeni ka gani wlh yanzu sai na kunna wayata na kira Sahil duk
sai ya tashi garin nan Aljanune da shi da kun sani wlh,Lalai tace ta tabbata tana
tafa hannaye Ibrahima baiyi karya ba ashe kuwa Mahaukacin ne kike so,Islaha daki ta
shiga ta barsu nan suna ta surutunsu, kwanciya tayi ta fashe da kuka tace ai koma
mene kaine ka jawo Sahil mutumin banza dan iska,ta dinga zagin Sahil,tunawa tayi
aljanu suna fada musu abu kar su fada masa,tace dan kirki ne Sahil ga hankali,yana
da mutunci,yaro na gari da shi.

Lalai da dare ta koma gidan Malamin ya sake buga kasa yace na fada bata ci
ba,ta fiku wayo naman boyewa tayi ta jefar daga baya,Lalai tace to yanzu ya kenan?
Wani garin magani ya bata yace bari mu bullo mata ta nan idan tana bacci ki barbada
mata maganin a jikinta,sai tana bacci amma,Lalai ta karbo ta dawo tana zuwa ta duba
daki babu Islaha babu dalilinta,ta duba ko ina na gidan bata nan,makwafta ta shiga
da gidajen yan uwa duk bata nan,kuma babu jakar kayanta,Lalai wajen masu machine na
haya taje ta tambaya ko sun ganta,wani a ciki yace yanzu na dawo nine na kaita
tasha can ta cikin birni inda ake shiga motar Lagos.

Lalai tace gidan Auntyn zata koma da sauki ai zamu kira a waya muji idan tana
can sai mu tura Ibrahim can sannan har maganin ma zai kai gareta sai ta soshi.
Islaha kuwa tana zuwa mota ta cika ta shige zuwa lagos sabo da a garin tafi sanin
mutane da yawa zata samu wajen zama ko aikin yi.

Ibrahim haushin Islaha taki sonshi gani yake kamar Maheera ce take zigata a
tunaninsa suna waya dole a boye,sai ya kara tsanar Maheera ya uzura mata,ita kanta
Maheera din sonta yake ita ya fara so amma jarabar Sohail tafi karfinsa,yaga Sohail
ya zurfafa bashi da mutunci kuma akan Maheera zai iya batawa da kowa,Kawai sai ya
dakko wata mace dattijuwa Igbo me suna Madam Oge ya kawota a sabuwar me
aikinsu,Maheera ya samu a bedroom ya shiga kai tsaye yace mun sallame ki a aiki ki
tattara ki koma gidan ubanki munafuka,mun dakko kwararriya,sannan Zayna ma da kike
gani gobe zata koma kano wlh kika ki tafiya sai na lalataki,gwara ma ki tafi tun
muna sheda juna.

Maheera ta kalle shi tace an fada maka dan ku nake zaune? Akwai dalilin zamana
kuma yanzu ma ni nafi karfin nayi muku aiki Sohail yayi kudi tun yaushe ma yace na
daina nice nace zan yi amma badan shi ba zan zauna, kuma dama dan shi nake yi sabo
da ina kai masa Office kula nake da abina kai kuwa sai walagigi kuma bazan so ka ba
Islaha ma tafi karfinka,har abada baza ka samu kamar mu ba kalle ni kalli Islaha ta
juya a gabansa tace kaga komai yaji to sai Sohail da Sahil,a hakan su muke so ba ku
ba.
Ibrahim yace har kudi ne da Sohail din? Nawa ya tara? Har yaushe ya fara aikin?
Sabo da an bashi yar mota da bata fi ta aiken cefane ba,sai gida irin na
gwauraye,kudin kuma nawa ne? Kudin cefanen wani ne a rana daya,Maheera tace ae a
hakan dai kake son yan matansu kuma kwalele sai ma kaga anyi biki.
Ibrahim yayi murmushin takaici yace aje a haifo dolaye masu suffar yan ruwa, maza
tun daga ranar da zaki samu cikinsa laulayinki shine Zana Zero kin dinga zana zero
kenan har ki haihu.

Inshaallah matarka ce zata zana kuma sai naga dama zan tafi yanzu ma sai na kai
masa abinci,Tsaki yaja ya juya yace ana korar ku kuna likewa ban taba ganin
talakawa irinku ba.
Maheera ta dade bata kai binci Office ba sai yau ta shirya girki iri iri ta
shirya abinta taci kwalliya cikin abayar da Sohail ya siya mata wata pink Egyptian
tayi kyau tana kamshi ta fito dauke da abincin a katuwar wledoji har biyu,Adnan ta
wuce a compound yana hutawa ya harde yana danna waya yana kallo ta fice,ya bita da
kallo shi kanshi Maheera tana tafiya da imaninsa,ko baka so sai ka kalleta komai
nata dagwas daidai da ita.

Juyowa tayi ta kama Adnan yana kallonta da sauri ya dauke kansa,Maheera ta juya
tayi tafiyarta,tana zuwa building din tun kafin ta fito a taxi ta kira Sohail a
waya ya fito,fitowa yayi sanye da gajeren wando da tshirts maroon,hannayensa a
aljihu ya fito yana murmushi.
Yace Sweet yau ma baza ki shigo ba? Sunan ya mata dadi tace me kace? baya ya juya
yace nima na manta,tace to juyo mana,ya juyo yace kunyarki nake ji yau,yau ma baza
ki shigo ba? Kai ta daga masa tana murmushi,kallonsa tayi tace ina kayan da ka fito
da su ai ba wannan bane,yace aiki ne yayi yawa na cire dama wannan suna mota
ai,fuskarsa ya kawo jikinta yana shinshinawa yace ya naji turare? me taxi ya gama
shanyewa bazan ji ba sai da aka gama jinsa a duniya zaki wani zo nan,Dariya Maheera
tayi tace kai malam Sohail,harararta yayi yace kinga ta inda muke fada dake ki
dinga fada min malam sai kace wani tsoho ya furta da shagwaba,dariya ta sake yi
tace to na daina.
Yau banyi aiki ba babu abinda na iya na manta aikin Office din,haka aka kyaleni
zaman kashe wando nake yi,ai Alhaji Saminu ya sani baida damuwa,bazai damu ba,Ya
damu mana ina ruwana ni cewar Sohail,Maheera tace wai Sohail idan anyi aure me
akeyi ne da kace zaka aureni? dariya yayi yace nima ban sani ba ai kece zaki fada
min shi yasa zan aureki tunda kin fini sani,Maheera tace ato nidai nasan baka san
komai ba yanzu haka zamu yi auren? tunda ke kin sani ai ba damuwa ya furta yana
gyara mata mayafinta,yace tafi gida to kawo abincin an gode miki,idan ka tashi daga
aiki kazo ka kaini gida yau zan koma gidanmu,Sohail yace kin hakura da aikin? tace
ae na hakura gwara muyi auren kawai,amma Sahil fa shi auren? Sohail yace zaiyi mana
shima kika sani ma ko yazo ya fini samun kudin,Karki damu ko ma mene ai komai nawa
nasa ne Accnt dinmu duka kowa yana iya amfani da na kowa duk abinda yaga dama zai
iya yi nima haka,nafi so muyi auren tare da shi amma shi yace ta Islaha yake yi
yanzu inda zai ganta yake tunani.

Maheera tace kai ka tabbata so na kake a matsayin matar aure? Sahil yace a'a
kinki nake yi, Karki dameni,to kace you love me bazan fada ba na gaji kullum sai
nace I love you ni na gaji i hate you zance,Dariya tayi tace anya Sohail ba lafiya
kake samu ba? Watarana fa magana kake fada min ko?
Sohail yace kanki ake ji dai, wannan kayan fa?ya tambaya.
tace Kai ne ka siya min ko ka manta?

Sohail yace shi sam ba shi ya siya ba,sai idan wani ne ya siya miki kike min
karya,Maheera baki ta bude tace kai fa ka siya min wallahi amma kace ba kai bane,to
yaushe na siya? kawai ki dinga fakewa sabo da ina da dan kudi komai na gani a
jikinki sai kice nine na siya miki,Maheera ta zaro ido tace to a tambayi Sahil ai
yana wajen ka bani,ai ba a karya a gabanmu to ki sani Sahil yana Office dina yanzu
haka tare muka zo da shi, Maheera tace a kira shi din.

Wayarsa ya dauka ya kira Sahil ya fito,ya kalli Maheera yace ai ban gane ki ba
ashe kece kinyi kyau da yawa ne,Sohail yace kaima ka fada wai nine na siya mata
kayan nan wai kana wajen ma,Sahil ya karewa kayan kallo yace a'a Maheera kawai dai
ki fada masa gaskiya idan kece ma kika siya ai normal ne na mene zaki kala masa
sharri kice shine ya siya miki kaya,Maheera ta tsaya kamar gunki baki bude tace
Allah ya kyauta ta ajiye abincin ta juya zata tafi Sohail ya fisgo hannunta a ina
kika samu rigar? Amana ta zaki ci? ka siya min abu kazo kana masifa kai ba kai bane
me zan maka,ko kaga ina kula wani,sannan bani da iko kaga abu a wajena sai kace
lallai wani ne ya bani ai,sabo da kaga mu bamu da kudi shine zaka dinga min haka.

Sahil yayi dariya yace yawwa Maheera karki kyale shi wlh rainaki zaiyi ,to kai
kana kallo me zaka ce ta harare ka fa,sai ka kyaleta? Sohail baya son fushin
Maheera yace to naji ni na siya shike nan a bar zancen jira na maida ke
gida,Maheera ta juya tana tafiya zata yi tafiyarta wani me mota yayi slow a kusa da
ita ya sauke glass kasa yana binta a hankali yana mata magana,Sohail kamar walkiya
sai ganinsa suka yi yazo wajen ya rike hannun Maheera suka ci gaba da tafiya a haka
yana mata magana yace Sweet I love you,kallonsa tayi tasan jarabar kishinsa ne ya
kawo shi,Me mota yana ta magana anki kulashi tafiya yayi kawai,yana tafiya Sohail
yace dan iska kawai, ya tare mata taxi harda biyan kudin motar ya saka ta a
mota,tana shiga ya leka ciki yace naji riga ni na siya ko ba ni bane nine shike nan
magana ta wuce,murmushi tayi abinta tace bye.

Office ya wuce suka ci abinci harda wasu ma ma'aikatan,Sahil yace ka kira Daddy
kace a tura a nemo auren Maheera kawai ka huta da wannan kaunar idan ka ajiyeta a
gida ai ka huta,Sohail ne ya dauki wayarsa ya manta rabon da ya kira Daddy a duniya
shima Daddy haka,yana kira Daddy ya daga yace wai Sohail yau ba jiran gaisuwa yace
ya akayi sohail?

Sohail yace Daddy kiranka nayi ayi min aure kawai,Daddy yayi dariya ya furta to
kana da budurwar ne? Sohail yace ae ina da abata kuma ta yarda su suka ce ma na
tura sabo da haka aje ko kuma na kai masallaci al'ummar Annabi su daura wallahi
idan baka yarda ba sai nace ni maraya ne bani da uba kawai a daura min,Daddy yayi
mamaki yace to ku wanne aiki zaku iya bare ta kai ga aure Sohail waye zai yarda ya
baku yarsa sannan ita budurwar amma marar galibu ce ko?

Sohail yace lallai wato mu ba mutane bane? Daddy yace ba haka bane ai gaskiya ce
sabo da lalurarku,to a hakan na samu kuma ko ka yarda ko baka yarda za a daura
aure,Daddy yace gaskiya ban yarda bada yawu na ba, bada sa hannuna ba a zalunci
yar mutane.

Sohail yace ni da amincewa ta da yawu na harda hawayena na kara ciki, ba yawu ba


harda gumin jikina da yake tsatsafowa wlh sai dai kaji an daura ni dama bance kasa
yawunka ba,idan zaka zubar ka zuba a shara a aurena kar a samun yawu ya kashe
wayarsa.
Daddy yace Allah ya sawwake to a haka a bawa mutum aure da ya za a rike mace a
haka nima ana min magana gatsal.

Sohail kuwa yana kashe waya ya sanar da Sahil abinda Daddy yace,Sohail yace gobe
weekend ai mun san Jigawa din har garin su kawu Nafiu muje mu fada musu a bamu ko
mutum biyu ne nima na sha babbar riga da hula muje a nemo maka auren inda hali a
daura ma daga baya a kai amarya ko ya kace? Sohail yace ai dama kaine waliyi na
karka sake wani ya karbar min aure dangi marasa mutunci ba wanda yake ta tamu duk
rabu da su ana zuwa naka nine wakilin ango suje su karata da furfurar su.

Washe gari kuwa Flight Sahil ya biya suka ware jigawa,daga can suka shiga mota
taxi har garin danginsu,gidan Kawu Nafiu suka dira,Kawu Nafiu yana zaure ya gansu
katsam,yace yau yan biyu ne a gidana?

Sohail ko zama basu yi ba yace badan Allah muka zo ba,ba zuwa gaisheka muka yi
ba,dama ai kaima baku damu da mu ba cewa kuke bamu da lafiya,Sahil yace dole ce
tasa muka zo.
Kawu Nafiu inda sabo sun saba jin shirmen twins,yace to ku shigo muje
ciki,Sohail yace a'a barmu a nan dakin matarka kamar mashekarin Jaki, wata baban
bola da ita,tana yi mana wani gani gani ita su Adnan take so baza mu je ba.

Kawu Nafiu yasan matarsa kazama ce ta gaske kuwa dakinta sai me dauriya,yace to
ku zauna,zama suka yi a gefen tabarma,yace meke tafe daku? Aure Sahil ya furta
kafin ya rufe baki sun bada amsa,kana da budurwar ne? Ae duk muna da ita amma tawa
tayi zuciya yanzu an rasa inda take ko jiya Allah sai da nayi kuka ko Sohail bai
sani ba,Kawu ina jin jiki soyayya nake tana ta bani wahala kalleni duk na tsiyace
na bushe na kekashe,dan Allah kawu kuyi min addua kafin zuciyata ta buga,Sunanta
Islaha,kawu Ko kai ka ganta sai ka so ta sai munyi takara da kai,amma kana gani zan
kasa ka na aure ta.

Kawu dariya ya dinga yi yace Allah Sahil? Sahil an sosa masa inda yake masa
kaikayi yace yarinya ce kai Kawu gangariya, great girl,ta Sohail kuwa kasan Dawisu?
Kawu yace ae yace to Dawisu ce,sabo da haka ayi gaggawar aurar da Sohail tasa tana
hannu yanzu.
Sohail ya fara karin bayani yace yar mutunci ce kawu ko kai sai ta baka
tarbiyya,kawu zaiyi magana Sohail yace dakata kawu karka ga kana da furfura kaima
fa kuskure kanayi tunda ko kai baka damu da mu ba,kana nuna mana banbanci sannan
matanka biyu zaluntar daya kake yi,Abu sabo da tana da hakuri shine kake zaluntarta
amma Zulai marar mutunci amma kafi tsoronta badan Allah bama yi mata abu kake
yi,kaga Maheera ta baza tayi haka ba.

Kawu yasan hali Allah yasa ba a gaban matan suka fada ba,Sabo da haka tana so na
ina sonta iyayenta sunce a tura dangi kuma da uba ake ado dole aga dangin ubana shi
yasa ma nazo amma badan haka ba wlh baza muzo ba,to me zamu zo muyi maka,Kawu yace
to mahaifinku ya yarda? Ko bai yarda ba sai kunje cewar Sahil,da kudinmu muna da
aikin yi yanzu da gida da mota zamu iya,ko gidanka sai mun rike ku ba tare da mun
girgiza ba,kullum kuma sai anci nama ba ma garau garau ba,amma karka sa rai bafa
rike ku zamuyi ba sisi baza ku samu ba kuje Adnan su baku.

Kawu yace to ni yanzu naje mahiufinku bai yarda ba,Sohail yace kayi masa magana
ai yana jin maganarka wlh kawu idan baka je sai an kwana ana zuba ma bulala yau
kaji na fada maka sati za ayi kullum da dare sai an zaneka gwara ma kaje kawai ka
lallaba shi kuma kuna zuwa ni bana son wannan kudin kaza kudin kaza kawai ayi
balance na komai a fada min.

Kawu yace wai da gaske kudin kuka yi ne? Sahil yace zancen kake so Kawu ka
tambayi dangin Maheera idan kaje sai da suka lalace da kudinmu,tun a waje suke
ci,Sohail yace Kanwar Maheera yarinyar nan Juwairiyya har ta fara gurun wuya sabo
da yanzu komai suna da shi ba tunanin an dora da rana ana tunanin na dare,Kawu
dariya yayi yace kun kyauta,Sahil yace zamu baka kudin mota kai da Kawu Tukur kaje
ka samu Daddy kwandala ba mu ce a taimaka mana ba,kawai aje a nema mana,kuma nine
wakilin ango.

Kawu yace to madalla za aje gobe Inshaallah nasan yana gida,idan ma baku je ba
jikinku zai fada muku cewar Sohail,ya zaro damin kudin a aljihu ya balle wrapper
guda yace gashi,sabo da Allah dai sauran ka kashe kuma kayi adalci a gidanka kar ka
sake da kudinmu ka siyawa Zulai tsire ka kyale Abu da tuwo,Kawu hannu na rawa ya
karba yace na gode za aje inshaallah za a daura ma.

Mikewa suka yi suka ce ka kira su Abu mu gaisa a nan mu baza mu shiga ba,Ya
mike yaga kudi harda sauri ya shiga ya kira su Abu suka fito tare da Zulai,Zulai
tace au wai dama kune shine baza ku shiga ba?
Sahil yace wa zai shiga kuna ta kazanta a gida sai kace bola,ko ruwanku baza mu sha
ba kuji gaskiya, babu ga amarya ba ga uwar gida ba me tashin wani kuna zaluntar
Kawu wlh ku gyara halinku Ina yininku Sahil ya furta ko yawu bai hadiya ba kamar
uban su.

Zulai tasan hali suka rufawa kansu asiri suka yi shuru suka amsa gaisuwa,Sahil
ya basu 5k ko wacce yace gashi nan a samu a dinga gyara daki,suka amsa suna
godiya,Sohail hannu a cikin aljihu yace in mun dawo kawo muku amarya Allah yasa
muzo baku canja ba sai dai kuga wannan jeren samirar na dakin ku suna ruftowa kasa
sai anyi daga daga da su,Zulai ta zaro ido dan tun suna yara ta taba dukan Sohail
kwana tayi bata yi bacci ba ana tsikara mata allurai a jiki.

Mu zamu je wajen Kawu Tukur,suka musu sallama suka tafi.


Kawu yana tsakar gidansa yana cin abinci a saman tabarma suka shiga kai tsaye
gidan,gidane shima kamar na Kawu Nafiu shima na bulon siminti komai a sumulmule,
zama suka yi a gefensa shi gidansa da tsafta me tsafta ne.

Suka ce Kawu ina yini yace lafiya lau yan biyu kune? Ae mune cewar Sohail,meke
tafe...aure mun yiwa Kawu Nafiu bayani kawai zakuyi maganar da shi,sannan kaima ga
kudin mota suka bashi shima,yaga kudi ya rude,yace zanje naji me ake ciki yanzu
Inshaallah,Sahil yace ba maganar kin aiwatarwa idan ba haka ba zai fada maka wlh an
tanadi bulalai kawai kuje,suka zauna shima suka kora masa warning,ko ba da sanin
Daddy ba kuje kawai da uwar kudinmu,Kawu yace InshaAllah za ayi ma ai haka ake so.
Ina matar taka? Yace wanka take yanzu zata fito,Sahil yace to bari mu jira ta,
gashi 5k zamu bata baza mu baka ba sai ka rage mata ko ka hanata.
Matar ce ta fito tace Sohail wai kune? Sohail yace mune ke kam kin huta bakya
kazanta gashi ya mika mata ta karba tace an gode to bamu gaisa ba,mun gaji tunda
muka zo muke gaishe gaishe kai tashi mu tafi cewar Sohail suka barta babu gaisuwa
suka yi tafiyarsu,sai lallonsu ake yi a garin ana cewa turawa ne suka zo.
Me taxi yana jiransu suka shiga suka koma airport suka bi jirgi abinsu.

Suna komawa ya kira Maheera ya fada mata yace ta fada za azo gobe wajen
manyanta,Maheera tayi mamaki sai murna take yi bata taba zaton da gaske zai iya
hakan ba,sabo da abin nasu sai sunyi gaba suyi baya basu da tabbas sam.

Su kawu Nafiu yau suna kano gidan dan uwansu Alhaji Ali,tunda suka zo suke
faman ganar da shi akan ya amince yaki yarda,da kyar dai yace na yarda amma wlh
bazan yi bincike ba duk abinda ya biyo baya ba ruwana kar iyayen yarinya su kawo
min kara tunda sun san yaran basu da kan gado,Kawu Nafiu yace ka daina haka duk fa
kaika haife su,kuma aure Rahma ne ka sani ko shine silar warkewar su,Daddy yace ba
ruwana koma wace suje nidai ba abinda ya dameni Allah sanya Alkhairi abinda kuka yi
ku fada min,badai daurin aure bane zanje inshaallah sauran kuma ba ruwana.

Kawu Nafiu yayi hamdala yace a ransa mun tsallake bulalai,dama su kansu tsoron
bulalar da suka ji yasa suka jajir ce din,kuma ba wata bulala da za a musu wayo su
Sahil suka musu tunda sunga ana jin tsoron su,Kawu Nafiu Sohail ya kira a waya ya
fada masa yanda suka yi da Daddy,Sohail yace ko daurin auren ma ba sai yazo ba amma
da na su Adnan ne ai da tuni shi zai raba IV, idan cikin shegenmu yayi ya fada mana
ai ba sai ya zauna yana haka ba,mene dan ya fadi gaskiya mun san sharrin shedan ne.

To mudai gobe zamuje dangin matar a turo mana addreshi,Maheera wajen walliyyan
nata ma suna Suleja nan zasu zo an tura musu Address.

Washe gari kuwa da rana suka isa,gidan Waliyin Maheera me kyau katon gida me
gate babu batun wahala a gidan,su Kawu Nafiu palo aka kaisu me kyau aka cika musu
gabansu da kayan ci sha komai cikin girma aka yi musu Sahil a nan yazo ya same su
harda shan babbar riga da hula kamar wani ango ka rantse yaune bikin ya sha farar
shadda,komai cif cif shi,Kawu suka boye dariyarsu yanda suka ga Sahil ya nutsu abu
kalau kamar wani cikakke.

Kawu da waliyan Maheera suma su uku suka zauna wanda waliyan Maheera sun san
komai akan su Sohail mahaifiyar Maheera bata boye musu ba,sabo da a magana ta aure
ba wasa da boye boye, amma tunda yarinya tana so kuma ba wani aibu bane da su dangi
sun bincika kuma dai yanzu in kana da kudi an gama kawai,su ma dai sun yiwa su kawu
cikakken bayanin asalinsu da komai basu boye ba.

Su Kawu Nafiu sunyi naam mutanen kirki ne,nan dai suka gama maganganunsu aka
yanke kudin aure da komai komai nan take Sahil ya biya ta accnt,sadaki kadai dubu
dari biyu ga sauran kudade shima daban duk na wani bidia ya biya.
Rana kuma ance wata uku amma Sahil yace mu mun shirya amarya ma ba abinda za a
kawota da shi sai kayan sawa kawai sati biyu,Kawu yace Lefen fa? Sahil yace to ai
matar Ogan Sohail an bata kudin komai kila ma ta hada,Kawu Nafiu yayi mamaki a
ransa yace lallai yaran nan da gaske suke yi ashe suna da tunani haka ganewa ne ba
ayi,har sun san su hada lefe a boye.
Kawu Tukur ma mamaki ya gama kama shi.

Sahil sai da aka gama komai lafiya zasu tafi yace ina da magana,suka ce
bismillah, angon Sohail ko an kai amaryar munce ko dakinta bazai shiga ba sai an
daura nawa tukun yanzu abotar su zasu ci gaba da yi a gidan kawai, jirana zasu yi.
Waliyan Allah yasa sun san zancen Su Kawu Nafiu kunya ta kamasu suka ce kai muje
da Allah,Sahil yace ai gaskiya ce kar a ganta bata da ciki a zarge ta ace juya ce,
bazai yi komai ba sai nima nayi,Waliyan Maheera suka yi dariya dai suka raka su
suka shiga motar su,
Sahil ya kaisu tasha suka shiga mota ya sake biyan kudin mota ya musu godiya,yace
kun tsallake rijiya da baya amma da kun sha bulalai,dariya suka yi sosai ya juya ya
shiga mota ya ja ya tafi.

Direct gidan su Adnan ya wuce sun kulle gidan Sohail ance na Amarya ne baza a
kara shiga ba,Komai har kujeru an rufe su da ledoji,Aisha matar Alhaji Saminu taje
ta sake ganin gidan duk abinda babu na mace da ake bukata ta saka Sohail ya zuba ta
sake canja musu tsarin gidan gaba daya,komai da ita ake shawara,itama tana kokari
tana dorasu a hanya sosai kamar yayarsu,kuma Alhaji Saminu ne ya hada su ya kaisu
har gidansa yace ko mene suzo gidansa ga matarsa su dinga shawara da ita musamman a
maganar auren.
Ga Aisha yar gayu ce da son gayu ga shishigin tsiya ka rantse yayarsu ce uwa daya
uba daya.
Itama Maheera har ta san Aisha sosai.

Tunda aka saka bikin Amarya ta fara gyaran jikinta Komai Aunty Aisha tace a bayar
amarya tayi ta dage sai gyara amarya akeyi da kudin Sohail,Maheera Amarya ita murna
take in ta tuna Sohail zata aura duk haukar nan ko a jikinta.
Kullum gwada number Islaha take ko zata same ta amma shuru bata shiga sam.

