Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel by Ashwarmediahausa
Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel by Ashwarmediahausa
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
00️⃣11️⃣0 1
.......Ƙaddarorin rayuwa tamkar TASWIRA ce dake zane a takardar lissafin rayuwar kowanne ɗan adam, duk
yanda ka so gogesu ko san kauce musu ba lallai ne ka samu makaman yaƙin ba balle GARKUWAR kare
kanka daga isowarsu gareka ko mai gajartar tsahon shekaru ko yawaitarsu. A wasu lokutan mukanyi kuka
ne da hawaye, sai dai kukan ZUCIYA shine mafi ciwo da ɗacin kuka da yafi kassara rayuwarmu da
nasarorinmu a ɓoye ko a zahirance da bama iya mantawa. Dan a wasu lokutan har tambarin tabon da
zamu iya ringa tunawa a lokaci bayan lokacin yake bar mana.
A farkon haihuwar mu iyayenmu sune GARKUWARMU, dan sukan sadaukar da komai nasu ne domin
lulluɓe RAYUWARMU da dukkan fatansu. Sukan rainemu da shauƙi da yaƙini har zuwa girmanmu. Hakan
yake saka SOYAYYAR su bata taɓa iya goguwa a ZUKATANMU, sannan takan banbanta da irin kowacce
soyayya da zata biyo bayanta. Koda hukuntamu sukai mukaji zafi mukai kuka wannan soyayyar tasu bata
taɓa canja kanta a ZUKATANMU saboda su ɗin sune dai ɗaya tamkar da dubu a dukkan abubuwan dake
zagaye damu na NASARA ko akasinta.
A lokacin da girmanmu ke ƙara yawaita sai TSUFA ya riskesu. Mu kuma ƘURUCIYA ta baibayemu. Sai dai
me daga lokacin daka iya tantance ma'anar FARI da ƁAKI a yau ɗinka da gobenka littafin ƘADDARARKA
kuma ya fara kenan da manyan zanukan layukan dake bayyana JARABAWOYINKA. Gwagwarmaya ta zama
ƙawa ko abokin RAYUWARKA. Yaƙin ba yana farawa da gwagwarmayar RAYUWAR DUNIYAR kawai bane ba.
Harda ta neman LAHIRA da zaɓama kai makoma ƙyaƙyƙyawa ko akasinta. Domin kuwa fara rayuwar girman
na farawa ne da daidaiton mizanin ayyukan samun LADANKA da kuma ZUNUBI duk a bayyane kuma a
rubuce ga wanda ya HALICCEKA. Iyayenmu kan gama gwagwarmayar ƙuruciyarmu, sannan su koma ta
girmanmu babu gajiyawa saboda su ɗin na dabanne a cikin daban a garemu.
A lissafin fara fahimtar kanka da tabbatar da WANENE kai, da wahala kaga babu armashin soyayyar
ƙuruciya da takanyi kutse a ƙaddararka. Ba soyayyar bace ba kawai abar kallo ko zama daban a gareka ko
wanda ke tare da rayuwarka. A yaya SOYAYYAR ta FARA? Ko ta ƙare? Ko ta kasance? Ko ta cigaba da
wanzuwa? Itace madubin dubawarka ko masu juriyar bibiyar labarinka.
★ Ƴammata ne uku sanye cikin kayan hidimar ƙasa. Tsaye suke a bakin titi kowacce hannunta riƙe da
hannun trolling alamar abin hawa suke jira. Dan suna ma ta ƙoƙarin tsaida napep amma mafi yawanci sai
kaga akwai wani a ciki ta yanda bazai isa su ukun duk su shiga ciki ba. Cikin ɗan damuwa da ƙosawa ta
tsakkiyarsu da bata da yawan fara'ar fuska ta ɗaga kai tana kallon sararin samaniya dake haɗa hadari. Ko
kaɗan bata fatan ruwan nan ya taɓa ta. Dan hakan baya zama mai sauƙi a gareta shiyyasa tafi kowa
damuwa da samun abin hawan nasu, daɗin daɗawa tafiyarsu mai nisa ce. Dan kuwa jihar Kaduna suka
nufa.
Fara tasowar iskar hadarin ta sata duban ƴan uwan nata idanunta na cika da ƙwalla. Sai dai kafin ta
samu damar cewa wani abu wata jar mota tai parking a gabansu. Su duka idanu suka zubama motar, sai
dai buɗewa da fitowar matashin saurayin dake ciki ya saka biyu a cikinsu sakin murmushi da mamaki.
Yayinda ta tsakkiyar sun nan dai ta sake haɗe ƙyaƙyƙyawar fuskarta tana mai kauda kanta gefe. Shi kam
saurayin nan gaba ɗaya hankalinsa na kanta. Ya ƙaraso gabansu dai-dai saitinta ya tsaya tare da faɗin,
“Yanzu duk saurin da nake sai da kika nema guje min?”.
Fuska ta sake haɗewa tana ɗan matsawa baya. Kansa ya ɗan sosa yana mai sakin murmushi. Hankalinsa
ya maida ga sauran biyu cikin jifansu da harar wasa ya ce, “Amana batace dai haka ba friends. Kamar ni ina
daku amma a so haɗa kai da ku a gudu min”.
Dariya suka ɗanyi a lokaci ɗaya. Ta gefen damarsa mai ɗan jiki kaɗan ta bashi amsa da, “Ina ai bazamu
taɓa yarda hakan ta kasance ba. Ko an gudu maka mu zamu kawoka har wajen ɓuyar RK. Amma ai mana
afuwa mutuniyar taka ce ta addabemu da tafiyar sassafen nan. Kasan jiya ko barcin kirki batai ba saboda
farin cikin zata koma gida taga Ammie”.
“Ko dai tana farin cikin zata gudu daga Jos ta bar ɗan nacinta ba?”. Ya faɗa idonsa a kan budurwar
tsakkiyar dai. Da sauri ta gefen haggunta ta amshe da “Haba RK kaima kasan ba haka bane sam”.
“Humm Aneesa dama ai baƙya son laifinta ke tuni na fahimci haka. Duk ta inda aka ɓullo sai kin kareta.
Ni dai yanzu ku shiga mota muje kunga ruwa na shirin sakkowa karya jiƙa min sarauniyata”. Kafin wani
cikinsu ya bashi amsa a hankali ta fara jan akwatinta domin barin wajen. Saurin riƙo akwatin yay, hakan ya
sata tsayawa cak batare da ta juyo ba. Zai yi magana Aneesa tai saurin girgiza masa kai tare da amsar
akwatin. Babu musu ya sakar mata yaja da baya.
Akwatin tai ƙoƙarin ƙara ja Aneesa ta sake riƙewa. Hakan ya sata juyowa a fusace zatai magana a zatonta
shine sai taga Aneesa. Idanunta tai wani irin lumshewa da cizar gefen lips ɗin ta irin na takaicin nan kawai.
Hakan ya saka Aneesa sakin murmushi dan tasan ta gama ƙurewa a fusata. “Kiyi haƙuri dan ALLAH” ta faɗa
da sauri, bata jira amsarta ba ta cigaba da faɗin, “Kiyi haƙuri mu bisa _Maanal_, kalla garin nan ki gani
hadari ne da akoda yaushe za'a iya fara ruwa. Kinfi kowa sannin illar da hakan yake miki. Kema kin san
iyakarsa yace zai kaimu tasha ne kawai. Daga yau ne fa an rabu shike nan kuma. Dan ALLAH kada ki bari
kuyi irin wannan rabuwar da shi. RK bai cancanci hakan daga gareki ba. Ko bazaki taɓa amince masa ba
kada ki munana masa a yau ɗin nan da zamu rabu. Yanda baki wulaƙantasa ba a baya yanzu karki aikata. A
rabu lafiya daga haka kuma bashi ke nan ba tunda ko lambarki dai yanzu bai da ita ballema kice zai cigaba
da takura miki, ba kuma sanin gidanku yay ba idan kika cire sunan gari”.
A hankali ta buɗe idanunta da suka gama kaɗawa, ga hawaye sun cika su zubowa kawai ya rage. Lips
ɗinta ta buɗe zatai magana ruwa yay wani irin kecewa lokaci guda. Gaba ɗaya ta rikice. Har bata ma san
Aneesa taja hannunta ta tura cikin motar ba itama ta shiga. Sai da taji babu saukar ruwan a kanta sai
ƙararsa sannan ta farga ta ɗago kanta data cusa cikin ƙafafunta da sauri. Waigowar da zatai suka haɗa ido
da RK daya wani zuba mata ido kamar zai cinyeta. Nata ta janye da sauri tana mai juyawa ta kalla ƙawayen
nata. Da sauri Zeezah ta nuna Aneesa alamar babu ruwanta itace. Aneesar ma saita marairaice mata fuska
alamar kartace komai dan ALLAH. Harara ta sakar mata tare da ɗauke kanta, sai kawai ta juya tana goge
fuskarta da ruwa ya fara taɓawa da handkhachief.....
Tunda motar ta fara tafiya babu wanda yay magana. Ga ruwa ana kwararawa kamar da bakin ƙwarya.
Tuni wasu motocin ma sun koma gefen titin sun tsaya. Ganin sunzo sun wuce tasha yasa Zeezah yinƙurin
yin magana. Da sauri RK dake kallonsu ta mirror yay mata alamar roƙon tai shiru. Haɗiye maganar tayi tana
murmushi, sai kuma ta ɗan dubi Maanal da kanta ke sunkuye novel a hannunta alamar karatu takeyi,
shiyyasa bata san wainar da ake toyawa ba ma.
Shima dai RK ya raba hankalinsa biyu ne. Rabi ga tuƙi rabi a kallonta. Maanal ƙyaƙyawar yarinya ce
kuma nutsatstsiya. Za'a iya kiranta tsaka tsaki a tsaho, a wani gurin kuwa ma wasu kai tsaye zasu kirata
doguwar duk da ba shalleliya bace, sannan bata da wani jikin kirki. A duk wanda ya santa musamman a
tsukun shekarun nan zai iya sakata a jerin miskilayen mutane. Bata da yawan magana, hakama bata da
fara'a ko yawan walwala sam. Dan da wahala kaga murmushi ma a fuskar Maanal balle akai ga dariya.
Akoda yaushe fuskarta ciɗin-ciɗin take. Hatta da magana ma sai taso take yinta. In har ba wani abu take
mai muhimmanci ba to akoda yaushe zaka samu novel a hannunta tana karantawa. Hakan na nufin ita ɗin
mayyar karance-karance ce. Dan zamu iya cewa ma yawan karance-karance nata ne yasa koda yaushe zaka
samu idanunta da eyeglasses fari tas da mutane da yawa basa iya ɓoye mata cewar yana mata matuƙar
ƙyau. Itama kanta tasan yana mata ƙyawun, dan takai tun ma tana sakashi domin karatu, har ya zame mata
jiki akoda yaushe zaka ganshi tare da ita in har ba barci take ba ko wani abinda ba'a buƙatarsa. Sai dai
kuma abinda kowa bai sani ba wani dalili ne daban ya ɗabi'antata da yawan daka gilashin akoda yaushe
bawai dan karance-karance kawai ba, duk da a ɓangaren karatun ma yana bata gudummawa matuƙa........
✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
_________________
_______________
00️⃣22️⃣0 2
.......Ganin tafiyar taƙi ƙarewa yasata kai hannu ta ɗan gyara eyeglasses ɗin tare da ɗagowa ta kalla titi, har
yanzu ruwa ake zulawa, sai dai hakan bai hanata fahimtar har sun fara barin gari Jos ba. Da mamaki a karo
na farko ta dubi RK da tunda ta ɗago ya kama kansa daga satar kallonta da yake yi. Kamar zatai magana sai
kuma ta kauda kanta. Sake maidawa tayi ga book ɗin, sai dai ba karatun take ba tayi shiru ne kawai tana
juya maganar da take son fitarwa. Sai da ta mula dan kanta sannan a hankali cikin sassanyar muryarta da
take matuƙar zama mafi girman rowa ga masu son ji irinsu RK ta furta. “Bayan waccan tashar akwai wata
ne a gaba naga mun wuce?”.
Har cikin tsakkiyar kai yaji gajeren zancen nata. Sai da ya wani lumshe idanunsa ya fuɗe tare da sakin
murmushi sannan ya bata amsa da, “Bazan iya saukeki a ko'ina cikin ruwan nan ba kiyi haƙuri sai a Abuja”.
Ɗagowa tai kamar zata kallesa sai kuma ta fasa. Sake maida kanta tai ga buk ɗin kawai tana ɗan cizar
gefen lips ɗinta. Murmushi ya ɗan saki shima dan ya fahimci wannan cizar lips ɗin nata takan yisa a duk
sanda takai ƙarshen takaicin da har ta rasa abin cewa.
“Kiyi haƙuri Please”.
Ya sake faɗa a hankali. Bata tanka masa ba, sai ma sake maida kanta tai a karatun kawai. Shima sai yay
gum da bakinsa ya maida hankalinsa gasu Zezaa tunda dai ya samu da alama ta haƙuran. Tanata karatunta
suna hirarsu. Yawan sakkota a hirar tasu da dariyar da suke ya fara gundurarta, sai kawai ta manna
Bluetooth a kunnenta ta ajiye book ɗin ta lumshe idanunta. A haka barci ya kwasheta tana sauraren
karatun Alkur'ani data sanya daga bakin Gwani Abdullahi Zaria. Har suna gab da shigowa garin Abuja
ruwan akeyi, har kuma lokacin Maanal barci take sosai dan sam batai isashen barci jiya ba. Addu'a yay tayi
da fatan subar Abuja bata farka ba. Dan yasan zata iya tuburewa akan ya ajiyesu anan ɗin, aiko addu'ar
tasa bata amsu ba. Dan sun wuce zuba kaɗan kuwa ta farka. Agogo ta fara kalla sannan ta juya tana kallon
su Zezaah.
“Muna ina ne yanzu?”..
Ɗan kallon juna sukayi, sai Zezaah tai tsulum tace, “Mun fita a Abuja”.
Da mamaki Maanal dake kallon titi ta ce, “Mun fita fa? Wannan ba hanyar suleja bace? Ko nan ba
madalla bane?”. Yanda ta ƙare maganar tana kallon RK ya sashi ɗan sosa goshinsa yana furzar da iska. Sai
kuma ya jinjina mata kai ganin ta wani tsaresa da idanunta dake matuƙar firgita masa lissafi. Kanta ta
ɗauke tana faɗin, “To Alhamdullah sai ka sauke mu a dikko kawai ai zamu samu motar Kaduna a wajen”.
Sosai fuskarsa ta nuna damuwa. A marairaice ya ce, “Haba miya rage Baby, tunda mukazo nan can ma
bazai gagara ba. Kiyi haƙuri mu ƙarasa, ina Abuja ina Kaduna”.
Yanda yake mata magana kamar zai yi kuka yasa haushi ya sake kamata. Mutumin nan sam baya
ganewa, ta rasa mi kuma zata masa ya gane ɗin. Duk yanda taso hanasa kaisu kadunar hakan bai yiwu ba.
Dole tana ji tana gani ya ɗauki hanya. Hankalinta ta sake maidawa akan novel ɗinta ta sharesa. Sai su
Zeezah ne keta hirarsu da shi. Yanzun ma ko sun sakkota bata tankawa. Suna isowa Kawo tace ita anan zata
sauka. Yi yay kamar bai jita ba. Cikin ɓacin rai ta juya tana kallon su Neesa. Cikin jin haushi, duk da muryar
tata na fita ne da sanyinta da nutsuwa ta furta, “Malamai kusa ya saukeni anan tunda naga da sawarku
yake komai”.
Kafimma su bata amsa RK yay saurin faɗin, “Sorry Baby babu ruwansu. Ni dai fatana sai na direki har
ƙofar gida dan ALLAH”.
Yanzu kam harara ta zuba masa. Ya wani lumshe idanu da buɗewa a lokaci guda ya saukesu a kanta. Da
tasan ta'asar da harar nan ke masa data tausaya masa ta bari. Ganin dai zata kife da shi yay ƴar gyaran
murya yana wani marairaice fuska. “Please ki tausaya min hararar nan illa take min”. Ya faɗa a wani irin
hankali kamar mai raɗa har yana ƙoƙarin ɗan matso ta. Janye jikinta tai ta lafe a murfin tana rumtse ido da
ƙarfi. Daga haka bata sake magana ba. Su Neesa ne suka shiga nuna masa hanya har anguwarsu Maanal
ɗin data kasance cikin manyan anguwannin da kadunawa ke ji da su (Ina da tambaya?, wai Kaduna akwai
anguwanni masu ƙyau dan ALLAH ko sai sun zo Kanon mu suke gani kawai 😂. 🏃🏃🏃Bari na ware kafin ƴan
Kaduna su maidani awara yau ɗin nan kun san bazazzage ba sauƙi). 😘Dai-dai ƙofar wani katafaren farin
gate da akaima ado da golden suka tsaya. Ya wani sauke ajiyar zuciya yana kallon gidan da ƙyau. Eh lallai
ashe itama ƴar masu kuɗi ce. Dan gidan nan kam dai ya kai a kirashi gida.....
Fitar Maanal a motar ta sashi saurin katsewar tunanin sa. Shima da sauri ya buɗe ya fita. Dai-dai tana
ƙoƙarin buɗe booth. Shine yay saurin sakko mata da akwatin ta. Ya juya da nufin sauke nasu Neesa taja
kayanta. Su Aneesa da suka gama fahimtar mi take shirin yi duk suka fito. Magana Zezaah tai yunƙurin
mata tai mata wani kallo na babu ruwanki da ni taja akwatinta tai gaba. Sai da tai ɗan taku uku zuwa huɗu
ta juyo ta kalla RK daya zama kamar gunki a tsaye. Idanunta dake cikin gilashi ta ɗan lumshe ta buɗe a
kansa. “Mun gode da ƙoƙarinka. ALLAH yabar zuminci. Amma zan baka haƙuri dan ALLAH karka cigaba da
wahalar da kanka, kamar yanda na faɗa maka gaskiya tun a farko itace dai har yanzu. ALLAH ya haɗamu da
alkairinsa a yafi juna”..
Kafin yay wani yunƙuri harta shige gida. Ƙoƙarin binta yay da hanzari mai gadi dake tsaye daga ciki ya
babbake ko'ina ya hanashi. Dole ya dakata yana mai kai hannu ya ɗan dafe goshinsa da furzar da iska mai
nauyi...........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
00️⃣33️⃣0 3
______________
_______________
........“Kayi haƙuri dan ALLAH RK”. Aneesa ta dawo da RK dake bin maigadi da kallo idanunsa sun kaɗa sosai.
Iska ya ɗan sake furzarwa batare daya daina kallon maigadi ɗin ba. Sai kuma yay murmushi da gyara
tsaiwarsa hannayensa duka biyu a cikin aljihu. Kansa ya ɗan girgiza tare da juyo da dubansa yana kallon
Aneesar fuskarsa da murmushin dake bayyana damuwarsa. “Baku min laifin komai ba Aneesa. Haka itama
banji haushinta ba sam. Sai dai bazan iya rabuwa da ita ba kamar yanda take buƙata. Da gaske ina son
ƙawarku matuƙar so da ban taɓama wata mace ba da sunan soyayya ta aure. In dai zan jure waccan
shekara gudar data shuɗe mizai hana na iya jure wannan balle yau dana san gidansu. Zan cigaba da farauta
nasan watarana zan dace in sha ALLAH”
Zezaah da ranta yakai ƙololuwar ɓaci ta ce, “Humm amma RK kasan dai Maanal da kafiya. Wlhy duk
abinda tace bazatai ba bafa zatayin ba. Ya kamata kaima ka gane hakan tunda dai kagani. Shekara ɗaya cur
ana abu ɗaya amma komai bai canja ba. Taya yanzu kake tunanin zata canja da kuke nesa da juna?”.
“Nabar komai a hannun UBANGIJI, shine mai sarrafa zuciyoyi a yanda yaso ai Zulfah, ina ji a raina zata
canja”. RK ya bata amsa yana haɗiye damuwarsa. Aneesa ce tai ɗan murmushi, har cikin ranta tausayinsa
take ji. Murya ta kwantar cike da son kwantar masa da hankali ta ce, “In sha ALLAHU kam tunda ka dogara
da ALLAH zakaci riba. In dai Maanal matarka ce kuwa sai ka aura, itama nasan ba tana yin komai danta
wulaƙantaka bane, akwai dai wani dalili, saboda duk wanda yasan Maanal sani na gaskiya yasan bata da
wulaƙanci, na nesa da itane kawai ke mata kallon girman kai amma sam ba haka bane ba wlhy”.
“Nima shaida ne Aneesa, shiyyasa nake mata uziri”.
“Nagode sosai daka fahimci haka RK. Bari muje mu ƙarasa gida muma, mun gode sosai da ƙoƙarin ka,
ALLAH yabar zuminci ya saka da alkairi. Mun tasoka tun daga Jos”.
Murmushi ya saki mai sanyi. Sai kuma ya girgiza kansa tare da shafa kwantaccen sajensa ya ce, “Babu
damuwa. Dama Abuja zanzo ai. Ku ba nan anguwar kuke ba kenan?.”
“Eh anguwannin duk daban-dabanne”. Zeezah ta bashi amsa.
“Oh to ku muje na kaiku ai har gida kuma. Kunga idan na tashi dawowa saina tattaroku dan ƴar darun
nan tawa al'amarin ta sai da ku a kusa”.
Dariya sukayi gaba ɗaya. Babu musu suka koma motar yaja suka bar anguwar. A gidan su Zezaah duk
suka ce ya saukesu. Dan basu da nisa da Aneesa da ƙafa ma zata ƙarasa. Su Zeezah dai ba masu kuɗi bane
ba. Amma akwai rufin asirin ALLAH. Da alama ƴar darun tasa ta fisu komai dai kam. Godiya suka masa da
sake bashi haƙuri. Ya tabbatar musu babu komai sai ya dawo dubasu zuwa weekend. Zai kuma kirasu a
waya in sha ALLAH. Daga haka yaja motarsa ya wuce...
★★★★★
A hankali ta jingina da jikin gate ɗin ƙwalla na cika mata ido. Dauriya kawai takeyi, amma tausayi RK ke
bata matuƙa. Ta jima da fahimtar irin ɗunbin soyayyar da yake mata a cikin idanunsa. Sai dai tasan bazata
iya bashi abinda yake buƙatar ba. Kota bashi ma zata cutar da shi ne kawai dan bazai taɓa samunta yanda
yake huƙata ba. Dan zuciyarta ta jima da mutuwa. Mutuwa irin wadda mushenta ma baida daɗin kallo. A
zahiri take Maanal, amma a zuciya tuni ta mutu, ta mutu babu ita a wannan rayuwar... RK na tuna mata
abubuwa da yawa a rayuwarta da sam bata son tunawa, shiyyasa akoda yaushe take yakicesa a jikinta ta
ƙarfin tsiya. Amma shi ya kasa fahimtar akwai wani ciwo ne a zuciyarta da ya jima da raunata ta ta yanda
babu wani ɗa namiji da zai sake morarta.....
Raff-raff!! Sautin tafi da dariya ya sata dawowa hayyacinta. Hannu ta kai ta share guntun hawayenta
kafin ta kai dubanta ga mai dariyar da basai an mata ƙarin bayani ba tasan Huznah ce. Ita ɗince kuwa.
Ƙyaƙyƙyawar budurwa fara doguwa san kowa ƙin wanda bai samu ba. Zata girmeta a shekaru, girma ma
bana wasa ba dan Huznah zata iya zama kusan sa'ar babbar yayarsu duk da dai ita yayar tasu zata iya
girmarta....
“Agola kafi ɗan masu gida. Wato iskanci yayi lagwada har ba'a so dawowa gida ba kenan?”. Huznah
ta faɗa tana watsa mata kallon wulaƙanci.
Idan gate ɗin da ke kusa da su ta motsa to Maanal ta tanka. Dan kuwa daga kallo ɗayan nan bata sake
dubar ko sashen da Huznah take ba taja akwatinta tai gaba cikin tafiyarta mai sanyi da tarin nutsuwar da
kowa ke ɗauka iyayi da yanga ce. Sai dai kuma hakan a gareta normal ne. Dan tun ma tana tashen rashin
jinta tafiyarta mai sanyi ce.
Ba ƙaramin takaici rashin tankawar ya saka Huznah ba. Cikin haushi ta lailayo ashariya ta maka ma
Maanal. Sai dai yanzun ma bata samu amsa ba, Maanal ɗin kuma bata waiwayo ta dubeta ba harta shige
ɗaya daga cikin ɓangarorin gidan. Domin ɓangare har biyar ne a gidan ciff kasancewar matan mai gidan
uku ne. Sai sashensa, sai kuma na samarin yaransa. Ƴammatan dai kowacce tana sashen uwarta ne....
Shigowarta sashen nasu da abinda ta taras ya wanke mata gaba ɗaya damuwarta. Dan kuwa taci karo da
ƴan uwanta biyu da yaransu duka sunzo gidan domin dawowar tata kawai. Ai tuni ta watsar da damuwar
RK data Huznah suka rungume juna. Sosai suke matuƙar ƙaunar junansu ta yanda idan ka gansu kai kanka
sai sun matuƙar burgeka.
“Amma Didi kikace min ke bazaki wani zo tarbata ba”.
Dariya wadda ta kira da Didin tayi tana mai dungure mata kai da faɗin, “Naƙi zuwa babarki ta ƙulaceni
Auta”.
A tare suka kwashe da dariya, dai-dai nan wata dattijuwar mata cikin kwalliya ta fito daga wani lungu
mai nuni da hanyar kitchen ne dan hannunta riƙe yake da wani ɗan bowl. Tuni Maanal ta saki yayunta ta
nufi matar da sauri ta wani daka tsalle ta rungumeta. Dariya yayunta da yaransu suka sanya. Yayinda matar
ke faɗin, “Oh ya ALLAHU jama'a sai yaushe Maanal zata girma ne? Yanzu idan kika karyani fa?”.
Cike da shagwaɓa, tare da sake shigewa jikin matar ta ce, “Ni dai bazan taɓa girma ba Ammie. Nayi
kewarki fiye da kowa da komai. I really miss you Ammie na”.
Ƙaramar dariya Ammien ta saki mai ƙayatarwa, tare da sake rungume ɗiyar tata a jikinta tana mai
sumbatar kanta da faɗin, “Nima nayi kewarki sosai Maanal. Congratulations my Auta, yau dai finally an
gama boko.”
“Kai Ammie dama ana gama boko?”. Ta faɗa cikin dariya mai ƙayatarwa da mutane da yawa basu san
tana yi ba. Itama Ammien dai dariyar ta sake yi, sai kuma ta ɗagota tana mai ƙare mata kallo da ƙyau.
“Auta duk kin sake rame min, kina lafiya kuwa?”.
Kanta ta kwantar a jikin hannun Ammien data riƙe, sai kuma ta amsa da, “Lafiya Lau nake Ammie.
Kewarki ce kawai ta hanani sukuni”.
“Oh wai kin damu mutane da kewar Ammie kawai. Kina nufin mu bakiyi kewarmu ba ne Auta?”.
“To Sarkin kishi, ALLAH Ammie ban taɓa ganin mai kishinki sama da Didi Amal ba. Kijifa dan ALLAH,
nayi kewarki itama dole sai nayi kewarta?”.
Jefota da filo Amal tayi, da sauri ta kauce tana murmushi. Yayinda Didi Shahidah da Ammie da yaransu ke
musu dariya..........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
00️⃣44️⃣0 4
______________
________________
.......Bayan an natsa da murnar dawowar tata da gaishe-gaishe Ammie tace ta wuce ta gaida mutanen
gidan. Fuska ta ɓata kamar zatai kuka, sai kuma ta shiga roƙon Ammien akan dan ALLAH ta barta taje tai
wanka ta canja kayanta tukunna. Ammie zata ƙi su Amal suka tayata roƙonta. Dole ta barta taje ta fara
wankan sannan, yayinda su kuma suka cigaba da aikin shirya abinci dan dama girki suke sanda ta shigo.
Ɗakin da yake mallakinta ta shiga, an gyarashi tsaf ga ƙamshi mai daɗi na turaren da take matuƙar so na
tashi a cikinsa. Sosai ɗakin ya haɗu, sai dai haɗuwar tasa baisa ta taɓa jin daɗin zaman gidan ba. Kawai dai
tana zaune ne saboda mahaifiyarta na'a cikin gidan ne. Duk kuma inda Ammie take rayuwa koda a dokar
daji ne itama zata zauna ta rayu saboda a duniya bata haɗa komai da soyayyar da takema mahaifiyarta ba.
Ita ɗin dabance a zuciyarta. Idan tace daban tana nufin daban a cikin dukan daban. (ALLAH ka gafartama
iyayenmu, wanda suke raye ka bamu ikon ƙyautata musu😭).
Jacket ɗinta ta fara cirewa, tare da ƙurama rigar ido tana mai sakin murmushi. Finally yau ta gama
sarvese, duk da Ammie tace boko ta ƙare, itafa a gareta yanzu ne aka saka ɗanba, sai dai Ammie tayi haƙuri
amma sai taga ƙarshen biro in har ana ganinsa. Sanin yaran can zasu iya shigowa su fara addabarta yasa
taƙarasa zame kayan nata da sauri-sauri ta ciri towol daga Waldrop ɗinta fari tas ta ɗaura. Bayin ta nufa
dan tasan duk abinda zata iya buƙata Ammie ta saka mata shi kasancewar ta jima bata gida. Dan watanni
biyar kenan bata zo ko weekend ba. Tunma data wuce sarvese sau ɗaya tazo gida, ɓacin ran data gumtsa a
zuwan yasa tai alƙawarin ƙin sake zuwa har sai ta kammala. Alhamdullah kuma gashi sai da ta kammala
ɗin.
Wanka tayi na gaske. Dan sai da ta tabbatar ko'ina na jikinta ya mata yanda take so sannan ta fito tana
raɓar ruwa da ƙamshin shower gel ɗin ta mai shegen daɗi daya gauraya da na sabulunta da turaren wanka.
Maanal tasan sirrin gyaran jiki da kula da jikin ma. Dan yarinya ce ƴar ƙwalisa akwai son gayu. Damma ba
Maanal ɗin da bace data taso da shegen son kwalliya kamar ƴar aljanun. Tana tsaka da shafa mai Amal ta
shigo. Cike da tsokana ta ƙaraso gareta tana faɗin, “Uhm kaga ƴar ƙwalisar gidanmu Autar Ammie. Irin
wannan ƙamshi haka kamar zaki tashi gari”.
Murmushi mai sanyi Maanal ta saki da ɗan girgiza kanta tana ajiye man hannunta data matsa. Wanda
ta matsa ɗin ta fara shafawa a fuska tana faɗin, “ALLAH Didi sai kisa a rataye mutum a tsakiyar kasuwa.
Daddyn su Safnah na haƙuri dake gaskiya. Yanzu mine abin wani ƙwalisa anan daga shafa mai dai sai
wanka. Ni ko fauda bazan shafaba ma”.
“A'a wlhy dole ki shafa. Zakije gaida waɗan can ƴan tsirkun ai sai kin cakare. Dama ga ɗan mutuminki
yazo garin, dan muna shigowa da shi na fara cin karo a harabar gidan nan ɗazun”.
Cak Manaal ta dakata daga shafa man da take zuciyarta na wani irin motsawa da ƙarfi, a take fara'ar
fuskarta ta ɓace ɓat. Sai kuma ta fara haɗiyar numfashi da sauri-sauri. Fahimtar hakan ya saka Amal
wayancewa da faɗin, “Amma ban sani ba ko shirin komawa yake a lokacin dan da akwati na gansa ma fa.
Fitinanniyar uwarsa a tare da shi ko rakkiya tai masa oho musu”.
A hankali Manaal ta saki numfashin data ɗan riƙe a maƙoshinta. Sai kuma ta cigaba da shafa manta
da kauda zancen ta hanyar faɗin, “Ina dai fatan kin soyo min fara ta Didi?”.
“Harma da su Alewar madara Munaya ta matsa nai miki”.
“Oh my sweet daughter ɗina, Shiyasa nake son yarinyar nan. She is my bestie”.
“Uhm kudai kuka sani. Ni tashi ki shirya ke ake jira aci abinci. Kin san yau akwai hira duk an haɗu”.
Murmushi tayi cike da jin daɗi, dan tafi kowa son irin wannan haɗuwar tasu. Takanji kamar su dawwama
a haka tare gaba ɗaya kamar yanda suke da can. A gurguje ta shirya cikin doguwar rigar Abaya milk color
da ɗan kwalliyar coffee kaɗan a jiki. Ta saka turarrukanta masu sauƙin ƙarfi. Suna ƙoƙarin fitowa Shahidah
ta shigo ɗakin, dariya suka sanya mata dan sun tuna baya. In dai kaga Shahidah tai irin wannan shigowar
fuska a ƙwaɓe to abinci aka ajiye zasu fara ci sukuma suka maƙale a ɗaki hira, ita kuma sam bata da jimirin
yunwa musamman idan ta dawo daga makaranta ta kwaso rana. Sai ta shigo cikin haushi tana faɗin
(“ALLAH idan baku fitoba zanci nawa ne”).
Baki suka haɗa wajen furta (“ALLAH idan baku fitoba zanci nawa ne”). Ai ba shiri Shahidah ta sanya
dariya da musu daƙƙuwa. Daga haka suka rankaya suka fito inda Ammie ke zaune a tsakkiyar falon da ƴan
jikokinta zagaye da ita. Dan a anan aka shirya abincin yanda za'aji daɗin ci fiye da saman table.
Manaal na zama yaran duk suka matso kusa da ita kowa na faɗin tare da ita shi dai zai ci. Ganin abin zai
zama rigima ta miƙe tana faɗin, “Kunga ku jira ku gani”. Kitchen ta shiga sai gata da babban faranti ta
ɗakko, ganin haka Ammie tace, “To ai kawai zuba gaba ɗaya anan Auta sai muci duka baki ɗaya”..
Cike da farin ciki suka ci suka ƙoshi, damma Ammie ta hana surutu. Bayan sun kammala babbar yarinyar
Didi Shahidah mai suna Barru ta gyara wajen tsaf sauran yaran na tayata. Maanal ya gyara zama da tunanin
Ammie ta manta da batun zuwa gaida mutanen gida sai Ammien ta harareta da faɗin, “Oya tashi kije gaida
mutane”.
Fuska Maanal ta ƙwaɓe sai dai babu yanda zatai dole ta miƙe. Hannun ƴar gaban goshinta Munaya ta
kama suka wuce tare. ALLAH badan Ammie ba babu inda zataje. Da sashen Hajiya Yaya ta fara. Hajiya Yaya
itace uwargida a wannan gida na Alhaji Usman Chalawa. Tanada yara bakwai tare dashi. Babban shine
kaɗai namiji sauran duk mata ne. Macece mai son mulki da ƙyamar talaka. Dan mahaifinta kamar ma shine
silar arziƙin mijin nasu shiyyasa take jin komai na gidan ta isa da shi kuma dole a bita har shi kansa mai
gidan ma. Sai dai kasancewar shi ɗin tsayayyen namiji ne a gidansa yasa wani abun bata da power a kansa,
dan in ma ta nuna ƙarfa-ƙarfar yakan saurin taka mata birki. Kasancewar ta mace ta farko a gidan part
ɗinta yafi na kowa girma da tsaruwa, sai dai hakan ba yana nufin na sauran matan ma bai haɗu bane. A'a a
komai dai natan yana sama dana kowa kasancewar ita ta fara tarewa a cikinsa.
Sai da Maanal ta dana door bell har sau biyu kafin ta tura ƙofar falon da sallama duk da tasan ba sallai a
jita ba kasancewarsa ƙaton gaske ne. Ilai kuwa babu wanda ya amsa mata sallamar duk da kuwa kusan duk
yaran na falon harma da ita kanta Hajiya Yayan. Sai dai kasancewar ta danna door bell kafin shigowar yasa
duk suka maido hankalinsu ga ƙofar dan son ganin mai shigowar. Suna yin tozali da Maanal wasu a cikinsu
suka kauda kawunansu cikin jan tsaki. Yayinda Hajiya yaya ta zubama Manaal ɗin idanu tamkar zata cinyeta
da su. Sai Autar Hajiya Yayan da zata iya zama sa'ar Manaal ɗin mai suna Amrah ce tai murmushi tare da
miƙewa cike da farin ciki tana faɗin, “Oyoyo mutanen Jos sauka haka babu notis”.
Murmushi Manaal ɗin tai mata, yayinda ita kuma ta rungumeta. A dai-dai nan idon Manaal ɗin ya kai ga
ƙaton dining table dake gefensu kaɗan. Sosai zuciyarta ta motsa sakamakon saukar ƙwayoyin idanunta
akan wanda ke zaune a wajen shima ya zubo ma inda take idanunsa masu kaifi.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
00️⃣55️⃣0 5
______________
________________
......Da sauri ta kauda idanun nata tamkar bata ganshi ba. Sai ma cikin wayancewa ta ɗago Amrah tana
faɗin, “Wai haka kika ƙara lukucewa matar nan?”.
Dariya Amarhn tayi da kai mata mintsini a gefen hannunta itama tana faɗin, “Ke dai zauna nan kamar
za'a hureki. Ni kin san bana wasa da cikina”.
Murmushi kawai Manaal ɗin tayi batare data bata amsa ba. Hakan yasa Amrah jan hannun Munaya tana
mata wasa. Da wannan damar Maanal ta ƙarasa cikin falon sosai. Cike da girmamawa ta kai duƙe duk da
kallon wulaƙancin da Hajiya Yaya ke mata da sauran yaran ta shiga gaidata a mutunce. A yatsine ta amsa
mata sau ɗaya ta ɗauke kanta. Hakan ya ƙona ran Maanal matuƙa amma sai ta daure, fuskarta da ɗan
murmushi ta maida ga sauran yaran ta shiga gaishesu dan duk sun girmeta. Babu wanda ya amsa mata sai
ma tsoki da wasu suka ja mata. Dai-dai nan saurayin nan dake zaune a dining ya miƙe zai fita a falon yana
kai waya kunnensa alamar zaiyi magana.
“Ina kuma zakaje Yazeed?”.
Uwar ta ƙatse masa hanzari da ƴar tsawa-tsawa. Cikin dakiyarsa ya juyo da hannu yay mata nuni da waya
zaiyi, batare da ya jira sake cewarta ba ya fice abinsa.
“Hummm! Wai shi mai wayo fa Mamma”.
Ɗaya daga cikin ƴammatan ta faɗa fuska a kumbure. Kafin wani ya bata amsa Maanal taja hannun
Munaya suka fice suma. Duk rakata sukai da harara, sai kuma wadda tai maganar ta miƙe zumbur tana
faɗin, “Ina zuwa bari na muku leƙen asiri. Dan nasan ko rantsuwa zanyi babu kaffara dan ita Yaya ya fita a
falon nan babu wata waya da zai amsa”.
“ALLAH nima na fahimci haka Nanah, dan tunda ta shigo ya dakata da cin abincin ma sai wani binta da
kallo yake. Kinga muje”.
A hasale Hajiya Yaya ta furta, “Aiko da naci ubansa a gidan nan yau. Tunda na rabashi da yarinyar nan na
kuma haramta masa alaƙa da koda inuwarta ma balle ita. Amma kuje ku ganar min yana ina”.
Ai kafin ma uwar ta rufe baki sun fice da sauri har su uku. A dai-dai fitowar tasu kuma Manaal ke
shigewa sashen Hajiya Basariyya. Hajiya Basariyya itace mace ta biyu a gidan. Itama dai ɗin ba kanwar lasa
bace ba. Dan ba mutuncin ne da ita ba. Sai dai ita akwai banbanci tsakaninta da Hajiya Yaya. Dan a zahiri
baka isa fahimtar ita ɗin wacece ba saboda macece mai fuska biyu. A zahiri akwai faran-faran da jama'a da
son nuna ita ɗin ta ALLAH ce. Shiyyasa mutane da yawa sai ta gama musu illa suke farga da ita ɗin wacece.
Macijin sari ka noƙe ce ita ta bugawa a jarida. Yaranta biyar itama a gidan kuma duk mata, dan ita bata da
namiji ko ɗaya. Huznah da Maanal ta fara haɗuwa sanda ta dawo itace ƴarta ta farko. Itama ɗin dai family
nata akwai kuɗi, dan Yayanta daya riƙeta hamshaƙin mai arziƙi ne. Kuma babban aminin Alhaji Usman
Chalawa ne, suna huɗɗar kasuwanci sosai da har wasu ma ke ganin dukiyarsu a cuɗe take da juna.
Shiyyasa itama bata yarda Hajiya Yaya ta ɗaga mata hanci ta ɓangaren dukiya dan kar ce tasan kar. Kowa
najinsa a wani shege. Komawa su Nanah sukai nasu sashen cikin taɓe bakuna. Dan Manaal na ƙoƙarin
shiga sashen Hajiya Basariyya shi kuma yayansu nama ficewa a gidan da motarsa.
Tun ma kafin su ƙaraso Hajiya Yaya data cika tai tab ta fara jeho musu tambaya cikin huci dan macece
mai ƙiba sosai. Irin ƙibar nan bata wasa ba. Dan ko daga nesa ka hango ta kasan ALLAH yayi manyan mata a
wajen nan. Zaune duk suka zube cikin takaicin rashin samo abinda za'aci mutuncin Maanal da uwarta yau a
gidan. Nanah tace, “Mamma yama fita a mota. Ita kuma ta wuce sashen Momyn Suhana”.
Cikin ƙwafa da takaicin itama bata samu yanda take so ɗin ba ta ce, “Ya taimaki kansa. Dan wlhy da yau
har shegiyar uwartata sai sun bar gidan nan. Kai na tsani mutanen nan a rayuwata”.
“Ai bake kaɗai ba Mamma”. Cewar ƴarta ta biyu mai tana huci. Auren nata ne ya mutu kusan shekara
uku kenan tana gidan. Dama ita kawai ta aurar, rana ɗaya akai bikinsu da su Shahidah yayun Maanal.
Sauran kuma ALLAH bai kawo ba, ko muce ruwan ido da jiran ƴaƴan masu hannu da manda irinsu ya
hanasu auruwa. Burin kowannensu da ma uwarsu shine suyi auren ƙwarya tabi ƙwarya.. Buɗe shafin zagin
su Manaal sukai a falon kamar sun tare musu numfashi, sai Amrah ce keta ɓata fuska dan ita bata son
hakan. Ita birgeta ma Ammien take a rayuwarta mace mai dattako da sanin ya kamata. Babu ruwanta da
duk abinda iyayen nasu keyi a gidan sabgar gabanta takeyi kawai da ƴaƴanta. Ko su duk abinsu bazasu taɓa
cewa ga randa Ammien taima wani abu mara daɗi ba, amma tasa miyasa basa sonta da yaranta?...
A ɓangaren Maanal can ma door bell ta fara dannawa kafin ta shiga. Shima dai sashen Hajiya Basariyya
da suke kira da Momyn Suhana ya matuƙar haɗuwa. Girmansa kuma ɗaya dana Ammie. Ita dai bata falon
sai su Huznah da ƙannenta dake cin dafaffen gyaɗa suna hira. Duk sun zubar da kohon a saman lallausan
carpet ɗin tsakkiya ko'a jikinsu. Dan sun san mai-aiki ce zata gyara basu ba. Har zata juya batare data musu
magana ba sai ga Hajiya Basariyya ɗin ta fito daga kitchen riƙe da kofi tana waya fuskarta da murmushi.
“A'a ƴan Jos an dawo kenan?”.
Ta faɗa cikin katse hanzarin Maanal kamar tuni ƴarta Huznah bata kawo mata labarin dawowar Maanal ɗin
ba tun ɗazun. Juyowa Maanal ɗin tayi fuskarta kadaran kadahan ta ɗan kalla Hajiya Basariyya ɗin da nata
fuskan ke ɗauke da murmushi mai ƙayatarwa, sai dai acan ƙasan zuciyarta wani irin maƙoƙon tsanar
Maanal ɗin ne ke mata kaikawo. Risinawa Manaal tai tana gaisheta. Nan ma ta amsa cike da fara'a tana
nuna ma Maanal ɗin kujera da faɗin, “Haba sai kace wata baƙuwa zauna mana Maanal ga ƴan uwanki nan
na bikin cin gyaɗa ka kuci. Da fatan dai kun dawo lafiya? Kuma komai ya kammala?”.
Kai kawai Maanal ɗin ta jinjina mata kanta a ƙasa, sai dai yanzu da ɗan gajeren murmushi a fuskarta.
Ganin bata zauna ɗin ba Hajiya Basariyyar ta sake nuna mata kujera. Kai ta girgiza mata da kama hannun
Munaya ta ce, “A'a Momy mun gode dama munzo gaisheki ne kawai”.
“Masha ALLAH aiko ina godiya. Sai dai ni bana cin miƙe gaskiya azo mini hira dai. Suma su Shahidah ki
faɗa musu ina godiya sun barni da jira. Tun ɗazun har abinci nasa akayi dasu ga gyaɗa da aka dafa amma
shiru kake ji”.
“Zan faɗa musu in sha ALLAH Momy”. Maanal ta faɗa cikin muryarta mai zurfi da nutsuwa. Daga haka ta
kama hannun Munaya tana mata sallama. Da harara duk suka bita har Hajiya Basariyyar. Sai da ta gama
ficewar harda turo ƙofar Huznah taja tsoki da faɗin, “Ni wlhy Momy ina mamakinki, kiyita wani musu
magana mai daɗi. Shegu sunzo sun gaje mana gida baka isa kai magana ba Daddy ya kama faɗin yayansa
ne suma na halak. Ko ina suka zama ƴaƴan nasa agololi. Ni ko wanda ma yakema kallon ƴaƴan nasa ƙilama
da cikinsu tazo.”
“Hummm”.
Kawai Hajiya Basariyya ta faɗa tana kaiwa zaune batare data kula maganar Huznah ɗin ba. Hakan ya sake
bama yaran haushi suka cigaba da zagin Maanal dan kamar ma sunfi tsanarta fiye da sauran ƴaƴan
Ammien. Duk da kuwa sunƙi jinin Hameed ma da Waleed da Ammien ta haifa a gidan suke matsayin uba
ɗaya dasu. Balle da Daddyn ke tsananin nuna musu soyayya. Dan yanzu haka ma yana tare dasu ƙasar
Amurika yin hutu. Duk da dai yace taro zaije ya tafi da su. Amma babu wani taro kawai yaje dasu ne dan
hutawa na sati har biyu...
Rai ɓace Manaal ta koma sashensu. Sai dai yanda bata gayama kowa abinda ya faru ba babu wanda ya
tambayeta. Sai ma zama tai suka fara hirarsu. Babu jimawa kuma Daddy ya kira Ammie ta video call. Daga
nan suka gaisa da shi ya bama Hameed da Waleed da Ammien ta haifa a gidan. Ƙanensu kenan guda biyu.
Yarane matasa da zasu iya kai shekara sha biyar da sha uku. Suma duk kamanin Ammie suka biyo kamar su
Maanal ɗin. Sai dai su farare ne sun kwaso hasken fatar Alhaji Usman Chalawa sosai kasancewarsa farin
mutum tas..
Suna cikin hira da ƙannen nasu ne babu zato akai knocking ƙofar falon. Kafin wani yay magana a cikinsu
mai knocking ɗin har ya shigo. A take Maanal ta shanye fara'ar fuskarta da maganar da take da Waleed ko
nace faɗa irin na sako duk da kuwa ta girmesa sosai. Kauda kanta tai da jan mayafin abayarta daya zame ta
rufe gashinta da ƙyau, yayinda su Amaal ke masa barka da shigowa. Shiko yana amsawa da ɗan murmushi
hankalinsa akan yaransu dake gaishesa duk da sai da ya gama ƙarema Maanal kallo a kai-akaice.
Gaban Ammie da hankalinta itama ke kansa tana ɗan murmushi ya ƙaraso. Cike da girmamawar da yake
bata ya rissina yana gaisheta. Da kulawa take amsawa itama, kafin ta ɗora da faɗin, “Baka wuce Abujan ba
kenan?”.
“Eh Ammie fasawa nai saboda wanda zanje wajensa yace yana Lagos sai gobe zai dawo. Nima kawai
sai na bari sai goben na tafi dan bana son naje naita zaman jiransa ina kuma da abinda zan ɗanyi anan ɗin”.
“To ALLAH yayi jagora. Yay muku albarka, ya kuma saka muku hannu a dukan al'amuranku”.
“Amin ya rabbi Ammie Nagode sosai”. Ya faɗa cike da jin daɗi yana maida hankalinsa kan Maanal dake
ƙoƙarin tashi tabar falon. Kansa tsaye ya furta, “Ke ƴar hidimar ƙasa yaushe kika dawo?”........✍️
Hummm yanzu fa aka fara shimfiɗar bama wasan ba. Mi kuke tsammani. Yazeed, ga kuma RK. Ga
Maanal da bama musan alƙiblarta ba. Shin wai mi aka AJIYE A DUHUN nan ne? Ya dai kamata a haska
mana mu gani ko zamu tayasu lalube🏃🏃🏃🏃🏃.
Maza garzayo cikin tawagar littafan zafafa biyar da zasu zo muku da sabon salo na musamman in sha
ALLAHU. Kowanne da salonsa da kuma takunsa. Mi kuke jira, ai sai kawai kuzo ayi tafiyar nan daku karku
bari sai wasu sun baku labari.😘😘😘
A fa dun inda ZAFAFAN suke ZAFAFAN ne😘😘
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
00️⃣66️⃣0 6
ALBISHIRINKU
💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃
Idan kinada burin samun babban jari🤝 ko siyan wata babbar kadara irinsu gida mota ko gold fili ko Gona ko
canja kayan daki ko kinada yanmata kinaso kisaimusu kayan aure ko canja rayuwarki daga tunanin yauda
kullum xuwa lissafin dollars 💰daga Kwance 💃
Uhmmm garzayo kiyi rijista da 52U kiyi aiki kisha mamaki acikin shekarar nan rayuwarki xata canja ta
dalilin yin rijista da $21 kacal😱
Yar uwa kisani cewa a kullum muna fuskantar tashin hankali idan akace mana darajar dala tatashi😫
Kullum naira da muke kashewa darajarta Kara faduwa takeyi😩
52U harkar dollars ce Mai sauki ga samu 52U alkhairi ce rijista kawai xakayi da $21/35k bayan haka
baasaka kudi a 52U kuma 52U babu level level kawai rijista ne akeyi da kudi ba platforms bane ❌
Networking ne💯
Yanxu mu yan 52U idan akace mana dala tatashi murna mukeyi ba bakincikiba sbd inkanada dala
kacanjashi naira ninkuwa yakeyi💃
Kaya kullum farashinsa tashi yakeyi Baya saukowa muna rokon Allah yahoremana abin saya don ga tsada
gashi babu isheshshen kudin saya akwai kura wllh😂 Amma Inda kudin abin bazaimaka wahalaba😅
52U idan kayi rijista xata Baka jarin loan a dashboard Dinka Wanda kullum zaidinga juyuwa 💰
Kubiyoni domin Jin cikekken labarin 52U don koda kudinka saida rabonka abin na yan baiwane
52U ba platforms bane networking ne kuje kuyi bincike kafin kuyimin magana
08031507345
___________
______________
........Idanu Manaal ta ɗan rumtse kamar zatai wucewarta sai kuma ta dakata saboda hararar da Ammie ta
watsa mata, cikin sanyinta ta furta, “Yau ne Yaya, ina yini”.
Batare daya amsa ba ya sake furta, “Ai da yake ke baƙya zumunci ko a waya sai kinso ake jinki. ALLAH
ya sanya albarka to”.
Kasancewar ta fara tafiya a taƙaice ta amsa masa da Amin. Ganin da gaske barin falon zatai kuma harga
ALLAH dan ita yazo ya dakatar da ita da sake faɗin, “Zoki bani abinda kuka girka anan ɗin naci”.
Cak Maanal ta sake tsayawa zuciyarta na wani kalan harbawa da sauri-sauri, sai kuma ta yunƙura zata
cigaba da tafiya ranta na wani kalar jin zafinsa da mamakin rainin hankalinsa. Ba abinci suka samu yana ci a
sashensu ba? Shine dan guntun kutsugu zaizo nan kuma yace a bashi abinci......
“Wai nikam ba dake ake magana ba halan?”.
Ammie ta katse mata hanzari cikin kaushin murya. Jitai kamar zata saki ihu, sai dai babu yanda ta iya dole
ta furta, “Ammie nafa amsa“ daga haka ta nufi kitchen a maimakon hanyar bedroom ɗinta. Abincin ta zubo
mata tana faman ƙannan magana a ranta. Itafa wlhy da tasan ma yana gidan bazata dawo ba. Kuma ko
yanzu idan taji zai jima a KD ɗinne gara tabi Didi Shahidah Abuja har sai ya tafi ta dawo kawai. Da wannan
tunanin ta dawo da abincin. Tana ƙoƙarin nufo falon ya miƙe yana faɗin, “Bani anan”.
Kallon dining ɗin daya nufa tayi, sai kuma ta kalla Ammie kamar zata saki kuka. Ganin Ammien ta ɗauke
kanta ta maida dubanta gasu Didi Amaal. Da baki Amaal tai mata nuni da Ammie. Hawayen da suka cika
mata ido kawai ta haɗiye kafin ta taka a hankali ta ƙarasa inda yake zaune yana jiranta. Tray ɗin ta ajiye a
gabansa. Tana niyyar barin wajen ya dakatar da ita da faɗin, “Dawo ki zauna”.
Yanda yay maganar babu wani wasa kuma a gadarance ya sake kunna zuciyarsa. Sai dai kuma babu
yanda zatayi dole ta koma ta zauna dan tun fil azal shi baya wasa dasu. Sannan kaf ɗin gidan nan babu
wanda zai ce baya tsoron Yaya Yazeed. Mutum ne bamai yawan shiga sabgar kowa ba, amma baya ɗaukar
raini. Abincin ya ɗan fara ci a nutsensa yana lumshe ido, sai da yay kusan lauma uku ya ɗago yaɗan kalleta.
Fuskarsa babu wani walwala ko alamar wasa ya furta, “Abincin Ammie dabanne a gidan nan Manaal.
ALLAH dai yasa ki gadota iya girki dan ina son abinci sosai. Idan ko kina wasa da koya ki ƙara dagewa sosai
kinji”.
“Hummm” ta faɗa kawai batare da tace komai ba. Manyan idanunsa ya ɗan zuba mata yana ɗan sake
tsuke fuska. “Miye wani hummm. Kin san fa bana son halayyar nan naki ai ko? Tom zamu fara ai kenan.
Dama baki son ina fushi dake bane. Tunda nai tafiyar nan baki taɓa nemana a waya ba why?”.
Rasama mizata ce dashi tayi, tsahon lokaci bata tanka ba har sai da ya sake tsareta da kaifafan idanunsa
sannan ta motsa lips ɗinta da ƙyar ta amsa masa da “Ai ban san da wane layi zan sameka ba”.
“Hummm dama ba niyyar kiran nawa kike da shi ba. Ni wannan halin miskilancin naki ban san yaya zan
kwashe da shi ba Maanal. Amma ba komai zanyi maganinki ai. Yanzu ke miya samu naki layin da ban
samunki kwana biyu, ko blocking ɗina kikayi?”.
Nan ma ta jima bata amsashi ba. Kafin ta nisa da ƙyar ta amsa masa a taƙaice. “Matsala ya samu,
mizaisa nayi blocking ɗinka”.
“Sai kuma kika gagara zuwa ki gyara ko?”.
Shiru tai ta ƙi bashi amsa. Shima sai ya bar zancen dan yasan ɓacin rai kawai zai ƙarama kansa. Abincinsa
ya cigaba da ci, sai da yana gab da gamawa ne yake sake kallonta da faɗin, “Lokaci fa yayi da zaki cireni a
gidan gandun nan. Dan kasa isasshen barcin daren nan da nake ya fara isata haka nan Manaal”.
“Kamar ya?”.
Ta faɗa cikin ƙosawa da mamaki kuma, sai dai muryarta acan ƙasan maƙoshi da kuma sanyi. Idanunsa da
suka ƙanƙance lokaci guda ya ɗan lumshe mata ya sake buɗewa. Sai kuma ya wani maidasu ƙasa-ƙasa tare
da muryarsa ya furta, “Saboda ina buƙatarki a gefena. A tsakanin nan a matse nake da buƙatarki a kusa
dani. Dan haka zanma Daddy magana a tada zancen aurenmu tunda kin kammala karatu harda sarvese ai
nayi ƙoƙari sosai”.
Wani irin mugun bugawa ƙirjin Maanal ya shigayi. Yayinda jikinta ke wani tsuma. Cikin rawar murya da
sake bayyanar rauninta ta ce, “Yaya Yazeed Please ka ƙara min lokaci mana, ka......”
Spoon ɗin hannunsa ya ajiye cikin tsatstsareta da idanunsa da suka hanata cigaba da maganar tata.
“Manaal lokaci kuma? Miyyasa baƙya tausayina. Kin san shekarata nawa kuwa a duniya? 35 fa nake ƙoƙarin
cikawa. Kin san kuwa nakai maƙurar ƙurewa da buƙatar abokiyar rayuwa ko? A wancan karon kince kina
son kammala karatu, nayi miki wannan alfarmar, kika kammala kika sake roƙon haɗa masters naki na sake
kauda kaina saboda Dadday, yanzu harda su sarvese duk bance komai ba amma ki sake cewa na baki
lokaci. Ko kina son sai an samu matsala na far miki a cikin gidan nan ne saboda halin da nake ciki?”.
Zuciyarta ce ta sake harbawa da sauri, duk da kuwa bawani fahimtar zantukan nasa take ba kasancewar
hankalinta ya gama rabuwa biyu. Shima ganin tunaninta na neman yin nisa da shi ya kira sunanta murya a
ƙasan maƙoshi. Ajiyar zuciyar dawowa cikin hayyaci tayi, sai kuma takai hannu ta goge ƴar ƙwallar dake
neman gangaro mata. Cikin rawar muryar kuka ta ce, “Yaya Yazeed!”.
Idanunsa kawai ya zuba mata batare daya amsa ba. Dan shima dai miskilin ne kamar yanda ake zaginta
akan natan. Sai dai ita ɗin ta takashi ta shanye. Dan shi yakanyi magana a inda yaso idan yaso hakan. Ganin
taƙi cigaba da magana ya ce, “Ke nake saurare.”
Maganar take son yi sai kuma ta kasa, sai faman wasa take da dogayen yatsunta masu ɗauke da farce
masu haske dan babu ɗigon lalli a jikinsu duk da kuwa ita ma'abociyar sonshi ce. Nuni ya mata alamar ita
yake saurare. Itama saita ɗaga masa kanta tana ƙoƙarin shanye abinda ke mata kaikawo ta cigaba da faɗin,
“Mamma!. Ya kamata ka....”
“Maanal Please, kema kin san an wuce da wannan matsalar tuni, Mamma tsakaninta da Daddy ne bada
mu ba. Mizai sa ki ɗauka ki saka hakan a tsakkiyar rayuwarmu. So please indai ba so kike ki sake jana a ƙasa
ba kuma bayan na baya ki bani haɗin kai. Ina buƙatar abokiyar halitatta Maanal. Ina cikin takura matuƙa
akan hakan kada kisa na cutu”.
Idanunta ta rumtse da ƙarfi, kalamansa na mata wani kalar kuɗa a zuciya da ƙirji. Yayinda ta wani
gefe suke maimaita kansu a sigar ƙaddararta ta ƙuruciya. Rawa jikinta ke neman farayi saboda abinda ke
neman jijjigo gyanbon ƙasan ziciyarta da kowa ke tunanin ya jima da warkewa. Kamar wanda ke karantarta
ya ce, “Okay na baki dama kije kiyi shawara dama duk wanda kike ganin zakiyi. Kafin nan dai kafin Daddy
ya dawo ki tsaida min zance ɗaya. Idan ba haka ba sai dai kiji batun saka rana. Zuwa anjima ina son ganinki
a garden, ki zo min da layin naki dakeda matsala zan saka a dubashi”. Ya ƙare maganar yana miƙewa
abinsa. Har yay sallama dasu Ammie ya fice a sashen Maanal na zaune kamar gunki da aka dasa don tarihi
a dining area ɗin ta kasa tasowa. Saima wata irin zufa ce data cika mata gaban goshi. Yayinda hawaye ke
ambaliya a saman ƙyaƙyawar fuskarta. Amaal da dama tun ɗazun hankalinta ke kanta ce ta ƙaraso wajen
da sauri. Kamota tai cikin rawar jiki tana tambayarta mike faruwa? Maimakon amsa sai ta faɗa jikinta kawai
ta rungumeta tsam ta saki wani sirrin kuka mai ban tausayi. Rikicewa Amaal ɗin tayi, hakama Didi Shahidah
tuni ta taso ta nufosu. Ammie ce dai kallo ɗaya ta musu ta kauda kanta gefe, dan ta ɗaura ɗammarar itama
bazatai sanya a wannan karon akan Maanal ɗin ba. Ta gaji da zamanta haka gara ai auren nan ko hakan
zaisa ta manta da baya. Tana jiyo yanda ƴan uwanta ke sake jera mara tambayoyi a rikice batabi takansu ba
tama tashi tabar falon zuwa bedroom ɗin ta. Bakin gado takai zaune tare da fara sarrafa wayarta, sai kuma
ta kaita kunne alamar kira tayi. Babu kuwa jimawa aka ɗaga daga can, bayan sun gaisa da tambayar juna
iyali ta fara magana kamar haka.
“Nene na kiraki ne akan ƴar gidanki, yau dai ta dawo an kammala service”. Ta ɗan yi shiru alamar
saurare. Sai kuma tai murmushi da cigaba da faɗin, “Shine ma dalilin kiran naki Nene. Dan anyi sa'a shima
Yazeed ɗin yana gida yazo wani aiki kuma zai jima kamar yanda ya sanar min. To sai nake ganin hakan
damace da za'ayi kawai a huta. Dan nagaji da wannan ɗage-ɗagen saka ranar auren nasu shi kuma Baban
nasu na biye mata. Gara ayi a huta, idan taga abin bawasa bane tama ƙarasa nutsuwa. Saboda na fahimci
Maanal fa bazata taɓa kasancewa a yanda ake buƙata ba a haka gaskiya. Amma shi idan suka je can zai san
ta yanda zai ƙarasa mantar da ita komai dan yaron nada hankali da nutsuwa. Banga abinda Yazeed bai
mallaka ba da mace bazatai alfahari da shi ba ako'ina matsayin miji”. Nan ma tai shiri tana saurare. Ta jima
kafin ta amsa da, “Ni abun sake bani tsoro yake. Yanzu haka bakiga yanda ta dawo a fige ba wannan karon
kamar kazar fakat. Al'amarin Maanal na tayar min da hankali Nene wlhy”. Ta ƙare maganar muryarta na
rawa.
“Hakane Nene ina kan yimata iya ƙoƙari na. Dan ko sadakar nan wlhy kusan don itane bana iya
jinkirtawa. Amma dai a aiko mata da ruwan addu'ar ma sai ta cigaba da sha. ALLAH ya kawo iyakar komai
ya kuma bama yaron nan ƙwarin gwiwar kwantar mata da hankali ta sake manta komai”.
In sha ALLAHU Nene bana jin Yazeed. Yarone mai addini da sanin yakamata tamkar mahaifinsa. Dan sam
baida halin mahaifiyarsa, baya kuma biyema al'amarinta kamar ba daga jikinta ma ya fito ba.”
“To Amin ya rabbi sai kin shigo ɗin ma ƙarasa”. Daga haka sukai sallama.
★★“Auta dan ALLAH kibar kukan nan haka. Wlhy yana ɗaga mana hankali. Ki mana bayanin mike
faruwa ne? Ko wani abu yace dake mara daɗi?”.
Kanta ta shiga girgiza musu tare da share hawayenta. Sai kuma ta tashi daga kwanciyar datai a jikin Didi
Shahidah ta koma ta jingina da fuskar gadonta. “Didi dan ALLAH ku taimakeni, wlhy bana son auren nan
bana buƙatarsa dan bazan taɓa yin aure ba wannan alƙawarine da naima kaina. Amma su Ammie da Yaya
Yazeed sun kasa fahimtata. Wlhy kosun matsa nayi auren nan GANGAR JIKINA kawai zai aura, sannan
bazan taɓa biyayya irin ta aure ba a gareshi, bama shi ba ga kowanne ɗa namiji. Didi miyyasa bazai fahimta
bane, Maanal ta jima da mutuwa babu ita a wannan DUNIYAR ta mutane. Duk gangar jikin dake rayuwa da
matacciyar zuciya bashi da wani amfanin rayuwa. Amma sun kasa fahimta, sun kasa min uziri, dan ALLAH
ku ku fahimtar dasu maybe zasufi saurin yarda daku idan ni basa gane yarena. Koku fahimtar da Yaya
Yazeed shi maybe ya fisu gane illar yin AJIYA A DUHU da yayi, cigaba da matsawarsa kuma zai zama
ƙonewar komai daga hasken fitilar da yake ƙoƙarin haskawa don lalubo abinda ma babu shi koda a cikin
duhun....”
“Maanal Please...”
Didi Shahidah ta faɗa tana kamota jikinta ta sake rungumewa. Itama cikin murya da lallashi ta ce, “Please
ki kwantar da hankalinki mana. Kin san ba wani lafiyace ta isheki ba. Ciwonki baya buƙatar irin waɗannan
abubuwan kinfi kowa sani. Maanal iyayenmu suna son taimakon rayuwarki ne ba cuta miki ba. Sannan
Yazeed babu abinda ya rasa daga zama cikakken Namiji. Yana kuma matuƙar kaunarki, duk da boren
mahaifiyarsa akan al'amarinku bai taɓa canjawa ba. Miyyasa bazakiyi haƙuri ki manta da komai ba ki amshi
wannan ƙaddarar?......”
“Saboda ƙaddara tana tafiya ne da rayuwa Didi, ni kuma na riga na jima da Mutuwa, mi zaiyi da gawa?
Mi zai yi da gangar jikin da babu zuciya? Mi zaiyi da wadda labarinta ya jima da rubutuwa da ƙarewa? Tuni
fa Maanal ta gama mutuwa, na mutu! ni tamkar hawace Didi..”
“Keba gawa bace Maanal, ya kamata ki fahimci bafa komai a rayuwa kake samu hundred percent ba,
dole sai kayi haƙuri da wani abun sannan kake mallakar wani. Please ki amshi ƙaddararki a karon na biyu,
nasan zaki ji daɗin zama da Yaya Yazeed wlhy mutumin kirki ne, tunda kin san dai babu yanda za'ai a barki
haka babu aure. Kuma Yazeed ya dace dake matuƙa”.
“Didi ban musa miki kirkinsa ba ko nagartarsa ko cancantarsa. Duk abinda kuke hange min nasan fiye da
haka gareshi, sai dai bana buƙatar kowanne namiji a rayuwata gaba ɗaya ku fahimta mana dan
ALLAH”..........✍️
_Tofa, mace kuwa zai yiwu tace bata buƙatar namiji a cikin rayuwarta?????. Shin jama'a mike damun
Maanal ne haka?????🏃🏃🏃🏃🏃._
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
00️⃣77️⃣0 7
.......Hawaye ne suka cika idon Amaal, yayinda Shahidah ke ƙoƙarin shanye nata itama. Tausayin ƴar uwar
tasu na ƙara cika musu zuciya. Dai-dai nan Ammie ta shigo, kallo ɗaya tai musu su duka ta kauda kanta. Sai
kuma tai gyaran murya. A tare duk suka kalleta, Maanal ta share hawayenta da ƙoƙarin kaiwa kwance,
amma sai Ammie ta riƙota tana kaiwa zaune kusa da ita da faɗin, “Auta wai yaushe zaki bar shagwaɓa
ne?”.
Baki Maanal ta tura gaba da yin narai-narai da idanu zata sake sakin sabon kukan Ammien tai mata
hararar wasa. “Kina sakin min kuka zan zaneki ne tas a ɗakin nan”.
A tare suka kwashe da dariya, dan yanda Ammie tai maganar sai ya tuna musu baya. Kai Maanal ta zuba
fitina a rayuwarta, ga tsoron dukan masifa. Dan duk rashin mutuncin da zata zuba da Ammie tace zata
zaneta take nutsuwa. Ammie data ji daɗin ganin damuwar tasu ta kau sai ta cigaba da jansu da hira. Idan
ka gansu abin sha'awa kamar wata babbar yayarsu can ba mahaifiyarsu ba. Dan Ammie an mata aure da
ƙarancin shekaru ne, kuma ALLAH ya bata haihuwan da wuri, shiyyasa idan baka sani ba sai ka ma ɗauka
ba itace ta haifi su Shahidah ba, dan za'afi ganin Maanal a ƴar farinta kamar. Kamar wasa suka sha hira
sosai sai da aka kira Magrib Ammie ta fita. Babu wanda ya sake tada batun auren Maanal ɗin har dare. Sun
idar da salla Shahidah da Amaal suka shiga kitchen, yayinda Maanal ta nufi ɗakin Ammie dan tana son
tambayarta gobe in sha ALLAHU da wuri zata fita gyaran jiki. Ta samu Ammie akan abin salla tana waya da
mijinta, dan haka ta haye gadonta ta kwanta tana saurarenta. Sun jima kafin suyi sallama ta juyo ga Autar
tata tana tambayar, “Mi kuma ya faru ƴar shagwaɓar Ammie?”.
Murmushi Maanal ɗin tayi, cikin yanayinta na miskilaye da shagwaɓa ta ce, “Ammie ina son naje gyaran
jiki gobe in ALLAH ya kaimu, ban sani ba ko kina da kuɗi. Jibafa yanda jikina duk ya bushe ga kaina sai
ƙaiƙayi yake mun”.
“Uhm ko bani da kuɗi auta ai dole na nemosu, ke idan fitinar gyaran jikin nan naki ya tashi ai duk
fatarata baƙya raga min”.
Sosai Maanal takema zancen Ammien murmushi. Yayinda Ammien ke kallonta cike da jin daɗi, idan
taganta cikin farin ciki haka daɗi take ji, sai ta dinga ganin asalin Maanal ɗinta ta baya sarkin rikici da
kwaramniya, amma yanzu duk ta zama sanyi-sanyi ga miskilanci, sam bata son sabon yanayin nata na
wannan shekarun, sai dai babu yanda zatai tana mata addu'a. Katse mata murmushin tai da faɗin, “Ke
duba wayar nan taki tun ɗazun take haske alamar kira”. Amsa Maanal tayi da faɗin, “Inaga Zezaa ce ko
Anees....” sai kuma ta kasa ƙarasawa saboda ganin number mai kiran, dan ko saving batai ba, amma
nacinsa yasa tuni ta haddace lambarsa a kanta. Fuska ta ɗan tsuke, har zata maida wayar ta ajiye sai kuma
ta dakata, dan tasan shegen nacinsa ba lallai ya barta ba idan bata ɗaga ɗin ba. Inda Ammie take ta ɗan
kalla, ganin hankalinta baya kanta ta ɗaga tana mai kai wayar kunnenta. Can ƙasan maƙoshi cikin muryar
nan tata mai zurfi da rashin sakewa tai sallama. Tana jiyo sautin ajiyar zuciyar RK da ga can, dan haka ta
taɓe baki kawai.
“Baby duk kin saka hankalina tashi. Ai da nace idan nayi kira dubu baki amsa ba komai dare zan sake
kamo hanyar Kaduna ne”.
“Hummm” kawai tace a taƙaice tana ɗan satar kallon Ammie. Ganin ita take kallo yanzu sai ta ɗan sake
ɓata fuska. Yayinda kunenta ke sauraren RK dake magana cikin kulawa da tambayarta ta samu gida lafiya.
Cikin sake maida muryarta ƙasa sosai ta ce, “Alhamdullah ina yin abune”.
Ɗan jimm yay na damuwa da nuna ƙosawa da shi da tai, koda yake yau an samu cigaba ma ta ɗaga
wayar ai. Dan haka yay guntun murmushi da har tana iya jin sautinsa tare da furta, “Okay bari na barki.
Amma Please anjima na kira to?”. Da sauri ta ce, “Uhm-uhmm”.
“Why?”.
Ya tambaya kamar zai yi mata kuka. Banza ta masa. Dan ta matuƙar gajiya da shi. Sake haɗa ido da sukai da
Ammie ya sata yanke wayar tama kasheta gaba ɗaya tana wani sake tsuke fuska. Shifa wannan mutumin ta
kula sai ta masa fatattakar karan mahaukaciya zai ƙyale rayuwarta ta huta shima yaje ya hutama ransa. Bai
san yanda tai matuƙar tsanar maza bane a duniyarta ta yanzu daya kama kansa tuni. Amma ba komai,
tunda yanzu tabar garinsu tana da damar da zata buga masa warning na ƙarshen ƙarshe da kakkaɓesa daga
jikinta gaba ɗaya, yama barta taji da matsalar gabanta...
“Tunanin mi kuma kika tafi?”.
Ammie tai maganar tana taɓata. Ajiyar zuciya ta sauke da ɗan laɓe lips ɗinta tana kaiwa zaune kusa da
Ammien. Kwantar da kanta tayi a kafaɗarta tare da rungumota. Cikin son kauda wancan yanayin ta ce,
“Ammie yau tare da ke zanyi barci nayi kewarki”.
Murmushi Ammie tai da kai hannu ta shafa ƙyaƙyƙyawar fuskarta. “Nima nayi kewarki Auta. Amma
babu yanda zanyi tunda wataran ma inaji ina gani gidan miji zaki wuce ki barni”.
Tsam ta miƙe batare data ce komai ba ta ɗauki wayarta ta fice. Da kallo kawai Ammie ta bita. Wani irin
tausayinta da ƙaunarta na sake ratsa mata zuciya. Miƙewar tai itama ta fito. A kitchen ta samesu su
dukansu har Manaal ɗin. Ta ɗan duba abinda suke dafawar ta fita ta barsu. Yanzun ma a tare sukaci abincin
daren bayan sun kammala. Suna tsaka da ci sai ga Yazeed ya shigo sashen. Duk gaisheshi sukai bayan shima
ya gaida Ammie, yayinda Maanal tai kamar bata gansa ba tanata wasa da spoon a cikin abincin. Shiko
hankalinsa duk yana kanta, duk da dai magana suke da Ammie wadda su Maanal ɗin basa jin mi yake faɗa
mata. Bai wani jima ba yay musu sai da safe ya fita. Wata ƴar ajiyar zuciya Maanal ta sauke a hankali. Babu
wanda yay mata magana sai ma Ammie data shiga musu bayanin da Yazeed ɗin ya mata. Ashe zasuje Zaria
ne gobe idan ALLAH ya kaimu ita da shi halartar wani ɗaurin auren ƴar abokin maigidan. Sunyi addu'ar
ALLAH ya sanya alkairi su duka. Sai kuma ta ɗora da faɗin Maanal ɗin ta shirya sai ta mata rakkiya ita da
Amrah dan shi Yazeed ɗin zai rigasu tafiya ne da abokinsa. Ɓata fuska tayi zatai magana Ammie tai mata
daƙƙuwa. “Sai fa kinje daddawar gida da bata son fita”.