Free page 400 1&2

0175487861
Asmau Garba Muhammad
Gtbank

*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason
juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene
matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin
taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma
babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko
kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi
glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da
humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu
karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-
muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku
da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban
burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza.
Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka
tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin
kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da
kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*

AsmaBaffa
08061929616
[7/17, 3:18 PM] Asmabaffa: 🪸MUMMUNAR DABI'A 🪸

36-40

Official

By
AsmaBaffa
SADAUKARWA NE GA 'YATA TASNIM

Page naki ne
Ummu Lateefa

*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason
juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene
matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin
taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma
babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko
kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi
glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da
humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu
karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-
muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku
da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban
burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza.
Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka
tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin
kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da
kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*

MASU AUDIO BAN YARDA A SATAR MIN NOVEL BA IZINI NA BA

Maheera tana gwada kiran Islaha tace amma Islaha zuciyar tata tayi yawa da
nice bazan iya bama sam, karfin hali barawo da Sallama daga yar magana shike nan
wannan wacce irin zuciya ce haka,kin koma gidan ku ma ki bude wayar mana,sai taurin
kai haba,mutane kin san ba wasu lafiyayyu bane ki dauki zuciya da su.
Kiran Sohail ne ya shigo wayarta a nutse ta daga harda gyara murya tace Ango,Sohail
yana Office a zaune ya kasa aikin komai akan zaiyi aure,shi ba ma wajen wahala yake
ba amma dan signing da sauransu na shige da ficen kaya sam ya kasa,Ya aiki? Maheera
ta tambaya,ba yi nake ba da me zanji aiki sun min yawa ni,nauyi ya min yawa gaki ga
Office,a baya kuwa ba ruwana sai naga dama nake kiranki,yanzu kuwa idan ban kira ba
haka kike cewa na daina son ki,gashi ance za a daura aure ni na rasa wanne zanyi
wanne zan bari daga ciki,ga dinki an kai,Aunty tace na koma wai an gama lefe gida
nawa ake so na kasu.

Maheera dariya ta dinga yi tace dan dan wannan shine ya maka yawa? Yace ana
cikin haka Adnan ya kirani wai kudina basu kai na rike mace ba,Daddy ya fada musu
zanyi aure wai ni bana shawara da su me yasa ba a fada musu ba,anbi an dameni ni.

Murmushi tayi tace to Sohail idan munyi aure baka fada min aikin da zaka dinga
tayani ba,kasan maza suna taya matansu aiki,Ashe zaki fitsarin man kuli,na zauna
ina tayaki aiki duk kudina sun kare a kanki ko fili ban siya ba,ki kyale ni ma naji
da accnt dina da yake rarakewa gaba daya kin cinye min kudi tunda nace ina sonki
shike nan kullum accnt dina kasa yake yi,dama ba wani kudi ne da ni ba,sai na gama
wannan, sannan tun yanzu har kin kawo zancen aikin gida,mijin tace kike so na
koma,in kashe miki kudi inje Office in dawo in miki aiki lallai kina da aiki,nifa
baki isa ki juya ni ba, ki sani ma da saninki karki soma, zamu yi mummunan fada,kin
ma rainani.

Maheera tace daya fa na fada sai faman zuba kake yi daga nace ka tayani sunna
ce fa,Maheera gyaran jiki ake mata ana ta dirje mata fata,da zafi ta furta Sohail
yana ji a waya yace Allah ya kara sai da nace karki yi na taba gani an yiwa mama
Asmau bata ji dadi ba kin tafi za ayi miki,Maheera tace wai duk ba kai ake yiwa
ba,da sauri yace a'a a'a ba ruwana, kike yiwa kanki dai.

Ba abinda zai amfane da shi kin san dai sai Sahil yayi aure koma mene sai
ayi,Maheera tace jiransa za ayi kenan? Sosai ma,kasa tayi da murya ni kenan bazan
samu ciki na haihu ba,auro ki nayi ki haihu dama? ni sabo da tunaninki da nakeyi
yasa zan ajiye ki a gidana kinga na huta tunda kullum zan ganki,dariya tayi tace
Allah dai ya kawoni duk wannan tsarin naku sai na rusa shi .

Mu fa taurin kai ne da mu ki kyale mu kawai inda kika ganmu,Kamar Abun arziki ya


kira sunanta "Maheera"amsawa tayi na'am,Allah ya miki iyayi da shishigi sai kace
Aunty Aisha,ki ta tsara zance ke ga masaniya me sani,shi yasa Sahil yace Islaha ita
yar oya oya ce ke kuwa in kika dinga tsara magana kice wannan kice wancen ke dole
sai kin dora mutum a hanya ga shegen iyayi,magana ma wani a hankali kina fari
watarana kamar na mareki,dariya Maheera tayi duk yangar shi ake yiwa amma wai ba a
birge shi ba,takaici ya kama Maheera ta tuno dogon lokacin da ta dauka tana matsawa
kanta sai ta koyi dan iyayin nan da fari da sauransu na wayewa take ta faman yi
ashe shi bai ma san ana yi ba haushi yake ji.

Tace na daina daga yau Inshaallah zan dawo yanda nake zaka ga iskanci tunda
haka kace har nunawa nake ina kara zama ta gari dan a soni ashe shi ba ruwansa ta
furta a ranta,a fili tace
Za ayi dinner? Ta furta ya maganar Dinner? Sai bikin Sahil,komai ni ba a min ba
sai bikin Sahil bana so,gaba ta kaini cewar Sohail ya kashe wayarsa.

Sahil ne ya shigo Office din yace me kake yi haka ne kazo mu tafi,Sohail yace
soyayya na sha ta kashe min jiki,Sahil yace uhm gori zaka min sabo da ni bana yi?
Ni nace budurwarka ta bata,Sahil yace bata bace ba Inshaallah zata dawo,Channel din
da Sohail ya nacewa ta wa'azi ita yake saurara,Malam yana wa'azi yace matarka kuyi
wanka tare ka cudeta ta cudeka,Sahil yace ga bangaren ku nan masu aure,Sohail yace
ashe za a ayita ni na tsaya Maheera taga tsaraici na ai na shiga uku kuma baza ta
sake jin magana ta ba,dama kana ji yanda take min wasu tambayoyi na raini tace
wannan tace waccen,Sahil yace Allah kuwa yarinya iyayi haka,aini kawai in tana
magana zuba mata ido nake sai ka lalace a kallonta ko ina na fuskarta sai ta motsa
shi ,Sohail yace ashe kaima ka gani ko banyi niyya ba sai na bata kudi,Sahil yace
ahh ko ni na bada kudi irin wannan magana haka me style.

Sohail yace kai kuwa Islaha ce kullum a shirin ko ta kwana take kana kallonta
kasan bata da mutunci,Sahil yace 'ya'yana sun shiga uku na tausaya musu zasu ci
duka nidai nafi karfinta sai dai ta yiwa yaranta,Aunty ma data riketa bata isa dani
ba,ni zasu ce zasu kai yawon shakatawa,a cirani ban samo komai ba sai mata da suka
rainani ba abinda na tsinta,da wasa bana son jin sunan lagos a rayuwata.
Sohail tv ya kashe yace muje a karbo dinkunan biki,Aunty Aisha ta sa munyi dinki
da yawan gaske,Sahil yace sai kace mijinta dinkawa yake,ta damu mutane sutura itace
mutum sutura itace mutun amma ta bar mijinta da dinkin buba falau a gari,dariya
suka yi Sohail yace oga ai har Boubou ta mata ma zai iya sawa yaci kai ai.

Da dinkunan biki suka koma gida,Ibrahim da Adnan sai bacin rai suke yi wai
Sohail da suka fi rainawa shine ya samu aiki har ma zai riga Ibrahim Aure,Ibrahim
yace da ace ina da hali wallahi sai na hana auren nan,takaici wai kamar Sohail zai
auri Maheera guda wannan ai matar manya ce,Adnan yace ko wajen bazan je ba bare
nace Allah sanya Alkhairi,Amal ma baza tazo ba babu me tayasu biki gashi basu da
uwa ba dangin uwa,dangin Uba kuma tsoron tonon sililinsu suke yi ba me zuwa,Ibrahim
yace duk na buga musu waya nace kar wanda yazo ba a gayyar kowa,sai Kawu Nafiu da
Tukur naji su sunce da su za a daura dole,har kudi na tura musu cin hanci kar su zo
amma sunce sai sunzo.
Adnan yace nima na kira kawu Tukur nace kar suzo yace Twins ne suka tsorata su
sunce bulalai zasu sha idan basu zo anyi komai da su ba wai hanyar lafiya a bita da
shekara.
Amal ma tunda taji biki taji ance wai Sohail ne da gida guda ga motaa hankalinta
ya tashi,gashi mijinta ya hanata zuwa Abuja sunyi fada akan ya biyawa kishiyarta
makka a boye yanda Sahil yace.

Biki yana ta matsowa su Sohail sunyi gayya sosai duk mutanen su na kano da
abokai tunda a can suka taso an gayyace su basu manta ba,wasu ta waya wasu ta
Online wasu da katin Iv, Maheera ranar Friday zata yi yini da kamu shike nan,ranar
asabar a daura aure a kai Amarya.

Duk wanda yaga Iv din su Sohail sai yayi dariya sabo da iyalan Marigayi Alhaji
Ali aka saka,Late aka saka a jiki akan baya musu komai suka ce a saka Late
kawai,Shi kanshi Daddy din ko iv din ma basu tura masa ba a duniya ya gani.

Ya kira Sahil yace da raina da lafiyata ku kashe ni ku saka min Late dan ubanku,
Sahil yace ayi hakuri kuskuren computer ne, computer ce tayi karya,da aka je bugawa
ne anyi anyi ta saka kana raye kai rayayye ne taki yarda tace marigayi ne ya za
muyi ,Adnan ai nasu yasa kana raye ga Ibrahim ma nan gaba zai sa kana raye mene
abin damuwa to,ga su Adnan mu ai a barmu a mahaukatan mu,Daddy yace magana zaka
fada min? a'a ni na isa mufa bamu ce sai kazo daurin aurenmu ba kayi zamanka ka
zuba yawunka a can cikin shara ko ba yawunka za a daura,ba dole bama a sa maka Late
tunda an rasa inda ka nufa yaranka ne mu ba yaranka bane tsintar mu kayi oho,cikin
shege ne mu oho,idan ka fadi gaskiya waye zai tsire ka?.
Kai dan Allah rufe min baki shashashu mahaukatan banza ya ja tsaki ya kashe
wayarsa.

Twins dai gashi suna ta yada Iv duniya ta san Alhaji Ali sosai,duk wanda ya gani
ya dinga mamaki yaushe ya mutu,dama ya mutu ashe ,sai kiransa akeyi a waya ana
tambaya sai aji yana raye.
Bangaren Amarya sunyi anko kawaye komai an shirya shi Sohail ne ya kama musu
event center da kudin Alhaji Saminu da ya bashi gudunmuwa.
Alhaji Saminu da abokinsa sai Sahil su suka kai lefen Sohail akwati guda takwas
komai me kyau aka zuba,Maheera sai murna take yi bata zaci haka ba.
Sai kiran kawaye take a waya suna tururuwar kallo ana ta yabawa, a cikin kawaye
wata ana ce mata Saddiqa ta faki ido ta sace sarka me kyau,dama wasu kawayen da
biyu suke zuwa.

Sun fito zasu bar gidan sarka tana jakar Saddiqa Maheera ta rako su sai ga
Sahil yazo,Saddiqa ya kalla yace mayar mana da Sarka dan ubanki dake za'a hada a
aura da zaki sace mana sarka,Saddiqa tsoro ya kamata da ace a cikin kawaye ne sai
ta rantse ta ganta sanda ta dauka,yace ki zazzage jakarta ki karbi sarka idan ta
tafi da sarkar nan ke kinsani,ya fadawa Maheera.

Maheera ta fisge jakar Saddiqa ta zazzage sai ga sarkar me kyau a cikin


gidanta,mata suka fara sallallami da cakaki,kunya ta lullube saddiqa ta kwashe
jakarta da kayan ciki ta fice da gudu tana dana sani.
Maheera ya mikawa kaya a leda yace gashi nan daga wannan karki sake cewa a karbo
miki dinki sabo da ni kike jawowa yana cewa na kawo miki,Maheera dariya tayi tace
to mene,ai ke kika ziga shi dama, ya shiga mota ya tafi.
Maheera tana ta shagalinta kamar zata kai kanta gidan duk da tasan matsalar da
take gabanta ba ruwanta soyayya ta rufe mata ido,Mama ce ta kalleta ta hana kanta
sakewa sai faman shagali take shiryawa,ana cewa Amarya sai fara'a da murmushi,duk
inda ta zauna sai ta bada labarin halayen Sohail masu kyau.

Kawayenta ne mutum biyu suka zo wajenta Maheera tana tsakiyar su daya tace
Amarya,Maheera tace na'am wlh idan kuna fada sai naga kamar mafarki,har cewa nake
zanyi aure kuwa a duniya anya,to gashi cikin lokaci kadan Allah ya kawo har lokacin
ma na nema ya kure mu,kawar tace ai haka ikon Allah yake.
Maheera tace hmm ai kamar wasa muka fara kawance ba sai soyayya ba,muka fara love
gashi ya iya kula da mace baya son raini kuma amma akwai caring ku kunga yanda yake
min,ga kishi ban isa na dinga fita anyhow ba,Kawaye suba ta jin labari harda cewa
wayyo ke kama kin tsallake.

Maheera ta durawa wata kawarta ashar yar burar...Walida har magana take fada min
akan zata yi aure wai ta barmu da zaman kan layi kiji shegiya,tazo taga mijina wlh
kamar bature,bari ku ganshi dan dai kawai na yarda da ku zan nuna muku shi,ta jawo
wayarta ta nuna musu Sohail tace kalle shi,yan matan suka saki shewa gaskiya kin
dace,Maheera har da wani gyara baki tace in fada muku badan yana Office ba da yanzu
zance yazo ku gaisa,to a isar mana da gaisuwa cewar dayar kawar.

Ana zuwa ganin lefe haka Maheera take zakewa tana nunawa,wasu mata dangi sunzo
Juwairiyya tana nuna musu Maheera cewa take baki bude musu akwatin takalman ba,a
nuna musu na kayan baccin,suna daga kayan tana cewa wannan fa material ne Aunty
Sa'a amma a haka kamar shadda,Mama tana jinta har ta gaji da halin Maheera rashin
kunyar da take,idan kuwa Sohail ya kira waya ko su waye a gaban su zata ce Sweet ne
miko min wayar ta tashi da gudu ta shige daki.

Mutanen suna tafiya Mama tace Maheera abinda kike yi ya isheni,a haka a ganki
shuru shuru kamar kin shiryu kin nutsu amma sai rashin kunya kike yi,a kanki aka
fara aure yau ni naji tsiya, ki taka a sannu wlh angon nan naki kin san irinsa amma
ke ko a jikinki naga ma kunyar ma kin daina a gaban kowa nunawa kike murna kike yi
zaki aure ki huta.

Maheera tace ba abinda zai faru sai Alkhairi Mama ki dinga addua fata na gari
lamiri,Mama tace hmm kina dai ji yace sai ya jira dan uwansa babu abinda zai shiga
tsakani in banda ba hankali yaushe za ayi haka,Maheera tace nifa zan iya rayuwata
haka ba komai ba sai anyi komai ba dama ni ban san komai ba me zai dameni zan iya
kare rayuwata a haka,dariya kawai Mama tayi tace baza ki gane bane bakya hangen
nesa.
Maheera tace magana dai ta kare tunda aure ba fashi inshaallah kawai kiyi addua
yafi,to shike nan Allah ya sa alkhairi.

Juwairiyya ce ta shugo gidan da wasu dinkunan tace Aunty yaushe za ayi lalle ne?
Maheera tace sai ana gobe biki kar ya goge da wuri kafin a kaini ya goge,yaya gidan
nawa kunje kun gano? Juwairiyya tace mun gano wlh ya hadu komai akwai munje mun
kara gyara ko ina an shirya duk wani kayan kyale kyale ke baki gani ba,Maheera tace
mashaallah,Mama tana ji tace nidai na shiga uku haka kika koma? So hauka ne
Maheera?Maheera tace kowa fa da zamaninsa Umma,ni dama dan na samu miji na kara
zama ta gari,Mama ta dora hannu a kai.

Ana gobe daurin aure Maheera ansha gyaran gashi anci lalle gaba daya ta canja
tayi kyau sai kamshi take,fatarta in banda sheki ba abinda take yi,baki kullum a
washe ana jin dadi za a auri Sohail.
Ranar kuma tayi yininta da kamu ya kayatar yayi kyau sosai anci an sha anyi liki
iya mata amma.

Washe gari ranar daurin aure tun 4am Sohail ya farka kaya a goge amma ya wani
jona dutsen guga ya sake goge musu kaya har Sahil,ga abokansu sunyi kara da yawa
sun zo har mudassir me fada da matarsa shima ya shirya duk da shi a gari yake.
Su Adnan sabo da bakin ciki suka sallami me aiki Madam Oge suka ce taje gida sai
bayan biki dan kar ma ta dafawa abokan da suka zo daga wasu wuraren abinci.

Suna kallo ma daga gidan Alhaji Saminu ake kawowa iri iri safe rana dare komai
akwai kaci ka sha,ba a taba musu abinci ko daya ba.
Busy suka zama dan kar ma su shiga lamarin bikin kullum basa zama a gida.

Ranar daurin aure Ango ya riga kowa shiryawa suna ta tsokanarsa suna masa
tsiya,Farar shadda suka saka shi da Sahil ba banbanci,da babbar riga da hula kamar
a jikinsu a dinka,suma taci gyara a saka yar hula a goshi.
Turare ya fesa yafi kala nawa a jikinsa,Sahil yace Allah sarki Me Tallaja ana ta
ci da rabonta.
Kawu Nafiu,da Kawu Tukur sai Daddy da abokansa mutum biyu rak sune suka zo a dangi.

Daddy ya kira Adnan a waya yace ya kamata suje,suna ta jin haushi suka shirya suka
je haka,lokacin da suka je ma an rigada an daura auren 11:30am.

Ana daurawa Daddy ya tashi suka tafi yana cewa yana da meeting,Sohail ya kalli
Sahil yace kaga bai tambayi ya aikin da nake ba,a ina nake yi,wanne iri ne ko a
jikinsa,sannan matar ma ba ruwansa bai san wace ba,Sahil yace kyale shi ya tafi ba
komai.

Abokai ne suka yi kara sosai duk abinda akeyi na biki a al'ada sunyi abinsu ba
ruwansu,na nesa ne suka koma da wuri sai iya wanda suke gari su dama ba wasu abokan
ne da su da yawa ba.
Amarya ta sha leshi me kyau pink and black,irin kyan da tayi ba a magana,sai da
za ayi pics ango yace bazai yi ba,da kyar abokai suka sashi dole ya shiga aka musu
da Amarya,sai cuno baki yake wai dole aka masa.

Su mudassir sune suka tattara kayan ango suka kai gidan Amarya,ango yace kafata
kafar Sahil yazo mu tafi, 3 bedrooms ne da dakinsa,Sahil yace zan dawo ai daga
baya,Sohail yaki yarda dole aka kai kayan Sahil can dakinsa idan ba haka ba amarya
baza taga ango ba.

Mudassir ne yace da Sahil yayi wayo kar ya kwana a gidan ya barsu sai nan da
satikai sai ya koma,Sahil yace to kamar ya gane suka koya masa yanda zai fice da
dare ya dawo gidan su Adnan ya dinga kwana,yace to.

Zuwa yamma Maheera dangin su maza suka kirata suka mata nasiha sosai akan zaman
aure,Mama ma tayi nata nasihar tace na sanki da son kai Maheera nasan hali karki je
ki nuna son kanki,Maheera tace Allah bazan yi ba na gane gaskiya,to shike nan Allah
yasa,bayan sun gama Nasiha akace ta shirya za a kaita angwaye zasu zo daukan
Amarya.

Sai lokacin kuma ta fara kuka,dariya ma ta basu,angon kansa tun biki saura
kwana uku basa waya sai a daurin aure suka hadu,wanka tayi ta canja kaya cikin wani
material dark blue ta sha kyau sosai kamar wata yar India,kayanta da lefe komai an
tattara an kai can gidanta,Maheera ta kira kanwarta gefe tace an kai min wannan
takardun nawa gidana iceko bazan zo ganin gida da wuri ba sai nayi kiba na canja,
Juwairiyya tace ke kama Aunty wannan son da kike masa yafi nasa ai,tace daga na
fadi gaskiya sai tayi shuru.
Juwairiyya sune a kan gaba kanwar Amarya,tuni sun shige mota,Motar Alhaji Saminu
itace za a sa amarya ciki.
Bayan Amarya ta shirya dattijai suka fito da ita kanta a lullube aka sata a
mota,motoci sun kai goma aka tafi kai Amarya Alhaji Saminu ya bada wasu motocin da
driver guda hudu,komai anyi cikin aminci da rufin asiri.
Bayan an kai Amarya gidanta kowa sai yabawa yake ana ta yi mata murna,Aunty
Aisha itace tayi ruwa tayi tsaki komai sai da aka aiwatar na Al'ada,Amarya aka bari
daga ita sai wata kawarta guda daya Mardiyya,itama bata dade ba saurayinta yazo ya
dauketa ya maidata gida aka bar Amarya ita kadai a saman makeken bed ya sha gyara.

Shima bangaren ango abokan duk sun tafi saura Mudassir kawai,shine ya siyo kaji
da kayan makulashe,yace to ango taso mu tafi, Sahil yace yanzu kaimu za ayi shike
nan gida kuma,Mudassir yayi dariya,Sohail yace Shike nan kuma har abada bazan dawo
nan da zama ba rayuwa kenan,yau Allah yayi tashin mu,Mudassir yace dan Allah muje
ku dai Allah ya shirye ku, haka suka tafi gidan Amarya harda Sahil.

Amarya tana jin mota tace Alhmdllh dama tsoro nake ji,tace oh ina tare da
Aljani da kansa mene abin tsoro kuma,Sohail ne a gaba yana shiga yace ni ba sai an
nuna min gidana ba,ni da gidana ace dole sai an rakani ai nasan dakin ku
kyakeni,Sahil ga room dinka Mudassir a gaida iyali,ya karbi ledojin ya mikawa Sahil
nasa yace karbi, Mudassir ya dinga dariya yace butulci zaka min? dariya yayi yace
to kaine da naci ai, Mudassir yace to sai da safe,mun gode sosai cewar Sahil ya
raka Mudassir har mota, Mudassir yace shiga mota mu tafi na saukeka a gidan su
Adnan yanda muka tsara,Sahil yace tab ga gidanmu mun dawo kace na koma bazan koma
ba, soyayya fa zaka hana su yi,Sahil yace ba abinda za ayi sai an jira ni,Mudassir
ya buga ya buga yaki yarda,haka ya tafi ya kulle musu gidan ya wuce room
dinsa,wanka yayi yaci kayan dadinsa yana kallon film a dakinsa har yayi bacci.

Ango kuwa Amarya na zaune ya shiga da sallama,murmushi tayi ta cikin


mayafi,hannu yasa ya fyalle mayafin yace mene haka kin sanni na sanki ki zauna kina
boye fuska.
Har ya juya zai shiga toilet ya fasa ya dawo ya leka fuskarta yace naga kamar
kinyi kuka,Maheera tace uhm rabuwa da gida wasa ne,nan ba wani gidan kika dawo ba?
murmushi tayi me kyau zata yi fari yace dakata karki fara na gaji.

Dariya tayi tana kallo ya bude kayansa ya dakko wasu kayan baccinsa ruwan zuma
sababbi,ya dauki man shafawarsa da turare da komai ya shige toilet,Maheera tayi
murmushi tace idan ka shirya a gabana menene to,kofa ya rufe amma bai sa key ba,sai
da yayi wankansa da brush ya dade yana faman shiryawa sai da ya shafa mai yayi
komai har gashinsa ya gyara yana shafa turaren kaya Maheera ta gaji ta bude toilet
din,da sauri ya juyo yace Allah ya fiki na shirya to,dariya tayi tace to me kake yi
haka ne? Kin takura min daga aurenki kin dameni fa.

Kayi Alwala? yace yanzu zanyi ya juya baya,da tsokana Maheera ta rungume
shi,Laaaaaa ya furta kamar an masa wani abu ya tsaya a haka kanta ta kwantar a
bayansa tare da furta wayyo ni duniya dadi,Ido ya zaro waje yace ke Maheera uwaki
ni na hadu da yar duniya wlh dama Sahil yace zaki karya alkawari,hannu yasa ya
banbareta daga jikinsa da masifa yace ki daina bana so ni.

Murmushi tayi ta ture shi tace matsa nayi alwala,Alwala tayi ta bishi suka
fito,Sallah ya ja su tace ashe ka sani,kwafa ya ja yace me kika maida ni ne? Sallah
ya tayar suka yi ya musu addua yanda ake yi,suna idarwa ta rike hannunsa kwacewa
yayi ya harareta,dariya tayi tsokanarsa take ta faman yi.

Sai da ta shiga wanka ya sauke ajiyar zuciya yace an takura min ni wayyo Allah
aure wahala yanzu na gane da maza suke ta fada halin mata ba kyau,shi yasa maza
kowa kuka yake da aure wahala na rasa ganewa sai yau.

Daure da guntun towel ta fito ya saki baki yana kallonta Maheera tana murna ta
tafi da Imaninsa sai ji tayi ya furta wai ke haka kike dama aka baniva dukunkune?
Ashe lukuta ce ke amma a haka kamar siririya ni siririya nake so,Maheera bata
kulashi taci gaba da shirinta,ya zauna kuma sai kallonta yake kamar zai cinye ta
har ta shirya ta dauko wata gantalalliyar rigar bacci da Aunty Aisha ta bata kalar
kayansa na bacci ta zabo sharara da ita komai a waje da siririn pant dinta gata
guntuwa rigar,Sohail yana gani ta saka abarta ta zare Towel din ya juya baya da
sauri tare da furta na jawa kaina sai da Daddy yace kar nayi auren nan na kafe sai
nayi gashi na hadu da gamo na.
Maheera tana jinsa tana boye dariyarta,inda yake zaune a gefen bed ta koma gabansa
ta tsaya inda ya juya baya,sake juyawa yayi ya kalli gefe can,saman cinyarsa ta
zauna ya dinga zamewa kamar tsutsa yana zukewa,gashinsa ya sosa ya girgiza kansa
kamar haukar ta motsa,kugunta ya rike ya dagata yace wai ke bakya zama kawai,dariya
tayi zata sake taba shi yace ga abinci zo kici.