“Nifa Ammie ba cewa zan bazanje ba. Amma gyaran jikina fa?”.
“Ki tashi da wuri ayo miki, tunda sai sha biyu ma zamu wuce in sha ALLAHU ”.
Badan taso ba dai ta amsa da to, dan taji Yazeed shima zai je. Sai dai sauƙinta tafiyan nasu ba ɗaya
bane...
Kamar yanda ta faɗa a ɗakin Ammie tai kwanciyarta manne da ita kamar za'a ƙwace mata ita ko wata
ƴar goye can. Dan da Ammien ta tashi sallar dare ma da ƙyar ta ɓangare ta a jikinta. Bata kuma jima da fara
sallar ba itama Maanal ɗin ta tashi tayo alwala. Haka take itama akwai yawan ibada kamar Ammien, dan ko
sanda take tashen rashin jinta dama Maanal akwai son addini, tun bata kai girma ba zatace zatai azumin
litinin da Alhamis, ko an hanata kuma sai tayi sai dai ta kaisa a galabaice. Kusan ƙarfe uku da rabi barci ya
fara rinjayar idonta, addu'a tayi ta koma saman gadon ta kwanta tabar Ammie anan.....
Koda suka idar da sallar asubahi ma sake hayewa gadon tayi tai kwanciyarta, dan barcine sosai a idonta,
sai kuma jikinta dake mata kamar babu daɗi. Da ƙyar Ammie ta tasheta wajen ƙarfe takwas akan ta tashi ta
shirya taje gyaran jikin nan, idan ba hakaba sai dai ta bari sai gobe idan ALLAH ya kaimu dan babu fashi da
ita za'aje Zaria. Dole ta tashi badan taso ba ta kimtsa. A falo ta samu ƴan uwanta suna hira da karyawa,
saboda saurin da take gaishesu kawai tayi ta haɗa shayi a wani gora mai ƙyau na ƴan gayu ta wuce tana
faɗa musu saita dawo.
Tsokanarta suka shiga yi akan ko gayyata ma babu. Ta fice tana faɗa musu susha zamansu baza'a
cinyema Ammie kuɗin account ɗinta ba. Idan kuma suna da kuɗi su taho. Babu kowa a harabar gidan sai
masu gadi su biyu da mai bayin fulawoyi daketa yi, da alama sauran ma'aikatan duk sun kammala nasu aiki
sun wuce. Dan dama mai sharan tsakar gida ne da mai wanki. Kamar yanda ta saba cikin girmamawa ta
gaidasu, suka amsa mata da kulawa da tambayarta gajiyar tafiya. Koda ta fito tana kallon titin da fatan
samun napep da wuri dan gidan nasu a bakin titi yake sai kawai idonta akan Yaya Yazeed dake tsaye jikin
motarsa yana waya, sai dai shima idonsa a kanta. Sai da gabanta ya faɗi, amma sai ta dake tana ambaton
sunan ALLAH. Tafiya ta farayi a ƙafa tana mai fatan zuwan napep yanzu, sai dai ko taku goma batai ba taji
horn a bayanta. Sosai ta rumtse idanunta tare da cije lips, sai kuma ta sake ɗaga ƙafa zata cigaba da
tafiyarta ya ɗan sha gabanta da motar tare da sauke glass ɗin. Cikin gizagonsa da tsare gida ya furta, “Wai
nikam yaushe raini yay ƙarfi tsakanina da ke haka Maanal?”.
Fuska ta ɗan sake tsukewa da juyowa ta kallesa. “Toni Yaya minai maka na raini?”.
Cikin tsareta da kaifafan idanunsa ya ce, “Oh bama ki sani ba ko? Zan gyara miki zama ne. Ina zaki je da
wannan safiyan haka?”.
(Kama gyaran tsaiwa ba zama ba) ta faɗa a ziciyarta. A fili kam sai ta amsa masa da, “Nan zanje kusa
wankin kai”.
“Okay, bismillah shigo na ajiyeki”.
Baki ta buɗe zatai magana ya harareta. Dole ta shiga hankalinta dan tasan halinsa shi baya son wargi.
Zagayawa tai ta ɗayan side ɗin da har ya buɗe mata, haka ta shiga tana ƙunƙuni cikin ranta. Jan motar yay
suka cigaba da tafiya yana wani shegen tuƙi a hankali kamar baya so, zatai magana wayarsa ta shiga ƙara
alamar kira. Ɗaga wayar yay ya saka a hansfree tare da yin sallama. Daga can aka amsa masa da faɗin,
“Oga kayi haƙuri ka jini shiru jiya da nace zan kira”.
Amsa masa yay da, “Eh ai harna shaƙa ma. Dan yanzu kamar ma bazan ɗaga kiranka ba dai na daure
na ɗaga ɗin. Kasan ni bana son wasa da abu mai muhimmanci Hashim”.
“Na sani oga kayi haƙuri. Wlhy ina gaya maka sai kusan 2 na samu ganawa da AA ɗin. Shima mintuna
ashirin ya yarda zai ganni da ƙyar da taimakon yaron nan nasa da nake gaya maka cousen ɗina ne”.
“Mtsoww! Mutumin nan fa na lura ɗan wulaƙanci ne Hashim. Kodan yaga muna buƙatar kayan nan
yake ta garamu haka ne? Shi ana tattalin customers shi yana yanƙwana mutane”.
“Tom oga sai dai haƙuri, sai dai kuma ni yanda na fahimcesa kamar ba wulaƙanci bane ba. Yariga da yayi
ƙarfine sosai. Dan wlhy manyan ƙasashen Larabawa nan yake huɗɗa dasu sosai. Kai harma turawan
tako'ina kayansu shiga sukeyi. Gashi abin mamaki yaro ne ƙarami dan indai bakuyi shekaru dai-dai ba to kai
zakama iya girmarsa wlhy. Amma yana da wayo da ban mamaki. Yanzu dai na taƙaice maka batu ya bamu
damar haɗuwar da shi a cikin Companyn *_MAWAAD_* ɗin. Ya kuma tabbatar min da in dai mukabi
ƙa'idar komai daya dace zamu dinga samun kayan nasu fiyema da yanda muke buƙata”.
Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi da faɗin, “Alhamdulillahi Hashim naji daɗin wannan labari. Kaga an
gama da wannan matsalar kenan. Nasan Daddy ma zaiji daɗi sosai abu kusan shekara munata fama”.
“Wlhy kuwa oga ai dole ai farin ciki. Yanzu dai na tura maka komai ta email sai ka duba”.
“Okay ba damuwa zamuyi magana”. Daga haka ya yanke kiran tare da juyowa yana kallon Maanal da duk
ke sauraren wayar tasu amma a zahiri hankalinta nakan wayarta tana duba saƙon da RK ya tura mata.
“Madam!”.
Ya faɗa a hankali cikin katseta. Jitai kamar ya dakar mata zuciya da guduma. Amma sai ta daure ta amsa
da faɗin, “Kai yaya minene kuma wata Madam?”.
Ɗan dubanta yay yana murmushi mai ƙayatarwa, sai kuma ya maida hankalinsa ga titin yana faɗin, “Ai
Madam ɗin ce. Kwana nawa ya rage kuma Manaal. Ke yanzu a yanda muken nan bakiji inama ace mu ɗin
ma'aurata bane?”.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
00️⃣88️⃣0 8
______________
Assalamu alaikum
Ina Neman mutane 20 dazasuyi register da company 52u a karkashin link Dina akan $21 wato 35k a kudin
mu na Nigeria account din zaibude a cikin 5-6 weeks idan account din yabude nikuma nayi alkawarin
zanbiya mutum 20 dinnan salary 10k kowani mutum na tsawon wata 5 kunga riba biyu kenan kuka samu
ga ribar kudin ku yadawo harda riba ga account din kun na 52u zanbude a wata na shida sai kudin ga
kwasa duk kudin ku duk wata 💃🏽💃🏽💃🏽mai ra,ayi yamin magana
https://chat.whatsapp.com/K0ECLn6O3WS1fnfCggOeu5
08083531881
______________
.......Shirun da tai na kusan minti biyu batare data amsashi ba ya sashi ɗan kallonta. Kanta tai saurin
kaudawa tana mai ƙoƙarin haɗiye ɗacin daya mamayeta. Shima sai ya ɗauke kansa bai sake magana ba.
Babu jimawa suka iso gaban gidan da take zuwa gyaran jikin, wanda yasani ne tuni saboda yanda take
ma'abociyar zuwa gidan kusan duk ƙarshen wata. Jikinta har tsuma yake nason ta fita a motar, dan bata so
ya sake mata wata magana amma sai taji motar a ɓame alamar ya saka luck. Dole ta ɗan dakata tana
rumtse idanunta. Sai kuma ta juyo ta dubesa, ganin shima ita yake kallo ta maida kan ta duƙar. Murmushin
ya sake saki kaɗan da ɗauke idanunsa a kanta cikin son basar da yanayin ke bashi a jikinsa. “Ki tayani
murna?”.
Batare data sake kallonsa ba ciki-ciki ta ce, “Tami?”.
“Akan albishir ɗin da akai min yanzu a waya. Mutumin nan kusan shekara guda kenan muna son haɗa
Bussines dashi amma ko ganinsa ya gagara a gareni. Amma yau kinji har zan samu ganinsa, nasan Daddy
zaiji daɗi akan hakan shima matuƙa”.
Karo na farko tai ɗan murmushi. Sai kuma ta ce, “ALLAH ya tabbatar da alkairi a haɗuwar taku to”.
“Amin ya rabbi dear. Ammafa nasha wahala sosai. Mutumin ya riga yayi nisa ne matuƙa saboda yanda
yake huɗɗa da manyan mutane na wajen ƙasar nan dama cikin gida Nigeria. Nasan dai bazaki rasa jin
Mawaad ba”.
“Ina dai ganin sunan Companyn a jikin buhunan shinkafa, ban sani ba ko sune ko kuma da
banbanci”.
“Yes sune. Dan yana harkar noma yanzu matuƙa a ƙasar nan. Kuma Kinga wannan harkar ma bai wani
jima da farata ba. Amma da yake ALLAH ALLAH ne cikin ƙanƙanin lokaci nan ma yayi zarra.”
“ALLAH sarki”. Kawai Maanal tace dan bataga ma'anar bata wannan labari ba ita kam da dam bata da
alaƙa da shi. Cikin marairaicewa ta ce, “Yaya bara naje kada na makara Ammie tace zamu rakata anguwa”.
Amsa mata yay da “Okay bari na barki ki wuce. Inata baki labarin abinda bai shafeki ba, haka nake
buƙatar rayuwata Manaal, wato iyalinna su dinga sanin komaina dan su kasance masu min addu'a. Dan
haka sai ki shirya, dan zaki dinga raba farinciki da mijinki hakama akasinsa idan ya gitta” ya ƙare maganar
yana miƙa mata atm card ɗinsa. Kanta ta girgiza masa da sauri. “A'a yaya ga Ammie ta bani nata zanyi
amfani da shi. Hararta ya ɗan yi da zare atm ɗin Ammien ya ajiye mata nasa a cinyarta. “Kiyi amfani da na
mijinki, dan nike da hakkin hakan ba Ammie ba. Idan kin kammala ki kirani dan ba nisa zanyi ba”.
Yanda ya tsatstsareta da ido yasa ta kasa magana. Dole ta buɗe motar ta fita dan shi in baiso wasa ba
dole kaji shakkarsa. Bai bar wajen ba har saida yaga ta shige. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali da jingina
jikinsa da kujera yana mai lumshe idanunsa. Ya jima a hakan dan yaci kusan mintuna biyar kafin ya tada
motar yabar wajen yana mai danne abinda ke tsikarar zuciyarsa game da ita.....
★★★
Yanda Maanal ta samu tarba a ciki zai tabbatar maka akwai shaƙuwa da sanayya sosai tsakaninta da mai
gyaran. Dan duk miskilancintan nan sai murmushi take da ɗan maidama mai gyaran hiranta dan tana mata
tambaya ne akan Jos. Basu wani jima ba aka fara gyaran saboda tun jiya ta sanar mata. Kafin tazo ta haɗa
komai. Gyara sosai jikinta ya sha. Ga turarruka kamar wata amarya. Hatta kanta da ƙafafunta zuwa farce an
musu ƙal. Haka Maanal take akwai son gyara jiki, ƴar gayuce sosai da son kwalliya, sai dai yanzu yanayi
yasata ɓarar da kwalliyar gefe gyaran jikinta da tsafta ne dai tana nan da abinta akoda yaushe. Sun gama a
ƙurarren lokaci, dan har Ammie na kiranta a waya ma. A gurguje ta bata ta cire kuɗin aikinta tare da amso
kayan ƙamshin data haɗa mata suka fito zata mata rakkiya. Turus taja ta tsaya da ganin motar Yaya Yazeed
a ƙofar gidan, kafin ma ta samu abin faɗa ya buɗe mata gefensa alamar ta shigo. Ganin fuskarsa babu wasa
sam yasa batai magana ba ta shiga kawai. Sallama sukai da mai gyaran bayan ta gaida shi ya amsa mata
ciki-ciki yaja motar suka wuce. Shiru motar har sun ɗan yi nisa a tafiyar cikin ƙarfin hali ta ce, “Yaya dama
baka wuceba ne?”.
“Mi kika gani?”.
Ya faɗa cikin wata irin kasalliyar murya data bata mamaki. Gashi yaƙi kallonta sam a yanzu. Itama sai
kawai ta ce, “Ba komai”.
Bai sake magana ba, itama tai shiru har suka iso gida. Sai da ya gama parking ta miƙa masa atm ɗin tana
godiya. Kansa kawai ya ɗaga mata batare daya kalleta ba ko tankawa yanzu ma. Itama sai kawai ta buɗe
motar tai ficewarta. Da Hajiya Yaya dake daga can ƙofar sashensu da wata baƙuwa suka haɗa ido, ganin irin
kallon da suke mata yasa duk ta tsargu, amma sai ta dake ta nufesu badan taso ba, sai dan mahaifiyarta ta
mata tarbiyya na girmama duk wanda ke gaba da ita. Sannan kodan Yaya Yazeed dake iya ƙoƙarin sa na
girmama Ammie zata iya shanye komai daga mahaifiyarsa itama.
“Tofa, kice agola kafi ɗan masu gida an dawo kenan?”.
Matar da suke tare da Hajiya Yayan ta faɗa cikin yamutse fuska idonta akan Maanal dai-dai tana isowa
inda suke. Wani harbawa zuciyarta tayi har tsakkiyar kanta. Ba wai yau ne karo na farko da aka fara kiranta
da sunan AGOLA gidan ba, amma har yanzu ta gagara sabawa. A duk sanda aka kirata da shi kuma tana jin
matuƙar ɗaci da zafi a ranta. Har takanyi yunkurin son barin gidan, sai dai yinƙurin nata baya zuwa ko'ina
take komawa tai laƙwas saboda wasu dalilai. Hawayen da suka cika mata idanu ta haɗiye, tare da dai-daita
kanta sannan ta ɗan risina fuskarta da murmushi ta ce, “Barka da gida Mamma. Aunty ina yini”.
Kafin Hajiya Yaya ta amsa wadda ta kira da aunty ɗin ta sauri ta cafe zancen cikin masifa, “Oh kaji wani
ɗan iskan gaisuwa wai barka da gida sai kace wasu sa'oinki?”.
Cikin sake hasala Hajiya Yaya ta ce, “Kinga da yawa ai, idan batai iyayi ba ai bata cika jinin Asiya ba,
Amma wai a haka Alhaji ke neman ƙaƙabama jinina ita”.
“Humm kar kiga laifinsa wlhy Yaya, tunda uwarta ta shanyesa kina ganin shima Yazeed ɗin zasu barsa
ne. Balle suna ganinsa shine gidan da uban gaba ɗaya”. ta faɗa tana mai ballama Maanal wata shegiyar
harara.
Tsamm Maanal ta miƙe kafin Hajiya Yaya ta bama ƙanwar tata amsa. Cikin ɗan sassarfa tabar wajen tana
mai jin ɗaci da ciwo sosai a zuciyarta game da cin mutuncinsu ga Ammien ta. Tarasa mi Ammie ta tsare
musu a gidan da su duka basa ƙaunarta...
Shikam Yazeed tana fita ya kife kansa a saman steering yana mai cije bakinsa da masifar ƙarfi. Kai bazai
yiwu ba, dolene ya zigirgiɗi Daddy azo ayita ta ƙare a bashi matarsa. Dan gaskiya yana cikin tashin hankali,
da yasan ma abinda gyaran jikin nan zai zame masa yanzun nan daya hana yarinyar nan yinsa ko kuma yaƙi
komawa ɗakkota. Ɗan buga glass ɗin saitinsa da akai da ɗan ƙarfi ya sashi ɗagowa. Sai da ya ɗan saisaita
kansa kafin ya sauke glass ɗin. Da Hajiya Yaya yaci karo, ai da sauri ya janye idanunsa da sukai wani irin
kaɗawar da duk mai hankali idan ya kallesa zai fahimci halin da yake ciki. Ita kanta Hajiya Yayan sai da taji
wani iri a ranta, amma ta dake cikin masifa ta ce, “Yazeed miye haɗinka da waccan yarinyar? A ina ka
ɗakkota?”.
Ɗan gyaran muryarsa data koma can ƙasa yayi, kafin ya furta, “Mamma anan ƙofar gida ne mai napep
ya ajiyeta shine nace ta shigo na ƙaraso ciki da ita. Wani abu ne ya faru?”.
Wata hararar bana son rainin wayo ta balla masa. Kafin cikin masifarta ta furta, “Yazeed! Yazeed wlhy
ka kiyayen, ni zaka maida sakarai ko....”
“No Mamma ba hak....”
Hannu ta ɗaga masa cikin tsawa, “Bana son ji, ka sameni ciki yanzun nan”. Tana gama faɗa ta juya ta bar
wajen. Iska mai kauri ya furzar daga bakinsa tare da sake maida kansa jikin steering yana mai lumshe
idanunsa. Yafi mintuna biyar a haka sannan ya buɗe motar ya fita yana mai saka glass a idanunsa domin
ɓoye abinda ke cikinsu. A falo ya sami mahaifiyar tasa da ƴar uwarta. Cikin girmamawa ya gaida innar tasa
dake wani binsa da kallon ƙurilla kamar mai son gano halin da yake a ciki batare data amsa masa
gaisuwarsa ba ta ce, “Yazeed! Anya kuwa kana son nemawa mahaifiyarka mutunci damu ƴan uwanta a
gidan nan. Wai kai bazaka bar batun yarinyar nan ba ne shin ko yaya kake nufi?”.
Sai da ya ɗan haɗiye abinda ke masa yawo a maƙoshi sannan ya furta, “Aunty Please mun wuce
maganar nan fa tuni. Dan ALLAH a barta kawai”.
“Anƙi a bari ɗin dan ubanka. Yazeed ni dai kake son cigaba da tozartawa ko? Ni dai mahaifiyarka dana
sha baƙar wahalar rainon ciki ka da naƙudar haihuwarka da shayar da kai. Asiya dai ta fini muhimmanci a
wajenka ko? Shike nan kaje kayi duk abinda kake ganin dai-dai ne agareka. Amma ka sani ko mutuwa nayi
kurwata bazata barka zaman aure da yarinyar can ba. Dan na riga na maka mata kamar yanda na faɗa
maka. Garama ka shirya tun kafin takaimu da bakanta a cikin gidan nan. Amma bari shi Alhajin dake ɗaure
maka ƙugu ya dawo gidan ina dai-dai dashi wlhy”.
Kasa iya furta komai Yazeed yayi, sai wani irin haɗiyar zuciya yake acan ƙasan ransa dan mutum ne mai
zuciyar tsiya dama. Haka suka cigaba da masa masifa bai iya sake cemusu komai ba har sai da ALLAH ya
taimakesa Daddy yay kiran wayarsa sannan ya tashi ya fita domin amsawa. Daga haka bai koma wajen su
ba ya gudu sashensa dan ya shirya gashi har yana neman makara....
________
A ɓangaren Manaal bata sanarma Ammie komai ba. Sai ma ƴan uwanta ne da suka zagayeta suna yaba
irin ƙyawun da gyaran yay mata. Daga haka Ammie ta korata dan ta shirya kada su makara. Saboda tasanta
da nauyin shiri. Aiko bata kammala shirin ba sai da Ammie tai mata tsiya-tsiya. Faɗan Ammien yasa ta fito
ɗauko da ɗan box ɗin da take ajiye kayan ƴan kunne da makamantansu ciki a hannu tana neman agogon
da zata saka da zobe. Su Amal ne dake musu dariya suka amsa suna duba mata. Dai-dai fitowar Ammie
tana faɗin, “K muje ai ba dole sai kinsa wani agogo can ba bana son shiririta”.
Jin hakan ya sata miƙewa dan tasan kaɗan daga aikin Ammien ta maketa ma saboda bata ƙaunar jira,
da sauri Shahidah da takamo hannunta ta ɗaura mata wanda ta zaro kalar silba kawai ta shiga ɗaura mata
batare da su duka sun maida hankali akansa ba. Daga haka suka fice hannunta riƙe da ƴar bag ɗinta sai
gwangwanin maltina data ɗauka saboda yunwan da take ji kasancewar bawani break ɗin kirki tayi ba ta fita
gyaran jikin, yanzu kuma Ammie tace bazata zauna cin abinci ba aiba itace ta hanata ci ɗazun ba sai dai ta
bari idan sunje gidan bikin taci. Itako tasan bazata taɓa iyawa ba cin abinci a gidan biki koda na wanda ta
sani ne balle wannan, duk da kamar gidane can ɗin ma saboda alaƙar dake tsakanin mai gidan da uban
amaryar mai matuƙar ƙarfi ce, ta wani gefen ma za'a iya cewa akwai zuminci. Koda yake su sai dai suyi kara
saboda Ammie kawai amatsayinsu na ƴaƴanta...........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
00️⃣99️⃣0 9
______________
Lady's collection and more
Zumar kiba
Zumar breast
Zumar hips
Zumar infection
Zumar sliming
Zumar sabon budurci
Back to virgin
Abayas
Atamfa
Less
Hijabs
Supplements
Kitchen items and more Muna maraba da masu siyan Daya ko
08169307477
Address bayan gidan drugs katsina State. Kayanmu nada inganci da zasu birge mai saye fiye da yanda yake
zato. Maza ku garzayo kada ayi babu ku.
_______________
.........Tunda suka fito ya zuba mata ido daga inda yake tsaye jikin mota. Itakam sam bata lura da shi ba tana
ta ƙoƙarin gyara kayan data zubo a handbag ɗinta dataƙi rufuwa. Sai da suka iso gab da shi ta tsinkayi
muryarsa yana gaida Ammie. Yayinda Amrah ta taɓota itama tana gaida Ammien. Ɗagowa tai ta dubi
Amrah ɗin, suka sakarma juna murmushi, harta maida kanta sai kuma ta ɗan ɗago dan sai yanzu
hankalinta ya kai garesa sosai. A take ta shanye murmushin saman fuskarta ziciyarta na takurewa waje
ɗaya a ƙirjinta. Tabbas da tasan tafiyar nan tare zata kasance musu ALLAH duk yanda zatai da sai tayi ta
zame kanta a masu yinta. Amma yanzu babu yanda ta iya dole ta dake. Ganin su Ammie sun shige itama ta
fara ƙoƙarin shiga kusa da su amma sai Amrah tai saurin rufe murfin tana faɗin, “Kije wajen Yaya mana
gashi can ya buɗe miki”.
Tsaye tai kawai tama gagara cewa komai, koda ta saci kallon Ammie sai taga ta ɗan harareta, dole ta
shiga kusa da shi ɗin tana faman sauke ajiyar zuciya. Ɗan karkatowa yay inda take kaɗan kamar zai ɗauka
abu a ƙasan ƙafafunsu. Cikin raɗa ya furta, “You look so good dear”. Kasa cemasa komai tayi, sai ma
takurewa data ɗanyi jikin kujerar, yayinda shi kuma ya ɗaga yana gyara zamansa tamkar bashi yay maganar
ba dan fuskarsa sam babu wani walwalan kirki.
Sun fara tafiya shiru motar babu mai magana. Sai da suna gab da barin titin anguwar gaba ɗaya kamar
ance ta kalla hannunta idanunta suka sauka akan agogon da Didi Shahidah ta ɗaura mata. Ba ƙaramin
bugawa ƙirjinta yay ba har kana iya ganin yanda maƙoshinta ke kaiwa da komawa a wuyanta. Ta ƙurama
agogon ido wani abu mai shegen nauyi na sake saukar mata a dukkan illahirin jikinta. Bata masan wani
ƙarfi yazo mata ba tasa ɗayan hannunta ta fincike agogon, kamar zatai wurgi da shi waje sai kuma ta daure
ta ɓalle bag ɗinta ta jefashi ciki batare data zuge zip ɗin ba ta maida kanta ta nannaɗe cikin ƙafafunta data
ɗage gaba ɗaya zuwa saman kujerar. A take wasu hawaye masu zafin gaske da raɗaɗi suka fara zirara mata.
Yanda tayi ɗin sai sukai tunanin ko barci take, musamman Ammie da tasan bawani barcin kirki ta samu ba
a safiyar yau dama daren. Shima Yazeed daya ɗauka barcin tayi sai kawai ya farama Ammie hira. A haka har
suka iso Zaria kasancewar tafiyar ba wata mai yawa bace ba. Da yake Yazeed yasan hanya basu wani sha
wahala ba nan ma suka iso. Sun sami anguwar kanta da mutane sosai balle ƙofar gidan daya kasance
masha ALLAH dan har Ammie na faɗin, “Anya Yazeed zamu iya keta mutanen nan zuwa cikin gidan kuwa?”.
Amsa ya bata da faɗin, “Ammie zaku iya shiyyasa ma nai parking tanan ganin yafi ƙarancin mutane. Zan
bidaku ta baya ne akwai wata ƙofa dana sani Uncle na amfani da ita nasan zata kasance buɗe yau kodan
baƙinsa”.
Cikin gamsuwa Ammie ta ce, “To Alhamdullah hakan ma yayi”.
Sun firfito yayinda a kallo ɗaya Ammie ta fahimci Manaal tayi kuka duk da gilashin dake a idonta. Sai dai
ta fassara kukan nata da zaman gaba da aka sakata yi ne dole. Dan haka ta watsar da ita tama haɗe fuska.
A wannan yanayin suka shiga gidan ta inda Yazeed ɗin ya faɗa. Aiko sai suka samu sauƙi jama'a anan sai
falon Uncle ɗin ne ma da mutane dan akwai takalma kusan ƙafa bakwai a wajen masu ƙyau. Wucewarsu
sukai zuwa cikin gida dan itama Ammien ba wannan ne zuwanta na farko ba. Hakama Amrah. Maanal ce
dai bata taɓa zuwa ba dama sai yau ɗin. Amma ta ɗan san yaran gidan saboda suna zuwa can gidan nasu
lokaci-lokaci...
★-----------
Babu jimawa da shigewar su Maanal tawagar ango da abokansa suka iso ƙofar gidan. Cikin tsari da
nutsuwa tarin motocinsu suka layantu dai-dai inda Yaya Yazeed yay parking motarsa. Firfitowa duk suka
shiga yi, kowa ka kalla shar da shi cikin dakakken yadi mai shegen ƙyau da tsada, wasu kuma shaddoji. Sai
shima ango dake sanye da shadda fara ƙal tanata maiƙo da ɗaukar idanu. Sun gama firfitowa sai motar
dake kusa data Yazeed ce kawai wanda ke ciki baida alamar fitowar, sai da angon ya juya yana ɗan kalle-
kalle da faɗin, “Wai Uncle fa?”.
Duk motar suka kalla. Kafin wani a cikin abokan yace, “Bai kai ga fitowa ba kamar ma suna magana ne
da Uncle Nass”.
“Oh ai fa an haɗu. Ni dai suyi su fito kar a fara neman waliyyai aga duk basa kusa. Bara ma na taɓa su
Uncle Fawzan suma”.
Dariya abokan nasa suka sanya masa da shaƙiyanci. Yayinda yay gefe yana dariya. Wanda dai ya ambata
da Uncles basu fito a motar ba sai kusan bayan mintuna talatin, suma ɗin dai ba tsoffi bane, matasane da
shekarunsu ya haura talatin kaɗan, ɗaya ma zai iya girman ɗayan. Wanda bai kai shekarun ba dake sanye
cikin yadi milk ne ya fito ta sashen da motar Yazeed take. Ɗan jingina yay da motar yana amsa waya kansa
a sunkuye ta yanda ko fuskarsa ba'a wani gani da ƙyau. Yaci fin mintuna biyu a haka kafin ya katse wayar
yana mai kai wa duƙe ya ɗauki abinda idonsa ya sauka a kai tun fitowarsa dake yashe a ƙasa. Agogo ne
silver na mata mai ƙyau sosai, juyawa yay ya kalla motar daya jingina batare da yayima agogon wani kallon
tsaf ba. Har ya kai hannu zai aza agogon saman motar da tunanin maybe masu motar ne suka yadda sai
kuma ya fasa. Tunanin ajiyewa yay a hannunsa dan maybe su haɗu da masu motar sai ya basu, kada ya
ajiye kuma wani ya ɗauka dan a ɗan kallon fisha da yay ma agogon ya fahimci mai daraja ne da za'a iya
sayensa da kuɗi masu yawa. Motar da suka fito ya buɗe ya jefa agogon sit ɗin mai zaman banza daya zauna
dan ɗayan ne yayo driving ɗin. Daga haka ya juya abinsa kawai....
______________★
Duk da yawan taron jama'a bai hana ai musu tarba ta musamman ba da girmamawa da mutuntawa. Dan
can ƙuryar ɗakin amaryar gidan aka kaisu tare da musu sauka ta musamman da abinci da kayan ciye-ciye
irin na biki. Sai nan nan Hajiya Majdiya keyi da Ammie dan tuntuni take son su jone su zama ƙawaye
Ammien ce dai bata maida hankali ba. Ita kuma ba komai yasa hakan ba sai sanin uwargidanta jone suke
da Hajiya Yaya 5&6, ko bikin nan ma dan na yarinyar matar tsakkiya ce shiyyasa Hajiya Yayan bata zo ba
saboda suna matuƙar adawa da juna. Ita kuma aminiyar Hajiya Basariyya ce dan ita tun sassafe ma tana
nan Zaria ɗin da duka yaranta kuma kwana zasuyi dan har Abuja inda za'akai amarya zasuje ma.
Ƙorafin da take tayi yasa Ammie bama su Maanal umarnin cin abincin. Amrah ce ta zuba ma Ammie
sannan ta zuba musu. Maanal na cewa ta ƙoshi Hajiya Majdiya tace, “Haba ɗiyata kada kimin haka mana,
idan kuma baƙya sonshi na canjo miki wani ko na dafo miki yanzun nan”.
Da sauri ta ɗauki spoon ta saka cikin abincin, hakan ya saka Amra kwashewa da dariya. Sunci abincin
Ammie da Hajiya Majdiya na hira sai ga wata budurwar yarinya ta shigo ɗakin. Zasu iya zama sa'anni dasu
Maanal, tayi ƙyau cikin lass da nake ƙyautata zaton ankonsu kenan dan ƴammata da yawa na dashi a wajen
bikin. Tafawa suka ɗan yi da Amrah alamar sun san juna sosai sai kuma ta ɗan zunguri Maanal cike da
tsokana ta furta, “Kurman Ammie”. Hararta Maanal ta ɗan yi duk da ba wani sabo sukai ba gaskiya, dan ko
gidan sukaje iyakar Maanal ɗin da su gaisuwa ne. Cikin dariyar da suke ta gaida Ammie, yayinda Amrah ke
faɗin, “Amma fa sunan nan ya dace da ita sosai, Najwa kin iya saka suna ALLAH”.
Dariya Ammie da Hajiya Majdiya suka sake yi. Nan dai suka cigaba da tsokanar Maanal ita da Amrahn.
Bayan sun tsagaita ta dubi Maman nata tana faɗin, “Ummy Uncle Rafeeq fa ya iso”.
“Oh Masha ALLAH har ya ƙaraso, da'alama gudun nashi na tsiya yayi kenan. Yana ina?”.
“Na kaisa ƙaramin falonki wai yunwa yake ji, sai yaci abinci zai fita wajen ɗaurin aure”.
Ƴar dariya tai da faɗin, “Acici kenan mala'ikun tauna. Ga key dama na haɗa masa abincin ai. Idan kin
ɗauka ki rufe min kitchen ɗin, sai ya gama sai nazo mu gaisa”.
Amsa tai tana miƙewa, sai kuma ta kalli su Amrah, “Ku taso muje kunzo kun ƙunshe a nan. Amrah karfa
ki bari Maanal ta koya miki halinta”.
Da sauri Amra ta ce, “Da naga takaina. Maanal fa ko maijego bazata faɗa mata zaman ɗaki ba, magana
kuwa yakan iya sati batayi da kowa ba”.
Hararar su Maanal tayi batare data motsa ba ko yin magana. Ganin haka suka fahimci bazanje ba. Dan
haka Najma tai saurin kai ƙararta wajen Ammie. “Ammie kinga wai bazata ba”.
Kallon Maanal Ammie tayi dole ta miƙe badan taso ba suka fita. Kitchen ɗin ta shiga ta ɗauka basket ɗin
da aka shirya kayan abincin sanan suka bi wani ƙofa, roƙonsu take akan suje kai amarya Abuja dan ALLAH.
Yayinda Amrah ke bata amsa da basuzo da wasu kaya ba. Dai-dai zasu shiga take cewa baga nata kayan ba
tasan zasu musu ai, kokuma idan zasu wuce Abujan su tsaya kd ɗin su ɗauki kayan. Shigarsu tasa babu
wanda ya bata amsa. Falone ƙarami amma yayi ƙyau sosai cikin tsari.
“I'm sorry Uncle na barka kana jira”. Ta faɗa dai-dai tana ƙarasawa gaban mutumin dake zaune ya ɗan
juya ma ƙofa baya ta yanda basa ganin fuskarsa da ƙyau. Juyowa yay ya kallo ta inda suke cikin sigar harara,
sai idanunsa cikin na Maanal.
Cak kuwa ta tsaya kamar wadda aka buge mata ƙafafu da sanda, hakama numfashinta sai da yay rawa.
Shima ɗin da wani kalar mamaki ya zuba mata idanunsa har yana ɗan warosu waje na kasa ɓoye mamaki.
Sai yanda yay ɗin ya saka su Amrah kallon Maanal ɗin suma cike da tambayoyi.
Lips ɗinsa ne suka ɗan motsa a hankali ya faɗi abinda ita da su duk basu ji ba. Yayinda Najma ta furta,
“Uncle ko ka sansu ne?”.
Maimakon amsa mata sai ya saki wani ƙayataccen murmushi kawai da kai hannu ya ɗan shafo sajensa
siriri yana lumshe idanu da kauda kansa gefe. Itama Maanal janye nata idanun tayi a hankali daga garesa,
sai kuma ta juya da nufin fita. Najma ce ta riƙota da sauri tana faɗin, “Kimma isa madam. Dawo ku gaisa. Ai
mu wannan abin farin ciki ne agaremu Uncle Rafeeq da budurwa a yau”.
Da sauri Maanal ta harareta da faɗin, “Aka faɗa miki”.
“Basai an faɗa mana ba komai ya bayyana kansa ko Amrah?”. Tai maganar da kallon Amrah da jikinta
duk yay sanyi. Murmushin yaƙe ta mata da faɗin, “Ai kam dai gara mu sani”. Maanal zatayi magana suka ja
hannunta suka ƙarasa cikin falon dole badan taso ba. Zama sukayi ita da Amrah, yayinda Najma ta duƙa
gabansa tana haɗa masa abincin. Shiko ya zuba ma Maanal ido ko ƙyaftawa baiyi. Ita kuma data ɗago taga
ita ɗin yake kallo sai ta ɗan hararesa, shi kuma ya sakar mata murmushi. A haka Amrah ta gaishesa. Ya
amsa mata cike da basarwa kafin ya maida dubansa ga Najma, cikin sigar tambaya yay mata nuni da
Maanal. Juyawa tai ta kalleta itama da ƴar dariya a fuskarta ta ce, Ƙawayena ne kuma ƴan uwana.”
“Uhm yayi ƙyau” ya faɗa yana maido kallonsa kan Maanal dai. Hakan yasa cikin dauriya da sake tsuke
fuska ta ce masa “Ina yini”.
Kansa tsaye ya amsa da, “Ya gajiyar tafiya? Da ƙin amsa min waya?”.
Jitai kamar ta ja abu ta wulwula masa bisa kai amma dai ta daure kodan su Najma, batare data
kallesa ba ta ce, “Hummm”.
Shima Humm ɗin ya faɗa yana ɗaukar spoon ya fara cin abincinsa.
“Oh oh mukam an sakamu a duhu, Uncle Please ka mana bayani”.
“To uwar gulma anƙi ɗin. Ga ƙofa maza kama gabanki idan na gama zan nemoki. Auntyn ma kice ta hutar
da kanta ma gaisa bayan an ɗaura auren”.
“Oyooooo!! Korarmu ma ake, kinga Amrah taso mu ware to”. Tai maganar tana kama hannun Amrah
suka nufi ƙofa. Miƙewa itama Maanal tayi dan bazata yarda a barsu su biyu ba, sai taga shima ya miƙe
idanunsa a kanta kamar zai cinyenta da su.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
______________
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
____________
........Fuska ta ɓata sosai kafin ta kallesa babu wasa. “Kasan fa bana son irin haka ko?”.
Kansa ya ɗan rausayar gefe yana murmushi da raba idanunsa a kanta. Cikin raɗa-raɗa ya ce, “Sam ban
sani ba sai dai yanzu da kika faɗa min”.
Harararsa ta sake yi zata raɓasa ta wuce yay saurin shan gabanta yana ƙara faɗaɗa murmushinsa. “ALLAH
idan kika ce sai kin fita tare zamu fita ne, kuma duk inda kika shiga sai na biki a gidan nan kin dai sani”.
Ɗagowa tai da mamaki ta kallesa, “Ka bini fa?”.
“Yes gwada kuma ki gani, kin dai sai ni nafi mayen ƙarfe ai garama ki koma ki zauna kawai”.
Kanta kawai ta ɗan girgiza, a zuciyata tana faɗin (Kai guy ɗin nan bala'i ne). A fili kam sai kawai ta koma
ta zauna a kujerar dake kusa da ƙofar dama anan ta tashi. Ajiyar zuciya ya sauke shima tare da komawa ya
zauna a inda ya tashi. Sai da ya ɗiba abincin zai kai baki sannan ya ɗago ya kalleta. “Bismillah”. Kanta ta
girgiza masa kawai batace komai ba. Shima sai bai damu ba ya cigaba da faɗin, “Ina su Aneesa?”.
“Gida”.
Ta faɗa a taƙaice.
Kansa ya jinjina kawai shima. Sai kuma falon yay ɗan shiru, a can ƙasan zuciyarsa wani irin farin cikine ke
ɗawainiya da shi. Har dai ya kasa dannewa sai da ya furta, “Ashe ma ni a gida nake farauta amma naita
wahalar da kaina. Ya kuke da su Najma?”.
Ɗagowa tayi na ɗan kallesa, ganin shima ita yake kallo sai ta maida kanta ga wayata kawai.
“Humm zama da miskilin mutum dai sai haƙuri, shike nan tunda bazaki sanar min ba. In tai wari naji. Ni
bara na faɗa miki nawa alaƙan da su to. Mahaifiyarta Yaya tace uwa ɗaya uba ɗaya. Nine autan ɗakinsu,
shiyyasa kikaji Najma na kirana Uncle”.
Har cikin rai sai da taji tashin hankalin alaƙar tasu. Amma sai ta dake a taƙaice ta ce, “Masha ALLAH”.
Murmushi yayi da ɗan girgiza kansa. Dai-dai nan Hajiya Majdiya tayi sallama. Amsawa yay yana mai maida
dubansa ga ƙofar tare da bata izinin shigowa. Koda ta shigo idonta a kansu, fuskarta kuma ƙawace da
murmushi. “Auta na kasa haƙuri ne ALLAH, yanzu Najma taje mana da wani daddaɗan labari”.
“Kai wannan yarinya da gulma take aunty”.
Cikin dariya Hajiya Majdiya ta ce, “Aini gulmar tata ta biyani. Kai idan hakan ta kasance zanyi matuƙar
farin ciki Rafeeq. Kaga tuwona maina kenan, ALLAH ya tabbatar da alkairi dai”.
Ko kunya Babu ya amsa da, “Amin aunty. Sai kita tayani addu'a dan gimbiyar har yanzu taƙi bani
babban fili koda na zuwa gidane a sanni. Kuma shekara ɗaya kenan muna tare”.
“Kai haba shekara ɗaya fa? Wai kodai dama itace kake faɗa mana ni da Aunty Babba kwanaki wadda
kuka haɗu a jos?”.
“Tabbas itace aunty”.
“Ikon ALLAH, ni ashema abu a kusa dani yake haka. Karka wani damu kanka Maanal yarinyar kirki ce
kamar yanda kake mutumin kirki. Na tabbatar itama zata soka”.
Ko kunya babu ya kalli Maanal yana wani ɗage gira da faɗin, “Wai haka?”.
Da sauri ta ɗauke kanta zuciyata na wani irin gudu da sauri-sauri. Yayinda take jin wani irin takaicinsa na
yanda ya ɗaureta gaba ɗaya a wajen matar da take matuƙar ganin girma da kimarta. (Ya ilahi, RK kuwa
nada hankali?) Ta ayyana a zuciyarta tana jin kamar ta saki kuka. Ita sai ma taji tausayin Hajiya Majdiya ɗin
yanda taketa farin ciki kamar ma ance an aura masa Maanal ɗin.....
Bayan ficewarta ta kallesa da idanunta da suka kaɗa dan masifar dake cin ranta. Sai dai tana motsa
baki zatayi magana ya mike yana dariya. “Koma mi kike son faɗa haɗiye abinki ni na tafi wajen ɗaurin aure,
ALLAH yasa muma azo namu nan kusa”. Yay ficewarsa yana kashe min ido ɗaya ga dariyar rainin wayo yana
yi. Yana fita baifi da mintuna biyu ba, kafin Maanal ta gama tattaro abinda ya dunƙule mata nunfashi
Najma da Amra suka dawo. Rungumeta Najma tai tana farin ciki wai zata zama matar Uncle ɗinta.
Surutanta take amma ita Maanal sam bata wani fahimtar komai....
_____________★
“Wai nikam lafiya duk kin zama wata sukuku ko duk gajiyar bikin ce haka Auta?”.
Didi Shahidah ce mai maganar tana zama kusa da Manaal dake kwance a doguwar kujera idanunta a
lumshe. Tunda suka shigo gidan ta zube a wajen tana bitar abinda ya faru a Zaria. Ƙaramin murmushi ta
sakar ma ƴar uwar tata. Sai kuma ta yunƙura ta tashi zaune sosai. “Babu komai Didi. Kawai na kwanta ne
dai”.
Murmushi Didin tai mata, sai kuma ta kai hannu ta ɗan shafi fuskarta. “Auta gyaran jikin nan na amsarki
sosai. Idan kika yosa duk sai ki canja kamar wata amarya dake”.
Da sauri Maanal ta ɓata fuska. Zatai magana aka buga ƙofar falon da ƙarfi har duk sai da suka razana.
Hajiya Yaya ce sai yaranta biyu biye da ita. Cikin hargagi da masifa ta shiga ƙwala kiran ainahin sunan
Ammie. Duk miƙewa sukayi, dan yanda take a birkice zakasan babu lafiya. Ita kanta Ammie da sauri ta fito
ɗankwalinta a hannu.
“Ya salam Hajiya miya faru?”. Ammien ta faɗa tana ƙarasowa cikin falon da sassarfa.
“Oh tambayata ma kike miya faru? Wai Asiya nikam kodai ke kika haifar min Yazeed a gidan nan ne?”.
A hankali Ammie ta sauke ajiyar zuciya tana mai girgiza kanta. Sai kuma a nutsenta ta bata amsa da
“Hajiya kiyi hakuri ban san akanmi kike magana ba. Yazeed ai kowa yasan kece kika haifesa”.
“To kuwa tunda kin san ni na haifi abina ki fitar min sabgar yaro. Dan wlhy idan ma kina mafarki ne ki
farka. Ki kuma je ki sanarma bokanki anan anfi ƙarfinki anfi ƙarfin tsafinsa. Alhajin dai da kika iya mallaka
har kika aura kinci nasara, wataran kuma ruwa zai ƙarema ɗan kada shima. Amma Yazeed har gaban abada
bazai auri wannan ƴar taki ba, wancan ya samu ya gudu da ƙyar ko nace uwarsa ta miƙe tsaye a kanku
shine ni za'a ƙaƙudubar min yaro da tsafi da asiri a haɗashi da sauran ciwo. Kuma wlhy daga yau sai yau,
kika sake ɗaukar min yaro ya kaiki anguwa duk abinda nai miki kece kika jashi a gidan nan, mayyar mata
kawai.......”
“Haba Mamma nafa miki bayani Daddy ne yace muje ba laifin Ammie bane ba”. Yazeed daya shigo falon
ya katseta cikin sarƙewar murya. Kansa ta juya da masifa kamar zata cinyesa. Harda faɗin idan har bai rabu
da Maanal ba ALLAH sai ta ɗaga masa mama. Sai kuma ta juyo ga Ammien ta cigaba da mata zagi na rashin
mutunci da gori. Gaba ɗaya rayukansu Shahidah sun gama ɓaci, yayinda Amal ta kasa haƙuri ta yunƙura
zata tanka mata Ammie ta hanata. Dole tai shiru. Da gudu Maanal tabar falon kuka mai ƙarfi na ƙwace
mata. Hakan yasa Amal bin bayanta itama zuciyarta kamar zata kama da wuta. Sam bata so Ammie ta
hanata ba. Amma koba yau ba ta ɗauki alwashin sai ta gogema matar nan abinda ke kanta. Haba wanna
abin ya isa haka mana. Tasara miyyasa mutanen nan basu da adalci sam, kowa dai Ammiensu kowa
Amminsu sai kace itace kaɗai kishiyarsu. Taga dai suma kishiyoyin juna ne, amma basa fitinar juna sai
Ammie, shin sai yaushe ne Ammiensu zataji daɗin rayuwar aurenta?. A gidan mahaifinsu bata zauna lafiya
ba, fitinar miji data uwar miji, aka dawo ta kishiya har sai da ta bar musu gidan, yanzu kuma anan ta
kishiyoyi har biyu....
Sosai Hajiya Yaya ta diga jidali da tujara wa Ammie kamar ta samu ɗiyarta. Ammien kuma bata tanka ba
bata bar ƴaƴanta sun tanka ba. Hakan kuma shine mafi mata ciwo, kai su duka su wannan shirun da
Ammien ke musu akoda yaushe na ƙona musu zuciya da ruhinsu. So da yawa suna mata abu dan ta tanka
amma sai ta basar. Da ƙyar Yazeed ya lallaɓata ta fita. Suka bar Ammie da su Manaal cikin matsanancin
ɓacin rai. Ga Ammie ta hana kowa maganar har dare sashen nasu babu daɗi. Hakan yasa duk suka kwanta
da wuri. Sai can cikin dare Maanal ta bar ɗakinsu da ayanzu yake nata ita kaɗai sai idan sauran ƴan uwan
nata sunzo gidan ne ta koma na Ammien. Ta sameta tana salla, dan haka itama ta fasa kwanciyar tayo
alwala tabi sahunta. Sai da sukai sallar asubahi suka ɗan sake kwanciya Maanal ɗin dai nata daurewa dan
bata jin daɗi......
____________
“Wai Auta bazaki tashi a barcin nan naki ba haka nan. Jibafa lokaci ko kari bakiyi ba, ga ƴan uwanki na
jiranki ki rakasu gidan mai gyaran jiki. Suna fara damunki kuma nasan zaki manta da yunwar cikinki ne ku
tafi”.
Kaɗan Maanal ta buɗe idanunta ta ɗan kalla Ammie mai maganar ta maida ta lumshe tare da sake
naɗe jikinta waje guda. A yanayin mai barci da yanayin muryarta mai zurfi ta amsa da, “Ammie bana jin
daɗi”. Da sauri Ammie ta ajiye abinda ke hannunta ta nufeta. Zama tai a bakin gadon tare da janye duvet
ɗin da take a ciki ta ɗaura hannunta a goshinta, da sauri ta janye ta maida a wuyanta. “Ya salam, Manaal
kinga tashi muje asibiti jikinki zafi, amma bayan kinyi sallar asubahi ne ma zazzaɓin nan dai?”.
Hannun Ammien ta riƙo ta rungume a ƙirjinta. Cikin rauni ta furta, “Ammie abinne zai zo, ga kuma
ƙirjina yamin nauyi, kwana biyu kenan kullum da safe nake zazzaɓin, shekaran jiya ma da muka taho banda
lafiya”.
Sosai rauni da damuwa suka bayyana a fuskar Ammie. Muryarta har rawa yake wajen furta, “Yaushe ya
dawo yimiki kuma Maanal?”.
“Ammie duka watannin nan da banzo gida ba yanayi. Na ƙarshen nan kwanana uku a hospital ma,
hakkin ma ji nake kamar zai dawo”.
“Ya arrahaman. Amma a watannin nan idan na tambaye ki kuma kita cewa babu damuwa. Haka kika
dinga shiga cikin halin nan Manaal amma kina ɓoye min? Shiyyasa tunda naga duk kin sake figewa nasan
kin ɓoyemin abubuwa ne. Nikam wannan ciwon naki na tayarmin da hankali, dan ALLAH Maanal ki cirema
ranki duk wani abu, itafa rayuwa ɗaya ce, sannan bawa baya kasancewa a cikinta sai da jarabawa dama.
Bakiga na haƙura nima na manta komai ba, hakama ƴan uwanki?”.
“ALLAH Ammie babu abinda na sakama raina, kune kuke ganin kamar har yanzu ina riƙe da abubuwa,
amma sam ba haka bane ba. Nifa musulma ce, kuma nasan minene rayuwa da ƙaddara. Ki cigaba da min
addu'a kawai Ammie”.
“In sha ALLAHU koda yaushe cikin yi muku nake. Kuma Alhamdullah da sauyin rayuwa da UBANGIJI ya
bamu mai tazara sosai, idan mukai dubi da baya. Tashi kiyi wanka naima bana maigadi magana ko zamuje
wajen mai maganin nan tunda nasa anji daɗinsa”.
“Amma Ammie shima kuma gashi ya dawo ai”.
“Duk da haka Manaal, ai kin samu ban iska tunda an samu sassaucin wahalar nan da kike sha kusan na
shekaru bakwai”.
Kanta ta ɗan jinjina cike da damuwa. Dan ita kanta ciwon nan na ɗaga hankalinta, ga shi kusan duk
sanda zatai period sai abun ya ƙwaɓe mata da ciwon mara da take fama da shi shima, dan kamar ciwon
maran yana zama sanadin tada ciwon zuciyar ne sakamakon tuno mata da abubuwan da suka faru baya da
hakan keyi a duk irin lokacin. Har rama take farayi idan akace maka lokacin nan ya matso mata. Dan ita
kaɗai tasan irin kalar azabar da take sha a rayuwarta. Duk yanda zata misalta ba lallai a fahimta ba.
Shiyyasa idan akace mata haihuwa nada ciwo sai taita mamaki da ganin anya zata kai azabar da take sha a
ciwon mara idan zatai period. Itafa nata ma dabanne dana duk wanda ta taɓa sani, ƴan uwanta ma duk
sunayin ciwon idan zasuyi prioud ɗin, amma bai kai ko rabin nata ba. Kuma sunayin aure duk suka daina.
Ammie tace ita suka gado, dan itama tasha fama har sai da ta haihu sannan. To ita abin nata ya zama biyu
ne, ga ciwon zuciya kuma, shiyyasa hankalin kowa ke matuƙar tashi a duk sanda irin haka ya taso
musamman akan ita Manaal da nata yafi tsauri.
Ammie da kanta ta taimaka mata har zuwa bayi bayan ta haɗa mata ruwan zafi. Haka ta daure tayo
wankan ta fito sai kuma rawar sanyi. Kasa zaman shafa mai ma tayi ta haye gadon ta sake ƙudundunewa.
Dai-dai nan Amaal da Shahidah da Ammie tai kira a waya ta sanar musu suma Baba maigadi magana akan
maganin Maanal ɗin dan ɗan uwansa ne ke bata suka shigo ɗakin. Su kansu su Shahidahn duk fuskokinsu
sun nuna damuwa. Ƙarasawa sukayi inda Manaal ɗin ke ƙudundune suna mata sannu. Sai kuma Shahidah
ta juya ta fita tana faɗin bari na amso maganin dan kamar sallamar Baba maigadin. Ilai kuwa shine, dan
babu jimawa ta dawo da magani a gora. Da taimakon Ammie suka bama Maanal ɗin saboda rashin sonta
da magani. Tana gama sha kuwa sai amai, dama haka yake mata, sosai tayi aman har ta basu tausayi. Haka
suka taimaka mata suka gyara mata jiki ta sake yo wanka ta canja kaya ta koma ta kwanta. Cikin amincin
UBANGIJI sai kuma barci mai nauyi sosai yay awan gaba da ita. Ajiyar zuciya suka dinga saki a tare, saboda
in sha ALLAHU suna ganin kuma shike nan.
Barci kuwa tayi sosai, dan bata farka ba sai bayan azhar. Alhamdullah taji daɗin jikin, ta samu ta sake yin
wanka Ammie da kanta ta bata abinci, sai da taci sosai dan Ammien nata lallaɓata ga kuma waya da sukai
da Nene zata zo gobe in ALLAH ya kaimu ya sake sakata jin daɗi saboda matuƙar son Nene da take a
rayuwarta. Ga kuma ƴan uwanta zagaye da ita. Hakkanne ya sake ƙarfafata zuwa bayan la'asar tace suje ta
rakasu gidan mai gyaran jikin zata iya. Koda sukace a'a sai Ammie tace suje ai fitar zata saka ta sake jin
ƙarfin jikinta ta kuma warware. Da wannan shawarar sukai amfani suka tafi........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
1️⃣1️⃣1️⃣1️⃣
______________
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
_________
.........Fitarsu babu jimawa ashe masifar Hajiya Yaya ta jiya bata ƙare ba. Dan yau yinin nan guda bata gidan,
sai yanzu zuwa yamma sai gata ita da ƙanwarta da suke kira Aunty Sabuwa a gida da yaranta ƴammata
guda biyu. Nan fa wata sabuwar fitinar ta tashi dan har sashen Ammie suka sameta wai sun sake zuwa
mata gargaɗi ita da Maanal akan Yazeed. Yayinda aka nuna ƙaramar ƴar Aunty Sabuwar wai itace Yazeed
zai aura dan haka sai Maanal da Ammie su maida maitarsu a kansa. Ba ƙaramin zafi kalaman sukaima
Ammie ba. Ga shi lokacin su Manaal ma basa gidan taje raka su Shahidah gidan mai gyaran jikin da za'ai
musu. A yanzun kam kasa daurewa Ammie tai ta yayyaɓa musu magana. Fuskarta kuma ɗauke da
murmushin da yake ƙona zuciyarsu ta kalli Sabuwa mai kora bayanin..
“ALLAH sarki ai mu wannan abin farin cikinmu ne Sabuwa. Ina kuma taya Yazeed murna da fatan alkairi
dan ko bai auri Maanal ba har gobe ɗa yake a gareni tunda ina auren mahaifinsa. Daga ke har Yaya kuma
ku daina ɗagama kanku hankali akan Maanal, dan ita dama sam bata buƙatar wannan haɗin, ta karɓa ne
kawai dan maida alkairi da hallaci. Har miye abin kace nace da ɓacin rai akan abinda ALLAH ne maiyi kawai.
Wani rabon zafi ne da shi musamman ma na aure, idan aka tsananta sai ya kawar da rayuwa kuma ayi
abinda ba'a son a bayan ran masu adawar”.
“Oh kina nufin zaki kawar damu kenan ki aurama Yazeed ƴar ki?”.
Hajiya Yaya da kalaman Ammie suka shige ta ta faɗa a hargitse. Murmushin Ammie ta sake yi da faɗin,
“Rayuwa da mutuwa ai na ALLAH ne kawai Hajiya. Ina fargar da kune dan ikon ALLAH yafi gaban wasa, ku
daina matsawa da yawa dan ALLAH”.
Wannan fa kalamai na Ammie sune suka sake tunzura wutar wannan harmutsi. Dan takai har Hajiya
Yaya na iƙirarin maka Ammie a kotu wai tace zata kashe su ta aurama Yazeed ƴarta. Haka ta kira maigidan
tana zazzaga masifa. Ta gama ta fice zuwa gidansu ita da ƴar uwarta suka sanar da mahaifinsu. Lokacin da
su Manaal suka dawo gidan sun tadda komai a hargitse matuƙa. Ga su Hajiya Basariyya ƴan biki sun dawo
daga Abuja ita da yaranta. Aiko ta shiga tai kane-kane tana ƙarama wutar fetur a bayan fage. A yau kam
Maanal data jima da mutuwa mai rashin ragi ga duk wanda ya taɓata sai gata ta dawo. Wani irin ɓacin rai
ya rufe idanunta. Cikin razananniyar tsawa ta ce, “Kai haba ya isa haka mana. Nace ya isa!! Ya isa!!!. Wai
shi Yazeed ɗin anyisa da gold ne ko diamond ko tagulla ko azurfa ne? Ko na taɓa ce muku dama ina son
aurensa ne? Gashi nan ku tambayesa ko sau ɗaya nata amsa masa ina son sa? Shin Yazeed na taɓa cewa
ina sonka? Ka faɗa musu mana ko zasu kama kawunansu. Ni nan da kuke ganina bama Yazeed ba kowanne
namiji bana buƙata, domin Manaal ta jima da amincewa zata rayu a matsayinta na MACE kawai batare da
kowanne NAMIJI ba takowanne fanni. Kun taɓa ganin wanda ya mutu yana son kasancewa da rayayye? Mi
matacce zaiyi da rayayye? Ko shi rayayyen mi zaiyi da matacce?. Dan haka idan kunso ku aurama Yazeed
mata huɗu a rana ɗaya ko duka matan duniya shine zaku birgeni ko kanku dan ALLAH, damuwarku ce
wannan. Ku daina fakewa da maganar Yazeed kuna cin zarafin Ammien mu, idan ba haka ba wlhy wlhy
zakuga ainahin Maanal kuwa. Dan kaf ɗinku sai kunsha matuƙar mamaki ba tsoro yasa ake ƙyaleku ba
girmama kaine da darajar shi Yazeed ɗin da Daddy. Saboda ina girmama waɗan nan mutanen guda biyu a
cikin TARIHINA. Zan iya ce muku sune suka saka zuciyata banbanta sunan MAZA daga jam'in da nai musu.
Amma tunda kunce ku baku san kawaici ba kumuje zuwa daga yau a gidan nan ni daku ɗan halak ka fasa.
Na fiku iy.....”
“Manaal!!”.
Ammie ta faɗa cikin tsawa tana ƙoƙarin riƙota. Kanta ta shiga girgizawa sai kuma ta fashe da kuka mai ban
tausayi tana cigaba da faɗin, “Ammie ki barni na gaji, nagaji haka nan Ammie. Mi mukayima rayuwa ne? Mi
muka tare musu ne? Mi mukayi musu da zafi haka da kowa ke son ganin ya wulaƙanta rayuwarmu, na taɓa
ce musu bazan rayuwu ba sai da wani NAMIJI ne Ammie?. Basa tunanin kafin su ina dake ba! Basa tunanin
ba dole bane sai mace ta rayu da namiji zata amsa sunan mace? Basa tunanin na haƙura da wanda ma yay
sanadin kawoni wannan duniyar bisa izinin UBANGIJI balle su, su ɗin nan da ba komai ba a rayuwata. Su
ɗin nan da zan iya canjawa da ire-irensu a duk lokacin da naso. A tunaninsu dole-dole sai da sune zan
RAYU?! Ko babu su zan rayu Ammie, zan rayu dake kaɗai da ƴan uwana kun isheni, kun wadatar dani a
wannan rayuwar, bana buƙatar kowanne namiji, suje, suje ban buƙatarsu.....” kuka ya sarƙe ta sai tari.
Ɓull!!! Ɓull!! Jini ya dinga ambulowa ta bakinta ta hanci.
Wani irin firgitaccen kukan tashin hankali Ammie ta saki jikinta dake riƙe dana Maanal na rawa. Tuni
Shahidah, Manaal da Yazeed sun yo kansu a ɗari. Su kansu su Hajiya Yaya da tawagarta da sauran jama'ar
gidan al'amarin ya matuƙar firgitasu. Dan a wai-wai suke jin Maanal nada matsalar ciwo mai haɗari, amma
basu taɓa ganinta a ciwon ba, kai zasu ma iya rantsuwa basu taɓa ganin ana aman jini ba sai yau
musamman wannan da takeyi ta baki ta hanci.
Kowa ya rikice an rasa mai cewa a tafi asibiti. Sai baba maigadi ne daya iso wajen a hargitse yake faɗin
asibiti ya kamata a tafi. Da wannan magana tashi suka zabura gaba ɗaya. Cak Yazeed ya ɗauki Maanal
daketa aman jini ya nufi hanyar gate a maimakon motocin gidan saboda tsabar yanda ya rikice. Shahidah,
Amal, Ammie suka take masa baya sai Amara da itama ta zabura ta bisu tana kuka. Fitowar Yazeed dai-dai
da isowar RK ƙofar gidan, dan haka a cikin rikicewa Amal ta buɗe motar RK ɗin kawai tana cema Yazeed ɗin
ya shiga batare data tantance motar waye ba itama. Shima bai wani tantance komai ba ya saka Maanal a
ciki, da sauri itama Ammie ta shiga ta rungumeta tana kuka da faɗin, “Haba Maanal ya zaki mun haka, dan
ALLAH kiyi haƙuri kada ki tafi ki barmu mu muna sonki, muna tsananin ƙaunar Maanal. Muna buƙatar ki a
duniyar mu Maanal...”
Wannan furuci na Ammie shi ya zaburar da RK da ya tsaya yana kallon ikon ALLAH, sai kuma lokacin ya
gane Ammie da Amra dake kuka. Duk da halin da Maanal ke ciki itama bai gagara ganeta ɗin ba. Ai da wani
irin tashin hankali ya tada motar, Yazeed ya shiga kusa da shi suka bar anguwar. Napep Amal da Shahidah
da Amrah suka tare suma suka bi bayansu....
Yazeed ne ya faɗa masa asibitin da zasu je, inda Maanal ke ganin likita kenan. Asibitin kuɗin ne,
kasancewar kafin su isa ma Yazeed ya kira abokin nasa doctor Nazeer ya sanar masa zuwansu suna isowa
suka samu nurses har huɗu da Doctor Nazeer ɗin kansa na jiransu a waje. Da ƙyar aka iya ɓanɓare Manaal
daga jikin Ammie. A kallo ɗaya idan kai mata zakai tunanin bazata sake rayuwa ba. Dan yanda take
yunƙurowa ƙirjinta na ɗagawa tana aman jinin kaɗai ke nuna akwai sauran numfashi a tare da ita. A haka
dai aka shiga da ita ciki kowa a kiɗime. Dai-dai nan suma su Shahidah da suka biyosu a napep suka iso...
Abu kamar wasa sai ga ƙaramar magana ta zama babba. Dan yanda doctors ke shiga da fita ɗakin da
aka shiga da Maanal basa ko sauraren kowa zai tabbatar maka al'amarin yayi tsamari da yawa. Dan har
zuwa goman dare babu wani bayani mai daɗi. Zuwa sannan Nene ta iso, (Nene ƙanwar mahaifiyar Ammie
ce da yanzu take kallo kamar mahaifiya. Zamu iya cewa ma ta sandinta Ammie da ƴaƴanta suka zo cikin
Kaduna. Ita a anguwar dosa take, ita da zuri'arta. Dan itama yaranta huɗu duk maza a yanzu haka duk suna
da aure da ƴaƴansu suma, sai ɗaya ce kawai mace itama dai tayi aure).
Har wannan lokacin RK na asibitin, hasalima tuni ya shige cikin likitocin da shi ake bama Maanal
taimako kasancewarsa shima ƙwararren likita masani a fannoni da dama daya shafi aikin. I'd card ɗinsa
kawai ya nunama Doctor Nazeer ya amince masa shiga cikinsu aka rufu kan Maanal. Haka shina Yazeed
tsaye yake da ƙafafunsa. Duk abinda akace ana buƙata kafin wani dogon lokaci zakaga ya kawosa. Sai su
Ammie suka kasance ƴan addu'a da share hawaye. Daga can gidan dai babu wanda ya biyo bayansu, sai dai
Yazeed ya kira mahaifinsu ya sanar masa. Ya kuma tabbatar masa a yau ɗin nan zai baro inda yake zuwa
Nigeria. Domin shima hankalinsa yay matuƙar tashi bana wasa ba. Koda yasa Yazeed ya haɗashi da Ammie
kasa magana tayi sai kuka data fashe masa da shi kawai. Sai hakan ya sake birkita masa lissafi gaba ɗaya
babu shiri ya fara neman ticket ta online......
___________
Alhaji Usman Chalawa bai iso ba sai washe gari wajen misalin ƙarfe ɗaya na rana. Babu wanda yasan da
dawowar tasa a cikin matansa, dan hatta ita ma Ammien bai sanar mata ba. Sai Yazeed kawai ya sani. Shi
kuma tashin hankali ya mantar da shi sanar ma kowa sai da Daddyn ya tura masa saƙon yazo ya ɗaukesu
sun kusa sauka sannan ya tuna. Ya bar asibitin ne dai-dai lokacin RK na bada shawarar yima Maanal
transfer zuwa Abuja. Dan gaskiya jikin nata sam babu daɗi. Su kansu likitocin sun fara karaya, RK ɗin ne ma
ke ƙarfafasu duk da shima gwiyawunsa a sare suke yana dakewane kawai da ƙarfafa kansa...
Kai tsaye asibiti Yazeed yayo dasu Daddyn. Rungume Ammie su Waleed sukayi, yayinda take kallon
mijin nata cikin karaya idanunta cike da ƙwalla. Cike da kulawa ya girgiza mata kansa alamar kar tai kuka.
Sai kawai tai ƙasa da kanta tana mai rungume Hameed da Waleed sosai a jikinta. Idanun nasa ya ɗauke
cike da damuwa ya maida kan su Shahidah dake gaishesa. Ya amsa musu da kulawa yana tambayarsu mai
jiki. Maimakon amsa sai suka fara hawaye suma. Jiyay gaba ɗaya zuciyarsa ta ƙara karaya, da ƙyar ya iya
gaishe da Nene, sannan ya wuce office ɗin doctor inda suke meeting shi da su RK. Doctor ne yay ma RK
bayanin matsayin Daddy a wajen Maanal duk da tare da Yazeed suka shigo, dan RK bai ɓoyema doctor
alaƙarsa da Maanal ɗin ba. Cikin girmamawa RK ya rissina ya gaishe da Daddyn. Nan ma doctor ya sanarma
Daddy RK likita ne, ya kuma masa bayanin shawaran da suke akai yanzu haka game da maida Manaal ɗin
Abuja. Babu wani musu Daddy ya yarda, tare da ƙarfafasu cewar ayi komai yanda ya kamata ama bar ɓata
lokaci, bari yaje ya bincika ko akwai jirgi mai wucewa yanzu sai su wuce a ciki zaifi mota sauri....
Hakan kuwa akayi, dan zuwa la'asar an gama shirya Maanal zuwa tashar jirgin ƙasa. Zasuyi gaba harda
Nene da su Shahidah. Ammie kuma sai zuwa gobe in ALLAH ya kaimu da safe zasu bisu ita da Daddy kamar
yanda ya buƙata.
Suna isowa Abuja ambulance ce tazo ta ɗauki Maanal dan tuni RK ya gama booking komai. Shi da
Yazeed ne suka bi ambulance ɗin, yayinda mijin Shahidah da yazo shima ya ɗauki su Shahidah ɗin da Nene
da Amal. Yaran duk suna Kaduna sai gobe idan ALLAH ya kaimu Ammie zata taho da su nan. KK HOSPITAL
asibiti ne mai tsanani ƙyau da kowa ya sani a cikin Abuja. Suna da ƙwararrun likitoci da suka san aikinsu
ƙwarai da gaske. Suna ƙoƙari matuka wajen bama mara lafiya kulawa yanda ya kamata, ga sauƙin kashe
kuɗi dan talaka da mai arziƙi duk zasu iya biya. Babu wani ɓata lokaci cike da kulawa aka shiga da Maanal,
yanda ake girmama RK a asibitin yasa suka fahimci eh lallai yana da wani matsayi babba a wajen.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
1️⃣2️⃣1️⃣2️⃣
______________
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
__________
.......Yau kwanakin Maanal biyu a KK HOSPITAL. Zamu iya cewa Alhamdullahi abubuwa sun fara dai-daita,
duk da dai har zuwa yau ba'a barin kowa shiga inda take sai doctors kawai. Tun a jiya su Ammie suka iso
suma ita da Daddy. Tsabar munafunci na Hajiya Basariyya sai ta ce zata biyosu taga jikin Maanal ɗin. Dan a
waccan ranar da Daddy ya dawo tunda ya koma gida ya rufesu da faɗa ita da Hajiya Yaya akan ƙin zuwansu
asibiti, sai dai faɗan nasa yafi tsamari akan Hajiya Yaya data zama itace sanadin komai, dan yama sanar
mata ya haramtawa Sabuwa zuwa masa gida, idan kuma tai gigin zuwa ALLAH sai ya saka jami'an tsaro sun
kamata. Itama kuma ta jira hukuncinsa bayan Maanal ta warke dan yanzu baida lokacinta. Tofa wannan
abu da Hajiya Basariyya dake laɓe taji yasa ta dawo ta lallaɓa Daddyn ta bashi haƙuri akan nata laifin daya
faɗa naƙin zuwa asibiti kawai, ta kumaji duk halin da ake ciki akan maida Maanal Abuja shine ta maƙale
itama zata bisu. Ammie bata san da batun ba sai da suka fito zasu wuce taga Hajiya Basariyyan. Sosai ta
sake jinjina makircin matar a ranta, dan ta jima da gane wacece Basariyya, sai dai bata taɓa nuna mata ba
ta barta da halinta. A lokacin ma murmushi kawai tai batace komai ba, hakan kuma sai ya ƙonama Hajiya
Basariyyan rai, ta rasa wacece Ammie, ta rasa ta inda zata kamo lagon matar, ta rasa ta inda zata shiga
jikinta kamar yanda take shiga jikin Hajiya Yaya tasan sirrinta. Amma ba komai, idan tasan wata ai bata san
wata ba.
Anan Abujan itama ta kwana dan Daddyn nada gida anan ɗin dan yana harkar sayen gidaje da sayarwa
ne. Kasancewar komai akwai a gidan yasa sauka kawai sukai anan ɗin. A yanzu ma haka tana a asibitin tare
da su. A ɗakin da aka kwantar da Maanal ɗin ɗakine na musamman kamar palor da bedroom, dan haka
duk suna a palor ɗin zaune itama Maanal na daga ciki babu mai shiga sai dai su leƙata ta jikin ƙofar glass
ɗin. Shahidah da Amal suka iso ɗauke da abinci, bayan duk sun gaishesu suna ƙoƙarin zama Daddy da RK
suka shigo ɗakin sai wani ba'indiyen likita da shine akan case ɗin Manaal ɗin ma. Gaishe da Daddy su
Shahidah sukayi, sannan suka gaisa da su RK da suma suke gaida su Ammie. Su RK na ƙoƙarin barin wajen
kamar daga sama sai Hajiya Basariyya cewa tai, “Nikam likitan nan kamar na sanka”. Yanda tai maganar
idonta akan RK ya sakashi fahimtar da shi take, kallonta ya ɗan yi sai kuma ya rissinar da kansa tunda bai
san matsayinta ba a garesu ya ce, “Mommy zata iya yiwuwa. Sai dai ban san a ina kika sanni ba”.
Batare data damu da kallon harara da Daddy ke mata ba ta ce, “A zaria gidan Alhaji Saminu Ashafa”.
Cikin jinjina kai RK ya bata amsa da, “Ni ƙanin amaryarsa ne Majdiya”.
Kafin Hajiya Basariyya ta samu yin magana Ammie da Daddy suka dubeshi. Abinda ya faru a ranar da
sukaje ɗaurin aure gidan Alhaji Saminun ya shiga dawo mata a rai. In dai batai kuskuren fahimta ba shine
yaron da Hajiya Majdiya ke mata bayanin yana son Maanal kenan. Wani irin sanyi taji a ranta, dan koba
komai ita dai yaron ya shiga ranta a lokaci guda, sannan ta samu karɓuwar addu'ar ta akan al'amarin
Maanal ɗin da Yazeed tunda ga raba gardama yazo.. Shikam Daddy murmushi yayi cike da nuna mamaki ya
ce, “Ikon ALLAH ashe ma kai ɗin na gida ne doctor. Ai nasan Hajiya Majdiya kuwa sosai saboda Alhaji
Saminu aminine kuma ɗan uwana ta fanin mahaifiya, zan iya cemaka ma neman auren Majdiya da komai
dani akayisa”.
Wani ɗan karen daɗi ne ya ratsa RK har cikin maƙwallaton zuciya. Sai yake jin gaba ɗaya matsakarsa ma
shi ta ƙare kenan. Nan take ya ƙara sakewa da Daddy. A karo na farko Daddy ya shiga ɗakin da Maanal ke
kwance shi da Ammie da Nene kawai. Sosai tausayin Maanal ya ƙara mamayesu, dan Ammie kasa daurewa
tayi sai da tai kuka. Duk wanda yaga Maanal ɗin sai yayi matuƙar tausaya mata. Numfashi ma sai da
taimakon na'urori take yinsa. Duk ta sake figewa. Sun mata addu'a suka fito aka bar Nene kawai dan doctor
ya buƙaci a ɗan goge mata jiki a canja mata kayan jikinta. Da ance Ammie tayi amma ta nuna bazata iya ba.