Zama tayi tace kai fa? Yace na koshi,tace gwara ma kazo kaci tun kafin nazo na
kwanta a jikinka kuma a haka zan baka da hannuna,da sauri ya dawo ya zauna,amma
lokacin da ka gasa min kafa me yasa ka tabani muka yi kokawa? Sannan watarana da
muka yi party Islaha har abinci ta baka a baki kuma kaci,Sohail yace ni din?
Yaushe? Shi sam ya rantse ba shine ba,duk sun manta ma anyi wani party har Sahil
din babu me iya tunawa.

Maheera haka suka ci abincin tare suka koshi ta tattara komai zata fita yace
kin manta saka hijab karki ga Sahil a palo yana kallo,tace kace kai a dukunkune aka
baka baka damu ba ina ruwanka da wani kuma,fuska ya bata yace kin rainani ko? Ni na
isa ta dawo ta saka ta fita,tana dawowa ta samu ya jera pillows a tsakiya kar ma ta
taba shi wai,yace kowa ya kwanta a barinsa,tace to ta kashe light tayi kwanciyarta
a bangare daya shima haka,yace to baza kiyi addua ba? Ai yi nake,yace okay ki hada
dani ai nayi aure ba sai nayi ba tunda cewa aka yi ki kula dani, ya juya yayi
kwanciyarsa wai tayi da shi kawai.

Maheera a ranta tace na shiga uku ni Maheera wannan kaddara wacce iri ce,da haka
tayi bacci itama dama su sarakan bacci ne har ya lula,duk ya har gitsa pillon da ya
jera su babu ko daya duk sun fado kasa.

Farkawa Maheera tayi taga duk pillows din sun watse kasa,murmushi tayi ta koma
jikinsa tana dariya a boye hannunsa ta jawo ta dora a kugunta ta matsa jikinsa ta
manne ta rungume shi bai sani ba sai da asuba tayi ya farka a hankali ya bude
idonsa,tunawa yayi ai Maheera ce yayi aure murmushi yayi yanzu kuma"
yana kare mata kallo,kwanciyarta ta gyara sosai,hannunsa daya ya mika yana daga
kwance ya kunna light haske ya bayyana.

Wuyan rigar Maheera ya zazzage ana hango Boobs a waje chakare chakare,Sohail
baki ya rufe da tafin hannu daya,yaci gaba da kallonsu da baki ya nuna su yace uhm
shi yasa take wani kin saka hijab yau na gansu Allah ya toni asirinta bata da
katabus,idonsa ya lumshe yace kuci gaba da kallona ina jin dadina ya koma
baccinsa,yana komawa baccin aka kwalla kiran sallah ya sake farkawa yace yau makara
zanyi Maheera tana nan.
Yanzu kuma yace na gode Mama zan dawo gaisuwar surukai ko dan wannan runguma da
kika tarbiyyantar da yarki a kai ga nacin jikina ta makale min,tarbiyyarki tayi
Mama,ban kashe kudina a banza ba.

Maheera ce ta farka a hankali ta yunkura zata tashi taji ya riketa gam yace
makara zamu yi yau,tana murza ido tace da hankalin mu da sanin mu ai ba a wasa da
sallah tashi muyi sallah,Sohail yace bazanyi ba ni yanzu makara zanyi yau,ta matsa
masa yace naji zanyi amma bazan je masallaci ba ni wlh,tace ae tashi muje,harararta
yayi ya mika mata hannu yace dagani jawo shi tayi ya tashi, yace karfa kice kece
kika tashe ni ganin dama nayi baki isa kin iya dagani ba.

Toilet din ya shige ya kulle,ta zauna ta jirashi sai da yayi wanka da brush ya
fito,Maheera tace munfa makara ka zauna wanka,yace wankan tsarki nayi ance duk
wanda yayi aure sai yayi wankan tsarki kullum,Dariya zata karasa Maheera ta shige
toilet kawai tace yau nidai na shiga uku a haka zan rayu.

Kafin ta fito yayi sallah yana Azkhar dinsa dake yaga dama,tace to matsa zanyi
Sallah ya tashi ya bata waje ta saka kaya ta gabatar da Sallah tayiwa Twins addua
sosai sannan ta cire kayanta sai na bacci ta kwanta,kwanciya yayi a samanta ihu ta
saki ya dagata da sauri yana dariya yace ba haka kike so ba.

A gefenta ya kwanta yana kallonta yace tsaya na miki wani abu karki fadawa
Sahil zai ce na karya Alkawari,Maheera tayi murmushi tace kace kar a taba ka kai
baka so nice yar iska shi yasa na kyaleka,uhm uhm karki kyaleni please yace.

Jikinsa ya dawo da ita ta lafe yace sai kace mage wai ke zan fasa ma,na daina
to cewar Maheera,carbin hannunsa ya ajiye a nutse kamar wanda yasan kan lamari ya
hade fuskar su waje daya hancinsu yana gugan na juna,Maheera idanuwa ta lumshe
tana jiran tsammani fuskarsa ya janye har ya matsa ya kyaleta tana a haka kamar
gunki ido a lumshe tana ta jira,sai data dawo hayyacinta taga baya ma
jikinta,kunyar kanta taji ta shiga sosa gashi tace a ranta me yake damuna ne zai
rainani ma,dan guntun tsaki ta ja tare da kwanciya itama.

Sai wurin 9am ta tashi jin ana buga kofa, Shima Sohail farkawa yayi jin karar
door bell,zata mike yace kwanta bari naje irin jarumin nan,yana fitowa ya bude kofa
yaga driver Aunty Aisha ta aiko shi da lafiyayyen abinci,karba yayi suka gaisa da
driver yace mun gode ya rufe kofar.
Dakin Sahil ya shiga ya samu Sahil yana baccin gajiya ya ja masa kofar ya fito
ya ajiye abincin a dining ya koma bedroom ya samu Maheera ta shiga wanka.

Islaha kuwa tana komawa Lagos can gidan wata hajiya Kulu uwar tuwo taje itace
take yiwa 'yan mata hanyar aiki a gidan masu kudi ko a wajen yan tuwo tuwo,Hajiya
Kulu tana ganinta tace Islaha yau kece a gidan nawa daga ina haka na ganki da uban
kaya? Islaha tace wlh Hajiya Kulu korata Aunty tayi kin sai dai halinta da abinda
suke yi,Hajiya kulu tace bata kyauta ba wlh wasu ke bata wasu shi yasa ake ganin
duk wanda yayi sana'ar tuwo tuwo a banza ake kallon mutum kawai dan duniya ne.

Yanzu ya dangin naku? Islaha ta bata labarin komai tun daga korar da Aunty tayi
mata har da haduwarta da Sahil da barinta a gidan su,Hajiya Kulu ta kalli Islaha
yanda take sharbar kuka wai dan a tausaya mata tana cewa kowa yaki ya tausaya min,
tace na sha wuya tana shesheka,Hajiya Kulu tace to ai ke kuruciya ce ta muku yawa
har su Sahil din kika ce sunansa ko? su in banda shirme ai wani za a samu ya raka
ki gidanku,ke kuma daga sunyi magana sai ki bar gida cikin dare suma suna da
gaskiyar su bai kamata ba,Yanzu to shi Sahil din sonki yake ko kece kike son sa?

Islaha tana hawaye tace wlh ina sonsa,mutumin nan inda kisan ya min asiri ni ba
kula samari nake ba amma ina ganinsa naji zuciyata ta buga,nidai sai sonsa nake yi
ba ji ba gani,nayi adduar nayi adduar sai naji na kara sonsa,nifa ko sunansa kika
fada dadi nake ji, idan na hadu da wanda ya sanshi sai naji ina sonsa,Ibrahim
yayansa da yake zuwa sabo da son Sahil sai naji dadi idan na gashi sabo da naga dan
uwan Sahil,zuciyata sai azalzalata take na koma can wajensa,amma ina dagewa ina
daurewa wlh idan na gaji mutunci na zan zubar na koma wajensa.

Hajiya Kulu tayi dariya kamar ba gobe tace dan Allah karki zubar da ajinki
mutum ya kore ki haba Islaha,Islaha tana goge hawaye tace wlh idan na gaji zubar da
ajina zanyi bazan iya da wannan kadadarrariyar soyayya ba,Aljanunsa ne suka shige
ni suka cuce ni suka sa nake sonsa,har mafarkinsa nake yi munyi aure, ina gajiya
zan barar da mutunci na.

Hajiya Kulu tace to Islaha yanzu akan namiji kike wannan uban kuka haka? Mene ma
bazan yi ba namiji halittar Allah nifa zan iya haukacewa akan Sahil,ina ta daurewa
duk sanda na gaji zan fusata na kai kaina,Hajiya Kulu tace to kiyi hakuri mana haka
a samu aiki da wajen zamanki sai a san yanda za ayi ko? Islaha tace ayi sauri to.

Hajiya Kulu ta san Aunty tun suna tuwo tuwo a tasha tun Islaha tana karama har
suka yi kudi suka dawo Lagos,dama kuma sunfi shiri da Islaha sabo da wahalar da
Aunty ke bata,Hajiya kulu ita ba yar iska bace shi yasa ma sam basu fiye mutunci da
Aunty ba.

Islaha sallah tayi ta zauna Hajiya kulu ta kawo mata abinci shinkafa da miya da
nama yanka uku sai salat da ruwa,Islaha tana kuka tana cin abinci wai dan Hajiya
Kulu ta raimake ta.
Sai da ta koshi sannan tayi wanka ta zauna ta zuba tagumi tana tunanin Sahil.

Sai da ta kwana uku a gidan Hajiya kulu tace Islaha kawai ki zauna a wajena ki
dinga tayani siyar da abinci a wajen saida abinci na mana nan gaba idan an samu
aiki me kyau sai na kaiki can, Islaha tace ba damuwa,daga ranar Islaha bata sake
kuka ba, idan suka shirya abinci a gida sai a zuba a manyan kuloli su jera a cikin
kurar ruwa su tura zuwa layin da Hajiya kulu ke siyar da abinci,wata rumfarta ce da
katon tabir da benchi sun kai hudu na zaman samari masu siyen abinci,Tebir din kuma
a samansa suke jera kulolin.

Islaha kurar ta turo sanye take cikin riga da skert na atamfa tana tura kura
sai ga Khalisat,Khairat,Aunty da Shema'u sai Yaseer shine ke tuka su a motar
Shema'u,da sauri Aunty tace tsaya tsaya ga Islaha can tana tura kura ta koma tuwo
tuwo.

Aunty duk da ita ta kori Islaha bata ji dadin ganinta a haka ba yar yayarta ce
ta jini,a gaban Islaha yayi parking,Yaseer yace Aunty baki kyauta ba wlh banji dadi
ba bai kamata ba,Khalisat tace shegiya gwara haka gwara da aka koreta bata da
kunya,na samo saurayina kyakyawa ta rabani da shi.

Aunty ce ta bude mota ta fito tana bulbula kamshi ta sha kitson Attach,Islaha
tana ganin itace ta dauke kai,Murmushi Aunty tayi tace kin iya rashin kunya baki da
abinda kika taka a kasa yanzu ina amfanin wannan rayuwar? kizo mu koma gida kici
gaba da zama amma sai in zaki canja hali kibi umarni na,Islaha tace Allah ya kiyaye
ni ba asararriya bace.

Gwara nayi wannan sana'ar ta fimin na bawa maza kaina,Aunty tace kije jiki
magayi ta shiga mota tace Yaseer muje naga alama bata ji jiki ba,Yaseer yace ke
Aunty...ja mota muje ko naci uwarka wlh,motar ya ja suka bar Islaha a tsaye,kurarta
ta tura tana hawaye har ta kai abincin rumfa.

Maza da yawa sunzo siya su suka dora mata abincin a saman tebir sannan ta fara
zuba musu tana karbar kudinta,wani matashi yace ki sa naman kato fa ke,Islaha ta
kalle shi kawai ta zuba masa a robar take away, ya karba yace kudin sai na
dawo,tace hey.... don't Dear me miko min kudina bana son wasa ta bata rai,ba shiri
ya mika mata kudinta ta karba ta saka a jaka ta bashi canjinsa,sai daga baya
Hajiya kulu tazo.

Amarya ce taci gayu cikin sabuwar atamfa doguwar riga ta mata mugun
kyau,dauri taci ture kaga tsiya baya ta gyara gashinta har baya ta sa ribbon kalar
atamfar dark green,tana kamshi Sohail ya kalleta yana murmushi,Murmushin tayi masa
itama,kinyi kyau yace,tace na gode kaje kayi kaima,yace nayi da asuba sai
anjima,tace oh na tuna,yace ae bana karya dan a so ni,tace nima haka,yace aka sani
ko na amarci kike yi,Maheera fuska ta bata ta juya,hannunta ya ruko yace hijab din
fa,tace sai kace na sa kana nan kaya kullum kace sai na saka Hijab ina gidan
mijina,Sahil fa yana nan,to a haka wacce shiga nayi ta rashin dacewa kowa zai iya
ganina a haka haba Sohail wannan wanne irin kishi ne, Sohail yace namijin kishi ne
dani.

Juyawa tayi zata fice yace dan Allah to sa mayafi please Baby,dariya tayi ita
zai wa wayo har da Baby,zuwa tayi ta dauki mayafi kalar kayan ta yafa tace Allah
idan kace Baby sai naji ko nayi fushi gaba daya na huce,yace Baby wuya a waje da
gashin da dai Hijab dinne,harararsa tayi yace to jeki na hakura muje ya mike yabi
bayanta sai kakkareta yake.

Sahil yana palo shi karinsa yake suka fito suka iske shi yana cin
abincin,Maheera tace ina kwana Sahil? Kallo daya yayi mata yace lafiya lau Amarya
ta Ango,Sohail hannu ya mika masa suka gaisa yace nazo da safe kana bacci,Sahil
yace zo kaji,Sohail ya duka ya mika masa kunne yace iceko ba aci amanata ba? A jira
Islaha fa,Sohail shima da rada yace banyi komai ba,sai faman kus kus suke,Maheera
ta wuce Dining ta zauna tayi serving kanta tayi serving Sohail ta hada masa tea da
komai sannan tace Sweet yunwa nake ji.

Sohail zama yayi a dining yace har kin zuba min komai? tace ae yace Allah ya miki
Albarka,bari na baki a baki,Maheera tace a ranta abu kamar hawa da sauka ayi daidai
a dawo a kauce, chips din ya tsikaro da fork spoon ya sa mata a baki Maheera ta
tauna jin dadi yau tafi kowa a duniya jin da takewa kanta,sai murmushin jin dadi
take Sohail yana bata a baki tana ci yana ci shima, Sahil yana can daga palo yana
cewa a dai tsaya iya nan.

Sohail yace karka damu yana sa tissue yana gogewa Maheera baki,Maheera dadi ya
kashe ta tace haiiiiii Sweet tana wani sosa cinya kamar wacce Aljanu suka shigeta

Sahil ya kalleta dariya ta bashi ma ya dauke kansa yace sabo da anga bani da ita
shine ake cusa min takaici,dariya Sohail yayi ya yace zata dawo ne kaima kaji ka
daina damuwa,ni da zaka yarda ma da na aikeka,Sahil yace Ina? yace kaje ka gaida
babar Maheera kafin nazo kace na gode da aka bani ita,Maheera harda rufe fuska sabo
da farin ciki,Sahil yace bazan je ba gidan Aunty Aisha zanje tace naje wai za a
kawo garar Maheera zan taho da su nan,Sohail yace har wata gara za a kawo ni na
yafe kar a kashe min zuciya a barni nayi cefane na.

Sahil yace wlh sai mun karba in ba haka ba ta shiga uku da gorin dangin miji,na
dinga gori kenan na dinga ce mata yar rashin gara,gwara ma a karba,Maheera tace sai
ku kashe mutum da dariya jeka dan Allah,Sahil ya karbi key ya fita.

Yana fita Maheera ta mike tsaye Sohail yace zauna ke wai bakya zama kawai sai
kin hau min jikina,Maheera tace to wai ba mijina bane ni shike nan bazan ci abincin
ba ma ta juya zata tafi,da sauri ya riketa yace to zauna kadan amma karki dade ya
gyara mata cinya,Maheera ta zauna ita kanta ba sabawa tayi ba kawai so take ta
canja shi ya gane me akeyi.

Sahil yana fita yaga motocin Daddy sunzo kofar gidan,Sahil yayi mamaki,parking
suka yi driver ya bude masa kofa ya fito,Sahil yace Daddy kaine kazo gidan nan?
Daddy yace ae nine zuwa nayi naga zahiri,Sahil ya juya yace to muje suka shugo har
palo,Maheera tana saman cinyar Sohail a zaune suna cin abinci sai dariya suke
yi,Sallama suka ji kawai.

Daddy ya zaro ido ganin gida mashaallah,Maheera da sauri ta mike tsaye tana
gyara mayafinta,Sohail yace Daddy? Alhaji Ali ya kalli gidan yace uhm ashe kuwa da
gaske kuke yi shi yasa na kawo muku ziyarar bazata.

Maheera ta mike taje palon tace sannu da zuwa Daddy,zauna Daddy,Daddy yaso
ganeta yace kece yar aikin su Adnan ce ai,tace ae nice,zama yayi yana mamaki yace
Allah me iko kamarki kika amince lallai kowa baya rasa masoyi,ina ganin ai ko kamar
su Adnan a yanda Allah ya tsaraki ko kamar su Adnan sai sun kai ruwa rana sai kuma
gashi to Allah me iko.
Maheera dai durkusawa tayi har kasa ta gaida shi ya amsa yana ta faman furta
Allah me iko.
Sahil yace kar dai ka kyasa Daddy ba kyau,shi yasa aka ce ka samu wata yar bazawara
ka aura ka dinga mai da yawu amma kaki,an rasa me keka yi,idan baza ka iya ba mu
yan mata kawo kansu suke wajen mu ka bamu zabi muyi maka hanya da dai dai kai,kunya
Maheera da Daddy suka ji amma su twins ko a jikin su.
Sohail yace Daddy ina kwana da sassafe sai ka taho gidan Amarya,ai ba a zuwa
gidan yara da sassafe,Sahil yace ina kwana Daddy ya amsa duk sai da suka rusuna
sannan suka gaishe shi.
Maheera ta dinga kawo abinci tana dire masa,su farfesu ya zaci ma ita ta
girka,ta shiga kitchen ta kawo lemuka da ruwa tace Daddy ga abinci dan Allah ko
kadan kaci.

Daddy ya cika da mamaki sabo da saka ido sai da yaci ya tabbatar yaji ya girkin
yake,yaji dadi,Sohail yace ba ita tayi bama nata yafi wannan dadi na gidan Aunty ne
wannan,ai wannan ka taba cin girkinta kaji wlh ko kakar mu Iya me Koko bata kaita
iya girki ba,Daddy har sinasir ta iya,Daddy yace zaka ci uwarka Sohail ni kake
fadawa ko Iya me koko bata iya ba,uwar tawa mahaifiya, Sohail yace to yan zamani
sai yan zamani ai,Sahil yace wannan Special ce ba irin su Zayna bace me hanci kamar
tulu.

Maheera tana durkushe a kasa,Sahil yace tashi ai kin nemi Taskirar zaman ya
isa haka,Daddy yayi shuru yana jinsu yayi murmushi,Sohail yace nidai ko kowa bai
yaba ba tunda ni na yaba ina son abata shike nan.
To ku zauna cewar Daddy,zama suka yi yace shi aure da kuke gani Ibada ne,Sohail
yace a'a mu ba sai an mana nasiha ba mun sani,da can ba a damu damu ba sai da aka
ga munyi abinmu,ko gudun muwa ba a bamu ba,a barmu idan ma duka ne mu nadawa matan
namu,kudin mu ne,Daddy yace ai shike nan ya mike zai tafi Maheera tace Daddy ka
gaida gida.

Yace Madalla Madalla ya fita ya tafi Sahil ya bishi yana cewa da ka tsaya an
kawo garar ko kwano uku ka dauki shinkafar ba komai wlh mu har abada mahaifin mu ne
kai.
Daddy ya rufe motar yana dariya ya sauke glass Sohail yace gara ai ana bawa gidan
iyaye nasu Daddy ka tsaya ka tafi da ta gida duk da cewar gwauro ne kai.

Daddy son gulmarsa tasa yace Sohail yanzu kai wai hankalinka ya kwanta ko kai ga
ango? Sohail yace ya hankali na bazai kwanta ba da mace fa na kwana jiya,kai kuwa
yaushe rabo,ni wlh na daina jin haushi ma in kayi mana wani abun Daddy na gano
dalili babu mace.
Daddy ya bawa driver Umarni ya ja mota ya tafi sai dariya yake ta yaran nasa yanda
suke wanke shi tas.

Washe gari Daddy ya kira Sohail da Sahil yace suzo zasu gaisa da wani Ogansa a
harkar Business,yace yana bukatar yaga yaransa gaba daya.
Sohail yana kwance yayi pillow da cinyar Maheera suna kallo a hakan ma da kyar ya
yarda ya kwanta a cinyarta itace ta nace sai ya kwanta.
Sahil ne ya fito a shirye yace ka manta Daddy na jira,Sohail ya mike zaune
Maheera tace ai ya shirya shima,Sahil yace da jallabiyar zai fita? tace ni to bana
so wata ta ganshi,Sohail yace kyaleta muje Sahil hakan wannan yarinyar bata yarda
dani,ai zata zo fita ne Allah zai kaimu itama ai tana so ta yafa mayafi,muje
wallahi kika bari na fita haka kullum da hijab zaki fita.
Dariya Sahil yayi,Maheera tace muhe to ka canja abinka,tashi yayi ya wuce bedroom
kafin ta shiga ya kulle ya sa key kar taga tsaraicinsa shi kam.
Sai da ya shirya ya fito ya wani mika mata turare fesa min,Maheera ta karba ta
fesa masa,Sahil tausayinta yaji tabbas tana da matukar hakuri sosai ba karamin son
Sohail take ba.
Sai da ta rakashi har mota suka tafi.

Suna tafiya Sahil yace tana sonka da yawa kaji dadinka,ka kula da ita,ance fa ana
tabe tabe mata suna so ka dinga yi mata kar dai a zurfafa sai Islaha tazo,Sohail
yace karka damu ina jiranku ba abinda ma zanyi.

Ko nisa basu yi ba ya kira Maheera ta daga yace yaya gidan? murmushi tayi tace
lafiya lau,me zan siyo miki to? tace duk abinda ya dace,yace to shike nan,ki dinga
hakuri dani kinji,tace to ba damuwa ai,yau kiyi girki da dare nace wa Aunty kar ta
kawo,Maheera tace ae hakan yafi kar a wahalar da ita,dan Allah karka bari wata ta
kalle ka,yace su da idon su sai na hanasu yaro da kyawunsa,Allah ya musu ido na isa
idan nace bazan bari ba nayi karya gaskiya,wannan karyar soyayyar da ake fada bada
ni ba,Maheera ta dinga dariya tace gaskiya fa ka fada kuma,yace duk karya suke muku
maza,makaryatan banza makaryatan wofi,Allah yayiwa bawa ido wa ya isa ya hanasu
gani,gani me kyau dani Alhmdllh ahh su kalla su kwashi garabasa ni dai bazan ce ina
son su ba ko ya kika ce? Maheera tayi dariya tace I love you sai ka dawo,missing
you already ya furta,yana kashe waya Sahil yana driving yace ana ci min mutunci a
kasar nan.

Suna shiga palon su Adnan suka samu Daddy da wani babban mutum,ga su Adnan a
gefe suna hira ga kayan abinci ana ta ci,dattijon yana dagowa yaga Sahil,Sahil ma
ya gane shi shine wanda ya gyarawa mota a Lagos,Baki Dattijon ya bude yana murmushi
yace Sahil kaine a nan? Me kake yi?na dade ina nemanka na rasa ina zan ganka zo nan
zo,Sahil yana ta murmushi ya karasa gaban Dattijon,su Adnan da Daddy suna ta
mamaki.

Free page 1&2 400 ne

AsmaBaffa
08061929616
[7/17, 3:18 PM] Asmabaffa: 🪸MUMMUNAR DABIA🪸
41-45

Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA NE 'YATA TASNIM

Page naki ne
Mhiz Awwal

MASU AUDIO BAN YARDA WANI KO WATA YA SATAR MIN NOVEL BA IZINI BA.

Alhaji Umaru yace ikon Allah,Daddy ne yayi magana yace wai a ina kasan Sahil ai
Dana nane na cikina,Alhaji Umaru yace a Lagos ya basu labari,Adnan baki suka
tabe,Alhaji Umaru ya rike Sahil yace ga me kama da shi ba babanci,Sahil yace yan
biyu ne mu, mashaallah,me ka karanta ne ma? Daddy ne ya bashi amsa yace dake basu
da lafiya ai sune yarana da na baka labari basu da lafiya masu Aljanu,to to sune?
Ae sune basa iya komai na rayuwa,kaga su Adnan su sunyi karatu me zurfi cewar
Daddy.
Alhaji Umaru yace laifinka ne baka dai fahimci inda basirarsu take ba,baka kula
da su ba ka jansu a jiki ta ya zaka gane,sun fara university naga baza su iya ba
kawai na cire su,Alhaji Umaru yace baka kyauta ba,Business ai ba sai da boko ba kai
ka sani,sannan magani ma ai ya kamata a tsaya a nema musu magani,Daddy ya furta
anyi anyi abin yaki.
Sohail yace gashi ni na samu aiki a kamfani kuma da gidana nayi aure,Alhaji Umaru
yana murmushi ya furta mashaallah naji dadi,yanzu saura Sahil ko shima zan bashi
aiki babba ma kuwa ni da kaina zan koya masa komai na bangaren Business zan gano
inda ya cancanta na ajiye shi.

Sahil yana ji yace nifa bazan je Lagos ba,indai a lagos zaka bani aiki ka rike
abinka gaskiya bana so na gode,Alhaji Umaru yace comon ina da kamfani da yawa a
kasar nan ko a nan ma baka da matsala ko ina ka zaba,zo ku zauna ya jawo Sohail da
Sahil suka zauna kusa da shi,su Adnan ransu idan yayi dubu to ya baci.
Daddy bai ce komai ba kallo kawai yake yi sai daga baya yace anya Sahil zai iya
kuwa? Alhaji Umaru yace zai iya ba damuwa zan koya masa,ba yanda suka iya shuru
suka yi,Alhaji Umaru yace da ka daure muje Lagos just 1day ma sai ka dawo ka fara
aikin akwai takardu da zaka cike,Sahil yace nifa bazan je wannan garin ba na tsane
shi.

Sohail ne yayi magana yace ni zan rakaka muje mene abin kikiyar Lagos zan rakaka
sai muje tare kawai,nidai bazan yi ko sati daya ba,kwana daya aka ce cewar
Sohail,kamar daga sama Sahil yaji ance Islaha tana can,shuru yayi kamar yana
sauraren magana da sauri yace zanje ko wata daya ne zanyi.
Daddy da sauri yace to kaji irin abin nasu hawa da sauka yanzu hankali anjima
hauka, Alhaji Umaru ko a jikinsa yace wannan ba wani abu bane ni zan ji da shi
kaine baka fahimce su ba ai ba a haka.

Suna ta hira Maheera taga shuru shuru masifar kishi ne da ita dole sai an kula
da ita,kiran Sohail tayi a waya,yau tayi sa'a yan soyayyar suna kansa yana dagawa a
gaban kowa yace Sweet ya aka yi ne? Maheera sabo da jin dadi yatsanta karami ta sa
a baki tana murmushi tace ya Daddy din? har yanzu baku gama ba? Kina son ganina ne?
Maheera tace ae ai nafi so kullum najika kusa dani,Sohail yace an gama gani nan
tunda kika ce na dawo to ai uzuri ya kare ko uzurin waye ajiye shi zanyi,Maheera
tace idan baka gama ba ku gama,inaaa...sam na gama ai tunda kika kirani,nifa
maganarki kadai nake ji duk fadin duniya ba wani me sani ko ya hanani,Daddy yana ji
ya girgiza kai a ransa yace har ni ban isa ba na haifi da yace macece ta isa da
shi.
Sohail yana wayarsa harda harde kafa minti nawa kika bani? Tace 20mnt,mikewa yayi
yace to gani nan,Sahil ya kalla yace zaka tafi ne ko na barka anan? Sahil yace me
zanyi muje kawai ni kaina idan ina ina ganin soyayyarku dadi nake ji.

Alhaji Umaru shi gani yake ba wani abu bane sabo da zaman Lagos da yake yi,Daddy
ne yake fada a gaban manya kuke irin wannan baku san darajar manya ba,Ibrahim ya
furta ai masoya ne,Adnan takaaici ya hana shi magana ma,so yake ma ya samu dama ya
illata Maheera kowa ya huta yaji haushin aurenta da Sohail yayi gwara ta auri
bare,kamar Sohail mahaukaci ya auri irin Maheera shi a ganinsa bai dace ba.

Alhaji Umaru ne ya rike Sahil yace zauna kai shi ya tafi tunda ai zamuyi
maganar aikin ko? Sahil ya zauna yace kawai dai dan kaine ni ba a son raina ba
gaskiya,Sohail yace ni zan tafi a taxi kai ka dawo a motar, Sahil yace ko kace ma
na dawo a taxi baka isa ba sai dai ka bar motar a nan,dariya Sohail yayi ya
tafiyarsa yana cewa Ogan Daddy ka gaida gida mun gode,Alhaji Umaru yace madalla,ni
bana gane su ma sam.
A nan Alhaji Umaru yace da Sahil ka shirya tare zamu tafi Lagos a jirgi,Sahil
dai ba a son ransa ba amma idan ya tuna ance Islaha tana can sai murna.

Sohail sai da ya tsaya ya yiwa Amarya siyayya na kayan ci sosai sannan ya koma
gida,taci sabon wanka na daban yana shugowa ta rungume shi,Sohail kallonta yayi
kawai bai ce komai ba,Maheera ta furta ya baka yi magana ba? ya zanyi dake kin zama
fitsararriya sai ciwon kai kike sa min,Maheera murmushi ta saki suka zauna ta
karbi ledar tace duk nawa ne wannan? Sohail ya daga mata kai sama alamar ae,tace na
gode Allah ya kara budi,yace ameen Islaha dai tana can tana walagigi da bata tafi
ba ai da tuni itama ta zama babbar mace,Maheera tace zata dawo Inshaallah wlh
kullum sai na gwada kiranta bata shiga.

Maheera ta kalle shi yace menene? tace ina tunano sanda zan haihu a gidan
nan,Sohail ido ya zaro,tace ei mu cika gida da yara abinmu,Sohail yace ki cika gida
da yara? Me zanyi dasu? kiwo zan dinga kada su da sanda ko me,ni baza a haihu ba ya
furta,Maheera tace Sohail shine auren, mu da ba ayi haka ba ai baza a haife mu
ba,burin ko wanne ma'aurata kenan,Sohail yace sanda za a haifeni da na sani ma ita
me haifar tawa tun ina ciki zamuyi mutuwar kasko da ita,dariya ta kama Maheera
kwanciya tayi a jikinsa,ya gaji da halinta kyaleta yayi.

Kwanan Alhaji Umaru biyu ya tafi da Sahil Lagos,suna zuwa garin aka fada masa
layin da Islaha take,Alhaji Umaru tun a hanya cikin motar da driver ya dakko su a
Airport yaga Sahil ya canja duk hankalinsa ya tashi,yace lafiya kuwa? Sahil yace
budurwa ta wajenta zanje dan Allah ka sauke ni,zanzo gidan naka anjima,Alhaji Umaru
bai musa masa ba ya bashi katin gidansa yace ga Address ka shiga taxi ka mika katin
za a kawoka,Kudi ya zaro da yawa ya bashi,Sahil ya karba yace na gode,driver yana
parking ya fice da sauri ko jakarsa bai dauka ba,Alhaji Umaru suka ja mota sai
gida.
Sahil sanye yake cikin kana nan kaya Navy color ya sha kyau yana tafiya a kafa ya
gaji ya hau machine,sai kace aljani har layin da Islaha take siyar da abinci amma
bai san ina ne wajen ba,basu nuna masa ba,tafiya ya dinga yi yabi nan yabi can
shuru.

Islaha kuwa ta gama jera abinci ta manta da lalitar saka kudi ta koma gida ta
dauro ta a saman cikinta tana tafiya a hankali ta harde hannayenta a baya tana
sanye cikin riga da skert yan kanti da siririn mayafi a kanta,tana tafiya tana
walagigi a hanya ga rana,a hankali take tafiya,Hajiya Kulu ce ta iske ta a hanya
tace ke Islaha koma gida ki kula da bakin nan da nayi ban san halin su ba kar su
dankara min sata.
Daga nan Islaha ta juya gida tana tafiya a hanya tana ta faman tunanin
Sahil,tsaki ta ja tace kai bazan iya ba Abuja zan tafi gobe wlh,wayarta ta kalla
kamar ta kunna sai ta fasa kawai.
Sahil kuwa har wajen da Islaha take siyar da abinci yaje ba kowa sai Hajiya
Kulu,tsayawa yayi a wajen yana ta faman kalle kalle,Hajiya kulu ta kalle shi tace
Alhaji wa kake nema ko tambaya kake yi ne? Sahil ba komai kawai ya furta ya juya ya
bar wajen.
Kamar ya dora hannu a kai ya kwala ihu haka ya juya gashi ba wani bayani da aka
sake masa,Taxi ya shiga ya wuce gidan Alhaji Umaru.

Islaha kuwa shiri tayi tace gwara ma naje can Abuja kawai na huta sai dai kawai
su ganni ba zato,zuwa yamma bayan Hajiya Kulu ta dawo Islaha ta sanar mata zata je
Abuja gobe,Hajiya Kulu tayi murmushi tace yan mata ba kunya za aje wajen saurayi to
idan kinje kun shirya dai ki dawo yafi mutunci ya dinga zuwa zance,Islaha tace ae
ai dama.

Bangaren Sahil kuwa yana zuwa gidan Alhaji Umaru a lekki gidane duniya guda
Aljannar duniya sai ka bace a gidan sabo da girman gidan,duk wani alatu akwai,iso
security ya masa kasancewar an san da zuwansa me gidan ya fada musu.

Har palon Alhaji Umaru katafaren gaske in banda kamshi da sanyi ba abinda ke
tashi,Kujera ya nema ya zauna ba kowa a palon sai shi daya,can bayan kamar 5mnt sai
yaji karar takalmi me tsini an shigo palon,kallo daya yayiwa wajen yaga wata
budurwa ce kyakyawa da ita baka ce amma tana da kyau da diri mashaallah,skin dinta
me kyau sosai.
Sanye take cikin wata Jallabiyya fara ta mata wacce ake yayi me tsada ta mata
kyau matuka,takalminta da mayafinta black,tayi acuci ta nada,Sahil take ta faman
Satar kallo,a ranta tace wow,ban taba ganin me kyan wannan ba tunda nake a
duniya,suturar jikinsa ta kalla ta wayance da duba abu a palon kamar tayi mantuwa.
Gyaran gashinsa ta kalla tace ya Allah guy ne wannan na karshe ya iya wanka,dama
da irin wannan a duniya?,ko kallonta Sahil baiyi ba,wayarsa ya dauka sabuwa Iphone
wacce Sohail ya siya musu,Sohail ya kira a waya ya fada masa sun sauka
lafiya,Sohail Alhmdllh film nake kallo sai anjima mayi magana ya kashe wayar tare
da maida hankalinsa kan tv..

Maheera ce ta samu rana Sahil yayi tafiya Bum short ta saka da wata
matsiyaciyar riga,shine ta fito ta wuce zata je kitchen har tafiya ta canja Sohail
a ransa yace sai kace yar American film,fitowa tayi dauke da cup da lemo a
ciki,kafin ta karaso ma Sohail yanzu ya saba a jikinsa take zama har ya gyara sai
yaga ta zauna a gefensa amma sai da ta dora kanta a kafadarsa yace ai nasan ya zama
dole ,Murmushi tayi ta mika masa lemon ya karba tare da furta na gode,Maheera
tunawa tayi zata goge kayanta data wanke a washing machine,tashi tayi ta kwaso su
ta jona ion,mikewa yayi yace kawo na goge miki.

Bai taba taya ta aiki ba tunda tazo sai yau,suna tsaye a wajen gugar yana ta
mata guga a saman abin guga,ta bayansa ta koma ta rungume shi hannayenta ta saman
kirjinsa,Sohail yace karki taba min nono na,dariya tayi inda ya saba da halin
Maheera har ya gaji ya daina fada kyaleta yake yi,a haka yake mata gugar,sai da ya
kusa gamawa yace na gaji karba tayi taci gaba da gogewa ya koma ta bayanta ya
rungumeta,dariya tayi tace ai ba cewa nayi ka min ba yace ai na zaci karfi ake
karawa na aiki shi yasa na miki ki goge da yawa.

Hannayensa ya maida saman kirjinta Maheera a ranta tace ya fara ganewa,kasa


gugar tayi tace na gaji sai anjima a karasa,Sohail ya kalleta yace sannan ya dora
bakinsa a kunnenta yace ke dai kice kin kasa ai na zaci ke jaruma ce,ki daina raina
ni nasan me akeyi" cizonta yayi kadan a kunne,yar kara tayi tace da zafi fa tana
shagwabe fuska dariya suka.
zama suka yi a kujerar dake palo Maheera ta kyale shi ya huta.

Sahil shi dai ko kallon budurwar baiyi ba yanda bata kulashi ba shima haka,wata
Babbar mace ce ta shigo sanye cikin kaya na alfarma doguwar riga ce a jikinta yar
kasar Dubai,sallama tayi Sahil ya kalleta,zama tayi da fara'a tace sannu da zuwa
samari,Sahil da girmamawa ya gaida ta, tace ya hanya barka da zuwa,yace yawwa
kawai,Me aiki ta kira tace ta kawo masa abinci da kayan sha,Sahil aka dinga jera
masa kayan abinci a gabansa yace Mama ya isa haka,ya daga zuwana za a cutar dani"
idan ba so kike cikina ya rude ba wanne zanci wanne zan bari a ciki,Dariyar Hajiya
Suwaiba tayi tace duk sai an kawo ka zaba ai,Sahil yace yanzu haka kuma idan ba a
cinye ba zubarwa zaku yi ko ga wasu can bayin Allah suna kwana da yunwa,tace ai
akwai masu aiki.
Budurwar ta dawo jikin Mamanta ta wani lafe ta zauna ta kwanta a jikinta,Hajiya
Suwaiba tace kin gaida bako kuwa? Sai lokacin tace ina yini, Sahil lfy ya furta
kawa,sai da Alhaji Umaru ya fito sannan yasa aka raka Sahil dakinsa yace a kai masa
abincin can ya huta tukun haka aka yi kuwa,sai bayan yayi wanka yaci abinci sannan
zuwa dare ya koma part din Alhaji Umaru.

Washe gari Islaha tana idar da Sallar asubah ta shirya tsaf ta yiwa Hajiya Kulu
sallama ta wuce tasha ta hau mota abinta sai Abuja,sai da suka kusa zuwa ma sannan
ta kunna wayarta amma bata kira kowa ba,Bangaren Sahil kuwa shi da Alhaji Umaru ya
kira shi,da takardu suka zauna duk wacce ya karanta ya fassara sai da yayi sharp
sharp,ya cike duk abinda ya dace,Sahil yace to da abaya ne sanda bamu girma haka ba
babu abinda zan iya karanta maka,Alhaji Umaru yace sauki ya samu ashe,dariya suka
yi.

Washe gari da safe suka karasa aikin nasu Alhaji Umaru yace Sahil kai baza kayi
auren ba? Sahil yace zanyi mana watarana,Alhaji Umaru yaji dadi ya furta, kaga
'yata? Yace na ganta wata marar tarbiyya bata da tarbiyya, Alhaji Umaru yace wlh
rashin ji ne na yaran zamani ana mata fada daidai gwargwado,Sahil yace bakwa cin
ubanta shi yasa ta fi karfinku, ya sunanta ma? Alhaji Umaru yace Amatullah,Sahil
yace ai da kun sani Harira kuka saka mata tafi dacewa da sunan,Alhaji Umaru yayi
dariya yace ita kadai na haifa a duniya,ina so ta samu tsayayyen namiji me Amana
wanda zai tsaya mata ya kula da dukiyarta ko ba raina.

Sahil yana ji yace Allah yasa ka samu me Amanar a zamanin nan,yanzu tsayayyun
maza sun kare a duniya sai irinmu lusarai masu matacciyar zuciya,wai dan kar ace ya
aure ta,yaci gaba yanzu dan ta'adda mutum daya da zai zare wuka duk guduwa zamuyi,a
gaban mutane a gari da rana zaka ga ana kwacen waya da sauran su amma ba me iya
katabus sai kallo shi dai tunda ba kansa bala'in ya fada ba babu ruwansa,ai mu
yanzu a kasar nan mun koma idan jifa ya wuce kanka to ya fada kan uban kowa, kayi
addua kawai Allah ya bata na gari, idan zata ta mike ma ta mike ta kula da dukiyar
tata da kanta,what man can do woman can do better,ai yanzu mata ma sun jajirce sun
daina kashe zuciyar su,tunda kace har phd ne da ita ai bata da matsala ba sai ta
samu miji me kular mata da dukiya ba.

Alhaji Umaru yace ai bata da wayo ne bata san ta duniya ba sam bata san rayuwa
ba,Wannan laifinku ne ku kai yar banza kauye a bata horo me tsanani,Alhaji Umaru
dariya yayi duk ta inda ya bullo Sahil yana da amsa,gajiya yayi yace kai me zai
hana ka aureta wlh zan baka ita,ni na yarda da kai na aminta da kai.
Sahil yace gaskiya kana sona Ogan Daddy,kuma naji dadi,banga wanda ya ganmu ya
so mu haka ba, ka bani aiki a halin da nake ciki kuma ka yarda dani,baka kasan waye
ni ba kace zaka bani kyakyawar yarka na gode Allah ya saka da Alkhairi amma kayi
hakuri wlh ba wai ina kin jininka bane na riga na bawa wata zuciyata yanzu haka
tana wajenta babu wacce zan bawa Amatullah, Alhaji Umaru murmushi yayi yace na
fahimceka kuma ina maka murna amma namiji ai mijin mace hudu ne,bayan ka auri
zabinka zaka iya auren Amatullah ba damuwa,Sahil gumi ya goge yace ni dai Islaha
masifaffiya ce baza ta yarda ba gaskiya,bazan ma iya adalci ba,ni bani da
adalci,Alhaji Umaru yace kana namijin? Sahil yace ni Azzalumi ne gaskiya zan
zalunci yarka,kawai a bata wani ba tsayayye bane ni.

Alhaji Umaru dariya ta kamashi yace wannan gaskiyar taka yasa zan baka 'yata ka
aura...da sauri Sahil yace ni bani da wata gaskiya makaryaci ne,karya ce
dani,Alhaji Umaru yayi dariya yace tashi ka tafi time din Flight dinka yayi amma ka
sani kana da budurwa a nan ta biyu da zaka aura,kasan kuma idan na fadawa Daddy ko
baka yarda ba sai dai kaji an daura auren,Sahil yace zata sha saki kuwa a ranar
nidai ba ruwana, ina da budurwa fa,Alhaji Umaru a ransa yace a hankali zaka so
Amatullah ne na riga na fahimci halayarku a hankali kuna ganewa,Shi dai Alhaji
Umaru Sahil ya cancanta ya auri yarsa a wajensa.
Sahil bangarensa ya koma sai da ya karya yayi wanka ya fito cikin wasu kana nan
kayan fadar irin kyan da yayi bata lokaci ne,part din Alhaji Umaru ya shiga ya same
shi a palo tare da yarsa Amatullah sai shagwaba take yi, yace Sahil ka dage kai
gida zaka tafi? Sahil yace papers din duk ba nayi abinda kace ba? ai mun gama kace
zaka kirani idan wanda zamuyi aikin tare zaizo ko? Alhaji Umaru yace ae ai nufi na
ka sake hutawa amma abinda ya kawo ka an gama shi tun jiya da dare,Sahil murmushi
yayi yace nidai tafiya zanyi indai da wani abu kawai ka kirani,yace ai Abuja zaka
yi aikin karka damu naga baka son Lagos.

Sallama ya masa,Amatullah harda cewa Yaya Sahil ka gaida gida sai munyi
waya,Sahil yace ni bani da kanwa mace daga ni sai Sohail,Amal ce kuma yayar mu ce
itama,Juyawa yayi ya tafiyarsa.
Sahil da kudade masu nauyi ya wuce airport driver ya kaishi,Alhaji Umaru ne ya tura
masa,Sahil ya tambayi driver yace me ake siya a garin nan na tsaraba? Driver yace
hausawa ai in zasu koma doya suke siya sai manja,da kwakar manja,coconut da garin
kwaki shi zaka ga suna siya har Egusi suna siya.
Sahil yace kaini inda ake siyarwa,driver ya kaishi doya kadai ya siya ta kai
guda ashirin manya,dankalin turawa ma da yawa, ya siyi egusi da yawa shima sabo me
kyau,har garin kwaki wurin kwano uku ya siya,kwakar ruwa tafi goma,har kwakwar
manja,yaga guava masu kyau ya siya,tarkace ya siya,ya kashe kudi sosai yace shi fa
ba tafiya zai iyayi da su ba sai dai a sa a mota a kai can ya karba a Abuja,kayansa
aka shirya masa waje daya aka saka a mota ya biya kudin kaya motar ma ta rigashi
tafiya daga Lagos zuwa Abuja.
Yana hanya Islaha ma tana hanya a lokacin.

Ya riga ta zuwa kasancewar ita a mota ne,yana komawa Maheera ta bude kofa yace
Amarya kina wulakanci a gidan nan karki kashe min dan uwa da wanka,dariya tayi
Maheera tace ina tsarabar? Sahil yace ni ban taho da komai ba amma na sa a mota za
a kawo in sunzo zasu kirani naje na karba,me ka siyo? idan an kawo zaki gani ya
wuce dakinsa,Islaha sai gaf da magriba ta sauka,tana zuwa gidan su Adnan ta
wuce,knocking tayi,Madam Oge ce ta fito tare da bude kofar tace can i help you?
Ibrahim ne ya leko sai yaga Islaha yayi mamaki,yace ina kika shiga zuwana garinku
sau uku kin gudu,Islaha tace ni ba wajenka nazo ba ina Maheera?

Ibrahim yace ta mutu,kyale shi tayi ta zaro wayarta zata kira Maheera yace muje
na kaiki gidansu ma, tace idan kasan wasa kake ka kyale ni,yace ba wasa ai tayi
aure,Islaha tace aure? da wuri haka har tayi aure har yaushe na bar gidan,wa ta
aura?Ibrahim yace muje na kaiki,motarsa ya bude ta ajiye kayanta a baya ta shiga
gaban mota yaja suka tafi.

Magana ya mata yace yaushe zan kai kudin aure ne? Islaha ta masa shuru,yace ke
yanzu kinfi son mahaukaci sabo da kyau? tana jinsa yana ta zagin su Sohail tace wai
wacce irin rayuwa ce wannan taku dan uwanka ubanku daya amma ku dinga irin
wannan,wacce irin kiyayya ce haka,me suka muku? aji tsoron duniya gaskiya,banza ya
mata sabo da kishin da yake taso masa.

Har Estate din Sohail ya kai Islaha a kofar gidan yayi parking yace sabo da son
da nake miki na kawo ki amma badan haka ba babu abinda zai kawo ni,tana zaune a
motar tace dan Allah ku daina yi musu haka yan uwanku ne fa,suna haka Sahil ya fito
cikin motar ya kalla,kamar Islaha ya gani,gaban motar ta bude ta fito,Ibrahim yana
ganin Sahil yayi murmushin mugunta,motar ya bude ya fito Islaha ta dauki jakarta
ita kanta ganin Sahil wai haushinsa take ji ya koreta sai ta juya tana yiwa Ibrahim
magana harda kirkiro dariya.

Sahil yana ganin haka ya wuce abinsa har ya tafi ya kasa hakura ya dawo,
Ibrahim sai damka yaji kawai ya shake shi,kamar zai kashe shi,sai kakarin mutuwa
yake,da hannu daya kacal ya shake shi amma sai da ya raba shi da kasa ya daga shi
cak,Islaha ta saki ihu tana neman agaji,ga unguwa ba mutane,wasu samari ne suka ga
abinda ke faruwa,idon Sahil ya canja sai huci yake jikinsa yana rawa,agaji suka
kawo da kyar aka kwaci Ibrahim a hannun Sahil,Ibrahim yana hakki yana shafa wuyansa
yace ni ka yiwa haka kana kanina? Wlh sai kasan kayi min haka, Sahil tsaki ya ja
yace duk abinda zaka yi kayi,Ibrahim zai sake magana Sahil ya nufi inda yake,ai da
gudu ya zaga tare da fadawa motarsa ya ja ya bar wajen a guje,yasan karfin aljanu
ne da su yanzu sai su illata mutum a banza.

Islaha ya kalla ta kalle shi tsoro taji sosai yanda ya bata rai kamar zaiyi
gunduwa gunduwa da ita haka ya koma ya nufi inda take idonsa sai zallar bacin rai a
ciki,Juyawa tayi da gudu tana tibi tibi wai gudu take yi abinda taku daya zai
kamata,Juyowa tayi taga ya biyota, wayyooo tace tana gudu,dariya ma ta bashi yanda
take gudun.
Tsayawa yayi ta tsaya nesa da shi tana hakki tace karya nake ba kulashi nake
ba,to dawo yace, Wayarta ta dakko ta kira Maheera,Maheera mamaki tayi tana kwance a
palo taga kiran Islaha,dagawa tayi tare da furta Islaha kece? Ina kofar gida ki
bude min dan Allah Sahil zai duke ni,Maheera ta bude kofar taga Islaha can nesa
Sahil a nesa shima,Islaha ta shige ciki da gudu,Sahil yayi tafiyarsa inda
zaije,farin ciki yake.

Yace yau duk garin nan ba wanda ya isa ya kaini nishadi,harda canja taku,yau kowa
sai ya shiga uku da mutunci na.
Sohail kuwa ya tsaya siyowa Maheera kayan ciye ciye bai dawo gida da wuri ba sai
da Sahil yaje ya karbo tsarabarsa ta lagos sannan Sohail shima yayi parking da
motarsa ya fito sai ga Sahil a taxi da kaya a buhu har biyu manya,yace wai sai da
ka siyo wani abu amma a mota ka dora mene haka? Sahil yace ina ruwanka na Maheera
ne ba itace me girki ba,Me taxi din ya bawa kudi yace shigar min da shi ciki
please,Sohail yace tab ya barsu a nan haka kawai ya shiga ya kallar min mata,Me
taxi yayi murmushi,Sahil yace jeka to na bar maka kudin,yayi godiya ya tafi,da
kansu suka dauki kayan suka shigar da su da kyar, su biyu amma daukan kaya ya zama
aiki sai wahala suke sha a haka suka shigar da shi da kyar.

Maheera da Islaha sun shige bedroom sai labari suke bawa juna bayan
rabuwa,Islaha tace ashe dai Allah ya buda gashi har kin auri Sohail saura muga
ciki,Maheera murmushi tayi tace bayan ke ake jira ba abinda aka yi,Islaha ta bude
baki Maheera tace wlh bama ko romance wai sai kin dawo Sahil ya aure ki,Islaha ta
dinga dariya tace kinga ta kanki Maheera Allah ya kara hakuri,yanzu ni tunanina
idan aka aureni nima aka ki yin komai fa muka dora a haka,Maheera tace a hankali
zasu gane karki damu,kawai dai ki dinga hakuri da su tunda kin san halinsu.