Sai dai Nene tayi. Tsaf Nene ta gogema Manaal jiki aka canja mata kaya. Doctor da RK suka shigo, hakan
yasa Nene fita ta basu waje dan suyi aikinsu. Ta tarar da Hajiya Basariyya cike fam da takaici, wai tana
fushine ita ba'ace ta shiga ta duba Maanal ba, shine taima Daddy ƙorafi akan hakan. Shi kuma yaƙi tanka
mata shine ta cika tai fam. Ita dai Ammie haƙuri ta bata, yayinda su Amal ke mamakin abinda Hajiya
Basariyyan tayi. Ita kanta Nene abin ya bata mamaki, dan bataga abin wani ƙorafi ba a wajen tunda gasu
Shahidah suma ba'a barsu sun ganta ba. Ita kanta dan Ammie tace bazata iya gogema Maanal ɗin jiki bane
aka barta ta shigan. A haka Yazeed da yaje Kaduna ya dawo ya samesu, tare da duk yaran gidan yake tafe,
amma abin mamaki yau ɗin ma Hajiya Yaya bata zo ba....
Da mamaki Amrah ke kallon RK, har dai ta kasa haƙuri sai da tayi magana. Murmushi yay mata da
tambayarta ya gajiyar biki. Hakan data faru tsakanin Amrah da RK sai ya tsayama Yazeed a zuciya har sai da
ya kira Amrah ɗin gefe ya binciketa. Kanta tsaye ta sanar masa abinda ta sani. Yayi mamaki ƙwarai da
gaske. Haba no wonder yake mamakin yanda RK ɗin ke tsaye very serious akan case ɗin Manaal ɗin. Ya
jima yana son haɗa al'amarin a ransa amma ya gaza samun makama, tunda shi dai sun fitone kawai suka
samu motar RK ɗin a ƙofar gida, daga wannan taimakon kuma na kawosu asibiti baiyi tunanin cigaba da
ganinsa ba amma sai yaga ya tsaya tsayin daka komai anayi da shi, yayi tunanin kawai tausayi da taimakone
sai da aka dawo Abujar nan ya ɗan fara zargi a ransa sai kuma dai yay saurin kaudawa tunda bashi da
tabbas musamman ganin RK ɗin matsayin likita shima. Ashe kuwa hakanne.
A ranar su Amrah suka koma Kaduna harda Hajiya Basariyya data wuce bisa tirsasawar Daddy dan
kuwa badan taso ba, taso ace sai taga kwal uwar daka. Ta zata da Daddyn zasu tafi sai yace mata shi yana
nan har sai yaga yanda hali yayi akan jikin Maanal ɗin. Hakan ya masifar ƙona mata rai, dan ta kalla abunne
a sigar rainin hankali irin na maza kawai. A ganinta Daddyn nason holewa da Ammie ne a wannan
ƙayataccen gida shine ya fake da ciwon agola. Ita Ammie tsaf ta fahimci manufar Hajiya Basariyya ɗin,
amma sai ta basar kawai tama dinga ƙarfafa Daddy ɗin akan yaje suma suna da hakki a kansa, tunda dai
Maanal ɗin tana samun dukkan kulawa anan ɗin gasu kuma ga Yazeed shi yaje ya huta gashi ya dawo daga
tafiya. Sam Daddy ƙin saurararta yayi, daga ƙarshe ma ya fara fushi da ita dole tai shiru ta zuba masa ido
kawai su Hajiya Basariyyan suka wuce...
A ɓangaren Yazeed kuwa ya fara janye jikinsa daga RK. Tun RK ɗin bai fara fahimta ba har ya fahimta.
Dan sai wani isa ma Yazeed ke nuna masa akan Maanal ɗin yanzu da gadara. Mamaki hakan ya bama RK,
dan shi a zatonsa Yazeed da Maanal uwa ɗaya uba suke ko uba ɗaya dan yana ɗan tantamar Ammie ta isa
haihuwar kamar Yazeed ɗin. Bai daiyi magana ba yabar abin a ransa dan ganin iya gudun ruwan Yazeed
ɗin. Ana cikin wannan dambarwa a tsakaninsu Hajiya Majdiya yayarsa tazo duba Maanal ita da yaranta tun
daga Zaria. Dan shine ya kirata yake sanar mata, aiko baiwar ALLAH sai gata tazo. Ammie tayi mamakin
hakan kasancewar batai waya da Hajiya Majdiya ɗin ba akan hakan. Sai Hajiya Majdiyan ke sanar mata,
“Sirikinki ne ya kirani yake sanar min ai.”
Murmushi Ammie tai da faɗin, “Haba nayi mamaki fa, sai kuma hankalina bai kawo nan ɗin ba. Ai babu
abinda zamuce da Rafeeq sai fatan alkairi. ALLAH yay masa albarka”.
“Amin ya rabbi. Yaya jikin nata yanzu? Dan naga hankalinsa a tashe yake matuƙa yau har cewa yay na
nema masa masu saukar Alkur'ani yana son ai mata”.
Ajiyar zuciya Ammie ta sauke. Zuciyarta na sake jin nutsuwa da RK ɗin. “ALLAH sarki, ALLAH ya saka masa
da alkairi. To Alhamdullahi zamu ce. Sai dai har yanzu bata san wanda ke kanta ba. Amma dai suna
tabbatar mana bugun zuciyarta na dai-daita zuwa yanzu. Kowane lokaci kuma zata iya farfaɗowa cikin
hayyacinta.”
“ALLAH ya bata lafiya, yasa ya zama kaffara. Abin tausayi yarinya ƙarama haka da wannan irin babban
ciwo mai haɗarin gaske, ALLAH ka bamu ikon cinye jarabawoyinmu. Shiyyasa gata nan sanyi-sanyi ko
kuzarin kirki bata da shi. Ban taɓa sanin tana da wannan lalurarba ai da tuni na haɗaku da Rafeeq ɗin dan
aikinsa ne. Yanzu haka reshen wannan asibitin suka buɗe acan garin jos shine yaje can da kansa yake riƙe
da asibitin kusan shekara ɗaya kenan, anan ne ma ALLAH ya haɗasa da ita”.
Murmushi Ammie tayi tare da jera addu'a ma RK ɗin. Ganin yanda Ammie ta ɗauki zancen da
muhimmanci Hajiya Majdiya ta cigaba dama ɗan uwanta campaign wajen Ammie. Yinin gaba ɗaya suna a
tare sai bayan Magrib RK ya ɗaukesu ya maida can gidan babbar yayarsu dake nan Abujan zasu kwana
anan dan sai gobe idan ALLAH ya kaimu zasu koma Zaria. Sosai Ammie taji daɗin kasancewa da Hajiya
Majdiya a wannan rana. Dan zaman ya sake tasirantar da abinda take ji a zuciyarta game da RK da Maanal
idan har ALLAH ya tashi kafaɗunta. Bata ɓoyema Nene da su Shahidah ba akan alaƙar Dr Rafeeq ɗin da
Maanal. Suma sai abin yay musu daɗi matuƙa, dan suna ganin idan har ALLAH ya baiwa Maanal lafiya
wannan itace hanya mafi sauƙi da maganar Yazeed zata janye cikin sauƙi batare da sun ɓata ran Daddy ba
kamar yanda duk suke gudu. Dan gwara dai a haƙura da batun Yazeed ɗin nan haka nan tunda dama ita
wadda ake dan ita bawai tana sonsa bane. Abu na biyu sudai a haka yanayin Dr RK ya musu hundred
percent, dan mutum ne mai sauƙin kai ga girmama na gaba da shi, ga yanda yake ɗawainiya dasu a asibitin
nan cike da mutuntawa ma abin a soshi ne. Shi kansa Daddyn sun fahimci RK ɗin ya shiga ransa. Sai dai
babbar matsalar sun san ga Yazeed za'a sameta kam. Dan kowa yasan Yazeed na matuƙar son Maanal
wannan a bayyane yake. Sannan shi kansa mutumin kirki ne, dan yana da nagartattun halaye masu yawan
gaske daya gada ga Daddy, tako ina Yazeed ya cancanci zama mijin Maanal kodan halaccinsa garesu, dan
hatta Daddy ya sansu ne a dalilin Yazeed. Sannan kodan Daddy a bama Yazeed auren Maanal, mahaifiyarsa
ce kawai matsalar gaskiya, dan Hajiya Yaya sam ba kanwar lasa bace. Bata da kirki ko misƙala zarratin,
kanta kawai ta sani, kuma tabbas zata iya aikata komai akan wannan auren kamar yanda take shan faɗa
idan har akayisa. ALLAH dai ya bama Maanal ɗin lafiya, zasu cigaba da tayata addu'ar zaɓin alkairi dan duk
MAZAJE biyun nan sun matuƙar cancanta da aurenta...
★ A mota Hajiya Majdiya ke bama RK labarin hirarrakinsu da Ammie, babu abinda yake sai murmushi
da ƙara jin ƙaunar ƴar uwar tasa. Sai da ta gama bashi labari tsaf sannan ya jeho mata tambayar abinda ke
cimasa zuciya..
“Humm Aunty Alhamdullah na samu karɓuwa wajen Ammie da ƴan uwan Maanal, sai dai ba duka ba”.
“Kamar ya ba duka ba miye matsalar to?”.
“Yazeed Aunty, Yazeed shine matsalar kuma na fahimci yana da ƙarfin faɗa aji akan ƴan uwan nasa. Da
farko dai ni da shi normal gaskiya. Amma kwana biyun nan ban san miyyasa ba ko ya fahimci alaƙata da
Maanal ɗin sai naga yana jajja baya dani, sannan yana min gadara da al'amarin Maanal ɗin. Dan ma baida
yanda zaiyi ne kasancewata ɗaya daga cikin likitocinta shiyyasa. Har abin ya fara bani mamaki dan kamar
wani mai kishi da ni. Sai dai nasan ba hakan bane tunda mizai sakashi yin kishi akan wadda suke Uba ɗaya
ne ko uwa ɗaya ma ban sani ba”. Ya ƙare maganar cikin damuwa sosai.
Fuskar Hajiya Majdiya cike da damuwa itama ta furta, “To kodai Yazeed ma son Maanal yake?”.
“What?!!!”..
RK ya faɗa a ɗan razane yana taka birki da sauri.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
1️⃣3️⃣1️⃣3️⃣
______________
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
______________
........“Kamar ya sonta Aunty? Wace magana kike haka? Ba mahaifinsu ɗaya ba?”.
“Ba mahaifinsu ɗaya ba Rafeeq. Dan Alhaji Usman bashi ne ya haifi Maanal ba ita da yan uwanta biyu
mata. Ƙannen Maanal maza biyu da kake gani Waleed da Hameed sune ƴaƴan dake tsakaninsa da Hajiya
Asiya. Kaga ko zata iya kasancewa Yazeed son Maanal yake yi shiyyasa. Kuma kamar yanda ka faɗa ya
fahimci kana sonta ne a yanzu shiyyasa ya canja maka. Amma ka bari zan bincika komai in sha ALLAHU”.
Wata irin zufa ce ta gauraye illahirin jikin RK. Idanunsa har sun kaɗa na damuwa. Yana ganin ya fara bin
hanyar nasara ashe akwai sabuwar ƙura a tafiyar, dan tabbas indai har Yazeed son Maanal yake da wahala
shi ya samu. Ammie dai bazataƙi ɗan mijinta ba, haka shima Alhaji Usman ɗin bazai ƙi ɗansa ba, ita kanta
Maanal ɗin bashi da tabbacin bata son Yazeed ɗin ma a.....
“Kaga ka kwantar da hankalinka fa, in sha ALLAHU komai zai kasance cikin sauƙi. Ba nace zaka iya
samun Maanal bane cikin sauƙi, ban kuma ce bazaka iya samunta ba tunda komai na ALLAH ne. Dan haɗin
Yazeed da Maanal zai yi matuƙar wahala saboda nasan wacece mahaifiyar Yazeed. Hajiya Sadiyya da
wahala ta amince da wannan haɗin musamman yanda nasan tayi bala'in tsanar Hajiya Asiya. Dan haka
kada ka karaya da izinin ALLAH nasara tamu ce, kai dai kawai ka cigaba da neman soyayyar yarinyar shine
babban makami a hannunka bayan goyon bayan Hajiya Asiya a yanzu”.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke. Sai kuma ya zari handkhachief ya goge zufar goshinsa. “Hakane kam
Aunty, ina jin tsorone kawai kar ya kasance itama Maanal ɗin tana sonshi, wannan kam kinga bazan iya
jayayya da kowa ba tunda itace mai zaman auren.”
“Eh tabbas kam, amma nidai ban taɓa jin akwai wata alaƙar soyayya a tsakaninsu ɗin ba gaskiya.
Tunda da akwai na faɗa maka mahaifiyar Yazeed sai a hankali ce, da sam bazata bari a zauna lafiya ba.
Amma yanzu ma inda wata shawara, ka samu lokaci ka shigo Zaria wajen Abbansu Najma. Ka masa bayani
a matsayin kana son ya maka iso wajen Alhaji Usman ɗin akan maganar mana, ni kuma kafin kazo zan sake
bincikawar kamar yanda nayi maka alƙawari”.
Ajiyar zuciya mai haɗe da ƙayataccen murmushi RK ya saki, sai kuma ya kama hannun ƴar uwar tasa ta
sumbata yana faɗin, “ALLAH ya saki a aljanna Aunty na mai share kuka na”.
Dariya tayi tana mai kai masa ɗan rankwashi a kai, hakan ne ya sakashi shima yin dariyar sannan ya tada
motar suka cigaba da tafiya......
✨✨✨✨✨✨✨
Alhamdullah wannan zuri'a suna cikin farin cikin farfaɗowar Maanal a yau, duk da ba'a barsu sun ganta
ba har zuwa yanzu saboda likita dake tare da ita hakan bai hana bayyanar murmushi a fuskokinsu ba. Sai
da su Dr Ranjet suka gama mata dukkan abinda ya dace kafin su ka buƙaci Nene dake goge mata jiki kullum
ta shiga ta goge matan. Shahidah da Amal kuma sukai shirin komawa gida haɗo mata abincin da Doctor
yace zata iya ci. Bayan kammalawar Nene Daddy da Ammie ne suka fara shiga. Tana kwance fayau da ita
saboda ramar da tayi na ciwo. Gaba ɗaya na'urorin da aka sanya mata a kwanakin da suka gabata an
janyesu, sai igiyar daketa jikin hancinta kawai. Jin ƙamshin turaren Daddy kusa da ita sosai ya sakata buɗe
idanunta da suka ɗan kumburo, daga cikinsu sun ɗan yi ja sun kuma ƙara girma. Daga shi har Ammie dake
tsaye ta zubama idanun, sai kuma a hankali ta saki murmushi mai sanyi tare da miƙa musu hannunta.
Ammie dake murmushi tana hawaye ce ta kama hannun tana kaiwa zaune bakin gadon kusa da ita. Yayin
da shi kuma Daddy ya ɗan duƙo ya shafa kanta yana murmushi shima, kafin yakai zaune a kujerar gaban
gadon.
“Sannu kinji Daughter. ALLAH ya baki lafiya yasa kaffara ne”.
Kanta ta ɗan jinjina tana sakin murmushi, sai kuma ta motsa lips ɗinta a hankali ta furta, “Amin Daddy
nagode”.
Murmushi ya sake mata, tausayin yarinyar da ƙaunarta na sake gauraye zuciyarsa. Maanal ta maida
kallonta ga Ammie dake sharar hawaye. Nan ma a hankali ta ce, “Ammie ki daina kuka na samu lafiya fa”.
Kai Ammie ta shiga jinjina mata tana share hawayen da sakin ƴar dariya. “Na daina Maanal kinji, ALLAH ya
ƙara miki lafiya da nisan kwana. ALLAH yasa kaffara ne, ALLAH ya rabaki da wannan ciwo gaba ɗaya”.
“Amin Ammie nagode. Ina su Didi fa?”.
“Sunje gida yimiki abinci yanzu zakiga sun dawo. Ko kina son cin wani abune a kirasu su yi miki?”.
Ɗan shiru tayi alamar tunani, sai kuma ta kalla Daddy dake ta kallonsu yana murmushi, itama ɗan
murmushin ta masa sannan ta sake maida dubanta ga Ammien. “Ammie sumin faten dankali, sai kunun
gyaɗa”
“To shike nan bari na kirasu karsu taho”.
Kai Maanal ta jinjina mata, yayinda Ammie ke ƙoƙarin kiran su Amal. Dai-dai nan Yazeed ya shigo ɗakin
da sallama Waleed riƙe da hannunsa, sai Hameed biye da su. Daddy ne ya amsa masa. Yayinda ita kuma ta
zuba musu raunannun idanunta. Da sauri Hameed da Waleed sukayo inda take cike da farin cikin ganin
idanunta a buɗe. Hannunta duk suka kama suka riƙe suna kaiwa durƙushe daga ƙasa ta yanda fuskokinsu
zasu daidaita da tata.
“Alhamdullahi Didi ta samu lafiya”. Cewar Hameed yana sake ƙanƙame hannunta. Shima Waleed cike da
ɗoki ya furta, “ALLAH mun gode maka yau muna cikin farin ciki Daddy Didi ta buɗe ido”.
Ƙaramar dariya Daddy yayi da faɗin, “Alhamdullahi” shima. Maanal cikin magana a hankali tace, “Ƴan
turai kamarku daban”. Dariya duk suka ƙyalƙyale da shi. Itama saita maida kallonta ga Yazeed dake tsaye
kawai yana kallonsu fuskarsa ƙawace da murmushin farin ciki. Kallon da take masa ya sashi ƙarasa
ƙarasowa gaban gadon sosai. Sai kawai ta lumshe nata idanun a hankali ta kuma sake buɗewa duk a lokaci
guda.
“Alhamdullahi. Sannu Maanal ALLAH ya ƙara lafiya yasa kaffarane kinji”.
Murmushi ta sakar masa a karo na farko, murya can ƙasa ta ce, “Amin Yaya nagode”.
Amsa mata yay cike da farin ciki, jiyake tamkar ya rungumeta a jikinsa sai dai babu damar hakan. Balle
ma ga Ammie a wajen ga Daddy. Suna a hakan dai kuma sai ga RK. Tunda ya shigo idanunsa akan Maanal
ɗin ne shima, itama dai shi ɗin take kallo da ɗunbin mamaki. Yayinda zuciyarta ke raya mata (shi wannan
duk inda naje sai ya bini ne shin?) Rashin mai bata amsa yasata janye idanunta a zahiri daga kansa. Shima
sai dai janye nasan yayi tare da ƙarasowa ya gaida Daddy da Ammie cike da girmamawa. Maanal ta sake
shan mamakin ganin yanda duka amsa masa da kulawa da alamar sanayya sosai kuma. Dubansa ya maida
a kanta yana mai ɗan kashe mata ido, hakanne ya sakata yimasa ƙaramar harara. Murmushi ya saki mai
faɗi da ƙoƙarin ɗaukar file ɗinta dake a drower ɗin gefen gadon yana faɗin, “Gawa taƙi rami yaya jikin?”.
Dariya Daddy da su Waleed sukayi, yayinda Ammie tai ɗan murmushi kawai. Yazeed kam fuska ya sake
tamkewa kamar bai san minene dariya ba. Yayinda Maanal ta ɗan tsuke fuska itama tana hararar RK ɗin
yanzu ma. Yi yay kamar bai ganta ba ya miƙama Yazeed hannu cike da shaƙiyanci yana faɗin, “Babban Yaya
barka ƙanwa ta miƙe. ALLAH ya ƙara lafiya yasa kaffara ne ya kiyaye gaba”.
Rasa abinyi Yazeed yayi, sai mamakin RK ɗin ke sake mamaye masa zuciya. Wani gefe kuma na tunanin
RK fa bawai yasan ainahin alaƙarsa da Maanal bane, dan kuwa kallon yayanta uba ɗaya yake masa kenan.
Daurewa yay ya ɗan sake fuska ganin Daddy na kallonsu ya bashi hannun shima suka gaisa yana amsawa
da, “Amin doctor muna godiya, kuma kunyi ƙoƙari ai sai fatan alkairi a gareku”.
“Doctor!”.
Manaal ta faɗa a hankali cikin suɓutar baki idonta akan RK. Kafin ma RK yay wani yunƙurin bata amsa
Waleed yabata amsar da “Eh mana Aunty shine likitanki tare da Dr Ranjet. Kuma yana da kirki kullum sai
yaje damu yawo ya saya mana abubuwa, yana kuma cemana mu dinga miki addu'a a dallarmu ALLAH ya
baki lafiya ko warke gaba ɗaya ki daina wannan ciwon ”.
Sake dai kallon RK ɗin Maanal tayi kawai, zuciyarta na wani irin motsawa a ƙirjinta da sauri-sauri kamar
ma ciwon nason dawowa sabone komi. Ganin kallon da Ammie ke mata ta sata lumshe idanu kawai tai
shiru dan ita kam bata kuma san abin faɗaba bayan hakan. Ɓoyayyen murmushi kawai RK yayi yana cigaba
da dudduba abinda ya kamata, sai kuma ya fara mata tambayoyi a hankali. Dole ta buɗe idanunta a kansa
dan yanda yake magana can ƙasa-ƙasa tsigar jikinta har tashi take. Kasa amsa masa ko ɗaya tayi da baki, sai
jinjina masa kai kawai da girgizawa. Wani irin kishi ne ya turniƙe Yazeed, dan shi mutum ne mai kishi sosai.
Rai a ɓace ya ɗan duƙo shima gareta murya can ƙasan maƙoshi ya furta, “Kina son cin wani abu Miss?”.
Idanunta ta ɗan maida garesa, “Yaya su Didi na zuwa da abinci ai”. Ta faɗa a hankali dan muryan baya
fita sosai. Cikin jinjina mata kansa ya ce, “Na sani, ko ɗan fruit haka baƙya so? Ko wani abu bayan
abincin?”.
“Zanci apple to, amma green”.
“An gama Baby”. Ya faɗa cikin raɗa ta yanda ita kaɗai taji sai RK dake kusa da su sosai. Saurin kauda kanta
tayi, sai kuma ta kalla sashen da Ammie da Daddy suke. Ganin hankalinsu na kan su Waleed yasa ta sauke
ajiyar zuciya. RK ta ɗan kalla, sai taga shima yay wani kicin-kicin da fuska yanata rubutu a file ɗin ta. Tana
ƙoƙarin janyewa ya ɗago nasa idanun sai caraf a nata. Wani miskilin murmushi ya sakar mata tare da sake
duƙowa kusa da ita gab, cikin raɗar shima ya furta, “Apple yana cikin abinda bazaki ci ba a yanzu wife to
be, dan haka kada ki ma wahalar da Yayanmu”. Ya ƙare maganar da kashe mata ido ɗaya sai kuma ya kalla
Yazeed ya sakar masa wani ɗan iskan murmushin rainin hankali.
(Nikam mike damun waɗan nan?) Maanal ta faɗa a zuciyarta dan tama rasa yanda zata masalta
al'amarin nasu. Tana fama da kanta sunzo sun sakata tsakkiya da shirmensu ya ilahil alamin. Shigowar su
Shahidah ne ya taimaketa. Cike da farin ciki sukazo suka rungumeta suna hawayen daɗin ganinta. Itama
farin cikin take ji a ranta matuƙa. Nanfa suka shiga nan nan da ita. Sai kawai Daddy da Ammie suka fita tare
da su Waleed. Dan ba'aso suyi yawa a ɗakin sam. A hakan ma dan RK najin nauyinsu shiyyasa baiyi magana
ba. Ganin Yazeed bashi da niyyar fita a ɗakin RK ya dubesa cikin danne kishinsa ya furta, “Yauwa babban
yaya inama son magana da kai. Dan akwai alluran da za'a mata zuwa 6pm naga kamar babu shi anan ya
ƙare, ko zaka samo mana shi a pharmacy please?”. Yayi maganar ne idanunsa a kan takardun hannunsa
yana kuma ɗan tafiya, dan haka baka isa gane ainahinsa ba kai tsaye. Bin bayansa Yazeed ɗin yayi batare da
yace komai ba. Maanal ta bisu da kallo ƙasa-ƙasa.
Da taimakon yayun nata biyu ta ɗan ci abincin, nurse ɗin dake kula da magungunan ta ta shigo ta bata.
Babu wani jimawa barci mai nauyi yay awon gaba da ita. Dama haka doctors ɗin suke buƙata ta dinga barci
isashe dan zuciyarta da brain ɗinta su samu nutsuwa.........✍️
_Team
😌 RK & Team Yazeed ina miƙo gaisuwar ban girma😌 👌._
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
1️⃣4️⃣1️⃣4️⃣
.......A ɓangaren Yazeed da RK kam suna fita Yazeed ya tsaya cak. Kallonsa RK ya juyo yanayi, sai kuma ya
saki lalataccen murmushi yana dawowa da baya inda Yazeed ɗin yake. “A'a babban Yaya yaka tsaya kuma?
Ya kamata muje ko”.
Murya a sarƙe Yazeed ya amsa masa da, “Rubuta sunan alluran ka bani anan. Sannan ka daina wani
kirana Babban yaya dan ban san alaƙar data maidani yayanka ba”.
Hannu RK ya kai ya shafo bayan ƙeyarsa yana murmushi irin na ƴan duniya shi a dole irin yaji kunyar
nan. “Haba bazan iya kiranka da sunanka ba gaskiya. Ko a bayan ma kafin na fahimci kai Yayan Maanal ne
yasa nake kira. Yanzu kam dana sani sam bazan iya hakan ba”.
“Ni ba yayan Maanal bane kawai mijin da zata aura ne”. Yazeed ya faɗa a gadarance. Wani irin mugun
dukan zuciyar RK furucin yayi, amma sai ya dake cike da basarwa ya furta, “Irin wannan wasan ai saika saka
zuciyata ta buga babban yaya, kona ɗauka baka son aura min ita ne. Please mubar zancen haka ga sunan
allurar”.
Yana miƙa masa ƴar takardar da yay rubutun yabar wajen da sauri dan baya buƙatar sake jin wani furuci
daga Yazeed ɗin bayan wanda yaji. Shifa wlhy san Maanal yake. Kuma baya jin zai iya barma Yazeed ɗin
koma mi za'ayi. Sai dai suyi yaƙi mai rabo ya ɗauka. Babu ruwansa da ƙarfin alaƙarsu kowa ya iya allonsa
kawai ya warke.
Da wani irin kallo Yazeed ya bisa kawai batare da ya sake cewa komai ba shima yabar wajen...
_________★
Ganin jikin Maanal Alhamdullah Ammie ta matsama Yazeed komawa kan saboginsa. Shima Daddy ta
damesa da roƙon ya koma Kaduna kada su shiga hakkin sauran matansa. Yazeed dai ya jitane kawai. Dan ya
ƙudura a ransa bafa zai tafi ya bar Maanal a hannun wannan kuren likitan ba RK. Dan haka ƙafarsa ƙafarta
idan ta samu lafiya. Shi kam Daddy sai da sukai ƴar rigima sannan ya yarda zai wuce Kaduna ɗin, amma
kuma dole sai tare da ita, yace nan da kwana biyu ta dawo ta sake dubata tunda dai ga Nene gasu
Shahidah. Ita dai Ammie tace hakan yafi mata duk da bata so hakan ba, dan tana son kasancewa da
Maanal ɗin itama amma babu yanda ta iya haka ta haƙura suka tafi bisa shawarar Nene dan itama tafi son
yaje ga sauran matansa kar abin ya zama wani daban kuma. Yazeed dai ya nuna mata akwai aikin da yake
anan ɗin dan gobe ma zaiyi zama da masu Companyn Mawaad ne.. Wucewar Daddy da Ammie kamar ya
buɗema Yazeed da RK wani filin TAKUN SAƘA ne, dan kuwa kowa ya riƙe wuta yana baje kolin hajarsa.
Yayinda ita kuma take nuna bama ta fahimci inda suka dosa ba su duka. Tun suna abin a kaikaice har ya
fara bayyana kansa sosai, dan takai da Yazeed ya shigo duba Maanal tsalam zakaga RK a ɗakin ya shigo
kamar wanda aka jeho. A wajen su Amal taji duk yanda akai aka kawota Abuja. Nan ta fahimci RK yaje
gidansu ne sai ya kasance a dai-dai lokacin da take a halin taimako. Hakan ya kwaranye mata mamakin
ganin nasa anan. Sai dai kasancewarsa likita bai bar bata mamaki ba. Dan har sukai zamansu a Jos suka
gama bai taɓa nuna musu ga aikinsa ba. Kai ita tama sha yin gulmarsa da jifansa da kalmar mara aikinyi,
sannan a tunaninta shi ɗin ɗan Jos ɗin ne ma ai.
Yau Nene ta ɗan tashi da ciwon kai, dan haka ta wuce gida dan ta ɗan huta. Dama itace ke kwana da ita
anan, da safe zuwa goma sai ta wuce gida idan su Amaal sun zo, sukuma suke yini da ita anan har sai dare
idan Nenen ta dawo sukuma sai su wuce. Daga Nene har Amal suna a gidan Shahidah ne yanzu, dan bayan
wucewar su Ammie sai itama Nene ta koma can gudun karta zauna ita kaɗai anan ɗin duk da ma ƙarfin
zaman nata a asibitin ne dai. Bayan wucewarta Maanal ta tashi a barci, da taimakon Nurse tai wanka, kafin
ta fito an gyara ɗakin, tana ƙoƙarin zama a bakin gado take tambayar Nurse ɗin, “Nene fa?”.
Amsa ta bata da, “Doctor Rafeeq ya kaita gida ta huta kanta na ciwo”.
Shiru kawai Maanal tayi, mamakin RK na sake kasheta, gaba ɗaya fa yabi ya kanainaye mata ƴan uwa
kowa ya sanshi. Yanzu haka kullum Waleed da Hameed na manne da shi har sai da suka wuce aka samu
lafiya. Haka idan su Didi sunzo zaizo ya zauna wai yazo gaishesu duk hararar da take masa baya ma nuna ya
gani. Itako yaya zatai da wannan bawan ALLAH. Babu ma abinda ke damunta sai zaman marina da suke
tsakaninsa da Yaya Yazeed, hatta gaisuwa sama-sama sukeyinta yanzu ma ta rasa mike damun kawunansu
haka.... Shigowarsa ɗakin shi da Doctor Ranjet ya katse mata tunaninta, da sauri taja hulanta ta saka tana
ɓata fuska. Ɗauke kai RK yay kamar bai ganta ba yama hau duba magungunanta. Shi dai Dr Ranjet
matsowa yay kusa da ita yana tsokanarta, haka yake mata dan shi mutum ne mai wasa sosai. Dole ta daure
ta ɗan masa murmushi dan turancinsa na sata nishaɗi, kullum gaya mata yake ita ɗin mai sa'a ce. Ruhunta
nada tauri sosai, saboda da wahala kaga mai irin matsalarta ya shiga irin yanayin data shiga kuma ya tashi
ya cigaba da rayuwa, dan shi kansa a randa aka kawota asibitin baimayi tunanin zata kai washe gari a raye
ba. Dai-dai Dr Ranjet na ƙoƙarin mata wata allura da kullum a irin wannan lokacin ake mata RK ya ƙaraso
wajen. Kujera yaja ya zauna yana mai zuba mata ido dan sai ɓata fuska take tana kallon allurar. Amma tana
juyowa suka haɗa ido da shi sai ta ɗaure fuska ta fiske abinta. Kansa ya kauda kawai yana murmushi baice
komai ba. Allurar akai mata, ana gamawa ta kwanta saboda jiri take sakata. Idonta a rufe har fin mintuna
biyar Doctor yay mata sauran abinda ya rage har ya fice da kusan mintuna biyar sannan ta iya buɗe
idanunta da suka kaɗa sosai. A kansa ta saukesu, sai kuma ta janye da sauri ganin shima ita yake kallo.
“Nifa bana son haka, azo a tasa mutum gaba ai haramunne ma wannan”.
Murmushi ya saki mai faɗi yana mai janye idanun nasa daga gareta. Sai kuma ya furzar da huci kaɗan a
hankali ya furta, “To amin afuwa sarauniya. Sonki ne kawai ke neman zubar dani amma ke kina ɗaukar
komai wasa”.
Shiru ta masa bata tanka ba. Shima sai ya bar zancen ya kama wani daban. “Ni kam banga Zizaah da
Aneesa ba, ko basu san baki da lafiya bane?”.
Kansa ta jinjina masa alamar eh.
“A gaskiya ya kamata su sani. In sha ALLAHU anjima zan kirasu na sanar musu kuwa”.
“Ni dai ban saka ba”.
Idanu ya ɗan waro waje. “Saboda mi?”.
“Ba saboda komai ba, kawai dan mutum na ciwo sai anta talla da shi. Yanzu miyyasa ka kai Nene gida
ma?”.
“Saboda taje ta huta. Ba su Didi na zuwa ba”.
Hararsa ta ɗan yi, kafin tace, “To idan kuma ina buƙatar wani abu fa kafin su suzo?”.
“Ba gani ba sai ki sakani nai miki. Ai shiyyasa nazo nan na zauna a madadin Nenen. Faɗi mi kike buƙata
gimbiyar Rafeeq?”.
Baki ta buɗe zatai magana tsulum sai ga sallamar Yazeed. Kafin ma su gama amsashi ya riga ya shigo.
Kallon kallo sukaima juna shi da RK ɗin sai kuma kowa ya janye cike da basarwa. Takowa yazeed ɗin ya
ƙarasa yi ta ɗayan side ɗin. Saboda neman magana sai ya zauna a bakin gadon kusa da ƙafafun Maanal. A
hankali ta matsar da ƙafafun nata dake cikin bargo, dan RK ya wani zubama ƙafafun nata ido kamar mai
kallon television duk da a lulluɓe suke a bargon. Cikin dauriya ta gaida Yazeed. Ya amsa mata idanunsa kafe
a kanta....
“Yaya jikin naki?”.
“Na samu sauƙi Yaya. Ya aiki?”.
“Alhamdullahi. Tunda kin samu sauƙi sai sallama kenan ko?”.
Maimakon amsa saita sakar masa ɗan murmushin yaƙe kawai. Abinda ke hannunsa ya miƙa mata. “Ga
abinda kikace kina so, shine maimakon ki sanar min kika kama faɗama su Shahidah ko? Bana gaya miki duk
abinda kike buƙata yanzu ki sanar min ba. Domin nine da hakkin yimiki shi ai, kwana nawa ya rage mana
zama ma'aurata”.
Kanta kawai ta jinjina masa da faɗin, “Nagode”. Yayinda RK ya saki wani ɗan iskan murmushi yana sake
yin balance a kujerar. Sai kuma ya wani laɓe baki yana kauda kansa. Duk Yazeed na lure da shi, dama kuma
yayi furucin domin shi ne.
“Ina Nene?”.
“Taje gida bata jin daɗi”.
“Ayya ALLAH ya bata lafiya. Ai tana ƙoƙari ma ga jikin girma. Su su Shahidah fa?”.
“Basu ƙaraso ba, suna hanya dai sukace”.
“Okay yayi”.
Ya faɗa yana zaro wayarsa da ake kira. Ɗagawa yay tare da kaiwa kunne, sai kuma ya miƙe saboda masifar
da Mamma ke masa daga can, dan har ita Maanal ɗin taji furucinta na farko ma. Sassanyar ajiyar zuciya
Maanal ta sauke ƙasa-ƙasa dai-dai Yazeed ɗin na fita. Hakan yasa RK tuntsurewa da wata dariyar
wulaƙanci. Kallonta ta maida garesa cikin mamaki. Shiko ya wani ɗage mata gira cike da neman rigima ya
ce, “Amma dai kina matuƙar tsoron wannan yayan naki fa. Irin wannan sauke ajiyar zuciya haka”.
Ƙin kulashi Maanal tayi, sai dai maimaita kalmar tsoron daya ambata tanama Yazeed ɗin take a
zuciyarta. Shima bai sake cewa komai ba ya kawo hannu zai ɗauki abinda Yazeed ɗin ya bata tai saurin
ɗaukewa tana ɓata fuska.
“Wai kai idan baka shiga rayuwar mutum ba da abinda ba'a sakaka ba baka jin daɗi ne halan?”.
“Oh haka kike fassarani ashe?”.
“Hummm”.
Kawai tai shiru. A ransa yace miskilatu kenan. Magana fal cikinta amma bata son yi. A fili kam zaiyi magana
sai ga Yazeed ya dawo. Bai fasa ba ya cigaba da faɗin, “Birthday na ya kusa mi zaki bani as gift?”.
“Humm”.
Maanal ɗin ta faɗa idonta akan Yazeed daya iso gaban RK ɗin rai a ɓace. Shi kuma yayi kamar bai gansa
ba. Cikin fusata ya ce, “Malam ina son magana da kai”.
Sai lokacin RK ya dubesa. Sai kuma ya nuna kansa cike da rainin wayo wai shi? A kausashe Yazeed ya ce,
“Eh”.
“Okay to Bismillah ai gani. You are free zaka iya maganarka kawai”.
“Ba'a nan ba”.
Yanda yay maganar a fusace ya saka Maanal dake saurarensu kallon Yazeed ɗin a karo na farko. Sai kuma
ta kalla RK dake wani shegen murmushi baida alamar motsawa balle aje ga batun tashin. A hasale Yazeed
ya sake buɗe baki zaiyi magana Shahidah da Amaal sai mijin Shahidah ɗin sukai sallama. Dole ya haɗiye
maganar yana mai furzar da huci, sai kuma ya juya suka fara gaisawa da mijin Shahidah. Shima RK miƙewa
yay yana amsa gaisuwar su Amal, kafin ya juya ga mijin Shahidah ɗin shima suka fara gaisawa. Daga haka
ya fice a ɗakin. Hankalin Manaal naga su Amal Yazeed shima ya sulale ya fita, sai da ta ɗago da nufin yin
magana dashi kawai taga wayam. Waige-waige ta fara cikin mamaki, cikin tsokana Mijin Shahidah ya ce,
“Oh in dai samarinki ne ai sun fice auta”.
Fuska ta ƙwaɓe kamar zatai kuka ta ce, “Kai Uncle Sadeeq”.
Dariya suka sanya mata su duka....
★★★
Sam RK bai san Yazeed na bin bayansa ba. Dan hankalinsa ma nakan wayarsa fuskarsa da murmushi
saboda saƙon da yake karantawa. Jin ansha gabansa ya tsaya cak tare da ɗagowa. Kallon ido cikin ido
sukaima juna shi da Yazeed ɗin kaikace zakuna ne jirace da juna a filin daga.
“Doctor ina son maka gargaɗin farko da ƙarshe akan yarinyar nan”.
“Saboda mi?”. RK ya faɗa yana tsatstsare Yazeed da ido. Shima Yazeed ɗin cikin dakiya ya bashi amsa
da, “Saboda ita ɗin matar dazan aura ce. Akwai ranar aurena akanta. Kasan kuma nema akan nema
haramun ne sai dai idan kana da ƙarancin ilimin addini ne kuma na maka ƙarin bayani yanda zaka fahimta”.
Maganar Yazeed ta ƙarshe-ƙarshe ta zafi RK, amma sai ya danne yama saki murmushi da ƙoƙarin raɓashi
alamar zai wuce abinsa. Cikin zafin nama Yazeed ɗin ya sake shan gabansa. Kallonsa RK ya sake yi yana
ƙoƙarin danne ɓacin ransa, dan shima fa ya iya zuciyar nan, dalili ne kawai ke sakashi danne tasa ba tsoro
ba.
“Yazeed why???”.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭_*
[2/11, 8:42 PM] Maryam anas: *_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
1️⃣5️⃣1️⃣5️⃣
........“Why kake son mu dinga kasancewa a wannan yanayin ni da kai?. Ina fa ganin girmanka ne matuƙa
shiyyasa kaga ina barin komai a yanda yake. Please respect your self mana. Kai namiji ne, nima namiji ne
kowa ya cigaba da gwada sa'arsa mai rabo sai ya ɗauka a cikinmu. Dan har yanzu banga dalilin da zaisa na
iya janyewa ɗin ba”.
“Haka kace?”.
Murmushi RK ya sakar masa da kashe ido ɗaya kawai ya zagayesa ya bar wajen. Hakan ya sake hasala
Yazeed matuƙa. Tabbas shi ɗin mutum ne mai haƙuri da dattako. Amma yana da tsananin kishi akan abinda
yake so shiyyasa yake zafafawa akan al'amarin Maanal matuƙa. A zuciyarsa yake tunanin dolene ya koyama
guy ɗin nan hankali, dan haka a daren yau zai wuce Kaduna dan gara ya zauna ayita ta ƙare shi da Daddy.
Mamma dai ce matsalar zai rumtse ido kawai komai ma ya faru daga baya yasan zata sakko ta yafe
masa.....
Kiran daya shigo masa a wayane ya katse tunaninsa. Ganin ƙanwarsa Badiyya ce kamar zai share sai
kuma dai ya ɗaga. Yana kai wayar kunnensa ya janye da sauri saboda abinda ta sanar masa.. Yana sauke
wayar daga kunnensa sai kuma ga text massage ɗin Ammie itama ya shigo masa. Ai bai tsaya sauraren
komai ba yabar asibitin......
_____________
“Wai Daddyn Yazeed mikake nufi da ni ne a gidan nan? Katafi kai da matanka holewarku bance komai
ba, ka dawo ranar girkina kace baka buƙatar komai daga gareni. Na zuba maka ido nan ma, washe gari
Basariyya tai girki ita jiyama haka. Yau kuma ƴar sonka ta amsa”.
Idan kujerun dake falon sun motsa Alhaji Usman ya motsa kenan. Tamkar ma bai san da zaman Hajiya
Yaya a falon ba yake kallon labaransa yana shan fruits da Ammie ta haɗo masa. Hakan ne ya sake sakata
fusata, cikin matuƙar ɓacin rai ta ja remote ɗin dake a Centre table ta kashe tvn gaba ɗaya. Karo na farko
ya juyo ya kalleta fuskarsa a matuƙar haɗe. Itama kallon nasa take tana huci.
“Sadiyya bar falon nan kafin ranki yafi haka ɓaci”. Har cikin ranta taji tsoron fitar kakkausar muryarsa.
Amma sai ta dake dan gara dai ayita ta ƙare. Itama a fusacen ta ce, “Babu inda zanje wlhy. Dan nifa na gaji
da abinda ake min a gidan nan. Ubana ya dasa inuwa wasu banzaye suzo su zagayeta domin sha suna min
gadara.”
“Hummm”.
Ya faɗa kawai yana miƙewa. Bedroom ɗinsa ya shige tare da rufo ƙofar ya barta a falo tana jidali ita kaɗai.
Haka dama yake mata, ita kuma sai take ɗauka kamar tsoronta yake ji ko tafi ƙarfinsa ne. Bata san yana
hakan bane kawai saboda wani dalilinsa daban, amma badan gorin da take masa ba akoda yaushe.
Tsautsayi rabon faɗan nan ya koma kan Ammie sai gata ta shigo sashen batare da tasan Hajiya Yaya na nan
ba. Aiko ina wuta Hajiya Yaya ta saka Ammie, nanfa ta shiga mata gori da cin mutunci. Ita dai Ammie komai
batace da ita ba ta ajiye basket ɗin hannunta dake ɗauke da kayan abincin maigidan a saman d/table.
Rashin tankawar da batai ba itama sai ya sake fusata Hajiya Yaya, a matuƙar zafafe ta nufi d/table ɗin da
niyyar kifar da kayan abincin Ammie ta tare tana girgiza mata kai.
“Kiyi haƙuri Hajiya kar kiyi haka dan ALLAH. Koba komai shi ɗin abincine, yana da darajar da
wulaƙantashi kuskurene takowace irin fuska”.
“To mama Asiya shawara kike bani ko umarni?”
“Babu ko ɗaya da nake baki a ciki kiyi haƙuri”.
“Anƙi ayi haƙurin munafuka kawai, kullum sum-sum ita a dole ta ALLAH amma dafinki yafi na baƙin
kumurcin maciji. Kin mallake min miji da bin bokaye, kin cika mana gida da agololi har kina shirin ganin kin
mannawa ɗana. Wlhy Asiya sai naga bayanki a gidan nan”.
“Idan ta juya ba.....”
Alhaji Usman daya fito ya faɗa a zafafe. Juyowa sukai su duka suna kallonsa. Fuskarsa a ɗaure ya cigaba
da faɗin, “Idan ta juya kam zakiga bayanta Sadiyya. Amma kiga bayanta akan zama dani har gaban abada
bazakiga hakan ba da iznin UBANGIJI. Asiya ajiye abinci, idan kin isa dan ALLAH ki zubar da shi ni kuma
wlhy yau sai na baki mamaki irin wanda baki taɓa zato ko tsammani ba. Ke Sadiyya bafa wai ina tsoronki
bane a gidan nan. Karki ƙureni a wannan karon wlhy idan ba hakaba zakiyi matuƙar dana sani.”
“Dana sani na nawa kuma ai nayi dana sani tun daga randa na amince na aureka....” sai kuma ta fashe
da kuka “Kai dai burinka kullum ka wulaƙantani a ƙasan ƙanwar bayana koma nace sa'ar ɗana ko, shike nan
ga gidan nan na bar maka, ka kwaɗata ka cinye dan ALLAH” fuuuu ta fice daga falon. Tsaki yaja kawai tare
da juyawa zai koma bedroom ɗinsa. Hankalin Ammie ne ya tashi, cikin sauri tabi bayansa, kusan a tare suka
shigo bedroom. Jin yanda ta faɗo masa ya sashi juyowa yana kallonta.
“Dan ALLAH ka bita karta tafi ɗin da gaske, na roƙeka Abban Hameed. Bana fatan kowacce matsala ta
kasance tsakaninka da matanka a dalilin.....”
“Asia!”.
Ya faɗa cikin katseta. Kanta ta shiga girgiza masa sai ga hawaye. Zata sake magana kawai ya jawota jikinsa
ya rungumeta. Sosai take bashi tausayi, mace ce mai haƙuri da juriya akan komai na rayuwa. Tana da
kawaici da saurin sallamawa koda abu zai cutar da itane ko zuri'arta. Duk abinda kaga ta masa musu a kai
to ka duba wannan abun kuwa. Komai yace ita mai biyayya ce a gareshi ko bai dace da ita ba. Wannan
halayen nata ne suka mamayesa cikin ƙanƙanin lokaci yake jinta ƙololuwa a saman matan da ya aura tun
yana da jajayen sawunsa. Hanata duk wata damar sake magana yayi, ba kuma ta sake yi ɗin ba ta haƙura
saboda ita ɗin mai biyayyace a garesa. Fitowarsu falo babu jimawa tana zuba masa abinci sai ga
Asalamiyya ta shigo tana kuka ita da Basirah.
“Daddy dan ALLAH ka kazo ka hana Mamma tafiya. Gata can ta haɗa kaya zuwa mota zata tafi Daddy”.
A birkice Ammie ke kallonsu, sai kuma ta yunƙura jikinta na rawa zata nufesu. Cikin bada umarni Daddy
da tun kallo ɗaya da yay ma su Asalamiyyar bai sake ba ya dakatar da ita. “Asia koma ki zauna”.
Kallonsa Ammie tai kamar zata fashe da kuka. “Daddyn Hameed kana fa jin abinda suke faɗa”.
“Cigaba da zuba min abinci nace. Ku kuma ku bar falon nan!!!”. Ya ƙare maganar a tsawace. Zabura sukai
saboda tsawar ta shigesu. Har rige-rigen fita suke daga fallon. Kallonsa Ammie ta sake yi zatai magana ya
ɗaga mata hannu. Dole tai shiru ta cigaba da zuba masa abincin hannunta sai rawa yake. Tsaf yake kallon
yanda hannun nata ke rawa amma sai bai tanka ba. Tana gama zuba masa abincin yaja ya fara ci hankalinsa
kwance.. Abu ya ishi Ammie ta rasa ina zata kama, sai kallon Daddy kawai take. Can dai ta jawo wayarta ta
shiga rubutama Yazeed text massage.....
______________★
Yau da wuri Nene ta dawo asibitin. Dan haka ta kora su Amaal gida suma saboda mijinta daya shigo
Abuja. Daga nan ma asibiti da yazo ya duba Maanal ɗaukar Amal ɗin yay suka wuce masaukinsa. Itama
Shahidah da mijinta yazo sai suka wuce kawai. Hakan yasa Maanal ta kasance daga ita dai Nene a ɗakin.
Sai kuma duk kaɗaici ya isheta. Dan Nene da zaran tayi sallar isha'i zakaga ta fara gyangyaɗi abinta. Gashi
babu waya a hannun Maanal ɗin, tana Kaduna aka barta, bakuma a kawo mataba har yanzu. Shiyyasa ma
taima Shahidah maganar a sayo mata kayan zane-zanen ta dan ta iya sosai, shine Yazeed yaji ya hana
Shahidah siyowa shi ya sayo mata. Tun ɗazun daya kawo mata su ta ajiye bata sake bi takansu ba. Sai yanzu
ta jawo ledan ta fiffito da su. Komai da take buƙata akwai, harma da wanda batace a sayo ba ya sayo. Dan
haka sai ta gyara zama kawai ta fara zanenta dan shine hubby nata tun tana yarinya. Maanal ta masifar iya
zane ta yanda idan ta zana abu sai ma ka ɗauka ba itace ta zana ɗin ba. Da farko ɗakin jiyyar tata ta fara
zanawa harda Nene dake zaune a kujera tana famar gyangyaɗi, sai ita kanta a yanayin da take zaune. Koda
ta gama taga komai ya mata sai ta tsinta kanta kuma da fara zana agogo. Abinda ta jima batayiba a rayuwar
zanenta kenan. Ta zana guda biyu tana akan na uku RK da Doctor Ranjet suka shigo ɗakin. Firgigit Nene ta
farka, yayinda Maanal tai ƙoƙarin rufe zanen nata amma sai caraf RK ya rikesa.
“Woow!, this is amazing”. Ya faɗa yana kallon zanen cike da matukar mamaki. Sai kuma ya kalleta. “Dan
ALLAH da gaske kece kikayi Baby?”.
Kafin ma Maanal ta bada amsa Nene ta cafe cikin taɓe baki. “Yo in dai Manaalu ce ai baka rabata da
zanen aljanai Rafeequ. Tun tana yarinya uwar tayi tayi amma ina harma an barta taitayi itace zata ƙare da
mafarkinsu ai ba wani ba”.
“Nene ai abune mai ƙyau wannan ɗin.....”
“Ɗan nan a al'adar yahudu da nasara ba. Amma mudai a musulunce banjin cewar abune mai ƙyau duk
da ni ɗin ba malama bace”.
Dariya RK yayi, sai kuma ya miƙama Nenen zanen yana faɗin, “Amma Nene kinyi fa ƙyau a wajen nan
kamar wata sarauniya a kujera”.
Ba ƙaramin zare ido Nene tayi ba tana kallon kanta an zane ras harda yanayin atamfarta. Duka ta kaima
Maanal itako ta kauce tana ƙara ɓata fuska. Aiko ta shiga zazzaga jaraba shi dai RK da Dr Ranjet na dariya
abinsu. Manaal dai ta miskile fuska kamar ba ita tai tsiyar ba. Sai da Nene tayi mai isarta sannan ta fice dan
idan anzo duba Maanal ɗin fita takeyi. Bayan fitar Nene Dr Ranjet na duba Maanal RK daya kasa ajiye
zanen ya dubi Maanal cikin serious ya ce, “Amma basirar nan naki bai kamata ya tafi a banza ba kawai,
yana da ƙyau mutane su amfana da shi”.
“Kamar ya?”.
Ta faɗa a ƙasan maƙoshi. Bai damu ba, dan zuwa yanzu ya sake fahimtar miskilancinta mai lasisi ne.
“Akwai Companyn da nasan suna matuƙar buƙatar aiki da mai irin wannan basirar taki”.
A daƙile ta furta, “Ba buƙata”.
Cikin ɗan girgiza kansa ya ce, “Wlhy seriously Baby akwai companyn da zakiyi wannan aikin fa kuma anan
Abuja ne, Please kada kice a'a dan ko kina gida zaki iya musu aiki ma”.
Rasama abinda zata cemasa tayi, dan yanda ya wani marairaice fuska ya tsareta da manyan idanunsa sai
ta ji ta kasa furta komai. Dr Ranjet ne ya saka baki a zancen nasu, “He is telling you the truth my patient..
Ko game da ciwonki idan kin samu abinda zai dinga maidaki busy zaisa ki rage saka damuwar abubuwa a
ranki da har zai dinga yawan tashi akai-akai”.
Shiru kamar bazatace komai ba. Sai zuwa can ta sauke ajiyar zuciya tana ɗan girgiza kanta. “Su Ammie
bazasu amince ba ne. Kadai ji abinda Nene ta faɗa ai”.
“In dai har kin amince zakiyin ki barni dasu kawai”.
“Mi zakace musu?”.
“Ke dai kawai ki amince zaki ji ai”.
“Zanyi tunani”.
Ta faɗa a taƙaice tana zamewa ta kwanta. Bai sake magana ba shima sai ɗaukar hoton zanen da yay a cikin
wayarsa kawai. Bayan fitarsu kafin barci yay awon gaba da Maanal tai zurfi matuƙa a tunanin zancen RK ɗin
da Dr Ranjet.....
__________★
Lokacin da Yazeed ya iso gidan sha ɗaya saura na dare. Dan haka ya samu Daddy ya ma kwanta. Sai ya
zarce sashen Ammie, samunsa yay shima a rufe, hakan na nufin tana sashen Daddy kenan dan su Waleed
ba nan suke kwana ba suma. Dole sashen Hajiya Yaya ya nufa inda ya tadda ƙannensa zaune a falo jugum-
jugum. Hatta da television bata aiki a kashe take yau. Da gudu Amrah tazo ta shige jikinsa tana sakin kuka
mai ban tausayi. Rungumetan yay shima yana ɗan shafa bayanta. Kusan mintuna biyu sannan ya ɗagota
tare da kama hannunta suka ƙarasa cikin falon. Nuni yay ma sauran da su zauna dan suma duk sun miƙe
tsaye. Shima ya kai zaunen Amrah a gefensa.
“Mike faruwa ne?”.
Kafinma ya rufe baki su duka sun saki kuka. Wadda ke bimasa da suke kira Suhana ce ta fara masa bayani
muryarta na rawa. “Yaya muma bamu san ainahin abinda ya farun ba. Kawai dai Mamma taje sashen
Daddy, babu jimawa sai gata ta dawo kuma tana hawaye. Mun tambayeta bata kulamuba ta hau haɗa
kayanta. Bamu sani ba ko sakinta Daddy yayi”.
“Saki?”.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
1️⃣6️⃣1️⃣6️⃣
..........“Haka muke tunani Yaya. Tunda bamu taɓa ganin Mamma ta haɗa kaya tabar gidan nan ba dan sun
samu matsala da Daddy.”
Basira ta bashi amsa cikin kuka. A take zufa ta gama wanke masa jiki, harma ya gagara cewa komai.
Badiyya ce ta sake katse masa tunani da faɗin, “Yaya kuma wlhy koma minene ya faru da sanya hannun
waccan munafukar matar a ciki. Dan tana a sashen Daddyn komai ya faru, ko sanda Mamma zata tafi da
muka je kiran sa itace ta hanashi”.
Cikin mamaki ya ce, “Ita wa?”.
Kai tsaye ta bashi amsa da, “Amaryarsa mana”.
Hararar daya zuba mata ya sata kame bakinta tana turashi gaba. Dama sun san ai bazai yarda ba tunda
agolan ƴarta ce budurwarsa. Bai sake cewa komai ba ya miƙe, sai da ya kusa kaiwa ƙofa ya juyo yana
kallonsu. “Kutashi kuje ku kwanta zuwa da safe koma miza'ai sai ayi. Ku kulle nan ɗin”.
Wasu sun amsa masa da to, wasu ko da hararar ƙasan idanu suka rakashi dan sun san babu damar yi a
zahiri mutum yaci dukan banza a daren nan balle ma babu Mamma.....
★★★
Washe gari koda Yazeed yazo ganawa da Daddy sai ya samu har ya fita. Sashen Ammie ya nufa, inda ya
taddata zaune jihum alamar tana tare da damuwa harma da ɓacin rai. Gaisheta yay da girmamawa kamar
yanda ya saba. Itama ta amsa masa cikin kulawa tana danne damuwarta.
“Yanzu ka iso ne?”.
“A'a tun da daddare. Around eleven na samu kunyi barci shiyyasa na haƙura har sai da safe. Yanzu kuma
naje sashen nashi naga alamar a rufe yake”.
“Nima nazo na haɗa masa breakfast na koma naga yabar gidan. Ka ganni tun ɗazun nake kiransa yana
rejecting daga ƙarshe ma ya kashe wayarsa gaba ɗaya.”
“Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un”. Yazeed ya shiga ambata yana mai dafe kansa da dukka hannayensa
biyu.
“Yazeed nikam da zakaji daka haƙura da batun auren nan na Maanal. Dan idan zamu duba gaskiya duk
batunsane tushen wannan matsalar. Kayima Hajiya biyayya ALLAH sai ya baka wadda tafi Maanal”.
“Amma Ammie ina sonta, wlhy matuƙar so nakema Maanal dan ALLAH kar kice haka, ke da Daddy ne
ƙwarin gwiwata. Sannan shima Daddy ai yanada hakki a kaina kuma yana son auren. Miyasa Mamma
bazata fahimta ba. Miyyasa bazata fahimci Aunty Sabuwa tana zugatane kawai saboda ta samu biyan tata
buƙatar na auri tata ƴar bane?”.
“Amma Yazeed ƴar uwartace fa, uwa ɗaya uba ɗaya. Taya bazata tayata son abinda take so ba.”
“Amma wlhy Ammie akwai manufa a zuciyar Aunty Sabuwa. Mamma ɗin ce kawai ta kasa fahimta”.
Rasa abincewa Ammie tayi, dan itakam wannan cakwakiya ta ma fara gundurarta wlhy. Tabbas tana
matuƙar son Maanal ta auri Yazeed kodan ƙyawawan halayyar yaron. Sai dai tana tsoron halin Hajiya Yaya
gaskiya. Sannan tana tausayi da fargabar jefa rayuwar yarinyarta mai raunin ciwo a cikin wani hali. Yazeed
shi kaɗai ke son auren nan sai mahaifinsa. Amma ƴan uwansa da mahaifiyarsa da mafi yawan danginta
basa so sam.....
________________★
“ALLAH nazata wasa kikeyi da kikace min gaki nan tahowa Zaria fa.”
“hhhh aina fahimci hakan a muryarki. Bazaki ganeba fitowar ta dole ce. Gidanmu ne keci da wuta na
gasken gaske kwana biyun nan”.
“Tofa wuta kuma Aminiya tami?”.
“Uhhm ke dai bari, tushen matsalar daga auren agolar gidanmu ne da maigidan yace zai ƙulla kusan
shekara uku kenan.....”
“Kar kice na katseki wai ƴar amaryar ku? To da wa?”.
“Ita fa, dawa kike tunani idan ba ɗan sonsa Yazeed ba. Tunda fa akai maganar dama uwar tasa tace bata
yarda ba. Shi kuma Daddyn Huznah bai maida kai ba yarinyar dai tana cigaba da karatu, shi kuma Yazeed
yana manne da yarinya. Bayan ta kammala karatun akaso tada zancen bansan miya faru ba dai kuma aka
dakata ta wuce service. Indai taƙaice miki batu ta gama service ɗin ne yanzu zancen ya sake tasowa shine
aketa dam-barwa. Ita uwar ɗan tace bafa za'ai ba, kwana takwas da suka shige sukazo itada ƴar barikin
ƙanwar nan tata sabuwa suka cima uwar ƴar mutunci randa muka bar nan kenan shine itakuma yarinyar ta
yanke jiki ta faɗi ta kama aman jini”.
“Aman jini kuma?”.
“Uhm kin san sunce wai ai tana da ciwon zuciya”.
“Tirƙashi, eh lallai dole kice gidanku naci da wuta. Ke nan yanzu yaya ake ciki kuma?”.
“Yarinyar na asibiti a Abuja yanzu haka. Ba shine nake faɗa miki nakoma Abuja ba nima harma naga
ƙanin Majdiya”.
“Oh ƙwarai anyi haka. Ko shiyyasa itama taje Abujan ita da yara duka dan gulma shine suka wuce gidan
Yaseerah wai ganin ɗaki. Aiko sai da na mata tujara daga ita har mijin nata data dawo”.
Dariya sosai suka kwashe da ita suna tafawa. Hajiya Basariyya ta ce, “Ai kinmin dai-dai wlhy. Kinga gobe
ai ta kiyaye”.
“Karma ta kiyaye na koya mata hankali. Mu munafuncin kishiya wanne bamu sani ba kuma”.
“Wlhy kuwa. Sai dai wanda kuma aka ɓoye a zuciya. Yanzu kin san miya sani zuwa Zaria ɗin?”.
“A'a sai kin faɗa”.
“Jiya uwar gadaran gidan namu ce ta wuce gida harda kaya cike da akwatina. Dan ya hanata girki a gidan
sai mu biyu mukeyi, shine jiya girkin ita shegiyar ne ita kuma taje ta samesu tai musu ɗibar karan
mahaukaciya. To ban sani ba ko sakinta yayi shine ta kwashi kaya ta tafi, dan naga ɗan ma ya dawo jiya da
dare su kuma matan sunata kuka. Yau kuma tunda safe mai gidan ya fice rai a ɓace matar son nasa itama
dai duk ta koma sukuku. Dan haka malam nakeso ki kira mana nan ina son a ƙarama wutar fetur ne ya sake
birkice musu. Sai kuma batun Huznah da yaron nan da suka haɗu a Abuja. Na fahimci kamar itace ta damu
da shi, dan sai ta yini kiransa a waya bai ma amsa mata ba sai ya gadama. Ina son a riƙe masa wuta gaskiya
san bana son nima ta rasashi. Nayi binciken yaron shi kansa bama ubansa ba wani shege ne. Dan
Companys ne da shi na abubuwa. Ga shima uban nasa sune ƙasar. Hakama ƴan uwansa biyu kowa ƙwaron
kansa ne duk da dai shi ƙanin ya fisu komai.”
“Humm wato ƙawata kina matuƙar birgeni, sam ke baki da wasa akan abu. Sha yanzu magani yanzu
kikema komai shiyyasa da wahala asha gabanki”.
“Yo ai babu zama ƙawata. Lamarin rayuwar nan kana sakaci sai a tafi a barka a ƙarshe bare mu dake
zagaye da shegun kishiyoyi, tako ina da hari ake kawo mana mune na tsaka. Kinga ko dole mutum ya nemo
garkuwa da takobin kai nasa harin ai.”
“Wannan gaskiya ne. Yanzu dai bara nasa Zaituna ta kira mana shi ta falon baya. Kin san gidan namu
dai cike yake da ƴan sa ido. Damma maigidan baya gari ne jiya da yamma yay tafiya.”
“Ato ai ansha hidima dole a koma nema kuma. ALLAH ya taimaki ƴan baya suma haka dai dan wlhy
rashin auren yaran nan ya fara tada min hankalina. Rigi-rigi sai samari sunzo kamar za'ayi sai ki nemesu ki
rasa”.
“To ke kuwa maƙiya cike da gida za'a barsu haka ne. Ke dai kin san yaƙi da gwagwarmayar da nasha
Kafin auren nan na Yaseerah ya yiwu. Yanzu saura Zaituna itama dai wani ya biyota a ƴan bikin so nake na
huta gajiyar nan na fara aiki a kansa. Dan babu wasa”.
Dariya suka kwashe da ita su duka suna mai taɓawa. Hajiya Basariyya ta ce, “Haka nake fata a nawa
gidan. Dan sai yaran nan sun gama aure kaf kafin yaran ɗakin gadararriyar can suyi sa. Na riga na shirya
yaƙarta ta wannan fanin”.
“Wlhy ina bayanki. Shegu ai idan sunce su mugunta suka iya gidan suka taras....”
_________★
Kwanakin Maanal goma sha shida a asibiti sannan aka bata sallama. Dai-dai da cikar Hajiya Yaya kwana
tara a gidansu. Daddy dai tun wannan fitar da yay daga gida a washe garin zuwan Yazeed bai koma ba. Sai
daga baya suka fahimci yama bar ƙasar ne sabgar gabansa. Dan kwanansa biyu da tafiya yasa Hajiya
Basariyya tabisa can. Komai Ammie batace ba akan hakan, damuwarta fushin da yake da ita da batasan
laifinta ba. Gefe kuma ga yaran Hajiya Yaya sun tasota da rashin kunya da rashin mutucin a gidan. Sai idan
Yazeed na gidan ne take samun sauƙin su. Dai-dai da su Hameed sun takurawa da zagi da duka. Wannan
dalilin ya saka yau koda su Shahidah suka kirata akan sallamar Maanal tace Maanal ɗin ta zauna anan
gidan Shahidah kawai. Nene sai ta biyo su Amaal ta dawo. Hakan yayma Maanal daɗi dan dama bata son
komawa Kadunan. Sai dai ita Nene ta fahimci akwai matsalane amma batace komai ba ta shanye a ranta
har sai ta koma. Dama tanata mamakin abinda ya hana Ammie sake dawowa Abujan. Kullum sai dai suyi
video call safe da yamma. Takance suyi haƙuri da rashin daowarta akwai abinda take yi ne.
Badan Maanal tasoba ta yarda RK yay musu rakkiya har gidan Shahidah. Cikin farin ciki su Munaya
sukazo suka rungumeta. Itama haɗasu tai ta rungume tana mai jin kewarsu dan sau ɗaya sukaje dubata
asibiti aka hana zuwa dasu saboda bata son hayaniya a lokacin. Har cikin falo suna manne da ita. Kafin su
fara rige-rigen zuwa ɗakko mata gift da kowa ya tanada mata.
“I love you yarana”.
Ta faɗa a hankali tana rungumesu....
“Kina da son yara kamar haka, amma kiketa ɓata mana lokaci”. RK dake gefen kujerar da take ya faɗa a
hankali ta yanda itace kawai taji. Ɗago yaran kawai tai daga jikinta batare da ta kallesa ba. Shima sai ya
basar saboda isowar Amal ɗauke da ƙaramin tire ta haɗo masa abin sha. Godiya yay mata hankalinsa
kwance ya ɓalle ruwa ya tsiyaya a kofi ya hau sha. Ita Maanal ma sai ƙarfin halin nasa ya ɗaure mata kai.
Kasa jurewa tai sai da ta ɗan zuba masa ido. Yanda take kallon nasa ne ya sashi sauke kofin daga bakinsa
shima yana kallonta. Sai kuma ya wani ɗan ƙyaƙyƙyafta idanunsa. Nata idanun ta ɗauke tana ɗan yamutse
fuska da faɗin, “Kai ko kunya baka ji?”..
“Ikon ALLAH kunyar mi zanji?. Gidan yayata nake fa. Idan kuma so kike na fara jin kunyar ki bani damar
sakaki a gidana na miki alƙawarin ko'ina naje aka bani ko miye bazanci ba sai naki”.
Kallo ta jefa masa mai kama da harara sai kuma ta girgiza kai kawai ta miƙe. Harta gama hayewa
upstairs idonsa a kanta, sai da takai step ɗin ƙarshe itama ta ɗan juyo dan tana jin kaifafan idanunsa na
yawo a kanta. Da sauri ya ɗauke kansa ya basar. Ita kuma taja ƙaramin tsaki ta ida hayewa. Daga haka bata
sake sanin sanda yabar gidan ba. Dan wanka ta samu tayi a ɗakin Shahidah tai kwanciyarta sai barci. Dama
sunce zata dinga samun isashen barci yanzu hakan ne zai dawo da kuzarinta data rasa...
Bayan sallar la'asar Nene dasu Amaal suka wuce. Sai suka koma daga ita sai Shahidah da mijinta da
yaranta biyu a gidan kawai. Sai kuma masu aikinta guda biyu. Jitai kuma duk babu daɗi, dan tana matuƙar
son ta gansu su duka a waje ɗaya hakan na sakata a farin ciki. Sai dai yaya ta iya aure ya rarrabasu. Hira
suke da Shahidah, koma ace Shahidah ke hiran dan Maanal dai daga guntun murmushi sai eh ko a'a ne
nata. Muneff ne ya shigo da ɗan gudunsa, autan Shahidah, dan daga shi dai har yanzu bata sake ba ko tana
hutawane ko ta tsaya oho mata.
“Muneff ban hanaka wannan guje-gujen ba wai nikam?”.
Shahidah ta faɗa cikin taka masa birki. Yaron bai damu ba ya ce, “Mamy Uncle Yazeed ne yazo”.
“Uncle Yazeed na kd?”.
“Eh Mamy. Yana waje ma”.
Kallon Maanal Shahidah tayi. Itama Maanal ɗin ita take kallo. “Kije ki shigo da shi”.
“Ni Didi ƙafata ke ciwo”.
Kai kawai Shahidah ta girgiza tana miƙewa. Hijjab ɗinta da takan ajiye a falo saboda baƙi irin haka ta
ɗauka ta saka sannan ta fita. Babu wani jimawa sai gata ta dawo Yazeed biye da ita. Yana shigowa idonsa
akan Maanal ya fara sauka. Itako ta ƙurama television ido kamar bata san da shigowar tasa ba.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
1️⃣7️⃣1️⃣7️⃣
.......Sai da suka gama gaisawa da Shahidah sannan ta ɗan kallesa ta ce, “Yaya Yazeed ina yini”.
Sai da yaja kusan minti ɗaya kafin ya amsa da, “Lafiya lau. Yaya jikin naki?”.
“Alhamdullahi”.
“Masha ALLAH”. Ya faɗa yana maida kallonsa ga Shahidah. “Shine aka sallameku Shahidah ban sani ba. Sai
da naje asibitin yanzu akace kuna gida”.
“Kayi haƙuri Yaya Yazeed anyi kuskure kam. Amma banyi tunanin zaka dawo yau bane, azatona kuma
kasan da sallamar ne ma wlhy. Tunda muma munje kai musu breakfast Nene ke sanar mana ai doctor yace
zai sallemeta yau, da daddare yake sanar musu.”
“ALLAH ya ƙara lafiya to, ya kuma kiyaye gaba. Ina su Nenen?”.
“Nene ai yanzu na tabbata suna gab da shiga Kaduna. Mijin Amal ne ya wuce dasu gaba ɗaya”.
“Kai da sauri haka?. Ita Nene ko ɗan hutawa bazatayi ba”.
“Aikam bazata zauna ba. A hakama dan zaman asibiti ne. Yau kam muna dawowa tace bafa zata sake
kwana a garin nan ba”.
Murmushi kawai yay da faɗin, “Shike nan zan sameta har gida ai. To kema sai ki shirya mu wuce da
safe ko, tunda yanzu yamma dai tayi kam”. Ya ƙare maganar idonsa akan Maanal.
“Ni Ammie tace ai na zauna anan”.
“Anan kuma? To saboda mi?”.
Shahidah ce ta bashi amsa da, “Bana zaton wani abune gaskiya. Inaga dai tana son ta ɗan ƙara murmurewa
ne dan suma likitocin sunyi gargaɗi sosai akan ta huta a waje mai ƙarancin jama'a da hayaniya. Amma tana
ƙara murmurewa zata dawo Yaya Yazeed”.
Badan ya gamsu da bayanin Shahidahn ba ya ce, “Okay shike nan ALLAH yasa kaffara ne. Nima dai ina
nan Abujan har zuwa jibi in sha ALLAHU, dan akwai abinda zanyi”.
“ALLAH ya taimaka ya bada nasara”. Shahidah ta faɗa cike da girmamawa. Dan suna matuƙar giramam
yazeed, koba komai suma yana girmama musu Ammien su. Su kansu yana mutuntasu, dan bazasuce ya
taɓa musu wani abu na ashsha ba tun daga zamansu gidansu har zuwa aurensu. Hasalima a auren nasu ya
zame musu tamkar babban yaya ne a komai. Tashi tai ta bar musu falon. Hakan yasa shi tashi ya koma
kujerar kusa da Maanal shima. Cike da kulawa murya can ƙasa ya ce, “Baki jin komai dai zuwa yanzu?”.
Kanta ta jinjina masa alamar eh.
“Alhamdullahi haka ake so ai. Nasan kece kikacema Ammie baki son komawa KD ko?”.
Cikin marairaice fuska kamar zatai kuka ta ce, “Ni ALLAH babu ruwana.”
Kallonta kawai ya tsaya yi, sai kuma ya ɗan murmusa tare da duƙo da kansa kaɗan murya ƙasa-ƙasa ya
furta, “Adana shagwaɓar nan ba yanzu ba”.
Kanta ta duƙar ziciyarta na gudu da sauri-sauri a ƙirjinta kamar zata fito waje. Sai kuma ta yunƙura zata
tashi. Cikin bada umarni ya ce, “Koma ki zauna”. Babu yanda ta iya dole ta koma ta zauna ɗin tana ɓata
fuska....
_______________★
“Da alama wannan karon mijinki yana son nai matuƙar cin mutuncinsa Sadiyya. Ki taho gida tsahon
kwanaki goma amma bai biyo bayanki ba saboda yana son nuna min iyakata. Ban san yaushe Usman ya
fara maida kansa sakarai a gidansa ba. Ace mace ke juyaka yarinya ƙarama”.
Hawaye Hajiya Yaya ta sake matsowa tare da duƙar da kai kamar ta ALLAH. Muryarta na rawa ta ce,
“Baba wlhy yamafi yanda kake zatonsa a yanzu. Ni shiyyasa ma nace kawai kasashi ya sakeni na gaji da
wannan zaman ƙuncin, ai ba haka mukai da shi ba. Shi da kansa yace min duk macen da zai kawo gidan
nan sai dai ta kasance a ƙarƙashin ikona da umarnina. Amma duk ya manta da wannan alƙawuran da
girmana agaban ƴaƴana da matansa yake tozartani. Wai har yake iya gaya min sai dai matarsa idan ta juya
naga bayanta amma ba'a zaman gidansa ba, wai ni Usman ke tarema mace faɗa a gabana Baba”. Ta fashe
da kuka.
“Kinga ya isa kukan haka kinji, barni da shi ai nasan maganinsa. Shi kuma Yazeedu daketa kai kawon ki
koma saboda baida kishin uwarsa shima zan gyara masa zama. Share hawayenki abinki zakiga matakin
dazan ɗauka jeki kwanta”.
Kai Hajiya Yaya ta jinjina tana miƙewa hannunta a saman ido tana share hawaye kamar wadda akacema
baban ne ya mutu. Sai da ta gama ficewa mahaifiyarta dake zaune a falon bata tofa ko a ba a maganar tasu
ta nisa a hankali. Tsohuwar kirki mara yawan son hayaniya kenan. Idanunta akan Baba ta ce, “Nikam da
zakaji shawarata dattijo da baka goya bayan Sadiyya ba a wannan karon. Kai kanka kasan halin yarinyar nan
sarai da abinda zata iya. Tunda kaga kuma Usman ya watsar da ita a wannan karon wlhy ba banza ba. Dan
haka ka kirashi cikin dattako ka zaunar dasu su duka kaji bakin kowa. Idan ta kama ma can gidan nasa
zakaje ka tasata gaba ka haɗasu har abokan zaman nata. Karfa dan ka raini Usman ya zama kana tauye
masa hakki akan ƴar da ka haifa.”
“Ai ke kinji matsalarki, idan har abu zai taso akan yaran nan sai kin nuna ban iya ba ke sarkin tawakkali
da gaskiya ko”.
“Ba haka bane Dattijo. Masu iya maganafa sunce kaso naka duniya ta ƙisa, ka ƙisa duniya ta soshi.
Usman na maka matuƙar biyyar da kosu ƴaƴan da ka haifa ba kowa ke maka irinta ba. To bai kamata a
cigaba da ƙasƙantar da shi ba akan abinda ya isa da shi. Wannan fa rayuwar aurensu ce. Kuma shine
shugaba a gidan, yin kutse a al'amarin kamar ƙasƙantar da shi ne. Dan ALLAH kada ka biyema yaran nan
ana ganin ka da kima da mutunci irin na uba kuma shugaba”.
Shiru yay na kusan minti biyu, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya. “Hakane kuma Adama nagode da
tunatarwa. In sha ALLAHU gobe zan tasata gaba muje gidan. Sai dai ance min shi Usman ɗin baya ƙasar,
amma dai inada tabbacin kamar yau ne da dare zai dawo”.
“To Alhmdllh gobe idan ALLAH ya kaimu ɗin sai kuje, ALLAH ya taƙaita al'amarin kuma ya daidaita su”.
“To Amin ya rabbi. Yarane sai addu'a kawai yanzu, sun maida aure wasan yara”......
__________★
Isowar dare Daddy da Hajiya Basariyya sukai ma gidan. Tafiyar kwana goma har sunyi fresh abinsu.
Babu wanda yasan da dawowar tasu, dan ita Ammie ma harta kwanta abinta. Cikin barci taji wayarta na
ƙara. Da ƙyar ta buɗe ido ta jawota dan ta manta ne ma bata kashe ba. Ɗagawa tai takai kunne tare da
sallama. Sai dai Muryar wanda ya amsa mata da umarnin daya bata ya sata watsakkewa sai kuma ta tashi
zaune. Jin abin tai kamar mafarki, amma dai ta miƙe ta ɗauka dogon hijjab ta saka sannan ta nufi kitchen.
Tea ɗin daya buƙata ta haɗa masa. Sai ta haɗa da ɗan snacks da fruits da bata rabo da su. Haka ta fito
gidan shiru alamar kowa ya kwanta ta nufi sashen maigidan. Takai hannu zatai knocking ta tsaya cak
sakamakon jin muryar Hajiya Basariyya na tashi a sama cikin faɗa...
“To amma dare yayi ai, ƙarfe nawa yanzu da zaka ɗaga waya ka kirata wai ta kawo maka abu. Ni banda
hannune ko abinda zata kawo makan banda shi a sashena? Randa kuka dawo Abuja wayasan kun dawo ba
sai tashi mukai muka ganku a gidan nan ba. Sai ni daka raina. Wai mi Asiya tafimu dashi ne? Mi take dashi
na mata da mu bamu da shi da kake son ganin ka fifitata a kammu?!!.......”
“Badariyya wai kina da hankali kuwa. Baki ganin dare yayi zaki zo kina min ihu a kaina. Da kike maganar
miyasa zan kirata ta kawo min abu ke da kika dawo daga tafiya mizaki bani? Sannan batun fin sauran mata
da kike sai yanzu kika san Asia tafi sauran mata ashe. To lallai kin makaro da kika kasa fahimtar hakan tun
tuni. Ita da na saka kika bini a ranar girkinta kinji tayi wani ƙorafi ne. Kuma randa muka dawo Abuja ni Asia
bata kwana a sashen nan ba, idan ma ta kwana ai matatace. Dan haka ki fice min anan shasha kawai tana
girma bata san ta girma ɗin ba”.
“Ni ce shashashar Daddy Huznah?”.
Banza yay mata bai tanka ba. Sai maida hankalinsa yay a kiran Ammie. Da sauri ta danne wayar gudun
kartai ƙara. Sai kuma ta daure tai knocking ƙofar. Umarnin shiga ya bata. Koda ta shigo kai tsaye a Centre
table ta ajiye tray ɗin, sai kuma ta shiga gaishesu su duka a tare da yimusu barka da dawowa. Daddy ne
kawai ya amsa mata. Zata juya tabar falon ya katse hanzarin ta. “Ina zaki kuma”.
Juyowa tai ta kallesa. “Zanje na kwanta ne, kuma ku samu ku ɗan rintsa ku huta gajiya ko”.
“Dawo ai anan zaki kwana”.
“Anan kuma Daddyn Hameed amma ai....”
Cikin katseta ya ɗaga mata hannu. Dole ta haɗiye abinda take son faɗar. Cikin ɓacin rai Hajiya Basariyya
taja akwatinta da hand bag ta fice a sashen tana jan tsaki. Da kallo Ammie ta bita harta gama ficewa. Tai
wani kalar masifar bugo ƙofar har sai da Ammie ta zabura. Cikin sanyin jiki ta maida dubanta ga Daddy
dake ƙoƙarin fara shan shayinsa hankali kwance. “Daddyn Hameed dan ALLAH....”
“Asia! Kin san bana son jan zance ko!”.
Ajiyar zuciya Ammie ta sauke kawai, badan taso ba tabi umarninsa a yanda yake buƙata.......
__________★
Washe gari kusan ƙarfe goma na safe sai ga baƙi. Ammie na tsaka da haɗama Daddy abinci zai fara ci
maigadi ya isar da saƙon zuwan Alhaji Mamman sirikin na Daddy kuma uban gidansa. Da sauri Daddy ya
miƙe tare da shiga ciki ya canjo kayan jikinsa zuwa jallabiya. Yayinda Ammie kuma ta fita ta ƙofar baya
domin ƙaro abincin. Bata wani jimaba ta koma ɗauke da wani kayan abincin. Ta samu har Daddy ya shigo
da shi falonsa shi da babban amininsa sai Hajiya Yaya. Ajiye kayan Ammie tai cike da girmamawa ta rissina
ta gaishesu batare data damu da hararar da Hajiya Yaya ke mata ba. Sun amsa mata da kulawa. Dan haka
kawai sai Alhaji Mamman ɗin yaji Ammien ta masa kwarjini da shiga ransa. Bai fi sau biyu ya taɓa ganinta
ba. Lokacin ruguntsumin aurenta sai kuma da sukaje da Daddy gaishesa bayan sun dawo Hajiya Yaya ta
dinga zuba tujara daga nan Ammie ta ɗau aniyar bazata sake zuwa gaidashin ba. Daga mutunci sai abu ya
zama fitina da cin mutunci, tun daga nan ko Daddy yace tazo suje sai tayi yanda tai ta zame jikinta. Abincin
ta shirya a gabansu sannan ta fita domin basu damar ci, duk da dai Baban yace sun gode bazasu ci ba
sukam. Amma Daddy nata roƙonsu. Dole dai suka ɗan taɓa kaɗan, kafin Baban yasa Daddy kira masa su
Ammie su duka. Dai-dai nan kuma Yazeed ya shigo falon daga gani isowarsa garin kenan. Dan tunda daren
jiya Ammie ta tura masa sako akan dawowar su Daddy ɗin, tare da bashi shawarar ya taho da safen dan ta
samesa a gida shiyyasa yay sakkon tahowa kafin ya sake guduwa. Yana fatan iyayen nasa su sasanta kansu
komai ya wuce kada abun yayta ƙara girma. Sai kuma akai sa'a ya samu kakan nasa yazo tare da mahaifiyar
tasa gidan. Cikin girmamawa ya gaida kakan nasa sannan ya gaida abokinsa. Sun amsa masa da kulawa da
tambayarsa aiki tare da tsokanarsa akan ƙara zama tuzuru babu aure. Murmushi kawai yay ya maida
hankalinsa a gaida Daddy sannan ya gaida Hajiya Yaya itama. Dai-dai nan Hajiya Basariyya da Ammie suka
shigo suma. Gaidasu yayi suma da girmamawa. Ammie ce kawai ta amsa masa da kulawa. Hajiya Basariyya
kam sama-sama dan tana cikin haushi ne. Ko su baba sama-sama ta gaishesu kamar an mata dole. Anan
ma sai Baban ya sake karantar abubuwa da dama. Bayan an natsa da gaishe-gaishe aminin Baba da suke
kira Alhaji Kallah ya buɗe taron da addu'a. Daga haka ya kalla Daddy cikin mutuntawa ya kirayi sunansa.
“Usman!”.
“Na'am Baba”.
Daddy ya amsa masa da girmamawa dan shima yana ɗaukarsa matsayin uba ne. Kai duk ma abokan Alhaji
Mamman a rayuwa Daddy na basu girma irin na uba ne. Alhaji Kalla ya cigaba da faɗin, “Mike faruwa
tsakaninka da iyalinka ka turata gida har tsahon kwanaki babu wani bayani”.
“Baba ni bani na tura ba”..........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
1️⃣8️⃣1️⃣8️⃣
.......“Ban gane ba Usman, kamin bayani yanda zan gane da ƙyau”.
Kai Daddy ya jinjinama Baba Kallah. Kafin ya gyara zamansa da ƙyau ya shiga zayyano masa abinda ya
sani. Kuma ma duk ita Hajiya Yaya ce ta kirashi a waya ta sanar masa. Daga ƙarshe ya dora da faɗin, “Gasu
nan baba ka tambayesu daga Asia ɗin har Basariyya akwai wanda na zaunar naima magana akan batun?
Na barsu ne har sanda yarinyar zata samu lafiya dan shine mafi muhimmanci. Amma sai ita ta nuna min
ban isa ba. Nace taje ta duba yarinyar ita da yara sashenta tace ban isa ba ita kuma Basariyya taje, hakan
yasa na dakatar da ita da shigowa wajena.....”
“Dolene to sai naje. Itama Basariyyan ai munafunci da gulma ne ya kaita badan ALLAH ba”. Hajiya Yaya
ta faɗa cikin katse Daddy. Tsawa Babanta ya daka mata shima, dole tai shiru tana kumbura fuska.
“Usman kamin dai-dai, dan abinda kayi ɗin shine mazantaka.” baba Kalla ya faɗa, sai kuma ya juya ga
Hajiya Yaya yana mai kiran sunanta. “Sadiyy! Dukkan abinda Usman ya faɗa haka akai?”.
Babu musu ta jin jina kanta. Sai kuma ta ɗora da faɗin, “Baba nifa tsakanina da ALLAH koda aurena zai
ƙare ne tsakanina da Usman sai dai ya ƙare a yau. Dan haka ku zama shaida ban amince Yazeed ya auri ƴar
Asiya ba. Idan kuma ba hakaba a shirye nake na fiddashi a cikin ƴaƴana na barma Asiya tunda haka naga
yake buƙata. Na gaya masa na masa faɗa amma yana maidani ban san abinda nake ba, to tunda haka ne
dai ya zaɓa ko ni ko yarinyar”.
Hankali tashe Yazeed ke duban mahaifiyar tasa. Zai yi magana Baba Kalla ya dakatar da shi ta hanyar
ɗaga masa hannu. Dole Yazeed yay shiru.
“Sadiyya miyyasa baki son shi haɗin nasu? Yarinyar nada wata illane da musulunci ya hanamu auren
irinsu?”.
“Illoli da yawa kuwa Baba. Ciwuwwuka sun gama zagaye rayuwarta. Sannan mu har yanzu bamu da
tabbacin ma suna da uba tunda mudai bamu taɓa ganin dangin uban nasu ba balle mu shaida, har bikin
yayunta akai a gidan nan mudai bamuga kowa ba, wama ya sani ko basu da uban ne shiyyasa sam ni jinina
bai wani haɗu da nata ba dan bana ƙaunar yarinyar nan, ba kuma na ƙaunar uwarta gata nan”. Ta ƙare
maganar da nuna Ammie babu nauyi ko kara. Kai baba Kalla ya girgiza da faɗin, “Ashsha Sadiyya, wannan
magana tayi tsauri da yawa. Kiyi ƙoƙari ki dinga gyara harshenki yayin magana. Dan haka karna sake jin irin
wannan zancen banzar ya fito. Munji baki son wannan haɗin, wacece kika fidda masa ke a matsayin
matar?”.
“Baba Nazeefar Sabuwa. Idan har Yazeed yana son yaga farin cikina to ya aurenta dan ita nasa
tushenta. Idan ko ba haka ba ya shirya rayuwar auren ƙunci da baƙin ciki, sannan duk abinda zata haifa
babu ruwana da su kamar yanda shima na ciresa daga cikin ƴaƴana.....”
Cikin takaicinta da harzuƙa Daddy ya ce, “Aiko baki isaba wlhy, Maanal na zaɓama yarona matsayin
matarsa ko kina so ko baki so, kuma wlhy first and last da zaki sake sheganta yaran nan idan ba hakaba
kuwa sai ranki ya ɓaci fiye da yanda kike zato....”
“Kaima kuwa baka isaba Usman, dan yanda kake jin kai uban Yazeed ne nima nice mahaifiyarsa. Nina
ɗauki cikinsa na tsawon wata tara, nai naƙudarsa na kumayi rainonsa haɗe da tarbiyya har yakai girman da
wata banza a banza daka kawo gidan ka kake ɗaukar ta a mutum ta isa ta mallake min shi, kai wlhy duk
abinda kake ji ka iya na iya fiye da iyawarka Usman, dan....
“Sadiyya!!!”.
Babanta ya katseta a tsawace. Shiru tai amma a ranta tana ƙunƙuni, dan ta ɗau aniyar koma miza'ayi sai
dai ayi amma Yazeed bazai auri ɗiyar Asiya ba dan ita zuwa yanzu ma ta fara tunanin basu da uban. Ganin
ran baba ya kai ƙolokuwar ɓaci hakama Daddy da ita Hajiya Yayan Ammie dake saurarensu kawai ziciyarta
na mata ƙuna cike da girmamawa ta kalla Baba. “Baba dan ALLAH ina neman alfarma”.
“Faɗi ko minene ɗiyata in dai ina da shi zan miki”.
Wani takaici ne ya lulluɓe zuciyar Hajiya Yaya ganin yanda Babanta ke bama Ammie muhimmanci a
zaman fiye da ita. Baki ta buɗe zatai magana ya harareta. Dole tai shiru ta cigaba da hare-harenta. Ammie
bata nuna ta damu ba ta cigaba da faɗin, “Baba dan ALLAH ku barta ta aura masa wadda take so. Domin
gaskiya ta faɗa Maanal bata dako isashiyar lafiya ma. A yanzu haka likitocin ma sunce tana matuƙar
buƙatar hutu ta yanda al'amuranta zasu dai-daita. Shi kuma Yazeed za'a cigaba da tauyesa babu aurene
saboda hakan. Bayan UBANGIJI ya halatta masa auren mata har uku ne. Idan har Maanal matarsa ce ko
zuwa nan gaba sai ayi......”
“Allah ya kiyaye, har abada bako za'ayi ba idan abinda kike tunani kenan ki ciresa kuwa....”
Hajiya Yaya ta katse Ammie a harzuƙe. Shima Daddy a harzuƙen ya katseta da faɗin, “Ashe kuwa zaki
mutu bayan anyi, dan Maanal ita na zaɓama Yazeed kuma shima itace zaɓinsa aure tsakaninsu babu fashi
da izinin UBANGIJI ko da Asiya data haifeta bata yardaba kuwa. Baba ku ƙyaleta, tunda ita bata san
masalaha ba dan ALLAH mu zuba aga ni da ita waye keda ƙarfin iko akan Yazeed ɗin.....”
“A'a Usman duk baza'a kai ga haka ba”. Baba Kalla ya faɗa. Batare da ya jira cewarsu ba ya cigaba da
faɗin, “Ku duka ku kwantar da hankalinku kuji. A matsayinku na iyayen Yazeedu duk kuna da iko a kansa,
amma fa ku sani shima yanada hakki a kanku. Aure dai ba wasa bane, ba kuma jeka ka dawo bane ba. Dan
haka ku masa adalci ku barshi ya zaɓi wadda ransa ya kwanta da ita koda a cikin zaɓin naku ne. Idan kuma
babu a cikinsu itace ma babbar masalaha ya auro daga can gefe shike nan matsala ta kare. Saboda haka kai
Yazeedu kana da wadda kake so ne?”.
A hankali kuma karo na farko Yazeed ya ɗago idanunsa da suka kaɗa sukai jajur saboda damuwa. Cikin
danne ƙuncin daya mamaye masa zuciya ya ce, “Baba idan har auren duka zaɓin nasu zai zama masalaha
na karɓa. Zan auri Maanal ɗin da Nazeefa....”
“Baka isa ba sai dai ka auri Nazeefa ita kaɗai....” Hajiya yaya ta katsesa cikin daka tsawa. Babanta ne
shima ya katseta a tsawacen. “Sadiyya bana son shashanci fa. Yaro ya kawo mafita kinama mutane rashin
hankali, ko kunyar idona baƙyaji bare nauyi. Shin kokin manta mune a gabanki bashi mijin naki kaɗai da
kika raina ba. Ana binki ta lalama kina wani botsarewa saboda wulakanci. To wlhy ki shiga hankalinki. Idan
kuma ba hakaba zan hanashi auren Zazeefa ɗin naga yaya zakiyi. Shashancin banza kai”.
Haƙuri ta fara bashi ranta a matuƙar dagule. Tayi hakanne kawai dan ganin yanda ransa ya ɓaci, ta
kuma san halin mahaifin nata idan yay magana baya canjawa. Gara ta lallaɓashi suje a haka ita tasan duk
ma hanyar da zatabi dan ganin ta tarwatsa wannan aure.... Shima Daddy haƙurin yaba baban, dan haka ya
cigaba da faɗin, “Shike nan magana ta ƙare zai auresu su dukan. Dan haka sai kuje ku fara shiri dan nan da
watanni biyu za'ayi a wuce wajan. Rana ɗaya za'a ɗaura auren.”
Wani irin motsawa zuciyar Ammie tayi da ƙarfi. Hakama Hajiya Basariyya da tun da aka zauna bata
tofa komai ba zuciyarta wani irin raɗaɗi take mata. Ina bazai yiwu ta bari ai wannan haɗin ba, sannan
bazata taɓa yarda aima Yazeed auren gata shi kaɗai ba wlhy, Gara a cigaba da wannan fitinar hakan yafi
sakata nishaɗi, zai kuma fi bada armashi idan yazam anyi auren Nazeefa da Yazeed ne farko. Ammie zatai
magana tai saurin katseta ta hanyar fara yi. “Baba mun gode ALLAH ya saka da alkairi ya kuma sanya
albarka a al'amarin. Sai dai nakega maganar ɗaura auren rana ɗaya kamar akwai damuwa musamman ga
ita Maanal. Tunda likitoci sunce abarta ta ɗan huta mizai hana a fara yin na Yazeed da Nazeefa daga baya
sai ayi da ita Maanal. Komai ma zaifi tafiya a cikin masalaha ni dai anawa ganin, zuwa lokacin itama Maanal
ta murmure dan yarinyar ta fyaɗu sosai a wannan karon, wlhy abin tausayi kamar bazata rayuba ma. Sai
itama Huznah ta samu miji, Inaga sai a haɗa dana Yazeed ɗin kawai ko yaya kukace”.
A maganar farko Hajiya Yaya wani irin daɗi da godema Hajiya Basariyya ta shigayi a zuciyarta. Daga
ƙarshe kuma sai taji zafi danta fahimci hassada Hajiya Basariyya ke son nunawa. Amma zata bita a hakan
dan itama ta ribantu. Itama dai Ammie har ranta taji daɗin zancen Hajiya Basariyya, duk da tasan tayi
hakanne badan ALLAH ba sai wata manufa tata. Shiko Daddy wani irin ƙuna zuciyarsa ta shigayi, saboda ya
jima da fuskantar wacece matar tasa. Cikin takaici kawai yake mata wani kallo mai kama da harara. A
ɓangaren Yazeed kuwa wani irin tsanar matar uban tashi ya fara ji a karo na farko a rayuwarsa. Duk da ya
jima da fahimtar halinta na munafunci dan ta sha haɗashi da Daddy a baya bai taɓa maida hankali ko
damuwa da lamarinta ba. Amma a yau ji yake kamar ya maketa dan baƙin ciki. Shifa ya amshi auren
Nazeefa ne kawai dan ya samu dai Mamma ta haƙura ya auri Maanal. Amma shine munafukar matar nan
zata kawo wannan ƙauli da ba'adin. Kasa daurewa yayi cikin sanyin murya ya ce, “Ummi anawa tunanin ai
ba komai bane. Idan ta dawo ƙarƙashina zama tafi samun kwanciyar hankalin da su likitocin ke buƙata.
Maanal na buƙatar hutu ne da kulawa. Kuma ina sha ALLAHU duk bazan gaza yin hakan akansu su duka
ba”.
Ganin kamar zancen ya shigi baba yasa Ammie saurin tare numfashinsa. “Hakane Yazeed, amma dan
ALLAH nima ina roƙonka da abi shawarar Hajiya. Saboda ya kamata aje neman auren Maanal wajen dangin
mahaifinta. Ita kanta kuma sake samun nutsuwar zaisa komai ya tafi mana dai-dai yanda ya kamata. Idan
akayi na Nazeefar kamar da wata biyar haka itama sai ayi natan. Kamar yau ne ai ka kwantar da hankalinka
kaji Yazeed”.
Ji Yazeed yay kamar ya fashe da ihu. Dan idanunsa har wani ɗan tara ƙwalla sukayi. Baba Kalla ne ya ce,
“To da gaskiyarsu kuma ta wani fanin idan muka kalla. Tabbas mai irin wannan ciwo mai haɗari ya kamata
abi dokar likitocin domin samar mata da nutsuwa. Sannan kamar yanda mahaifiyarta ta faɗa yana da ƙyau
aje neman aurenta wa mahaifinta. Dan haka kayi haƙuri Yazeedu kamar yau ne in sha ALLAHU. Kaima idan
akai haka zaifi baka nutsuwa da kwanciyar hankali. Ai rabon baima zoba ballantana ya wuce”.
Albarka duk suka saka da fatan ALLAH yasa haka shi yafi alkairi. Sai dai a ɓangaren Yazeed zuciyarsa a
matuƙar ƙuntace take. Haka shima Daddy sam wannan tsarin bai masa ba. Kawai dai dan anfi ƙarfinsa ne.
Amma ya ƙullaci Ammie da Hajiya Basariyya. Da haka dai taron ya watse.....
_________★
Bayan wucewar su Baba Ammie ta samu Daddy akan zataje gaishe da Nene tai mata godiya da ban
gajiya. Amma sai yace bai yarda ba. Abin ya bata mamaki, saboda a fusace yay maganar. Zata roƙesa kuma
ya ɗaga mata hannu da nuna mata ƙofa alamar ta fita. Tsantsar biyyarta garesa yasa bataja zancen ba ta
fitan, dan ta fahimci a fusace yake da ita ne, sai dai bata san ainahin laifin nata ba ita kam. Koda ta kira
Nene ta sanar mata ya hana, sai tace ta jirata gata nan zuwa ita....
________★
Hajiya Basariyya kam dariya ta dinga sheƙawa. Sai kuma tai kiran aminiyarta ta lambarta mata komai.
Dariyar suka haɗu sukayi tayi su duka. Sai da sukai mai isarsu cike da zolaya Hajiya Kamila daga can tace,
“Aminiyata ke kwalba ce wlhy uwar sharri. Cikin ƙanƙanin lokaci kinsa dole anbi yanda kike so. Ho tawajena
kina wuta fa”.
“To ni ɗin ta wasa ce aminiya ai idan sun san wata basu san wata ba. Idan har ina raye Asiya bata isa
samun abinda ni ban samu ba. Ita kanta Hajiya Sadiyya da take ganin kamar na mata aiki ne ta saurari
shirina akanta.”
“Kai ta wajena mi kike shirya mata ita kuma?”.
“hhhhh karki damu sai mun haɗu zaki ji komai da komai. Ke dai yanzu kice da Malam Nagode. Zuwa gobe
kuma zan turo miki Huznah ya mata dukkan abinda yace dan ina son shap-shap yaron nan ya kawo kasa
tunda har na gumtsa musu zancen kada a fara ɗaukata maƙaryaciya”.
“An gama ai karki wani damu kanki”.
“To shike nan sai tazo.”
Daga haka sukai sallama kowa ya yanke wayar. Hajiya Basariyya ta faɗa saman gado tana mai jin kanta a
sama can ƙolokuwa da tabbatar ma da kanta yau sa'a tata ce........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
1️⃣9️⃣1️⃣9️⃣
.......Sosai ƙannen Yazeed sukai farin cikin dawowar mahaifiyarsu gidan. Gaba ɗaya sun zagayeta anata
cakai-cakai kowa na bata labarin abinda ya faru da bata nan. Itako sai murmushin jin daɗi take yi
musamman akan abinda suka dinga ma Ammie. Suna a hakan Aunty Sabuwa ta samesu. Tashi Hajiya Yaya
tai suka shige ƙuryar ɗaki suka rufe kansu. Dama itace tai kiranta tunɗazun bayan wucewar su Babansu. Sai
da Aunty Sabuwa tasha fresh milk ɗin data ɗakko daga falo sosai sannan ta dire tana sauke ajiyar zuciya da
faɗin, “Kai nafa kwaso rana da yawa. Kin ganni nan daga tudun wada nake. Kin san munata shirye-shiryen
bikin ƴar ƙawata Sailuba. Ko sanda kika kirani muna tsaka da meeting ne ma dan tun sassafe na baro gida”
“Kai kar dai kice min bikin yarinyar nan har yazo?”.
“Wlhy kuwa yazo Yaya ai abin babu wuya...”
“Gaskiya ba wuya kam. Abin mamaki wai Sailuba da aurar da ƴa”.
“Hhh kai yaya da abin dariya kike. Yo ALLAH na tuba komu badan yaran nan sun tsaya ruwan ido ba ai da
tuni jikoki sun cika mana ko'ina.”
“Ai dan ubansu dole kam suzo su fito da mazajen aure dan na gaji da ganinsu ɗirka-ɗirka a gida sai yawo
bikin wasu da taron birthday party. Ba maneman nan suka rasa ba amma narasa mi sukema hange-
hangen”.
“A'a to yadai kamata wlhy Yaya. Yanzu abin sha'awa bakiga yarinyar nan yanda mijin ya haɗo lefe na
nunama sa'a da tsara ba. Jiya mukaje muka duba gida komai yaji gidansa kamar ka zauna kaita kallo. Kuma
karki daɗa karki raga yaron shagone wlhy. Amma komai babu raini”.
“To Sabuwa ai dama abin zuciya ce ba dukiya ba. Sai dai kuma kana gudun inda yaronka zai je ya
ƙasƙanta ne. Ko ka saida akuya ta dawo tana ci maka danga.”
“Da wannan kuma dan wannan. Yanzu dai zakije min baici ko?”.
“A mizai hana, ranar yinin biki insha ALLAHU zan zo, ai Sailuba nada mutunci da girmamawa. Yarinyar nan
ko sanda kike zaune a Kano indai tayo tanan anguwar dai ta shigo mun gaisa”.
“Sailuba ai bata da damuwa Yaya. Damma ALLAH ya bata shegen miji ne kawai. Wai shi uztazu. Ko akan
bikin nan sai da muka bisa ta ƙasa sannan fa ya amince da wannan shagulgulan amma da duk ya hana”.
“Oh kice dai kuna nan da halin bin malam nan maƙaryata ko Sabuwa?”.
“Ko ɗaya aunty kawai dai sai ta kama. Wani lokacin ne halin mazan nan sai ka haɗa da dabaru. Yanzu ko
ke abinda Yaya ke miki a gidan nan da zaki bari ai masa ɗaurin huhun goro ai da kin wuce wajen. Ko su su
Basariyyan haka nan suka zauna ne kike gani. Ai wlhy ba banza ba yake wannan rawar jikin akansu har shi
ma Yazeed ɗin”.
“Zan iya yadda dake wlhy Sabuwa, dan yau naga abu a gidan nan. Kai Basariyya makirar mata ce. Tabbas
na tsani Asiya kuma bana sonta amma wani lokacin gara min ita sau dubu akan Basariyya..........”
Tsaf Hajiya Yaya ta labartama Sabuwa yanda komai ya faru yau a zaman da akayi, har hukuncin da su
Baba suka yanke. Sosai Aunty Sabuwa ta sauke ajiyar zuciya da har sai da Hajiya Yaya ta ce, “Lafiyarki kuwa
irin wannan ajiyar zuciya haka?”.
“Wlhy ƙalau Yaya. Naji kawai abubuwan duk sun zo da sauƙi ne. Koba komai ai mu munafuncin
Basariyyan yaman rana yau, dan in dai an rigada anyi na Nazeefar Asiya kuma sai dai ta nema ma ƴarta
wani mijin amma ba Yazeed ba”.
“Nima haka nace ai, shiyyasa ma na ƙyalesu aje a hakan. Amma kuma kin san Basariyya maciji ce bata
ramin kanta. Mi kika fahimta a wannan salon nata?”.
“Hassada ce kawai wlhy Yaya. Tasan auren Yazeed sai ya zama na nunama tsara a gidan nan shiyyasa
take so ta cusa na ƴarta ayi tare. Kuma tayi na banza dan babu abinda zamu fasa sai ma mu ƙara in sha
ALLAHU. Ita waye ƴar nata zata aura ma shin?”.
“Yo waya sanan musu bata faɗa ba. Ai kin santa ita komai nata ƙunshe-ƙunshe saboda munafunci
bata so a sani. Amma nidai tunda nake a gidan nan ban taɓa ganin wani fitaccen baƙon mutunci da za'a
kirashi mijin aure yazo wajen Huznah ba. Sai dai idan ba'anan gida ake taɗin ba”.
“Eh ai munafuka ce zata iya tsara komai. Shiyyasa wlhy Yaya ki zagargari yaran nan suma su fiddo mazan
aure, in ba hakaba zataita kutsawa ne dan taga ta gama aurar da nata yaran duk ɗan abin arziƙin su
wawashe a barsu su da saura. Kina dai gidan nan agololi biyu sukai aure Yaya ya dinga ɓarin kuɗi kamar
babu gobe. Badan mun daƙile wannan ba ma dana uku kenan. To shi dama aurar da yara haka yake na
farko-farkon nan sunfi morewa, dan anfi kashe musu dukiya”.
Sosai zancen Aunty Sabuwa ya shigi Hajiya Yaya. Cikin juyayi ta ce, “Oh dama haka abin yake Sabuwa?
Amma shine baki fargar dani ba tuntuni”.
“Ba fargar dake ne banyi ba Yaya. Kin san auren agololin can munafuntarmu akai akaita komai kamar
talakawa zasu aura shiyyasa bamu bama abin muhimmanci ba. Sai daga bayan nan muke ganin ashe
lulluɓin biri akai mana da fatar kura. Kuma ko rantsuwa nayi banyin kaffara Yaya ne ya samawa yaran nan
mazansu. Shegu da yake suma burin su kenan gasu nan har da ƴaƴa bibbiyu”.
“Humm ai Daddyn Yazeed ya jima yana zaluntata a gidan nan ban farga ba. Kiga fa Asiya ta bayan
bayana wai itace da waɗan nan nasarorin. Babu komai zamu ɗauki mataki”.
“Babban ɗaukar mataki ALLAH Yaya kuɗi zaki fiddo ko ki shirya ma dake muje ayo miki aiki ɗan gaske.
Mufa ba bokaye muke bi ba. Malamai ne na zaure, kin ga ko kaje wajen malami ba bokaba ai babu batun
rasa sallar da ake cewa ta kwana arba'in ko?”.
“Hakane kuma. Inaga dai wannan karon zanje ɗin”.
“Haba koke fa yaya”.
(Humm ALLAH ai ba'a masa wayo ko dabara Sabuwa. Idan abu ya dameka ka miƙa lamarinka ga
UBANGIJI shi baya barci kuma baya mantuwa. Fafi yawan wasu abubuwan da muke ɗaukarsu damuwa a
rayuwarmu hassada ke mana jagora akansu. Amma mu sani rabonkafa rabonka ne. Sannan wani baya
canja maka ƙaddararka. Duniyar nan cike take da arziƙi, ka tsarkake zuciyarka ka nema naka kaima in dai
nakan ne wani bai isa tare maka wannan samun ba ko ya ƙarama kansa. Shima iya nasa kawai zai ci. Ya
rabbi ka yafe mana kurakuranmu😭 ka gafartama iyayenmu 🙏).
____________★
“Tabbas da manufa kam ta ƙarfafa maganar taki Asiya. Amma kada ki wani damu. Mu ALLAH yasa haka
shine mafi alkairi. Dan nima ta bakinki zuwa yanzu auren Maanal da yaron nan ya fita a raina. Duk kuwa da
shi ɗin mutumin kirki ne. Amma halin uwarsa da ƴan uwansa bazai bar Maanal zama lafiya ba. Gata ita mai
rauni. Ni yanzu abinda nake gani kawai mu lallaɓa Maanalu ta bama yaron nan Rafeeq dama ya shigo
sosai, shi kansa Yazeed ɗin ba lallai idan sun aura masa tasu ba su barshi haka ai”.
Tabbas hakanne Nene, ni kaina wlhy yaron nan Rafeeq yamin. Yaron a haka dai kamar baida wata
damuwa. Gashi kuma ɗan uwan Majdiya uwa ɗaya uba ɗaya. Majdiya mutuniyar kirkice ga addini. Dan
hatta yaranta tarbiyyarsu ta banbanta da sauran ƴaƴan gidansu. To dan dai yaran yanzu ne kai kana hango
musu alkairi su suna wani hange daban. Amma dai yanzu zanyi duk yanda zanyi ta cigaba da zama can
Abujan dan bana sha'awar dawowar Maanal gidan nan a yanzu kuma sam Nene wlhy”.
“Wannan ma tunani ne mai ƙyau. Gara ta zauna a can ɗin kusa da ƴar uwarta. Tunda shima can yake
Rafeeq ɗin sun ma fi samun shaƙuwa. To amma shi maigidan naki bazaiga an masa ba daidai ba?. Kinga dai
yanda yake matuƙar ƙaunar yaran nan da musu hidima. Tunda kuka dawo hannunsa bai taɓa bambanta
al'amarin su dana ƴaƴansa ba”.
“Tabbas hakane Nene. Nima idan na tuna hakan jikina yana sanyi. Dan ya musu abinda mahaifinsu da
ƴan uwansa suka gagara musu. To amma yaya zamuyi, matar nan wlhy ta wuce duk yanda kike tunani.
Nata ma mai sauƙi ne, dan babbar matsalarta itace ƙanwar nan tata. Saboda mashawarta ne bata moreba
kawai, amma duk masifarta ta wani fannin tafi Basariyya sauƙi”.
“To mu cigaba da addu'a, ALLAH ai bai manta da kowa ba. In sha ALLAHU komai zai kasance da sauƙi.
Yanzu dai sai kisan dabarar da zaki masa akan zamanta ɗin can dan a rabu lafiya har su gama wannan bikin
nasu. Saboda yanzu kam kema fa sai kinyi haƙuri, zakiga abubuwa da yawa wanda za'a dinga miki su da
gayyane.”
“Hakane Nene. In sha ALLAHU babu damuwa. Dama dai matsalar tawa Maanal ce. Dan su wannan
samarin babu ruwansu. Itace dai dama ina tsoron a jangwalo ciwon nan nata. Amma idan bata gidan koma
mi suke shirin yi suyita yi”.
Nene ta gamsu sosai. Dan haka suka cigaba da tattauna batun Maanal ɗin dai. Nene bata bar gidan ba
sai bayan magrib. Ammie ta rakota sukaci karo da Hajiya Yaya itama ta rako Sabuwa. Kallon banza suka
dinga musu. Dan Nene ma na gaishesu amma ko kulata basuyi ba sai ma tsaki da Sabuwa taja musu mai
ƙarfi. Abin ya ɓatama Ammie rai amma sai ta danne. Itama Nenen duk da nata ran ya ɓaci sai ta danne dan
bata son ƙarama Ammien damuwa...
_________★
Damuwa da ɓacin rai da tashin hankalin hukuncin da aka yanke yasa a ranar Yazeed ya koma Abuja
batare da sanin kowa ba. Ita kanta Hajiya Yayan sai da dare ta aika Basira kiransa ta dawo ta sanar mata
ɗakinsa ma a kulle yake. Waya ta ɗaga tai kiransa. Batare da amsa sallamarsa da gaisuwarsa ba tace yazo
tana nemansa. Haƙuri ya bata akan shi fa ya koma Abuja. Dan ya samu kira na gaggawa. Ranta ya matuƙar
ɓaci amma sai ta danne bisa shawarar da Sabuwa ta bata na a dinga lallaɓashi yanzu har ayi a gama lafiya.
Cikin sauƙaƙa murya tace shike nan idan ya dawo sayi magana. ALLAH ya bada sa'a.
Ya amsa mata da Amin, dan ko yaya ya ɗan ji sauƙi a ransa na jin bata fushi da shi. Yazeed mutum ne
mai kiyaye fushin iyaye, sannan yana da takatsantsan akan al'amarinsu. Ko wannan maganar Manaal ɗin
da ace babu goyon bayan Daddy duk son da yake mata da tuni ya haƙura saboda mutuntasu....
________★
A Abuja dai kam RK ya riƙema Maanal wuta. Dan kullum sai yazo gidan Shahidah sai ya fake da dubata
yazo yi kasancewar dama sun sanar dasu hakan. Sai dai abinda basu sani ba duk tsarin RK ne dama akan
batun zuwa gida dubatan kullum. Ya cigaba da kwaɗaita mata zancen aiki. Tun tana dojewa harta sanarma
Shahidah. A mamakinta sai Shahidah ta bata goyon bayan mizai hana ta amshi tayinsa. Ai abune mai ƙyau
neman nakanka musamman a wannan zamanin. Cikin damuwa Maanal ta ce, “Amma Didi kin san Ammie
bazata yarda ba. Hakama Daddy zaiga kamar mun nuna gazawarsa ne musamman idan mukai dubi da duk
yaransa mata babu wadda ya bari tayi aiki, ko ku sai da kukai aurene yace idan mazanku sun yarda kuyi
aikinku. Idan ni kuma nazo masa da sabon tsari sai yaga kodan bai haifemu bane ba”.
“Hakane Maanal. Amma idan aka duba naki al'amarin ke ai yana buƙatar uziri. Bazamu yanke hukunci
ba yanzu ki bari zan sanarma Ammie to. Itama Amal zanyi magana da ita. Amma ko nan Daddyn su Barru
shi goyon baya ya bada ɗari bisa ɗari, ya kuma ce in dai dan Daddy ne shi a barsa zaiyi magana da shi.
Kinga an samu sauƙi kenan ai”.
“Shike nan ALLAH ya zaɓa mana abinda yafi alkairi.”
“Amin ya rabbi, wannan dama itace addu'ar daya kamata kiyi tun farko. Sannan dan ALLAH idan yazo ki
daina ɗaɗɗaure masa fuskar nan taki, hakama idan ya kiraki kina ɗauka Auta. Wulaƙanci sam bashi da
ƙyau”.
“Didi ba wulaƙantasa nake ba nima. Bana son ya saki jiki akan abinda bazai samu bane kawai”.
“Hummm Maanal kenan. ALLAH dai ya zaɓa mana abinda yafi alkairi”.
Maimakon ta amsa da Amin sai Maanal ɗin kawai ta koma ta kwanta dama tana a ɗakinta ne tana
karatun novel ɗin nata na fama Shahidahn ta sameta........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
2️⃣0️⃣2️⃣0️⃣
........Shahidah ta kira Ammie ta sanar mata da komai game da abinda RK yazo ma Maanal da shi. A
mamakin Shahidah sai ji tai Ammie na maimaita kalmar Alhamdullah. Kasa daurewa tai ta ce, “Ammie kin
amince kenan kema tayi aikin?”.
“Sosai kuwa Shahidah. Dan wannan wata mafita ce da masalaha UBANGIJI ya kawo mana. Ban sanar
daku bane kawai amma tunda muka baro Abuja na dawo gidan nan a cikin cakwakiya ake da tashin hankali
duk kuma akan batun auren Maanal da Yazeed ne. Namayi mamaki da kikace yau kusan kwana biyar bai
leƙoku ba tunda yana Abujar shima.”
“Wlhy kuwa bai zoba Ammie, nama zata ko yana Kaduna ko yayi tafiya ne wani waje. Amma naga yana
ƙoƙarin kiranta a waya yaji lafiyarta. Wai Ammie miya faru ko ɗaura musu aure kukai? Ko har yanzu
Mamma ɗin ce ke tijarar bata son?”.
Ƴar dariya Ammien tayi da faɗin, “Kefa daɗina dake shirme Shahidah. Auren lafiya kuma yarinyata na a
wannan halin na ciwo mai girma irin wannan hauka nake zan bari a mata aure bada amincewarta ba. Akan
dai Hajiya Yaya ne da batun auren......”
Tsaf Ammie ta zayyanema Shahidah yanda komai ya faru da kuma matsayar da ake akai yanzu.
“Kai wannan mata ALLAH ya rabamu da masifarta Ammie. Ita dai ta sani mu ALLAH yasa haka shine
mafi alkairi ma, dan wlhy garama ta auri Rafeeq ɗin amma haɗata kishi da wannan ƴar iskar yarinyar
sangartacciya ai wani hatsarinne. Zasu iya haɗe kai su dinga cutar da ita watarana mu wayi gari zuciyar tata
ta buga. Amma kinga Rafeeq ɗin nan wlhy Ammie yana da hankali da tarbiyya. Damma Maanal ɗin ce taƙi
sakin jiki da shi kin dai san halinta”.
“Karki damu a hankali ne. Kudai ku cigaba da tayata da addu'a. Watarana ai sai labari. Amma in sha
ALLAHU batun Yazeed kam nima bana mata fatansa kuma suje can su ƙarata. Yanzu ki bani zuwa gobe zan
yi magana da Daddyn naku, idan ya tirje sai shi mijin naki ya masa magana ko naje Zaria na haɗashi da
abokin nasa.”
“Shike nan ma Ammie wlhy dama haka kikayi”.
“A'a bari dai na fara masa magana dan bana son butsutsunsa. Yaya jikin autar?”.
“Alhamdullahi Ammie jikinta na ƙyau sosai. Dan naga har ta koma karance-karance novels ɗin nata na
fama. Gata can ma tana shiri Abban Barru yace idan ya dawo zai kaita bookstore ta samo wasu”.
“To Masha ALLAH, ALLAH ya ƙara lafiya. Nima zan shigo na sake ganinta in sha ALLAHU zuwa next
week haka komai ya ƙara lafawa.”
“ALLAH ya kaimu Ammie muna nan muna jiranki. Itama Amal tace next week zata dawo”.
“To shike nan idan naga zai mana dai-dai sai kawai mu taho tare, amma ni ranar zan dawo gaskiya”.
“Kai Ammie miyasa bazaki kwana ba?”.
“Daga dubiya sai kawai na kama kwana. Tunda ina jinku kullum a waya ai Alhmdllh ya wadatar, ba kuma
sai na zauna na kula da tsohon mijina ba da ƙananun ƴaƴana”.
Dariya sosai Shahidah ta sanya. Daga haka sukai sallama....
___________★
Kamar yanda Ammie taima Shahidah alƙawari ta tunkari Daddy da batun aikin Maanal. Sai dai kuma
kamar fa yanda tai tunani ya nuna ɓacin ransa. Ya kuma tujareta da masifa dan dama yana riƙe da
takaicinsu ita da Hajiya Basariyya a rai. Kasa magana Ammie tai sai duƙar da kanta kawai tai tana
saurarensa. Sai da yay mai isarsa yay shiru dan kansa sannan ta tashi ta kwanta dan dama itace da shi a
yau ɗin. Wasu irin hawaye ne masu zafi suka dinga rige-rigen sakko mata. Sosai tausayin kanta dana
iyalanta ke ƙara girma a zuciyarta. A rayuwarta tayi farin ciki ne da samun ƴancin kai na shekarun ƙuruciya
kawai. Amma tun daga randa aka lulluɓa mata zanen aure zata iya cewa daga lokacin ƘADDARARTA ta fara.
Daga lokacin ta fara tantance gatan iyaye da ɗacin rabuwa da su. Daga lokacin komai ya canja, sunanta na
Asiya sarauniya ya canja zuwa Asiya baiwa. Eh dole tace bauta, duk da a zahiri baza'a kalli rayuwar tata ata
mai bauta ba kasancewar wasu abubuwa sun mata ado a bayyane. Sai dai wanda yasan ainahinta ne kawai
zai san minene mizanin bautar da take magana da ƴancin kai. Ansha gwagwarmaya na tsawon shekaru
kafin ALLAH ya iyakance, iyakancewar bai zama sauƙi ba kai tsaye, wata sabuwar jarabawar aka sake shiga,
ta yanda zaren ƙaddarar ne ya kawota a wannan matsayin da take a yanzu kuma. Bazatai butulci ma
UBANGIJI ba, domin kuwa Alhamdullah, ta samu canje-canje masu yawan gaske a sabuwar rayuwarta, sai
dai anan ɗin ma ta gamu da wata jarabawar rayuwa a cikin mugayen kishiyoyi da kansu kawai suka sani......
“Asia! Kuka kike yi?”.
Furucin Daddy ya katse mata tunaninta. Da sauri ta saka hannu cikin dabara ta share hawayenta, sannan
ta juyo garesa fuskarta da murmushi. “A'a Daddyn Hameed wane irin kuka kuma. Kawai dai na kwanta ne”.
“Humm Asia kenan, nasan kuka kike, kina kuka saboda kina ganin kamar na tauye hakkin ki dana
ƴaƴank.....”
“Ya arrahaman”. Ta faɗa da sauri tana mai gaggawar ɗaura tafin hannunta a saman bakinsa. Zuuuu
hawayen da take riƙewa suka shiga zirarowa. Kanta ta fara girgiza masa da sakin kukan gaba ɗaya. “Dan
ALLAH kada kace haka Daddyn Hameed, ban taɓa raba ɗayan biyu a tsakanin su Maanal da sauran yaranka
ba. Ni kaina inama mantawa bakai ka haifesu ba, saboda kana musu dukkan abinda uba kema ƴaƴa. Kana
musu abinda mahaifinsu ya gagara musu. Taya zan kasance butulu waje rarrabe gaskiya da akasinta. Dan
ALLAH ka gafarceni idan nayi kuskure, wlhy ban nema amincewarka ga Maanal tayi aiki dan baƙanta maka
rai ba ko ƙasƙantar da dokar ka b.....”
“Shiiiii!! Ya isa kukan haka to”.
Daddy ya faɗa yana mai jawota jikinsa ya rungume murmushi shimfiɗe a fuskarsa. A hankali yake shafa
bayanta cike da lallashi. Tsahon minti ɗaya kafin ya furta, “Nasani Asia. Na kuma yarda dake ɗari bisa ɗari.
Domin nasha gwadaki akan yaran nan batare da kin sani ba ke kanki kuma kina cinye jarabawar. Babu
abinda zance dake sai godiya. Domin tabbas a cikin matana kina gaba a wadda nake alfahari da ita. Bance
miki suma sauran sun gaza ba ko basu da martabar da nake kallonsu da ita ba. A'a ku dukanku kowa da
inda yake tausasa min da kuma inda yake tsaurara min, amma kina da manyan lambar yabo kashi-kashi a
gareni da bazasu lissafu ba Asia. Hakama su Shahidah, ni kaina biyayyarsu a gareni da girmamawa yakan
sani manta ma bani na haifesu ba, ina jin alfahari da su, ina kuma godema ALLAH daya bani su matsayin
ƴaƴana a yanzu. Ba aiki bane bana son Maanal tayi, domin nima na fahimci hakan zai taimaka mata ya
ɗauke mata kewa musamman da nima nasan harkar zane-zane hubby nata ne. Kawai dai ina jin haushinki
ne da tunanin baki son haɗa jini dani, shiyyasa yau ba fanshe haushin ta nan, sai nake ganin kamar baki
son wannan haɗin da nake sonyi ne Asia. Alhalin ni kuma na ƙwaɗaitu ƙwarai da gaske da son ganin jinina
ya sake gauraya da naki kozan cigaba da samun nagartattun zuria daga tsatsonki a cikin zuri'ata. Hakan zai
sake dunƙulemu ya curemu waje guda. Tun akan Amal naso nayi wannan haɗin, sai na fahimci hankalin
Yazeed akan Maanal yake shiyyasa na ƙwallafa raina a kanta.”
“Kayi haƙuri Daddyn Hameed sam ba haka bane kamar yanda kake tunani. Ka fahimceni dan ALLAH.
Wlhy koda bana aurenka zan iya bama Yazeed auren Maanal. Domin ya taimakemu a gaɓar da muke
matuƙar bukatar taimako. Zanma iya cewa ALLAH ya ƙaddara Manaal nada sauran kwana ne a duniya
amma ya saka sanadin hakan a hannun Yazeed. Domin da ace kwannata ya ƙare tun a randa muka fara
haɗuwa da sai dai wani zancen ake ba wannan ba. Dan haka ban taɓa jin bazan bama Yazeed Maanal ba.
Kawai dai hankalina na matuƙar tashi kasancewar bakowane ɓangare bane ke buƙatar wannan haɗin,
hakan kuma zai iya cutar da Yazeed ɗin kansa da ita kuma Maanal ɗin dake fama da rauni irin na ciwo mai
haɗari. Amma yanzu masalahar da aka samu zai taimaka komai ya zama dai-dai itama ta samu sassauci
haka shima Yazeed ɗin. Dan koba komai Hajiya Yaya mahaifiyace tana da tata darajar. Sannan Yazeed ya
san komai daya shafi rayuwar Maanal, basai anyi sabon zama da zagaye-zagayen faɗa masa da fargabar zai
amsheta ko zai canja ra'ayi”
“Hakane Asia. Na kuma fahimceki yanzu ɗari bisa ɗari. Zan kuma cigaba da addu'ar zaɓin ALLAH akan
al'amarin insha ALLAHU. Sannan abinda ya shafeta ki daina wani damun a kansa kanki ai ƙaddara ce, bata
wuce kan kowa ba kuma, ALLAH kuma shine shaida bataje takai kanta ba domin yin hakan jarabawace,
wanda ma suke aikatawa kai tsaye ko suke zuwa bariki su kama ɗakin kansu suke auruwa cikin salama da
kwanciyar hankali yanzu a ƙasar nan balle ita. Saboda haka na amince Maanal tayi aikinta. ALLAH ya sanya
albarka ya kuma sa hakane yafi alkairi.”
Wani irin daɗi ne ya ratsa zuciyar Ammie. Ta ƙanƙame Daddy da ƙyau tana amsawa da amin. Shima
murmushi ya saki mai faɗin gaske da karɓarta sosai ya rungume. A ransa kuwa yana sake ganin fara aikin
Maanal ɗin wata masalaha ce. Dan zai fake da shi bayan anyi auren suyi zamansu acan, ita kuma wannan
zaɓin uwar Yazeed ɗin anan cikin gidan yake son ta zauna tare da su saboda wasu dalilansa......
Wani irin farin ciki ne ya mamaye Maanal lokacin da saƙon Daddy ya risketa akan amincewarsa tayi
aiki. Su kansu su Shahidah sai da suka tsaya suna kallonta ganin yanda taketa murmushi yau kamar ba
Maanal ba. Sai suma hakan ya sakasu a farin ciki. A karo na farko na tarihi Maanal taima RK text massage
da albishir ɗin amincewar Daddy. Ai ba'a haɗa awa guda ba sai ga bawan ALLAH a gidan. Yau ko lallaɓatan
da Shahidah keyi na taje ta samu RK ɗin ba'ai ba. Yana kiranta yace gashi a gidan sai gata babu jimawa ta
fita. Tunda ta fito ya zuba mata ido, sai ya zam tana takune tamkar da bugawar zuciyarsa. ALLAH ya
jarabcesa da son wannan halittar ƙwarai da gaske. Yana kuma fatan mallakarta in har hakan shine alkairi a
garesu. Maanal ta tsani kallo, dan haka sai da ta masa tsogumi akan kallon ƙurillar da yake matan. Baice
komai ba face basarwa yana sakin murmushi. Itama sai ta sharesa kawai ta shiga gaishesa. Ya amsa mata
da kulawa, kafin ya ɗora da tambayar yanda abubuwa suka kasance. A taƙaice ta faɗa masa, bai damu ba
dan ya gama karantar ta zuwa yanzu. Bata da son yin doguwar magana sai idan itace taso hakan da kanta.
Shine ya dinga zuba mata zance da yanda abubuwa zasu kasance. Ya kuma tabbatar mata nan da kwana
biyu zaizo ya amshi takardunta. Ya kuma buƙaci ta ɗan zazzana wasu samples na agogunan zaizo ya amsa
gobe idan ALLAH ya kaimu dan zai sake nunama mai Companyn. Duk da dai ya nuna masa wanda ta zana a
asibiti. Ta tabbatar masa babu damuwa zatayi ɗin, daga haka sukai sallama ya fice ita kuma ta shiga gida.
Kamar ko yanda sukai alƙawari a wannan daren ta nutsu ta zana agoguna masu shegen ƙyau da ɗaukar
hankali fin kala goma. Dan har gabannin asuba tana wannan aikin. Hakan ya saka mata makara. Tana yin
sallar asubahi kuma ta sake kwanciya. Bata farka ba sai ɗaya saura. Ta samu RK yazo ya amshi zanen ma.
Dan sun sanar masa tana barci yace kada a tasheta a barta tai barcinta, a bashi zanen kawai. Yana kuwa
amsa bai jima ba ya wuce abinsa. Sai da ta tashi take jin yazo ɗin ya amsa. Har ta ɗauka waya kamar zata
kirashi sai kuma dai ta fasa kawai. Tata tsumayen nasa kiran amma shima sai bai kira ɗin ba har dare. Sai
da tana shirin kwanciya ne ma saƙonsa ya shigo.
_“Ina Kaduna yanzu haka. Mun gana da Daddy da Ammie, na kuma amso takardunki suna hannuna.
Amma sai da safe zan dawo Abuja in sha ALLAHU. Kiyi barci cikin aminci tare da mafarki mai nutsuwa
gimbiyar mata”_.
Baki kawai ta taɓe tare da jefa wayar saman gado ta cigaba da saka maɓallan rigar barcinta. Sai kuma ta
tsaya cak kalamansa na dawo mata. Ya gana da Daddy da Ammie kamar yaya? Kai itafa shishshigin mutum
nan ya fara bata tsoro. Kaji bala'i ko mi ya kaisa Kaduna?. Rashin mai bata amsa ya sakata jan ƙaramin tsaki
ta haye gadon kawai ta kwanta. Addu'a tayi kamar yanda ta saba sannan ta kashe wutar ɗakin tana sauke
ajiyar zuciya.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
2️⃣1️⃣2️⃣1️⃣
.......Maanal bata sake jin labarin RK ba tun ranar. Ya dai kirata washe gari yace ya dawo Abuja. Daga haka
bata sake jinsa ba. Gashi ita kuma ta ƙagu taji yaya ake ciki. Dan haka kawai sai ta ƙwallafa ranta a aikin
saboda zaman waje ɗayan kuma ya isheta. Da yaran Shahidah sun wuce makaranta itama da mijinta duk
aiki suke fita, sai ita sai mai aiki kawai. Bata da aiki sai karatun novels da kwanciya. Amma kasancewarta
sarkin kamewa da dakiya sai bazaka taɓa fahimtar hakan ba kai tsaye. Sati ɗaya dayin hakan sai ga Ammie
da Amal sunzo. Matuƙar farin ciki Maanal ta kasance a wannan ranar, gashi weekend ne duk masu gidan
suna nan. Yini sukai dan Ammie tace bazata kwana ba. Babu irin shagwaɓar da Maanal bataima Ammie
akan ta kwana ɗin ba amma tace sam ita bata sanarma Daddy zata kwana ba. Haka babu yanda zasuyi
bayan magrib suka rakasu train station kasancewar jirgin ƙasan zasu bi. Dama a cikinsa suka zo....
Kwanakin su Ammie biyar da zuwa da daddare tana shirin kwanciya sai ga kiran RK. Ido kawai ta
sakama wayar tana kallo harta tsinke sannan ta kauda kanta. Sake kira akayi nan ma kamar bazata ɗauka
ba sai kuma dai mita tuna oho mata tai yunƙurin ɗaukar, sai kuma taga bashi ɗin bane Ya Yazeed ne. Fuska
ta ɓata shima kamar bazata ɗaga ba ta dai daure ta ɗauka. Gaisheshi ta farayi da girmamawa kamar yanda
ta saba. Shi kuma ya amsa mata cikin nutsatstsiyar muryarsa dake nuna alamar a kwance yake. Sun ɗan yi
shiru sai kuma ya katse shirun da faɗin, “Ina muka kwana akan batunmu Maanal?”.
Shiru tai kamar bazatace komai ba. Sai da ta mula dan kanta ta amsa masa da, “Yaya ni mikake son nace
to. Ni duk abinda su Daddy suka yanke zanyi biyayya a kansa kawai”.
“Saboda dama baki sona?”.
“Ni dai Yaya bance ba. Amma ka tausaya mun mana. In dai kai namiji ka haƙura ka musu biyayya ni kuma
sai naje nace ba haka ba.”
“Humm shike nan, amma ke yanzu baki jin kishin na fara auren wata kafin ke?”.
Karan farko ta saki murmushi mai faɗi, sai kuma ta zame ta kwanta. “Yaya ko naji kishi yaya zanyi. Ni dan
ALLAH mubar ma maganar nan kawai ALLAH yasa haka shine yafi alkairi”.
Murmushi taji ya saki da ga can, sai kuma ya ce, “Okay shike nan an barta. Tunda dai na gane ana
kishina na gode”.
Shiru ta masa batace komai ba. Shima daga haka yay mata sallama akan maybe gobe ma ya shigo
Abujan, zai kuma leƙo ya fara ganinta kafin ya fara sabgoginsa. Daga haka sukai sallama. Kamar jira RK
yake dama, Yazeed yana yankewa kiransa na shigowa shi kuma. Sai yanzu ma ta lura ya mata kira yafi goma
ashe sanda take wayar. Kanta kawai ta ɗan girgiza. Sai da tana gab da zata tsinke sannan ta ɗaga. Muryarsa
a cinkushe ya mata sallama. Amsawa tai itama ciki-cikin tai shiru. Tsahon minti ɗaya babu wanda ya sake
magana.
“Oh bama zaki gaisheni ba?”.
RK ɗin ya faɗa daga can. Yitai kamar bazata tanka masa ba sai kuma ta ce, “Good evening”.
“Humm good evening to baturiya. Fatan kin yini lafiya?”.
“Lau”.
Itama ta amsa masa a daƙile jin yana mata magana cikin wani ji da kai.
“Humm! saboda kina waya da wannan tsohon tuzurun saurayin naki da baya dariya shine kika
shareni.”
Ita dariya ma zancen nasa ya bata. Amma sai bata dara ɗin ba ta ce, “Hummm ashe kaima tsohon
tuzurun ne tunda ba girmarka yay ba”.
“Oh zaki shigar masa faɗan ne kenan?”.
Shiru ta masa taƙi tankawa. Shima sai ya saki zancen kawai. Amma ransa fal kishin Yazeed ɗin. “Baki da
kirki ALLAH, kwana kusan goma baki jini ba amma baki neman ba. Wannan wace irin soyayya ce?”.
“Kai dai ka sani. Rashin jinka kuma ai nasan lafiya ce ke ɓuya”.
“Humm borin kunya, ALLAH dai ya shirya min ke. Duk da baki tambaya ba bara na faɗa miki. Auntyna ce
bata da lafiya a randa na dawo Kaduna da yamma jikin ya tsananta, dole mukai gaggawar barin ƙasar da
ita. Tashin hankali yasani manta wayar da number ɗinki ke ciki. Jiyan nan muke dawowa”.
A hankali Maanal ta sauke numfashi da faɗin, “ALLAH sarki, ALLAH ya bata lafiya yasa kaffara ne. A
wace anguwa take?”.
“Amin ya rabbi nagode sosai. Zakije dubata ne kike tambayar anguwarsu?”.
“Ina ruwanka to. Kai dai ka faɗa min mana”.
Murmushi yayi daga can har tana iya jin fitar sautinsa. Sai kuma ya ce, “Okay ba damuwa zan tura miki
address ɗin. Sai dai kuma yanzu ma na kiraki ne akan batun aikin can. Sun buƙaci ganinki, sai ki shirya gobe
idan ALLAH ya kaimu kamar around eleven thirty haka zanzo na ɗaukeki”.
Wani irin sanyi ne ya tsargama Maanal. Amma sai ta danne cikin dakewarta ta ce, “Miyyasa bazaka bani
address ɗin ba kawai naje da kaina”.
“Kina tsoron na saida ki ne?”.
“Ai nasan nafi ƙarfin siyarwa”.
“Hhhh haka dai kikace. Bari na barki ki kwanta lokacin barcinki na wucewa. Sai nazo”.
Daga haka ya yanke kiran kafin tace komai. Murmushi ta saki itama, ta jima da fahimtar bayan naci RK
ɗan rigima ne na bugawa a jarida. Sam daga ganinsa baya jin magana. Bazatace tana sonshi ba. Amma
wasu abubuwa nashi sun ɗan fara birgeta kaɗan. Fasa kwanciyar tayi, ta tashi ta ɗauro alwala ta hau
nafilfilin neman nasara da zaɓin alkairi akan wannan aiki. Duk da dai dama tunda aka tsira zancen taketa
gayama ALLAH. Tayi raka'a biyun farko ta sallame ta ɗauki wayarta ta turama Ammie text. Tasanta bata
wasa da ƙiyamullaili, kusan za'ace ma ita suka gado dan tun suna yara tai musu wannan horon na ibada.
Kuma Alhamdullah su dukansu sun horu da wannan tarbiyyar tata. Dama itace mai ɗan raunin cikinsu
lokacin tana a ganiyar rashin ji. Amma yanzu Alhamdullah kam komai ya sauya kamar yanda jiyanta ta
zama tarihi mai ciwo da raɗaɗin tunawa agareta.....
*_WASHE GARI_*
Da safe ta sanarma Shahidah da mijinta komai. Sun tayata murna da fatan alkairi suma. Ta kumayi waya
da Ammie da Daddy dan itace da shi jiya da yau. Hakama Amal. Bayan wucewar su Shahidah nasu ayyukan
itama tai nata shirin. Kasancewar ta mai jinkirin shiri yasa ten nayi ta fara shirin nata. Sai ya zam kafin
eleven ma tayi ta gama komai duk dama bawani shiri bane na'azo a gani. Amma tayi ƙyau sosai cikin Abaya
ƙirar saudia baƙa. Daga ciki ta saka wandon jeans blue mai duhu da farar riga datai mata ƙyau. Ɗan kwalin
abayar kawai tai rolling a kanta ta saka turare mara ƙarfi bayan na wuta da kayanta keyi dama jikinta gaba
ɗaya da yuni gyara yasa ƙamshi ya kama. Sai ƴan tarkacenta data haɗa a hand bag ɗinta sannan ta fito.
Kitchen ta shiga ta saka ruwa a ƙyaƙyƙyawar bottle water ɗinta ƴar zamani sai ta ɗan saka Linda ta daka
mata snacks da basa rabo da shi a gidan kaɗan wai ko taji yunwa. Dan ta tsani sayen abincin waje a
rayuwarta. Shiyyasa da wahala kaga Maanal ta fita anguwar data san zata yini babu wani abin ci a tare da
ita. Tun Ammie na faɗa har ta saka mata ido ma. Falo ta dawo ta zauna kasancewar akwai sauran mintuna
ashirin, sai kawai ta buɗe novel ɗinta ta cigaba da dubawa. Tanayi tana ɗan cin shawarma ɗinta guda ɗaya
data ɗakko da drink a kofi. Batafi mintuna goma a wajen ba kira ya shigo wayarta. Ƙaramin tsaki taja a
ranta tana addu'ar ALLAH yada ba Yazeed bane ba. Numfashi ta ɗan sauke ganin RK ne. Sai da ta kalla
agogo sannan ta ɗaga. Yau dai bai roƙaba ta gaishesa. Sai shi kuma batare daya amsa ba yace ta fito gashi a
waje. Sake kallon agogo tayi da mamaki ta ce, “Akwai fa sauran ten minutes”.
“Oh kona koma sai ya cika na dawo?”.
“Humm”. Ta faɗa kawai tana yanke wayar. Linda ta ƙwalama kira. Da sauri sai gata tana faɗin, “Yes Aunty
kina bukatar wani abu ne?”.
“No Linda zan wuce ne dai. Dan ALLAH ki kula sosai da gidan duk da dai nasan kina ƙoƙari dama. Ai
baki manta ba dai Didi tace kima Uncle tuwon shinkafa ko?”.
“Eh aunty ban manta ba har ma na ɗora”.
“Yauwa to yayi, sai su Barrah kuma kisaka musu white rise kin san bazasu ci tuwon nan ba. Tunda akwai
stew a fright kema kin huta kenan. Nima na wuce sai na dawo”.
“To aunty, ALLAH yasa ayi nasara. Amma ke baza'a miki komai ba?”.
“No Linda na huttashsheki kinji, bamma san ni sanda zan dawoba. Komai na dawo na samu a gidan zanci
bye”.
“Okay bye bye”.
Tunda ta fito ya wani zuba mata idanu ko ƙyaftawa bayayi kamar yanda ya saba. Bashi kaɗai ba kowa
na faɗa a zuciya ko'a fili Maanal ƴar gayu ce gata kuma ƙyaƙyƙyawa. Ko bada kwalliya ta saka kaya ba
zakaga sun mata ƙyau. Balle kuma ace tayi kwalliyar ai abin sai wanda ya gani. Gata dai ba fara ba, amma
da wahala namiji ya kalleta bai sake mata kallo na biyu ba duk ustazancinsa da kamewa. Badan tafi sauran
mata ƙyawu ko wani abu ba, a'a itama kamar kowacce mace take, kuma komai nata irin na kowacce mace
ne. Sai dai yanayinta na kamewa da ɗaure fuska kan taka musu birki wajen yimata magana ko fuskantarta
kai tsaye. Sam bata da sakewa da mutane, sannan bata da yawan fara'a ko magana sai a inda taso yi ko ga
wanda taso yimawa....
Sai da ta tsaya a gabansa ta ɗan yamutse fuskarta da babu walwala sam. Dan bata son kallo sam, ko
yaya ake kallonta takan tsargu taji a jikinta, shi kuma taka kallo ɗabi'arsa ce. Yanda take faman yamutse
fuskar da sake ɗaureta ya sakashi sakin murmushi da warware hannunsa daya harɗe a ƙirjinsa. Sai kuma ya
ɗan furzar da iska mai nauyi a bakinsa yana sake zuba mata idanun. “Wannan ɗaure fuskar fa? Ko duk
laifin rashin cikar lokacin ne?”.
Maimakon amsa masa zancen nasa sai kawai ta basar tace masa, “Ina kwana?”.
“To lafiya ba ƙalau ba”.
Kamar zata sharesa sai kuma ta ɗan kallesa. Fuska ya marairaice mata kamar wani ɗan yaro. Janye idanun
nata tai kawai. Shima sai ya saki murmushi. Ƙofar motar ta buɗe mata yana faɗin, “Bismillah”. Komai
batace da shi ba ta shiga. Shima ya zagaya nasa ɓangare ya shiga. Motar yayma key suka fice a gidan. Sai da
sukai ɗan nisa a tafiya ya kalleta kaɗan ya maida hankalinsa ga titi. “Nace miki ina lafiya amma ba Lau ba,
baki tambayeni mike damuna ba?”.
Hankalinta na'akan novel ɗinta ta amsa masa da, “Ai banga alamar ciwo a tare da kai ba. Nasan neman
maganarka ne”.
“Oh oh, ni Rafeeq bin Kasheem. Ni har wani neman maganane da ni kuma?”.
“Humm”.
Kawai tace a taƙaice. Shima sai ya murmusa yana mai jinjina miskilancin yarinyar nan. Bai sake cemata
komai ba sai zuwa can a bazata yaji tana ce da shi “Yaya jikin Aunty?”.
Har cikin rai yaji daɗi, dan haka ya amsa mata fuskarsa ƙawace da murmushi. “Jikin Aunty babba
Alhamdullah. Duk da dai yau ban leƙata ba sai zuwa anjima. Da ƙyar ma na kuɓuto kaina a asibiti dan na zo
na kaikin nan.”
“Ai sai da nace ka barni naje kawai”.
“Bazan iya hakan ba ai. Shi abu mai daraja killacesa ake. Kaffa-kaffa da shi kuma akeyi. Fatana ma na
samu na ɓarar da waccan gwamnatin data tare min ko'ina. Sai kuma nayi sakaci wasu ƴan bani na'iya su
shigo neman hanyar min kutse?. Ko baki yarda ba”.
“Kaima kasan mi kake nufi”.
“Ki rantse kema baki sani ba?”.
Shiru ta masa. Dan tama gaji da surutun. Yasa ko fahimtar labarin batayi ma. Sun iso katafaren comyanin
*_MAWAAD_* daya tsaru da gini na zamani. Gashi babba sosai ta yanda hasashenta bai taɓa hasaso mata
ba. Yanda aka tsara ƙaton harabar wajen da furanni koraye da jajaye harma da wasu kalolin abin
ƙayatarwa, ga kwalta lafiyayya shimfiɗe. Hatta ababen hawa na ma'aikata an fakasu ne cikin tsari da
birgewa. Bawani hauma-hauma ko hayaniya. Sai securitys dake kula da tsarin shiga da fitar kowa a wajen
hatta cikin harabar. Dole ne wajen ya birgeka, dan duk iyayin mutum idan yazo *_MAWAAD COMPANY_*
sai tsarinsa ya birgeka..........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
2️⃣2️⃣2️⃣2️⃣
.........“Ya kikaga companyn?”. RK ya katse mata tunaninta. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta saki tare da juyowa ta
ɗan kallesa. Ganin shima ita ɗin yake kallo sai ta ɗauke kanta kawai. Cikin ɗan yamutse fuska ta ce, “Balaifi
komansu da tsari gaskiya. Sai dai ina fatan ba ƙawar gini bace kawai”.
Dariya ya ɗan yi a taƙaice. Ya ce, “Maanal bari na baki a buɗe, Mawaad Company ko kamfanin Rolex
bazasu nuna masa yatsa ba a ɓangaren agogo. Basa ɗaukar ma'aikaci sai wanda yasan abinda yake yi.
Sannan babu zancen sai ɗan wane ko sanayya, akwai turawa ma'aikata anan tun daga Chinese harma da
Europe da sauran ƙasashen baƙaƙen fata. Komansu da ƙa'ida da doka yake tafiya. Kayansu ba kayan yara
bane, manyan sarakuna da attajirai ke iya sayen kayansu a kowacce kusurwa ta duniya, tunda kikaga
turawan nan da larabawa na tururuwar amfani da agogunan Mawaad ai ba sai na cigaba da cewa komai
ba. Barama dai na daina cewa komai, ke da kanki zakizo kina bani labari watarana in sha ALLAHU. Abinda
nake so dake dai ki nutsu wajen interview nan. Dan harda boss ɗin companyn da kansa za ai miki ita, ina
nufin CEO na companyn. Duk da dai nasan banda matsala dake in sha ALLAHU. ALLAH ya bada sa'a da
nasara idan alkairi ne. Muje na rakaki har ciki. Zan jiraki har ki kammala sai muje ki duba Aunty babba ko?”.
“A'a ka koma wajen aikinka kawai ba damuwa. Idan na gama zan koma da kaina. Tunda bamu san
yanda abin zai kasance ba. Duba Aunty kuma basai ka kaini ba zanje da kaina ne”.
“Hummm” ya faɗa fuskarsa ɗauke da murmushi. Daga haka suka fito a tare. Idan ka gansu dolene su
birgeka matuƙa. Dan sun dace da juna. A jere suke tafiya cikin tsari da nutsuwa. Dan shima RK dai-daita
tafiyar tasa yay data Maanal duk da kasancewarta mai sanyin tafiya da tsantsar nutsuwar iya taku. Sam
bata da hauma-hauma ko garaje a tafiya ita. Sun tsaya a haɗaɗɗiyar ƙofar wajen data kasance ta zallar
gilashi, koda yake bama ƙofarba shi kansa ginin akwai gilashi sosai a cikinsa shiyyasa ya zauna da ƙyau
kaikace ba'a Nigeria kake ba a wata Chaina ce can dan sune mayu. Sai dai kuma a cikin Abuja wannan ba
komai bane kasancewar akwai gine-gine na ƙawa da ƙasaita da sukafi Mawaad Company komai ma. Duk da
sanin da securitys ɗin ƙofar sukaima RK sai da ya saka I'd card ɗin aikinsa akan wani computer sannan ƙofar
ta buɗe masa da kanta. Ya gaisa da securitys ɗin idanunsa akan Maanal datai kicin-kicin da fuska. Juyawa
yay ya musu ɗan taƙaitaccen bayani a kanta. Cikin gamsuwa suka shiga jinjina masa kai...
(Eh lallai ashe kallo na daga ciki) cewar Maanal a zuciya. Dan kuwa tabbas Companyn nan ya ginu da
iya nasa tsarin da ƙawa. Sun fara iske reseption, anan suka tsaya suka saka sunansu sukai signing kamar
yanda tsarin Companyn yake ga baƙo ga ma'aikaci, kafin ma'aikatan dake a floor na farko, zamu iya cewa
wani department ne anan na sashen Companyn, duk sun duƙufa aiki, yayinda wasu ke faman kai kawo da
uzirin gabansu daya shafi aiki. Tunda suka shigo wasu ke kallonsu, wasu na zungurar wanda basu gani ba,
yayinda wasu ke ƙuskus, wanda ke ɗan kusa da su kuma na gaishesu. RK kaɗai ke amsawa, Maanal kan ɗan
jinjina kanta kawai itadai tana mai kallon komai. Daga haka suka isa ga elevator, shi ya danna ta buɗe, ya
mata nunin ta fara shiga sannan shima ya shiga. Shine ya sake daddana number floor ɗin da zasuje sannan
ya matso kusa da ita yana magana a hankali. “Kin fara ganin yanda tsarin yake ba?”.
Maimakon amsa masa da baki sai ta ce masa, “Uhmm”. Kawai, dai-dai nan suka iso inda suke son zuwa.
Sai da ta gama buɗewa suka fito. Sun samu matashiyar budurwa ɗauke da files a hannu zata shiga elevator
ɗin. Tana ganin RK ta saki ɗan murmushi da faɗin, “A'a ashe shiyyasa yau garin kamar da hadari, ashe
babban baƙo ne damu a Mawaad”.
Murmushi yay mata da amsa mata da, “Kedai masheranciya ce Labibah. Ykk ya aikin?”.
“Babu wani sharri sai gaskiya. Aiki gashi nan muna ciki. Nikuma ina lafiya”.
“To Masha ALLAH. Iji dai boss na nan?”.
“Humm zaune kuwa. Kasan baya wasa ai sai da dalili ko zai leƙa office ɗin gwamnati. Yanzu naga ya dawo
dan ya shigo da safe sai kuma ya fita.”