Sohail ne ya kwalawa maheera kira me shago tashi tayi ta fito, murmushi suka
sakarwa juna tace yau kuma me shago nake? ta tambaya tare da rungume shi gashin
kansa ya sosa tare da mika mata ledar,tace me yasa kake sosa gashi ne? Kwarkwata
ce dani maybe,Sahil ya kawo miki tsaraba yace kiyi ta girki,dariya tayi tace ya dai
kawo maka kaine me gida ai naku ne ba na Maheera ba,Kitchen suka shiga ya nuna mata
buhu biyu ko budewa ba ayi ba,ta furta ashe abin na yi ne ,daurin da aka yiwa buhun
ta kwance da wuka taga doya tace dama tamu bata fi daya ba gaskiya yayi kokari tab
ga tsada,ta duba dayan taga dankalin turawa d,a ciki kuma ga ledar bacco biyu,ta
fito da su daya taga garin kwakwi yellow dariya suka yi har Sohail yace ke wannan
daraja ce da shi yanzu ajiye mana abinmu idan yunwar yamma ko ta rana ta taso ai ko
da marmari shanye abinmu zamu yi, Maheera tace har Eba zan na yi ma,aka fito da
Egusi da yawa,ga kwakwar manja ga kwakwar ruwa,ga kuma Guava,ga manja,Maheera tayi
dariya tace ni wannan Lagos indai haka ne a dinga zuwa wlh,Islaha tana zaune a
bedroom Sahil ya shigo tsoro taji ganin ya danna key a kofa.
Islaha sai zare ido take,ina kika tafi? Ya tambaya yana daga tsaye tace wai ranar
da na tafi bayan an gama party? Wanne party? Waye yayi party? Islaha tace party fa
wanda Sohail ya samu aiki har kuka ce ayi musanyan budurwa ka tuna? Wanne mahaukaci
ne ke musayar budurwa kin taba ji anyi? Party yaushe muka hada wani party kuma?
Islaha tace to ranar kuka ce na tafi da kanka kace na tafi wallahi zata yi kuka,ae
wannan nasan ni nace sai nace ki tafi da dare? Zuciya nayi Allah ya gani ni yanzu
ma ba dan kai nazo ba Wajen Maheera nazo,uhm naga alama ai cewa kika yi baza ki iya
zama ba a wajen Hajiya kulu dole sai kinzo kin ganni mu fa ba a mana karya,Kasan
Hajiya Kulu ne? Harararta yayi yace ban sani ba,kauyenku kika tafi ai,gidan
Lalai,duk abinda suka yi da Lalai sai da ya bata labari ,tun da ba a fada masa ba
sai yanzu da ta riga ta dawo,Islaha tace naci wahala a hannun Lalai har kanta
hannuna yayi sabo da daka,Sahil yace tab Lalai sai ta kwana a tsaye tana daga
yau,Islaha tace Kyaleta na yafe mata,ni ban yafe ba ya furta.

Yar uwata ce fa dattijuwa nace na yafe mata,ni ban yafe ba babu ruwana da wata
Lalai, Kofar Islaha ta mike zata bude ya rike hannunta yace Lagos din me ya kaiki
siyar da abinci? Tunda ka sani mene na tambaya kai fa ka koreni,ni ba wajenka nazo
ba yanzu,wajen Maheera nazo jibi kuma zan tafiya ta naci gaba da tuwo tuwo na a
bakin tasha kowa ya ganni, kuma shigar banza nake yi,dariya Sahil yayi yace to dan
kinyi shigar banza ai ba sabon abu bane da dan bente ma na taba ganinki ,naji to ka
bude kofar,Sohail ma da yake kwana da mace ba abinda ya mata har yanzu bare
ni,kullum baccin asara suke yi,Islaha tayi dariya tace dan Allah ka kyale su suyi
sunnar su mene sai an jira mu? Sahil yace me? ai ko ni Allah ya tsare ni da kallon
Taskirar mace bare Sohail,dariya Islaha tayi tace to shike nan ai, muje ni yunwa
nake ji,kofar ya bude suka fito,Maheera tana kitchen tana girki Sohail yana zaune
ya ja kujera ya zauna bazai tayata aikin ba ko daya,Islaha ce ta shigo tace me zan
gani haka kai da zaka mike ka tayata,Sohail yace so kike na zama mijin tace Allah
ya kiyaye tuwo fa take yi kawai sai na fara tuka tuwo,Maheera tana tuka tuwon
shinkafart tana jinsu.

Sahil yace maza sai dai su tuka nasu a Taskira,Sohail kunnensa ya toshe da
sauri,Maheera tace Sahil babu kunyar sirika,Sahil yace gamu muma Daddy fa har
England yaje ya tuka ya dawo,Sohail ya tashi yace karka koya mana iskanci,Ai Daddy
shi ba Bismillah bare a'uzu shi yasa muka zo a haka,sai da Sahil ya bari Islaha ta
dawo yace ni ai da nine nayi aure baka yi ba wlh bazan jiraka ba,ba dan iska bane
ni da zauna ina jiranka,Maheera ta kalli Sahil haka kace Sahil? haka nace me yasa
kuka jira ni,Islaha tayi dariya tace ai kunga sai ku dauki darasi.

Sohail yace an fada ma jiranka nake dama nima fakewa nake baza a ganni ba kaya
ba,Maheera tace Allah ya kyauta kawai ta kasa gane ina suka dosa suyi gaba su dawo
baya.

Yau Lalai da yamma ta kawo surfen masara ta zuba a turmi ta fara surfe abinta
tunda ta fara bata tsaya ba daka kawai take ba hutu ko digo har dare yayi masarar
tayi dugu dugu a turmi,ga uban zufa ta hada amma wani kaimi take karawa a dakan duf
duf duf duf daka ba tsayawa, Abdulrazaqu ya shigo tun daga kofar gida yake jin daka
na tashi ga dare yayi,maganar duniya Lalai ta kasa cewa kala kawai sai daka take,
Abdulrazaqu ya riketa amma taki dainawa sai zazzaginsa da tayi tace wlh ka sake
rikeni sai na tsine maka ka fita ka bar gidan nan zan tsine maka, Abdulrazaqu ya
fice da sauri yana tambaya me yake faruwa ne da Lalai,Lalai taci gaba da Daka
abinta makwafta na ji an rasa daga ina ake jin luguden daka,gashi kauye basa daka
da dare sannan karamin gari ne kusan kowa sai yaji.

Abdulrazaqu gidan yan uwa da makwafta ya shiga tare da kiransu su kawo dauki
Aljanu sun shigi Lalai,mutane suka taru a gidan Lalai amma kowa ya kasa kwace
tabarya,duk wanda yaje jikinta sai ta zubar da shi a kasa yaji rauni,malam Ishu
suka kira shi kuma ba malamin kirki bane kawai tsubbu ya iya,shima ya shigo da
babbar riga da rawaninsa yaje da Niyyar dakatar da Lalai,hannu tasa ta bugar da shi
nan take ta bazar da shi a kasa ya fadi baki duk ya fashe sai jini,mutane suna
ganin haka suka ce yo Malami ma bai sha ba bare mu suka firgita suka fara tserewa
aka rasa wanda zai dakatar da Lalai.

Allah sarki Abdulrazaqu shine ya zauna a gefe yana kallon Lalai tana ta faman
daka kafin safiya Masara ta koma gari tilis hade da dusar, hannunta duk ya
ruruce,tana daka ana tuna mata dakan da ta saka Islaha a kanta,kawai maganganu ake
mata a kunne akan wahalar da ta bawa Islaha,sai da gari ya waye anyi kiran sallah
sannan Lalai ta zube a wajen sumammiya, Abdulrazaqu yayi kanta da gudu yana bata
agaji.

Sahil ya takurawa Islaha kamar jela ta shiga kitchen ya bita,Maheera kawo na


tayaki cewar Islaha,Sahil yace a'a ki barta tayi abinta itace matar aure itace
nauyi ya hau kanta,idan ma bata yi ba mijinta ne zai sha wahala,Islaha tace harda
mu fa za aci,wa yace tace tuwo zata yi ai kinibibi ne sabo da taga kinzo shine ta
tsiro da tuwo,Sohail ka tayata mana duk bautar da ka yiwa su Adnan sai matarka zaka
kasa tayawa kuma kullum tare kuke bacci,gashi nan hannunka da jikinka duk sun kara
laushi sabo da yanda Maheera take takura maka da rungume rungume,Maheera tace
yaushe rabon da naji kana hira haka tunda Islaha ta tafi sai yau Sahil.

Sohail yana jinsu yace kanku ake ji,Islaha tukunyar miya ta bude tace me ya
rage? yanzu fa zanyi ki nika min Egusi,Sahil hannun Islaha ya bige yace da nasan
haka za ayi bazan kawo tsarabar nan ba ko hutawa bata yi ba,kina ganin yarinya ta
taho zubar da mutuncinta ki takura mata,Islaha dariya tayi ta rufe baki,Sohail
tashi yayi yace duk kuje baza a zauna ana wulakanta min mata ba.
Mikewa yayi ya taya Maheera girkin suka gama su Islaha suna palo taki magana
sosai wai yanga take nan ramawa take a haka wulakanci take yiwa Sahil a
ganinta,bayan kulashi take yi.

Sahil ne ya sata a gaba yana kallonta ya zuba tagumi yana kallonta kamar ya
samu tv,Sohail ne ya fito ya tsaya a gaban Islaha,Sahil ya ture shi gefe ba tare da
yayi magana ba yaci gaba da kallonsa,Islaha har gajiya tayi da kallon jarabar da
yake mata,Sohail yace kai wannan kallon ya wuce na musulunci sabo da kaga araharta
kawai a tura a kai kudi danginta a huta wannan wanne irin abu ne sai ka sa
budurcinta ya lalace ai.

Dariya suke mugun bawa Islaha,Maheera tana gamawa ta wuce tace bari nayi wanka
Sohail yace muje kiyi wankan ki bani na saka miki brazia burina kenan ni kullum na
dinga sakawa mata ita,Maheera tace au ba ni kadai ba mata ma? yace to yanzu ina
zanje na sawa wata idan ba ke ba,jeki ina kallo ai yanda kike sawa nayi degree,ka
daina jin kunyar tawa? Jin kunyar marar kunya asara ne muje kawai amma ni zan fara
wanka tace naji jeka,Toilet ya shiga sai data bari yana wanka ta bude toilet din,da
sauri ya tsuguna yana zuba mata ruwan masifa kamar zai cinye ta,masifar da yayi
bata taba ganin Sohail yayi fada ba sai yau,ba shiri ta fito ta zauna a gefen bed
ta zuba tagumi tace wai mijinka guda wannan wacce masifa ce.

Sai da ya gama ya fito idonsa har ya canja yayi ja sabo da masifarsa ta kalle
shi ba kaya,Maheera ta kalle shi ya dalla mata harara sai huci yake shi kadai,tace
Sohail ni fa matarka ce, baka san me akeyi ba idan anyi aure? A haka zamu rayu
kenan? tsaki ya ja tare da nuna ta da yatsa yace dan kawai kece amma duk ranar da
kika min haka ko da wasa wlh sai kin gane duniyar nan juyawa take,Maheera ta zaro
ido tace duk akan na kalleka kana wanka? An kalleka to wlh zan cire wannan towel
din naga yanda zaka yi,Sohail yace da kuwa kin kwana a bayan Uwarki yau,Uwata fa
kace ke kika jawo koma mene ai, ya sake jan tsaki ya juya yana shiryawa,Maheera ta
dade a tsaye sannan ta bawa zuciyarta hakuri da ta tuna yanda suke,Wanka ta shiga
ta fito yana ta shafa turare ya sanya 3qtr da riga armless yana ta fushi fuska ba
rahma.

Maheera tana satar kallonsa tsokanarsa tayi tace Sweet goyani,wani mugun kallon
ya mata,dariya tayi tace to na hakura shafa min mai yau daya dai,bai kula ta ba
uzurinsa yake,bayansa ta tako ta tsaya tace haba Sweet ka manta aurena fa
kayi,zamanka nake yi sabo da kai nazo nan nake zaune,na rabu da iyayena da kowa
nawa na yarda na dawo wajenka,ka manta ni me shago ce fa,baki ya turo da shagwaba
yace ai kece bakya ji na fada miki bana so,to na daina I'm sorry Sweet,rungume shi
tayi daga ita sai towel, murmushi yayi ka fasa saka min bra din? yace ke wasa nake
miki ina ni ina kallon wannan chamber taki,dariya tayi tace to jira na shirya sai
ka dauke ni ka goyani,daga na miki sau biyu ke baki san kadan ba,dan Allah ta
marairai ce masa,Okay to shirya,wayarsa ce tayi kara ya duba da sauri yaga a wajen
aiki ne aka sake kara masa matsayi,ihu yayi yace kinga an kara min girma yanzu,
Maheera murna tayi ta rungume shi suna ta murna,ya sake duba wayar yace tayani
karanta turancin nan ance naje gobe zamu tafi Meeting rivers state ko?,Maheera tace
Alhmdllh I'm so Happy,zamu kara zama masu kudi,Dama Oga yace yanzu indai aka canja
min matsayi to babu zama kuma kullum tafiye tafiye zan dinga yi,Maheera ta dan ji
damm sabo da ita ta saba da mijinta kullum suna tare suna kula da juna sannan so
take a hankali ta dan ganar da shi yanda ake soyayyar aure ko Allah zai sa ya gane.

Islaha sai da su Maheera suka fito sannan suka samu labarin,Murna suka tayasu
sosai,Sahil yafi kowa murna gashi shima zai fara nasa.
Maheera tace ke Islaha kece kika sha hanya kizo ga abinci fatan kuma kin kira
Hajiya kulu,Na kira ta na fada mata muna tare.

Dining suka zauna Sahil yace shi bazai ci tuwo ba,Maheera tace amma sai ka fada
min tun dazu na maka wani abin,Sohail yace yanzu ma ai tashi zaki yi ki masa ko da
yunwa zaki bar min shi? Sahil yace Jullof din taliya zaki min da kifi,Maheera ba
musu ta mike Islaha tace zauna naje nayi masa,Sahil yace ke kina da aure ne? Bana
son ki dinga shiga hurumin da ba naki ba,aikin matar aure sai matar aure,mu yanzu
muna da mata girki sai na me aure idan baki da aure kawai ke kazama ce.

Maheera haka ta shiga kitchen ta masa nasa ta kawo masa yace yawwa Sohail sa
mata Albarka,Sohail yace Allah miki Albarka Allah yasa ki haifo min yan
biyu,Maheera harda cewa ameen da sauri,yace taki ma samun cikin har yanzu
shuru,Islaha dariya tayi a ranta tana jinjinawa Maheera da zaman auren nan yaki
mata ciki yace itace taki samu.

A boye Maheera tace dan Allah Islaha kiyi sauri a daura muku aure ko na samu
sauki da twins ki daure ki janye min dayan ki rage min,Islaha tace bai ce ba zance
yazo aure ni ne.

Washe gari Sohail da sassafe suka yi Sallama yabi flight suka wuce,Sahil ne ya
kaishi airport din tare da Alhaji Saminu suka tafi sabo Sohail sai ana sasu a
hanya.
Kwanan Islaha daya tal a gidan Hajiya kulu ta kira tace ya kamata fa ki dawo gobe
tunda kin ganshi idan sonki yake yaje ya kai kudin aure danginki,bata yi musu ba
tace to zan dawo Inshaallah,Sahil yana ji ya fito yace naji kamar kina cewa gobe
zaki koma lagos,ae haka Hajiya Kulu tace,kamar abin kirki yace kira min ita muyi
magana,Kiran Hajiya kulu tayi a waya tace ga Sahil zaku gaisa,ya karba bayan sun
gaisa yace wai yarki ce Islaha? tace a'a Allah ne ya hadamu to na raba ku,dan Allah
ki kyaleta ta sarara,Hajiya kulu tace kaji yaro dan ubanka sanda ka koreta waye ya
riketa,ai ni sirikarka ce,Sahil yace sirikita tana kushewa ta rasu bani da wata
sirika,dama ni haka nake so ba ruwana da kunya ki zare min ido nima zare miki
zanyi,Hajiya Kulu tun a nan tace Islaha zata yi babban ganganci da rayuwarta yanzu
wannan zata aura shi yasa tace ba normal yake ba,ai kuwa zata yi kuka da idonta
watarana.

Sahil tuni ya kashe wayar yace sai dai ki jira Sohail ya dawo mu tafi kauyenku
da yan uwan Daddy a kai kudi,Islaha tace wlh baza su daura ba Ibrahim zasu
bani,Sahil yace zasu daura ki kyale su dai dai muke da su,Islaha tace to shike
nan,Amma baka kyauta ba da ka yiwa Hajiya Kulu haka ka bata hakuri,Tunani ya lula
yace sai kuma naga ban kyauta ba,sake kiranta to,Islaha ta sake kira tace dan Allah
Hajiya kiyi hakuri,Hajiya kulu tace na fahimta ai karki damu Islaha,Wayar ya karba
yace kiyi hakuri naga ban kyauta ba zanyi hakuri na kalle ki a sirikata watarana
idan ta kama
Hajiya Kulu ta jinjina kai tace ba komai na gode ta kashe wayar tace tab a haka
yarinyar nan zata kai kanta.

Maheera ita bakuwa tayi tana can tare da kawarta ce tazo Sadiya,suna zaune a
bedroom,Sadiya tace Maheera wani zance naji ance wai mijinki mahaukaci ne? ance
basu da hankali gaba dayansu,ana ta gulmar a gari, Maheera fuska ta bata tace nifa
bana son munafunci kizo har gidana kice da mijina mahaukaci,munafukar banza indai
wannan ne ya kawo ki tashi ki bar min gida,Sadiya tace daga fadar gaskiya,Islaha
tana palo tare da Sahil taga ya jawo belt a jikin wandonsa ya boye a bayansa ya
mike ya tare kofar palo ta fita.

Sadiya ce ta fito zata tafi sum sum Sahil ya tare hanya yace munafuka to naji
duk abinda kika ce,wato mu mahaukata ne,ke ubanki mene bayayi naga chacha yake yi
tun yana matashi yake chacha har yanzu bai daina ba,shine kika taho munafunci gidan
masu aure zaki rusa musu aure dama haka kuke yi kuna ziga mutane,Sadiya Tsoro taji
tace kayi hakuri,bazan hakura ba cewar Sahil,mijinta yana can ya tafi nema kinzo
kina munafunci zaki ziga masa mata,Belt dinsa ya fito da ita nan take ya zugawa
Sadiya daya,ta saki ihu kafin ta shanye ya kara mata,yace gobe kya kuma zuwa gulma
gidan wasu yaci gaba da zuba mata belt ta ko ina tana ihu tana rokonsa, gashi ya
tare hanyar fita,da kyar Islaha ta bude mata kofa ta fice da gudu ya taka zai bita
Islaha ta rike shi tana dariya,Maheera ma data fito dariya take tace wlh ka
birgeni,yace ai laifin ki ne da jaye jaye.

Tunda Sohail ya tafi sam ko time din waya baya samu,Maheera duk ta damu kanta
ita ya daina sonta,gashi har an kwashe 5days bai dawo ba,sai a kwana na shida ya
dawo yana dawowa yace zasu tafi Dubai next week,Maheera ta fashe da kuka wiwi a
bedroom,Sohail ya fito daga wanka yace menene Sweet? Me ya faru?

Ni wallahi wannan kudin ya ishe mu rayuwa me ake bukata ga gidan zama kana
aikinka daidai misali,muna ci muna koshi Alhmdllh yanzu ace wannan bai isa ba,shike
nan an dauke min mijina waya ma ta gagara,kana can zaka dinga yawo a gari mata
shike nan daga nan wata ta ganka ni na shiga uku na lalace.

Sohail yace kwantar da hankalinki Sweet kince zamu haihu wannan kudin fa mu nake
nemawa neman da nake yi dan wa nake yi? Shekara da shekaru tunda muka taso a bauta
muke da wahala ana neman aiki sanadinki na samu aiki gashi munyi aure to mene dan
an kara nema wasu kudin sabo da rayuwar gaba mu samu muji dadi da yaran da zamu
haifa gaba,Maheera tana kuka ta sakko kasa ta zauna zaman dirshan ta cire dankwali
ta jefar,gashinta da ya sha gyara yana sheki ya bayyana,tana ni dan Allah ka hakura
wannan ya ishe mu muna zaman mu kullum ni bana so kayi nisa,okay...okay...to nace
kayi min ciki na samu na cika gidan nan da yara idan ina ganin yarana ko zaka yi
tafiya bazan damu sosai ba,kace ba yanzu ba na rasa inda kasa gaba tsakani da Allah
ko tabani baka yi kuma shine dan kulawar ma yanzu ka samu canji sai dai kasashen
waje wallahi Allah ni bana so dan Allah ka tausaya min ,Kafafunsa ta rike tana
kuka,Sohail ya tsaya yana kallon ikon Allah ta haukace gaba daya.

Yace na dade ina ji ana cewa muna da aljanu ashe ba mu kadai bane,yanzu daga
tafiya sau daya? Wasu matan mazajen fa wasu sai su kwashe 6months basu zo gida ba
kuma suka hakura,mikewa tayi tsaye ta rirrike shi ni bazan iya ba,ba irinsu bace ni
na saba da mijina kullum muna tare sai dai a barni ni kadai dan Allah ni wannan
aikin kwai jaraba zai rabani da mijina Allah ya isa tsakanina da Alhaji Saminu.

Sohail girgizata yayi yace mene haka kwaya kika sha ne? Tana uban kuka ya zaunar
da ita yace dan Allah mene haka ne? Kinki fahimtata,bawan Allah ya bani aiki ya min
abin arziki sai ki zage shi kamar bakya so na,ki kwantar da hankalinki babu wacce
zan so ba wacce zan kula in kika ga na kula wata sai kaddara idan Allah yayi zan
kara aure,Maheera kasa ta zamo wayyo na shiga uku a hanya zaka hadu da wata garin
jarabar yawon aiki shike nan kishiya zaka min,ashe har kana tunanin kara aure ban
sani ba.
Sohail tagumi ya zuba wajen lallashi ya bata komai,gani tayi duk ransa ya baci ya
shiga damuwa,sakkowa tayi kuma tace to kaje na hakura dan Allah karka kula wata ka
dinga bani kulawa ko a waya waccen lokacin bana samun jin muryarka,Murmushi yayi
yana kallonta yace to kiyi hakuri zan gyara Inshaallah ki daina wannan borin haka
duk kin birkice kalli yanda kika hada gumi,duk a kaina kike wannan? To ba sonka
bane ya jawo nifa zan iya mutuwa a kanka,Sohail yayi dariya yace baza ki mutu bama
inshaallah sai nayi kudi munji dadi mun haifo yara kin aurar da yara suma yaran sun
haihu wanda aka haifa ma sun haihu,Maheera taji dadi ta rungume shi tace wayyooo
duniya ta....dariya yayi yace Baby...hannu ta yarfe tana jin kunya tace kana fada
sai naji kamar na sume ,kana fasa min kai,yace to abincina, fita tayi taje ta kawo
masa,Yace gobe zamuje kauyen su Islaha kafin na tafi Dubai,Yana ambatar tafiya
Maheera ta zuba tagumi,kin san ina sonki ba wata wacce zan kula,tace to ai ni
caring din please ni a kulani,yace to yana murmushi,abincin ma a baki take
bashi,yana mamaki a duniya shi kuwa da me zai biya Maheera,bashi da kudi ga halin
da yake ciki amma take masa mahaukacin so haka.

A ranar Sahil waya kawai yayiwa su Kawu Nafiu yace suzo za a kai kudin
aurensa,Ba ko musu suka ce muna tafe gobe,Sahil Address ya tura musu yace mu hadu a
kauyen zan tura muku kudin mota kar ku bata mana lokaci sannan idan kunne yaji jiki
ya tsira,su Kawu Nafiu da sauri suka ce ba damuwa.
Daddy ya kira,ya sanar masa yace to fa muma kuma Allah yayi zamu daure mu ja daya
ciki,Daddy yace ban gane ba ku ja daya wanne lokaci kuma? Yace aure nima
zanyi,Daddy ya ja tsaki yace a gidan ubanwa zaka saka ta a wannen gidan karami na
Sohail? Arna ne ku daki uku da palo kawai, Sahil yace sanda kayi auren fari naga a
gidan haya ka zauna daki ashirin da uku a gida daya,kowa daki daya daya,Mama Asmau
babu layin toilet da bata sha ba.

Daddy yace kaje kayi ba ruwana,Sahil ya furta dama kawai fada maka nayi ba wai
wani abu ba,to kaje Allah ya taimaka,Sahil yace Ameen matar sunanta Islaha yar duma
duma ce ma,ko kai ka ganta sai ka karar da dukiyarka a kanta,Daddy yace ni ina ni
ina yarinya ma da har zan karar da dukiyata a kanta,idan ma kana so baza ka samu ba
dai cewar Sahil,Kwafa Daddy ya ja,yace to me kake jira ka kashe wayar mana,da
kudina to a ciki cewar Sahil,"Daddy"yace na'am da masifa ya amsa,Sahil yace akwai
wata Hajiya Kulu me tuwo tuwo a tasha ta dace da kai wlh da zaka aure ta da ka huce
takaici,Daddy wayarsa ya kashe yana masifa me tuwo tuwo lallai yaran nan sun
rainani kamata da arzikina wanda a yanzu zan iya auren irin matan su hudu ma yara
yan mata,amma yazo ya fada min wata Kulu me tuwo tuwo da kuwa nayi asara.

Washe gari Sohail da Sahil suka tafi Taraba a motar haya,Islaha tana gefen Sahil
minti kadan ya kalleta ko motsi tayi sai yace mene ne? Me kike so? Itama Islaha duk
ta haukace irin Maheera soyayya ta gigitata,ga Maheera sai ziga Islaha take akan ta
auri Sahil tayi sauri.
a can suka samu su Kawu Nafiu,an gansu a motar haya ba wanda ya kula su a gindin
bishiya suka zauna,suma su Twins ba a motar gida suka je ba ga Islaha anje da ita.

Gidan Lalai ta musu jagora suka tsaya a waje Islaha ta shiga da Sallama,a
tsakar gida ta iske Lalai kwance saman tabarma hannayenta biyu a ruruce amma sunyi
sauki ta shanya su iska na fifita su.
Tana ganin Islaha tsoron Islaha ya kama Lalai,tace Islaha...ta mike da kyar tace
sannu da zuwa Islaha,Islaha tayi mamaki tace me ya same ki Lalai? tace mutanen boye
ne labari sai an zauna,Islaha tace da baki nake fa.