“Okay, to bari mu ƙarasa”.
“Babu damuwa. Sis.. barka tunda shi ya kasa gabatar min dake”.
Karan farko Maanal data ɗauke kai daga garesu ta ɗan juyo ta kalleta. Hannu ta bata kawai alamar suyi
musabaha batare da tace komai ba. Sai shine ya ce, “Labibah bazaki taɓa canjawa ba. Da kinyi haƙuri ai
zanzo da ita har office ɗinki ne idan na gama da boss”.
“Ato shike nan babu damuwa kuje. Nima zanje office ɗin CMO ne”.
“Okay tom ba damuwa sai mun fito”.
Daga haka ta saki hannun Maanal ta shige elevator ɗin su kuma suka wuce. Office ɗin Assistant ɗinsa
shine farko kafin na boss dake ciki. Ya tarbesu da girmamawa alamar akwai sanayya tsakaninsa da RK ɗin
sosai. Dan RK ɗin yata tsokanarsa kafin yace masa bari ya sanarma boss ɗin zuwansu. Ita dai Maanal
hankalinta ma nakan ɗan bin Office ɗin da kallo. Komai tsaf kuma ƙal babu wani tarkace ko hayaniya. Baifi
mintuna huɗu ba ya fito yana sanarma RK oga yace ya shiga shi kaɗai. Murmushi kawai RK yay da ɗan
girgiza kansa. Kafin ya matsa inda Maanal take zaune dan shi dama yana daga tsaye ne.
“Kinga ina zuwa. Minti biyar kawai”.
Kanta ta jinjina masa batare da nuna damuwar da yay tsoro ko ɓacin rai daga fuskarta ba. Daga haka ya
wuce ita kuma ta ciro novel ɗinta daga bag ta cigaba da karatunta. Shima Assistant ɗin barin Office ɗin yay
da alama akwai inda zaije. Kusan mintina huɗu sai gashi ya dawo. Mazauninsa ya koma ya zauna bayan ya
ajiyema Maanal ruwa da lemo. Baice mata komai ba itama batama kulashi ba balle kallon abinda ta ajiye.
Tana nan a zaune fin mintuna goma sannan RK ya fito. Zama yay a kusa da ita yana bata haƙurin
daɗewarsa. Cikin nuna rashin damuwa ta ce, “Ba komai”. Ta maita hankalinta ga book ɗinta. Shima dai
wayarsa aka kira, dan haka ya miƙe ya fita aka sake barinta ita da Assistant. Suna nan a haka wani ɗan abu
dake desk ɗinsa yay ƙara, miƙewa taga yayi ya nufi hanyar officer ɗin ogan kamar yanda suka faɗa. Bai wani
jima ba ya dawo, cikin mutuntawa yace mata ta taso suje. Littafinta ta saka a bag ta miƙe batare da tace
dashi komai ba. Ta wani elevator ba wanda suka shigo ita da RK ba suka shiga da Assistant ɗin, cikin
sakanni ya saukesu inda suka nufa, koda suka fito nan ma sai taga offices ne a wajen. Sun shiga wani waje
da alama ta nuna conference room ne, sai dai bai ƙarasa da ita can ciki ba ya nuna mata wajen zaman daga
nan ta inda aka shirya kamar masauƙin baƙi. Tana zama wata ta kawo kofin coffee ta ajiye mata da drink.
Atare suka bar wajen ita da Assistant ɗin sai ita kaɗai kenan. Babu abinda ta taɓa ta sake ciro novel ɗinta ta
cigaba da karatu......
Fin tsahon mintuna talatin tana a wajen babu wanda ya sake zuwa, har ranta ya ɗan fara sosuwa sai ga
wasu mutane uku sunzo sun gittata sun shiga conference room ɗin, tsakanin inda suka bin da inda take
akwai ƴar tazara, shiyyasa bata wani shaida kowa ba. Bayan shigewarsu fin mintuna biyar wasu biyu suka
sake wucewa, kasancewar bata ɗago ba a yanzu sai da suka gama shigewa taji motsin rufe ƙofa. Ƴan
mintuna kaɗan Assistant ya zo wajenta yace ta shiga. Kanta kawai ta jinjina masa tare da maida book ɗinta
a bag ta miƙe. A ranta tana mamakin wannan abu kamar wulaƙanci, ana tattalin ɗaukar ma'aikaci da alama
su nan yanga sukeyi. Da wannan tunanin ta tura glass door ɗin a hankali ta shiga da sallamar da bata
tunanin zasuma iya jinta saboda yanda ta yi ta ciki-ciki, dan wani irin bugawa ziciyarta ke mata da sauri-
sauri da batasan dalili ba, amma haka ta danne tana ƙarama zuciyar tata ƙarfi. Sai dai kuma da alama sun ji
sallamar tata ɗin, dan wasu a cikinsu sun amsa. Taji hakan ne a bayyane dan ba kallonsu take ba su duka.
Sai da ɗaya a cikinsu ya furta, “Bismillah zaki iya zama”. Sannan ta ɗan ɗago ta kallesu tana mai jinjina
kanta zuciyar tata dai na cigaba da bugu.
Mutane ukun dake fuskantar inda zata zauna kawai ta iya ma kallo cikin sakan biyu. Wanda ke zaune
kuma a kujerar dake gefen inda take bata ko kallesu ba. Sai kujerar dake tabbatar da oga kan zauna yayin
meeting shima bata wani dubesa ba. Shima kuma kansa a duƙufe yake yana duba wani magazine kamar
ma bai san da zaman kowa ba a wajen. Kujera ɗaya taja ta zauna zuciyarta na mamakin ai mutane biyar
kawai taga sun shigo, ya akai taga kusan takwas anan?, rashin mai bata amsa ya sata shiga gaidasu. Amsa
mata duk sukayi, sai dai bata jin shi wancan ya amsa ɗin. Shiru kamar na mintuna biyu kafin ɗaya a cikinsu
ya fara mata tambaya. Babu ko ɗar a tare da ita ta amsa masa. Kansa ya jinjina sosai dukansu suna
mamakin ta. Wanda ke tsakkiyar sa shima ya sake jeho mata tasa tambayar. Nan ma ta sake amsawa babu
ko wani ɗar. Dukansu kam sai da suka sake dubanta wannan karon saboda jarumtarta da kaifin basira da
suke kallo a bayyane, sai dai abinda basu sani ba dannewa kawai takeyi, dan tana cikin wani hali da ita
kanta ta gagara bashi fassara. Gashi a masu mata interview ba wai baƙaƙenmu bane balle ma ace hausawa.
Hausawa biyu ne ma kawai a cikinsu sai CEO ɗin da har yanzu bataga fuskarsa ba. Amma dai hannunsa
dake saƙale da wani shegen Designer agogo da zoben dake neman harmutsa tunaninta na azurfa ya nuna
bakin fata ne duk da kallon fisha tai masa kawai.
Na ukunne da baice komai ba tun ɗazun a yanzu cikin turancinsa mai fita da harshen Chinese ya furta
“Woow, You are amazing young lady”. Sai kuma ya shiga tafa mata. Suma sauran tafa matan suka farayi
suna mai kallon boss ɗin nasu da har yanzu bai tanka ba baima maida hankalinsa a kansu ba yanata duba
magazine ɗinsa hankali kwance. Ganin dai bashi da niyyar kulasu suka haƙura suka daina. Sun bata takarda
da kayan aiki tai zanen agogo a take anan, zanen da yay mugun basu mamaki da ƙaryatar dasu. Daga haka
File suka tura mata da mata bayanin zata cike tai singing a take anan. Bata musa ba taja file ɗin gabanta. Ta
ɗan dudduba abinda ke cikinsa kafin ta shiga gudanar da dukkan abinda suka buƙata zuciyarta na mata
wani irin sanyi ƙalau dan kuwa dai sun tabbatar mata da ɗaukarta aiki ne. Acan ƙasan ranta kuwa tana
mamakin nasu tsarin. Daga interview a take a wajen kuma babu batun kaje ka jira sai a tabbatar maka da
an ɗaukeka aiki. Haka dai ta gama cike komai tana zancen zucinta ta basu. Bayan sun dudduba suka
miƙama ogan nasu da sai a yanzu ya ajiye magazine ɗin ya fara duba file ɗin.
A karo na farko oga kwata-kwata da yay kamar bashi nan a wajen ya ɗago kansa bayan kammala duba
komai na file ɗin, cikin wani irin dakewar murya ya jeho mata tasa tambayar data tilastata kallonsa. A
yanzu ba bugun zuciya kawai taji ba, zuciyar tatace gaba ɗaya zata iya cewa ta tarwatse a dalilin kallon ido
cikin ido da sukaima juna. Suma, ɗaukewar numfashi, ko gushewar hankali ko tsatstsagewar zuciya batasan
yanda zata kira yanayin data tsinta kanta a wannan lokacin ba ma.........✍️
_Tofa jama'a mi kuma ke shirin faruwa anan?. CEO na Mawaad Company da Maanal? Kumuje zuwa
wasan na ainahi ma yanzun ne zai fara a duka ɓangarorin😆 in sha ALLAHU 😉_.
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
2️⃣3️⃣2️⃣3️⃣
........Fin mintuna biyu sunama juna kallon tsakkiyar idanu babu ko ƙyaftawa, yayinda sauran sukai kasare
suma suna kallonsu da mamaki. Da wani irin shegen salo CEO ɗin nasu ya juya mayan oily ayes ɗinsa masu
matuƙar haske kamar madara dake cikin haɗaɗɗen siririn farin gilashi tas tare da kauda fuskarsa gefe yana
mai furzar da wani irin huci. Sai kuma ya sake dawo da idanun nasa a kanta cike da barazana da isa da
basarwa ya furta, “Miss Maanal! Answer my question”.
Duk da cikin nutsuwa da sassanyar murya yay furucin, sai Maanal ta dinga jin kalaman ɗaya bayan ɗaya
suna mata wani irin amsa kuwwa da tartsatsi a cikin kunne, acan kuma sama ƙololuwa. Ga wani irin sanyi
yana saukar mata a gaɓan jiki da ƙasusuwanta tamkar yanayin yammaci ko safiya a lokacin tsananin
hunturu irin na ƙarshem Janairu ɗin nan.
“You are not serious Miss Maanal”. Ya faɗa cikin gizago da nutsatstsen sauti mai cike da aji yana mai
ɗan buga desk ɗin da yatsunsa biyu. Firgigit Maanal ta dawo a hayyacinta tamkar wadda aka farkar da ga
barci. Sai dai har yanzu sanyin nan na cigaba da ratsata tun daga saman kai har yatsun ƙafafu. Sam bata
san ta yanda akai ta buɗe lips ɗinta cikin dakiya da tarin nutsuwa ta bashi amsar tambayar tasa ba. Har
lokacin kuma idanunsu na a cikin na juna. A karo na biyu shine ya sake kauda kansa. Sai kuma ya ɗan
yamutse fuska da ɗaureta yana maida hankalinsa a kan sauran da sukai jugum-jugum suna kallon ikon
ALLAH. Duk da kuwa wannan ba sabon abu bane a wajensu. Ƴammata da yawa a cikin Companyn nan sun
jima da mutuwa akan boss ɗin nasu. Hakama masu shigowa domin bussines suka shiga fiye da irin yanayin
da Maanal ta tsinta kanta a yanzu. Bakuma wai dan ogan nasu yafi sauran maza bane, badan yafi kowa
ƙyau da iya ado bane, badan yafi kowa dukiya da cikar kamala bane. Kawai dai ALLAH ya bashi farin jini da
wani irin kwarjini da ko su kansu mazan yana cika musu waje duk da kasancewarsa yaro matashi da bai
wuce 30+ ba a duniya. Boss ɗinsu nada wasu qualities da mata da yawa ke buƙata a tattare da mazan
zamani na wannan ƙarni. Duk da dakewarsa da kamewa da ƙasaita hakan bai hana ƴammata kawo masa
hari ta kowacce kusurwa ba. Koda yake kuɗi fa babu abinda basa saka matan wannan zamanin, kai Bama
mata ba kowafa a wannan ƙarnin ya koma girmama matsayin bawa da abinda ke a hannunsa ne kawai. Sai
kana motsi akeyi da kai, sai ka zama wani ake girmamaka da son raɓarka. Da zarar baka dasu ko sun bar
hannunka sai kaga kowa ma ya janye jikinsa an zubar da kai a kwandon shara saboda dama can ana maka
soyayya da girmamawar ne saboda kana amsa sunan wane....
Miƙewarsa ta saka tunaninsu katsewa. Document ɗin ya tura gabansu tare da miƙewa da ƙyau yana
haɗe rigar suit ɗinsa ya saka botirin dake jikinta ƙwaya ɗaya tak. Batare da ya sake kallon inda Maanal take
ba ya nufi hanyar fita yana faɗin, “Zata fara aiki damu gobe in sha ALLAH”.
Daga haka ya fice abinsa cike da takun mazantaka da ƙasaita har ma da gayu na matasan samarin
wannan zamanin musamman irinsa da ke ji da kansu da MANDA A GIDAN SANYI😉😂....
___________★
A lokacin da anan Maanal ke Maawad company domin yin interview acan Kaduna su Daddy ne ke shirin
miƙa kuɗin auren Yazeed ga mahaifin Nazeefa ɗiyar Aunty Sabuwa saboda matsawar Hajiya Yaya akan
al'amarin. Ganin abin na neman zama wata fitinar kuma a tsakaninsu Ammie ta saka baki tanata roƙon
Daddy dan yace shifa sai ƙarshen shekara. Da ƙyar dai ya amince za'a kai ɗin bayan ita kanta Ammien ya
gaya mata baƙar magana. Duk da abin yay mata zafi sai tai murmushi kawai ta ƙyalesa.
An kai kuɗi inda suka samu tarba ta musamman kamar wasu bare. Dan abin har mamaki ya bama
Daddy ɗin. Amma dai sai ya danne kawai akai gaisuwar mutunci. Dana shi ne da amininsa Alhaji Sunusi na
Zaria. Sai maƙwafcinsa Alhaji Isa da wani abokinsa Alhaji Sulaiman. Abinda ya sake ɗaure musu kai ana
maganar tsaida date caraf mahaifin Nazeefa yace ai wata ɗaya ma ya isa. Dan shi a shirye yake dama.
Kallon kallo aka koma yi a tsakanin su Daddy, sai dai babu wanda yace komai sai Alhaji Isa ne ya ce, “Amma
Alhaji kodai a ɗan ƙara, ko kuma shi Alhaji Usman ɗin aji ta nashi ɓangaren”.
Caraf yace, “Alhaji bazaka gane ba, yanzu idan ƴarka ta samu miji ba'a sanya wlhy, mu da Alhaji Usman
ai duk ɗaya ne. Kawai a taimakeni ayi a hakan, kai ko auren ne a ɗaura to daga baya sai ayi bikin”.
Rasama abin cewa sukai su duka. Sai Daddy ne ya ɗan girgiza kansa kawai. Sai kuma ya gyara zamansa
tare da faɗin, “Shike nan ALLAH yasa haka shine mafi alkairi. Amma bayan wannan ɗin shi yaron akwai
wata kuma, itama idan anyi an gama kamar nan da watanni biyar haka sai ayi nata. Naso ma ayi gaba ɗaya
ne a huta sai kuma larura ta gitta, to shi ciwo ya wuce komai a rayuwa shiyyasa aka ɗan ɗaga natan za'a
fara shi wannan ɗin”.
Ɗan jimm Baban Nazeefar yayi, sai kuma zuwa can ya saki guntun murmushi da faɗin, “Babu damuwa
Alhaji Usman, ai duka gidane tunda itama ɗin dai ta gida ce. ALLAH ya kaimu lokacin”.
Da amin duk suka amsa baki ɗaya. Daga haka suka ƙarasa abinda ya rage aka bar saka rana a matsayin
wata biyu ɗin.
Suna fita a gidan Aunty Sabuwa dake laɓe ta afko falon, rungume mijin nata tayi cike da farin ciki, shima
sai yay murmushi a ransa yana faɗin (wannan farin cikin nawane ba naki ba Sabuwa, dan lokaci yayi da zan
maidama Alhaji Usman martani, lokaci yayi da zan ƙwaci abinda ya hanani a baya da ƙarfin tuwo. Lokaci
yayi da wasan na gaskiya zai fara tsakanina da shi....)
_Tofa masu karatu, shin mike a tsakanin Alhaji Badaru mahaifin Nazeefa da Daddy kuma?. Ku dai kumuje
zuwa mutanena_😋
___________★
“Wai hawayen nan basu isa haka ba ne Maanal? Tunda muka taho kike sharar hawaye inata magana
kinƙi cewa komai. Kin san kuwa yanda zuciyata ke ɗagawa da wannan yanayin naki. Please! Tell me! Is
something bothering you? Wani abu suka faɗa miki mara daɗi ne? Ko basu ɗaukeki aikin bane sukace?”.
Yanzun ma komai ƙin cewa da shi tayi, sai hankalinsa ya ƙara tashi matuƙa. A haka suka iso gidan
Shahidah. Ko parking kuma bai gama yi ba ta buɗe motar ta fita, shima saurin fitowar yayi sai dai harta
shige abinta cikin sassarfa da ɗan gudu-gudu. Hankalinsa ne ya sake tashi, sai kuma ya rasa inama ya
kamata ya kama. Kamar zai bita sai kuma ya dakata. Yayi hakan yafi sau uku sai kuma ya koma cikin motar
da sauri ya mata key ya bar gidan. Wani irin gudu ya dinga shararawa daya kawosa Mawaad Company cikin
ƙanƙanin lokaci. Yana shiga kai tsaye office ɗin Boss ɗin ya nufa. Ko jiran Assistant ɗinsa ya masa iso baima
yi ba yanzu. AS ɗin ne ya biyosa yana ƙoƙarin tsaida shi da sanar masa Boss yace kada abar kowa ya sake
shigo masa sai in har shine ya buƙata amma sam RK bai sauraresa ɗin ba ya afka Office ɗin kansa tsaye cike
da fushi kuma.
Shi dai shi kuma ƙoƙarin sake sanarma RK yake yi cikin damuwa da tashin hankali, dan tunda yake aiki a
ƙarƙashin ogansa bai taɓa ganinsa a wannan yanayin na yau daya gansa ya fito daga conference room ba.
Ya kuma tabbatar ba ƙaramin abu bane zai sakashi cewa kada abar kowa ya shigo inda yake ɗin.
Daga shigowar RK harta AS ɗin nasa da abinda yake ƙoƙarin faɗama RK ɗin duk a kunnensa ne, dan yana
tsaye jikin ƙaton ƙayataccen gilashin da akai ma kusan kowanne bango na Companyn gaba ɗaya ado da shi
hannayensa duka biyu a cikin aljihun suke ya zubama harabar wajen Companyn idanu koma ace ƙayatattun
gine-ginen birnin na Abuja. Sai da ya basu kusan mintuna uku kafin ya ɗan juyo kamar mai fama da ciwon
wuya ya zuba musu ido su duka biyun, sai kuma ya wani watsa musu ɗan iskan kallo ya ɗauke kansa..
Hakan yasa AS ƙoƙarin fara kare kansa cikin rawar murya da damuwa. Amma sai yay masa alamar yaje da
yatsunsa biyu cike da salo. Kai AS ɗin ya jinjina masa cike da girmamawa yana mai haɗiye abinda yaso
faɗar. Koda ya fice ya rufe musu ƙofar sake maida kansa yay ga kallon wajen batare da yayi magana ba
kamar yanda shima RK ɗin baiyi magana ba har lokacin.
Iska mai ƙarfin gaske RK yay wani irin fesarwa ta alamar tsantsar takaici. Sai kuma ya sake takowa cikin
Office ɗin sosai har inda yake shima ya tsaya kamar yanda yake a tsayen, batare daya kallesa ba ya furta,
“Miyasa tun farko ka yarda zaka ɗauketa aiki cikin girmamawa da darajtawa! Amma ka saɓa hakan? Kasan
matsayinta a wajena kuwa AA!?”.
Idanunsa da suka kaɗa sosai ya lumshe. Sai kuma ya saki wani ɗan siririn tsaki mai ɗan sautin da har
RK ɗin yaji. Shiru na tsawon mintuna fin huɗu har RK ɗin daya sake ƙuluwa da haushi ya fidda ran amsawar
tasa sai kuma ya ɗan karkato da kansa ya duba RK ɗin. Shima juyowar yay ya kallesa sukaima juna kallon
ido cikin ido kowanne ƙwayar idanunsa na bama ɗan uwansa dai-dai da amsar da yake buƙata ko nemar
mata fassara da fashin baƙi. AA ɗin ne ya fara janyewa yana sake sakin wani lalataccen murmushi a karo na
farko mai kama dana rainin hankali ko tsantsar takaici. Sai kuma ya maida fuskarsa ya tsuke tamkar ba
shiba, a dakensa a kuma karo na farko cikin muryarsa mai zurfi da amo ƙasa-ƙasa ya furta, “Calm down
first, let's talk when you're ready. Right now I need to be alone”.
Wani irin zuba masa ido RK yay cikin takaici, sai kuma ya saki murmushi mai ciwo shima daya sake
bayyana tsantsar bacin ransa. Juyawa yay yana kallon AA ɗin daya sake maida hankalinsa gaba ɗaya ga
kallon garin. Taunar lips ɗinsa ya shiga yi da ƙarfi kafin ya juya ya fita a Office ɗin batare da ya sake cewa
koman ba. A yanda ya ɗan bugo ƙofar ya sake saka AA lumshe idanunsa daga inda yake bai kuma juyo ba.
RK daya fita baiko kalla AS ba ya shige elevator. Har zai danna sai kuma ya fasa ya fito. Dogon hanya ɗin
yabi sai gashi ya fito wani wajen da jerin Offices duke har kusan guda biyar. Office na biyu yay knocking. Kai
tsaye aka bashi izinin shiga dan duk wanda ke'a cikin Office ɗin yana kallonsa ta hanyar camara. Ɗaya daga
cikin wanda sukama Maanal interview ne. Fuskarsa ƙawance da murmushin daya bama RK ɗin mamaki ya
tarbesa. Bayan ya nuna masa wajen zama zai miƙe ɗauka masa wani abun ya dakatar da shi.
“Director Mustapha thanks you basai ka kawo komai ba muyi magana kawai mana”.
“To ALLAH yasa dai lafiya?”.
Director Mustapha ya faɗa yana komawa ya zauna a mazauninsa.
“I'm sorry nasan dokane a companyn nan abinda zan tambayeka. Amma ina neman alfarmar sani ne
sakamakon wani dalili mai ƙarfi. Please yarinyar nan da kukama interview yanzu wani abu ya faru da ita ne
a wajenku ko aikin ne bata samu ba?”.
Ajiyar zuciya mai haɗe da murmushi Designer Director Mustapha ya saki, sai kuma ya girgiza kansa. “No
Doctor babu wani abu daya faru gaskiya. Hasalima an bata aikin dan har CEO ya bata damar fara zuwa
gobe idan ALLAH ya kaimu. Yanzun nan R&D Director ya fita anan na gama bashi list ɗin abinda office ɗin
ta zai buƙata a yau komai za'a gama haɗa mata shi. Shin wani abu ya faru ne?”.
“No! No! Babu wani abu daya faru. Nagode sosai”.
“Ai babu zancen godiya a tsakaninmu, yarinyar ta cancanci samun aikin dan gaskiya she is very smart and
amazing because she demonstrated excellent problem-solving skills and an innovative approach during
the interview. Tunda kaga babu wani ja'inja Boss ya bata dama da wuri haka ai kasan bata wasa bace. Haka
muma kowa ya gamsu da brain ɗinta wlhy”.
Murmushi RK ya masa cikin jinjina kai, sai kuma ya miƙa masa hannu yana miƙewa da faɗin, “Thanks
you Director”
“No worries doctor. I am on my job”.
Daga haka yay masa sallama ya fito a office ɗin dukkan damuwarsa da AA ya dasa masa na guduwa daga
cikin ƙirjinsa. Sai dai kuma hankalinsa nakan dalilin halin da Maanal ɗin ta shiga........✍️
_Tofa ƙaƙa raƙa ƙaƙa. Shin minene alaƙar Maanal da AA?, sannan minene alaƙar RK da AA kuma. Dan
tabbas alamu sun nuna akwai sanayya mai ƙarfin gaske a tsakaninsu. Hhhh badaƙala kenan, mi kike son
ji?😂 Ga wuri ga waina. To kawai mu haɗe a comments section 🤣🤣🤣🤣🏃._
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
2️⃣4️⃣2️⃣4️⃣
.........Wata irin ajiyar zuciya director Mustapha ya saki. Sai kuma ya saki murmushi a ransa yana mamakin
kansa da ɓoyema Doctor Rafeeq ɗin sauran gaskiyar abinda ya faru da yay... Kirane ya shigo daga landline
ɗin office ɗin, ganin daga office ɗin CEO ne ya sashi saurin ɗagawa. AS ne ya sanar masa CEO na buƙatar
ganinsa yanzun nan, kuma ya taho da file ɗin sabuwar staff ɗinsu. Bai wani tsaya wasa ba ya miƙe yana
dariya. A fili ya furta, “Anya babu wata a ƙasa akan yarinyar nan kuwa? To madai ji ma gani wai an binne
tsohuwa da ranta”.
Sai da AS ya shiga yay masa iso sannan ya shiga. A yanzu kam AA ɗin na zaune ne a kujerarsa ta aiki
saɓanin a yanda RK ya samesa ya kuma barshi. Gaisuwa Director Mustapha ya miƙa daga tsayen batare
daya zauna ba. Shima AA ɗin da hankalinsa ke kan computern desk ɗin batare daya amsa ba yay masa nuni
da vesitors chair ɗin gaban desk ɗin kawai. Zama yay, kafin cikin girmamawa ya ce, “Gani Sir. Dama ina
ƙoƙarin ƙarasa haɗa komai ne na kawo sai kuma ga kiran AS akan kana son ganina”.
Shiru bai amsa masa ba, yanata aikin gabansa kawai har lokacin hankalinsa nakan screen ɗin computer
ɗin, sai da yaja kusan mintuna uku kafin ya ajiye tare da maido hankalinsa kan Director Mustapha ɗin. “Am
sorry ina wani abune”. Ya faɗa cikin muryarsa mai zurfi. Da sauri Director Mustapha ya ce, “Babu komai
Sir”.
Kansa kawai ya jinjina masa. Sai kuma ya miƙa masa hannu alamar ya basa file ɗin. Miƙa masa yay da
sauri cikin girmamawa. Yayinda shi kuma ya shiga buɗesa yana duba komai daki-daki. Sai zuwa can ya ɗan
ɗago. “Baku ƙarasa bane?”.
“Eh sir! Saboda kana fita itama ta miƙe ta fice muna ƙoƙarin tsaidata amma bata sauraremu ba. Mun
cigaba da abinda ya dace ne kawai saboda ka bada umarnin hakan. Dan mu harma mun fara tunanin ko
tanada wani c......”
Muƙutt ya haɗiye zancen saboda wani shegen kallo da AA ɗin ya jefa masa. Sai kuma ya duƙar da kansa
yana shashshafa ƙeya. Shiru office ɗin ya ɗauka na kusan minti biyu kafin yay masa nuni da hannu alamar
yaje. Miƙewa yay tare da ɗan rissinawa na girmamawa sannan ya fice a office ɗin.....
Duk yanda yaso cigaba da aikin zuwa lokacin break hakan ya hagaresa. Dan wani irin zazzaɓi ne ma ke
neman rufesa. Ga ciwon kai. Dan hatta fararen idanunsa launinsu ya canja zuwa jaa sosai alamar akwai
wani abu dake damunsa. Sai dai sam fuskarsa bata nuna komai.
Kwanciya yay a office ɗin bayan dawowa sallar azhar, kamar wasa zazzaɓi mai azabar zafi ya rufesa,
ga wani irin sanyi da yake ji. Ya kulle kofar tare da ma AS gargaɗin baya buƙatar kowa. Hakan yasa ko
lokacin Asr AS bai masa knocking ba dan yasan ogansa baya wasa da salla. Ganin har biyar na yamma
lokacin ma'aikata sun fara tashi babu alamar zai fito hankalin AS ɗin ya fara tashi, ya dai daure dan yasansa
da iya yin over work. Kamar wasa har magrib companyn yayi shiru sai securitys. Dole fa yaje ya fara masa
knocking amma shiru kake ji wai malam yaci shirwa. Hankali tashe AS yay kiran wata number, bayan an
ɗaga yayi gaisuwa cikin girmamawa ya sanar da halin da boss ɗin nasa ke ciki. Banji mi aka sanar masa ba,
sai dai ya amsa da girmamawa yana sauke wayar. Yana nan yana faman kai-kawo a bakin ƙofar sai ga wani
nutsetstsen mutum da zai iya kaiwa shekara arba'in haka. Sosai yake kamanni da AA ɗin, hatta da rashin
yawan fara'ar fuska kamar AA ɗin dai. Gaisheshi AS yay da girmamawa. Ya jinjina masa kai yana amsawa,
sai kuma ya fiddo wani ɗan card a aljihun jallabiyarsa fara ƙal ya goga a jikin handle ɗin ƙofar. A take kuwa
ta rabe gida biyu ta buɗe. Gaba ɗaya an kashe wutan office ɗin, hakan ya saka gabansa faɗuwa, dan sun
san minene ganin AA a duhu yake nufi, wayarsa ya zaro ya kunna fitilar, hakan ya bashi damar ƙarasawa ga
makunan fitulun office ɗin ya kunna. A take haske ya gauraye ko'ina. Idanunsa suka sauka akan AA dake
kwance a kan sofa. Cike da sassarfa ya ƙarasa garesa yana kiran sunansa, amma shiru babu allamar zai
amsa, har ya zauna a saman table ɗin gaban sofa ɗin tare da kai hannunsa saman na AA daya dafe kai da
shi, hannun ya janye a hankali ya maye gurbinsa da nashi, sai da gabansa ya faɗin jin wani irin hucin zafi,
sanyin hannunsa yasa AA buɗe manyan oily idanunsa gently, sunyi wani irin mugun kaɗawa jazur, sam
babu hasken nan mai kama da madara a cikinsu yanzu, sai ƙyallinsu daya sake saka jan yin bauuu. Ga kuma
jijiyoyin kansa da suka sake fitowa ruɗu-ruɗu....
“Ya arrahaman Auta! Baka da lafiya amma kazo nan ka kwanta? Are you mad da baka san
muhimmancin lafiyarka bane?”.
Maimakon amsa masa sai AA ɗin ya maida idanun nasa kawai ya sake lumshewa. Tsaki mutumin yaja
tare da miƙewa ya tada AA ɗin shima. “Oya get up and go home?”.
Bai masa musu ba ya miƙe ɗin, haka ya kamashi suka fito yana bama AS da hankalinsa ya tashi da ganin
halin da boss ɗinsa yake ciki umarnin tattaro abubuwan AA ɗin. Cikin sauri ya amsa shi kuma ya wuce da
shi......
_____________★
A hankali yake juya steering kamar baya so. Yayinda gaba ɗayan hankalinsa ke akan al'amarin
Maanal. Yama rasa yaya zai fassara lamarin, musamman a yanzu daya koma Maawad yaji komai daya faru.
Shin murnar samun aikin ce ta sakata kukan? Ko kuwa mike faruwa?. Rashin mai bashi amsa ya sashi
ɗaukar hanyar gidan Shahidah, dan gaskiya yana buƙatar ganin Maanal ɗin. Ya ɗan yi nisa da tafiya kira ya
shigo masa. Kamar bazai ɗauka ba sai kuma dai ya ɗauka saboda ganin abokin aikinsa ne na asibiti. Neman
gaggawa ake masa zuwa asibiti yanzun nan, dole yay reverse zuwa asibitin dan yanda yaji Doctor ɗin a
rikice yasan akwai babbar matsala. Kafin ya isa kiran wasu doctors biyu ƴan uwansa ya sake shigo masa.
Dole ya ƙara gudu cikin ƙanƙanin lokaci sai gashi ya iso.....
_________★
A ɓangaren Maanal kuka taci sosai na tashin hankali. Dan har yamma ta kulle kanta a ɗaki taƙi ta fito.
Yara da suka dawo makaranta sunata buga mata bata kulasu ba. A haka shima baban nasu ya dawo ya tarar
da al'amarin. Linda ce ta sanar masa iya abinda ta sani na shigowar Maanal ɗin da gudu tana kuka ta wuce
ɗaki ta kulle kanta...
Hankalinsa ne ya tashi shima. Ya shiga knocking ƙofar yana kiran sunanta amma shiru. Sai ya fara
tunanin kodai batama rayene? Gata tare da ciwo mai haɗari. Wayar Shahidah ya kira yace ta dawo gida
yanzun nan. Hankali tashe ta shiga tambayarsa lafiya? Dan ita bata tashi a nata aikin ba. Amma sai yace ba
komai tazo dai kawai. Daga haka ya yanke kiran ya fita neman maigadi dan yazo su gwada ɓalla ƙofar. Babu
jimawa suka dawo, zuwa lokacin yaran nata kuka suna sake buga ƙofar. Sunta ƙoƙarin buge ƙofar amma
bata ɓallun ba, dole maigadi ya ce, “Yallaɓai sai dai fa a nemo wanda yasan aikin karma ayi ɓarna. Bara
muga na kira wani yaro dana sani”.
Kai kawai Uncle Sadeeq ɗin ya iya ɗaga masa. Dai-dai nan Shahidah ke shigowa a ruɗe. Cikin tashin
hankali take tambayarsa abinda ya faru. Bayani ya mata kamar yanda Linda ta masa. A take jikin Shahidah
ya kama rawa. Itama ƙofar ta fara bugawa muryarta na rawa tana kiran sunan Maanal ɗin amma shiru.
Wani tunani ne yazo mata, ta fita cikin sassarfa zuwa can baya inda windows ɗin ɗakin suke. Binta shima
mijin nata yay. Kwance suka hango Maanal sharɓan a gado babu alamar rai a tare da ita. Ai Shahidah bama
tasan tayi wani irin yin baya ba tana neman faɗuwa sai da mijinta ya tarota. Cikin rawar baki data murya ta
ce, “Honey ta rasu ko? Da alama Maanal bata numfashi”.
“In sha ALLAHU bata rasu ba Honey cool down. Zata iya yiwuwa suma tayi ko barci take”.
“Barci! Ina badai barci ba Honey.....”
Isowar su maigadi ya hanashi bata amsa. Kamata yay suka koma cikin gidan. Cikin abinda bai wuce
mintuna goma ba aka ɓalle ƙofar ɗakin. Daga Shahidah har mijinta da yaran a guje suka afka ciki. Lokaci
ɗaya ita da yaran suka zagaye Maanal ɗin. Koda ta cacumota sai tai mata wani jagab alamar babu rai tare
da ita. “ Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un”. Ta shiga ambata jikinta na rawa. Yayinda yaran suka fara ihun kuka
suna kiran Maanal ɗin. Shi kam mijinta ƙoƙarin neman number RK yake yi, sai dai sam taƙi shiga. Dole ya
koma neman Dr Ranjet. Cikin Sa'a kuwa sai ita ta shiga. Bayani ya masa a taƙaice, hankali tashe Dr Ranjet
yace gashi nan zuwa gidan RK ya shiga theater ɗin gaggawa ne tun ɗazun shiyyasa bazai samesa ba.
Alhamdullah Dr Ranjet ya iso akan lokaci tare da wata abokiyar aikinsa. Dandanan ya saka kowa ya fito
suka kasance su biyu kawai a ɗakin. Taimakon gaggawa suka shiga bama Maanal ɗin, sunfi awa ɗaya kafin
cikin amincin UBANGIJI ta farfaɗo. Dama ya tabbatar musu su kwantar da hankalinsu bugun zuciyarta ne
yay ƙasa sosai shiyyasa numfashinta ya dakata ma amma tana da rai. Basu bari kowa ya shigo ba sai da
suka gama dai-daita komai suka saka mata ruwa da allurai sannan.
Bayanin da Dr Ranjet yamusu ya saka su dinga sauke ajiyar zuciya a tare. Shahidah ta dinga share
hawaye. Su duka suka shiga tare da yaran da mijin nata, ganin Maanal ɗin na barcinta hankali kwance ya
sake saka musu nutsuwa. Bayan fitowarsu ne Dr Ranjet ke sanar musu dolene su kula sosai da shan
maganin Maanal ɗin, dan yanzu ma yana tunanin sakacin hakanne ya kawo wannan matsalar, duk da ya
fahimci akwai damuwa tattare da ita bai faɗa musu ba dai. Hakan kuwa ɗin ne kamar yanda yay hasashe,
dan yasa an kawo masa magungunan ya duba ashe kona safe bata sha ba ta fita. Ya sake tabbatar musu da
kula da shan maganin nata da shigarta kowacce matsalar damuwa komai ƙanƙantarta sannan suka wuce.
Dole yau Shahidah tare ta kwana da Maanal. Alhamdullah ta tashi cikin aminci kuma. Dukkan wata
kulawa Shahidah ce ta bata a wannan safiyar, harda yara kowa tattalinta yake yi, hatta da abinci tara suka
bata a baki, hakan ya sakasu makarar fita dan sai da ta sake komawa barci sannan. Bayan ta farka Linda tai
ƙoƙarin taimaka mata tai wanka taci abinci tare da sanar mata zuwan RK gidan har sau biyu, amma sai
Maanal ɗin taƙi cewa komai tana zaune kawai tana hawaye. Ana haka RK ya sake dawowa. Babu lallashin
da Linda batai mata ba akan taje su gaisa ko shi ya shigo amma taƙi, tanata kukanta kawai. Hankalinta sai
ya sake tashi tai kiran Shahidah dake a wajen aiki ta sanar mata. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa sai gata ta
dawo gidan...
★ “Haba Maanal wai mike faruwa ne duk kinbi kin ɗaga mana hankali. Jibafa office na baro saboda
kiran da Linda taimin duk da tarin ayyukan dake a gabana. Amma inata magana kinyi shiru sai kuka kikeyi.
Idan jikin naki ne kuma muje asibiti. Ko na kira Ammie ne dai?”.
Da sauri Maanal ta shiga girgiza mata kanta tana sharce hawayen da suka gagara tsaya mata. “Didi kar
ki kirata dan ALLAH. Ba wani abu baneba fa”.
“Haba Maanal ya zakice bawani abu bane gaki kinata faman kuka. Idan baki son na kira Ammien to ki
faɗa min mike faruwa ne? Wani abun Rafeeq ɗin ya miki jiyan da kuka fita? Ko aikin ne basu ɗaukeki ba?”.
“A'a Didi babu ɗaya daga ciki, ina son yai zan koma KD”.
“Okay mune mukai miki wani abu kenan?”.
“Kai Didi ni mi zaku min. ALLAH ki kwantar da hankalinki babu komai”.
“Batun kwantar da hankali kam bazai kwantu ba Maanal, yanzu fa kike cewa zaki tafi KD. Amma dai
bara na kira Ammien ni kam, ƙila ki sanar mata ko Nene. Ga Rafeeq can Linda tace yayi mayawa takai huɗu
tunda safe amma kinƙi fita, kinƙi cin abinci, kinƙi wanka Maanal why? Gara nai kiratan dai zai fi”.
Caraf ta riƙe mata hannun tana girgiza kanta. Yayinda idanunta suka cika da ƙwalla tab. “Please Didi karki
kirata zan gaya miki”. Kai Shahidah ta jinjina tare da sauke numfashi sai kuma ta sakar mata wayar da faɗin,
“To ina saurarenki, mike faruwa?”. Sai da Maanal taja kusan mintuna biyu kafin da ƙyar ta iya furta, “Didi
sun ɗaukeni aikin amma bazanyi ba”.
“Baza kiyi ba kamar ya? To saboda mi?. A wannan lokaci da aiki ke wahala Maanal. Kin samu cikin sauƙi
haka amma kice baza kiyi ba. Ko auren Yazeed ɗin kike so to? Ko kuma dan kinji jiya ankai kuɗinsa gidan su
Nazeefa ne har kika nema tadana kanki ciwo?”.
“Didi mizai sa na damu da auren Yaya Yazeed tunda ba'a kaina zata zauna ba.”
“To mike faruwa? Wajen aikin ne ya miki alamu na marasa ɗa'a ko me?”.
“A'a Didi kawai dai”.
“Miye kawai dai. Maanal ki fito kimin bayani mana yanda zan fahimta na kuma gamsu”.
Rasa yanda zataima Shahidah ɗin bayani tayi, ta fito fili ta sanar mata abinda idanunta suka gani a jiyan
ko kuwa ta shanye al'amarin a cikinta kawai ta dage akan aikinne bazatayi ba. To amma tasan nacin RK,
shima bazai barta ba ai. Sannan ita kanta Didi ba barinta zatai ta huta ba har sai ta san gaskiyar al'amarin.
Sanin gaskiyar kuma na nufin abinda zata ɓoye a yanzu dan sai sun san komai. (Ya arrahaman) ita ina ya
kamata ta kama ne?.....
“Maanal!!”
Shahidah ta kirata tana mai girgizata. Firgigit ta dawo hayyacinta kamar wadda aka tada daga barci, sai
kuma ta sauke ajiyar zuciya tare da kai hannunta saman goshi tana murzawa a hankali.
“ALLAH Maanal tambaya ta ƙarshe zan miki daga nan zan kira Ammie ne kawai tunda ni baki son nasan
damuwarki”.
Jin yanda Shahidah tai maganar a hasale tana ƙoƙarin miƙewa yasa Maanal saurin kamo hannunta ta
dawo da ita. Idanunta cike da ƙwalla ta ce, “Didi ba ɓoye miki nake ba wlhy, kema kin sani bana taɓa ɓoye
muku komai a rayuwata. Kawai dai na fasa yin aikin ne saboda companyn na Bes...” sai kuma ta canja ta
ce, *_“AA Darma_* ne?”.
Cikin matuƙar razani Shahidah ta miƙe zumbur hannunta dafe da ƙirji ta ce, “What!! Kina nufin
*_Ajwaad!!_* Maanal!”.
“Shi Didi, shi! Shi! ɗin dai.” Maanal ta faɗa wasu hawaye masu zafi na sake gangaro mata.
Jagwab Shahidah ta koma ta zauna tana mai dafe kanta da duka hannaye biyu, ita kanta jikinta tsuma
yake, sai kuma ta ɗago tare da jawo Maanal ɗin jikinta ta rungume dan kuka take mai ban tausayi da tsuma
zuciya. Cikin sarƙewar murya ta ce, “Maanal kuma kin gansa ya ganki? Kin tabbatar shi ɗin ne dai?”.
Kai Maanal ɗin ta jinjina mata, “Ya ganni sosai, amma ya nuna kamar ma bai taɓa sanina ba tamkar a
wancan ranar da yay......” nan dai ta labarta mata duk yanda komai ya faru. Gaba ɗaya mamaki ya gama
kashe Shahidah, amma sai ta danne ta shiga Lallashinta har sai da tai shiru. Daga haka ma ta ciro
maganinta ta bata kasancewar lokacin shan na rana yayi. Tana sha babu jimawa ta ɓingire wani barcin.
Lallaɓawa Shahidah tai ta gyara mata kwanciya, sannan ta saka mata ac kaɗan ta kashe mata fitilar ɗakin ta
fice..........✍️
_Tofa, wanene *AA Darma* a rayuwar Maanal Habeeb Giro?. Karku gajiya kumuje zuwa dan yanzune
labarin AJIYA A DUHU ma zai fara. Labarin nan fa akwai cakwakiya ta musamman mutane na. Ni bamma
san team ɗin wa zan kasance ba bana. Karna zaɓi AA ace min mayyar kuɗi🥲🥱🤪🏃_
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
2️⃣5️⃣2️⃣5️⃣
........Nata ɗakin ta nufa tanata faman sauke ajiyar zuciya. Yayinda abubuwa masu yawa ke mata kaikawo a
cikin rai tamkar sun faru sun wuce ne a cikin film. Tana shiga ɗakin wayarta ta ɗauka domin kiran Ammie.
Har tayi dailing no ɗin nata sai kuma ta katse da sauri, dan kuwa ziciyarta ta tsawatar mata akan ba ita ya
kamata ta kira ba. Cikin gamsuwa da hakan ta maida alaƙar kiran ga Amal duk da tasan itama dai tana
wajen aiki yanzu haka. Sun gaisa kamar yanda suka saba cikin so da ƙaunar juna. Tare da tambayar yara da
bayan rabuwa. Sai kuma Amaal ta ciga da faɗin, “Didi ya naji muryarki duk ta canja kamar wadda ke'a cikin
damuwa? Kuma kamar ma a gida kike bakije office bane?”.
“Him ke dai bari Amaal, abin duniya ne ya isheni wlhy dawowa nayi. Akan Auta ne fa”.
“Ya ilahil'alamin miya faru kuma?. Kin saka gabana faɗuwa badai jikin nata bane kuma?”.
“Bashi bane duk da dai jiya taso rikita mana lissafi gaskiya. Amma Alhamdullah yau ta tashi normal. Sai
dai abinda yaso zama sanadin tada ciwon nata har yanzu yana tare da ita.”
“ Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un. Didi kimin bayani dan ALLAH yanda zan gane. Mi kuma ya sake faruwa
da Autar?”.
Komai daya faru Shahidah ta labartama Amaal kamar yanda Maanal ta sanar mata ita da kuma wanda ya
faru anan gidan. Ai Amaal batama san ta rikito a kujerar office ɗinta ba tana zunduma wata ƙatuwar
ashariya da maimaita sunan “Ajwaad fa? Na gidan Oum?”.
“Shi kuwa wlhy Amaal.”
“Kan babbar b... uba. Ke nan dama suna ƙasar nan Didi?”.
“To bazamu ce ba Amaal ALLAH kaɗai ya sani, amma nayi mamaki matuƙa nima, dan banyin zaton haka
daga Oum ba. Shin miya hanata neman mu?.”
“Humm Didi wannan maganar ta wuce ta waya. Ki saurari zuwana anjima kaɗan koda sassafe ne na
dawo saboda office. Kin gayama Ammie?”.
“A'a ki rufan asiri kin santa dai ai. Ke kaɗai na gayamawa. Ko Abban su Barrah ban sanarma komai ba
ma. Amma Daddyn Munaya zai barki?”.
“In sha ALLAHU zai bari barima kiga”...
_____________★
Sosai Hajiya Yaya da Aunty Sabuwa da ƴaƴansu suka haɗa wata ƴar ƙwarya-ƙwaryar walima a gidan
Aunty Sabuwa ɗin wai na murnar saka rana. Abin ma sai ya baka dariya da mamaki. Dan dj aka ɗakko ya
saki speakers iya maƙura aka cashe akaci kaji da lemuka. Ga taron ƙwayen Aunty Sabuwar ƴan duniya, dan
mafi yawansu zawrawa ne. Dan ita dai Hajiya Yaya tun abin na birgeta tana murmushi har ya fara tsikarin
zuciyarta. Amma sai ta danne ta basar. Kasancewar tasan Daddy na gari anayin la'asar ta tattaro su
Asalamiyya sukayo gida ransu a ɓace. Dan so sukai ta barsu su kwana acan su ƙara ɓararrajewa da ƙyau.
To ashe wasa farin girki, dan kuwa tafiyar su Hajiya Yaya kamar an buɗe wani sabon babin shagalinne a
gidan. Tsabar taɓara da zubewar mutunci sai ga mahaifin Nazeefar ya shigo fili wai shima ya taka rawa, liƙi
Sabuwa ta fara masa sauran ƙawayen ma suka rufu a kansu suna liƙesu ana dariya da shewa da shaƙiyanci
tunda shima ɗan duniyar ne. Sai daga baya ya fita ya barsu ya shige ciki, su kuma suka cigaba da
shagalinsu. Yayinda guri yay guri Sabuwa tama manta da wanzuwar miji a gidan, babban aminiyarta ta
zame jiki tai wuff tabi bayansa. Dama sun jima tare ita Sabuwa ce bata sani ba. Aiko ya sama ƙofa key suka
hau shagalinsu suma.
A taƙaice dai wannan taro bai tashi ba sai kusan sha biyun dare. Duk sun bi sun hana ƴan anguwa barci
anata musu ALLAH wadarai. Koda suka nutsu Sabuwa ke tambayar Hajiya Malika aminiyarta ina ta shige,
sai cemata tai ai gida taje saboda oga ya dawo neman wasu takardu bai gansu ba. Sai da ta koma ta
bashine ta dawo. Cike da shaƙiyanci suka hau tsokanarta wai bawasu takardu kodai-kodai. Dariya ta dinga
tuntsurawa ita dai. A haka Mijin Sabuwa ya sakko daga sama. Suna haɗa ido da Hajiya Malika suka wani
kashema juna idanun cike da salon shaiɗanci batare da kowa ya lura da su ba.
(Humm ALLAH ya ƙyauta. Hajiya Malika dai matar abokin Alhaji Sajid ce, kai yama wuce ace aboki sai
dai amini ɗan uwa. Hakan yasa suka ƙulle matansu suma suka zama aminan Sabuwa da Malika ɗin kenan.
Sosai suke aminta dan babu wani sirri na Sabuwa da Malika bata sani ba, hakama duk wani sirrin Malika
Sabuwa ta sanshi. Abota ce tun ta ƙuruciya. Ko lokacin da Sabuwa ta rabu da Alhaji Sajid ɗin Sabuwa da
Malika na tare, kusan ma za'ace da taimakonsu ne aka maida auren bayan Sabuwar taje tayi auren kisan
wuta saboda saki uku ne. Shi mijin Hajiya Malika sam ba mazauni bane ba, ɗan kasuwa ne da kullum yana
wacan ƙasa gobe yana waccan kamar wani ɗan sama jannati, da wannan damar Mijin Sabuwa ya samu kan
Hajiya Malika suke sheƙe a yarsu. Dan a yanzu haka ƴaƴan Hajiya Malika ba duka bane ɗiyan mijinta idan
za'a tantance, akwai gauraye dana mijin Sabuwa saboda yanda suke tare matuƙa kamar wata matarsa.
UBANGIJI kuma yay musu talala har yanzu babu wanda ya taɓa sanin wannan alaƙa tasu duk da tsahon
shekaru sai wata mai aikin da Hajiya Malika ta taɓa yi, ita kam ta kamasu dumu-dumu cikin aikata
al'amarin ta tsorata, itama hankalin Hajiya Malikan ya tashi amma sai Mijin Sabuwa yace karta damu ta jira
taga mi zaiyi. Aiko taga abinda zaiyi ɗin, dan a gabanta yayma yarinyar nan ƴar aikinta fyaɗe, daga nan yaja
mata dogon gargaɗi akan idan ma taje ta tona musu asiri saita haɗa da kanta, ya nuna mata video ɗin daya
saka Hajiya Malika ta ɗauka sanda yake tare da yarinyar. Hankalinta ya tashi, ta dinga kuka tana ramtsuwar
bazata faɗa ba wlhy. Basubi takanta ba sukace ya haɗa kayanta washe gari aka maida ta ƙauyensu. To
tundai daga nan babu abinda ya sake faruwa sai dai UBANGIJI na kallonsu, ba kuma su san ya musu talala
bane ba)
_________★
Kamar yanda Amaal tai alƙawari ta iso Abuja kusan takwas na dare. Alhamdullah zuwa sannan Maanal ta
farka. Dan shigarta wanka kenan Amaal ɗin ta iso. Ta fito taci karo da ita a ɗakinta sai tayi turus. Dariya
Amaal ta sanya mata tare da buɗe mata hannayenta alamar tazo gareta. A yanzu kam babu musu Maanal
ɗin ta nufota suka rungume juna, kai kace ba kwanan nan suka rabu ba.
Sai da Maanal ta shirya tai sallolin dake kanta sannan ta dawo tsakiyar yayun nata maganin kukanta ta
zauna. Abinci suka fara ci, yayinda Maanal ta shagwaɓe musu wai ita hannunta na ciwo bazata iya ci da shi
ba. Aiko su biyun duk suka dinga bata a baki. Hakan da sukai mata ma sai taci abincin sosai. Dagan nan ne
suka nutsu akan abinda ya tarasu.
Da farko dai sun fara lallashinta akan batun aiki tace ita fa ta fasa bazatayi ba. Hasalima tana son
komawa Kaduna ne kawai wajen Ammie.
Baki Amal ta taɓe cikin ɗan ɓacin rai dan dama tafi Shahidah zafi ta ce, “Oh Kaduna ko? Kenan auren
Yazeed ɗin kike son yi?”.
“Yazeed kuma? Didi ni na taɓa cema wani zan auri Yazeed?”.
“Ai basai kin faɗa ba gashi yanzu kin nuna mana. Wai Manaal mike damun kanki ne dan ALLAH?. Ke gaba
ɗaya tunaninki a bauɗe yake dana mutane, sai shegen taurin kai da kafiyar tsiya. To wlhy bari ma na fito
miki a mutum ki tattara hankalinki waje guda ki maidashi jikinki. Har mi akai akayi wani Ajwaad can da zai
hanaki samun cikar burinki....”
Hannun Amaal Shahidah ta jimƙe a nata tana girgiza mata kai alamar tayi shiru. Hakan ya saka Amaal ɗin
jan ƙaramin tsaki. “Didi ki barni da ita. Na kula sam Maanal bata tausayin kanta bata tausaya mana mu ƴan
uwanta. Wace irin rayuwace wannan ace mutum da taurin kai....”
“Kinga ya isa haka. Maanal bani hankalinki nan muyi magana ta gaskiya”. Shahidah ta faɗa tana kamo
hannun Maanal data tsurama Amaal idanu cikin nata. Dole ta janye daga kan Amaal ɗin ta maido kan
Shahidahn. “Maanal kiyi haƙuri bazamu takura miki ko tirsasaki akan abinda baƙya ra'ayi ba. Amma ina son
ki fahimci wani abu, mufa a yanzu bamu da maraba da marayu da suka rasa mahaifi da dukkan dangi.
ALLAH ne gatanmu sai Ammien mu sai kuma Nene kawai sai kammu. Dolene fa mutattara komai daya faru
a baya mu zubar da shi muyi mantawa irin ta AJIYA A DUHU duk da nasan akwai tabo da bazai taɓa
goguwa ba a zukatanmu amma komai na ALLAH ne. Sannan dole musan kammu mu kuma gina gobe
yaranmu masu tasowa. Maanal Daddy ya riƙemu babu banbanci da ƴaƴan daya haifa a cikinsa tunkan
Ammie ta haifa masa Waleed da Hameed. Kuma muma a yanzu babu wanda mukema kallon uba sama da
shi. Sai dai fa mu sani iyakarmu kiransa uban ne kawai a iyakar kayinmu, amma a wajen al'umma sunanmu
AGOLOLI a gidansa. Maanal ba fata nake ba, amma ki sani a yanzu ALLAH ya ɗauki rayuwar Daddy wlhy ko
Amminemu bazasu bari ta rayu a wannan ahalin ba. Saboda su Waleed ƙanana ne, basu kai girman da zasu
ƙwata mata ƴanci ba. Mu kuma komu yarda ko karmu yarda munada iyakarmu a gidan nan. To mikike
tunanin ya kamata muyi? Wannan aikin tuƙuru domin gina gobemu da goben yaranmu. Bazamu so mu
sake maimaita rayuwar baya ba Maanal, bazamu so mahaifiyarmu ta sake maimaita wahalhalun data sha a
kammu ba a shekarun baya, idan sannan muna da ƙuruciya yanzu munkai girman share mata kukanta,
mun girma Maanal mun girma”.
Kuka ya sarƙeta. Suma duk sai suka fara kukan, koda yake dama Maanal ita tuni ta fara hawaye. Kusan
mintuna biyu Shahidah ta share hawayenta da cigaba da faɗin, “Maanal bamu san mi gobe zatazo mana da
shi ba. Dan muma mata ne. Idan har Ammie zata iya riskar kanta a irin rayuwar da mukai a shekarun baya
bai kamata mu mushagala da tunanin komaima bazai faru ba saboda a yanzu rayuwarmu ta inganta. Karfa
mu manta da irin labarin gata da rayuwar Ammie tasha a hannun iyayenta, amma hakan bai hanata
fuskantar ƙalubale ba a hannun mijin aurenta da kowa ke gani hakan bazata faru ba. To muma bai kamata
ganinmu a cikin irin waɗan nan manyan gidajen yasa mu shagala ba. Bai kamata mu cigaba da zaman jiran
kullum a mana ba. Saboda haka ki dawo cikin hankalinki Maanal, ki tuna su waye mu a yanzu. Ki ajiye
abinda ya wuce baya ki manta da shi, ki kaishi cikin duhuwa ki ajiyesa tamkar ma ba'a taɓa yin komai ba.
Yanda Ajwaad ya nuna bai sanki ba ki zama JARUMA kema ki nuna baki sanshi ba, ki manta da shi, ki manta
da abinda ya shafesa, ki tsaya da ƙafafunki, kisa a ranki shi bai isa hanaki kaiwa ga cikar burinki ba, karki
wani damu da zamowarsa shugaban kamfanin ko matsayin nasa ke aiki ya kaiki domin kanki. To kiyi kuma
aiki tuƙuru a companyn nasa domin kanki da cigabanki. Maanal ki duba yanda Rafeeq ke hidima dake da
son ganin farin ciki ki, hatta Yazeed ma ni wlhy ban taɓa ƙin kasantuwar aurenku ba saboda mutumin kirki
ne. Koba komai yasan mutuncin mahaifiyarmu, ya taimakemu a lokacin da muka rasa taimako daga
jininmu ma. Kawai mahaifiyarsa ce matsala. Idan kuma da alkairi a zamanku sai ALLAH ya ɗauketa ku zauna
ɗin babu yanda zatayi. Amma dan ALLAH ki amshi al'amarin Rafeeq ki gwada ki gani shima. Ki kwantar da
hankalinki addu'ar mu na zagaye dake ki manta da baya, ki saka a ranki ƙaddarar data gitta rayuwarki
bazata hanaki aure ki zauna a gidan mijin ba har kuma ko samu farin ciki fiye da zatonki. Dan ALLAH shine
shaida baki je kin aikata dan son zuciyarki ba. Dan haka ki manta komai, dan ALLAH ki manta komai kije ki
fara aiki, abu nagaba kuma kiyi ƙoƙarin fidda mijin aure tsakanin Rafeeq da Yazeed kodan ki tabbatar ma
Ajwaad kina rayuwane domin kanki. Dan kuwa cikakkiyar amsa kika samu a jiyanki game da shi, idan a
baya hasashe kawai mukeyi bisa dalili yanzu ya tabbatar miki shi da kansa”.
Sosai Maanal take kuka yanzu kam, Amal ta jawota jikinta ta rungumeta itama tana kukan, sam basa
son tunawa da bata, basa son tunawa da ƙaddarar data ratsa rayuwar autarsu, basa so ba sa so. Cikin
rawar murya da son ture komai Amaal ta ce, “Duk abinda Didi ta gaya miki shine gaskiya wlhy Auta. Ki dake
zuciyarki kiyi abinda ya dace da rayuwarki a yanzu. Ki manta da abinda ya wuce kamar ma ba'ayi komai ba.
Koda wasa kada ki zubda daraja da kimarki ta ɗiya mace. Ki amshi ƙaddarki kamar yanda muma muka
rungumi tamu. Hakan da zamuyi sai ya ƙara ƙarfafa Ammien mu, ki duba kiga rayuwar data baro, mai cike
da tarin gwagwarmaya amma a yanzu ALLAH ya mata canji, canjin kuma baisa ace babu wasu jarabawoyin
ba kuma. Tunda anan ɗin ma tana fuskantar ƙalubalen bawai sun ƙare bane. To haka rayuwa take duk
yanda ka kai ga samun sauyi da nasara da jin daɗi dole ƙaddararka aminiyar NUMFASHINKA ce Maanal.
Tare suke tafiya a jefe ƙafa da ƙafa. Aminan juna ne tamkar gangar jiki da numfashi. Hakama jarabawarka
abokiyar gangagar jikinka ce. Kinga ko har abada babu ɗayan da zai rayu babu ɗaya a tsakanin gangar jiki
da numfashi ko?”.........✍️
🏃🏃🏃Hummmmmmmmmmmmmmm🥲
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
2️⃣6️⃣2️⃣6️⃣
.........“Hakane ƴan uwana, na gode da shawarwarin ku, kuma in sha ALLAHU zan yi aiki da su. Dan ALLAH
kuyi haƙuri da ɗaga muku hankalin da nakeyi a koda yaushe. Har yanzu ni mai RAUNI ce a cikinku, ina da
matuƙar rauni ƴan uwana na sani....”
Kuka ya sarƙeta, rungumeta sukai su duka tausayinta na sake ratsasu. Tabbas gaskiya ta faɗa ita ɗin mai
rauni ce a cikinsu. Dan ko lokacin ƙiruciyarsu kadai faɗama Maanal tsiwa da rashin kunya ga shegen
tsokanan faɗa. Amma akwai tsoro kamar farar kura. Sai kuma da jarabawar tasu ta fara ita ta ninku mata
sau biyu, duk da kuwa suma sau bibbiyu ne, amma ita tata tafi tasu ƙarfi ne. Ba komai yasa hakan ba sai
dan sun fita ƙarfin zuciya, sannan su dama basu samu kansu a irin yanayin data samu kanta ba a wancan
lokacin kasancewar sun fita hankali da wayo sosai. Sannan su komai dama anyinsa a wasa-wasa ne
bakamar ita ba.
Kusan raba wannan daren sukai zaune. Suna sake bama Maanal ƙwarin gwiwa da nasiha data sake
ƙarfafata ta kuma ji ta gamsu zataje tayi aikin. Hakan yasa washe gari yanda kowa yay shirin zuwa office
itama tayi, yayinda Amaal tun asuba ta kama hanyar Kaduna tunda dama da mota tazo. Sun fito Maanal na
ƙoƙarin shiga motar Shahidah sai ga motar RK ta shigo gidan. Dole ta ɗan dakata yayinda Uncle Sadeeq ke
dariyar ƙeta cike da tsokana ya dubi Maanal ɗin yana faɗin, “Ga majnoon nan lailah sai ki dakata”.
Dariya Shahidah tayi itama tana amsa masa, “Aifa sai Majnoon ɗin, Rafeeq sam baya gajiya shi kam”.
Maanal dai batace komai ba har RK ɗin ya daidaita parking ya fito a motar. Yayi matuƙar ƙyau cikin farar
shadda ɗinkin tazarce. Sai dai babu hula a kansa. Wajen Uncle Sadeeq ya fara zuwa suka gaisa cike da
mutunta juna da kulawa. Dan ta ko'ina fa RK ya kafa jam'iyyar sa. Sai kuma ya juya ga Shahidah itama ya
gaisheta da mutuntawa. Itama ta amsa masa da kulawa tana tambayarsa yaya aikinsa. Idanunsa akan
Maanal ya amsa mata da Alhamdullah.
Ganin irin kallon da yake mata ta ɗan hararesa sannan ta gaishesa a cinkushe. Maimakon amsawa sai
ya kalla agogon dake a tsintsiyar hannunsa yana faɗin, “Ashe da banyi sauri ba dana makara?”.
“A gaskiya kam daka makara. Amma ALLAH ya taimakeka, bari kaga muma muyi nan karmu makaran
wajen kallon lailah Majnoon”. Uncle Sadeeq ne da wannan magana cike da tsokana yana kallon Maanal.
Yayinda Shahidah ke ƴar dariya itama dai hankalin nata akan Maanal ɗin. Motocinsu suka shiga suka fice
abinsu aka bar Maanal tsaye sororo, wani irin daka zuciyarta ke mata yau a kansa. Sotake ta ƙarfafa kanta
game da shi ta bashi damar kamar yanda ƴan uwanta suka bata shawara a daren jiya. Sai dai ina ji take
anya kuwa zata iya hakan? Amma sai wani sashe na zuciyarta ke sake ƙarfafata....
“Good morning my queen”.
RK ya faɗa yana ɗan duƙowa kaɗan saitin kunnenta. Wani irin numfashi taja tare da jan jikinta baya duk
da bawani ya matseta bane akwai tazara a tsakaninsu. Murmushi yayi da ɗan ɗage mata gira sama ita
kuma ta hararesa tana kauda kanta. Sai kawai ya fashe da dariya. “Oh ni ɗan Mamana irin wannan harar da
akemin sai na sace amarya ai ko a sallar isha'i a ɗaura mana auren daga baya. ALLAH ki daina mun wannan
hararar rikita min lissafi kike gimbiya. Balle irin yanda nai kewar nan taki kwana biyu dubeni har wata rama
nayi marayan ALLAH abin tausayi”.
A yanda yake maganar batama san sanda taji murmushi na neman suɓuce mata ba. Amma sai ta dake
abinta ta danne tare da ɗan girgiza kanta ta ce, “ALLAH dai ya shiryeka”.
“Amin matar Rafeeq Kasheem Kura”.
Manaal bata kulashi ba, dan wayarta dake neman agaji, ƙoƙarin cirota ta shigayi a bag shi kuma ya amshi
ɗan lunch box ɗinta na abinci data haɗa. Yazeed ne ya bayyana ɓaro-ɓaro akan screen ɗin. Hakan ya saka
RK taɓe baki cike da basarwa yabar wajen. Da kallo kawai ta bisa ƙasa-ƙasa tana mai kai wayar kunnenta a
nutsenta tai masa sallama. Da kulawa ya amsa mata da ga can tare da tambayarta jikinta tace Alhamdullah
ta samu sauƙi.
“Masha ALLAH nima zuwa anjima zan shigo duk kin bi kin tadamin hankali da rashin ganinki tunda nazo
aikin ma yaƙi yuwumin yanda nake so. Amma yanzu na ɗan ji ƙarfi tunda na jiki Alhamdullah”.
Shiru tai ta kasa cemasa komai. Shima sai kawai ya saki murmushi daga can, tare da faɗin, “To sarkin
kunya bari na barki nima zan fitane ma na kiraki”.
“ALLAH ya tsare ya bada sa'ar abinda za'aje nema”.
“Amin ya rabbi mar'atussaliha”.
Ya faɗa can ƙasan maƙoshi cike da shauƙin so da ƙara jin tarin ƙaunarta har ƙarƙashin zuciyarsa. Wayar tai
ƙoƙarin maidawa cikin bag ɗin dai-dai da isowar RK wajen da mota. Fitowa yay ya buɗe mata mazaunin
gefensa ta shiga ta zauna ya rufe sannan ya zagaya ya shiga shima yay ma motar key suka fice. Yanata dai
ɗaɗɗaurewarsa bata kulashi ba. Dan ta fahimci yana masifar kishin Yazeed. Koyaya yaga wani abinda ya
shafi Yazeed a tattare da ita zai fara fushi. Itako sai dai yay tayi, dan Yazeed dai tare ya gansu, yazeed kuma
abin girmamawarta ne dan ya taka rawar gani a rayuwarsu a lokacin da kowa ya guje musu. Shiko fa daga
sama ya tsinceta.
Sunyi nisa a tafiyar motar shiru dan kansa ya yanke shirun nasu ta hanyar ɗan juyowa ya kalleta fuskar
dai babu walwala. Sai kuma ya maida kansa ga titi yana faɗin, “Har yanzu baki sanarma su Zulaiha kina
Abuja ba ne?”.
Shiru kamar bazata tanka masa ba sai kuma a can ƙasan maƙoshi ta ce, “Sun sani wani abu ya faru ne?”.
“No babu komai, nagane basu zo dubaki ba har yanzu”.
“Ni nace su barshi basai sunzo ba.”
“Okay”.
Ya faɗa yana ƙara damƙe steering da ƙyau. Daga haka suka sake yin shiru har suka iso Mawaad Company.
Yauma kamar wancan ranar komai a tsaftace a kuma nutse yake a companyn. Sai da ya daidaita parking da
ƙyau tana ƙoƙarin ɓalle murfin motar ta fita ya dakatar da ita. “Na musu reporting akan baki da lafiya
shiyyasa baki zo jiya ba kamar yanda suka buƙata. Dan haka ko sun tambayeki sai kisan amsar da zaki basu.
Please dan ALLAH ki kula, wajen nan cike yake da ƙartin banza kar'a tsinceni a titi muna raba hali da
al'umma”.
Ɗan kallonsa tai a karo na farko sai kuma ta janye lokaci guda tana mai girgiza kanta. Maimakon amsa
masa batunsa ta buɗe kawai ta fice abinta. Ta ɗan fara tafiya taji alamar ana binta a baya, juyowa tai da
taga shine riƙe da ƴar lunch box ɗinta. Tsayawa tai tare da miƙa masa hannu, amma sai ya girgiza mata kai
yana nuna mata hanya alamar suje. Babu yanda ta iya haka suka jera har cikin Companyn...
Wani irin lumshe idanu AA Darma dake zaune cikin motarsa daga baya dan driver ne yau ya kawo shi
Office ɗin tare da datse leɓensa ba ƙasa da ƙarfi. Sai dai sam bazaka taɓa fahimtar hakan ba kasancewar
jarida a hannunsa yana dubawa. Shima isowarsu kenan, kuma tun a hanya a wajen fitilar bada hannu yaga
motar RK ɗin, ya hango mace a motar amma baiga wacece ba. Sai dai haka kawai zuciyarsa ta bashi
wacece ɗin, dan haka koda suka iso kasancewar sun riga su RK ɗin shigowa Companyn sai bai fita a motar
ba. Komai daya faru a kan idanunsa ne dake sakaye a cikin glass mai matuƙar haske daya ƙawata ƙyawun
nutsatstsiyar fuskarsa. A hankali yay wurgi da jaridar hannun nasa a sit ɗin gefensa.
Shi dai driver bai san mike faruwa ba, amma yana tunanin ko wani abin ogan nasa yake shiyyasa. Suna
a haka RK ya fito fuskarsa cike da walwala kamar ba shine ya gama fushin kishin Yazeed ba. Motarsa ya
shiga abinsa yabar harabar companyn, securitys ɗin gate suka ɗage masa karfe da aka gitta a ƙofar bayan
gate ya fice. Wani siririn tsaki AA Darma ya saki a can ƙasan maƙoshinsa. Sai kuma ya ɓalle murfin motar
aɗan fusace ya fito batare daya ɗauki komai nasa dake a motar ba. Sanye yake cikin ash color ɗin suit masu
haske da sukai masa shegen ƙyau. Daga ciki black rigace mai wuyanta har saman wuya. Yanda yake taku
cike da bada faɗi da cika waje ma kawai abin kallo ne. Securitys sai gaidashi suke amma hannu kawai yake
iya ɗaga musu batare da ko kallonsu ba. Koda yazo ga ƙofar shiga da sauri aka buɗe masa ya shige drivern
sa biye da shi da tarkacensa. Tsitt kake ji ma'aikatan dake wajen sakamakon shigowar tasa. Sai kuma kowa
ya shiga faɗin, “Good morning Sir!”. Hannu kawai ya ɗaga musu sau ɗaya yay wucewarsa batare da ko
kallon kowa ba anan ma. Hakan ya sakasu fahimtar yau fa gizagon boss ɗin yafi na kullum, sai kowa ya ƙara
kama kansa.
Elevator ya shiga tare da danna floor ɗin ƙarshe 6th da office ɗinsa yake, shima drivern nasa ya shiga.
Ƙofar zata fara rufewa Maanal da AS da yay mata rakkiya office tai singing da ake buƙatar tayi suka iso
wajen. Shigowa sukai da sauri batare da hankalin AS ɗin yakai ga wanda ke cikin elevator ɗin ba
kasancewar ya ɗan juyama ƙofar baya yana danna waya. Balle kuma Maanal da itama gaba ɗaya nata
hankalin ke akan wayarta. Sai da suka gama shigowar AS ya shaƙi ƙamshin turaren boss. Sai kuma sukai ido
huɗu da driver. Ya juya da sauri nan ma sukai ido huɗu da AA Darma.
Cikin ɗan rawar baki ya ce, “So...sorry sir good morning. ALLAH bamma lura kaine a ciki ba. Zan kai
new staff ɗinmu office ɗinta ne bisa umarnin Director Mustapha”.
Kai kawai AA ɗin ya jinjina masa, yayinda Maanal da zuciyarta ke wani irin bugawa da sauri-sauri ta sake
dakewa abinta dan tunda AS ya fara magana ta ɗan ɗago ta gefen ido ta saci kallon wanda yakema wannan
rawar bakin sai ta ɗauke kanta. Ɗan duƙowa yayi kaɗan ƙasa-ƙasa ya furta, “Boss ne kiyi gaisuwa”.
Shiru tai kamar bazata kulashi ba sai kuma a hankali a can ƙasan maƙoshi batare data kalla kowa ba ta
furta, “Morning”. Daga haka taja bakinta tai shiru. Ita tai abin amma AS ta bari da ruɗani, sai wani irin
haɗiyar yawu yake yana kallon AA ɗin ta gefen ido ko zaice wani abu akan gaisuwar rainin wayon sabuwar
ma'aikaciyar tasu....
__________★
Fuska cike da murmushi Hajiya Basariyya ke kallon kayan da ƴar Tata Huznah ta baje a gabanta. Ba
kayan ci bane ba kuma na sakawa ba kayan da malam ne na Zaria ya haɗoma Huznah ɗin bayan ta ɗauki
tsawon kwanaki tana acan ana tsumata da wasu aikin. Ba kuma akan kowa akai hakan ba sai sabon
saurayinta data samo a birnin tarayya Abuja lokacin bikin ƴar ƙawar Hajiya Basariyya ɗin. Sam kayan babu
wani ƙyan gani ko birgewa a kallonsu. dan kuwa tarin guraye ne da ruwayen magani da layu sai garin
magungunan da turarruka na shafawa harda su hoda da kwalli na idonka idona. Sai da ta gama mata
bayanin komai dalla-dalla kafin ta ta fuska ɗauke da murmushi ta ce, “Kin daiga komai Ummi, bayan kuma
wanda yay mun a jikina dan na aikata iya aikatuwa. Yanzu dai babu zama dole na shirya na wuce Abuja.
Dan ya tabbatar min da in dai nayi komai yanda ya dace babu fashi auren mu zai kasance tare da na Yazeed
ne a gidan nan”.
“Kai Alhamdullah Masha ALLAH. ALLAH dai ya sakama malam da alkairi wlhy. Shiyyasa bana baƙin cikin
biyansa duk abinda ya buƙata dan shima ana samun biyan buƙatar daga nasa aikin. Tafiya Abuja kam dole
ne. Sai dai Daddynku nake tsoro dan yana gari. Dama da yaya ya bari kika tafi Zaria ɗin nan. Yanzu ko akace
Abuja nasan da rigima”.
Cikin matuƙar damuwa Huznah ta ce, “To Ummi yanzu yaya zamuyi kenan, dan ni dai ko ana ha maza ha
mata sai naje Abujar nan wlhy??”......✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
2️⃣7️⃣2️⃣7️⃣
........Maimakon Hajiya Basariyya taji haushin furucin ƴar tata sai ta tuntsure da dariya tana faɗin, “Ja'ira
wato ke ƴar daɗi soyayya ko? Kwantar ma da hankalinki komai zaizo da sauƙi bani lokaci dai nayi tunani.”