Lalai tana daga zaune da daura kirjinta zanin ma ya warware ya dawo cikinta nono
rabebe ana gani kamar takalmi yaraf a kwance,Islaha ta manta da nonon Lalai a waje
ta kira baki tace ku shigo,Lalai ba hannun da zata gyara zaninta,Sahil ne ya shugo.

Kallo daya yayiwa Lalai sai ya koma bayan kawu Nafiu yana ta kyalkyala
dariya,Sohail bai sani ba ya wuce gaba shima yayi arba da nonon Lalai,baya ya dawo
bayan Kawu Tukur yana ta dariya,yace Allah ya so ni na Matata chakare chakare
ne,Sahil handkerchief yasa a bakinsa ya cusa a ciki wai dan kar sauti ya fito.

Sohail yace mudai ba ruwanmu su Kawu Nafiu nake ji dai dai suce kar su
kyasa,Kawu Nafiu sai yanzu ya gane abinda suke yi,da sauri yace Allah ya kiyaye ko
ni na wuce ajin wannan me zan kalata a jikinta,bare kuma ni cewar Kawu Tukur.

Lalai ko a jikinta dake mutanen kauye ne,suka zauna a sabuwar tabarma,Sohail da


Sahil sun kasa boye dariyarsu sai dariya suke suna kallon juna,Lalai ce tace Islaha
miko musu ruwa mana,Sahil ya kalli Kawu Nafiu ya toshe bakinsa da hannu yace
kaiiii....yana dariya,a sace kawu Nafiu ya tsawatar musu ya dinga musu signa,Sohail
ne ya gaji da gani yace Islaha mu bamu saba ba azo a suturta nonon Iya.
kai ubanka kawu Nafiu ya zungure shi yana zaginsa kasa kasa.
Sahil yace Iya Lalai taci daka rannan,ai nine nan....ya karasa da dariya...dama
nace sai ta kwana tana daka,Lalai ido ta zaro,Sohail yace yes yin mune,shuru tayi
dan bata san kan abin ba.
Kawu Nafiu ne ya katse zancen suka gaisa da Lalai Islaha tana daura mata zani
Sahil yace Allah wannan kadai ya isheka comedy...Sohail yace sai ka kwana kana
kallon abinka kai ta dariya wallahi, wai Nonon Lalai suke nufi,Islaha ita kanta
dariya taci karfinta ga dariyar nonon Lalai ga na su Sohail.
Abdulrazaqu ne ya shigo yace wa nake gani kamar Islaha yau sai na tattaka ki a
gidan nan,shine kika mana asarar kudi sabo da ke yar iska ce yanzu kin lallabo kin
dawo a ciyar dake,shegiya tambadaddiya ke kam kinyi asara,yar tsiya a haka zaki
kare,ace yaro me kudi kamar Ibrahim,to ki sani har yau muna kan bakanmu Ibrahim
zaki aura me ruwan nairori,shi muke so shine zabin mu.
Lalai kuwa sanda take daka ita tasan me ta ji me ta gani,sai faman cewa
Abdulrazaqu take kai kayi shuru dan ubanka amma sai faman masifa yake ko bakin ma
bai kula da su ba,tun a waje yaji mutane na labari Islaha tazo shine ya taho da
masifarsa.

Free page 1&2 400 ne

0175487861
Asmau Garba Muhammad
Gtbank

AsmaBaffa
08061929616
[7/17, 3:18 PM] Asmabaffa: 🪸MUMMUNAR DABI'A 🪸
46-50

Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA NE GA 'YATA TASNIM

Page naki ne
MARYAM T BALIYA

MASU AUDIO BAN YARDA WANI KO WATA YA JUYA MIN NOVEL BA IZINI BA.

Sohail zaiyi magana Kawu Nafiu ya hanashi da sauri yace fadan yan uwa ne ba
ruwanku da shi,neman aure muka zo ku bari dan Allah muyi lafiya,shuru suka yi.
Lalai ce tayi magana tace marabanku lale marhabin sannunku da zuwa,Islaha baki muka
yi ne daga Amurka? ko kuwa daga ina an bar ni a duhu?
Su Kawu Nafiu ne suka gaishe ta sannan ya mata bayanin abinda ke tafe da su,yace
kuma Alhmdllh yaro da yarinya munga sun daidaita kansu shine muka zo a hada mu da
iyayenta maza domin shi neman aure da maza ake yinsa ba mata ba,Sohail yace kwarai
kuwa yafi inganci ma,Islaha dai ta shige daki taki fitowa wai ita kunya,amma ta
rabe a jikin bango tana jin me ake cewa.

Abdulrazaqu yana tsaye kerere da rigarsa ta gona dukun dukun ya furta mu baza mu
bawa kowa ba sai Ibrahim mun rigada mun masa Alkawari shi zamu bawa,Islaha ta
Ibrahim ce,Kawu Nafiu yace to ai mun ji labarin zuwan Ibrahim, abinda yayi Ibrahim
shi yayi Sahil gasu kannensa ne uban su daya,kuma dama Islaha budurwar Sahil ce tun
farko Ibrahim neman fada ne ya kawo shi.

Abdulrazaqu ya dora hannaye a kai yace yanzu na tabbatar 'yan uba masifa ne shi
yasa na godewa Allah da Lalai kadai Mahaifi na ya aura har ya koma ga Allah kuma ni
kadai ta haifa,Sohail ne yace kai lallai living thing ne babba yanzu kai kadai ta
haifa dama duk kaine ka dawo mata da nono haka sai kace inji ne a bakin ka sai kace
ta haifi yara ashirin,Kawu ne ya bigi Sohail,Sahil yace dama tun tana budurwa bata
yi farin jini ba babanka ne kadai yaje zance shima sai da kyar abokai suna ziga shi
lokacin tana tallan Alkaki.

Lalai tace wlh tunda nake ba kowa yasan zamanin da nayi tallan alkaki ba amma kai
aljani ne wlh wannan ba mutane bane ku tashi ku tafi wajen Iyayenta maza,bazan iya
ba dama tunda naga kyawunku haka naji a jikina ba mutane bane,Kawu Nafiu ne ya
wayance yace tsokana suka yi abin ne yazo a daidai ba haka suke nufi ba, Lalai ta
dan saurara a tsorace tace ina jinku,Kawu Nafiu yace kawai a raka mu wajen mazan.
Abdulrazaqu yace bazan je ba ita da take son auren ta taje ta kaiku ya juya tare
da ficewa.

Islaha ce ta fito daga daki Sahil yace a nan kika zauna kenan? Ina turmin
dakan? Islaha ta nuna masa,yace kinyi kokari gaskiya tafiya suka yi ta raka su
gidan Baffa Gali,ganin su Sohail yayi Imani akwai kudi da sauri ya kira maza uku a
dangi yace suzo anzo musu da maganar aure,har ya manta da Ibrahim,Kawu Tukur yace
Sohail da Sahil su basu waje su jira a waje,sabo da baza su bari ayi abin kirki
ba,suna mikewa Matar Baffa Gali ta fito dauke da danta a hannu ta zaro nono ta
gaban riga yaron yana dauke a hannunta bakinsa yana a nonon yana shan abinsa.

Sohail ya kalleta ta wuce bagazan bagazan ba wani tafiya ta nuna macece,tace


sannunku ta wuce, Sohail yace kai jama'a zanje na gwada akan Maheera, kun ganta da
Danta bata daina haihuwa ba ai na zaci tsohuwa ce,Kawu ne ya harare shi,Sahil yace
wato dai na fahimci a garin nan nono bashi da daraja da kima abin banza ne,Baffa
Gali yace kuma dai kwa fada nayi nayi ta gyara taki matan kauye sai hakuri.
Iska ce ta taso filfil Sohail yana boye dariyarsa yace iska tana ta fifita shi,wai
matarka ce? Baffa Gali yace ae me dakina ce,Sohail yace tab sannu,kuma idan ta wuce
kana jin ta birge ka a haka? Kawu ne ya kore su nace kuje waje zan neme ku.

Fita suka yi kofar gida Islaha tana ciki wajen matan Baffa Gali,wasu yan matan
kauye ne suka fito su uku suna tafiya,sai kallon su Sahil suke yi,Sohail ya kalle
su suka hada ido da sauri suka dauke idon su tare da karawa tafiyarsu sauri,Sohail
yace kai kuzo nan,a tsorace suka karaso 'yan matan,pic din Maheera dake kan wayar
sa ya nuna musu yace kunga wannan? Suka daga kai ae suna dariya suna jin kunya,yace
Sunanta Maheera duk duniya ba irinta a yanzu,kun san record din data kafa? ta kafa
tarihi babba,domin itace wacce ta aure ni,Dariya matan suka yi,sun zaci wani babban
abu zai fada da ta kafa tarihi a kai,Sahil yace ba kwaila bace irinku kuma,matan
suka ji kunya suka fece da gudu,suna cewa kinji kamshin su kuwa,rabewa suka yi suna
lekensu ta bayan bishiya, baki Sohail ya tabe suka ci gaba da hirar su da Sahil.

Baffa Gali da wuri suka Amince suka ce su ko yaushe suka shirya ba matsala su
saka ranar daurin aure,gani suke su Sohail wasu attajirai ne,sai da suka fito suka
bawa su Sohail labari yace ku fada yaushe kuka shirya? Sahil yace yanzu ma a
daura,Kai shashasha rana za a tsayar su sunce wata biyu,Sahil ido ya zaro yace zan
iya mutuwa sauri nake wata daya kawai zan iya hakuri, a matse nake Kawu bana
bacci,Kawu ya zaci irin sha'awar nan ce ta damu Sahil harda daukan abin da
muhimmanci yace to Inshaallah bari a fada musu.

Ya koma ya sanar musu,suna ta jira a basu kudin aure da komai su hau kai su
danne sai da aka kira Sohail aka fada masa har sadaki da komai suka ce million
daya,Sohail yace komai da komai? Suka ce ae mu yaran mu tsada ne da su,ba ragi?
Cewar Sohail,suka ce ba ragi,yace ku duba mana ko dubu hamsim ku kankare,ba kudi ne
damu ba kyawun ne kawai,suka ba ragi daga haka, yace ba matsala ya za muyi zan
tura mata a account.

wani dukul suka ji,Baffa Gali yace ai iyaye ake damkawa, Sohail yace akan na baku
bacci ya gagare ku gwara ku bari a bata abinta, kuka karbi kudin nan baza ku ji da
dadi ba da kanku zaku dawo da su, Baffa Gali ya zaci kara zasu kai su wajen yan
sanda irin ai zasu je wajen malamai su rufe musu baki sunci banza,nan take suka ce
ba matsala,Sohail yace akwai me account? Baffa Gali yace ina da shi,nan take ya
bayar aka tura masa,sai washe baki suke banza ta fadi.

Sallama suka musu suka fito,Baffa Gali yace munci banza yau zanje wajen malam Idi a
rufe musu baki babu wanda zai tambayi kudin,har Islaha baza ta taba bude baki tace
ina kudin aurenta ba,dariya suka yi Gali yace ai ni ko aron gona na karba ta mutum
to da kanka zaka zo ka siyar min da gonar, idan kuwa kudi na karba bashi to sai dai
a lahira na biya suna ta dariya.

Kawu Nafiu ne bayan sun fito yace ni naga saurin yardar su babu ko bincike sam
sam,basu san wa zasu bawa 'yar su ba sun yarda,wannan yarinya bata da gata wlh,ace
ba bincike kawai sun karbi kudin aure har an sa rana, Sahil yace sun taimaki kansu
da suka yarda badan haka ba duk sai sun kwana akan kayoyi yau.

Islaha tana fitowa Sahil yace Amarya kusa da su ta karasa tana murmushi,Sohail
yace an tura musu kudin aurenki komai da komai million daya kudina yanzu saura
kadan a accnt kin kara min arziki na dade ina tarawa.
Hawaye Islaha ta fara ta rike Sahil tana shagwaba
Allah....Allah...ni...uhmmmm...ya za ayi ku basu kudin...baza fa su bani ba...Sahil
yace wayyo Kawu dadi shagwaba,Kawu da sauri suka yi can gaba sunji abin na twins ba
kunya.

Kawu Nafiu,yace ayi sauri a aurar da Sahil wlh sai yayiwa yar mutane ciki bashi
da kunya, Kawu Tukur yace yanzu watakil da kake gani Matar Sohail watakil ciki ne
da ita,kasan irin yan shashashun yaran nan wlh sunfi kowa shegen sha'awa da son
mata,Kawu Nafiu yace baka gani ba nonon tsohuwa ma kalla suke.

Sahil yana wani Lallashin Islaha tace ya za ayi ku basu kudi kun san baza fa su
bani baaaaa.....ta karasa da kukan shagwaba,Sohail yayi dariya yace ka fara shiga
Masifa Sahil,ina nan ina fama da Maheera zaka gane aure ba hutu a cikinsa.

A haka suka koma gidan Lalai,Baffa Gali har da sawa a biyo su da fura da nono har
gidan Lalai,ga abinci rogo dafaffe da kuli,Lalai tana jikin bishiya inda suka barta
zani ya sake sutalewa ya koma kasan ciki,Sahil dariya ta kamashi yace muna ta zuwa
a sa'a,Kawu kalli suka sake sakin Dariya,Sahil ya juyo ya kalli Sohail yace yayi
malafa da shi.

Lalai tana kallon su aka kawo musu rogo da fura taga Ibrahim ma ko ruwan su bai
sha ba bare yaci abincin su,Sahil ne ya bude kwanon ya dauki sandar rogo fari tasss
da shi ya dafu sosai,Sohail yace kawu ga takwarar mu kawu rogo wlh,Kawu yace
takwara kuma waye me suna rogo anan? Sohail yace kawu ta wandonka ko basa kama irin
tamu ce dukkanmu maza suna kama data wando,Kawu ya dauki kwanon rogo daya yace muje
Tukur muje daga waje wannan yaran sai su kunya ta mu.

Sohail sunci iya rogon kawai,suna ta satar kallon Lalai,tace amma a nan zaku
bar Islaha har lokacin aure,Sahil yace ae da jakarta ta taho ma ai,tana nan sai an
daura sai na tafi da abata,Lalai tace hmmm kai ko kunya babu? Sahil yace ba gwara
ni ba iya a baki ne ba zani na saki ba kirji waje, shuru ta masa sai da suka yi
sallar la'asar suka tafi,a cikin gari zasu kwana sun kama hotel,Sohail ya kira
Maheera yana kwance a room dinsa yace sai gobe fa muna hotel,tace tsoro nake ji
fa,ba kowa kuma baka fada min ba sai yanzu dare yayi bare na kira Juwairiyya tazo
mu kwana tare,Ko na tafi gidan Aunty Aisha tunda dare baiyi ba yanzu nayi sallar
Isha? Da kyar ya amince ta shirya ta tafi gidan Alhaji Saminu.

Aunty Aisha tace sannu amarya yau ina da babbar bakuwa,Maheera tayi
murmushi,dakin da zata kwana ta kaita tace to abinci fa? Maheera tace Alhmdllh naci
kafin na fito,duk da haka sai da Aunty Aisha ta kawo mata.
Har part din Alhaji Saminu ta rakata suka gaisa sannan suka dawo dakin suna ta
hira,Aunty Aisha sai labarin magungunan mata take yiwa Maheera,Maheera bata ma
sansu ba,tace wai ke bakya amfani da ko wanne ne? Maheera tace uhm ina Amarya Aunty
Aisha,ni duk wannan shaye shayen ba yi nake ba tukun tunda ba abinda muka yi har
yau.

Ban gane ba? Maheera tace ko romance bamu taba yi ba to da alama ma bai san me
ake yi ba,Aunty Aisha ta rike baki tace duk uban soyayyar nan? Sannu Maheera Allah
ya miki Albarka da wata ce wlh da yanzu anji kansu,kuma wai suna karatun Qur'ani da
adduoi kuwa? Aljanu basa son me nacin karatun Qur'ani suna barin jikin
mutum,Maheera tace kullum sai sunyi wallahi ko da dare ko da safe,Azkhar ma baya
wuce su sabo da wacce ta rike su ta dora su a hanya.

Aunty Aisha tace kina addua kema? Maheera tace sosai kullum cikinta nake Aunty.
To ya kina nuna masa yanda abin yake? Nayi nayi yaki fahimta jikinsa ma bai so na
gani ba sutura,Aunty Aisha ta jinjina kai tace to fa,ikon Allah mu dage da musu
addua inshaallah zasu dawo dai dai cewar Maheera.
Washe gari da wuri ya kira Maheera yace ta koma gida,haka ta koma ta gyara
gidan tayi girki sabo da suna hanya.

Bayan sati biyu Maheera,Islaha da Aunty Aisha su suke shirin biki abinsu amma
Sahil yace ba abinda za ayi kawai aure za a daura su taho da Amarya,yanda aka
hadawa Maheera lefe haka aka hadawa Islaha.
Alhaji Umaru ne ya kira Sahil yace ya fara zuwa Office za a nuna masa aikinsa zai
fara,sai murna yake,bayan kwana biyu ya fara zuwa katafaren Office dinsa,kansa
wajen da Sahil yake aiki abin kallo ne.
Alhaji Umaru ne ya bawa Sahil gida katafaren gaske part biyu sama da kasa ko
wanne part,yace gudunmuwar aure ce su koma ciki shi da Sohail kowa da part
dinsa,amma komai iri daya ne a ciki abinda ke wannan part din shine a can,sai ka
rantse ma a daya kake ba babanci har komai na kitchen da furniture.
Kayan abinci an zuba,gidan ya sha fulawoyi da interlock ga wurin parking daban na
motoci,Sohail gidan da suke ciki sai dai a bawa wasu haya.

Islaha tunda taje ba wanda ya bata sisi a kudin aurenta,Lalai tsoro take ji bata
iya cewa Islaha komai bata ma iya sata aiki sai dai idan tayi girki Islaha tana ci
sai ta dinga gallawa Islaha harara,ko bi ta kanta Islaha bata yi sam.
Sahil yau ya kira Islaha yace yaya sun baki kudinki kuwa? Islaha tace sisi basu
bani ba,Sahil yace to kyale su karki tambaya kinji,tace to dan Allah iyaye nane
karka musu komai yace ba abinda zai faru ai.

A daren cikin dare Baffa Gali yana tsaka da bacci sai yaga an daga shi sama sai
ya tabo rufin kwano sai a sake shi ya fado saman tarin wata kaya,kayoyi ne cako
cako kamar Allura haka ake masa kawai,ihu yake da kururuwa mutane suka cika gidan
cikin dare ba a ganin kowa ba a wanda ke ganin wasu kayoyi a wajen,sannan ba a
ganin Baffa yana tashi sama amma Baffa Gali Ihu kawai yake da kururuwa a
kwance,jikinsa duk yayi bula bula kamar an caccake Allura,yana zan bata kudinta
wallahi ban cinye ba na tuba,yanda aka yiwa Baffa Gali shima haka sauran duk wanda
suka ci kudin nan ba wanda ya kwana lafiya,Amma Abdulrazaqu shi yaci banza duk
zagin da yayi ba abinda aka masa.

Da sassafe sai ga matar Baffa Gali da kudi a katuwar leda ta kawo gidan Lalai ta
damkawa Islaha tace gashi nan ki irga kwandala idan babu kiyi magana dan Allah inji
Baffanki Gali,yanzu suna asibiti duk an tafi dasu,anya Islaha ba Aljanu zaki aura
ba?
Islaha tace me ya faru da su? Lalai ta fada saman gado ta kudundune tace kudin
Aljanu a dakina ku fitar min da shi,na dade ina tunanin Islaha da Aljani take
soyayya,wlh ni nasan me na gani sanda na kwana ina daka,Islaha tayi dariya ta more
tace Lalai duk son kudinki ga dubu ashirin ko kifi kya ci,Lalai tana lullube tace
Allah ya kiyaye, Islaha ta ja kudi ta boye kasan gadon Lalai,Lalai ta fice da gudu
ta bar gidan,tun daga ranar Islaha kadai ke kwana a gidan, Lalai ta koma gidan
dangi sabo da akwai kudin Aljanu a dakinta.

Yau Sahil yana Office wani Hakeem shima babban ma'aikaci ne yazo ya bashi key
din sabuwar mota me tsadar gaske yace ta zuwa aiki ce dama suna bawa mutum mota
yawanci.
Murna wajen su Sohail ba a magana.
Biki yana ta kankama kamar wasa nan ma Daddy sai Iv ya gani kawai an kuma saka masa
marigayi,baiyi magana bama yasan halin su.
Ana gobe daurin aure Ibrahim da Adnan suka bar gari ma gaba daya suka wuce kasar
waje sabo da kar ma suje.

Ango ma ba wata gayya da suka yi,mudassir yayi yayi suyi gayya suka ce sun gaji
da biki ba a dade da yin na Sohail ba,ba a fi wata biyu da wani abu ba baza su
wahalar da mutane ba,mutane yan tsirari ne suka je daurin auren,Islaha dai gyaran
jiki sai ta dawo birni za ayi mata,tana can zaune gidan Lalai ita kadai kama
mayya,kowa tsoronta yake ji zance ya watsu Aljani zata aura.

Ana gobe Maheera da Aunty Aisha suka tafi can ,suka samu Islaha ba abinda ya
shafe ta a dangi duk an guje ta sabo da tsoron Aljanu,ita kadai ta hado cefanenta
ta dora katuwar tukunya wai miyar biki zata yi,Maheera suka dinga dariya,Komai na
girki ta tanadi abinta a cikin kudin auren ta iba,Aunty Aisha tace me zan gani
haka? Dariya Islaha tayi tace to sunki zuwa gaba daya dangina sun gujeni,wallahi
kowa naje har gida na fada musu gaba daya dangin uwa dana uba duk na fada musu har
makwafta duk sunce baza su zo ba,gidan Baffa Gali har rokon su nayi mazan dai sunce
za a daura aure da su a bisa laluri,Maheera suka shige dakin Lalai suna ta mamakin
kalar kauyen da gidan da Islaha take,kayansu suka ajiye suka fito,Islaha har girki
tayi musu suka ci abin su sannan suka fara girkinsu su uku rak,Maheera da Aunty
Aisha masifar Tausayin Islaha suka ji wai ita kadai a gida,ga dangi ma ace an rasa
me zuwa biki,Aunty Aisha tace Allah wadaran wannan dangi naku,baki mori yan uwa ba
wlh,tace uhm.
Sai da suka yi nisa dare yayi suna ta aiki sannan matan su Baffa Gali suka zo,sai
makwafta suma suka yi shahada suka shugo,ana yin sallar isha suka gudu.

Su uku suka yi miyar su ta taushe da tuwon shinkafa da safe sai farar shinkafa
da miya an yanka cabbage daban,pure water aka siyo da yawa,kafin yan daurin aure su
iso sun gama komai sunyi wanka,Idon Amarya duk ya tasa sabo da hayaki.
Sai 12 angwaye da su Daddy suka zo Daddy sai tsaki yake yana korafi,a rasa inda
mutum zai nemi aure sai wannan kauyen.
Sohail,Ango da abokai suna motar su sai nishadin su suke yi,Ango yace yau Islaha
shike nan sai abinda nace da ita kuma,Sohail yace uhmm zaka gane kurenka ne.

Sai 2pm aka daura bayan an idar da Sallah,ana daurawa Sahil ya mike yace ku
tashi abinda ya kawo mu ya kare an gama,Daddy ne ya ja babbar rigarsa wai yayi
shuru,Sohail yace yau ba ruwanka Ango lukwi cikin bargon ku,Baffa Nafiu ya harare
su,Mutanen kauyen sai sallallami suke angwaye yan iska ne.
Amarya Islaha ta zuba kyau duk da haka sabo da a cikin na lefe Maheera ta dakko
mata leshi dankarere milk and brown tayi kyau sosai,kayan lefen dama suna gida
Abuja,Sai da aka daura sannan Lalai tazo,ita da gidanta amma ka rantse bakuwa
ce,suka bata abinci tace o.o.o aci dadi lafiya Allah sanya Alkhairi,Maheera tace
haba Lalai,fafur taki ci,tace wlh bazan ci ba cikin dare a yaga min bakina biyu ba
ruwana,sauran yan garin almajirai da maza ne kawai suka iya cin abincin bikin
Islaha duk anki ci kowa tsoro yake ji.
Dan gidan Baffa Gali ya karbo shinkafa da miya zai shiga da ita Baffa Gali ya dawo
daga wajen daurin aure ya gani yace kar ka soma shigar min da ita gida,kana gani
har yanzu ban warke ba karfin hali kawai nake yi duk jikina a soke yake,fitar min
da masifa daga gida ya kori yaron da abincin.

Sahil shi ya yarda anyi pics sai kallonsu ake yi har abincin sunci abinsu,Daddy
tuni sunyi gaba sun bar kauyen,sai Mudassir,Sohail da Sahil,ga motar tayi musu
kadan tunda zasu taho da Amarya.
Aunty Aisha ce kadai a gaban mota,Muddassir driver,Sahil da Amarya a
baya,Sohail da Maheera suma a baya motar ta matse su,Sahil yace Amarya ta dawo
cinya zamu fi samun Space,Islaha tace a'a zamu je a haka,Sahil yace zanyi fushi
mala'iku su tsine miki tun daga taraba har Abuja,tashi tayi ta zauna a cinyarsa da
kyar yace yawwa Tallaja.

Mayafinta ya gyara mata suka tafi,Lalai ta leko taga mota ta tafi ta furta
jaraba sun tafi ta koma gidanta ta duba kasan gadon taga sun kwashe komai tace yafi
sauki.
Sahil yace ayi sauri Allah ya kaimu lafiya yau akwai kara'i,Maheera tana kallon
Sahil sai zumudi yake shi da Alama yasan kan gari,tausayin kanta taji,Sahil kana
kallonsa har ya canja yanayi shi idonsa ma ya canja zallar sha'awa ce kawai a
ciki,Islaha sai zare ido take yi a cinyarsa,cikin dare sosai suka dawo,Aunty Aisha
suka fara ajiyewa a gidanta sannan Muddassir ya tsaya nan ma ya musu siyayyar kayan
makulashe har da nasa da zai kai gida,da na Sohail ga kuma na Ango daban,har gida
ya sauke su ya musu sai da safe suna ta masa godiya suka wuce ciki.

Maheera tace wash na gaji,Sohai ya dauketa cak yana murmushi suka wuce part
dinsu.
Ango yana rike da Amarya a part dinsu suka wuce bedroom,Islaha tace ina dakina?
Yace yau fa ke ake jira malama dama a fara soyayya,Islaha taji tsoro tace da
gajiyar hanyar? Sahil yace to mene a ciki a kwanta tare a tashi,Islaha tayi dariya
ta zaci wani abu zasu yi babba sai taji ma wai kwanciya,yace ke Taskira zan gani
yau,ni ba abinda zan miki gani kawai zanyi,gani dai ba ci ba,murmushi tayi ta shiga
toilet.
Tana shiga Sahil yaga kiran Daddy,a hakan ma Daddy yafi kiran Sahil sabo da
gani yake yafi hankali,Sahil ya daga yace da dare haka sai kace anyi mutuwa? Daddy
yace Mahaifiyar ku ce tazo Nageria tana Airport yanzu haka a nan Abuja kuje ku
dakko ta gidanku,ta dade tana fada min zata zo ni na manta ma,Sahil yace Mahaifiya?
Ashe zata daskare a airport kuwa ina angon zanje dakko ta na santa ne ni,Daddy yace
ba fa wasa nake ba,uwa uwa ce kun sani Allah zai tuhume ku idan har kuka
wulakantata,kuje tana airport zaku ganta baturiya ce wata bushashiya me dogon
wuya,Sahil yace bushashiya me dogon wuya?Daddy yace ae,yace to zamu je,ya kashe
wayar,Islaha tana fitowa a wanka ya fada mata yace ance wata bushashiya me dogon
wuya, tace to kuje mana tana boye dariyarta,ya kira Sohail ya bashi labari Sohail
yace Bushashiya me dogon wuya muje mu ga zahiri,Maheera ya sanarwa.
Motar Sahil suka shiga suka tafi,suna ta nanata bushashiya me dogon wuya,har suka
je suna dube dube a wajen,Sohail yace Bushashiya me dogon wuya tana ina,can ya
hango wata batura kuwa dattijuwa karmashashiya ga wuya zololo,Sohail ya kalli Sahil
zasu yi dariya,Har inda take suka je,Sahil ya fara dariya yace Allah ya so mu bamu
yo kama da ke ba.

Baturiya tana kallon su ta gane su,sai washe baki take tana faman kallon su tana
hawaye,tazo zata rungume Sohail ya matsa da sauri yace inaaaa... Maheera yau sai ta
kwana tana kuka,da turanci tayi magana kasancewar bata jin hausa sai gaisuwa ta iya
shima dan ta taba auren Daddy ne,tana ta musu turanci sai suce su basa jin turanci
in ta iya hausa tayi in bata iya ba ta kama bakinta kawai,tana ta faman magana da
turanci shuru,da kyar dai Sohail ya danyi turanci yace su basa jin turanci wacece
ita ance babarsu ce,tace ae itace, Sohail yace ga kudi dai zamu baki kyauta ki koma
amma karki kara cewa ke uwar mu ce,mu bamu da wata uwa,rokon su ta fara su yafe
mata,Sahil yace wlh baza mu yafe ba,sai Allah ya tuhume ki a lahira,shuru tayi sai
kuma ta fara tambaya Muslim? Muslim? Wai musulmai ne?
Sahil yace sallah biyar kullum harda Nafeela,kwana nan zamu tafi makka duk wani
dan bakin ciki sai dai ya gani ya kyale,yaudararsu zata yi Baturiya tace itama tana
son musulunci,Sohail yace a'a kar a shigo mana wlh in ta shigo yanzu taci banza
Aljanna zata je, ta gama kare rayuwarta a club taci duniya da tsinke har ta tsufa
yanzu ta shigo ta wuce Aljanna baza ta sabu ba,Sahil yace Jesus ma ai Annabi ne ko
mu musulmai muna son Jesus kuyi zaman ku kawai,Hausa suke bata wani fahimta,haka ta
shiga mota ta bisu suka nufi gida.

Suna zuwa gida suka ga wasu kartai su uku sun fito daga gidan nasu da gudu sun
haye saman machine sun bar wajen kamar zasu tashi sama,a kofar gate Sohail yayi
parking suka bar Halley a mota suka shiga gidan da gudu,Islaha ya samu tana jan
kafafu a palo ta kasa tashi gaba daya tana uban kuka,Sahil yayi kanta da gudu yana
tambaya lafiya? tace bazan iya tashi ba wlh sun cutar dani,Sahil ya girgizata yana
tambaya me suka yi miki? Su waye,ban sansu ba nima idonta yana rufewa a wajen ta
fadi luuuu ta sume.

Sohail shima part dinsa ya shiga ya iske Maheera ita lafiya normal bacci ma
take bata san me akeyi ba.
Wajen Sahil ya fito da gudu lokacin Halley ta shigo ciki da akwatinta,Sohail yace
ka dauke ta mu kaita asibiti,daukanta Sahil yayi suka nufi asibiti.

Halley harda shiga mota ta bisu,an manta da Maheera tana bacci ma,suna tafiya
mutanen dai suka dawo gidan suka shiga part din Sohail,a firgice ta tashi taga
kartai a kanta su uku suna shirin yi mata fyade,Maheera ta samu waya dake gefenta
ta bugawa wanda ke kokarin cire wando,haukace musu tayi kawai suna kokawa sosai da
su,wani a ciki ya kifa mata mari yafi biyar sai da fuskarta ta kumbura.
Su Sahil har sun danyi nisa a mota,Sahil yace sauke ni Sahil na koma gida Maheera
tana can,Sohail birki yaci ya juya da motar ya sauke Sahil shi ya wuce
asibitin,Sahil yana shiga ya samu ma sun fara cirewa Maheera kaya tana ta ihu.

Duka daya ya yiwa me shirin fyade ya zube kasa a sume,sauran suka ja wanda ya
sume suna kokarin guduwa Sahil yayi kansu ya dinga lodar su kamar zaiyi kisan kai
sai da yaga basa motsi,Maheera kayan jikinta ta gyara,tana hawaye, 'yan sanda ya
kira,suka zo suka tafi dasu sannan ya zauna a gidan tare da Maheera yana jiran
Sohail ya dawo ya dauke su,ba a dade ba ya dawo ya dauke su suka tafi asibitin gaba
daya.

'Yan dabar da aka kama waya kawai aka yiwa yan sanda a daren aka sake su ko
kwana basu yi a Police station ba sabo da suna da daurin gindi,Su Sahil basu san
har an sake su ba ma sun tafi.
Sahil ko magana baya iyayi sabo da tsananin damuwar halin da yake ciki,tsoro
yake ji kar ace fyade suka yiwa matarsa yanda suka yi yunkurin yiwa Maheera.

Free page 1&2 400

0175487861
Asmau Garba Muhammad
Gtbank
AsmaBaffa
08061929616
[7/17, 3:18 PM] Asmabaffa: 🪸MUMMUNAR DABI'A 🪸
51-55

Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA NE GA 'YATA TASNIM

Page naki ne
Baby Ak

MASU AUDIO BAN YARDA WANI KO WATA YA JUYA MIN NOVEL BA IZINI BA.

Asibitin suka koma ana ta kula da Islaha ana bata agaji,bata farfado ba sam har
gari ya waye twins suna asibitin tare da Maheera,suna zaune sun tasa Islaha
gaba,Maheera tace kuje masallaci kuyi Sallah,Sahil yace to sallar ma zan iya
kuwa,addua zaka yi mata ai,Sohail yace muje,fitowa suka yi suka tafi
Masallaci,Sallar nan ba a hayyaci Sahil yayi ba,Maheera a ciki tayi sallah tana
zaune suka dawo asibitin,har 9am Sohail yaje ya musu take away na abinci ya
kawo,babu wanda ya iya cin komai har me siyowar.

Sai can wurin 11am Islaha ta farfado idonta ta bude a hankali tana kallon su
Maheera,Suka koma jikin gadon da sauri suna tambayarta ya jikin,Sahil yace wai me
suka miki ne? Maheera ta kalle su tace da sauki idonta ya ciko da hawaye sannan
tace Allura suka yi min a tafin kafafuna duka biyu bazan iya tafiya ba yanzu,Sahil
yace Innalillahi wa Innailayhirrajun amma akan ace fyade suka miki gwara
wannan,tana kuka tace to ai ba a san Allurar mece ba,watakil ta guba ce suka yi min
mutuwa zanyi shike nan ta karo sautin kukan ta.
Maheera hawayen tausayi ya zubo mata tace baza ki mutu ba inshaallah ba ita suka
miki ba,babban likitan ne ya shugo yana suka fada masa halin da ake ciki,yace ku
tsaya akwai test din da za ayi za san wacce allura ce,nan take yasa aka maida
Islaha wani bangaren daban,test suka yi mata na gaggawa,sai bayan an duba likitan
ya kira su Sohail yace, to gaskiya zan fada muku Allurar da suka mata baza ta sake
iya amfani da kafafunta ba a duniya,kafafunta baza su iya amfanuwa su motsa ba
itace Allurar da suka yi mata,babu kuma wani waje da zaku je su iya maganin abin ko
da kuwa za ace kasar waje ce.
Sahil yace ai ba kune Allah ba zata taka watarana inshaallah ni bazan yarda da
maganarku ba,Allah yana nan zai mana maganin abin,likita yace ina muku fatan
hakan,yanzu a jikinta kalau take lafiya,komai na jikinta zaiyi aiki kafafu ne kawai
sai ku siya mata wheelchair aci gaba da ganin likita kafin aga me Allah zaiyi.

Sahil jiki a sanyaye suka fito Maheera kadai suka fadawa,a ranar suka canjawa
Islaha asibiti wanda yafi wannan tsada,washe gari suma suka yi iya binciken su
abinda waccen likitan yace suma shi suka fada,komai sai dai Maheera ke yiwa Islaha
Sahil yana tayata duk da cewa ma Allah yasa tana amfani da dukkan sassan
jikinta,kafafu ne kawai suke da matsala. har sai da suka zage asibiti sun kai
bakwai duk abu daya suke fada.
Islaha sai da ta matsa sannan suka fada mata me ake ciki,taci kuka da kyar aka
lallasheta,Sahil yace nifa akan suyi miki fyade gwara wannan din yafi min,Islaha
tace gwara fyaden daga ya wuce ai shike nan amma wannan bazan fa yi tafiya ba na
zama gurguwa ina ji ina gani,Sahil ya kalleta yace haka aka ce miki to zaki yi
tafiya inshaallah,Aunty Aisha da Alhaji Saminu sai sintiri suke yi a hanya,Daddy
sun fada masa amma ko zuwa baiyi ba sai waya kawai,su Adnan sun dawo daga tafiya
sunji labari amma ko leke ba a gansu ba,har suka gama yawon jinyar su suka koma da
Islaha gida a Wheelchair Sohail yace InshaAllah nan gaba har kasar waje za a kaita
a gani,Maheera ce ta gyara kujerar Sahil ya dora Islaha a kai suka shiga cikin
gidan.

Islaha ta shiga damuwa matuka,abinta tafi karfi yafi karfinsa,hawaye ne ya


gangaro mata ganin Sahil yayi wankansa ya fito ita kuwa sai dai a kaita a zaunar da
ita,kallonta yayi yana murmushi yace ke komai kuka sai kace baki san kaddara ba ki
godewa Allah kina amfani da hannunwanki da komai kafafune fa kawai,yanzu in na
kaiki toilet komai zaki iya yiwa kanki ai da sauki,a gabanta ya tsuguna tana goge
hawayenta tace ina Amarya yanzu idan ka gaji dani fa a haka wata zaka
auro,tunaninki kenan? Ni da kika aure ni a marar lafiya fa? A haka fa kuka ganmu
kuka iya auren mu baku ji komai ba kuka ce kun ji kun gani sai nine akan lalura ta
faru kuma ba ke kika dorawa kanki ba kawai sai na juya miki baya,ki daina fadar
haka please.
su Sohail ma sun manta da Baturiya tunda ta bisu asibiti ina tayi oho basu ko tuna
ba.
Toilet ya kaita da kansa tayi wanka da brush,ya taimaka mata ta daura Alwala
sannan ya fito da ita har yau bai san ya jikin Islaha yake ba baya kallonta ba
sutura,Maheera ce ke mata komai yau ma sai da ta gama ta daura towel yaje ya tayata
alawala ya fito da ita.
Sallah tayi a zaune ta sha magunguna sai ga Maheera ta kawo abinci a katon
tire,Sahil yace ya zakiyi Maheera hutu bai ganki ba sannu Allah ya biyaki,murmushi
tayi tace wai ina Mummy baturiya ne kunce tazo ina take? Sahil sai yanzu ya tuna ma
yace ni tun ranar ma ban ganta ba,ina tayi ne? Basu san ita tun a daren ta nemi
hotel tayi tafiyarta ba,taga sam basa ma kulata sun manta wajen su tazo.
Sahil yace ai tana da wayo koma ina tayi zata fito ba yarinya bace.

Maheera tace Allah ya kyauta muku to,Sahil yace Ameen jeki to kinga ni nan
Amarya ce,Islaha ta saki kuka tace ni ka daina ce min Amarya haka ake amarya a
nakashe,Maheera ta fita tana dariya,mai ya dakko yace yau zan fara aikina,ni baza
ka shafa min ba zan iya abina,harararta yayi da wasa ya cire towel din juyawa tayi
da sauri ya kifa kansa a saman bed yace bazan iya gani ba,na jawa kaina nayi zaton
shege ne ni ashe ba haka bane,dariya ya bawa Islaha tace tab a haka ake mazajen? Ai
da mata basu yi aure ba,miko min rigata da nayi sallah na maida jikina,Idonsa a
rufe ya miko mata ta saka sannan ya bude idonsa yace kai yau naga abinda yafi
karfina,abincin ya jawo ya zuba musu ya dauketa tare da dorata saman bed ya zauna a
gefe suka ci abincin nasu tare.

Maheera sai da ta koma take tambayar Sohail ina Mummy? Yace tab? Wai ni nasan
inda tayi ma bani abinci ita tasan ina ta shiga wa yace kar ta tsaya a kusa
damu,wlh aka yi Kidnapping dinta ficika bazan biya ba,Maheera ta zuba masa abinci
suka ci abinsu,bayan sunyi shirin bacci yace jibi fa zan tafi Dubai,Maheera kwalla
ta zubo mata,murmushi yayi ya kashe light tare da kwantar da ita a saman bed,a
gefenta ya kwanta yace me kike so? ni bana son tafiye tafiyen nan kawai,shike nan?
to tafiya ta zama dole Maheera,sau nawa zan miki bayani ki gane amma kinki ganewa
haba Sweet,to nace maka ni yara nake so kaki yin komai ya kake so nayi,Sohail yace
wannan yara me zasu baki ne yan banza ma a haifo su sannan su damu mutum.

Shuru tayi tana sake sake a ranta,Sohail yace ya zanyi,kamar me jin tsoro haka
ya rungume Maheera a hankali ta makalkale shi tana murna,harararta ya shiga yi ai
shi dole aka masa,rigar tata ya janye a hankali yace mutum dan zaiyi tafiya shike
nan sai ya bada cin hanci....bakinsu ya hade waje daya yace a film dai na gani ana
yi nasan shi kike so,Maheera ko magana bata yi ba yana kushewa yana tsotse mata
baki,Maheera ta kara mannewa,Sohail yace ashe ba a banza ake yi ba,kin fini hankali
gaskiya,Maheera murmushi tayi suna ta faman kissing din juna,Sohail kasa dainawa
yayi ya wani rude ya zauce,sanda ya janye mata rigar bacci ma bai sani ba,kirjin
Maheera ya bayyana Sohail ya wani kunna light yace ayi abu a duhu tsakani da
Allah,Maheera duk ta canja kala kamar mayya,yace yayi shugabar yan iska har kin
koma haka sai kace kin saba da yi,dole na nemi magani,kunya Maheera taji ta kashe
light ya kunna yace ai gwara na ga me kike aikatawa ido da ido,A haka sumi sumi
dake kamar bakya aikata ba,Maheera ta kule cikin bargo tana dariya,Bargon ya shige
Maheera ta rungume shi ta baya ba kaya a jikinta,ajiyar zuciya ya sauke yace mijin
Lalai sai dai yaji kamar kasko ya rungume shi,juyowa yayi ya fara shafa gashinta a
hankali yana kissing dinta,Maheera farin ciki kamar me ashe ya iya ta furta a
ranta,wuyanta ya gangaro yana bi da kiss,Maheera makale shi tayi tana ta faman
shafa kirjinsa ta cire masa riga,yana gangarowa kirjinta ya fara shafa su da hannu
biyu yana murzawa yace ashe abubuwan wasa ne ina can ina game kullum a tv ban sani
ba sai latsa handle nake ga abin latsawa,dariya suka yi.

Maheera ita dai burinta ya gane ya koya ko nisa baiyi ba ya dakata ya juya baya
yayi kwanciyarsa yace kawai sai na zauna nayi ta abu daya bazan iya ba idan baza ki
so ni dan Allah ba to.
Dariya ya bawa maheera ta juya ta rungume shi a haka ba kaya,ya kuma juyowa yace
aci gaba? tace ae mana,shi kansa bazai iya hakuri bane amma yaki ganewa,yaci gaba
da latse Maheera ,bakinsa ta dora a saman boobs dinta,yace da girmana nidai na
shiga uku yau shike nan zan koma irin dan gidan Baffan Islaha,kar ya dawo irin na
Lalai ina rabaki da wannan aikin,Maheera ita uzurinta take ba ruwanta wai dole sai
ya gane,wandonsa zata janye ya rike yace sai na dawo daga tafiya,ki rabu dani
ni,Maheera ta cire pant dinta tace anyi anyi ka gane tun ana binka ta lumana
kaki,Suka hau kokawa da Sohail za a cire masa wando,ya sauka daga bed din da
sauri,Maheera tace ka dawo na fada maka,yace bazan dawo ba a maida ni wani dan iska
daga gwaji.

Dariya Maheera tayi ta maida kayanta tace ko banza ai kayi abinda baka taba yi
ba,yace ban yafe ba dai, tace ni din? Yace a'a na yafe miki,to zo mu kwanta na
daina kaga na maida kayana bacci zamu yi,dawowa yayi ya maida rigarsa ya
kwanta,bata masa komai ba haka suka yi bacci.
Islaha kuwa kwantar da ita yayi bayan sunyi shirin bacci Sahil yafi ganewa
shi,ya fara shafata tana kallonsa tace bani da lafiya kayi hakuri na warke Sahil
yace a kafa ne me ya dameni da kafafuwa iyakaci na Taskira bazan zo kafafu ba me
zasu tsinana min,Islaha taji tsoro tace ni dai wlh bana so ta zaci wani abu
zaiyi,yace gani ba ci ba wai mene haka,sai ayi ta zama da ku ana kallon ku.
Islaha tana hawaye harda shesheka tace nasan wayon maza wayo zaka min kuma kasan
bani da lafiya,yace to shike nan na hakura amma ni bazan iya kyaleki ba ki kwana
kawai sabo da jin dadi, bazai yuwu ba a dinga kyale ku kuna kwana lafiya ai bata
kamata ba.

Dariya ce tayi mugun kama Islaha ta goge hawayenta tana dariya,ya cire mata
rigar daga ita sai pant sai kare kirjinta take yi da hannu,Sahil ya zaro idanuwa
sai kuma ya fara dariya wai ya tuna na Lalai,yace Lalai ita kanta sai ta tsani
kanta,sai kace danmalele yarab,Islaha tayi dariya,ta juya ya riketa ya tsaya sai
kallo yake,sai da ya gaji ya ya fara kokarin zare mata pant, taki yarda,ta karfi ya
cire pant din yana kallon taskira yace waiiii...bari naje Break ya mike ya fito
tare da wucewa kitchen ya dakko ruwan sanyi ya kwankwada yace mata su suke da abin
gani, biscuits ya dakko yana ci ya dawo yace break naje na dawo,Islaha tace Allah
bacci nake ji sai dariya kake bani sai kace a makaranta harda tafiya break, kayanta
ta maida ya kashe light ya kwanta tare da dora kansa a kirjinta yana shakar kamshin
jikinta a haka bacci ya kwashe su.

Washe gari da wuri Maheera ta tashi ta shirya musu lafiyayyen breakfast ta kai
wa su Islaha bangaren su sannan ta koma tayi wanka, ta dau wanka cikin kananan
kaya,lokacin tazo ta tashi Sohail a bacci,idonsa ya bude a hankali yaga ta sha kyau
jawota yayi ta fada jikinsa ya rungumeta,tace abinci fa? Ya riga ya saba wankan
asuba shi yasa ma baiyi wani yanzu ba ya tashi ya kuskure bakinsa suka fito Dining
dinsu.
Islaha kuwa Sahil ne ya taimaka mata tayi wanka ta shirya idan ka ganta ka rantse
kafafun na tafiya,daukanta yayi ya fito da ita palo,da kansa ya bata abinci a baki
suna ci,Halley ta zo gidan daga hotel din da take,sanye cikin Wando palazo da riga
me siririn hannu, part din Sahil ta shiga kai tsaye ta same su a palo,Sahil ya dago
kai ya kalleta yace baiwar Allah dama kina duniyar? Shuru tayi dan bata jin me yake
fada,Islaha tace Hey Mum how are you? Halley tace no..no...not how are you
no...,How you,Islaha tace a rubuce haka yake kaji Baby,Sahil yace a rubuce How are
you yake,Halley tace but yanda ake fada ba haka ba,How you, Islaha tace How you?
Babu ko fara'a ta zauna abinta ta harde kafa,Sahil yace karki kara yin turanci a
gidan nan na haramta turanci ya fadawa Islaha,Halley tayi magana da turanci Sahil
yayi hausa,tace you muslim? Sahil ya fara karatun Qur'ani wai taji zahiri,Halley
mikewa tayi ita kanta a ciki bata san waye Sahil din ba waye Sohail sai Islaha ta
tambaya ta fada mata.

Gani tayi Islaha bata tafiya Halley harda hawaye ta ya danta zai auri
gurguwa,tashi tayi ta wuce wajen Sohail,Sahil yace lallai hawaye zai kare kuwa a
kasar na gani tana hawaye,Sohail yana zaune yana cin abinci ya kalle ta yace ashe
kina raye ai mun zaci anyi kidnapping dinki,Maheera ce ta bige shi ta gaida ta,
Halley ta zauna tana gyara gashinta,Sohail yace a kawo mata tuwo ido guba
ne,Maheera tace ko kai fa baka ci dumamen tuwon ba bare ita da take daga kasar
waje,Sohail yace to shike nan tunda kince haka bata abinda kika yi niyya,Maheera ta
mike zata hada mata Coffee da sauri ta tabe baki tace kar a bata bata sha ta sha
nata a hotel,Sohail yace gaba ta kaimu dama ni bada zuciya daya nace ba.

Halley ce ta gaji da danna waya ba wanda ke kulata su Sohail sun Haramta


turanci,Maheera zata yi magana Sohail yace na haramta turanci a gidan nan ko
gwalangwaje ne ban amince ayi shi ba,idan kuma kika ce ke shishigi zakiyi wlh sai
munyi fada na fada miki,ba ruwanki uwar mu ce ki rabu da ita in ta gaji ta tafi.

Halley kuwa Daddy ta kira tace ina zata samu tafinta ko mace wacce zata dinga
fassara mata abinda twins ke fada,Wani ya kira a Abuja ya hada Halley da wata mace
budurwa bahaushiya tana jin turanci za a dinga biyanta albashi.
Halley zuwa yamma me fassara tazo gidan,suna main palo gaba daya
Sahil,Sohail,Maheera da Islaha suna kallo,Halley ta shugo da guntun wandonta
kafafunta siri siri a ciki,Sohail yayi dariya yana kallon kaurin Halley da
cinyarta, Sahil ne ya tabo Sohail yace sanda zata haife mu taji jiki na sani,Islaha
suka danne dariyar su,Halley ta tambayi me fassara wacce ake kira da Sumayya,me
suka ce? Sumayya tasan in ta fadi abinda suka ce akwai kura,Sohail yace fassara
mata daidai me zata yi,Sumayya ta fassarawa Halley,Halley ta harare su tace ita fa
uwar su ce ita ta haife su,Me fassara tace tace mahaifiyar ku ce ita itace ta haife
ku,Sohail yace uhm ai dan bamu sani bane da tuni munyi mutuwar kasko tare da ita,Me
fassara ta fadawa Halley,turawa ba wahala sunyi kuka Halley sai hawaye take,Sahil
yace me aka miki daga fadar gaskiyaki mana kuka a nan sabo da Allah yayi fushi da
mu,muma kukan so muke muyi dama ce bamu samu ba,Me fassara tana ta faman
fassara,Halley ta goge hawayenta da tissue tace ni bakin cikina da kuka zama
musulmai,Sohail yayi dariya yace ai kuwa zaki kare a takaici domin kuwa a musulunci
zamu mutu,yanzu ma mun kusa tashi muyi sallar azahar, ga La'asar ta taho cewar
Sahil,Sumayya ta fassarawa baturiya,Halley ta kalle su ranta a bace Sahil yace
Allahu Akbar dan taji haushi.

Tashi tayi ta dauki akwatinta ta bar gidan motar data siya a Nigeria ta shiga
driver wanda ta dauka ya ja ta ya maida ta masaukinta hotel,Sohail ya mike ya sawa
kofa key.
Washe gari Sohail ya gama shirin tafiya dubai,Maheera sai kunci take yi ba a son
ranta ba,ganin ta damu kanta ya zauna a gefen bed ya jawo ta jikinsa a hankali ya
fara kissing dinta luf Maheera tayi,zip din rigarta ya zuge a hankali ya janye bra
dinta ya fara murza boobs dinta yasan haka kawai shine zai sa ta saki ranta.