“To Ummi nidai dan ALLAH kar tunanin naki ya wuce yau da gobe dai. Dan a matse nake gashi nayi
kewarsa ina son ganinsa.”
Anan ɗin ma dariya Hajiya Basariyya ta sanya abinta.
__________★
A can ɓangaren Aunty Sabuwa ma shiri takema ƴarta na mugayen mallaka, dan hatta da Hajiya Yaya
aba'a ƙyaleba tuni sunanta na wajen boka. Kai shi kansa Daddyn ba tsira yay ba da sauran ƙannen Yazeed
mata. Dan tace tako ina sai ta bama ƴarta garkuwa. Tako bayar ɗin gwagwargwadon abinda take ganin ya
wadaceta. Ga maganin mata ana ɗirkama Nazeefa kamar babu gobe, gefe kuma fetsararrun ƙawayen
uwarta su Hajiya Malika na koya mata kissa da kisisina harda salon kwanciya da miji.
A tacan ɓangaren Mahaifinta kuwa yana nasa shirin ne akan Daddy. Dan a wannan karon yaci alwashin
samawa kansa nasara akan Daddyn. Sai kuma shirin biki na ƴar gata da sukeyi da ga shi har Aunty Sabuwa
ɗin.
Ata nan ɓangaren Hajiya Yaya shirin suma suke na garari, dan a satin nan zata wuce Dubai ita da Baraka
da Asalamiyya su haɗo lefe da nasu kayan cin bikin. Da farko Daddy ya hana tafiyar, saboda ya fahimci ana
komai ne dan ƙuntatama Ammie. Amma sai Ammien ta dinga masa roko da magiya dan tasan hanawar
wata sabuwar rigima ce, kuma dai laifin a kanta da baya so zai ƙare. Dan tuni Hajiya Basariyya tayi uwa tayi
maɗaukiya a bikin shiyyasa ita ake kiranta ƴar baƙin ciki. Haka dai dole Daddy ya bari dan yana matuƙar jin
kunyar Ammie ta roƙesa abu ya kasa mata saboda dattakonta itama, sai dai da sharaɗin karsu wuce sati
ɗaya, idan kuma hakan ta faru zasu sha mamakinsa. To a hakan ma dai Ammie bata tsira ba dan sai da
tasha zagi da habaice-habaice. Ita dai bata kulasu ba kamar yanda ta saba. Sai ma ta maida hankali akan
shirin Daddy da shima yake yi dan wannan shine karo na biyu da zai aurar. Na farko ya aurar da su
Shahidah da Asalamiyya a rana ɗaya, duk da dai an kwashi matuƙar rikici a wannan aure dan Hajiya Yaya
cewa tai baza'a haɗa mata auren ƴa da agololi ba. Shiko yace tayi kaɗan tayi tsororo ma. Bayan dai an sha
fama dole ta haƙura akayi yanda ya tsara ɗin. Sai dai ita Asalamiyya ma nata auren bamai jimawa bane.
Dan a gida ma ta haifi ƴarta. To yanzu ko Yazeed kaɗai za'a aurar. Babban ɗansa kuma namiji, sannan ɗa
mafi soyuwa a garesa da Hajiya Yaya. Damma ALLAH ya ragewa aya zaƙinta auren ba wanda yake so bane
ba. Saboda har yanzu sam Daddy baya son wannan haɗin kawai dai babu yanda zai yi ne ya haƙura. Amma
yaci alwashin sai ya bama kowa mamaki a auren Maanal da Yazeed in sha ALLAHU.
To daga can gidan Alhaji Mamman ma dai shirin suke. Dan jikokin duka biyu nasu ne, dan haka dole
suma su taka tasu rawar da aljihunsu da kuma matsayinsu. Dan haka suka kasance cikin irin nasu shirin su
da sauran ƴaƴansu da dangi. Dan ko tafiya Dubai ta zama kamar za'ayi ta a tare ne bisa ɓangarori biyu. Ba
Hajiya Yaya da Asalamiyya da Baraka bane kawai a tafiyar harda mahaifiyar su Hajiya Yaya ɗin da kuma
wasu ƙannensu Hajiya Yayan su biyu, da harda Aunty Sabuwa amma ta zamewa tafiyar dan akwai binne-
binnen da suke son zuwa suyi a inda za'a saka amarya duk da ma Daddy ya ɓata musu tafiyar da buri wai
anan gidan su Yazeed ɗin zasu fara zama a tare da su. A yanzu hakama ana kan gyara sashen samarin gidan
da dama shine dai zaune a ciki kasancewarsa namiji tilo a baya sai yanzu da Ammie ta haifi Waleed da
Hameed. Suma acan ɗin suke amma yanzu Daddy yasa ana musu nasu ginin ata can bayan na Yazeed ɗin
kasancewar akwai fili sosai. Sai suka dawo sashen Ammie yanzu tunda ita kaɗaice. A wannan gini ma dai
sai da akai ɗan rikici, ɗan daga Hajiya Yaya har Hajiya Basariyya nunawa sukai basu yarda ba. Sai da Daddyn
yay musu kaca-kaca yace idan akwai wadda ta haifesa a cikinsu kota saya masa gidan ko suka haɗa kuɗi
suka saya to tazo ta hanashi yima yaransa wajen zama sannan suka kama kansu. Amma hakan bai hanasu
komawa gefe suna zagin Ammie ba da aibantata.
___________★
Shine ya fara fita a elevator ɗin, hakan yasa AS da driver rufa masa baya cikin hanzari. Cikin takaici da
ƙunar zuciya Maanal ta raka bayansu da harara kafin itama ta fito tana jan tsaki. Maimakon tabi bayansu
sai kawai ta samu waje ta zauna anan wajen elevator ɗin. Tsahon mintuna goma sai ga AS ya dawo wajen.
Da mamaki yake faɗin, “Ina can inata tunanin inda kika maƙale ashe kina nan.”
Ɗan ɗagowa tai kawai ta kallesa batare da tace dashi komai ba. Shima sai ya kama kansa dan ya fahimci
Maanal irin mutanen nan ne masu masifar miskilanci da kame kai. Har office ɗin Directors Mustapha ya
kaita, sai dai sun samu baya ciki da alama ya ɗan fita. Wajen zama ya nuna mata yana faɗin, “Ki jirasa anan
duk inda yake nasan baiyi nisa ba”.
Kanta kawai ta iya jinjina masa. Shima sai ya juya ya fita abinsa. Bayan futarsa ajiyar zuciya ta ɗan sauke
da numfashi mai ƙarfi. Dai-dai lokacin idanunta suka sauka akan hotuna huɗu da aka saka daga can saman
saitin inda kujerar mai office ɗin take. Hoton farko shugaban ƙasa ne a jiki, sai Ministan Abuja. Hoto na
biyu AA Darma ne da yay wani kalar masifar ƙyau, sanye yake cikin wasu shegun suit baƙaƙe da adon gold
a jikinsu mai matuƙar ƙyalli, yaɗan zauna a saman kujera mai tsaho ɗin nan, sai ya kasance kamar ya zauna
a karkace ƙafarsa ɗaya ya sakko ƙasa sosai ɗayar na daga jikin ƙarfen da akaima kujerar kwalliya.
Takalminsa baƙi da kwalliyar gold shima. Bai saka rigar suit ɗin ba, yana riƙe da ita ne kawai da hannunsa
na dama dake sanye da agogo kalar gold a saman kafaɗarsa, sai farar long sleeve shirt ɗin data sauna
ɗaran a jikinsa ta fiddo da girman jikin dake a buɗe. Ya saki wani mayataccen murmushi daya sakata
ƙurama cikakkiyar fuskarsa mai kwarjini da adon gashi ido. Idanunsa sanye da farin gilashi da tun ƙuruciya
tasan yana sakawa. Sun wani haska oily idanun nasa da suke farare tas kamar an watsa musu madara
tsabar yanda suke ƙyalli da ɗaukar idanu....
Kaɗan Director Mustapha ya ɗan bubbuga desk ɗin, dan sai sallama yake amma babu alamar tasan da
shigowarsa. Numfashi ta ɗan ja ta fesar cike da kame kanta da vasarwa ta dawo hayyacinta. Murmushi ya
ɗan yi a ƙasan ransa yace (Boss Sarkin sa'a. Akoda yaushe cikin kama zuciyar ƴammata yake).
Ita kam kicin-kicin ta sake yi da fuska sannan ta shiga gaishe da Director ɗin. Ya amsa mata da kulawa
tare da mata barka da zuwa. Kanta kawai ta jinjina masa shi kuma yakai zaune yana ɗaukar file ɗinta ya
shiga dubawa. Sai lokacin ta sake bin office ɗin da kallo daki-daki, idonta ta ƙarasa saukewa akan hoton AA
ɗin, sai kuma ya janye ta maida kan ɗayan hoton dake kusa da nasa da bata kalla ba. Mace ce sanye cikin
baƙin hijjab da niƙab, hatta idanun nata ana iya ganinsu ne kawai ta cikin sirrin farin gilashin data sanya.
Hakan yasa baka isa tantance wacece a hoton ba duk iya kallon ƙurullarka da bin ƙwaƙwaƙwafi, dan hoton
yasha editing ta yanda aka ɓadda kamanin komai.
A hankali ta taɓe baki da sake kauda kanta zuciyarta na ayyana ma maybe matarsa ce. Tunkuɗe tunanin
tayi gefe ta maida hankalinta ga Director Mustapha dake mata magana. Umarnin biyosa ya bata, babu
musu ta miƙe tare da ɗaukar hand bag ɗinta tabi bayansa. Wani office dake kusa da nashi suka shiga. Nan
ma sun sami mai office ɗin daya kasance ba bahaushe ba. Bayan sun gaisa ya amshi file ɗin hannun
Director Mustapha ya saka hannu. Daga haka suka fito. A ƙofa suka haɗu da wani matashin saurayi, cike da
girmamawa ya shiga gaida Director. Shima ya amsa masa da kulawa yana nuna masa Maanal.
“Itama Watch Designer ce, kaje da ita department naku, sit ɗin da aka shirya jiya nata ne”.
Fuskar saurayin da murmushi yana kallon Maanal ya amsa ma Director da girmamawa. Ita ko sai wani
basarwa take. Bai damu ba ya fara gaidata, sai ta amsa kamar wadda taji kunya. Shi dai director kallonsu
kawai yake yana sake jinjina miskilancin yarinyar.
Saurayin daya kira sunansa da Yaqub tun'a cikin Elevator ɗin ya gabatar mata da kansa matsayin Watch
Designer shima. Ɗan murmushi kawai Maanal ta masa. Dan ta fahimci yana da nutsuwa. Koda suka fito
anata kallonsu, bata damu ba dan ita babu wanda take kallo har suka iso rukunin su daya kasance matsayin
office. Su takwas ne, kuma duk artists ne suma ɗin, sai dai abin damuwar ita kaɗai ce mace a cikinsu.
Amma sai ta dake, dan tasan zata iya zama da kowa. Ta gaishesu tana sake ɗaure fuska ganin yanda suke
kallonta. Yayinda Yaqub ya gabatar da ita a wajensu shi dai. Suma ya shiga gabatar da su da sunayensu
ɗaya bayan ɗaya. Kafin ya nuna mata wajen zamanta dake a farko. Sun mata maraba da zuwa cikin farin
ciki, itama sai ta ɗan musu murmushi kaɗan. Daga haka takai zaune tana dudduba komai nata dake a
wajen. Batare data damu dasu ba kuma wayarta ta ɗauka ta shiga ɗaukar komai na iya wajenta hoto,
Ammie ta turamawa, alamar wayar a hannun Ammie take mintuna biyu ba'a ƙullaba sai ga video call ɗin
Ammien ya shigo. Murmushi mai sanyi Maanal ta saki tana mai gaggawar amsa kiran sai ga Ammie tar-tar
ta fito. Cikin murmushin farin ciki Maanal tace, “Uhm kaga amaryar Daddy”.
Daƙuwa Ammie tai mata itama tana murmushin ta ce, “Ungo naki nan ja'ira yau kuma nice bar
tsokanrki”.
Karo na farko Maanal ta sanya dariya, abinda kakan daɗe a yanzu baka gani ba a tare da ita. Duk ko sai
samarin suka shagala suna kallonta duk da su basa ganin Ammie sabo a desk ta ɗaura wayar. Ita ko cikin
rashin damuwa da wanzuwar su a wajen tace da Ammie, “Tom yi haƙuri Hajiya Ammie na. Ina fatan kin
tashi cikin aminci da ƙoshin lafiya tare da farin ciki a wannan rana ta laraba ranar samu inji Nene”.
Sosai murmushin Ammie ya sake ƙawatuwa. Da kulawa ta ce, “Alhamdullah Auta. Ya ƙarfin jikinki? Ya
kuma sabon office?”.
“Alhamdullahi Ammie na warke abuna. Sabon office kuma gashi ki sanya masa albarka daga bakinki mai
tsarki”. Tai maganar tana miƙewa da wayar a hannu ta maida back camara tana haska mata ko'ina na office
ɗin, sai dai koda wasa bata yarda ta hasko samarin nan ba. Sosai Ammie ta shiga yabawa da sanya albarka.
Ta kumayi addu'oi sosai ga autar tata. Sannan suka ɗan yi hira sukai sallama tace ta fara aikinta. Fuskarta
da murmushi ta ajiye wayar, ita kaɗai tasan irin tari-tarin ƙaunar da takema wannan baiwar ALLAH.
Mahaifiyarsu dabance a cikin daban ɗin da bazai ƙididdigu a zukatansu ba. Fatansu dai ALLAH ya ƙara mata
lafiya da nisan kwana masu albarka. (Tare da iyayenmu baki ɗaya. Ka gafartama wanda muka rasa ka yafe
musu KURAKURANSU😭 damu da muke raye baki ɗaya).
Jan kujerar tata tai har zuwa gaban kantar da aka ajiye musu a office ɗin dan kusan da ita ma aka zagaye
wajen. Komai na kayan zane-zanen da zasu iya buƙata akwai a wajen. A haka ta zazzaɓo duk abinda take
buƙata a lokacin ta sake burko tayoyin kujerar ta dawo da ita mazauninta. Sosai ta ringa ƙoƙarin ture komai
a ranta ta maida hankalinta ga fara abinda ya kawota duk da tana ji a jikinta sauran abokan aikinta
hankalinsu na a kanta ta wani sharesu tamkar ita ɗaya ce a wajen.
Wani zanen Designs na agoguna data ƙirƙira yanzun nan a kanta ta fara cike da ƙwarewa. Cikin
ƙanƙanin lokaci ya haɗa su tsaf su biyu kamar ka saka hannu ka ɗauka daga takardan. Bayan ta gama zana
su a dunƙule sai kuma ta koma zana ɓangare-ɓangare ɗin jikinsu kowanne tana saka masa suna da amfanin
da zai yi a cikin agogon. Hakanne ya ja mata lokaci sosai dan har ƙarfe ɗayan rana. Jin ana kiran sallar zuhur
daga masallacin cikin companyn ya sata sauke ajiyar zuciya da ajiye kayan aikin nata ta miƙar da hannunta
da ya ɗan sage da ambaton sunan ALLAH.
Miƙewa tai zuwa window ɗin office ɗin ta leƙa batare data ma kowa magana ba, dan daga wajen ana
hango masallacin. Hango ma'aikata tayi nata fita zuwa ƙatuwar harabar companyn. Ganin mazansu da
matansu ne yasa ta fahimci masallacin harda mata kenan. Dan wasu ma na ƙoƙarin shigane yayinda wasu
suka kasance rukuni-rukini suna hirarsu. Sai wasu dake alwala ta can ƙarshen katangar inda aka tanada
domin hakan. Huci taɗan furzar daga bakinta tare da barin wajen, dai-dai suma su Yaqub na miƙewa.
Sauran fita sukai gulma fal bakinsu, yayinda shi kuma Yaqub yazo inda take.
Shine ya sanar mata tazo suje salla. Kanta kawai ta jinjina masa ta baro wajen ALLAH ya sota ta taho da
hijjab kasancewar yau ma shigar Abaya ce a jikinta ƙirar Dubai ruwan ƙasa. Hijjab ɗin ta buɗe ta saka bayan
ta zame hularta da ɗan kwalin abayar data naɗo a kanta ta ajiye saboda hijjabin ya rufe mata gashinta
sosai. Hankalinta kwance kuma kanta tsaye ta fito a office ɗin daga ita sai wayarta kawai a hannu. Kusan
duk an fice ma, dan wajen yayi tsitt, dan haka a gaggauce ta nufi elevator jin za'a tada sallar kasancewar su
suna a 4th floor ne. Bata gama dai-daita tsaiwarta ba kawai taji shigowar mutum babu ko sallama. Dan
haka ta ɗago manyan idanunta domin ganin wane sallamemmen ne haka........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭_*
[2/11, 8:42 PM] Maryam anas: *_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
2️⃣8️⃣2️⃣8️⃣
.......Saurin janye idanun nata tai ƙirjinta na wani masifar dokawa. Sai dai ta wani dake a zahiri yayinda
fuskarta ke sake komawa ciɗin-ciɗin fiye da yanda tashi take. Boss ne da kansa ba wani ba. Wato AA
Darma, da alama shima ya makara fita sallar ne, dan illahirin fuskarsa da hannayensa da ƙafarsa dake
sanye da slippers daya saka dan ba takalman da yazo dasu a ƙafarsa bane cover shoes sai nason ruwa suke
yi. Elevator na tsayawa itace tai saurin fara ficewa dan harga ALLAH jinta take kamar an matse a cikin rami
tsabar yanda ya cika ko'ina da kwarjininsa. Da kallo ya ɗan bita, sai kuma miya tuna oho yay saurin janye
idanunsa shima yana fita daga elevator ɗin.
Dukansu basu samu raka'ar farko ba. Koda aka idar da sallar mafi yawan ma'aikatan sun wuce kitchen
ne kai tsaye, dan ana musu abincin rana a wajen harma dana safe. A manyan dai ba kowa ne ke nufar
kitchen ɗin ba sai wanda yaso hakan kasancewar suna da damar sakawa a kawo musu har office. Manaal
ma daba gama sanin tsarin tai ba duk da an bata komai a rubuce tun a ranar interview karantawa ne batai
ba office ta koma. Hankalinta a rarrabe sai dai tana iya ƙoƙarin ta na ganin ta saita kanta ta buɗe lunch box
ɗinta ta fidda abincinta ta hau ci tana cigaba da sarrafa computer ɗinta domin maida aikin zanen da tayi a
ciki. A haka a shiririce ta gama shigar da komai kafin ta naɗesa a flash drive ta ajiye. Koda an buƙacesa a
wajen meeting da shi zatai amfani. Knocking ƙofar akayi, batare da ta canja daga yanda take ba ta bada
iznin shigowa dan ita kaɗaice har yanzu su Yaqub babu wanda ya dawo. Wata budurwa ce da bazasu wuce
sa'anni ba. Sanye take da skirt da riga na atamfa sai ɗan mayafi data yana. Cikin girmamawa ta gaishe da
Maanal ɗin. Amsa mata tai da kulawa. Hakan sai ya saka yarinyar farin ciki dan yanzu ake gulmar Maanal
ɗin a ƙasa cewar dagani zatayi girman kai, sai kuma ita tazo taga ba hakan ba yanzu.
“Sunana Mabaruka Rabi'u. Ina ɗaya daga cikin Sales and Marketing Department. HOD ne yace a sanar
miki ana buƙatarki a ƙasa idan babu damuwa”.
Cikin ɗan sakewar fuska da ba murmushi take ba Maanal ta ce, “Okay sister Mabaruka ba damuwa gani
nan tafe”.
Murmushi Maburaka ta mata tare da sake ɗan rissinawar girmamawa ta furta, “Na barki lafiya”. Daga
haka ta fice a office ɗin. Ajiyar numfashi Maanal ta ɗan sauke, sai kuma ta shiga tattara tarkacen kayan da
taci abinci ta maidasu a lunch box ɗin. Ruwa tasha ta ɗan gyara fuskarta sannan ta miƙe ta fice a nutsenta
daga ita sai wayarta a hannu. A First floor ta samu kusan dukkan ƙananun ma'aikatan harda waɗanda ba
nan ɗinne mazauninsu ba. Sai dai da'alama duk an tattarasu anan ɗinne dan har su Yaqub ma suna a wajen
ashe. Duk da cika mata idon da sukai haka ta dake ta gaishe da HOD dake ta faman sakar mata murmushi.
Yana ɗaya daga cikin wanda sukai mata interview. Amsa mata yay da kulawa, kafin ya juya ga ma'aikatan
yay sallama. Duk amsawar sukayi duk da kuwa ba dukane musulmai ba a wajen. Ɗan juyowa yay tare da
nuna musu Maanal cikin harshen turanci ta ce. “Wannan itace sabuwar _Watch Designer_ ɗin Mawaad
Company da aka sake ƙaro mana in sha ALLAHU, zatai muku introducing kanta”.
Tafi suka shiga yi gaba ɗayansu. Hakan yasa Maanal ɗan sakin murmushi tana binsu da kallo, sai da suka
lafa sannan ta gyara tsaiwarta cike da nitsuwa ta furta, Sunana Maanal Habeeb Giro. Junior Watch
Designer kamar yanda aikina HOD ya faɗa. Ina fatan zan samu haɗin kai da yarda daga gareku baki ɗaya”.
“In sha ALLAHU!!”.
Suka faɗa cikin haɗa baki. Murmushi ta sakar musu a karo na biyu mai matuƙar taushi. Sai kuma ta haɗe
hannayenta waje guda ta sake furta, “Ina mika godiya a gareku da fatan alkairi baki ɗaya. ALLAH ya bamu
ƙwarin gwiwar sauke hakkin dake kayinmu baki ɗaya”.
Nan ma sun amsa mata da amin. Daga haka HOD ya ɗan ƙara mata bayani akansu. Kafin ya sallamesu
kowa ya koma kan nasa aikin. Ita kuma suka nufi elevator tare da shi. Sai faman zuba mata surutu yake ita
dai batace komai ba sai ɗan murmushi da take masa na karar haɗuwar farko. Conference room suka nufa
kai tsaye daga nan. In da ta sami dukkanin shugabannin da alama su ake jira ma a wajen. Wajen zama duk
suka nema, a dai-dai kuma lokacin CEO ya shigo AS ɗinsa biye da shi. Duk miƙewa sukai alamar
girmamawa, sai da ya zauna AS ɗinsa ya ajiye masa kayan hannunsa gabansa sannan ya ɗan ɗago ya
dubesu. Zaunen suka kai suma a nutse, daga haka room ɗin yay ɗan shiru na kusan mintuna uku kafin ya
ajiye tab ɗin hannunsa da yake sarrafawa yay gyaran murya yana kallonsu cike da dakewa da nutsuwarsa.
Suma sake nutsuwar sukai da maida hankalinsu garesa. Banda Maanal da tun kallon farko data masa a
sanda yake shigowa ta ɗauke kanta bata sake ba. Gaba ɗaya jinta take a takure a wajen dan su biyu ne
kawai mata. Sallama yay musu kafin ya sauke dubansa ga tab ɗin gabansa ya fara magana acan ƙasan
maƙoshi. “Wannan taro ne daya haɗa ɓangarori guda biyu, wato na shugabanni da kuma ƙirƙira da zane na
wannan company. Wato Executive Team da kuma Design and development. Kafin kai tsaye mu fara abinda
ya kawo mu akwai sabuwar staff data shigo cikinmu zai ƙyautu ta gabatar da kanta anan”.
Ji Maanal tai kamar ta kai masa naushi dan haushi, amma sai ta dake taƙi koda motsi sai da CTO dake
gefenta yay mata magana ƙasa-ƙasa. “Sistet Maanal”.
Komai batace ba ta miƙe cike da kamewa ta furta, “Sunana Maanal Habeeb Umar Giro. Junior Watch
Designer in sha ALLAHU”.
Sunyi welcoming nata baki ɗaya tare da mata fatan alkairi. Bayan ta koma ta zauna ya cigaba da faɗin,
makasudin shi wannan zaman akan sabon project namu ne in sha ALLAHU. Wasu sun san da shi wasu basu
sani ba saboda rashin samun zaman meeting da ba'aiba a wancan satin gaba ɗaya. Akwai Companyn da
zamu fitar ma sabon agogo, sun kuma bamu zaɓi kafin mu sake zama dasu. Dan haka Design and
development ko kuna da wani sabon design da zaku gabatar mana mu duba?”.
Bayan Maanal akwai Watch Designers Directors har uku a wajen, sai dai dukansu kowanne nada iya
limit ɗin aikinsa ta yanda baya shiga aikin wani. Hakan yasa ɗaya daga cikinsu ɗagowa ya ɗan dubi Boss
ɗin. “E to Sir bamu san ko yaya tsarin project ɗin zai kasance ba. Sai musan a cikinmu wazai bada sample”
Kansa ya ɗan gyaɗa, sai kuma ya kai dubansa ga Sales and Marketing Manager. Da sauri ya miƙe dan
yasan minene ma'anar kallon. Bayani yay a taƙaice, Dan haka sai duk suka maida hankalinsu ga Director
Steven. Kansa ta gyaɗa shima tare da maida kallonsa ga Maanal, suma sauran duk sai suka koma kallonta.
Yanda suke kallon natane ya bata mamaki, kafin ta nema ƙarin bayani Director Steven ya ce, “Wannan
aikinki ne Sister Maanal. Idan kinada wani sample na zane a ƙasa company na buƙatar gani, idan kuma
babu zaki iya neman lamanin samarwa”.
Gaba ɗaya sai Maanal taji ma kamar zata daburce. Amma ta shiga ambaton ALLAH tare da aro jarumta.
Cikin ƴar dakiyar da nutsuwar data azama kanta ta dole ta bata ta jinjina ma Director kanta. Sai kuma ta
ɗan kallesu itama ta fara bayani. “Zan iya gabatar da wanda ke a hannuna ɗin idan basuyi ba sai na sake
wasu sabbi”.
Cikin gamsu duk suka gyaɗa mata kai, kafin boss ya gama shan ƙamshinsa batare daya kalleta ba ya
furta, “Zaki iya nunawa”.
Bata tanka ba, sai dai ta miƙe hannunta ɗauke da flash drive data naɗe zanen ɗazun da tayi. Amsa
Director Steven yayi a matsayinsa na shugaban sashenta, ya nufi ƙaton television dake kusan bango guda a
room ɗin yay connecting, atake ɗan tambarin data saka na farko mai ɗauke da zanen agogo mai ƙyau da
zanen fuskarta a tsakkiya ya bayyana. Remote ɗin Director Steven ya miƙa mata, dole ta fito daga inda take
tsaye ta koma gaban tvn. A nutsenta ta fara danna hoto na biyu ya fito, agogone mai ƙyau da tsari matuƙa
duk da kasancewar a zane yake. A take duk suka shiga ambaton, “Woow!! Woow!!” a hankali. Shi dai boss
kaimai baice ba, amma fa ya zubama hoton idanu yanda ya kamata, bayani tayi cikakke akan agogon da
tsarinsa da nauyinsa. Sai kuma ta koma nuna sassan jikinsa da sunayen data basu da yanda yakama ace
ingancinsu ya kasance. Da ƙarshe tai bayanin yanda agogon zai iya buƙatar ingantaccen aiki kafin fitar da
shi. Tafa mata suka shigayi tamkar conference room ɗin zai buga shima. Dan har ga ALLAH tayi matuƙar
gama birgesu, tayi dukkan bayanin da har sauran ɓangarorin zasu iya yi. Ashekaru kaf ɗinsu babu wanda
bai bata fin shekara goma zuwa ashirin ba, dan itace ƙarshen ƙanƙanta da ƙarancin shekaru a cikin nasu,
hatta da ɗayar macen zata iya girmar Shahidah ma balle ita. Taji daɗin yanda suka yaba mata duk da shi
mai gayya da aikin baice komai ba dai. Sai da duk suka lafa itama ta dawo ta zauna a nata mazauni kafin
yay ƴar gyaran murya.
“Zamuyi nazari akan wannan ɗin, amma WD Maanal zata iya samar mana da wasu samples kamar uku
bayan wannan daga nan zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu. Sai ku haɗasu a sake tattaunawa”.
Duk sun gamsu da hakan. Dan haka ba'a wani sake jan zancen ba taron ya watse. Shine ya fara ficewa a
room ɗin AS ɗinsa biye da shi. Duk miƙewa suma sukai hankalinsu akan Maanal suna sake jinjinama
ƙoƙarin ta da ƙarfafata. Itako sai wani ɗan karen daɗi take ji kamar ta ciji uwawunta. Ta ƙara ta fita a wajen
ta kira Ammie ta bata labari, kai har RK sai yasha labari yau....
Koda Maanal ta koma office zaman wasu sabbin samples na zanen ta fara dan babu wasa batare data
kula kowa ba. Garama Yaqub ya mata sannu da zuwa. Tayi nisa a aikin nata akai mudu knocking ƙofa.
Batare data ɗago ba ita dai taji sauran na magana da shi. Saurayine kamar su Yaqub da zai iya girmarta ita
kam a shekaru, amma kasancewarsu oganninsa cike da girmamawa ya gaishesu. Sai kuma ya maida
hankalinsa kan Maanal. Hakanne ya sata ɗagowa ta ɗan kallesa. Duk da tayi mamaki sai ta danne, ta amsa
masa da kai. Bai damuba ya cigaba da faɗin, “Sister Maanal kinada visitor”.
“Visitor?”.
Ta maimaita da mamaki. Sake tabbatar mata da hakan yay ta ha hanyar jinjina kansa. Ta ɗan yi shiru
kamar mai nazari tana wasa da pencil akan lips ɗinta sai kuma ta ce, “Okay ina zuwa”.
Da girmamawa ya amsa mata da, “Ai kamar ɗan gida yake. Bari na masa iso”. Bai jira amsarta ba ya juya
ya fita. Ba'a rufa mintuna biyar ba aka sake knocking ƙofar. Zamanta ta gyara da veil ɗinta, yayinda hankalin
su Zaharadeen duk yana akan mai shigowar. Yana buɗe ƙofar ƙamshin turarensa na rige-rigen fara iso mata
a hanci, hakan yasa ta ɗan ɗago idanu ta kallesa. Murmushi ya sakar mata yana jingina da ƙofar tare da
harɗe ƙafafunsa da hannayensa a ƙirji. Sai kuma ya laluba aljihunsa ya ciro wayarsa ƙirar kamfanin
Samsung mai ƙyawu da tsada ya shiga mata hotuna. Hararsa ta ɗan yi tana mai girgiza kanta ta maida ga
abinda take yi. Sai da ya gama dan kansa kafin ya kai duƙe ya ɗauki abinda ya ajiye a ƙasa yana ƙarasa
shigowa da faɗin, “Oh oh my queen Kinga kuwa yanda kujerar nan tai matuƙar dacewa da ke. Kin gama
cika Watch Designer Maanal ɗinki Tawajena. Dan haka ina tayaki murnar shiga sabon Office. Amin afuwa
dana kasance a late, tun safe naso nayi hakan uziri yasa ban zauna ba na koma asibiti. Naso tahowa da
rana hakan bai yiwu ba kuma dai”.
Ita dai kallonsa kawai take yana tsiyaya surutunsa kamar yanda sauran ma ke kallonsa suna murmushi.
Hannu ya shiga basu, suna amsa da sauri da kuma girmamawa dan sun san yana da wani babban matsayi
da kima a companyn. Dai da ya gama gaisawa da su ya maido hankalinsa kanta yana fiddo cake mai ƙyau
daga cikin kwalinsa. Sai kuma ya tsitstsira abu a kansa kamar wata mai shirin hure birthday cake ya kunna
masa wuta. Ɗauka yay ya zagaya ta inda take ya ajiye a gabanta sosai bayan ya tattare kayan zanen dake a
gabanta ya ɗauke su gefe........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
2️⃣9️⃣2️⃣9️⃣
.........“Bismillanku”. Ya faɗa idonsa akansu Zaharadeen. Sai kuma ya koma ga ƙofa yana faɗin, “Kuma ku
shigo”.
Mamakine ya kamata ganin ma'aikatansu kusan su goma sun shigo harda AS ɗin Boss. Gaishesu sukai
saboda kusan dukansu suna a sama da su. Da kai kawai ta iya amsa musu ita dai saboda al'ajabin RK. Daga
haka ta juyo tana masa wani kallon. Ganin yanda ta zuba masa manyan idanun nata masu rikitashi ya wani
langaɓe kansa da marairaice fuska yana ɗan duƙowa gab da ita ta yanda ita kaɗaice zata iya jinsa a
maganar da zaiyi. “Please ki daina min irin kallon nan kina rikita min lissafi na ne”.
Harara ta ɗan sakar masa tare da janye idanun gaba ɗaya. Babu yanda ta iya da fitinar RK dole ta hure
kamar yanda yake buƙata, dan ya tabbatar mata idan batayi hakan ba babu inda zaije yau. Ganin yaja
kujera ya zauna ga mutane ya cika musu office da su ya sata hurewar kawai dan kaɗan kenan daga aikinsa
ya zauna ɗin. Cake ne dai duk yanda yayi taci ta gutsira ta bashi a baki ƙi tayi, sai ma tai kicin-kicin da fuska
ta yanda dole ya haƙura dan baya son yaga ta haɗe masa ƙyaƙyƙyawar fuskar nan tata damuwa yake shiga.
Haka dole da kansa ya gutsira yaci ya miƙama wanda ya gayyato da su Yaqub dake a office ɗin kowa ya
yanka yasa a baki. Daga hakan nutsuwa yay sosai yay mata addu'oin fatan alkairi da nasara a wannan aikin,
ita harma hakan yaso bata mamaki, yayinda sauran ke amsawa da amin.
Bayan ficewar kowa ya wani zabga tagumi yana kallonta. Itako ta sake maida hankalinta ne a aikinta. Sai
da taji kallon nasa na neman cutar da ita ta ɗago ta kallesa tare da sakar masa ƴar harara, sai kuma tai
masa nuni da su Yaqub da ido. Murmushi ya saki mai ƙayatarwa da gyara zamansa. Ita kuma ta maida
kanta yay ƙoƙarin dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta.
“Maanal”.
Har tsakkiyar kanta taji yanda ya ambaci sunan nata. Kodan ba cika kiranta da sunan yay ba akoda yaushe
oho. Sake ɗagowar tayi ta dubesa batare data amsa ba. Bai damuba ya cigaba da faɗin, “Maanal dan
ALLAH ki iyakance min wahalar nan mana, na isa aure fa, ga kuma mata a kusa dani miya rage kuma dan
ALLAH?”. A hankali yake maganar yanda ita kaɗai ke jinsa, duk da kuwa su Zaharadeen sarakan gulma sun
baza kunne amma basa jiyo komai.
Lips ɗinta ta ɗan cije zuciyarta na mata nauyi, (miyyasa su basa fahimta ne, miyyasa bazasu gane ba.
Ita fa Maanal, wannan Maanal ɗin da suke gani gaba ɗaya a yanzu babu zuciya a ƙirjinta, in dai zuciyace ta
soyayya ta ta jima da mutuwa......)
“Maanal!!”.
Ya sake katse mata tunani, yanzu ma bata amsa ba sai dai ta janye idanunta da suka cika da ƙwalla daga
kansa. Aikinta ta cigaba da yi tana ƙoƙarin haɗiye hawayen. Shima sai yay murmushi kawai tare da miƙewa
gaba ɗayansa.
“Ƙarfe nawa zaki tashi?”.
Batare data ɗago ba dan bata son yaga yanayinta ta ce, “Bazan iya cewa ba, saboda ina son kammala
aikin nan duka a yau ɗin”.
Ɗan jimm yay sai kuma ya jinjina kai da faɗin, “Okay bari na kiraki kawai, ko kuma zuwa six, I will come
back kawai”.
“Okay thanks”.
Ta faɗa a taƙaice. Shima sai ya ɗan murmusa kawai ya juya ya fita abinsa yana ma su Zaharadeen dallama.
Fitarsa bai fi da mintuna biyar ba kira ya shigo a wayar gabanta. Koda ta ɗaga sai ta samu AS ɗin Boss ne,
wai boss ɗin na son ganinta a office ɗinsa. Idan tace kaɗan ya rage zuciyarta ta wantsalo ta baki kar kuyi
mamaki, ta jima shiru da kan wayar a kunnenta bata iya ta ajiye ba. Sai zuwa can ta kife ta da ƙyar ta miƙe
cikin ƙarfafa kanta. A dakenta ta isa office ɗin, bayan sun gaisa da AS ya miƙe yana faɗin, “Bismillah”. Komai
batace masa ba, yana gaba tana biye da shi har cikin office ɗin. Karo na farko kenan data shigo office ɗin.
Ƙaton gaske ne, ya kuma ƙayatu da abubuwan more rayuwa matuƙa gaya. Tamkar ba office ba komai dake
a cikinsa fari ne ƙal, hatta da kujerar zamansa da desk kai komai da komai. Sai kuma Mable's ɗin da aka
shimfiɗa a ƙasan ya kasance baƙi wulik tamkar wata ajiyayyar kwalba. Ƙamshi kam ba'a magana, ga ac
kamar an ƙuresa da gayya. A cikin sakanni da basu wuce biyar ba taima office ɗin wannan kallon.
Yana zaune a mazauninsa hankalinsa gaba ɗaya nakan computer ɗin gabansa, yayinda hannunsa ke
danna keyboard dinta, na haggu kuma riƙe da document. Yanzu kam ya cire rigar saman suit ɗin nasa sai ta
cikin kawai. Duk da shigowar tasu bai ɗago ba balle ya nuna yasan da su. Cike da girmamawa AS da ya ɗan
matsa kusan gaban desk ɗin sosai ya ɗan rissina tare da faɗin, “Sir gata tazo”.
Sai da ya ɗan ja sakan kusan biyu kafin ya ɗago mayan fararen idanunsa da ke nuna matuƙar gajiya da
aiki ya sauke akan AS ɗin nasa. Sai kuma yay luu da idanun ya ɗaukesu daga kansa ya maida ga computer
ɗin tare da ɗan kai hannu ya gyara gilashinsa. A can ƙasan maƙoshi ya furta, “Zaka iya tafiya”.
Sake rissinawar girmamawa AS yay ya juya ya nufi ƙofa. Sai da yazo saitin da Maanal ke tsaye tayi kicin-
kicin da fuska matuƙa a hankali ya furta, “Sister Maanal bismillah ki ƙarasa”. Daga haka ya fice. Yitai kamar
bazata ƙarasa ɗin ba, dan ta ɓata fin minti ɗaya kafin ta ɗaga ƙafarta da ƙyar. Koda tazo inda yake
maimakon ta zauna sai tai tsaye abinta. Shima yi yay tamkar ya manta da ita sai aikinsa yake kawai hankali
kwance. Sunja fin mintuna uku a haka kafin ya ɗago kansa a hankali ya wani zuba mata idanu, sai kuma ya
sake ɗaure fuska fiye da yanda ta shigo ta samesa. Cikin ƙausasa harshensa, da tsaurara kalamansa ya
furta, “Ba'a baki tsare-tsare da dokin wannan companyn bane?”.
A yanda yay maganar yasa ta ɗago nata idanun ta kallesa. Kallon ido cikin ido suka zubama juna, fin miti
ɗaya kafin ta janye nata, sai kuma ta canja yanayinta, cikin yanayin girmamawa irin na oga dana ƙasa ta
furta, “Am sorry Sir, an bani tun ranar farko da nazo”.
Kamar wanda yaji haushin yanda tayi ɗin sai ya wani cije lips tare da ɗauke kansa a lokaci guda. Buɗe-
buɗen document ɗin gabansa ya fara yi, sai da ya sake jan minti ɗaya a hakan, sannan ya cigaba da magana
batare da ya kalleta ba. “Wannan Companyn ba lambu soyayya bane ko club. Idan buƙatar ganinki yake ko
zuwa gareki ai yasan inda kike. Karya sake zuwa min nan da shirme in ba haka ba zan ɗauki mataki a kanku
ku duka zaki tafiya”.
Tafasa zuciyar Maanal take, tafasa irin mai yunƙurowar nan daga ƙirji zuwa maƙoshi har ka dinga jin
turirin a cikin bakinka. Karo na biyu ta ɗago ta dubesa kamar zatayi magana sai kuma ta haɗiye, shiru ta
sake yi tana daidaita kanta. Zuwa wasu sakanni kanta a duƙe da girmamawa ta ce, “Kayi haƙuri sir, in sha
ALLAH zamu kiyaye. Na barka lafiya”. Daga haka ta juya ta fita abinta. Wani irin wurgi yay da file ɗin
hannunsa tare da dukan desk da ƙarfin masifa, sannan yay baya ya kwantar da jikinsa gaba ɗaya a kujerar
yana furzar da huci masu masifar zafi...
____________★
“Abuja?”.
Daddy ya faɗa da wani irin mamaki ƙarara a fuskarsa yana ƙarema Huznah kallo daga sama har ƙasa.
Cikin dake yanayin tsoronta dake neman bayyana ta jinjina masa kai.
“Eh Daddy, dan ALLAH ka barni naje sati ɗaya kawai zanyi. Kaga tunda muka duba Maanal sau ɗaya babu
wanda ya sake komawa a cikinmu. Shiyyasa nake son naje na sake dubata na kuma sada zumunci kodan su
Shahidah su cirema kansu tunanin dan bakai ka haifesu ba shiyya bama son zumunci da su”.
Rasama abinda zaice mata Daddyn yayi, sai kawai ya zuba mata idanu sosai fiye da farko. Shi ba
mazaunin gida bane kam koda yaushe, amma yana hankalce da abubuwa da yawa da suka shafi gidan nasa
da iyalansa baki ɗaya, zai iya cewa ko lokacin auren su Shahidah a kaf ƴaƴansa idan ka cire Yazeed babu
wanda yay ma su Shahidah rakkiya gidan miji, a lokacin ma su duka anan Kaduna aka ajiyesu, dan daga
bayane ita Shahidah suka koma Abujan sakamakon ƙarin girma da mijinta ya samu.....
“Uhm Daddynsu dan ALLAH kada ka kawo komai a ranka..” Hajiya Basariyya ta faɗa cikin son kauda ma
Daddy hankali, dan duk tattaunawar tasa da Huznah itama tana a falon kasancewar girkinta ne, juyowa yay
yana kallonta dan haka ta sake marairaice fuska ta cigaba da faɗin, “Nasan zakai tunanin abubuwa da yawa
a ranka game da hakan, sai dai ka tuna al'amarin UBANGIJI yafi na kowa, shi kuma mai canja kowa ne a
lokacin da yaso, eh tabbas da anyi kuskure, sai dai abinda ya faru a ɗan tsakanin nan yasa na koyi darasi da
yawa, sannan ina da burin naga na gyara kuskurena ni da yarana duka. Dan ALLAH ka barta taje, na baka
tabbacin in sha ALLAHU ba zaka ji komai mara ƙyau ba sai daddaɗa.”
Shi Daddy ma rasa abinda zaice yayi, ga uwar da ƴar sun wani tsatstsaresa da idanu. Yafi mintuna uku a
haka kafin yaja numfashi ya fesar, cikin ɗan jinjina kai yace, “Kije zanyi tunani”.
Jiki a sanyaye Huznah ta miƙe tana masa godiya. Koda ta fita sai Hajiya Basariyya ta sake fuskantarsa,
cikin kwantar da murya da daɗin baki taita tsara masa magana, tun bai maida hankali gareta ba har ya
nutsu yana saurarenta. Sai dai amsar da taso ji bai bata ɗin ba a wannan daren. Da safe kamar yanda ta
saba bayan ya baro massaci sallar asuba, kasancewa baya shigowa da wuri sai gari yay shaa ya wuce
sashen Hajiya Yaya, haka yake yi a kowacce safiya in dai yana gida zai shiga ya duba kowacce a sashenta,
hatta mai girgi yana shiga dan ganin lafiyar yaransa. Bayan ya koma nasa sashe kuma duk su bishi su
gaishesa.
Daga sashen Hajiya Yaya na Hajiya Basariyya ya shiga, duk kuwa da ita tana nashi sashe, bai wani ja
lokaci ba ya wuce na Ammie. Kamar yanda ya sani ya sameta zaune tana azkar itama. Dan sam bata barcin
safe. Zama yay daga bakin gadonta daya sha gyara, dan tana tashi sallar asuba take gyara kayanta kafin ma
ta shiga toilet. Cikin nutsuwarta da dukkanin ƴaƴanta suka gada ta ajiye littafin hannunta ta juyo tana
gaishesa. Da kulawa ya amsa mata fuskarsa da ɗan murmushi, itama murmushin ta sakar masa kafin ta
miƙe, fita tayi, babu jimawa ta dawo ɗauke da ƙaramin tray da kofi a samansa daketa tururi. Rissinawa tai
ta miƙa masa, ya ɗauka yana murmushi da faɗin, “ALLAH yay miki albarka ke da zuri'arki baki ɗaya”.
“Amin ya rabbi tare da kai da zuri'arka kaima”. Ta amsa masa da girmamawa. Ba wani abu bane shayi ne
mai ɗan karan daɗi na wasu itatuwa masu muhimmanci da take dafa masa safe da yamma. Idan ranar
girkinta ne takan basa, idan ranar da ba girkinta ba ne kuma idan ya shigo da safe yakan sha anan, da
yamma kuma taba yara su kai masa ko idan ya shigo yimusu sai da safe. Da farko an ɗauki rikici akan
wannan bada shayi tsakaninsa da sauran matansa, dan sai da suka bi kwaf-kwaf suka gane abinda ke
sakashi jimawa a sashen Ammie ɗin a duk sanda zai shiga da nufin gaisuwa. Rikici yay rikici Ammie tace ya
raba musu kayan shayin kowa ya dinga dafo masa a ranar girkinsa. Badan yaso ba yayi hakan, sai dai baya
jin kaf ɗin su sunyi masa sau bibbiyu suka ɓarar wai su gaskiya bazasu iya wannan wahala ba, ace daka yi
sallar asuba sanda zaka koma ka huta ka wani tafi dahuwar shayi kitchen, daga nan aka samu maslaha
Ammie jurau ɗin ta cigaba da dafa masa.
Sai da ya kammala shan shayinsa tsaf kafin ya fuskanceta. Cikin tausasawa da kulawa ya dubeta tare da
kiran sunanta. Amsa masa tayi itama da girmamawa.
Ya ce, “Jiya Huznah da uwarta sun sameni wai tana son zuwa wajen ƴar uwarta Shahidah tai sati ɗaya”.
Wani irin bugawa da ƙarfi ƙirjin Ammie yayi, babu shiri ta ɗago da sauri ta zubama Daddy idanu.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
3️⃣0️⃣3️⃣0️⃣
........Shima kallonta yake tashi zuciyar na rawa. Amma a mamakinsa sai ya ga ta saki murmushi kamar
yanda ta saba. Cike da jarumtar danne dukkan abinda zuciyarta ke kissima mata ta ce, “ALLAH na gode
maka da naga wannan rana Daddyn Hameed. Wlhy bakaji yanda naji wani irin shock ba. Wannan ai abun
farin cikine a garemu, dan wata hanya ce ta samun haɗin kan yaran nan ne da muketa fata tuntuni. Ni
Huznah ta biyani ALLAH yay mata albarka”.
“Humm Asia! Shin baƙya tunanin akwai wani dalili?”.
“Haba Daddynsu wane dalili kuma? Dan ALLAH kada ka ɓatama yarinya ƙyaƙyawar niyyarta mana”.
Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi, acan ƙasan ransa yana sake jin matuƙar ƙaunarta da jin alfahari da
ita. Ita ɗin ta dabance a duniyarsa. Shi yasan da sauran ne cikin ƴaƴan Asia wani yace zai je gidansu sai anyi
bala'i kuma ace wani daliline zai kaisu. Amma ita gashi maimakon tai zaton sharri kai tsaye saboda komai a
bayyane yake sai tayi na alkairi. Jawota kawai yay jikinsa ya rungume. Murya a raunane ya ce, “Asia ALLAH
yay miki albarka kinji. Tabbas UBANGIJI yamin babbar ni'ima da samunki”.
“Nima haka Daddyn Hameed, kai ɗin babbar ni'ima ce a gareni daga cikin ni'imomin UBANGIJI na. Bani
da abin faɗa sai cigaba da godiya a garesa”.
Sosai ya saki murmushi mai ƙayatarwa, sai kuma ya sake kai hannu ya rungumota tare da ƙoƙarin haɗe
bakinsu. Da sauri ta kauce tana dariya, sai ma ta zare jikinta gaba ɗaya ta miƙe daga kusa da shi. Fuska ya
ɓata da mata nunin ta dawo amma ta maƙe masa kafaɗa.
“Shike nan ni kike ma rowa ko?”.
Murmushi ta masa kawai.
Ya ɗan ƙara jinjina kansa da nufar ƙofa yana faɗin, “Zan rama”. Ya fice. Nan ma murmushin kawai tayi, sai
da taji ficewarsa daga sashin gaba ɗaya ta koma jagwab a saman gadonta zuciyarta na wani irin harbawa.
_(Jiya Huznah da uwarta sun sameni wai tana son zuwa wajen ƴar uwarta Shahidah tai sati ɗaya)_
kalamansa suka shiga dawo mata cikin kunne da amsa kuwwa. A bayyane cikin dafe kanta ta ce, “Ya
ilahil'alamin Basariyya mi kike shirya min kuma? Ni nasan dole wannan zancen akwai wata a ƙasa”. Rashin
mai bata amsa yaa sata yin shiru ta cigaba da zancen zuci. Ta jima a haka kafin hankalinta ya dawo jikinta ta
miƙe ta shiga kitchen haɗama su Waleed abincin breakfast dana tafiya makaranta. Tana aikin tana tunani
nan ma harta kammala. Tana cikin haɗa musu suka shigo sanye da uniform ɗinsu. Duk gaisheta sukayi suna
mai rungumeta, tai musu murmushi tana amsawa. “Har an shirya ƴan makaranta?”.
Kawunansu duk suka shiga ɗaga mata. Sai kuma cike da shagwaɓa irin ta autoci Waleed ya ce, “Ammie
mikika dafa min?”.
“Oh tama dafa maka bata dafa mana ba, kuji min ɗan iya”. Cewar Hameed yana hararsa da kai dankali
bakinsa. Murmushi Ammie tai da faɗin, “Ni dai kunga kuyi ku wuce bana son surutu yau ɗin nan. Kowa ya
duba abinda yake so shi aka dafa masa”.
Murna suka shiga yi, sai kuma suka ɗauki wanda zasu ci suka koma work table dake kitchen ɗin kowa
yaja kujera sukai zaman ci. Ammie kuwa ta fara ɗan wawwanke kwanikan data ɓata dan bata son taga
ambar kaya da datti, duk da tasan yanzu mai aikinta zata zo ta fara aikin ta gwammace ta tsaftace waɗan
nan ɗin kafin ta iso. Tana kammalawa suma suka kammala. Sallama sukai mata kowa ya ɗauka lunch box
ɗinsa suka fice. Sai kuma six dan makarantarsu tana tare da islamiyya ne...
Koda ta koma ɗaki saita gagara shiga wankan datai niyya, zama tai ta ɗauki waya ta shiga kiran Nene.
Ba'a wani ɗauki tsawon lokaci ba Nenen ta amsa kuwa. Sai dai suka gaisa da tambayar juna gida kafin
Ammie ta ce, “Nene yau zan sameki a gida?”.
Daga can Nene ta ce, “Eh bazanje ko'ina ba. Dama nina naso kiran naki ai sai kika kirani, zaki shigo ne?”.
“Eh Nene indai ya bari zuwa anjima kaɗan zan shigo”.
“To shike nan sai kinzo ɗin ina saurarenki”.
Daga haka sukai sallama kowa ta yanke.....
★ Sai kusan sha biyu Ammie ta samu damar barin gidan. Dan da ƙyar Daddy ya barta dan ma tace masa
kitso zataje. Da yake yasan tana zuwa kitson kuma bai kawo komai a ransa ba. Shi irin mutanen nan ne da
sam basa son yawan fitar iyalansu, sunfi buƙatar ko yaushe kina gida, shiyyasa a cikinsu babu mai fita aiki
ko wani business. Ammien ce ma taga bazata iya wannan kashe kan ba komai sai abinda namiji ya baka
tuni ta fara kasuwancinta a gidan Nene. Kuma Alhamdullah komai yana tafiya dai-dai.
Gidan Nene gida ne a matsayin family house. Dan kuwa ita da duka matan ƴaƴanta suna a cikinsa. ALLAH
yayima mijinta rasuwa tuni, ita ta cigaba da gwagwarmaya da yaran har suka girma. Yanda ta horesu yasa
duk suna da sana'o'in su, dan babu mai zaman banza. Badai kuɗi garesu ba amma ci da sha gwargwado da
sutura irin ta gidan mai rufin asiri sun wuce da wannan kam. Sashen Babban ɗan Nenen ta fara shiga,
matansa biyu, yaso auren Ammie a baya matarsa nata zuba rashin mutunci akan hakan sai ALLAH ma bai
ƙaddara ba, to ashe kishiyar dai na bibiyarta, dan bayan Ammien tayi aure ya auro budurwa gal a leda
yanzu haka haihuwarta uku a gidan itama. Wannan dalilin ne yasa sama-sama suke da Ammien. Koda ta
shiga a kitchen ta samu Maman Salima kamar yanda suke kiranta, ta wani zubama Ammien ido zuciyarta
na bugawa, tuni murmushin fuskarta kuma ta ɓace. A yanzu kam ba kishin Ammie ne ke damunta ba
hassada ce. Ko'a jikin Ammie ta gaisheta da tambayarta yaranta. Daga kitchen ɗin ta amsa a daƙile, sai dai
idonta na'akan suturar jikin Ammie.
“A'a Aunty Asiya ce a gidan namu?”.
Amarya dake leƙowa daga falonta ta faɗa. Murmushi Ammie tai mata da faɗin, “Aiko nice Amarya”.
“To sannu da zuwa Bismillah ki shigo”.
Babu musu Ammie ta shiga, falon ƙal an gyara shi sai ƙamshin turaren wuta yake kamar bamai ƙananun
yara ba. Gashi da gani tana fama da laulayin wani cikin ne ma. Cike da girmamawa ta gaida Ammie kafin ta
fita sai gata da ruwa.
Ammie ta ce, “Amarya ai da baki wahala ba ma. Ina yaran nawa ko duk an wuce makaranta?”.
“Duk sun wuce shiyyasa ai muka samu lafiya Aunty, sai Ameen kawai yana barci ne”.
“A'a ai shima ko ya kamata a sakashi makarantar tunda naji bakinsa akwai surutu”.
cikin dariya Amarya ta ce, “Sosai kuwa Aunty”.
Bayan Ammie ta sha ruwan ta fito, amarya biye da ita har ɗayan sashen. Nan kam mace ɗaya ce, itama ta
amshi Ammie da girmamawa da mutuntawa, bayan sun gaisa ta fito ta shiga wajen sauran suma su biyu.
Daga haka ta shiga wajen Nene. A falonta ta sameta zaune ta baje kaya tanata lissafi. Sai wata dake gefenta
tana tayata. Da mamaki Ammie ta furta, “A'a Saratu yaushe a gari? Nene shine baki sanar min munada da
baƙuwa ba?”.
Murmushi wadda aka kira Saratun tayi, yayinda Nene ta ɗan taɓe baki da faɗin, “Zuwan nata ne dama
ya sani nemanki, tunda ita dai fitinar gidanta bata ƙarewa”.
“Tofa wani abunne kuma ya faru Nene?”.
“Humm Asiya ke dai cire mayafi a kawo miki abinci, ga waina can nasa tun ɗazun aka sayo miki gidan
Hajiyayye ALLAH yasa ma bata huce ba. Saratu ɗakko mata”.
Kasancewar Ammie na son wainar sosai ta zauna taci, sai da ta ƙoshi sannan suka fara maganar Saratun.
Sosai ran Ammie ya ɓaci, tace bako zata bar gidan ba har sai sauran ƴan uwanta sun dawo ai zama akan
al'amarin Saratun, wannan karon dole su ɗauki mataki akan mijin nan nata mara mutunci, dan bazasu
yarda da auren duka ba. Bayan sun gama tattauna wannan suka koma batun nasu gidan, ita kanta Nene ta
jinjina batun zuwan Huznah Abuja. Amma sai ta kwantarma Ammie da hankali akan ta barta taje ɗin,
amma sun kira Shahidah sun gaya mata komai, sun kuma mata gargaɗin ta sanya ido sosai. Ammie dai bata
bar gidan nene ba sai bayan magriba da sauran ƴaƴan Nene huɗu ringis suka dawo kasuwa suka tattauna
batun Saratun. Da zata tafi sai ta wuce da Saratu can gidanta akan zata huta kwana biyu.
_________★
Washe gari ƴan Dubai suka wuce domin haɗo kayan lefe dana shagalin biki harma da kayan ɗakin
amarya. Itama Huznah ta wuce Abuja, sai dai abinda ya sake tabbatar ma da Ammie akwai wata a ƙasa ko
sallama Huznah batai mata ba. Sai bayan ta tafine uwar ta shigo tana cema Ammien tayi hakuri wai driver
ne ya azalzali Huznah ɗin shiyyasa bata shigo ba. Murmushi kawai Ammie tai ta ce, “Babu komai ai ALLAH
ya tsare hanya ya kaisu lafiya”. Daga haka bata sake tofa komai ba dole Hajiya Basariyya ɗin ta fito tana
taɓe baki, dan taso ne Ammie ta biye mata su ɗan yi gulmar ƴan tafiya Dubai. Itama Ammien kuma ta
ganota shiyyasa ta mata haka...
Maanal bata san wainar da ake toyawa ba. Da safe dai sanda Shahidah zata sauketa ne a office take
gaya mata zuwan Huznah ɗin. Dan yanzu itace ke kaita, wani lokacin ta dawo a taxi. Tun randa AA Darma
yay mata wannan gargaɗin ta so yima RK magana, sai kuma wani ikon ALLAH ma a daren ranar RK ɗin yay
tafiyar gaggawa har yanzu bai dawo ba. Dan itama a waya ya kirata ya sanar mata. Busy kuma da yayi sosai
yasa ba koyaushe suke waya ba sai ya samu lokaci. Amma ya tabbatar mata bazai wuce kwanaki biyar ba.
Yau kuma kwanansa huɗu kenan gobe idan ALLAH ya kaimu take saka ran dawowarsa. Yazeed dai ne da
yake yana garin yanzu kullum da dare sai yazo gidan Shahidah ɗin, dan da farko yaso ya mata fushi akan
batun aiki wai bata sanar masa ba sai Daddy ya gaya masa, haƙuri kawai ta bashi da nuna masa ai Daddy
ɗin dan ya isa da su ne su duka shiyyasa. Ya dai ƙyaleta kawai, amma a ransa ya gama ƙudirar wannan aikin
sai ta barsa duk da yanada planing ɗin anan Abuja ɗin zata zauna ita ko anyi bikin su.
A gajiye ta fito daga office ɗinta zuwa office ɗin Designer Director ɗin dake kula da aikin nata, har yanzu
dai suna akan project ɗin nan daya haye mata. Bayan tayi knocking aka bata izinin shiga. Ganin yana haɗa
kaya alamar zai tashi ne a sanyaye tace, “Director badai zaka tashi bane ba?”.
Kallonta yay fuskarsa da murmushi, dan yanzu kam ta fara sabawa da su. Yanda kuma take girmamasu
da bawa kowa hakkinsa da kame kanta yasa su jin ƙaunarta a rayukansu.
“Lallai baƙya kallon agogo, bakiji yanda company yay tsit ba kusan duk an wuce ai”.
Agogon ta kalla kafin ta sake dubansa, dan tabbas magrib tama kusa. “Ayya ALLAH ban lura ba. Dan
ALLAH ka samun hannu a document ɗin nan, so nake yanzu na miƙasa office ɗin CEO idan ALLAH ya
taimakeni da safe sai ya duba shi da wuri kafin zaman meeting”.
“Wayyo baƙya jin tausayina ALLAH, kinji bayana kuwa ga Madam nata kira na yau birthday ɗinta. Amma
kawo nayi sauri”.
Godiya ta masa tare da matsawa ta ajiye masa file ɗin, tana daga tsaye ya shiga dubawa. Ɗagowa yay ya
dubeta cike da tsokana ya ce, “Anya ba kwanan nan zan baki kujerar nan ba Manaal Giro? Ke ɗin ƙuruwace
fa. Ɗan murmushi kawai tai masa kanta a ƙasa dan iyakarta da su kenan, shiyyasa duk da yanda take
girmamasun wasu ke mata kallon mai girman kai da faɗin rai. Wasu a cikinsu duk sun ƙyasa, sai dai
kamewarta na zame musu barazana, ga kuma RK da kowa ya tabbatar budurwarsa ce a companyn yanzu
duk da kuwa yau ne take cika kwanta na takwas a Companyn. Bayan ya saka mata hannun ta karɓa tana
masa godiya. Sallama ta masa ta fice, haka ya bita da kallo zuciyarsa na zallo. Tun ranar farko da sukama
Maanal interview yarinyar tai masifar shiga masa rai. Abinda ya faru tsakaninta da Boss yaso taka masa
birki, amma daga baya sai yaga kuma komai bai sake faruwa ba, sai sabon soyayyarta a zuciyarsa ya dawo
fil, sai dai kuma Maanal babu sakin fuska........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
3️⃣1️⃣3️⃣1️⃣
.......Ita kam koda takai file office ɗin Boss ta ajema AS office ɗinsa ta koma ta cigaba da aiki, dan akwai
abinda take son kammalawa kafin ta wuce gida. Kiran sallar magriba ya sata ƙarasawa sauri-sauri sannan ta
tashi tayo alwala ta haɗa kayanta ta kashe komai ta fito dan su Yaqub tuni duk sun wuce sai ita kaɗai. Shiru
babu motsin kowa duk an wuce. Sai offices ɗai-ɗaine ƴan over work irinta koma wanda suka fita ke'a buɗe.
Ƙananun ma'aikata ma ta wuce kusan mutane huɗu basu wuce ba, koda ta fito harabar companyn ma
motoci biyar kawai ta gani sai mashin biyu alamar na wanda suka ragene. Idanunta suka sauka akan motar
boss. Janyewa tai tana taɓe baki, shi dama ai yafi kowa iya over work, dan kullum shine ƙarshen barin
office. Masallaci ta nufa domin gabatar da magriba. Bayan an idar koda ta fito bata koma ciki ba, hanyar
gate ta nufa abinta a ƙafa. Street ɗin shiru babu yawaitar mutane a ƙafa sai motoci, sai dai ko'ina akwai
haske kamar kana wata ƙasa ba Nigeria ba. Taxi nada wahalar samu a wajen kasancewar duk manyan
ma'aikatu ne ata wajen, sai gidajen cin abinci da suma ba laifi suke da yawa ta wajen da shopping malls
guda biyu dake can farkon shigowa. Tsoron kar dare ya sake mata ya sata cigaba da tafiya a ƙafa tana jin
nadamar kaiwa haka bata tafi gida ba, har Shahidah cewa tai zata aiko a ɗauketa idan ta gama tunda tace
ita karta biyo ɗaukarta yau tana da aiki amma tace mata a'a zata hau taxi. Tayo tafiya babu laifi zuciyarta ta
fara karaya, dan ƙafafunta sun fara gajiya. Mamakine ya kamata ganin ƴammata tsaitsaye kamar masu jira
azo ɗaukarsu, amma abinda zai baka mamaki suna da yawa duk da kowanne yana tsaye ne shi kaɗai ko su
biyu. Cigaba tai da tafiyarta dai tana ɗan kallonsu sai taji ana horn, da sauri duk hankalin ƴammatan ya
koma wajen motar, wasu ma duk sun nufi motar ne, sai dai kuma mai motar bai tsaya ba ya cigaba da bin
bayan Maanal ne ana kuma horn ɗin dai. Da sauri ta ɗan ja da baya sakamakon shan gabanta da akai da
motar, cikin wani irin ɓacin rai ta ɗago dai-dai mai motar na sauke glass ɗinsa. Babban mutum ne da a
shekaru ma zai iya haihuwar su Shahidah bama ita ba, yana daga baya kwance driver ɗinsa a gaba, cikin
tsareta da ido ya sakar mata murmushi. Ɗauke kanta tai da sauri ta raɓa ta wuce wani irin ɓacin rai na
mamayeta. Jin an ƙara biyo bayanta da mota ana mata horn again ta tsaya cak, cikin matuƙar fusata da
harzuƙa ta ɗago dan ta gama shirya yima tsohon banzar nan zagin ƙare dangi, amma sai kawai taga motar
boss ba wancan bane. Kafin ta iya haɗiye abinda ke bakinta AS ya fito daga gaba, kai tsaye inda take ya iso,
furkarsa da murmushi ya furta, “Sister Maanal bismillah ki shiga”. Yay maganar yana miƙa mata hannu da
nufin amsar kayan hannunta. Kai ta girgiza masa tare da janye hannun nata tana faɗin, “Karka damu na
gode”.
“Idan shi bai dace ba, inaga ni kamar zan dace tunda dama ni na fara tayawa”. A bazata taji muryar
tsohon nan cikin kunnenta daga bayanta. Jitai gaba ɗaya kamar ta daburce, ga zuciyarta na wani kalar
bugawa da sauri-sauri har numfashinta na neman fara yin sama-sama. Babu alamar wasa ko ragi a tare da
ita ta juya ga tsohon nan, hannu ta ɗaga da nufin nunashi a hankali taji saukar wani tattausan hannu ya
riƙe mata yatsu, batare da cewa komai ba yaja hannun nata. Ƙoƙarin fisgewa ta fara sai dai bai bata damar
hakan ba har ya iso da ita jikin mota. Sai lokacin ta iya zuba masa manyan idanunta da suka kaɗa, shima
kallon nata yake cikin ido. Kusan minti ɗaya suna kallon juna kafin ya zare kayan hannunta tare da motsa
lips ɗinsa a hankali ya furta, “Get in”.
Rasama mi zata ce masa tayi, dan sam babu ko ɗigon wargi a fuskarsa. Yayi masifar yin kicin-kicin da
ita kamar zatai aman wuta. Bai kuma sake cemata komai ba ya zagaya ɗaya side ɗin ya shiga mazauninsa
ya ɗauke kai. Dattijon Alhajin nan dake tsaye ransa a matuƙar ɓace ya sake takowa inda Maanal take. Ai
yana buɗe baki zaiyi magana kawai ta shige motar, shiko AS ya rufe mata murfin ruf tare da kallon Alhaji
fuska da murmushi ya furta, “Bye bye grandpa”. Shima ya zagaya ya shige motar driver yaja suka wuce.
Da wani irin kallon ɓacin rai dattijon yabi motar da kallo, sai kuma ya jinjina kansa tare da cije lips da
ƙarfi ya koma tashi motar. Da sauri driver ɗinsa ya buɗe masa ya shiga ya maida ya rufe suma suka bar
wajen....
Sosai Maanal ta takure jikinta waje guda, yayinda idanunta ke'a lumshe bugun zuciyarta kuwa gaba
ɗaya ya sauya daga normal bugu. Ambaton sunan ALLAH kawai takeyi tare da ƙoƙarin danne kukan dake
son kufce mata.
AA Darma dake a gefenta kam tunda ta shigo bai ko kalleta ba. Gaba ɗaya ya tattara hankalinsa ne ga
document ɗin hannunsa da dama shi yake dubawa kafin suga Maanal ɗin, koda yake bama shine ya ganta
ba, AS ne ya ganta cike da mamaki ya furta (kai wannan ai Sister Maanal ce Alhaji Bukar ya tsare a hanya
halan bata sami abin hawa bane har yanzu). Driver na tambayar AS wacece ita ɗin AA Darman ya daka
masa tsawa akan su dakata, shine dalilin tsayawar tasu.
A yanzun ma driver ne cikin ɗari-ɗari ya furta, “Sir! Zamu fara saukeka ne kafin a kaita?”.
Shiru bashi da alamar amsawa. Sai da ya mula dan kansa batare da ya bar abinda yake ba ya bashi amsa
a taƙaice. “Fara ajiye ta”.
“Okay sir. Sister ina muka nufa?”. Ya maida akalar tambayarsa akan Maanal. Shiru bata amsa ba sai da ya
sake maimaita tambayar sannan ta dawo hayyacinta. Cikin ƙoƙarin danne komai da yanayin nan nata na
kamewa ta furta, “Samu waje kawai zan sauka na ƙarasa a taxi”.
Kallon AA Darma drivern yay ta mirror ɗin gaba da tunanin ko zaiyi magana. Amma sai yaga ko kallon
inda wani cikinsu yake bai yiba ma. Dan haka sai ya kalla AS cikin marairaicewa. Murmushi AS yayi tare da
juyowa saitin inda Maanal ɗin take, “Please Sister Maanal bafa zamu ajiyeki ko'ina ba sai gida”.
Rasama mi zatace tayi, sai kawai ta faɗa masa sunan anguwar a taƙaice. Bai gaji ba ya sake tambayar
street, nan ma kamar bazata kula shi ba sai kuma dai ta faɗa. Daga haka bata sake magana ba ta maida
idanunta ta rufe. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso abinka da lafiyayyar mota a saman lafiyayyar kwalta.
Shigowarsu cikin street ɗin ya sa AS sake mata tambayar inda za'a sauketa. A taƙaice ta ce “Nan ma yayi”.
Shi dai driver tunda taƙi faɗar no ɗin gidan da zataje ai sai kawai ya samu waje ya tsaya abinsa. Itako ta
kama handle ɗin motar ta buɗe da nufin fita. Sai kuma ta ɗan juyi domin ɗaukar kayanta da AA Darma ya
amsa a ɗazun akai rashin Sa'a shima ya kawo hannu kan kayan da nufin ɗauke file ɗin daya ɗora kawai ta
riƙe masa hannu. Da sauri ta jiyo jin ta kama abu, dai-dai shima yana kallon hannun nasa da yaji an cafke. A
tare suka dubi hannun sai kuma suka kalli juna. Maanal ta saurin yarfar da hannun tamkar wadda ta kama
wuta, yayinda shi kuma ya wani irin dunƙule hannun nasa waje guda tare da dimtse lips ɗinsa da hakori
tamkar zai kai naushi. Sauka Maanal ɗin tayi tare da zare kayan nata ta ajiye masa file ɗin batare data sake
gigin kallon ko inda yake ba taima AS godiya da driver tai gaba abinta ko waiwayen motar bata sake yi ba.
Shima driver sai kawai ta tada motar suka wuce.
Tunda suka tafin AA Darma hannun nasa kawai ya zuba ma ido tamkar mai karanta wani abu a jikinsa
ko cigaba da ganin hannun Maanal ɗin. Kamar ance ya kalla inda ta tashi idonsa ya sauka akan ɗan abin
hannunta da alama wajen yarfar da hannu da tai sanda ta kama nashi ya cire batare data kula ba. Hannu
ya kai a hankali ya ɗauka ɗan hannun ya juya. Mai ƙyau ne sosai kalar golden, an masa kwalliya da fararen
stones, da gani ba wani mai tsada bane, amma yayi ƙyau sosai. Yanda ya tsirama ɗan hannun ido yana kalli
da jujjuyashi haka su AS ke kallonsa zuciyarsu cike da gulma, suna ganin zai ɗago suka kama kansu. Shi ko a
cikin aljihun jacket ɗin suit ɗinsa na ciki ya cusa ɗan hannun kawai ya gyara zamansa......
_____________★
_________★
Maanal kam data shiga gida tamkar wadda aka koro har ta bama maigadi tsoro waje ta samu a harabar
gidan ta zauna, sai da ta huta taci kukanta sosai ta ɗan samu nutsuwa sannan ta miƙe. Wajen fanfo da ake
bama flowers ruwa taje ta wanke fuskarta sannan ta shiga ciki. Turus taja ta tsaya tana kallon Huznah dake
zaune a falo tana cin abinci. Yayinda su Barrah dake homework sukayo kanta da gudu suna mata oyoyo.....
Rungumesu tai idanunta na kan Huznah ɗin da itama ita take kallo, dai-dai nan Shahidah ta fito daga
kitchen. “Aini yanzu nake tunanin zuwa na biki kafin Daddynsu Barrah ya dawo gidan nan”.
Shahidah ta katsema Maanal da Huznah kallon-kallon da sukema juna da furucinta. Dan murmushi
Maanal ɗin tayi da kaiwa zaune tana faɗin, “Didi ai nima kaɗan ya rage na kiraki a waya, ashe wajen nan
haka ake wahalar taxi”.
“Ai dolene, waje duk ma'aikatu ke kuwa. Ya aikin?”.
“Alhamdullah ya naku?”.
“Yana can mun baro sai kuma gobe idan ALLAH ya kaimu. Bakiga baƙuwa ba ne?”.
Sam Maanal babu ruwanta da ɓoye-ɓoye dan ita ƴar sak ce, sai ta ɗan kalli inda Huznah take da faɗin,
“Na ganta Didi. Mamaki ne ya kasheni ai na kasa magana. Sannu da zuwa”.
Cikin ɗan basarwa Huznah ta ce, “Yauwa sannunki kema”. Daga haka ta maida kanta ga abincinta. Itama
Maanal sai bata sake magana ba ta miƙe.
“Didi bara na ɗan watsa ruwa, ina Linda dan ALLAH ta dama min kunun gyaɗa kafin na fito, Barrah jeki
gaya mata”..
Amsawa Barrahn tai tare da miƙewa ta nufi kitchen ɗin da ɗan gudu tana jiran Linda, ita kuma tai hanyar
ɗakinta.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
3️⃣2️⃣3️⃣2️⃣
......Da mamaki Maanal ta dinga bin akwatin Huznah da aka kai ɗakinta da kallo, sai dai batace komai ba ta
tuɓe kayanta ta nufi bathroom. Wanka tayo da alwala, sai da ta gyara jikinta tsaf tai sallar isha'i sannan ta
dawo falon. Kunun da ta saka Linda ta haɗa mata kawai ta ɗan sha, sai magungunanta da Shahidah ke bata
da kanta dan ma kada tai wasa. Suna nan suna ƴar hira ita da Shahidahn dan Huznah ba saka musu baki
take ba sai ma latse-latse take a waya kamar bata falon mai gidan ya dawo...
Dalilin dawowar tasa yasa Shahidah shigewa part ɗinsa, aka bar su Maanal kawai. Sai itama ta miƙe ta
taimakawa Linda suka kwashe su Barrah da sukai barci a falon. Daga haka tacema Huznah ita zata shige ta
kwanta. A ciki Huznah ta amsa mata, Maanal bata damu ba tai wucewarta. Ita kuma ta rakata da harara.
Maanal na shiga ɗakin kiran RK ya shigo mata, bata ɗaga ba sai da takai kwance, ta gaisheshi a mutunce
kamar yanda ta saba, daga haka ta fara mata hira da albishir ɗin gobe in sha ALLAHU yana hanya. Ganin
yanata jan hirar ta fara masa hamma, dole yay mata sallama. Kamar jira sai ga Yazeed shima ya kira, jitai
kamar zatai kuka, haka dai ta ɗaga.
“Dawa kike waya haka Maanal?”.
Furucinsa na farko kenan maimakon amsa mata sallamar da tai masa, muryarsa a cinkushe. Sai da ta ɗan
yi jimm kafin a nutsenta ta bashi amsa da, “Rafeeq ne!”.
“Rafeeq!?”.
Sai da ta ɗan lumshe ido saboda yanda ya maimaita sunan RK ɗin a kausashe yanzu kafin ta ce,
“Uhhum!”.
“Okay yayi ƙyau”. Ya faɗa yana yanke wayar. Shiru tayi na mamakinsa, Yazeed mutum ne mai nutsuwa
da fahimta, sannan yana da haƙuri, zata iya cewa tunda ta haɗu da RK bai taɓa tunkararta akan al'amarinsa
ba sai dai can a tsakaninsu. Amma yau minene ya hasalashi haka? Kai ita kam taga takanta. RK ya nuna
fushi idan ya ganta da Yazeed ko tana waya da shi, yanzu shima kuma ga Yazeed ɗin zai fara nashi. Ita kam
dan ALLAH karsu rikita mata lissafi mana, suma barta da abinda ya dameta...
Tana cikin wannan yanayin Huznah ta shigo, bata mata sallama ba dan haka itama tai kamar bata san
da shigowarta ba. A gadarance ta jefa wayarta saman gadon, fuuu ta wuce bathroom, ita dai Maanal binta
tayi da kallon mamaki, bata jimaba ta fito, ta buɗe akwatinta ta canja kaya sannan ta hawo gadon. A
mamakin Maanal dai taji Huznah na jera fillos a tsakkiyarsu, sai kawai abin ya bata mamaki ta saki
murmushi. Bata kulata ba tai addu'a taja barko.
Barci take son yi saboda gajiya da tayi ga gobe ma dole ta fita aiki, amma Huznah ta hanata sai charting
take, kuma voice note. Tun Maanal na dauriya har dai ta miƙe tsam a gadon ta koma saman sofa doguwa
dake a ɗakin, kwanciyar bata mata wani daɗi ba amma ta haƙura anan ɗin duk da nan ɗin ma ba tsira tai
ba tana jin Huznah ɗin da bata fasa abinda take ba harda su ɓaɓɓaka dariya kamar ba dare ba. Daga ƙarshe
bata san sanda tayi barci ba ita dai, dan itama ALLAH ya taimaketa barcin yay awon gaba da ita. Da asuba
kuma koda ta tasheta ƙin tashi tayi, sai kawai ta ƙyaleta. Har gari ya waye tai shirin fita aiki Huznah taƙi
tashi salla. Sai kawai ta fice abinta tana nema mata shiriyar UBANGIJI.
Yau ma Shahidah ce ta ajiyeta a office sannan ta wuce nata aikin, tun a harabar companyn suke gaisawa
da mutane har ta shigo. Dama dai tsakaninta da kowa gaisuwar ce, rashin yawan fara'arta da yawan
magana ma kesa mafi yawansu ke kiranta da sunan mai girman kai. Ƴan rukuninsu mutum uku ne kawai
sukazo, ta gaisa da su taja kujerarta ta zauna. Dama ita kaɗaice mace a cikinsu, shiyayasa daga gaisuwa sai
zancen aiki ke haɗata da su. ALLAH kuma ya taimaketa kujerarta itace farkon shigowa, suma ganin yanda
take haɗe fuska da kame kanta yasa suke shakkar shige mata duk da wasunsu na kwaɗayin hakan tun ma a
ran farko da tazo. Aikinta ta kamayi kawai kamar yanda ta saba, a haka sauran suka iso, kowa yazo zata
ɗago su gaisa daga haka ta maida kanta ga aikinta. Kusan eleven ta tashi zuwa office ɗin Director
Mustapha. Duk da kallo suka bita, wanda ke zama kusa da ita cikin yin ƙasa da murya yace ma na kusa da
shi, “Wato yarinyar nan akwai girman kai wlhy Ema..”.
Caraf Yaqub da ke facing ɗinsa ya ce, “Ba wani girman kai wlhy, ta dai san kanta ne. Idan mace ta cika
faran-faran ace ma ballagaza, idan ta kame kanta ace girman kai. Kufa lura ita kamar yanayintane ma haka,
miskila ce kawai”.
“Tab ai ni kuma bana son miskilar mace gaskiya. Ita mace ko yaya da sauƙin kai tafi daɗin rayuwa”.
“A wajenka ba.....”
“Oh to kodai santa kake yine wai Yakub”.
“To laifi ne idan na sota Zaharadeen, naga dai namiji ne ni. Kuma ɗin inda zata amsa muku son nata
kuke shiyyasa kuke gulmarta. Yarinya na girmamaku amma bakwa gani. Yanzu da sakewa take cikinmu da
surutu da fara'a sai kuma ace ta saki kanta a tsakkiyar maza. Ta kuma kama kanta kunzo kunayi da ita
mtsooww!”.
Ya miƙe ya bar musu wajen. Duk da kallo suka bisa, sai kuma suka kalla juna cikin yamutse fuska.
“Wannan guy ɗin na kula fa son yarinyar nan yake”.
“Oh kai sai yau ka gane, ai na jima da fahimtar hakan. Kuma banga laifinsa ba dan koni ALLAH na
ƙyasa”.
Dariya suka sanya a tare harda tafawa.
Maanal kam da bata ma san sunai ba kanta tsaye office ɗin Designer Director Mustapha ta nufa. Tana
shiga Elevator massage ya shigo wayarta, ƙoƙarin dubawa ta fara yi sai taga Yazeed ne. Nutsuwa tai a
karanta saƙon, sai ya zam har elevator ɗin ta tsaya hankalinta nakan wayar, a haka tai ƙoƙarin fitowa batare
da duban gabanta ba. A dai-dai lokacin da CEO AA Darma ke isowa ga elevator ɗin Assistant ɗinsa biye da
shi. Ya riga ya kawo jiki, kamar yanda itama ta riga ta taho gashi hankalinta ba a wajen yake ba balle taja da
baya kawai sai jitai ta bugi abu. A ɗan razane tayi baya, wayarta ta suɓuce ƙasa hakama gilashin idanunta
da document ɗin duk suka tarwatse kasa.
Sosai ta ɗago cikin ɓacin rai dan ganin wanene da wannan aikin bayan ta gama bin kayan da kallo ɗaya
bayan ɗaya. Shima sai hakan ya zam dai-dai da tashi ɗagowar bayan ya gama bin kayan da kallo
musamman zanen agogon da yay masifar ɗaukar hankalinsa. Wani kalar zubama juna ido sukai kowanne
fuskarsa a matuƙar tamke, sai dai na Maanal ɗin ya ɗan cika da ruwan hawaye dan har ƙyallinsu ya nuna.
Yanda tai masa ƙiri da idanu sai ka ɗauka zata fara zazzaga masa ruwan bala'i ne, dan tuni AS ɗinsa da
wasu da suka zo wajen bayan faruwar accident ɗin duk sunyi kasare cikin ɗunbin mamaki suna son suga
mizai faru. Amma mi, a mamakin kowa sai suka ji cikin sanyin murya Maanal ɗin ta furta,
“I'm sorry Sir”.
Ta ƙare maganar da rissinar da idanunta harma da kanta cikin nuna girmamawa. Shi kansa wani irin
rumtse idanu yay da masifar ƙarfi, sai kuma ya zagayeta ya shige cikin elventor ɗin batare da yace komai
ba. Wannan abu ya bama kowa mamaki, hatta da AS ɗinsa daya gama tattaro ma Maanal kayayyakinta.
Wannan shine abu na biyu daya faru tsakanin Boss da Maanal ko yace na uku harda kaita gida da sukai jiya.
Shi sai ma ya rasa kalar tunanin da zai yi akan al'amarin.
Sauran ma duk sun ma Maanal sorry, kanta kawai ta jinjina musu da ɗan yin murmushi ta wuce zuwa
office ɗin Director Mustapha. Bayan tayi knocking aka bata iznin shiga. Ta gaishesa da girmamawa kamar
yanda ta saba yima kowa. Shiko ya amsa fuskarsa da murmushi tare da nuna mata kujera. Kanta ta ɗan
girgiza masa da ajiye document ɗin hannunta saman desk ɗinsa.
“Sir dama na kammala ne shiyyasa nace bara na kawo maka sai ka duba”.
“Yauwa sister Maanal dama kamar kin san yanzu nake shirin nemo ki, dan ban jima da baro office ɗin
CEO ba akan batun. Woow ai sai naga ma kamar waɗan nan sunfi ma wancan ɗin ƙyau”.
Ita dai Maanal komai batace da shi ba kanta a ƙasa, sai da ya gama santinsa sannan ya sallameta akan
ta zama cikin shiri koyaushe za'a iya nemansa a conference room. Koda ta koma saita samu har gulmar
abinda ya faru tsakaninta da CEO ɗin taje can. Dan ta wuce wasune nayi batare da su sun farga da ita ba.
Kowa bata kula ba har abokan zamanta da wasu ke ɗan ƙus-ƙus ta zauna ta cigaba da aikinta.
Bayan anje break daga massalaci Maanal ta dawo kan aikinta, dan tunda tazo companyn bata taɓa zuwa
kitchen cin abinci ba. Kullum da abinda zata ci take zuwa daga gida, dan haka bata taɓa maida hankalinta
ba. Tana cikin aikin ta samu kira daga head of design office ana nemanta a conference room. Tashi tai
ɗauke da drive ɗin data haɗa abinda zata gabatar ta wuce. Batayi mamakin ganin duk manyan companyn a
wajen meeting ɗin ba, dan ta fahimci project ɗin nada matuƙar muhimmanci. Sai da ta gaidasu cikin
girmamawa sannan ta zauna a kujerar da aka nuna mata. Kusan zaman mintuna biyu sannan CEO ya shigo
AS nashi biye da shi. Dukansu miƙewa sukai domin girmamawa, sai da ya zauna a kujerar da AS ya gyara
masa sannan yay musu nunin su zauna. Duk zaman sukayi, ita dai Maanal bata yarda ko inda yake ta kalla
ba. Sai da Director Steven ya mata magana sannan ta tashi. Kamar waccan ranar yau ma ta gabatar da
sabbin zanenta, tare da bayanai akan yanda zai iya kasancewa. Yau ɗin ma dai kowa ya yaba mata matuƙa,
dan hatta shi kansa CEO ɗin a mamakinta ya wani zuba mata ido, ita dai kame kanta ta ƙarayi. Tattaunawar
ta cigaba da gudana, musamman ta ɓangaren Head of design and engineering da R&D Director da Sales
and Marketing Manager sai shi CEO ɗin dake ɗan saka baki. Sun kwashi kusan awa ɗaya da rabi kafin a
tashi, yau kam Maanal ita ta fara fitowa daga conference room ɗin tana sauke numfashin gajiya. Har ga
ALLAH ta gaji sosai, dan surutun nan na wahalar da ita matuƙa. Kai tsaye elevator ta nufa. Koda ta fito floor
ɗinsu sai ta samu anata ƙus-ƙus, bata fahimci ƙus-ƙus ɗin na minene ba sai da ta ƙarasa group ɗinsu. Sama-
sama take tsintar gulmar da su Zaharadeen suke suma, wai wata ƙyaƙyƙyawar budurwa ce tazo neman
CEO. Sai dai an hanata shigowa kasancewar yana meeting tana a reseption dan tace ko zai kwana a
meeting ɗin zata jirasa. Abinda ya kawo gulmace-gulmacen kuwa securitys da suka hanata shigowa taima
tas tare da sanar musu cewar basu san matsayinta bane shiyyasa, to itace matar da CEO ɗin zai aura.
Wannan furuci nata shine dalilin ƴan ƙananun maganganun dan kowa dai yasan wanene CEO ɗin akan
mata. Hatta hoton dake zagaye da duka offices ɗin companyn kowa yayi gulmarsa ya bari dan babu wanda
yasan matsayin mai hoton ko sanin wacece ita. Musamman ma daya kasance bawani gane ainahin wanda
ke'a hoton ake ba sam. Abinda kowa ya yarda da shi kawai koma wacece tanada muhimmanci a wajensa.
Sai kuma ga ita wannan budurwa tazo da sabon zancen daya ɗauki hankalin kowa.
Shigowar wani abokin aikinsu sai dai ba'a rukuninsu yake ba ya sakasu maida hankali wajensa su duka
banda Maanal da kunnenta ne kawai ke wajen. Cikin gulma yake sanar musu gafa shi can AS na CEO yazo
ya shiga da budurwar nan da'alama zancen dai gaskiya ne ita ɗin matar da CEO ɗin zai aura ɗin ce. Duka
sosai zuciyar Maanal take yi, sai da ta dinga ambaton sunayen ALLAH da sauri-sauri sannan ta ɗan fara jin
dai-daituwa. Daga haka taji gaba ɗaya aikin da take yama fita mata a rai........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
3️⃣3️⃣3️⃣3️⃣
.........Yau kam za'a iya cewa itace ta riga kowa fara tattara kayan tashi tun lokaci bai gama cika sosai ba.
Dan zuciyarta gaba ɗaya a ƙuntace take. Ga ƙirjinta ya mata wani irin nauyi sosai. Tamkar an saita sai ga
kiran RK ya shigo mata. Kamar bazata amsa ba sai kuma ta ɗaga, sallamarta kawai ya amsa yace ta fito
gashi a waje yana sauri ne bazai shigo ciki ba. Ajiyar zuciya ta sauke tare da amsa masa da gata nan. Daga
haka taima sauran sallama kamar yanda ta saba ta wuce.
“Kai mutuniyarku kamar fa yanayinta ya sake canjawa tunda akace ga budurwar CEO”. Zaharadeen yay
maganar yana gumtse dariya.
Caraf Yusuf yace, “ALLAH nima na lura da hakan, anya kuwa itama bata faɗa tarko ba? Kasan CEO da farin
jini wajen matan kamfanin nan kamar ya musu turaren asiri”.
Dariya suka kwashe da shi, Ema dake jin hausar sama-sama dan da Hausa suke gulmar ya ce, “Baku ji
labarin ɗazu ba, itama sonshi take shiyyasa take mana wulaƙanci, in dai CEO ne duk zasuyi su gama
maitarsu”.
Tsaki yakub yayi tare da miƙewa yana faɗin, “ALLAH ya shirye ku, kuna maza amma gulma ta riga ta
muku katutu. Haka kawai kuna ma baiwar ALLAH ƙazafin abinda baku da ilimi a kansa.”
Caaa suka yo masa da masifa suma, bai kulasu ba yay wucewarsa ya barsu....
★ ★★ ★
__________★
Washe gari sai ga Yazeed wai yazo kaita office da kansa. Rasama abin cewa Maanal tayi, tadai cigaba
da cusa breakfast ɗin da Shahidah ta tsareta yi saboda shan magani. A haka yazo ya samesu. Ta gama shan
maganin tana tattara kayanta sai ga maigadi yazo yana sanar mata ga RK yazo, wai ya kira wayarta switch
off. Gaba ɗaya sai Maanal ma ta kasa motsi, idanunta cike da ƙwalla ta kai dubanta ga Shahidah da abin
yama fara bata dariya. Dan ita kam Yazeed da RK ɗin yanzu dariya al'amarin nasu ke bata. Kowanne baya
iya ɓoye kishinsa akan Maanal. Ta wani gefen kuma tausayi suke bata su duka ukun ma. Inda Yazeed yake
Shahidah ta juya, sai ta samu wayam alamar ya fita.
“Tofa, shi kuma Ya Yazeed yaushe ya fita”.
Da sauri Maanal ta juya inda Yazeed ɗin yake, itama ganin wajen empty sai ta ɗan waro idanunta tare da
maida kallonta ga Shahidah. “Didi ina kuma yaje?”.
“Wajen abokin takararsa mana. Ai wannan samari naki Maanal na kula kowanne da zafinsa yake. ALLAH
dai yasa a rabu lafiya kawai. Kinga muje kawai ni na saukeki da kaina sai a raba rigimar. Ya kamata ma su
duka ki hutar dasu zuwa kaiki da ɗakkokin nan dan na fahimci abin yana neman ɗaukar wata hanya ne a
tsakaninsu”.
Koda suka fito sun samu rayukan Yazeed da RK ɗin duk a ɓace, kallo ɗaya Maanal tai musu ta wuce ga
motar Shahidah tai shigewarta. Sai ita Shahidahn ce ta ƙarasa wajensu. Maanal bata san mi yayar tata ta
sanar musu ba, koda ta dawo motar kuma batai mata bayani ba ta tayar suka fice.
Haka ta kasance a office babu wani walwala a tare da ita. Dan fuskarta tafi kowacce rana kasancewa a
tsuke. Yau ma anyi zama tsakaninta da Marketing and sales manager, sai Head of operation da quality
control manager, bayan sun gama meeting akai kiranta da mata tambayoyi akan dai wannan zane nata da
company zai fitar. Yau ma da yake bata buƙatar kowa yazo ɗaukarta da wuri ta tashi. Ta fito harabar
companyn hankalinta akan agogon hannunta tana kallon lokaci suka kusa cin karo da assistant ɗin CEO.
Haƙuri ya shiga bata itama ta bashi. Ta raɓesa zata wuce idonta ya sauka akan AA Darma ɗin dake tsaye shi
da wani dattijo suna magana. Yau dai sanye yake cikin farar shadda ƙal datai masa shegen ƙyau da sake
fitowarsa a cikakken bahaushensa ɗan arewaci dan harda hula. Da sauri ta kauda kanta tare da ƙara sauri a
takunta duk da hakan bai hanata kasancewa a nutsenta ba.
Sarai AA Darma ya ganta shima. Amma ya basar ya cigaba da maganarsa da Alhaji Wakili. Alhaji Wakili
tamkar uba ne a wajensa, dan kuwa abokine ga mahaifinsu, sai kuma huɗɗar kasuwanci ta haɗasu, dan
yanzu haka ma akan wannan project da zasuyi wanda Maanal tai zanen agogon Alhaji Wakili ɗinne ya kawo
mutanen....
Dai-dai Maanal ta fito gate ɗin da nufin samun abun hawa wata taxi ke ƙoƙarin shiga cikin Companyn. Sai
dai securitys sun hana mai taxi ɗin shiga, sun tabbatar masa da dole wanda ke ciki sai dai ya fito ya ƙarasa
ciki da ƙafarsa. Yanda aka buɗe ƙofar motar a fusace ya ɗan ja hankalin Maanal, a mamakinta sai taga
Huznah ce ke fita a motar. Jitai ma gaba ɗaya ta ƙame a wajen ganin yanda Huznah ɗin ke musu masifa da
tabbatar musu akanta zasu iya rasa aikinsu. Sukuwa dai securitys ɗin sunce bafa zasu bar mai taxi ya shiga
ba dan dokar companyn ce hakan. Ko ma'aikatan wajen indai motar haya suka shigo ƙa'ida anan suke
sauka su ƙarasa ciki da ƙafarsu.
Ran Huznah ya kai maƙura a ɓaci, kuma dole ta haƙuran ta sallami mai taxi ɗin ta ƙarasa da ƙafar zuwa
ciki. Ga ma'aikatan sun fara fitowa sai kallonta ake ana ƙus-ƙus, itako tana wani yauƙi da taku ɗai-ɗai.
Maanal dai tuni ta shige taxi ɗin da Huznah ɗin ta fita. Haka ta iso gida al'amarin nata mata kaikawo. Har
jitai ta ƙagara Didin ta ta shigo. Zuwa duba Auntyn RK yasata watsar da komai bayan tayi wanka ta shiga
kitchen. Da taimakon Linda ta fara haɗa cake da wasu ƴan kalolin snacks da suka shirya zatayi dan dubiyar
ita da Shahidah. Suna tsaka da aikin Shahidah ta shigo tare da yara data biya ta ɗakko a makaranta yau da
kanta. Dama haka take musu duk juma'a sai dai idan aiki ya mata yawane tabar driver ya ɗakko su kamar
yanda ya saba.
Joining ɗinsu tayi a kitchen ɗin, anan ne Maanal ke labarta mata batun Huznah. Itama mamaki sosai tayi
Shahidahn, sai dai basu iya hasaso abinda ya kai Huznah Maawad company ba, har kuma suka kammala
aikin bata dawo gidan ba. Dama ba kowa take sanarma zata fita ba, ko jiya Shahidah bata san da fitar tata
ba hakama yau ɗin. Ganin har anyi la'asar RK bai kirata ba bai kuma zo gidan ba ta fara tunanin ko lafiya?
Gashi ta riga ta ɗauri niyyar zuwa dubiyar nan yau dai ta huta. Kuma jiya da dare ta sanar masa da anyi
la'asar yazo ya kaita dan Didi tace bata yarda sai bayan magrib ɗin nan ba. Jitai kamar ta sharesa, sai kuma
dai ta danne zuciyarta ta tura masa gajeren saƙo, daga haka ta koma falo ta zauna dan ta shirya tsaf
hakama Barrah da Haneeff da zasu mata rakkiya tsaf suke.
Sai kusan huɗu da rabi RK ya iso gidan, yana sanye da shadda shima yanzu ruwan zuma harda hula. A
ranta ta ɗan taɓe baki da faɗin (idan anga kuna wankan shaddoji sai juma'a kawai) a fili kam tayi kicin-kicin
da fuska daga gaisuwa bata sake kulashi ba, dan shima dai fuskar tashi yau babu walwala. Da alama tun
fushin safen ne bai gama sakinsa ba........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
3️⃣4️⃣3️⃣4️⃣
........A motar ma gaba ɗaya sai ya maida hankalinsa akan tuƙi da surutun su Barrah ya shareta, itama dai
hankalin nata naga duba wasu novels da Aneesa ta tura mata sunayen su. Tafiyar tasu ba wata mai nisa
bace suka iso. Gidane daya amsa suna gida, dan ko'a cikin garin Abujar kasan mai shi yaci ya ƙoshi. Sai da
security ɗin ƙofar yazo har inda suke yaga waye sannan ya danna remote ɗin hannunsa gate ɗin fari tas ya
zuge kansa. Godiya RK ya masa tare da shigewa cikin katafaren gidan daya yalwatu da shuke-shuke masu
matuƙar ƙayatarwa da bama zuciya nutsuwa. Kafin yau Maanal na jinjina girma da tsaruwar gidan Daddy,
hakama gidan Didinta Shahidah gidane mai ƙyau da ƙawa. Sai dai gidan nan ya matuƙar disashe mata
waɗan can da take tunanin babu kamarsu. Hatta da parking space a tsare yake anan.
Tunda suka fito su kansu yaran ke bin ko'ina da kallo baki a buɗe, Haneeff dai daya kasa haƙuri
matsowa yay kusa da Maanal cikin raɗa ya ce, “Mie-mie! Uncle R house ya haɗu kamar ba'a Nigeria ba”.
Kasa cema yaron komai tayi, sai hannunsa daya riƙo nata ta ɗan matsa kaɗan. Dai-dai nan RK dake
tattaro kayan tsarabar da bai san ko minene ba ya juyo garesu. Ƙaramin murmushi ya mata ganin yanda
take binsa da kallo, batare da yace komai ba ya nuna mata hanya alamar suje, tare da kama hannun
Barrah. Ɗauke kanta tayi kamar bata fahimta ba, sai ya sake sakin murmushi yay gaba, dan wannan yana
ɗaya daga cikin halayenta dake matuƙar birgesa. A gidan sassa ne har kusan shida. Kuma kowanne da
tsarinsa, sannan tsakaninsa da ɗan uwansa akwai ƴar tazara ta yanda baka isa sanin mi nacan keyi ba, ko
shi yasan mi kakeyi a naka part ɗin.
Part na tsakkiya a hannun dama suka nufa, RK ya danna bell tare da ɗan juyowa ya kalla Maanal. “Ni dai
kar aje ana fushi dani a gaban Aunty na”. Yay maganar yana kashe mata ido ɗaya. Harararsa ta ɗan yi
kawai, tare da ɗauke kanta. Shi kuma sai ya sake sakin murmushi. Zaiyi magana aka buɗe ƙofar. Matashiyar
budurwa ce da bazata wuce sa'ar Maanal ba, cike da girmamawa ta ɗan rissina tanama RK ɗin sannu da
zuwa. Duk da jikinta fes yake cikin tsafta a kallo ɗaya zaka fahimci mai aiki ce, sai dai masu aikin ma irin
wanda ke samun kular nan dan babu wani nakasu a tare da ita. Kayan hannun RK ɗin ta amsa, yayinda shi
kuma cikin dakewa kamar bashi ba yake tambayarta “Aunty fa!?”.
“Tana upstairs....”
Kansa kawai ya jinjina mata, batare da yace komai ba suka ƙarasa shiga cikin falon da yasha black &
golden color na kujeru da labulale, sai wani irin ƙamshin turaren wuta ke tashi mai ratsa zuciya. Ga sanyin
ac mai kashe jiki. Gaba ɗaya jikin Maanal sai ya ƙara sanyi. Bata sake tsinkewa da al'amarin ba sai da ya
danna wani maɓalli ƙofar glass ɗin dake kamar bango guda ta zuge kanta suka shigo wani falon, nan kam
komai golden yellow & white ne, shima dai babu kowa sai ƙamshi dake tashi, wayar da yake dannawa ya
kai kunnesa, ba'a wani jima ba aka ɗaga.
“Aunt mun iso”. Ya faɗa cike da girmamawa. Maanal dai data zama kamar wata gunkiya bata san amsar
da aka bashi ba taga ya juyo ya kalleta da murmushi, sai kuma ya furta, “Okay gamu nan”. Yana yanke
wayar.
“Sorry muje tana sama”.
Ya sake faɗa idanunsa akan Maanal ɗin. Kanta kawai ta jinjina masa batare da tace komai ba. Sai dai tana
mamakin ta ina kuma zasu bi zuwa saman dan bataga hanya ba sam anan. Amma a mamakinta sai ya nufi
wata ƙofa da su, anan ne taga ƙafar benen da shima aka ƙawata matuƙa, dan hatta a ƙasansa ma wasu
kujeru ne guda biyu aka tsara da gani wajen zaiyi daɗin hutawa. Haka dai suka haura upstairs ɗin Maanal
na sake jinjina jin daɗin da masu hannu da shuni keyi a ƙasar nan. Dole su manta da talaka, dole talaka
yasha wahala dan bataga ta yanda za'a iya tunawa da rayuwarsa ba anan. A sama ma wani tsararren falon
suka samu, wanda aka ƙawata da ash color na kujeru dama labulalen, nan ɗin ma dai ƙamshin turaren ne
yay musu sallama da sanyin ac kaɗan, sai kuma nutsatstsiyar muryar dattijuwar dake musu lale marhabun
cike da ƙasaita. Kasancewar RK ya rufe Maanal yasa bata ganin dattijuwar itama bata ganinta, sai dai
muryar ta wani irin dakar mata ƙirji.
“Rafeeq ƙaniyarka, dalla gyara ka wani rufe min ƙanwar tawa bana ganinta”.
Dariya RK yayi tare da matsawa gefe yana faɗin, “Oh Aunt ni yau baki son ganina kenan?”.
Baki ta buɗe zata bashi amsa amma sai ta gagara hakan, sakamakon saukar idanunta akan Maanal da
ita nata idanun ke kallon ƙasa, dan RK ɗin na matsawa daga rufetan da yay ta rissinar da idanunta saboda
yanda bugun zuciyarta ke ƙara ƙarfi. Ga wani irin yanayi mai wahalar fassara dake ratsata. Hakama
zuciyarta ta mata nauyi matuƙa a cikin ƙirjinta.....
Gaisuwar Barrah da Haneeff ce ta katse dattijuwar daga kallon Maanal, ta saki ajiyar zuciya da sakin
murmushi tana miƙama yaran hannu da faɗin, “Ƙanwata kinga ƙaraso mana, Bismillah zo gareni”.
Sake motsawa zuciyar Maanal tayi a karo na babu adadi, dan Muryar nan tana mata wani irin amsa
kuwwa ne da maimaita kanta a matsayin wata murya da amonta ya faru ya kuma shuɗe a duniyarta ta
baya. Amma sai ta dake, cikin yanayinta na nutsuwa ta cigaba da taka lallausan carpet ɗin dake tsakkiyar
kujerun zuwa inda dattijuwar take zaune, dan tana zaune ne daga ƙasa abinta duk da tima-timan kujerun
dake falon. Cak Maanal ta tsaya yayinda take gab da kaiwa inda dattijuwar take, bakomai ya sakata
tsayawar ba sai murya ta biyu data daki tsakiyar kunnenta tayi amsa kuwwa a cikin kanta. Sam batai zaton
akwai wani bayan dattijuwar a cikin falon ba duk da taji wani ƙamshi bayan na turaren da aka saka a gidan
da wanda ta tabbatar dattijuwar keyi. Sai da RK ke faɗin, “Wai dama da gaske kake daga massallaci gida
zakayo ashe?”.
“Kaje nemana ne?”.
AA dake kishingiɗe a saman lallausan carpet ɗin kusa gab da dattijuwar dan filo ne kawai ya raba
tsakaninsu gabansa wasu document ne barbaje, sai dai a hannunsa shi novel ne yake karantawa, a
maimakon shaddar ɗazun yanzu kam ƙananun kaya ne baƙaƙe a jikinsa. Amsar da RK ya bashi yana nuna
Maanal da faɗin, “No naje ɗaukar Maanal ne kawai dai” ya sashi wani kallar ɗago idanunsa ya sauke a kan
Maanal ɗin data kasa gaba ta kasa baya. Dai-dai nan itama Dattijuwar da hankalin ta ke akan su Barrah ta
ɗago tana maimaita sunan.
“MAANAL!” Sai kuma ta miƙe zaram. “Rafeeq da gaske Maanal ɗina ce kamar yanda zuciyata ta ayyana
min yanzu-yanzu ko suna ne yazo ɗaya, to amma akwai kamanni mafa” ta kai ƙarshen maganar tana
ƙarasowa inda Maanal take. Lallausan hannunta mai ɗauke da zabba masu ƙyau da ɗaukar idanu, tare da
bangles takai kan haɓar Maanal data lumshe idanunta da suka cika da ƙwalla ta ɗago. Sosai take raba
idanunta akan fuskar Maanal ɗin, sai kuma ta juyo ta kalla RK da shima ya miƙe cike da mamaki, janyewa
tai ta maida ga AA da ya maida idanunsa ga book ɗin hannunsa sai dai tuni abinda yake karantawar ya
suɓuce masa.
“Auta gane min nan, wlhy Maanal ce ko? Ko Auta Manaal ɗina ne dai ba wata ba. Ajwaad taso, taso
dan ALLAH ka tayani gani ko idanun nawane dai ba Baby ba bace....”
Da wani irin ƙarfi AA ya rumtse idanunsa batare daya ɗago ɗin ba, ko motsima baiyi ba daga yanda yake.
Sai RK ne ya ƙaraso wajen cikin sassarfa yana faɗin, “Aunt da gaske kin san Maanal ɗina? Maanal Please!
Da gaske kema kin san Aunty na?”. Duk ya ruɗe da farin ciki shi kam.
Cikin rawar muryar kuka Maanal da tausayin yanda dattijuwar ta rikice ya sake mamayeta, a hankali
ta shige jikinta tana faɗin, “Oum nice, Maanal ɗinki ce Oum. Dama baki manta dani ba, dama zan sake
ganinki? Ashe muna da rabon sake haɗuwa kafin na koma ga ALLAH”. Wani irin kuka mai ban tausayi ya
suɓuce mata, sai dai hakan bai hana muryarta fita cikin nutsuwa da sanyi ba. Sanyin dake bayyana tasirinsa
a jikin AA, duk yanda yake sake kamewa da dakewa abin na neman fito da kansa. Dan Barrah da kukan
Auntyn tasu ya sakasu yin narai-narai da idanu suma zasuyi kukan ta matsa gab da shi tana faɗin, “Uncle
kaga Mie-mie na kuka ita da Grandma”. Amma ina baiji yarinyar ba, sai da ta ɗan girgiza shi sannan firgigit
ya buɗe idanunsa da suka kaɗa matuƙa tare da ɗagosu ya sauke akan yarinyar. Dai-dai kuma Barrah ta
miƙe ta nufi inda Maanal take ta rungume mata ƙafafu tana kiran sunanta.
Ɗago Maanal Oum tai daga jikinta itama tana share nata hawayen ga murmushi yaƙi barin fuskarta.
Hannayenta duka biyu tasa tana sharema Manaal hawayenta da suka gagara tsayawa, dan gaba ɗaya ma ta
kasa cewa komai saboda ita kaɗai tasan irin kalar farin cikin da take ciki. Juyawa tai ga RK da ke kallonsu
cikin ruɗani, murmushi ta sakar masa shima. “Rafeeq ALLAH yay maka albarka kaji, yau kam kayi mun
babbar ƙyauta daka kawo min ɗiyata har gida.....”
“Aunty duk kin ruɗar dani wlhy, wai kin santa ne daman?”.
“Sosai kuwa Rafeeq, zan iya cemaka kusan nice na raini Maanal ma”.
“What!? Raino fa?”.
“Ƙwarai ma kuwa. Haihuwar Maanal ne kawai ba'ayi a gabana ba. Kunga bismillah kumuje mu zauna”.
RK dai da ƙyar ya kai zaune, sai dai idanunsa akan Oum da Maanal kamar mai tsoron su ɓace masa.
Waya Oum ta ɗauka tare da bada umarnin a kawo ruwa. Babu jimawa kuwa sai ga yarinyar nan data buɗe
musu ƙofa ɗauke da tray wata da bazata wuce sha huɗu ba biye da ita. Cike da ladabi da girmamawa suka
ajiye kayan a saman Centre table, sai kuma suka shiga gaishe da su RK. A dai-dai nan Oum dake riƙe da
hannun Maanal kamar mai gudun a ƙwace mata ke tambayarta,
“Ina ƴar uwata Maanal? Ina su Shahidah da Abban ku?”.
“Oum Ammie na nan lafiya Lau, hakama su Didi, wannan ma yaran Didi Shahidah ne”.
“Masha ALLAH! Masha ALLAH! Yanzu yaran Shahidah ne wannan? Kai jama'a ALLAH mai alkairi. Kuzo
nan kuyi haƙuri ganin ƴata ya ɗauke min hankali”. Tai maganar tana kamo su Haneeff da sukai ƙwale-kwale
saboda kukan Maanal ɗin. Cikin ɗari-ɗari bakamar ɗazu da farko ba suka ƙaraso wajen Oum ɗin, sai da
Maanal ta kallesu da sakar musu ɗan murmushi ta ce, “Itama Grandma ce ku gaisheta ku faɗa mata
sunayenku”.
Karo na farko yaran suka saki ajiyar zuciya, sai kuma suka shiga gaishe da Oum ɗin. Barrah ta faɗa mata
sunanta, da sauri Oum ta kalla Maanal. Murmushi Maanal ɗin tai mata da jinjina kanta. “Eh Oum sunanki
aka saka mata, Ammie ce taso sakawa tun akan su Waleed, sai kuma suka kasance maza. Shine Didi na
haihuwa aka saka”.
Wani irin rungume Barrah Ammie tayi a jikinta, ƙauna matuƙar ƙaunar Ammie na ratsa ƙashinta da
ɓargo. Muryarta na ɗan rawa ta ce, “ALLAH sarki ƴar uwata. Ashe Asiya bata manta da ni ba”.
Murmushi mai ciwo da ƙuna Maanal ta saki batare data iya cewa komai ba. Sai wasa take da yatsunta
kawai. Oum ta juya ga AA tana faɗin, “Auta kaji fa ashe Asiya bata manta dani ba. Sunana aka sakama ɗiyar
Shahidah”.
Karo na farko ya saki wani irin murmushi mai ban mamaki, irin mai maƙalewa a gefen bakin nan da
sai kana kallon mutum kake sanin yayi, sai kuma ya yunƙura a hankali ya riƙo hannun Barrah, matsota yay
jikinsa kawai ya rungumeta. A mamakin kowa dake falon sai ji sukai ya furta, “I love you so much tunda
kikaci sunan Oum na, ALLAH ya albarkaci rayuwarki”.
“Uncle ni banda ni?”.
Haneeff ya faɗa babu zato. Dariya Oum da RK da masu aikin nan sukayi, yayinda Maanal tai ɗan murmushi
da girgiza kanta. Shi kam AA idanunsa ya buɗe sosai a kan yaron, sai kuma shima ya sakar masa
murmushin da miƙa masa hannu ya riƙosa, cikin maganar nan tasa ƙasa-ƙasa ya ce, “Kaima ALLAH yay
maka albarka”.
Cike da farin ciki Haneeff ya amsa masa. Shima RK da Oum duk suka amsa............✍️
🤔Nayi tambaya ko nayi shiru wai???.. kai Bara dai na haɗiye kayana🥱. Idan kuma akwai mai irin tunani na
mu haɗu a comment 🏃🏃🏃🏃🏃
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
3️⃣5️⃣3️⃣5️⃣
........Sosai zuciyar RK ke yin kaikawo a ƙirjinsa matuƙa akan wannan al'amari. Ba komai ya kawo hakan ba
mamakin Maanal da AA da koda wasa basu taɓa nuna masa sun san juna ba. Sannan miyyasa AA ɗin bai
sanar da Oum fara aikin Maanal a companyn sa ba kusan sati uku kenan. Ko shima dai bai san Maanal ɗin
bane? Alaƙar iya Oum ɗin ce kawai da su Maanal ɗin?. Zuciyarsa na ƙoƙarin gamsuwa da hakan sai ga
sallamar yayan AA ɗin, da'alama ma yanzu ya shigo gidan daga wajen aiki.
Zama yay a kujera yana sauke numfashi. Oum dake kallonsa cike da tausayawa na jera masa sannu.
Amsawa yay fuskarsa da murmushi sai kuma ya ɗora da gaisheta. Sai kuma ya juya ga RK yana faɗin,
“Barka da juma'a Uncle”.
Amsa masa RK yay shima yana murmushin. “Wai sai yanzu kake dawowa gida? Ƙarfe biyar fa?”.
“To ya muka iya Uncle. Bakaga shi Autan Oum da yake ɗan shagwaɓa ne ya gudo wajenta da wuri ba”.
Dariya RK yayi ganin yanda AA ya dallo musu harara su duka ya maida idonsa ga novel ɗinsa batare da yace
komai ba. Sai da suka tsagaita Maanal da kanta ke ƙasa ta shiga gaisheshi ita da su Barrah. Kallonta ya ɗan
yi, sai kuma ya ɗauke idonsa ya maida gasu Barrah yana amsa musu da murmushi. Kasancewarsa mutum
mai barkwanci idonsa akan RK yake faɗin, “Uncle R kodai Momyn tamu ce ne wai? Dan ɗazun Oum ke
sanar min zaka kawota yau”.
Kallon Maanal RK yayi yana mai jinjina kansa fuska ɗauke da murmushi. “Gatanan ai na kawo muku”.
“Kai kai Masha ALLAH, Momyn mu ai ban san ke bace dana durƙusa har ƙasa. Matar Uncle Rafeeq fa.
Bara kiga na taso ki saka min albarka ga ɗanki yazo gaisheki”.
Dariya Oum da RK sukayi, yayinda Maanal ta ɗan ɗago ta kallesa a karo na farko. Dai-dai yana ƙoƙarin
sake yin magana amma sai maganar tasa ta maƙale a saman harshe saboda saukar idanunsa akan Maanal.
Ɗan wara idanunsa yayi na rikicewa, sai kuma ya maida kallonsa ga Oum dake sakin murmushi itama
idonta a kansa. Ai da wani irin sauri ya miƙe ya ƙarasa kusa da Oum ɗin ya zauna, tare da kai bakinsa saitin
kunnenta ya ce, “Oum idona ne kokuwa dai kaina ne ya kwance da gajiyar aiki? Wai kin san wa nake gani
kuwa? Little fa, Bestyn Auta?”.
Kai Oum ta jinjina masa fuskarta na ɗan komawa damuwa, itama a hankalin ta ce, “Itace Fawzan,
Maanal ce. Itace kuma Rafeeq ya kawo mana matsayin wadda zai aura”.
Ai zaram sukaga Fawzan ya miƙe yana faɗin, “What!!” gaba ɗaya idanunsa a waje sosai, sai kuma ya juya
yana kallon AA daya wani share kowa yana sauraren surutun Haneeff, idanunsa kuma nakan novel da
tunda su Maanal suka shigo ya daina fahimtar labarin. Sake ɗaukewa yay daga kan AA ɗin ya maida ga
Maanal daketa ƙoƙarin saisaita kanta. Murmushi ta sakar masa mai sanyi, cikin muryarta mai zurfi da
rashin son hayaniya ta ce, “Yaya F”.
Maimakon amsawa sai yakai zaune jagwab a kujera yana faɗin, “Ya ilahil'alamina da gaske Little ɗin ce
dai Oum. Ni abin ma sai yake min kamar mafarki wlhy”.
“Bakai kaɗai ba Fawzan, ni kaina kallon komai nake kamar a mafarki, yau Rafeeq ya haɗa zuminci sai
dai ALLAH ya saka masa da alkairi. Kalla yaran nan yaran Shahidah ne su duka, macen sunana aka saka
mata ma”.
Kallonsa ya maida ga yaran, sai kuma ya kalla Maanal. “Little! Su Shahidah duk sunyi aure kenan?”.
Kan Maanal a ƙasa ta ce, “Eh yaya. Itama Didi Amal yaranta biyu”.
Wani murmushi ya saki mai kama dana damuwa, sai kuma ya jinjina kansa, “ALLAH sarki rayuwa komai
sai kaga yana faruwa kamar a mafarki. Oum jiba dai Autar ki duk ta canja, komai na Little ya canja kamar ba
ita ba. Ji yanda ta zama shiru-shiru, ba surutu yanzu, komai nata ya canja, ta girma ta ƙara tsayi”.
Murmushi sosai Oum tayi itama idonta akan Maanal datai ƙasa da kanta kawai tana wasa da yatsun
hannunta. “Sosai kam Auta ta canja Fawzan, badan fuskar na nan ba ma sai nace an canja min ita gaba
ɗaya. Girma yazo”.
“A girma yazo kam Oum, ko'a mafarki akace min little zata koma shiru-shiru haka za'a kwana gardama
dani ban yarda ba. Little ina Ammie da Abbah fa?”.
“Lafiya lau Yaya, Ammie na Kaduna itama”.
“Ban gane ba, kun dawo Kaduna ne yanzu?”.
Kai kawai Maanal ta jinjina masa. Cikin mamaki ya ɗan juya ya kalla Oum, itama shi take kallo, kamar
zaiyi magana sai kuma yay shiru saboda maganar da RK yayi....
“Nifa gaba ɗaya sai sake sakani a wani irin dogon tunani mai rikitarwa kuke wlhy Aunty, wacece
Maanal a wajenku dan ALLAH? Ya akai kuma ni ban santa ba?”.
“Ai kwantar da hankalinka Uncle kada ka wani ruɗar da kanka. Maanal dai ɗiyar Oum ce, mu kuma
ƙanwa ce. Abinda yasa baka santa ba lokacin da mukai zaman Kano ne, kai kuma sannan kuna Paris”.
Da mamaki RK yace, “Kenan har AA ya santa?”.
Su dukansu juyawa sukai suka kalla AA ɗin da furucin RK ɗin ya wani daki zuciyarsa, hakan ya sashi
tsayawa cak da karatun da yake duk da dama tun ɗazun ba fahimta yake ba. Kai Fawzan ya jinjinama RK.
Sai kuma ya ce, “Tabbas ya santa”.
Cike da mamaki RK da ke kallon AA ya ce, “Lallai, amma gaskiya na sake yarda kai abin tsoro ne AA.
Amma shine koda wasa baka nuna min kasanta ba. Aunty kusan fa 3 weeks da fara aikin Maanal a
companynsa shiyyasa kikaga inata ƙara jinjina mamakina ai”.
Kallon juna Oum da Fawzan sukayi, sai kuma suka kalla AA ɗin da har yanzu dai yana a yanda yake, sai
ka rantse baya falon ko kuma baya jin mima suke faɗa akansa. Fawzan ya girgiza kansa kawai da
murmusawa, “Ai autan Oum sai addu'a Uncle. Little kice har an kammala karatu?” ya maida hankalinsa ga
Maanal.
Idanunta ta janye daga satar kallon AA ɗin itama. Ta amsa ma Fawzan da, “Eh Yaya har sarvese nayi”.
“Kai Masha ALLAH, kinga rigimarki ta saka kin kammala karatu da ƙarancin shekarunki, kai Little
rigima”.
Hannu Maanal tasa ta rufe fuskarta dan tuna baya. Yayinda Oum keta dariya itama tana tuno abubuwa
kamar labarin Film. A mamakin su sai sukaga AA ya miƙe batare da yacema kowa komai ba ya nufi hanyar
ficewa daga falon. Da kallo kawai suka bisa.... Sai da ya taka step na farko batare daya jiyo ba ya ce, “Oum
na wuce massalaci”. Murmushi Oum tayi da masa addu'a, yayinda RK ya miƙe yana faɗin, “Ɗan rainin
hankali shine bazakace mu tashi lokacin salla yayi ba”. Fawzan ma miƙewa yay yana dariya. Sai kuma ya
fara raira waƙar Hamisu breaker _Ƴar Arewa_.
“Duk wanda yay gamo da abin ƙauna baisan rabewa, in dai ko ya rabe duk nishaɗi nai yay tarwatsewa.
Sirrin farin ciki soyayya in ba takurawa, mai so aso shi kanso babu abinda bazai iyaba.
Na durkusa akan gwiwata idan kuskure nai. Kiyafiya gyaran dan kamin har maganai.
Nemanki na karaɗe kauye na koma birane, fito na ganki Ni kallon kauna kinji yar arewa...
Sissiran dake cikin raina duka ne zan baiyyanawa. So yayi tsitstsige na takawa yay min illatarwa.
Ni bani fasa yarda domin kin zam rayuwata, manta dake hakan ban san yaushene zan iya ba
Kukan da ni nake da kishirwa bata gushe ba, duk da na sani rabuwa bata zamto mutuwa ba.....
Harara mai lasisi AA ya wurgama Fawzan tare da wucewa da sauri-sauri kan stairscase ɗin. Hakan yasa
Fawzan kwashewa da dariya Oum kuma na murmushi. Shi ko RK da bai fahimci inda waƙar Fawzan ɗin ya
nufa ba sai ca yay “To ɗana kodai kaima waƙa zaka koma ne?”.
Shi dai Fawzan dariya kawai yake yi yana cigaba da bin AA da har ya gama sauka daga steps ɗin da
kallo...
Haka suka fice harda Haneeff. Oum kuma ta shiga da Maanal da Barru ɗakinta. Gaba ɗaya idanun Oum
sun kasa daina kallon Maanal da dukkan motsinta har suka idar da salla. Tana son mata tambayoyi sai dai
yanayin Maanal ɗin yasata haɗiyewa, sai ɗan abinda ba'a rasa ba dai da take tambaya Maanal ɗin na bata
amsa. Kiran Shahidah yasa Maanal cema Oum zasu tafi gida. Amma sai Oum ɗin ta amshi wayar tai kiran
Shahidah back.
Koda Shahidah ta ɗaga taji ba muryar Maanal bace sai tayi ɗan jim. Cikin girmamawa ta shiga gaida
Oum. Itako ta amsa mata tana murmushi. “ALLAH sarki Shidan Abba an girma, an zama iyaye”.
Da wani irin zabura Shahidah ta dafe ƙirji da faɗin, “Oum!”. Sai kuma ta cire wayar daga kunnenta tana
sake duba number ɗin. Da gaske no ɗin Maanal ce dai, amma kuma sunan da aka kirata da shi mutum ɗaya
ke kiranta da shi a duniyar nan, sake maida wayar tayi kunnenta ta ce, “Maanal!”.
“Ni ɗin ce dai har yanzu Shahidah. Oum ɗinku ce, yau gani ga ɗiyata a kusa dani Rafeeq ya kawo min
ita har gida”.
Ba ƙaramin motsawa zuciyar Shahidah tayi ba. Ai babu shiri ta furta, “Oum kenan kece auntyn Rafeeq da
Maanal suka zo gaidawa?”.
“Tabbas nice Shahidah, kinga wata hikimar UBANGIJI kuma ko. Dan haka ina roƙon a bar min ɗiyata
da jikokina su kwana anan, gobe in sha ALLAHU da kaina zan maidosu gida tunda weekend ne”.
Koda wasa Shahidah bazata taɓa iya musu da Oum ba, dan haka babu jayayya ta sallama. Sai dai tana
yanke wayar ta maida akalar kiran nata ga Amaal.
★★
“Ni wlhy gaba ɗaya kin hatgitsani Didi wai dan ALLAH da gaske kike yi?”.
“Humm Amaal wlhy nima a hargitsen nake. Kema kin san bazanyi miki wasa da wannan zancen ba”.
“Tofa wannan fa shi ake kira da rikita-rikita. Kenan fa idan lissafin yayi dai-dai Rafeeq Uncle ɗin Ajwaad
ne? Amma ya akai bamu san Rafeeq ba duk yanda yake da kusanci da Oum haka?”.
“Nima wannan tunanin nakeyi, sai dai kuma wani abu yazo raina. Kin san iyayen Oum na ainahi a lokacin
basa Nigeria kamar. Idan baki manta ba muntaɓa jin tana sanar ma Ammie riƙonta akai a gidan Alhaji
Abdulkarim Sardauna. Kingako kenan Rafeeq a lokacin baya Nigeria.”
“Tab ɗin, UBANGIJI mai hikima. Didi ni wlhy ma sai yanzu nima wani abu ke dawo min a rai. Kin manta
randa muka fara gabin Hajiya Majdiya nake cemuku kamar tana min kamanni da wani amma na manta mai
fuskar. Ke da Ammie kukace na cika ƙwaƙwale-ƙwakwalen cewa mutane na kamanni da wasu. To ALLAH
kamanin Oum na gani a tare da ita”.
“Ya ALLAH, tabbas anyi haka kuwa Amaal. Kigafa wani al'amari mai ban mamaki, an rabu amma ashe
ana tare da juna ta inda sam ba'a sani ba. Ni yanzu ma yaya zamu tunkari Ammie da zancen nan Amaal?”.
“Abinda nake hasasowa a zuciyata kenan, Ammie zatai matuƙar farin ciki. Sai dai kuma Auta Didi, ita
nake tausayi da tunani a wannan gaɓar, dan dole ne ɗayan biyu, rabuwa da Rafeeq duk da dama bawani ta
amshesa bane, sai kuma auren Yazeed”.
“Humm Amaal kenan, na fahimci kumafa har yanzu kun kasa fahimtar Ajwaad na'a zuciyar Auta daram,
shiyyasa ta kasa amsar kowane namiji a rayuwarta. Abinda ya faru ne kawai ke danne soyayyar da tsiya-
tsiya.”
“Na sani Didi, sai dai kema kin san kafiyar Maanal. Kin san idan har tace tabar abu tofa ta barsa ɗin
kenan, kuma shi kansa Rafeeq alaƙarsa da Ajwaad sai shi zaisa ta rabu da shi rabuwa ta gaske a yanzu.
Kinga kuwa babu wata mafitar data rage mata kuma sai na auren Yazeed, dan dama shigowar Rafeeq ɗin
rayuwarta ne kaɗai hope ɗin mu. Babu shi kuwa da kunya a tunkari Daddy da batun ƙin auren ɗansa ko?”.
“Wato Amaal wannan batun na buƙatar zama gaskiya. In sha ALLAHU next week zan shigo kd. Badan
ma Oum ɗin tace gobe zata shigo nan ba da goben zanzo.”
“Hakan ma yayi ALLAH ya kaimu, dan nima ban jima da zuwa Abujan bane, yanzu ko nace zanzo sai
Abban Munaya yata mita.”
“Ai yama yi ƙoƙari, tsakanin nan kunsha zarya sosai. Ki bari zan shigo ɗin kawai. Bara naje kin san ƴar
iskar yarinyar nan na nan gashi babu su Maanal sai Linda kawai, da safe mayi waya”.
“Okay ba damuwa ALLAH ya tashemu lafiya”....
________________
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
3️⃣6️⃣3️⃣6️⃣
______________
https://chat.whatsapp.com/KU8Mqd2Mo530Pc14hc7QOG *ROYAL JELLY* *(MAIDA TSOHUWA YARINYA)* 🔥💃💃
Wani kayan sai amale wannan supplement shi akecema maida tsohuwa yarinya ita Kuma yarinya ta koma
jaririya😂 Ina kuke Mata masu aji waanda sukeso suga suna walwali kamar tauraro toh gafa dama tasamu
kiyi washar washar abinki.....🔥⭐⭐👑 Royal jelly nasa jikin mace yayi glowing mace jikinta yayi Kamar tangaram
😍😍 ⭐👑 Royal jelly natsoro da gashin mace yayi kyau ⭐👑 Royal jelly na gyara mace ciki da wajenta ⭐👑
royal jelly na fidda shape din mace...💃💃⭐👑 Royal jelly na Hana fatar mace tamukewa , yasa tayi looking
fresh ⭐👑 Yanasa mace yayi looking under age dinta💃💃💃kiji ana wacce ke kullun kamar wata budurwa🔥🔥 ⭐👑
Royal jelly nakara hasken Ido yakuma gyara gashin ido 🔥⭐👑 Royal jelly na tsirar da farce da kwarinshi... Idan
kinji ana maganar glowing to kici birki a royal jelly 🔥🔥⭐👑💃🏼💃🏼 Haseer supplements ta kawo muku
supplement kaloli sai wanda ranki keso hajiya a cikin farashi mai sauqi Phone: 08038796871
_____________
..........“Alhaji Aliyu Darma ba shike auren babbar ɗiyar Dr Kasheem Kura ba kuwa?”.
“Eh shine, kamar ma itace ta haifi shi yaron nan AA Darma ɗin ai”.
“Okay! Ok! Ok na gane. Yanzu ita yarinyar minene aikinta a kamfanin?”.
“Eh wannan ne dai nake kan bincike ranka ya daɗe. Amma in sha ALLAHU a cikin satin nan zan kammala
shima. Na fara kawo maka wannan ɗin ne dai”.
“Ba damuwa Rabilu, hakan ma kayi ƙoƙari. Amma ina son ka binciko min ainahin mahaifin yarinyar
shima”.
“To ranka ya daɗe in sha ALLAHU an gama. Wannan itace lambar wayarta”.
“Ok ka samu Oler a waje zai baka kuɗin zuba mai”
“Nagode sosai ALLAH ya ƙara girma da ɗaukaka Ranka ya daɗe”. Rabilu ya cigaba da jera godiya kamar ba
gobe...
Yana ficewa Sen.. Bukar yay wani murmushin ƙasaita, tare da shafo sajensa da furfura ta gama yima
ƙawanya. Tabbas love at first sight ne ya shigesa na yarinyar nan. Dolene ta shigo a cikamakin matansa uku
matsayin ta huɗu, koba komai ya samu ta sakawa a gaban mota dan amaryarsa ya fahimci itama yara sun
fara tsofar da ita. Dan ta bari ƙiba ta fara zama mata, shiko sam baya ƙaunar mace tayi ƙiba, hakanne ma
ya sakashi ƙara aure na biyu saboda uwargidansa itama haka ta zama rabkekiya, yayi yayi suje a rage mata
ƙiba taƙi, sai kawai yayi ta biyu. Itama ɗin dai kwana biyu ta ƙibe masa. Haushi ya sashi auro ta uku, amma
abin mamaki itama yaga yanzu ta ɗakko hanyar yin ƙibar, to gara tun kafin ma suje ga hakan yayma tufkar
hanci. Dan Maanal zatai dai-dai da ra'ayinsa, gata ƙaramar yarinya. Murmushi ya sake saki, yana jin kamar
ya tashi ya fara taka rawa. Dan babu abinda yake sai siffanta surar Maanal a zuciyarsa......
___________★
Tsaye yake kawai ya zubama harabar gidan ido hannayensa duka a cikin aljihun baƙin wandonsa. A
kallo ɗaya zaka fahimci yayi matuƙar yin nisa a duniyar tunani. Dan har Fawzan daya shigo sashen nasa ya
iso inda yake babu alamar yasan da shi. Sai da ya kai hannu saman kafaɗarsa ya ɗan bubbuga sannan ya
juyo...
Murmushi Fawzan yay masa tare da masa alamar minene? da idanu. Sake tsuke fuska AA yay tare da
kauda kansa ya ce, “Nothing”.
Ƙaramar dariya kawai Fawzan yayi yana mai girgiza kansa. Sai kuma ya matsa jikin ƙarfen balcony ɗin ya
jingina tare da harɗe hannayensa a ƙirji shima ya zubama AA ɗin idanunsa. “Auta kenan, kai kasan ko zaka
ɓoyema kowa kanka banda ni nan. Dan na sanka fiye da yanda nasan yunwar cikina ai ko?”. Ya ƙare
maganar da wani ɗan ɗage gira sama.
Idanu AA ya lumshe tare da buɗewa duk a lokaci guda. Kamar zai yi magana sai kuma ya maida bakinsa
ya tsuke. Murmushi Fawzan ya saki sai kuma ya juya ya kalla inda idanun AA ɗin suke kallo, flat ɗin Oum ne
dan haka ya sake maido kallonsa ga AA ɗin.
“Ajwaad nasan har yanzu kana sonta, ba kuma zaka taɓa daina sonta ba. Wannan dama ce ta biyu
ALLAH ya sake baka, duk da nasan damar tazo da ƙalubale masu yawan gaske. Ka manta da abinda ya faru
a baya domin ƙaddararku ce kai da ita, babu wanda ya isa hana faruwarta. Tun kafin Uncle Rafeeq yay wuff
da ita kasan mai yiwuwa, dan yanzu 2025 muke ba shekarun baya da suka shuɗe ba, wannan Maanal ɗin
ba wadda ka sani bace a baya, dan tabbas Uncle Rafeeq shima yana sonta sosai.....”
Da ƙarfi AA ya rumtse idanunsa da suka sake kaɗawa, tare taune lip ɗinsa. Kalmar _Sonta..._ ɗin nan na
sukarsa.
Fawzan ya cigaba da faɗin, “Sai dai hakan ba yana nufin kai bazaka nuna taka bajintar ba, sai dai ka sani
wannan shiru-shirun naka fa da miskilanci dole ka ajiyesa gefe ka koma mata Bestien ta nada da kukai
wasan ƙuruciya tare, mai tare mata faɗa, mai damuwa da damuwarta sama da kowa. Dan bana raba ɗayan
biyu har yanzu kana nan daram a zuciyarta itama. Nasan Oum zata baka goyon baya ɗari bisa ɗari. Sai
kuma ƙalubale na biyu batun Nuratu, kasan dai su Abbah sun fara magana, akoda yaushe kuma zasu iya kai
kuɗi idan har baka kawo zaɓinka ba kamar yanda sukace. Dan haka sai kaje kayi tunani kafin lokaci ya ƙure
maka. Ina maka fatan nasara”. Ya ƙare maganar da ɗan bubbuga kafaɗar AA ɗin batare da ya jira cewarsa
ba yabar balcony ɗin.
Kasa ko motsi AA yay har Fawzan ya fita a sashen gaba ɗaya, daga ta harabar gidan ya kallosa yana
nuna masa kansa sai kuma ya ɗaga hannunsa yay masa nuni da agogo alamar lokaci daga haka yay
wucewarsa. Da kallo ya cigaba da binsa har ya shige sashensa. Dai-dai nan kira ya shigo wayarsa. Iska ya
ɗan furzar mai ƙarfi daga bakinsa kafin ya zarota daga aljihu yana kallon mai kiran. Oum ce da kanta, dan
haka ya ɗaga a kasalance ya kai wayar kunnensa yana mai zubama flat ɗinta idanu kamar zai iya hangota
daga nan.
“Auta na kana ina ne wai?”.
Idanunsa ya lumshe sai kuma ya saki ɗan murmushin gefen baki daya kasance ɗabi'arsa. Muryarsa can
ƙasa ya bata amsa. “Ina sashena Oum”.
“To maza zo ina nemanka”.
Daga haka ta yanke kiran. Wayar ya sauke daga kunnesa yana furzar da iska, sai kuma ya maidata a aljihun
batare da yace komai ba yabar balcony ɗin.....
____________
Gaba ɗayansu suna a kan d/table kamar yanda Oum ta sakasu yi. RK da Oum ne kawai ke hira, sai dai
kuma idanunsa nakan Maanal dake ta faman juya spoon a abincin da RK ɗin ya zuba mata da kansa. Tunda
ya zuba matan bata kai ko lauma ɗaya bakinta ba, da farko ma hankalinta na'a kan Novel ne. Sai da Oum
tai mata magana sannan ta rufe book ɗin ta ɗauki spoon ɗin. Shine kuma taketa faman juya abincin, ta
kuma zuba masa idanu kamar mai irgashi ko tantance abinda aka dafashi da shi. Ita Oum ta fahimci abinda
ya saka Maanal ɗin komawa hakan game da abincin, shiko RK sai ya ɗauka ko bata sonshi ne ko kuma dai
hankalinta na gida... Kaɗan yay gyaran murya tare da kiran sunanta. A hankali ta ɗago manyan idanunta da
kalarsu ta sauya kaɗan, a mamakinsa sai ta sakar masa murmushinta mai sanyi dake narkar da shi. Hakan
kuma yayi dai-dai da isowar AA dining area ɗin, kuma a kanta idanunsa suka fara sauka dan haka yaga
murmushin data sakar ma RK ɗin. Cak ya tsaya kamar wanda akama tsawa. Shiko RK sam baima gansa ba,
dan haka ya maidama Maanal ɗin murmushinta cikin ɗan ranƙwafowa gareta ta yanda ita kaɗai zata ji
abinda zai faɗa ya furta, “Gimbiya irin wannan murmushi haka ai sai kisa na ɓace ɓat. Dan ALLAH kici
abinci nan fa gidanku ne. Kin san kowa na cikinsa kafin ki sanni ma. Idan kuma baƙya sonshi a canja miki da
wani?”.
“Oum gani!”.
AA ya faɗa cikin kaushin muryar data fargar da kowa kasancewarsa a wajen. Sai kuma yanda yay maganar
da zafi-zafi ya bama RK mamaki dan abune da bai saba gani ba. AA bashi da yawan hayaniya, amma kuma
baida faɗa. Barshi dai da fushi da baƙar maganar tsiya kamar jikan banbaɗawa. Oum ko data fahimci inda
fushin ya dosa sai tayi murmushi kawai da faɗin, “Yauwa Autana maza zo ga abinci kada yay sanyi, dan
favorite ɗinka akayi”. Tai maganar tana kamo hannunsa ta zaunar da shi a kujera. Maanal kam ko ɗagowa
batai ba balle ma ta kalla inda AA ɗin yake, kai bama ta nuna tasan da zuwansa wajen ba sam. Hakan kuma
sai ya ƙara baƙanta masa rai, koda Oum ta zuba masa abincin ma ya ɗau kusan mintuna biyu kafin ya fara
ci, sai da ma ta sake masa magana da taɓashi.
Maanal ma dai ta fara tsakurar abincin. Duk da kuma yanda ta share kamar bata san da zuwan AA ɗin
ba tana satar kallonsa ne ta gefen ido. Yayinda RK ke mata magana lokaci-lokaci, sai dai maimakon amsa
ɗan murmushi kawai take masa da jinjina kanta ko girgizawa. Sai yanzu ne maganar Barrah ta sakata
ɗagowa, sai idanunta caraf cikin na AA. Wani shegen kallo ya zuba mata data fassara dana tsananin tsana
da ƙyama. Babu wani yanayi data nuna ko a fuska ta janye nata idanun zuwa kan Barrah ɗin. Daga haka
bata sake yarda ta kalla inda yake ba ma har suka kammala. Itace ta fara barin dining area ɗin, hakan yasa
RK tashi ya bita shima.
Da wani kalar yanayi AA ya lumshe oily ayes ɗinsa, batare da ya lura ba ya hankaɗe glass cup ɗin ruwan
da aka ajiye masa. Tarwatsewar kofin da ruwan cikin saman ƙyaƙyƙyawan farin tils ɗin ya saka hankalin
kowa dawowa wajen. Oum ta miƙe tana mai kamo hannun nasa da sauri ta ce, “Subahanallahi Auta bakaji
ciwoba dai ko?”.
Idanunsa dake lumshe har yanzu ya buɗe, sai kuma ya girgiza mata kansa batare da yayi magana ba. RK
da tuni ya ƙaraso wajen shima ne yay kiran masu aiki ta landline, kafin ya juyo ga AA ɗin yana masa sannu.
Ko kallonsa AA ɗin bai yi ba, shima kuma sai bai damu ba. Dan halinsa babu wanda bai sani ba a gidan
dama dangi baki ɗaya. Maanal dai na zaune daga inda take tana kallonsu kawai, amma bata da niyyar
tasowa ma. Haka masu aiki suka gyara wajen kamar komai bai faru ba, shima sai ya miƙe.
Oum ce dake binsa da kallo ta ce, “Abincin fa?”.
“Oum na ƙoshi, zanje na kwanta sai da safe”.
“Kwanciya da wuri-wuri haka? Gobe fa babu office”.
RK ne yay maganar yana binsa da kallo. Kansa ya jinjina masa kawai, sai da yaje ƙofa batare da ya juyo ba
ya furta, “Anan zaka kwana ne?”.
Kallon agogo RK yay, “No zan wuce dan inada aiki a asibiti ma zuwa nine. Dan har ma sun fara kirana.
Zanyi sallama da Maanal kawai”.
A taƙaice ya ce, “Okay” yay ficewarsa. Shima RK wajen Maanal ya koma, yayinda Oum tai shiru kawai
zuciyarta na mata kaikawo a ƙirji. Batare data sani ba ta zubama RK da Maanal idanu. Abubuwa ne da
yawa ke cuɗa kansu a zuciyarta fiye da yanda take nazarinsu tun ɗazun. Sai dai bata da wani abincewa a
wanan gaɓar gaba ɗaya....
★★★
Wanka yake son shiga yayi, sai dai haka kawai ya samu kansa da tsayawa jikin window ɗin falonsa ya
zubama harabar gidan ido ko nace flat ɗin Oum. Shi kansa bai san ma'anar tsaiwar tashi ba, amma ya
cigaba da tsayawar. Hannunsa ɗaya a aljihu ɗayan kuma yana faman ɗagosa ya kalla agogo alamar duba
mintuna. Mintuna ashirin ya ɗauka cif a wajen kafin abinda zuciyarsa ke jiran gani duk da yana faman
ƙaryata hakan su fito. RK ne gaba Maanal a bayansa, sai dai suna gama fitowa RK ɗin ya dai-daita tafiyar
tasu kafaɗa da kafaɗa, tare da ɗan ranƙwafowa gefen Maanal yana magana fuskarsa da wadataccen
murmushi hannayensa duk biyu goye a bayansa. Gani yay Maanal ɗin ta tsaya cak, tare da hararar RK ɗin,
amma shi sai hararar ta juye masa zuwa kallon soyayya ne, musamman daya ga yanda RK ɗin yay wata irin
dariya cike da nishaɗi yana kuma maganar da shi sam baya iya jiyowa daga nan. Da ƙarfi ya rumtse
idanunsa tare da datse laɓɓansa da haƙori tamkar zai hudashi. Haka yake idan har abu zai ɓata masa rai ko
zaiyi magana yanada ɗabi'ar rufe idanu.
Kamar wanda aka zabura ya wani irin buɗe idanun tare da fara takawa cike da nitsuwa da ƙasaitarsa
yayo waje. Kai tsaye sashen gaban Oum ya nufa tamkar wanda ake ingizawa, dai-dai nan motar RK ta gama
ficewa a gidan, yayinda Maanal dake tsaye har yanzu ta yunƙura zata koma sashen Oum ɗin tana sauke
ajiyar zuciya. Haka kawai yau kuma sai abubuwan RK ɗin ke mata tasiri a zuciya. Duk da dai tasan a
tsakanin nan tabbas bata jin zafinsa kamar sanda suna a Jos.
Da sauri taja da baya tare da tsayawa cak ganin mutum a gabanta gingirin. Sai a lokacin ni'imtaccen
ƙamshin turarensa ya wani bulala mata cikin hanci saboda yanda iska ta kaɗo mata shi sosai. Ɗan lumshe
idanunta dake a cikin gilashi tayi sai kuma ta buɗe a lokaci guda tana ƙoƙarin daidaita kanta. A dakenta, a
kuma nutsenta ta ɗago manyan idanuntan ta sauke akan ƙyaƙyƙyawar fuskarsa dake a tsuke, sai dai
tsukewar tata bai hana kwarjininsa da mutumtaka da gizagonsa bayyana ba. Shima idanun nasa dake cikin
fari tas ɗin eyeglasses ɗinsa dake matuƙar sake ƙawata fuskarsa da gwarzantashi akanta suke. Hakan yasa
suka zubama juna ido, kallo irin na tsakkiyar idanun nan. Sai dai sam Maanal bazata iya jurewa ba, dan
haka ta janye nata a hankali tare da rissinar da kanta. Cikin sabon yanayinta dake baƙanta masa zuciya da
ƙona masa ita ta furta, “Kayi haƙuri sir, ban san kataho bane”. Tai maganar ƙasa-ƙasa da ƴar muryarta mai
zurfi tana sake jan jikinta baya, tare da raɓawa ta gefensa zata zagayesa ta wuce.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
3️⃣7️⃣3️⃣7️⃣
______________
__________
........Babu shiri taja ta tsaya cak, sakamakon jin an cafke tsintsiyar hannunta. Idanunta ta lumshe da ƙarfi
sosai, zuciyarta na wani irin mahaukacin bugawa tamkar zata faso ƙirjinta ta fito. Sai dai me wannan
Maanal ɗin ba Little Maanal bace ta shekarun baya. Wannan Maanal ce, Maanal cikakkiya ɗiyar Ammien
ta. Wadda taga jiya taga yau take kuma fata da ganin gobe. Maanal ɗin data iya ɗauka da shanye abubuwa
masu nauyin gaske da ko namiji sai jarumine zai iya zama irinta. Tuni ta saita kanta cikin dakiya da jarumta.
Batare da ta juyo ko yin magana ba tai ƙoƙarin fisgar hannun nata. Sai dai me wannan rikon bana rago
bane, ba kuma na sakaran namiji bane. Dan riƙone akai mata irin na manyan sadaukai. Ta fahimci hakan ta
yanda koda ta fisgi hannun nata duk da da ƙarfi tayi shima bai ko motsa daga yanda yake ba, bai kuma juyo
ya kalleta ba balle yin magana.
Sosai zuciyarta ta fara hasala, hasala irin wadda har take jin ɗacinta a maƙoshi. Cikin bayyanar ɗacin a
harshenta ta furta, “Minene ma'anar hakan da kake yi?”.
Idan ginin gidan ya tanka shima zai tanka kenan, maimakon yin maganar ma sai fisgarta yay da ƙarfi yay
sashensa da ita. Tana ƙoƙarin tirjewa amma hakan bamai yiwuwa bane gareta. A haka ya bugi ƙofar sashen
nasa da ƙafa tare da tura kai ciki. Da wani kalar salo ya jefa Maanal saman lallausar kujerar falon, kafin tai
wani yunƙuri ya rufu a kanta ta hanyar ɗaura ƙafarsa ɗaya a kujerar ya dogare, ɗayar na a ƙasa.
Wani irin matsewa da matuƙar takura Maanal taji da tsaiwar tasa a haka, tuni jarumtar tata ke neman
suɓucewa, dan yanayin neman tuno mata da babban al'amarin daya shuɗe yake a rayuwarsu ta baya
amma tana fisgo dakiyarta da tsiya-tsiya. Komai ta haɗiye daga fuskarta da harshenta idanunta a rissine
dan bazata iya kallonsa ba ta furta, “Sir minene kake yi haka ne?......”
“Oh you're still pretending?”.
Ya faɗa cikin wani irin kaushi da ɗacin murya mai razanarwa. Dan ita kanta Maanal ɗin sai da taji kayan
cikinta sun kaɗa. Amma da yake itama yanzu gwanarce. Ta karantu daga kowanne irin salo da taku sai ta
zuba masa idanunta, wani shegen murmushi mai saka yin kamar zaka lumshe idanu ta sakar masa. A
nutsenta tana mai sake tsatstsaresa da idanu ta ce, “Pretending?! Dan mi zanyi pretending? Akan me
kuma? Yallaɓai”.
Wani kalar taune laɓɓansa yay da rufe idanu yana dunƙule hannunsa. Kamar zai kai mata duka sai kuma
miya tuna ya fasa. A maimakon hakan sai ya nunata da yatsansa manuniya.
“Na fiki zafin kai”.
Yanda yay furucin yana wani wara mata manyan oily fararen ayes ɗinsa masu girma da cikar gashi dake
cikin gilashi sai ta sake jin tsoro na mamayeta. Amma dai tai ƙoƙarin sake dakewa yanzu ma ta taɓe bakinta
ta dauke kanta kawai. Cikin ƙunƙuni ta ce, “Ina ruwana to da zafin kan naka”. Hannu ya kai zai cafko fuskar
tata, a zabure ta matsar da jikinta tayi ta gefen daya ajiye ƙafarsa, dan gaba ɗaya ji take kamar an sakata a
wani kurkuku dama. Hatta da iska bata shaƙa yanda ya kamata saboda kusancin nasu. Haka ta miƙe ta nufi
hanyar fita cikin sassarfa. Wani irin juyowa yay tare da sanya mata ƙafa sai gata a saman kujerar ta sake
zubewa.
Hannayensa duka ya zuba a cikin aljihun wandonsa yay wani irin tsaya mata bisa kai ya zuba mata
idanun sa tamkar zai haɗiyeta da su. “Ni kike ma ƙunƙuni?”.
Baki ta ɗan tura gaba, sai kuma ta kauda kai gefe, “Ni yaushe na maka ƙunƙuni?”.
Ƙwafa yayi cike da sake ƙuluwa, cikin kakkausan lafazin da bata san ya iya ba ya furta, “Na baki nan da
kwanaki uku kacal ki fito ki faɗama Rafeeq gaskiya. Idan ba haka ba kuma zaki sha mamaki”.
A karo na farko ta zuba masa wani irin kallo tana miƙewa akan ƙafafunta, a gabansa ta tsaya sunama
juna kallon ido cikin ido, cikin kausasa masa harshen itama ta ce, “Oh mamaki? Ai ba yau na fara shan
mamaki daga gareka ba daman. Gaskiya kuma bismillah ai ban hanaka sanar masaba kai, maza sanar masa
kafin iska ta rigaka. Ina dai iyaka yace ya janye daga aurena ko, sai me? Nace sai me idan yayi hakan? Ko
hakan sabon abu ne daga cikin rayuwata balle ya daman. Ba shi kaɗai ne namiji ba, dubu bayansa biye
suke dani kuma in har na basu dama tamkar ƙyaftawar ido zasu amsa da rawar jiki har suna shelantama
duniya samuna cike da murna da farin ciki. Balle nayi imanin ko ƴaƴa goma na haifa a duniya Rafeeq zai
amsheni ni da su da hannu biyu ya godema ALLAH saboda soyayyar da yake min ta dabance, SO na yake,
tsananin SO da wani mahaluki baitaɓa min kwatankwancinsa ba a wannan duniyar.....”