Maheera ta sakalo hannayenta ta wuyansa ta manne shi a jikinta tana nishi tana
cewa wash.....tana kara kankame shi tace i love you na yarda ka tafi Allah ya kaika
lafiya Sweet, Maheera yau ta samu dama ta rinjayi Sohail rogonsa ta fara
shafawa,wani shidewa yayi yana nishin dadi,yace da kyar.... me nake ji
haka....hakoransa suna hadewa,haukacewa yayi ya dauki Maheera ya jefa ta saman bed
ya kwanta a samanta ya dora bakinsa a saman boobs dinta yana sha yana murza
su,Maheera sai nishi take....sai da Sohail ya lula yana cirewa Maheera pant wayarsa
ta dinka kara,firgigit ya dawo hayyacinsa yayi sauri ya fisgo bedsheet ya rufe
jikinsa yana hararar Maheera,lips dinsa ya turo gaba ya dauki wayarsa,dariya
Maheera tayi tace ina ganin ikon Allah,Kawai cewa yayi gani nan ya kashe wayarsa ya
maida kayansa,Maheera ma kayanta ta maida tana ta murna,yace taso mu tafi sauri
nake kar nayi missing flight,mikewa tayi tazo ta sake rungume shi tana jin dadi
kamar an bata gidan Aljanna,tace Sohail ashe kana mikewa? Harararta yayi yace a
haka yake ke irin Rogo ne,dariya tayi jawota yayi yace kamar ma kar na tafi sai
tuno abin dazu nake yi....bakin su ya hade waje daya yana tsotsa kamar zasu cinye
juna,Kiransa Alhaji Saminu ya sake yi,da sauri ya saki Maheera yace kiyi hakuri sai
na dawo,kamar tayi kuka ta rakoshi,Sahil yana jiransa zai kaishi Airport suka
fito,yace me kake yi ne wai ina ta jira? Sohail yace iskanci na nake yi yau ba inda
ban taba ba,da sauri Maheera ta rufe masa baki,ya kwace bakinsa ya shiga mota yace
itace nan ta jawo,Sahil yayi dariya,yace ni ina ruwana ku kara yin abinku na rufe
idona,Maheera kunya taji ta juya ciki da sauri.

Mota yaja suka wuce,suna tafiya Sohail yace yau na koyi iskanci shike nan,Sahil
yace hmm bafa a fada kai shuru ake yi ba kyau sanda na samu Islaha na dinga holewa
ta ai ban fada ba shuru nayi duk da ba abinda ban gani ba,kirjinta ne su....Sohail
yace kace ba kyau a fadawa wani,Sahil yace sai kace munafuki ace baza a fadi abu
ba,Sohail ya furta yau in ka ganni sai naji na koma jariri,Na sha nonon Halley tun
tana kuruciyarta suna da kyau yanzu na samu sabo,Sahil yayi dariya yace Halley tun
tana da kuruciya basu da girma da kyar ake samun madara ciki,badan a kasar waje
bane tuni da cutar yunwa zamu taso.
Halley fa ance tana da miji,Sohail yace tab wannan ko waye yana cikin jarabawa,ga
kekashewa uhm uwar mu ce bari muyi shuru,idan tazo kace nayi tafiya Allah dai ya
biya ta ai ta haife mu ba damuwa mun yafe mata ko dan darajar haihuwa,ta dau
cikinmu ta haife mu.

Halley duk inda takai ga son su Sohail su saurareta abin yaci tura,ga Daddy din
yaki saurarenta kowa bata sani ba a kasar,bata jin dadin kasar gaba daya,daina zuwa
tayi gidan su Sahil ta samu Sumayya tana koya mata Yaren Hausa,gida ta nema ta kama
haya me kyau ta zauna tana koyon Hausa.
Amal kuwa cikinta sai girma yake sosai,yayin da Zayna ta budewa Adnan ruwan
masifa akan taki samun ciki,Adnan ya rasa inda zai sa kansa da Zayna ita sai ta
haihu,ya rasa inda zai sa kansa da rashin mutuncin da Zayna ke masa,har Abuja
tazo,a gajiye ya dawo daga Office yana zuwa ya isketa a bedroom,rike shi tayi tace
wallahi bazan yarda ba malam kazo kawai kayi min ciki,lusari kawai baka iya abin
arziki ai da kana yi da na samu ciki tun tuni ga Amal nan cikinta sai girma yake.

Adnan yace wai meke damun ki ne? Wandonsa ta rike tana girgiza shi ya kwada mata
mari tare da hankade ta ya hau jibgarta tana ihu Allah ya kawo Ibrahim ya kwace ta
da kyar amma duk da haka cewa take wlh ban yarda ba tsafi kayi da yaran da zan
haifa shi yasa kuke da kudi,tunda ka aure ni kayi sacrifice da yaran da zan haifa
shi yasa naki haihuwa ka bawa dodo yarana,Ibrahim ya kalle ta yace ke dan an
taimakeki an aure ki ma shine kike wa mutane maganar banza,kece juya ai idan ba
haka ina laifin Yaya a nan.
Zayna tana goge hawaye ta durawa Ibrahim ashar ya daga hannu zai kwashe ta da
mari Adnan ya rike hannunsa ya furta kyaleta ki tattara ki koma gidan ubanki sai na
neme ki,Zayna tace an fada maka bani da gata ta juya ta kwaso kayanta ta fice.
Maheera taje cafane ta dawo ta hadu da Zayna da akwati zata shiga taxi zuwa
Tasha,Maheera ta kalle ta shekeke,itama Zayna kallon banza tayiwa Maheera, Maheera
tace ko har anyi kora ne? Ko kin kashe aurenki dai Sohail yafi karfinki yanzu,Zayna
takaici ya kamata wato tsabar masifar kishin Maheera da tsohuwar budurwa ma kishi
take,Zayna tace ban fita bane, kuma kinci sa'a yayan mijinki nake aure da na nuna
miki wallahi sai na auri mijinki,Maheera tayi dariya tace da kuwa an fitar da
gawarki,ki dai cire shi a ranki yafi karfinki in ma zaki zauna ki rike Adnan dinki
ki rike wani tsalle tsalle da yaji ba naki bane ko a hanya kika kallar min miji sai
kin san bani da mutunci wlh.

Maheera sai cece kuce suke yi da Zayna a hanya haka kawai ta tsokani Zayna.
Zayna kwafa taja ta juya zata shiga taxi Maheera tace tsohuwar guzuma sa'ar su
Sohail shekarunku daya dai,maganar ta yiwa Zayna zafi matuka tace zamu hadu ne ta
shiga mota ta wuce.
Maheera gida ta koma ta wuce wajen Islaha tana bata labari tace da gani ba
tafiyar gida na lafiya bane,idonta yayi jajir ya kumbura ga kumatunta sun
tasa,matar da take hawa jirgi yau a taxi duk yanda aka yi ya jibgi shegiya,na
tsaneta shegiya tayi soyayya da mijina,Islaha dariya take faman yi tace wlh ki rage
kishi soyayyar kuruciya ma,Maheera tace ai idan na tuno Sohail da har gidansu suke
zuwa sai naji wani haushi,in ta ganshi ta dinga kallonsa kenan kamar mayya.
Islaha tace ai yanzu dole ta hakura,Maheera tace hmm,Sahil ne ya fito yana jinsu
suna ta gulmar Zayna yanda mata suka saba gutsiri tsoma,yace Allah sarki kai ansha
soyayya da zayna kamar ba gobe,na tuna sanda take rungume mu,Maheera nan take ta
canja fuska tayi shuru kamar ruwa ya cinye ta,Tashi tayi ta koma part dinta gashi
Sohail tunda ya tafi basa wata waya,sam sam babu kulawa,in ta kira ma sai taji suna
ta aiki sai maganar aiki kawai.
Hakuri tayi ta dangana,amma har ya kwashe sati uku baifi sau biyu suka yi waya
ba,Maheera ta shiga damuwa matuka,Sahil ne ma a haka yake lallabata.

Yau tana zaune ta zuba tagumi a palo tana tsaki ita kadai Sahil ya kawo mata
Islaha ya zaunar da ita ya fita Office,Islaha ta kalli Maheera tace dan Allah ki
samawa kanki lafiya kiyi hakuri,yanzu ni kalli fa abinda ya sameni na kasa, ki
godewa Allah ke lafiya kike ma,ni kalle ni fa,Maheera tace baza ki gane bane tunda
Sohail ya samu karin girma na rasa kansa na kasa gane masa kullum sai maganar
aiki,ina son mijina zan iya mutuwa a kansa,amma baya kula dani sam,ki duba tunda
muka yi aure yau wata nawa na kwashe watanni ba abinda ya shiga tsakanin mu,na
hakura amma yar waya ma ta gagara,ni ina jin ma ya samu wata sabuwar budurwar ya
manta dani,Islaha tace ba haka bane Maheera komai sai ana hakuri,kuka Maheera ta
saki waye ya isa yace bana hakuri a gidan nan Islaha,suna haka sai ga Sohail ya
dawo yana faman kwalawa Maheera kira Sweet....na dawo... surprise zan miki,baki
bude ya tsaya ganin tana sharbar kuka.

Karasawa yayi gabanta da sauri ya ajiye jakarsa a gefe ya tsuguna tare da dafa
kafadunta yace me ya faru Sweet,jikinta ta kwace tana kuka tace kawai ka kyaleni
kaje kayi aikinka tunda aiki ya fini a rayuwa,taya aiki zai fiki a wajena,daukanta
yayi suka shige bedroom,Islaha tana kallon su ta lula tunanin nakasar da tayi itama
ta fashe da kuka tace shike nan ni kowa yana soyayya banda ni,aje yawo a taka a
tafi wani waje ban dani,bani ma da gata ba wanda yazo ya dubani a dangi ko da wasa
taci gaba da kukanta.

Sohail yana shiga ciki Maheera tace mene amfanina tunda ka daina so na,aiki ya
fini badan haka ba wannan bai ishe mu rayuwar duniya ba,gidan mu na rufin
asiri,zamu ci mu sha Alhmdllh me ake bukata a hakura haka kace kai sai kayi
mahaukacin kudi,nace okay to kayi min ciki ko ba komai na dinga ganin yarana ina
jin dadi kace ba haka ba,nace naji na hakura da haihuwar ka dinga kula dani kana
nuna min love muna romance da sauran su shima ya gagara ya kake so nayi,kayi
tafiyarta sati uku ace ko waya sai ni na nemeka sau biyu,kace Sweet ina abu zan
kira baza ka kira ba,shike nan aiki ya rabani da masoyi na.
Ni gwara kana talaka kullum muna tare,sanda kafin ka samu aiki ko kafin a kara ma
girma kullum muna tare kana nuna min kauna amma yanzu komai babu ni an rabani da
masoyina,kuka take bilhaki tana tirje tirje,Sohail sai faman rirrike ta yake tana
fisgewa kamar me aljanu,ki tsaya na miki bayani,bazan ji ba babu abinda zaka ce
dani....bakinsa taji cikin nata shuru tayi ta fara tayashi,daukanta yayi yana
dariya tace da haka kake yi ai da an zauna lafiya,amma baza kayi ba sai aikin kudi,
saman bed ya kwantar da ita ya fara lalube ta,Maheera bata sake korafi ba,duk da
dai baiyi wani nisa ba ita hakan ya gamsar da ita taji dadi,Islaha sai gani tayi ta
fito tana nishadi.
Kwanan Sohail biyu rak yace Baby kinji zanje Morocco amma bazan dade ba sati daya
kawai dan Allah karki fushi,Maheera tace ohhhh ....nidai ta danyi guntun tsaki tace
shike nan ya zanyi za a rabani da mijina,dariya yayi yace babu me rabamu muna
tare,tace to shike nan..
Haka Sohail ya tafi daga can sai jinsa tayi sun tafi wata kasar nan ma bai dawo
ba ya wuce China,bayan sun dawo kwanansa daya tal da sasaafe suka tafi Lagos,har
tsoro yake ji yace da Maheera zaiyi tafiya,shi kansa yasan baya kyautawa amma ba
yanda zaiyi,tun tana magana har ta daina sai dai kawai tunani da damuwa da ta taru
tayi mata yawa.
A baya tana dan ganinsa taji dadi amma yanzu ganin Sohail ma aiki ne.

Tana ta hakuri sai da ta kwashe wata uku a haka baya zama,gwara ma a baya kullum
ko ba komai suna tare,Islaha dinma Sahil din ba wani zama yake ba amma gwara
ita,abinda ke damunta rashin lafiyarta ta kafafu sannan itama wani romance ma basa
yin komai yanzu ta aiki suke yi kawai.
Yar gidan Alhaji Umaru Amatullah kullum sai ta kira Sahil kamar mayya baya
dagawa,haka ta dinga masa text,baya bari Islaha ta gani yake gogewa.
Ga Alhaji Umaru ya dame shi ya fito ya auri Amatullah Sahil yaki yarda,ganin haka
Alhaji Umaru ya zage ya sanarwa Daddy.
Daddy farin ciki ma yake yau kamar Alhaji Umaru ace yana so ya hada zuria da shi
ai shi sai godiya da murna,jiki na rawa yace InshaAllah ko Sahil baya so sai ya
aure ta,Sahil yana can su suna ta shirin yi masa aure bai sani ba.

Yau Sohail ya dawo yana gida,duk da haka Maheera ba wanda ya kaita murna,yanda
suka saba soyayyar su haka suka yi bata ma nuna fushin ba tunda ta ganshi kusa da
ita,washe gari da sassafe ya shirya zai fita meeting,kofa ta tare tace wlh ba inda
zaka je yau na gaji,kullum aiki jiya ka dawo ina murna yau zamu zauna tare ka tashi
da sassafe kace zaka je wani meeting,Sohail yace kiyi hakuri Maheera lokaci ne
komai da kike gani duk don wa nake aikin nan? indai dan ni kake yi yau baza ka fita
ba, Lallashinta yayi taki yarda,lallashin duniya taki yarda har ransa ya baci yace
matsa to zan wuce tace wlh yau sai ka zaba ko aiki ko ni,harara ya balla mata yace
matsa min a hanya,tace na fada sai ka zaba yau ko aiki ko ni fa ato ta furta tana
jijjiga,Sohail ya ture ta yace na zabi aikin yafi ya furta cikin fushi,baki ta rufe
da hannaye biyu tace kace aiki ya fini,juyawa tayi tayi reverse ta dawo baya ta
sake youturn,ta fadi a kasa ta dinga kururuwar kuka shike nan an rabani da mijina
ya samo wata yar kasar waje....taci kuka kamar ranta zai fita,ta fito part din
Islaha tana hawaye tace yau wai Sohail ya zabi aikinsa over me,akaina gwara aiki
yafi masa,Islaha tace babu lafiya zama bai ganmu ba,mun shiga uku gwara ke da
kafafunki,Ai kuwa ba shakka wata ya samu wacce ta fiki wlh karki yarda.

Maheera ta zauna ta zuba tagumi irin tunanin mata marar kai shi suka dinga
yi,Maheera bata ce komai ba ta tashi ta lallaba ta koma part dinta ta saka hijab
har kasa ta nufi Office din Alhaji Saminu.
Sohail yana can a wani hotel suna meeting kamar sun samu lafiya yanzu haka suke
komai na aikin sun goge.

Maheera taci sa'a yana Office ta shiga har ciki ta fadi a kasa ta zauna zaman
dirshan,Alhaji Saminu yace lafiya kuwa Maheera? Tana kuka tace mijina ya daina so
na ka rabani da mijina dan girman Allah indai har dan ni ka bashi aiki ka sallame
shi ni kawai burina ka sallami mijina a aiki yafi min komai,indai har sabo da ni ka
bashi aiki ka kore shi kawai, mijina ya daina kaunata kun rabani da mijina,na shiga
uku na jawa kaina,Alhaji Saminu yace dakata kiji...ni bazan ji wata maganarka ba
kawai ka kori mijina daga aiki.
Alhaji Saminu yace mijinki yana aikinsa lafiya yana samun kudi muna jin dadin
aikinsa bai yi mana komai ba amma haka kawai ba laifin komai mu kore shi daga
aiki,ae ai dan ni kace ka bashi aiki to ka sallame shi.
Alhaji Saminu ya buga ya buga duk wani kokari na ya fahimtar da Maheera amma
taki ita kawai a kori Sohail gwara suyi soyayya ya kula da ita,yace bashi da kudi
da me zai kula dake? kowa burinsa ya samu aikin yi ya dogara da kansa yanzu kina
matarsa sabo da soyayya kawai kice a kore shi bai mana laifin komai ba,Maheera tace
ai dai sabo da ni kace ka bashi aiki to bana so a sallame shi kawai mijina ya dawo
gareni ya kula da ni.
Mamakin mata ya kashe Aljaji Saminu yace shike nan kije kiyi tunani,ni ba wani
tunani da zanyi na gama kawai ka kore shi,yace shike nan jeki ba damuwa zanyi yanda
kika ce tunda dan ke nayi amma wlh duk abinda ya biyo baya karki dawo min,tace naji
ni a dawo min da mijina.

Bayan kwana biyu Sohail suna kwance da Maheera suna kallo a Bedroom ya dora
hannunsa a kirjinta yana shafawa kawai yaji karar message,yana dubawa wai an
sallame shi daga aiki aka tura masa,Alhaji Saminu ya kira a waya cikin gigita ya
tambaya nan take yace laifin me nayi aka kore ni? Yace ba laifin komai kawai
kamfani bazai ci gaba da aiki da kai ba,Sohail ya kashe waya ya nunawa Maheera yace
kinga wai kawai an turo min letter duk kokarin da na yiwa kamfanin nan,na bada
rayuwata da lokacina da komai kawai ace an koreni,idan ma kora ce akan nayi laifi
ai bazan damu ba amma ace banyi laifin komai ba,Maheera gaba daya sai jikinta yayi
sanyi ganin yanda Sohail ya damu ya sulale a hankali ya zauna a kasa ya dora
hannaye a kai yana hawaye,tace Baby kayi hakuri Allah zai baka wani,tashi yayi yana
layi kamar dan giya ya koma palo ya fada saman kujera ya kwanta kawai,Fitowa tayi
yace bana bukatar wani a kusa dani dan Allah ki tafi,duk da haka zama tayi tana
lallashinsa amma ina.
Sahil bai sani bama sai washe gari da Maheera taga Sohail yaki ci yaki sha
sannan ko bacci baiyi ba haka ya kwana idonsa biyu taje ta fadawa Sahil an kori
Sohail a aiki ne,shi kansa Sahil tambaya yake me yayi? tace sunce ba komai.
Da sauri ya taho wajen Sohail ya samu ya kulle kansa a daki kawai baya bukatar
ganin kowa ma,Suka yi suka yi ya bude kofar yaki budewa sam,sai da kyar da Maheera
tace zata tafi gidansu sannan ya bude kofar,Sahil ya shiga ciki ya zauna yana ta
lallashinsa yana masa Nasiha akan kaddara.

Maheera kuwa ganin yanda Sohail ya canja duk ya fada lokaci guda sai kuka
take,kwanciyar hankali da soyayya da take tunanin zata samu sai ma dagulewa da abin
yayi.
Yar soyayyar da take rainawa yanzu babu ta kare aikin Sohail ya kwanta shi kadai
yayi tunani yayi hawaye,sannan babu bacci ya daina bacci amma duk da haka yana
sauraron Maheeransa bai san itace ta sa a kore shi ba.

Bayan sati biyu Rashin bacci da yake yi da kuma baya cin abinci yasa Maheera
kullum cikin kuka da dana sani take,gashi tsoro take ji ta fadi gaskiya,tana ta
rokonsa tana kuka dan Allah Sweet ka tashi kaci abinci so kake ka kashe kanka akan
aiki,Please tana lallaba shi,ganin itace haka ya mike zai je Dining a nan wajen ya
zube a sume,tayi kansa da gudu tana kuka,ruwa ta ebo da gudu ta yayyafa masa ya
farfado,ta sake tafiya da gudu ta kira Sahil dawowarsa kenan daga Office yazo suka
wuce da shi asibiti.

Bayan gwaje gwaje likita yace hawan jini ne ya kamashi ga rashin cin abinci da
damuwa ta masa yawa,Maheera ta tsure gaba daya.
Kwanan su daya a asibiti yaji sauki aka sallame su,baya kula kowa ko magana sai
dole yake yi kamar ba Sohail ba lokaci guda ya canja.
Suna komawa gida washe gari da sassafe Maheera ta saci jiki ta fice daga gidan
ta tafi Office din Alhaji Saminu,da kuka ta shiga Office din tana ka taimaka min
rabin raina zai mutu ya barni,bani da kwanciyar hankali,nidai dan Allah a dawo masa
da aikinsa idan ma a kasar wajen zai zauna ya zauna na hakura zan jira haka wallahi
ina son mijjna ba sai yayi min soyayyar ba na hakura da soyayyar,mijina ya daina
bacci ya daina cin abinci magana ta gagara,bazan iya rayuwa ba nafi so na ganshi
cikin farin ciki.
Dan Allah ka tausaya masa a bashi aikinsa,jarabar mummunan halina ya jawo min
ina son mijina wlh,Alhaji Saminu ne ya dakatar da ita fuskarsa a daure,yace kinga
Kamfani ba wajen wasa bane,taimakonku nayi kuma nayi abinda zan iya,Kina tunanin
samun aiki a kasar nan sauki ne,na bashi aiki yana aikinsa normal kamfani na jin
dadinsa shima yana jin dadin kamfani ya samu experience ya goge kince a sallame shi
bai yiwa kowa komai ba,ku mata baku da hankali kawai aiki kuke yi da ka sabo da
rashin hankali kizo kice a sallami mijinki daga aiki akan soyayya,nayi abinda zan
iya,tashi ki bar min Office,Maheera ta durkusa a gaban Alhaji Saminu tana rokonsa
tana kuka kamar ranta zai fita amma ya koreta gaba daya ransa a bace.

Dole ta koma gida jiki ba kwari gaba daya ta koma a sanyaye tace hali irin nawa
na son kai ya jawo min na shiga uku,tana shigowa palonta ta samu Sohail a tsaye
yana jiranta ransa a bace,tana ganinsa a haka tasan Aljanu ma sun sanar masa abinda
tayi,yace ina kika je? da baya da baya ta fara ja tace ahm...dam...uhmmm....gidanmu
naj...tsawa ya daka mata yace kinji kunya Maheera,ban taba sanin haka kike da
mummunan hali ba sai yau,ba abinda nayi kisa a kore ni daga aiki sabo da wata
bukatar ki,aikin da na dade shekara da shekaru ban samu ba,kawai sabo da an bani
aiki ta dalilinki shine kika je kika sa a kore ni,ya nuna kansa yace ni Maheera
zaki sa a sallama a aiki ba tare da laifin komai ba,yana magana yana matsawa kusa
da ita,hawaye take yi tace wlh banyi dan wani abuba dan kawai ina sonka ne baka min
soyayya baka kula dani,ban san zaka shiga damuwa haka ba,da na sani bazan je nace
ba...to gani yanzu ranki yayi fari ko? an koreni na dawo gida mu zauna tare dake,ki
cinye ni gani ki cinyeni sabo da soyayya ko caring, sai ki cinye ni,yasa kirjinsa
ya tankadeta sai da ta fadi a kasa.
Yace nayi dana sanin saninki ma a rayuwa tashi ki bar min gida,tashi bana son
ganinki,Maheera ta fashe da kuka tace wallahi bazan iya ba ni bazan rabu da kai ba
ina sonka.

Ki bar mana gida na fada miki,wlh bazan tafi ba gidan mijina nane bazan tafi ba
har abada muna tare,Zuwa tayi zata rungume shi ya wanketa da Mari yace dauki
kayanki ki bar min gida kafin na miki Illa,Maheera tace sai dai ka kashe ni wlh ba
inda zanje mu mutu tare,Sahil ne yaji hayaniya ya shigo,Sohail yana hawaye yace
sabo da an bani aiki ta dalilinta taje tasa aka kore ni banyi laifin komai ba,da
laifi nayi bazan damu ba,wahalar da nasha ina aiki na bada rayuwata da lokacina
sabo da ita nake wannan wahalar sabo da na samu taji dadin duniya shine taje tayi
min haka,Sahil yaji abinda ya faru,yace Maheera kece kika iya aikata haka?
Subhannallah kawai ki tafi gida ina baki shawara kinga Sohail idan ransa ya baci
bama bacin rai wani ya zauna ki tafi kawai ni kaina na tsane ki wlh,Sohail ne ya
harari Sahil yace ka tsaneta kai a wa? Ina ruwanka,kan Maheera ya juya da tsawa
dalla ki tafi ki bar min gida,Maheera tana kuka ta wuce sama kawai ta hado kayanta
ta wuce ta gaban Sohail zata tafi hannunta ya rike ta juyo da sauri yace wlh idan
kika fita ko wani waje da aure na ban yafe ba,hannunta ta janye tace ka yafe min
ban san haka zara faru ba,jeki kawai ya furta da karaji,ta juya ta fito,taje part
din Islaha dake kwance a palo tana jin hayaniyar komai a kunnenta,Sallama ta yiwa
Islaha,Suna kuka duka su biyun, Maheera tace na jawa kaina,Islaha kinga yanda
Allah yayi dani ko,naso ace ina nan ko dan lalurarki idan basa nan ni kinga ina
kusa dake amma an samu matsala na aikata kuskure.....Allah ya baki lafiya
Islaha.... ta fice da sauri tana kuka,Sohail sama ya haura labile ya bude yana
kallon Maheera ta fita daga gidan.
Taxi ta shiga ta nufi gidan su tana kuka kamar ranta zai fita,shi kansa me Taxi
din gajiya ma yayi da jin kukan.
Islaha an barta tana kukanta bata san aure ake shirin daurawa mijinta ba shi
kansa bai ma sani ba sabo da kawai an dauke su mahaukata sai abinda aka ga dama ake
musu,jira Daddy yake kawai sai ya rage saura 3days ya sanar da Sahil,sun tsara
yanda zasu bullo masa wanda dole ma ya amince a daura.

NA GAMA FREE PAGE

400 NE 1&2

0175487861
Asmau Garba Muhammad Gtbank

AsmaBaffa
08061929616

You might also like