“Ƙarya kike yi!!! I said you are lying!!!!!”.
Ya faɗa cikin wani irin ƙaraji idanunsa da suka kaɗa jazur na firfitowa tamkar zai mareta. Matuƙar
tsorata tayi, dan ta gama yarda marin nata zai yi kawai, sai da taji shiru sannan ta buɗe idanunta data
rumtse. Suma sun kaɗa sunyi jazur kamar nashi. Cikin dakiya da sake tsatstsaresa da idanun ta ce, “Kai ka
ɗauka ƙaryar ne, amma ni da yake nunama soyayyar zan bada labari. Zan kuma tabbatar maka da hakan
nan da ƙanƙanin lokaci. Wata ɗaya kacal zuwa biyu zan zama MATARSA, MALLAKINSA ta har ABADA in sha
ALLAHU”. Ta raɓashi tai wucewarta fuuuu.
Baiyi wani yunƙurin dakatar da ita ba a yanzu, dan bai ma motsa daga yanda yake tsayen ba harta
gama ficewa. Sai lokacin yay wani irin kai hannu ya hankaɗar da flower base ɗin dake ata bayan kujerar
mai tsananin ƙyau da ƙayatarwa. Jikake tatsatsa ya tarwatse a ƙasa komai ya zama pieces.
“I will teach you lesson”.
Ya faɗa da tsananin kaushin murya dake bayyana dukkan fushinsa. Daga haka ya juya zuwa cikin
bedroom ɗinsa. Kayan jikinsa ya fara zarewa kawai yana wulli da su, kafin ya wuce cikin closet ɗinsa ya
ratsa ya shige bathroom. Ƙaton gaske ne shima. An kuma tsarashi da kayayyakin toilet masu ƙawa tamkar
ba banɗaki ba. Ƙarƙashin shower yaje kawai ya buɗe duka ukun ruwa suka fara saukar masa a jiki
shaaaaa!! Tamkar irin ruwan samar nan mai zuwa babu zato. Hannayensa kawai ya dafe a jikin glass ɗin da
aka zagaye wajen wankan da shi ruwan na cigaba da saukar masa. Yafi mintuna talatin a haka dan har
numfashinsa ya fara fisga alamar ruwan ya masa yawa sannan ya kashe, a haka ya cigaba da tsaiwar ruwan
daya saukar masa na kwararewa musamman na cikin sumarsa dake lashe kuɗaɗe da shi kansa bai san
adadi ba. Ada shi ba ma'abocin tara suma bane, amma wasu dalilai suka sakashi fara tarawar harta zama
ɗabi'arsa. Ba tara sumar kawai ba, abubuwa da yawa ya ɗabi'antu da su ne daga baya bisa wasu dalilai.
Kuma a yanzu sun zama halittarsa kuma jinin jikinsa da shi kansa bai taɓa tunanin raba kansa da su ɗin
ba...
Ya jima a hakan, dan sai da zuciyarsa ta koma ta kwanta cikin ƙirjinsa luf kafin yayi wanka kamar yanda
ya saba da brush ya fito, idanun nan sunyi matuƙar juyewa da komawa jajaye. Gaban mirror ya tsaya yana
goge jikinsa, kafin ya shafa mansa mara hayaniya ya feshe jikinsa da sprys ɗinsa masu ƙamshin tsiya da
saka zuciya nutsuwa. Ya kuma gyara kansa da kwantaccen gashin dake lafe a kumatunsa, ya sama bakinsa
ƙamshi. Tausasan kayan barci farare tas ya sanya, ya sake feshe jikinsa da turarurrukansa na barci tamkar
ba kwanciya zaiyi ba sannan ya nufi katafaren bed ɗinsa dake a wani kalar dunƙule waje guda tamkar zero.
Zama yay ya jingina da gadon tare da kai hannu ya rage fitulun ɗakin ya maida mai duhun haske sai bed
side lamp kawai dake kunne itama ta gefensa. Sai da yaja lallausan duvet ɗinsa ya rufe ƙafafunsa zuwa
ƙugu sannan ya ɗauki eyeglasses ɗinsa dake ajiye kusa da novel ɗinsa dake a bed side drawer ɗin ya saka,
novel ɗin shima ya ɗauka. Alamar daya saka a inda ya tsaya ya sashi buɗewa kai tsaye ya fara karatu cike
da son kauda komai dake cinkushe da zuciyarsa.....
___________★
Kamar yanda ta saba damunsa a kowanne dare da sakwanni yau ma tsaf ta kammala shirin barcinta ta
faɗa saman gado. Jinta take wani free yau ita kaɗai a ɗaki babu Maanal. Sai hakan ke sakata nishaɗi tun
ɗazun. Yayinda tuni ta kaima uwarta gulmar fitar Maanal ɗin da saurayi da rashin dawowar tata. Nan
sukasha gulmarsu da aibanta Maanal ɗin wai tana can an kaita hotel yawon fasiƙanci dai aka fake fa
dubiya. Bayan sun kammala wayar ne tai abubuwan da malam ya bata tai shirin barci shine ta ɗauki waya.
Kai tsaye data ɗin ta ta buɗe. First WhatsApp ta fara shiga, duk da ta fahimci kamar bai cika damuwa da
WhatsApp ɗin ba sam. Amma tanan take saurin gane idan yana online. Koda yake da wahala ma kaga ya
kashe data shi kam. Yanzun ma dai kamar yanda tai fata yana online ɗin, cike da farin ciki ta tura masa
sallama da gaisuwa kamar yanda ta wajabtama kanta a yanzu. Ganin fin minti biyar babu amsa ta shiga
masa WhatsApp call. Amma har ya kashe ba'a amsata ba. Fita tai ta koma ta tura masa ainahin massege,
nan ma mintuna biyar shiru. Sai tai direct call kawai tana fatan ya ɗauka koda bazai ce mata komai ɗin ba
kamar yanda ya yi mata. Dan data taki sa'a ya ɗauka har sau kusan uku data kira shi, sai dai daga sallama
da amsa mata gaisuwa a cinkushe baya sake cewa komai zai barta taita surutunta harna tsahon mintinan
data fahimci batasu yake daga haka a takaice yace goodnight ya yanke wayarsa. Kota sake kira kuma bazai
amsa ba. Sau biyu yana mata haka, sakamakon roƙon wannan alfarmar datai a garesa jiya data bisa office,
a lokacin bai tanka mata ba, amma data kira ɗin bayan ya gama bata wahala sai ya amsata a jiyan, hakama
yau da safe. Shine ta samu hope ɗin sake kiransa yanzu ma da fatan ya ɗaga ɗin dan tanada yaƙinin aikin
malam ya fara karɓuwa. A wajen bikin Yaseerah ko kallo bata ishesaba fa, amma a wannan karon gashi ya
kulata har a office data samesa ya kuma bada mota aka maidata gida, ai dole tace aikin malam yayi.
A kasalance ta ajiye wayar ganin kira har uku babu amsa, amma sai zuciyarta sam bata gajiyaba, har
yanzu tana jin zalama da fatan ya amsa ɗin. Sake tura masa text massage tayi har uku na roƙon ya ɗaga
kiran, ta watsap ɗin ma ta tura masa, sannan ta sake kira. Sai dai yanzun ma babu alamar zai ɗaga mata.
Idanunta na zubar da hawaye ta tura masa tsararren sabon saƙo masu kalamai masu armashi da kashe
zuciya sannan ta kwanta badan taso hakan ba. Ta jima batai barci ba hawaye na bin fuskarta. Ita kanta bata
san irin son da takema bawan ALLAHn nan ba. Amma tabbas mai zafi ne. Matuƙar zafin da ta tattabar idan
bata mallakesa a matsayin miji ba akwai ƙura......
___________★
Maanal bata koma sashen Oum ba sai da ta tabbatar ta daidaita kanta da nutsuwarta a waje. Dan sai
da tasha kukanta sannan ta share hawayenta tsaf ta koma sashen Oum ɗin. A falo ta sameta mai aikinta na
kwashe su Barrah da sukai barci za'a kaisu ɗaki ai musu shirin barci kamar yanda taji Oum ɗin na bada
umarni. Komai batace ba, sai zama tai tana murmushi da faɗin, “Oum duk munzo mun sakaki wahala”.
Harararta Oum tayi cikin sigar wasa. “Oh haka kike ɗauka shiyyasa kika kasa sakin jiki dani. Gaba ɗaya
kamar ba Lillyn babban yaya ba, kamar ba Autar Oum ba, kamar ba Bestien Auta ba. Maanal kin canja min,
matuƙar canjawa da mamakin hakan ya kasa barina”.
Kai kawai Maanal ta duƙar tana murmushinta mai sanyi, sai kuma ta furta, “Nama manta banga Babban
Yaya da matarsa da Mamy da Abbah ba?”.
“Uhm sai yanzu kika tuna da su? To suna nan abinsu. Mamy tana tare da Abbanku ne a ƙasar Oman,
Amma ina ƙyautata zaton nan da kwana biyu suna hanya insha ALLAHU. Babban yaya kuma da matarsa da
matar Fawzan da yara suna Kano ana bikin ƴar ƙanwar Mamy ɗin ne kin san kuma itama Saheeba kamar
ƙanwa ce a wajenta. Shine matar Fawzan ta mata rakkiya shima yau Babban yaya ya wuce da yammar nan
dan yana fita kuna shigowa. Ɗaurin auren safe ne shiyyasa yaje ya kwana sai ya dawo goben idan ALLAH ya
kaimu. Su kuma sai biki ya tashi, Fawzan da Auta aiki ya hanasu zuwa, ni kuma jikin nawa ne sai a hankali”
Cikin gamsuwa Maanal ta jinjina mata kai batare data sake cewa komai ba, sai dai tayi mata addu'ar
lafiya mai dorewa. Daga haka itama Oum ɗin ta zuba mata ido kawai. Sai kuma zuwa can ta katse shirun
nasu da faɗin, “Rafeeq ɗin ya wuce kenan?”.
Batare data ɗago ba ta ce, “Eh wai ana jiransa a asibiti ne”.
“Uhm ai ya riga da ya ɗaurama kansa irin aikin Papa. Gashi nan gaba ɗaya nauyin ya koma kansa yanzu,
dan ma Papan na ƙoƙarin rage masa wasu abubuwanne. Mu kuma so muke shi ya huta saboda tsufa, dan
ma ALLAH ya bashi jiki mai ƙyau ne da kuma zuciyar taimakon al'ummar. Tun yaushe kuke tare da Rafeeq
Maanal?”.
Matuƙar dukan zuciyarta tambayar tai, dan har sai da ta motsa mata a cikin ƙirji, maƙoshinta ya ɗan
bushe saida ta haɗiyi yawu da ƙyar. Yanzun ma bata ɗago ba kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta ta
bama Oum ɗin amsa cikin Muryar tan nan ƙasa-ƙasa.
“Shekara ɗaya kenan Oum, a Jos inda nayi sarvese”.
“Oh iko ALLAH, dama kece yaketa bani labarin ya samu a Jos ashe. ALLAH mai girma kenan. Ya jima yana
faɗa mana ni da Majdiya, sai dai bamu maida hankali ba saboda sanin halinsa sarai. An jima ana fama da
shi akan aure yana botsarewa da faɗin shi baiga wadda tai masa ba. Har Papa ya fusata zai haɗashi da wata
yarinyar abokinsa sai gashi da zancen ki. Amma sai babu wanda ya ɗauka serious ne. Ko kwanciyar asibitin
nan naƙi zuwa ne saboda ban wani yarda da gasken yake ba duk da Majdiya ta sake tabbatar min. Ashe
nayi sake da tuni naga ɗiyata da ƴar uwata. Nayi kewar Asiya matuƙa Maanal. Haka ke da su Amaal, idan na
tunaku a raina har hawaye nake wani lokacin. Bana fatan ALLAH ya sake maimaita min abinda ya faru a
baya”.
Hawayen da suka cika idonta suka gangaro. Hannu tasa ta sharesu da sauri tana murmushi mai ciwo. Sai
kuma ta miƙe tana faɗin, “Kinga tashi muje kiyi shirin barci ki kwanta. Dan Rafeeq ya jaddada min ki
kwanta da wuri”. Ta ƙare maganar tana ƴar dariya da kama hannun Maanal ɗin da jikinta yay wani kalar
sanyi ƙalau.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?
id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
3️⃣8️⃣3️⃣8️⃣
______________
_________
........A haɗaɗɗen bayin Oum Maanal tayi wanka. Ita dai sai bin ko'ina take da kallo. Tun can baya tasan su
Oum nada kuɗi, amma komai nasu ya sake canjawa daga sanin datai masan. Ita kanta Oum ɗin ta sake
gogewa ko tsufa batayi. Da waɗan nan tune-tunen ta fito a wankan. Rigar wanka ce dan haka bata ɗan ji
takura ba sosai, koda yake Oum bata cikin mutanen daya kamata acema tana jin kunya, to mi zata ɓoye
mata, matar da tun bata san kanta ba take mata wanka harda goyo. Tasha kwana a gadon Oum daga ita sai
pant. Oum da Bestyn ta ne suka fara sanin jinin haila yazo mata. Kalmar (Besty) ta sake maimaita kanta a
cikin zuciyarta, sai kawai taji zuciyar tata ta mata nauyi. Ture tunanin tayi da ƙarfi ta maida hankalinta ga
bin ɗakin da kallo. Oum ta fita, sai kaya da aka ajiye a saman gado. Kayan ta matsa ta ɗaga. Wando da riga
ne na barci, sunada yalwar da bazasu matseta ba ko kaɗan. Bata wani ɓata lokaci ba ta sanya, tana gama
sanyawa Oum ta shigo ɗakin hannunta ɗauke da wani ɗan basket mai ƙyau golden. A gefen Maanal ta
ajiye, Maanal ta kalleta tana mata sannu sannan ta kalla kayan. Mayukane da zasuyi dai-dai da fatarta, ba
daidai da fatarta kawai ba ta jima da saninsu, dan dasu take amfani ada, bayan ita kuma mutum ɗaya tasan
yana amfani da su a gidan....
Kamar Oum tasan mi take tunanin ta katseta da faɗin, “Nasan nawa bazasu ma skin ɗinki ba. Shiyyasa
na kira Auta ya kawo miki nasa dan nasan fatanku yana ɗaukar mai iri ɗaya ne, sai kuma akai sa'a irin
wanda ma kike amfani da su ne. Maza ki shafa kada jikinki ya bushe bara nima nai wankan”. Daga haka
Oum ɗin ta miƙe batare da ta jira cewarta ba. Maanal ta jima bata motsa ba idanunta akan kayan shafar,
wani abu ne mai nauyi ke tsikarar mata zuciya. Yayinda tunaninta ke kai kawo da tambayar kanta miyyasa
ya cigaba da amfani da irin manta? Miyyasa wasu abubuwa nashi har yanzu suna a yanda ta sansu,
waɗansu kuma a baya suke yawan faɗa akan tana so yayi su yaƙi yi. Amma a yanzu duk sai taga yana yin
su.....
Knocking ƙofar da akayi ya sata ture tunaninta gefe ta kalla ƙofar, jin an ƙara na biyu yasa ta miƙewa ta
ɗan gyarama su Barrah bargo sannan ta nufi ƙofar, duk zatonta cikin masu aikin Oum ne. Sai dai tana
buɗewa taci karo da abinda bashi tai zato ba. Muƙut ta maida abinda tai niyyar faɗa ta haɗiye abinta tare
da janye idanunta daga kansa taja jikinta baya ta koma tai zamanta a inda ta taso. Sai lokacin ya ƙarasa
shigowa ɗakin hannayensa duka biyu zube cikin farin wandon kayan barcin sa. Tafiya yake cike da ƙasaita,
ga mayataccen ƙamshinsa duk ya rikita ɗakin. Baiko kalleta ba ya wuce closet ɗin Oum kansa tsaye kuma
hankalinsa kwance. Ƙasa-ƙasa Maanal ta bisa da kallo, tana mamakin mi kuma ya kawo shi yanzu. Bata da
mai bata amsa, sai ma kira daya shigo wayarta a dai-dai lokacin. Wayar dake acan saman mirror ta ɗan
zubama ido, sai ta tsinta kanta da jin nauyin jiki har kiran ya tsinke. Wani kiran ne ya sake shigowa, sai
hakan yay dai-dai kuma da fitowar AA hannunsa ɗauke da wata bag ƙarama. Har ya wuce batare daya
kalleta ba itama ta miƙe da nufin ɗaukar wayar sai ta hangesa agaban mirror ɗin kamar mai neman wani
abu. Komawa tai ta zauna, sai kawai jin ƙarar wayarta tai a ƙasa. Da sauri ta ɗago, wayar tata ce kuwa,
yayinda shi kuma yake duƙe yana duba abu a drawer ɗin jikin mirror ɗin tamkar ma baiga abinda ya faru
ba. Oum dake fitowa ta ce, “Subahannahi kako yaddoma Auta waya Auta”.
Tsabar rainin hankali irin na AA sai ya juyo irin as bai lura ɗin nan ba ya ɗauki wayar yana jujjuyawa,
ƙarasowa itama Oum ɗin tai inda yake ta amshi wayar ta duba. Gaba ɗaya tayi tatsa-tatsa. Screen ɗin yay
wani irin zuuuuu alamar ya tashi aiki shima. Babbar waya ce, dan SS ce babba Daddy ya saya mata ita gift
ɗin kammala karatun ta.
“Auta kayi ɓarna”.
Oum ta faɗa tana sake jujjuya wayar. Fuskarsa dake a tsuke ya yamutsa babu alamar damuwa a tattare da
shi ya ce, “Oum ban lura bane. Kawo zanba Ahmad da safe ya gyaro”. Yay maganar yana miƙama Oum
hannu. Kanta kawai ta girgiza da ɗora masa wayar a hannunsa. Shi kuma batare daya ce komai ba ya ɗauka
bag ɗinsa ya fice. Ajiyar zuciya Oum ta sauke tare da juyawa ta dubi Maanal. “Karki damu kinji Auta, nasan
in sha ALLAHU zai bada a gyara kafin wucewar mu goben”.
Murmushin yaƙe kawai Maanal taima Oum. “Babu komai Oum”. Itama Oum ɗin sai tai murmushi tana
jinjina mata kanta. Haka sukai shirin barci suka kwanta. Dan har Oum ɗin kwanciyarta tai a gadon tana
faɗin, “ALLAH ya yarda yau zan sake kwanciya gado ɗaya da Babyna”.
Siririyar dariya Maanal ta saki, yayinda Oum ke tayata itama zuciyarta cike da nishaɗin yanayin.....
__________★
Washe gari da safe bayan sunyi wanka suna dining da shirin karyawa harda Ya Fawzan AA ya shigo. Da
mamaki Oum daya fara gaidawa take kallonsa. Dan a shirye yake tsaf cikin baƙaƙen suit da suka sake fiddo
ainahin cikar haibarsa da madarar ƙyau.
“Yau ba Saturday ba na ganka da shirin office?”. Oum ta faɗa cikin kasa haƙuri. Hannu ya miƙama Yaya
Fawzan yana bata amsa da, “Oum project ɗin nan da nake gaya miki yau zamu fara aikinsa da Engineers
ɗinmu”.
“Okay aina ma shafa'a, ALLAH yasa ayi cikin nasara ya kuma ɗaga darajarsa. Maza to zauna ka karya dan
bazaka fita da yunwa ba”.
Agogon hannunsa mai matuƙar nauyin kuɗi da zama designer daba ako ina zakaje ka samesa ba sai
ga wanda ya isa ya kalla. Cikin ɗan ɓata fuska ya ce, “Oum Please zansha coffee a office”.
“Ban yarda ba kuwa. Zauna in ba hakaba nasa Fawzan ya riƙe min kai na maka ɗura”.
Dariya sosai Fawzan yake yi, ya ce, “Tsaf kuwa zan danne miki shi Oum dan wannan girman jikin nasa da
ƙarfuna suka bubbuɗe ba tsoro zai bani ba.”
Harararsa AA yayi, dan dole yakai hannu yaja kofin gaban Maanal da tunda ya shigo tai masa kallo ɗaya
ta maida kanta bata sake ba, daga tsayen da yake ya kai shayin bakinsa, dai-dai Maanal ɗin tana ɗagowa ta
kallesa da mamaki, hakama Fawzan da Oum duk kallonsa sukayi. Amma ya wani basar kamar bai gani ba.
Sai Oum ce tai masa nuni da kujera. “Maza zauna tunda kadai san babu ƙyau shan abu daga tsaye”.
Baice komai ba ya zauna ɗin, sai faman kallon agogonsa yake yi alamar dai a ƙagare yake. Barrah da
Haneeff ne suka fito daga kitchen tare da mai aiki. Dan sunce su noodles zasu ci shine taje dafa musu suka
bita. Ganin AA ya sasu nufosa, cikin haɗa baki da ɗokin ganinsa sukace, “Uncle good morning”.
A mamakin kowa sai ya saki murmushin nan nasa na rowa tare da shafa kawunansu ya na amsawa.
“Good morning Handsome & Oum na. Fatan kun tashi lafiya?”.
“Uncle Alhamdullah”.
Suka faɗa cikin haɗa baki. Murmushi ya sake sakar musu da cewa, “Masha ALLAH”. Daga haka ya miƙe
yana ajiye kofin da sauran shayi a inda ya ɗauka. Sai Maanal ta samu kanta da tsurama kofin ido kawai har
yay sallama dasu Oum ya fita kafin ta farga. Yaya Fawzan ne ya katseta. Kayan shayin ya tura gabanta yana
faɗin, “Haɗa wani shayin tunda ya shanye miki kinji Lilly”.
Ɗan murmushin yaƙe Maanal tayi, cikin muryar nan tata mai sanyi ta ce, “Yaya akwai a ciki ya isheni”.
“Kin tabbatar?”.
Kanta ta jinjina masa. Oum dai Murmushin ta take irin na manya batace komai ba. Sun kammala
breakfast ɗin babu jimawa sai ga RK. Da gudu su Haneeff suka maƙalƙalesa suna murna. Hakan yasa Oum
sake fahimtar akwai shaƙuwa sosai tsakaninsa da yaran. Fawzan ma har yanzu yana a sashen Oum ɗin suna
hira, sai kawai RK ɗin ya baje aka dora da shi bayan mai aiki ta haɗo masa breakfast dan yace bai karya ba.
Anan falon ya karya suna hirar, idonsa akan Maanal dake kwance kanta a cinyar Oum tana karatun novel
ɗin nata na fama. Sai ƙara jinjina shaƙuwar Oum ɗin yake da Maanal ɗin, dan kuwa yanda Maanal ɗin ta
saki jiki ya ishesa shaida. Musamman idan yay dubi da miskilancin tsiya irin na Maanal ɗin....
____________
Da mamaki Shahidah ke sauraren Linda dake mata bayanin fitar Huznah tun 8. Ranta ne ya fara ɓaci da
iskancin Huznah ɗin. Yaya tana a gidanta amma bata da mutuncin da zata dinga gaya mata zata fita. Kai ko
gaisuwa tunda Huznah tazo gidan nan bata jin ta mata. Shi kansa Abbansu Barrah duk kawaicinsa yau da
safe sai da yay magana. Shine ma dalilin da yasa yanzu da zasuyi zaman breakfast taima Linda magana
akan ta tado Huznah ɗin su karya. Amma sai take sanar mata wai ta fita tun 8. Da alama kuma anguwa ta
tafi dan taci gayu.
Komai batace da Linda ɗin ba ta juya tabar dining ɗin. Bedroom ɗin ta ta shiga ta ɗau waya tayi kiran
Ammie. A lokacin Ammie na tare da Daddy dan yau itace da shi. Bata ɗaga kiran ba har ya tsinke. Cikin
hikima tacema Daddy tana zuwa dan wayar tata dama a silent take. Sashenta ta koma sannan tai kiran
Shahidah ɗin. Bayan ta amsa gaisuwar da Shahidahn ke mata ta ce, “Mike faruwa da safen nan kira
Shahidah?”.
Cikin matuƙar ɗacin murya Shahidah ta ce, “Ammie akan yarinyar nan ne Huznah. Nifa gaskiya ina jin
tsoro. Tunda tazo fa ba zama take ba, da mun fita aiki take shiryawa itama ta fice gidan nan wani lokacin
ma sai mu rigata dawowa. Yau kuma da take weekend ma kinji tun 8 tabar gidan nan. Ammie ina jin tsoron
kar wani abu ya faru ace a zamanta nan ne ban saka ido a kanta ba fa”.
Numfashi mai nauyi Ammie ta sauke. Cike da nazarin maganganun Shahidah ɗin ta ce, “Kenan akwai
dai abinda tazo yi Abujan, saboda uban ya barta suka jinginata da zuwa gidanki ta zauna. Ki kwantar da
hankalinki in sha ALLAHU babu abinda zai faru. Zuwa anjima zan kira Yazeed nai masa bayani ya sanya ido
a kanta tunda yana Abujar.”
Ajiyar zuciya Shahidah ta sauke cike da gamsuwa tace, “Yauwa Ammie hakan dai yafi kam gaskiya. Dan
shi kaɗai ne maganinta nikam bajin maganata zatai ba tana ganin shekarunmu ɗaya. Yasu Hameed da
Aunty Sakina”.
“Lafiyarsu ƙalau gaba ɗaya. Ya batun dubiyar da su Auta sukaje jiyan?”.
Gaban Shahidah ne ya faɗi, amma sai cikin wayancewa ta ce, “Lafiya lau Ammie babu wata damuwa.
Dan yanzu haka ma barci takeyi”.
“To Alhamdullah, dan inata tunanin kar taje gidan mutane ta nuna bata son yaronsu. Ni kuma harga
ALLAH yaron ya shiga raina saboda nutsuwarsa da sanin darajar mutane. Tunda al'amarin Yazeed ya koma
wani iri gara ta haƙura da Rafeeq ɗin ayi a wuce wajen zaman nan nata damuna yake yi”.
“Ammie adai cigaba da addu'a, in sha ALLAHU komai zai dai-daita, nawa ma Maanal ɗin take, rigimarta
ce ta sata gama karatu da da wuri amma da yanzu ne fa ma ya kamata ta shiga jami'a. Rafeeq kam baida
matsala mutumin kirki ne. Ya cancanta ai masa komai, kuma sun dace da Maanal ɗin. Sai dai nasan akwai
rikici Ammie.....”
“Rikicin mi kuma? Wani abu ya faru ne?”.
“A'a babu abinda ya faru Ammie. Kawai nasan janyewar Yazeed akan Maanal bazai kasance mai sauƙi ba.
Dan yana matuƙar sonta, auren nan dan baida yanda zai yi ne kawai uwarsa tafi ƙarfinsa ne. Yanzu haka
kullum cikin roƙon Maanal yake akan ta bari a haɗa bikin ayi gaba ɗaya zaifi samun kwanciyar hankali. Ni
wlhy duk sai ma tausayinsa ya fara damuna”.
“Nima ina jin tausayin nasa Shahidah. Sai dai su haƙura da junan sai yafi alkairi fiye da yin, dan nasan
wacece Hajiya Sadiyya. Komai zata iya yi kamar yanda ta faɗa. ALLAH dai ya kawo mafita cikin sauƙi. Bari
anjima mayi wayar na bar babanku shi kaɗai ina wajensa kika kira”.
“To Ammie ba damuwa sai anjima”...........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
3️⃣9️⃣3️⃣9️⃣
______________
.........A ɓangaren Huznah tana can gidan Yaseerah. Dan dama sunyi da ita yau da wuri zataje gidan
kasancewar tunda tazo sai dai tayi zuwan fisha. Ta samu ko barci basu tashi ba. Saboda weekend ne mijinta
na gida. Sai kawai ta shige ɗayan bedroom ɗin Yaseerah ta kwanta itama ta ɗora barcin da bata samu yi ba
a daren jiya isashe.
Sai wajen sha ɗaya Yaseerah da mijinta suka fito. Suna a d/table zasu fara breakfast mai aikinta ke sanar
mata zuwan Huznah ɗin. Mijin nata ta kalla tana ɗan murmushi. “Baby Uncle ɗinka fa ya rikita min ƙawata.
Munata binsa kuma yaƙi bamu muhimmanci. Yakamata ka shiga lamarin nan haka nan”.
Murmushi yay shima dakai kofin tea bakinsa. “Ai dama na faɗa mata tun farko, shi bana wasan yara
bane. Dama Uncle Fawzan ne da sauƙi, amma Uncle AA tab ɗin, ina tausaya mata ALLAH. Da zata ji
shawarata da ta jima da manta ta taɓama saninsa kawai.”
“Bazan iya haka ba Abdul-hakeem. Dan a yanzu bani da wani burin daya wuce mallakar Uncle ɗinka.”
Muryar Huznah da basu san da zuwanta wajen ba ta ratsa kunnunwansu. Gaba ɗayansu juyawa sukai
suna kallonta, ganin yanda hawaye ke sauka mata da gudu a saman ƙyaƙyƙyawar fuskar ta ya sasu miƙewa.
Hannunta Yaseerah ta kamo ta zaunar a kujerar kusa da ita, itama takai zaune tana riƙe hannunta alamar
lallashi. Shima zama yay mijin Yaseerah ɗin, wani irin tausayin Huznah na ratsa shi. Tabbas yasan ta
ɗaukarma kanta abinda yafi ƙarfinta, amma ko ya cigaba da gaya mata gaskiya yasan ba lallai ta fahimcesa
ba. Gyaran murya yay a hankali, hakan ya sasu ɗagowa su duka suka kallesa..
“In sha ALLAHU zan taimakeki. Sai dai ki sani wlhy Uncle AA nada wahalar sha'ani. Amma akwai mafita
ɗaya da nake miki hasashen idan kin gwada maybe ki dace....”
Jikin Huznah har rawa yake ta ce, “Wace irin mafita ce. Komai wahalarta ALLAH zan gwada, komai
ƙalubalenta kuma zan jure”.
Kansa ya jinjina mata, sai kuma ya sauke numfashi. “Batun yanzu ba nasan Grandma suna fama da Uncle
AA yay aure. Kuma a yanzu haka ma suna gab da masa auren ne amma bani da tabbacin sun sama masa
matar ko basu sama masa ba, duk da dai akwai wata sister ɗin mu dake sonsa matuƙa kuma naga duk
dangi nason a gaɗasu aure, shine dai bai maida hankali ba. To ina ganin mafita ɗaya ce na baki number ɗin
grandma, ko kuma ki shirya na kaiku ke da Yaseerah kamar zaku gaisheta sai muce ai ke budurwar Uncle
AA ɗin ce. Idan ALLAH ya taimaka aka dace sai kiga ya amsheki dole bisa umarninsu. Hakan yayi miki?”.
Cike da zumuɗi ta amsa masa, tana share hawayenta ga dariya. Shima murmushi yayi hakama
Yaseerah. Ya ce, “Sai ki zama cikin shiri dan sai nan da kwana uku”.
“Miyasa ba yau ba?”.
Ta faɗa cikin damuwa.
“Bata nan ne shiyyasa, amma ina saran dawowarta gobe ko jibi in sha ALLAHU”.
Ajiyar zuciya Huznah ta sauke. Badan taso hakan ba tace ALLAH ya kaimu. Dai-dai nan kira ya shigo
wayarta. Koda ta duba sai taci karo da Yaya Yazeed. Mamaki ta kamata, dan hakan kan jima bai faru ba
ganin kiran yayan nasu. Haka dai ta daure ta ɗaga dan tasan in har wayar ta tsinke bata ɗaya ba sai taci
ubanta a hannunsa. Ko amsa sallamarta baiyi ba cikin kaushin murya ya ce, “Kina ina nazo gidan Shahidah
baƙya nan?”.
Rawa jikinta ya fara, cikin karkarwar harshe tace, “Yaya wlhy bawani wajefa naje ba ina gidan Yaseerah
ne nazo gaisheta”.
“Na baki mintuna ashirin kawai ki dawo gida. Idan ba haka ba hummmm!”. Ya yanke kiran. Kanta tai
wani irin dafewa dan takaici, batama san ta fara antayama Yazeed ɗin zagi ba Yaseerah na tayata. Babu dai
yanda zatai dole ta kimtsa mijin Yaseerah ɗin ya ɗauketa domin maidata da kansa. Dan hakan kawai zatai
ta kuɓuta daga bala'in Yaya Yazeed. Dabarar tata kuwa ta taimaketa, dan ganin Abdul-hakeem ɗin ya
sassauta tanadin da Yazeed ɗin yay mata. Sai dai duk da haka taci zagi da faɗa akan fitar sassafe babu
kuma sanarwa. Ya kuma ja mata dogon gargaɗi akan in har ta kara fita a gidan wlhy sai ya mata dukan
mutuwa.
Yana tafiya ta koma ɗaki tai kiran uwarta ta gaya mata tana kuka. Zage-zage itama Hajiya Basariyyar ta
dinga yi da tsinar Yazeed ɗin. Sai da sukai san ransu ta koma lallashin Huznah da kwantar mata da hankali
akan zatama Yazeed ɗin magana da kanta. Daga haka sukai sallama. Bata ko ƙara fita a ɗakin ba duk
ɓuruntun da su Shahidahn keyi akan shirin tarbar baƙi su Oum. Sai ma nacin son samun AA take a waya
amma hakan ya gagara. Da alama ma yayi blocking ɗin ta ne ita bata gane ba. Ai ko saita zauna tanata
kuka. Sai da tayi mai isarta barci yay awon gaba da ita.....
___________★
Ƙarfe huɗu da kusan rabi danƙareriyar motar Fawzan ta iso gidan. Yana gama parking Barrah da
Haneeff suka fice zuwa cikin gida aguje suna ƙwala kiran mamansu. Dariya Fawzan ya dingayi, dan shi
ALLAH ya ɗaura masa son yara matuƙa. Kodan har yanzu ALLAH bai bashi bane. Dan matarsa bata taɓa ko
ɓatan wata ba shekara shida kenan. Oum ma dariya take ma yaran. Maanal dai komai batace ba, sai ma
jagorantar su Oum tayi zuwa cikin gidan. Sun sami Shahidah na ƙoƙarin fitowa tarbar su Oum, dan haka
sukaci karo a ƙofa. Cike da wani irin farin ciki Shahidah da Oum suka rungume juna. Sai kawai Shahidahn ta
saki kuka. Harga ALLAH tana matuƙar son Oum, dan mace ce ƴar halak da bazasu taɓa mantawaba a
tarihinsu. Ta matuƙar taka rawar gani a garesu da Ammien su ta yanda baki yayi kaɗan ya bada labari.
Itama Oum ɗin hawaye take da murmushi duk a lokaci ɗaya, ta ɗago Shahidah tana mai share mata
hawaye. “Uhm-uhm kefa yanzu kin girma Sheedan Oum, ke uwa ce babbar yaya kuma”.
Dariya Shahidah ta shigayi, hakama Fawzan dan tuno wani abu daya shuɗe. Maanal ma dai murmushi ne
mai faɗi akan fuskarta. Abinda a yanzu yake da matuƙar tsada da wahala a gareta. Sai da Shahidah ta saki
Oum sannan ta lura da Fawzan, cike da mamaki ta riƙe haɓa da faɗin, “Oh ni ALLAH wanake gani haka ya
zama dattijo?”.
“A'a tsoho na zama ba dattijo ba”. Fawzan ya bata amsa yana hararta. Dariya duk suka sanya masa.
Shahidah ta ce, “ALLAH kuwa ka yarda ka zama dattijo yanzu Yaya Fawzan”.
“Kema kin zama dattijuwar ai”.
Ya faɗa dai-dai suna kaiwa zaune a ƙayataccen falon nata. Dai-dai nan mijinta ya fito. Cike da mamaki
idonsa akan Fawzan ya ce, “Kai kai wanake gani haka kamar Darma a gidana”.
“Ya arrahaman Busam!”.
Shima Fawzan ya ambaci sunansa yana miƙewa. A tare suka cafke alamar lallai sun san junan kuwa sani
bana wasaba. Ai sai su Oum suka koma ƴan kallo. Sai da ƙyar Shahidah ta iya faɗin, “Nifa ban gane ba, wai
dama kun san juna ne?”.
“Farin sani ma kuwa. Darma tare mukai degree master namu ai a Germany, sannan a yanzu haka akwai
alaƙar aiki a tskaninmu. Kawai dai baya son zumuncine shiyyasa baki taɓa ganinsa a gidan nan ba.....”
“Wulaƙanci ai kai zumuncin kake so?”.
“Nadai fika tunda ni naje gidanka har sau biyu”. Cewar Abban su Barrah. Dariya Fawzan yay da faɗin,
“Gori kenan. To yanzu ai gashi ALLAH ya kawoni, ashema ni ƙanwata kake aure kai wannan abin kunya da
yawa yake”.
“Ato kaima dai ka faɗa”.
Cike da girmamawa Abban Barrah ya gaida Oum. Itama ta amsa masa da kulawa cike da farin ciki. Nan fa
aka ɓalle taɗi tsakanin Oum da Shahidah, Fawzan da Abban Barrah. Yayinda Linda tuni ta cika musu
gabansu da kayan ciye-ciye Maanal na tayata. Duk wannan bidiri da ake Huznah na ɗaki tana shaƙar barci
abinta. Sai da Maanal ta taje ɗakin ajiye kaya ta ganta baje a gado. Komai bataceba ta ajiye ta dawo wajen
su Oum. Sai ga RK da dama yay musu alkawarin samunsu a gidan. Nan fa hirar ta ƙara armashi dan tuni
Abban Barrah ya janyesu sun koma falon baƙi dan Oum ta sake itama suyi tasu hirar. Hakan yama Oum ɗin
daɗi sosai, dan ta samu tattauna abubuwa da yawa da Shahidah wanda Maanal ta kasa sanar mata komai
saboda zurfin ciki da miskilanci. Sai da akai magriba sun dawo Huznah ta fito. A ɗan yatsine ta gaishe su,
sai dai saukar idanunta akan Fawzan yaso birkita mata lissafi. Sai da ta nutsu ta fahimci ashe ba AA ɗinta
bane kammanni ne kawai. Dan suna kama sosai da AA ɗin, sai dai wasu abubuwa da suka ɗan babbanta
su. Hakama kuma suna kamanni da Oum matuƙa. Hankalin Huznah ne ya tashi, dan haka kawai take ji a
ranta wannan mutumin na kama da AA ɗin ta hakama matar, sai dai yanda ta gaishesu yasa daga amsa
gaisuwar kowa ya watsar da ita musamman RK da kamar basu ƙaunar juna ita da shi.
Su Oum na gidan nan har tara, dan har sai da Autan ta ya kirata yana damunta shi dai ta dawo ya koma
gida tun ɗazun duk basa nan gida babu daɗi kuma yana jin yunwa. Dariya Oum take masa da tsokanarsa
akan wannan hali nasa na ɗafa, ya girma amma bai san ya girma ba koda yaushe yana laƙafe da ita. Idan tai
masa aure yaya kenan. Shi dai roƙonta ya cigaba da yi akan su taho kawai. Tace shi bazai zo ya samesu
anan ba yace ya gaji. Ƙyalesa tai tace gasu nan tahowa. Amma wayar Maanal fa ba'a gyara bane?. Sai
cemata yay eh wai mai gyaran yace sai Monday ma.
“ALLAH ya kaimu” ta bashi amsa tare da sanar masa gasu nan dawowa. Sosai Shahidah ta haɗama
Oum shata ta arziƙi, duk da tasan tafi ƙarfin duk abinda ta batan. Saboda suma su Maanal haka Oum ɗin ta
haɗo musu abubuwa iri-iri na tsaraba. Da suka fito kuma sai da suka shiga super market ma aka ƙara wasu
sayayyar. Huznah dai duk jikinta yayi sanyi da ganin waɗan nan ƴan gayun mutane gogaggu wayyayun ƴan
boko da hutu da jin dadi ya gama ratsawa. Sai kuma gefe ɗaya na zuciyarta ya kasa samun nitsuwa akan
kamannin Fawzan da AA ɗinta da kuma Oum. Jiki a sanyaye ta biyo su Maanal rakkiyar su Oum har mota.
Maanal na manne da Oum ɗin sai shagwaɓa take mata cikin maganar nan tata ƙasa-ƙasa dake sake narkar
da RK tana baƙanta ran Huznah da ganin tsantsar iskanci ne kawai da bariki kesa Maanal ɗin maida
muryarta haka. Gefe kuma Fwazan na tsokanarta wai sun saka musu Oum ɗin su tsakkiya da shagwaɓar
tsiya, ita tayi Auta yayi.
Dariya kawai Oum tayi da faɗin, “Babu ruwanka barni da kayana, suyi abinsu san ransu ko Auta?”.
Cike da jin kunaya Maanal ta ɓoye fuskarta a jikin Shahidah. Dariya suka sanya mata. Daga haka sukai
sallama Oum na sanar mata wayarta zata taso mata ƙeyar AA ya kawo mata idan an gyara. Kai kawai ta iya
ɗagama Oum tana ɗan murmushi, amma a ranta tasan bamai yiwuwa bane ya kawo da kansan. Shima
kansa Fawzan murmushi yayi yaja mota suka fice. Sai RK dake tsaye jikin tasa. Ciki su Shahidah suka koma
da yaran aka bar Maanal a wajensa zasuyi sallama, kamar zata sharesa. Sai dai ganin yanda Huznah ke
wani binsu da kallon ƙwaf ya sata nufarsa....
“Humm dama haka kika iya shagwaɓa my queen?”.
RK ya faɗa yana binta da kallo ƙasa-ƙasa. Murmushi kawai tai masa mai sanyi kanta a ƙasa. Batare da tace
komai ba. Shima sai ya saki murmushin da sake maida hannunsa ya harɗe a ƙirjinsa. “Koda yake ma ni
fushi fa nake dake”.
Ɗan ɗagowa tai ta kallesa da faɗin, “Akan mi?”.
“Humm akan komai ma. Yanzu ace akwai alaƙa mai ƙarfi irin haka a tsakaninki da AA amma ban taɓa sani
ba Maanal, ko'a fuska baki nuna min ba shima haka kuka wani rufeni a duhu. Zaman amana kenan?”.
Sosai gaban Maanal ya faɗi, ta zuba masa ido, ganin shima ya zuba mata nasa idanun tai saurin janye
natan zuciyarta na duka. A ranta kuwa tunani take wace alaƙar a ciki yake magana kenan? Badai yaji komai
ba? Badai yasan komai ba? Shi AA ɗin ne ya sanar masa kenan kamar yanda yace zai yi ko kuwa? Dan
tanada yaƙinin Oum bazata faɗa masa ba duk da kasancewarsa jininta ƙani uwa ɗaya uba ɗaya.
Cikin wani irin sanyi ta ce, “Mi kaji a kaina?”..........✍️
😨😨😨😨😨0
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
4️⃣0️⃣4️⃣0️⃣
______________
___________★
Washe gari lahadi Maanal ta tashi da burin fita gyaran jiki. Sai ga Yazeed yazo gidan. Jin inda take shirin
zuwa yace tazo ya sauketa kawai. Haka badan taso ba suka wuce ita da Barrah da Huznah data maƙale
akan zataje. Kasancewar Huznah a motar yasa Yazeed kama kansa. Dan shi fa agaban Maanal ne kawai
dama zakaji muryarsa ko sauƙin kansa. Amma ƙannesa da sauran mutane shi mai matuƙar kamun kai ne da
tsare gida. Ya dai tambayeta wayarta da yake kira baya samu ta sanar masa accident ɗin data samu, yayi
addu'ar ALLAH ya kiyaye gaba daga haka ya kaisu wajen gyaran jikin. Yau ma kamar waccan ranar atm
ɗinsa ya bata, ya kuma ce idan sun kammala ta kiranshi. Bataƙi amsa ba tai godiya kawai kodan idon
Huznah ƴar saka ido.
Haka suka shiga wajen gyaran jikin. Sun sami mutane ba masu yawa ba, kasancewar sun fito da wuri
sannan mai wajen ƙawar Shahidah ce. Ana tsaka da musu gyaran ita Maanal ana wanke mata kai, Huznah
kuma wankin ƙafa da gyaran farce wata ƙyaƙyƙyawar mata ko budurwa za'a kirata ko bazawra ne ma oho
ta shigo wajen ita da ƙawarta. A fuska dai kam akwai ruwan ƙyau, sai dai a jiki haka take slim babu gaba
babu baya. Duk rashin jiki irin na Maanal sai ta ganta da ƙyan fasali akan matar. Dan Maanal rashin jikin ne
dai kawai bata da, amma tanada cikar halittar jiki gwargwado duk da suma bawani na manyan mataba can.
Amma dai duk inda mace zata kira kanta mace kam itama zata buɗe baki.
Yanda yarinyar ke yamutse-yamuste da shan ƙamshi ne yaja hankalin mafi yawan mutanen dake a
wajen kanta. Tuni wasu suka ɗan fara mata magana tana amsawa da gyar, banda Maanal da ko kallon inda
take batai ba. Ana gama ma wanke mata kai ta ɗauka novel ɗinta ta cigaba da karatu, yayinda Barrah da
akema kitso ke gefenta tana game da wayar wajen RK. Ashe yarinyar nan hankalinta nakan Maanal data
watsar da ƙurarsu. Sai hakan yay mata zafi ta shiga habaici da yaɓa magana ƙawarta na tayata da mata
kirari da dariyar iskanci. A hakan ma Maanal bata ma nuna tasan bayan ita da wasu ma a shagon ba.
Cikin masu aikin wajen ce ta ce, “Oh ni, yau dai da alama da fitina kika fito gida Nurry, irin wannan
takale-takale shin na miye? Dawa kike anan?”.
Sai da ta watsawa mai aikin harara sannan ta tauna chewing gum ɗin bakinta ya bada wani ƙas-ƙas ta
ce, “Da ƙananun karuwan Abuja mana. Masu baro gidan ubale suzo nan su kama hotel suna girman kai da
ɗaukar kansu wata tsiya. Ƴan iska ɗaya bayan ɗaya sai mun saitasu gidan iyayensu da ake cin masara sun
bar mana garin mu shegu ƴaƴan talakawa”.
Dariya ƙawarta ta ƙyal-ƙyale da shi tana zuba mata wani kirari. “Sai dake tawajena, sa gabanki inda kike
so. Kuɗi ya haifeki, cikinsu kika girma gidan su zaki zama matar aure. Kaga amarya a gidan tauraron
matasan ƙasar nan kaf mai kiran kuɗi koda kwance suzo su masa bargo a gado. Yi yanda kike so kune Abuja
dama ƙasar gaba ɗaya ai ko anƙi ko an so dai da ku”.
Wani yyyuuuuu Nurry ɗin tai da idanunta manya dake a juye kamar ƴar shaye-shaye. Cike da jin
alfaharin Kirarin ƙawar tata ta wani watsama Maanal kallon banza. Hakan datai ya saka kowa fahimtar da
Maanal ɗin take. Wani shegen murmushi Huznah ta saki na jin daɗi, sai kawai ta dubi Nurry ɗin fuska da
murmushi ta ce, “Hy Mss”.
Da farko Nurry kallonta tai zata watsar, sai kuma dai taga itama Huznah ɗin ba daga baya ba. Jiki da
suttura duk sun nuna ƴar wani ce. A ɗan yangance ta amsa da “Hy” itama tana watsama Huznah yatsu
biyu. Tsam Huznah ta miƙe kasancewar an gama mata ta koma kusa da Nurry ɗin. Sai lokacin Maanal ta
ɗan kallesu, kanta ta ɗan girgiza kawai ta miƙe tabar musu wajen ma gaba ɗaya ta koma sashen ƙunshi dan
tana son a mata ɗan jan lalli a yatsunta da ɗan baƙi kaɗan a hannun kawai.
Ai hakan kamar yama Huznah daɗi ne. Tuni ta baje a tsakkiyar su Nurry aka ɗora hira harda musayar
numbers. Haka dai akai musu gyaran jikin nan har bayan la'asar sannan suka fito domin komawa gida.
Kasancewar Maanal bata kira Yazeed ba duk da yace ta kirashin sai ta tare taxi dan su tafi, sai kawai
Huznah catai suje ita su Nurry zasu sauketa. Dan kusan tare suka fito da su Maanal ɗin suma. Ko ci kanki
Maanal batace mata ba suka shige taxi ita da Barrah suka wuce abinsu. Ita kuma ta shiga jibgegiyar motar
Nurry da take driving da kanta suka tafi.....
_________★
Safiyar litinin safiya ce da duk wani ma'aikaci jininsa ke akan farcensa. Kamar dai anan gidan su
Shahidah. Ita da yara da mijinta da Maanal duk sunyi shirin tafiya aiki. Kamar yanda suka saba tsaf dasu
cikin kwalliya ta birgewa da tsarin addini. Huznah nacan ana shan barci dan jiya bata dawo gidan ba daga
bin su Nurry sai bayan isha'i, haka kuma ta kusa raba dare tana charting dan groups su Nurryn suka sakata
na WhatsApp kala-kala. Tana yi tana neman mutumin nata sai dai har yanzu bai cireta a black list ɗin daya
Saka ta ba da alama. Haka ta haƙura tunda ta ɗau ɗamarar komawa office ɗinsa a yau litinin kawai.
Mai kai yara makaranta ya kwashesu Barrah. Abbansu ya wuce. Itama sai suka tafi da Shahidah. Har
ƙofar gate ɗinsu ta kaita. Ta fito tana murmushi saboda maganar da Shahidahn tai mata dai-dai da isowar
motar AA. Kamar ance ta kalla wajen sai ko idanunta a kansa. Yana zaune a bayan motar cikin ƙasaita da
cikar kamala, kayansa dai na kullum ne suit a fagen aiki, sai dai na yau milk color ne, idan ka cire long
sleeve shirt ɗin ciki data kasance coffee. Gajiyayyun idanunsa na cikin fari tas ɗin gilashinsa na ko yaushe
dake ƙara cikar kamala da ƙyawun da ALLAH yay masa mai sanyi. Sumar nan da sajensa sun sha gyara luf-
luf da su. A zahiri idanunsa a rissine yake da alama akwai abinda yake dubawa, sai dai kuma a kaikaice
idanunsa akan Maanal suke. Amma bazaka taɓa fahimtar hakan ba akai mai kallonsa daga nesa ko kusa.
Dan kallone irin na basarwa da iya taku. Kasancewar an sauke gilashin kaɗan tuni ƙamshin turarensa ya iso
har inda su Maanal suke. Sai dai itama fa daga kallo ɗayan datai masa ta janye idanunta bata sake gigin
kallon koda sashen da motar take ba. Sallama sukai da Shahidah da sam hankalinta bai kai ga AA ɗin ba ita.
Ita kuma ta fara takawa a hankali cikin takunta na nutsuwa zuwa cikin Companyn........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
4️⃣1️⃣4️⃣1️⃣
______________
Amma bari in kira Besty nah Huriyyah nasan zata samu maganin wannan damuwar tawa.
Tunda na kira Huriyya na faɗa mata abunda ke hanani Bacci ta faɗa mun wani sirri da ya girgizani.
Wato ashe itama da ta fara business online kuma bata ciniki amms tunda aka bata number din Coach
Saddiqah komai ya fara tafiya daidai a kasuwancin ta ( Talk with Saddeeqah).
Tunda ta shiga OPERATION CINIKI DOLE ONLINE BOOTHCAMP komai ya warware mata ciniki babu kama
hannun yaro. https://wa.link/8al2f0
Ai ba shiri na nemi Coach Saddiqatu nima domin in shiga tsarinta na Saddeeqah Biz Growth Academy.
Kuma Alhamdullilah ina shiga nafara ganin canji a business dina, har ma sabon online business na buɗe
daga cikin abunda na koya a Operation Ciniki Dole Online Boothcamp.
https://wa.link/8al2f0
Gaskiya wanda ya koya a wurin ƙwararriya ya huta domin ko dubu 100,000 akace in biya in shiga
OPERATION CINIKI DOLE ONLINE zan biya domin amfanin da na samu cikin Boothcamp bazan iya faɗaba,
gashi yanzu na samu na sayi machine din delivery na maida daki guda shago cikin gida na.
Hurayyah ta taimaka da ta haɗa ni da Coach Saddiqah. OPERATION CINIKI DOLE ONLINE ya bani damar yin
ciniki yadda ya kamata ba tare da wana damuwa ba.
Indai kina business ko kina son ki fara Operation Ciniki Dole Online Boothcamp shine ajin farko da Coach
Saddiqah zata rike hannun ki ta nuna miki duk wani sirri da dabaru na kasuwancin online.
Daga rashin ciniki zaki koma sold out domin kuwa zaki dinga yin 6 figures monthly, in kin shiga OPERATION
CINIKI DOLE ONLINE BOOTHCAMP baki ga sauyi mai kyau a business dinki ba za'a maida miki kudinki bayan
90days.
Da Naira Dubu Goma kacal Pre-lunching Price zaki samu damar shiga OCD.( Kina biya zaki fara kwasar ilimi)
Zakuma ki iya jira sai 20th January ki biya Naira Dubu Ashirin.
______________
.......Sanye take da doguwar riga ta atamfa da ɗinkin yay ƙyau sosai, tayi ɗaurin zara Buhari da yay matuƙar
zauna mata kamar ta ɗauka ta ɗora a kanne ba hannu ya naɗa ba. Kasancewar kalar atamfar blue ne da
fari ta ɗaura farin gyale ba wani ƙato ba sosai tun daga saman kanta sai ta baɗesa a kafaɗunta duka amma
ya rufe mata ƙirji duka. Ta baya kuma rigar bata matseta ba shiyyasa sam babu ta inda jikinta ke nuna da
wani zai ce ta fidda tsiraici. Kamar ko yaushe tana maƙale da sirrin farin gilashinta da ke ƙawata fuskarta da
kwarjini na musamman. Yayinda sam fuskar babu alamar wasa da wani zai kawo mata wargi dan tsuke take
tamau, ba wata kwalliya tayi ba a fuskar mai yawa, amma tayi ƙyau sosai. Ƙamshinta mai sanyi da saka
zuciya nutsuwa. Yanda take takunta a nutse sai ka ɗauka yanga ce da tsatsar iyayi. Amma halitartace hakan
sam bata da garaje ko gaggawa. Duk wanda ta haɗu da shi mace ko namiji takan gaisheshi batare da ko
kallonka tayi ba ta wuce abinta. Idan kuma kai ne ka fara ambata sunanta ga ƴan wanda suka santa takan
kallekan ta ɗan ɗaga maka hannu.
Isowarta ga ƙofar shiga dai-dai da tunkarowar AA shima assistant ɗinsa biye da shi da tarkacensa a
hannunsa. Yayinda shi kuma waya manne a kunnensa yana magana cikin nutsuwar nan tasa kamar baya
son magana.. dan ko assistant ɗin nasa bazaice ga abinda yake faɗa ba kai tsaye a wayar. Amma da yake da
aka kira wayar tana a hannunsa shine ya ta miƙa masa yaga ansaka My D, Wato mahaifinsa. Yanda yake
taku dake sake tabbatarwa shi ɗin tsayayyen namiji ne ingarman gaske. Mai lafiya da ji da ƙarfin ƙuruciya
dana motsa jiki ya isa abin kallo ga masu kallon nasa. Balle azo ɓangaren iya ado da tsara shi. AA yasan
sirrin gayu da ƙamshi, dan yana cikin manyan Handsome da duniya bazata taɓa takokin manna hotonsa
ako ina ba ta faɗa da tabbatarwa. Yanda kowanne ma'aikaci sai ya ɗaura I'd card ɗinsa na aiki ƙofa ke bashi
damar shigewa haka shima oga da kansa. Dan haka koda suka iso sai assistant nashi ya ɗora nasa id ɗin shi,
dai-dai da itama Maanal data tsaya ciro nata a bag ɗinta ta ɗaura. Hannunta ɗaya riƙe da lunch box ɗinta,
ɗayan kuma bag ɗin na'a kafaɗarta maƙale, dan mai irin kamar school bag ɗin nan ce amma ta gayu kuma
ƙarama. Ɗan zubama lunch box ɗin idanunsa yayi sai kuma ya janye tare da shigewa yana magana a
hankali da sai da ya ɗan gittata taji muryarsa acan ƙasan maƙoshi yana faɗin, “Yes Aba I hear you”.
Da kallo ta ɗan bisa sai kuma ta taɓe baki kaɗan tana yamutsa fuskar da ƙarasawa reception ta saka
hannu kamar yanda dokar companyn take. Anan ne suka haɗu da Yaqub. Murmushi ya sakar mata da
faɗin, “Good morning sister Maanal”. Kallonsa ta ɗan yi sai itama ta saki masa ɗan murmushi mai tsayawa
iya motsin fuskar nan. Nutsuwar Yaqub ɗin da rashin hayaniya yasa take ganin mutuncinsa. Cikin ƴar
siririyar muryarta ta ce, “Good morning ɗan uwa. Ya weekend?”.
“Alhamdullahi mun shata kam mun more”.
Malalacin Murmushin ta ɗan sake yi kawai. Batare da ta sake cemasa komai ba ta wuce. Binta yay suka
jera. Duk da bawata magana suke ba sai da aka dinga binsu da kallo. Koda suka iso nasu ma office ɗin su
Zaharadeen duk zuba musu ido sukai. Kallo ɗaya tai musu ta kauda kanta da faɗin, “Good morning”. A
jimlace. Wasu sun amsa wasu kuma na binta da kallon dai. Ita kuma ta sake yin kicin-kicin da fuska ta gyara
kujerarta bayan ta kakkaɓe ta zauna. Sai kuma ta warware tissue da ta ajiye a wajen ta fara goge
abubuwanta duk da komai a tsaftace yake ƙal. Amma ita ƙa'idarta ne in har zata fara aiki saita sake goge
komai nata har keyboard kafin ta fara. Batafi zaman mintuna arba'in ba ta samu kira daga office ɗin Design
Director. Miƙewa tai kawai sai wayarta a hannu ta wuce. Su Zaharadeen suka bita da kallo cike da gulma.
Sai dai ita bama tasan sunayi ba.
Cikin girmamawa da mutuntawa ta gaishe da Director Mustapha. Ya amsa mata da kulawa da binta da
wani munafukin kallo. Kujera ya nuna mata alamar ta zauna. Bata musa ba ta zauna ɗin.
“Yauwa Sister Maanal zamuje can Workshop dan kin san aiki yayi nisa. Akwai abinda ake buƙatarki a
wajen domin tattaunawa, tun jiya ma Watchmakers da horologists ɗin sukaso ganin ki sai CEO yace sai
yau”.
Kai kawai Maanal ta jinjina masa a girmamame. Shima sai bai sake cewa komai ba ya miƙe yana sake
jinjina girman kai da miskilancin yarinyar a ransa. Dan da yawansu a Company haka sukema yanayin
maanal ɗin fassara yaransu da manyansu. A tare da shi suka isa Workshop ɗin. Wajene da yaji kayan aiki
harda na tashin hankali. Dan ingantattun matchings ne da ko'a masu jajayen kunnuwan sai companyn da
yaci ya ƙoshi ke dasu. Ga komai a tsare kuma a tsaftace. Cikin girmamawa suka gaisa da kowa. Tanata
kallon abubuwa wani a cikin horologists ɗin na mata bayani oga kwata-kwata ya iso. Kamar dai ko yaushe
AS ɗinsa biye da shi. Gaisheshi suka shiga yi cikin girmamawa. Ya amsa musu da kulawa shima. Sai lokacin
Maanal da bata ko kalla sashen da yake ba ta furta, “Good morning Sir”.
A taƙaice kuma ciki-ciki ya amsa da, “Morning”. Yana maida hankalinsa ga Director Mustapha. Gaba
yay suka bisa a baya har zuwa inda ake buƙatar ganninsu. Batare da Maanal ta farga ba sai ta tsinceta a
kusa da shi tsaye gefensa na dama. Matsawa taso yi sai dai babu dama dan gabanta glass ne. Dole ta
haƙura mayataccen ƙamshinsa na addabar hancinta. Lokacin da aka ajiye samfarin agogon data zana da
hannunta sai taji notukan kanta na ƙoƙarin kwancewa. Yau mafarkinta ya zama gaskiya. ALLAH mai girma.
Da ƙyar ta iya haɗiye hawayen da suka cika mata ido ta saita kanta tana al'ajabin komai da yaba ƙoƙarin
Watchmakers ɗin harma da horologists ɗin, duk da kafin yau ta taɓa ganin aikinta a zahirance. Kai da ganin
agogon kasan bana siye da ƙananun kuɗi bane. Bayan wanda aka haɗa ɗin sai pieces da suma aka ajiye nan
fa suka shiga tattaunawa. Ɗan abinda Maanal ɗin ta ƙara musu bayani kadan ne ma, sai dai ta sake ƙayatar
da su da fahimtar lallai za'aje da yarinyar a cikin Companyn dan tanada brain sosai.........
__________★
Anan kaduna kam ALLAH ne yayma matafiya dawowa. Wato Hajiya Yaya da maƙarabbanta. Su dai su
Ammie basu san da dawowar tasu ba ma. Sai da suka dawo ɗin tana zaune a falo Sakina na mata kitso
Waleed ya shigo yake gaya mata. Duk da taji mamaki sai batace komai ba tace yaran suje su gaisheta.
Shiru Waleed yayi alamar bai son zuwa. Sai tayi murmushi tana miƙewa. Kitchen ta nufa ta haɗo abinci
a cikin basket ta bashi tace suje dashi su kai. Nan ɗin ma amsa sukai jikinsu duk a sanyaye suka fita. Basu
wani jimaba ko sai gasu sun dawo Hameed harda hawaye fuskarsa zane da sayin mari. Sam Ammie bata
tambayesu miya faru ba, koda Waleed ma zai faɗa sai ta girgiza masa kai da nuna masa hanyar kitchen
alamar yaje ya kai mata kayan abincin da suka dawo dasu ba'a taɓa komai ba.
“Amma aunty ai ya kamata kiji miyya faru? Jibafa fuskar Hameed harda sahun mari”.
Murmushi Ammien ta saki kamar bazatace komai ba, sai zuwa can tace, “Sakina kenan, to minene
amfanin jin? Sakawa kai ɓacin rai ne fa kawai. Koma minene ya faru ai ya rigada ya faru ɗin, sai a barsa ya
wuce kawai”.
“Hummm Aunty wlhy yanayin rayuwarki na birgeni, a ɗan zaman nan na kwanaki a gidan nan na ƙara
samun ilimin zaman duniya. Zuwa yanzu na ɗaura ɗammarar ko sakina Salihu yayi na sake wani auren
nima zan sake wasu abubuwa daga tawa rayuwar”.
“ALLAH sarki ƙanwata ALLAH ya zaɓa mana abinda yafi alkairi to”.
“Amin ya rabbi aunty”.
★★
A sashen Hajiya Yaya kuwa tunda suka kora su Hameed da abincin da suka kawo bayan Basira ta falle
fuskar Waleed da mari sakamakon maida mata magana da yayi sai suka bude sabon shafin zagin Ammie da
ƴaƴanta musamman ma Maanal da tafi kowa tsaya musu a rai. Sunyi mai isarsu kafin su saki zancen su
koma kan Hajiya Basariyya da taje wai gaishesu da musu sannu da zuwa.
A gabanta dai an amsa, dan a cewar Hajiya Yayan idan ma da gara gara Hajiya Basariyya ɗin duk da
kuwa itama a baya ansha gwagwarmaya, amma zuwan Ammie yasa take ɗan jin sassaucin Hajiya Basariyya
a yanzu. Ita kanta Hajiya Basariyya ɗin tana fitowa daga sashen ta wani taɓe baki da jan tsaki. Tana isa
sashenta suka baje kolin yi da su Hajiya Yayan ita da ƴaƴanta itama.
Wannan rayuwar daga Hajiya Yaya har Hajiya Basariyya sun ɗabi'antar da yaransu a kanta tun suna
ƙanana. Shiyyasa yaran sam basa ganin girman matan uban nasu idan ka cire Yazeed da Amrah da halinsu
ya fita daban a cikin ƴaƴan Hajiya Yaya. Ita kam Hajiya Basariyya ma ai bata da zakkar na kirki har yanzu, ko
sai nan gaba yaran sun ƙarasa kaiwa hankalin girma oho. Dan manyan su Huznah ne kawai masu shekaru....
____________
Zaman cikin Workshop ɗin ya jasu lokaci mai ɗan tazara, dan sai da akai kiran azhar suka sami fitowa.
Kasancewar itace ta fara fitowa kanta tsaye ga elevator ta nufa. Sai dai tana zuwa zata danna domin
buɗewa ta figowa ta buɗe kanta alamar wani zai fito. Haka kawai ta samu kanta da maida hankali ga
wajen. Sai ko idanunta akan Huznah data fito cikin matuƙar kwalliya data sakata yin ƙyau ainun. Hannunta
ɗauke da basket alamar kayan abinci ne a ciki. Kallon kallo suka tsaya yima juna. Dan itama Huznah na
fitowa idanunta akan Maanal ɗin suka sauka. Sunyi ma juna kallon fin minti ɗaya kafin Maanal ɗin ta fara
janyewa cike da miskilancinta. Batare da tace da Huznah ɗin komai ba kuma tai shigewarta elevator ɗin
tabar Huznah ɗin sake da baki tana kallonta. Gefe kuma masu shigi da fici ne da suka fassara al'amarin da
wani abu daban can. Domin tuni sun gumtsa gulma.
Har Maanal ta koma ga wajen zamanta mamakin Huznah na mata kaikawo, shin wajen wa take zuwa
ne ai a companyn nan? Wannan shine gani na biyu datai mata. Sai dai a wancan ganin ma bata san wajen
wa tazo ba tunda tana shigowa ne ita kuma tana fita. Kasancewar lokacin salla ne abubuwan hannunta
kawai ta ajiye inda ya kamata ta fita dan mafi yawa duk an fice salla. Sai wanda ba musulmai ba da kuma
masu fashin salla kawai. Sai masu wasa da ita kuma dakan fifita aikinsu sama da tashi yin sallar akan lokaci.
Duk da dokar mai kamfanin ce idan lokacin salla yayi dole ka ajiye kaje kayo in har kana cikin masu yinta
kafin ka cigaba da aikinka. Amma hakan baya hana wasu tauye lokacin...
★★
Cike da takun yanga da yauƙi Huznah ta nufi office ɗin AA. Sai dai tana isowa office ɗin Assistant nashi da
ke farko kafin nasa acan ƙurya sukaci karo shi ya fito. Fuskarsa sai raɓar ruwa take yana ƙoƙarin gyara
hannun long sleeve shirt ɗinsa, ya cire ta cikin sai ƴar ta saman shirt ɗin kawai data kasance milk itama. Shi
baima lura da ita ba sam kasancewar hankalinsa yayi wajen sallar sai da tace da shi, “Hy my boss”. Sannan.
Duk da a hakan ma da farko baiko kalla inda take ba yay shirin wucewa dan bai kawo da shi ɗin ake ba.
Sannan bai riƙe muryarta ba balle yasan ita ɗin ce tunda ya tabbatar ma'aikatansa babu wanda keda ido da
kwallin masa wannan kiran tsagerancin. Yanda ya kama girmansa haka suke tsantsar girmamashi ako ina
daga samansu har ƙasa.
Ɗan saurin shan gabansa da tayi ne ya sakashi kallonta a karo na farko, murmushi ta sakar masa da
ɗaga masa yatsunta biyu cike da iyayi ta ce, “Please boss da kai fa n.....”✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
4️⃣2️⃣4️⃣2️⃣
______________
Amma bari in kira Besty nah Huriyyah nasan zata samu maganin wannan damuwar tawa.
Tunda na kira Huriyya na faɗa mata abunda ke hanani Bacci ta faɗa mun wani sirri da ya girgizani.
Wato ashe itama da ta fara business online kuma bata ciniki amms tunda aka bata number din Coach
Saddiqah komai ya fara tafiya daidai a kasuwancin ta ( Talk with Saddeeqah).
Tunda ta shiga OPERATION CINIKI DOLE ONLINE BOOTHCAMP komai ya warware mata ciniki babu kama
hannun yaro. https://wa.link/8al2f0
Ai ba shiri na nemi Coach Saddiqatu nima domin in shiga tsarinta na Saddeeqah Biz Growth Academy.
Kuma Alhamdullilah ina shiga nafara ganin canji a business dina, har ma sabon online business na buɗe
daga cikin abunda na koya a Operation Ciniki Dole Online Boothcamp.
https://wa.link/8al2f0
Gaskiya wanda ya koya a wurin ƙwararriya ya huta domin ko dubu 100,000 akace in biya in shiga
OPERATION CINIKI DOLE ONLINE zan biya domin amfanin da na samu cikin Boothcamp bazan iya faɗaba,
gashi yanzu na samu na sayi machine din delivery na maida daki guda shago cikin gida na.
Hurayyah ta taimaka da ta haɗa ni da Coach Saddiqah. OPERATION CINIKI DOLE ONLINE ya bani damar yin
ciniki yadda ya kamata ba tare da wana damuwa ba.
Indai kina business ko kina son ki fara Operation Ciniki Dole Online Boothcamp shine ajin farko da Coach
Saddiqah zata rike hannun ki ta nuna miki duk wani sirri da dabaru na kasuwancin online.
Daga rashin ciniki zaki koma sold out domin kuwa zaki dinga yin 6 figures monthly, in kin shiga OPERATION
CINIKI DOLE ONLINE BOOTHCAMP baki ga sauyi mai kyau a business dinki ba za'a maida miki kudinki bayan
90days.
Da Naira Dubu Goma kacal Pre-lunching Price zaki samu damar shiga OCD.( Kina biya zaki fara kwasar ilimi)
Zakuma ki iya jira sai 20th January ki biya Naira Dubu Ashirin.
____________
........Yanda ya wani kalar zuba mata mayatattun idanunsa masu kaifi da cikar kamala yasa zuciyarta
girgizawa. A take harshenta ya fara rawa, sauran abin faɗar tata ya kama gabansa. Sai ta koma in ina da
rawar lips. Komai baice mata ba ya raɓata ya wuce abinsa. Da ƙyar AS ɗinsa dake kallon komai ya iya danne
dariyarsa. Dan shi kam dariya ma Huznah ke bashi. Da tasan manyan matan da suka sha gwagwarmaya da
faɗi tashi akan boss ɗin nan nasa da bata wahal da kanta ba. Amma dai zai cigaba da bin series ɗin domin
ganin inda zai kasance the end. Shine ya bata wajen zama sannan ya wuce massalaci shima a gurguje dan
har an tada salla. Maimakon itama tayi hankalin cewa zataje tai sallar saita gyara zama a lallausar kujerar
dake a office ɗin AS ɗin. Ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya suna charting da sabuwar ƙawarta Nurry dake bata
shawarwarin yanda zatai da AA ɗin yau, dan tun jiya ta juye mata komai sai dai bata sanar mata wanene
shi ba. Gefe kuma tana yi da Yaseerah itama dake ƙara ƙarfafata...
★ Kamar yanda ta saba ana idar da salla ƙoƙarin komawa kan aikinta tayi, ba kamar sauran daketa
tururuwar wucewa cin abinci ba. Cikin ɗan sauri Yaqub ya cimmata, jin mutum a kusa da ita ya sata kallon
gefen nata. Sai ta ɗan sauke ajiyar zuciya ganin Yaqub ne. Gaishe shi tayi kamar yanda al'adarta take ba in
har tai kowacce salla zata gaida na kusa da ita. Shima sai ya amsa da kulawa yana murmushi tare da
tambayarta miyyasa bata son zuwa cin abinci. Murmushi kawai tayi kaɗan, kamar bazata amsashi ba ta dai
buɗe baki da ƙyar dan ƴan miskilancin na kusa ta amsashi da, “Ina zuwa da nawa”.
Murmushi kawai shima yayi, daga haka suka cigaba da tafiya a jere. Sai dai bawata magana ma suke ta
kirki ba, amma duk wanda ya kallesu sai ya sake kallo, harda masu ƴar gulma akan ɗan kusancin nasu daya
fara bayyana kansa ga kowa musamman a kwanaki biyun nan.
Sunzo gab da shiga akai kiran wayar hannun Maanal. Tsayawa tai tana kallon mai kiran, RK ɗin ne ba
wani ba, dan haka ta koma gefe tana amsawa. Shima Yaqub sai ya tsaya jiranta. Cikin takunsa na ƙasaita
yazo ya gitta su, sai dai kamar ance Maanal ta kalla sashen da yake kawai ta hango wata shegen harara
daya zuba mata. Baki ta ɗan murguɗa da kauda kanta gefe ta cigaba da wayarta, dan zuwa yanzu tana ɗan
jin nutsuwar tarayyarta da RK ɗin, duk da bata buƙatarsa a matsayin da shi yake kallon kansa a gareta,
bama shi ba kowanne namiji ita bata buƙata. Basu wani jima a wayar ba sukai sallama dan shima zai shiga
theater yace. Ƙarasa shiga sukai ita da Yaqub, sai dai tana zama ta samu kira daga office ɗin AS ɗin CEO wai
ana nemanta. Rasama abin faɗa tayi, amma sai ta miƙe tana rufe ɗan bowl ɗin data zubo snacks da zataci.
Koda ta iso tayi mamakin ganin Huznah zaune har yanzu, sai dai bata nuna ba ko'a fuska ta isa ga AS ɗin.
Phone ɗin gabansa ya daddana tare da kaiwa kunne alamar kira, an ɗan jima ba'a ɗaga masa ba, ana
ɗagawar kuma cikin girmamawa kamar yana gabansa ya furta, “Sir gata tazo”. Ɗan shiru yay alamar
saurare, sai kuma ya gyaɗa kai yana faɗin, “Okay sir”. Yana ajiye kan wayar ya dubeta fuskarsa da
murmushi.
“Sister Maanal ki ƙarasa ciki”.
Kanta kawai ta gyaɗa masa. Yayinda Huznah ta miƙe ranta a ɓace. “Wane kalar rainin wayo ne ina zaune
ina jira kace wata ta shiga kuma?”.
Cikin girmamawa ya ce, “Am sorry Mss. Ita ɗin staff ɗinmu ce, ganinta nada banbanci da ke. Sannan kiyi
haƙuri boss baya son hayaniya sam. Musamman a irin wannan lokacin.”
Hararar sa ta ɗan yi, yay mata murmushi da faɗin, “Kiyi haƙuri idan ya bada umarnin ki shiga kema zaki
shiga”.
Tsaki kawai taja masa ta koma ta zauna. A ranta tana jin zata iya kwana a wajen har sai ta samu izinin
shiga wajensa yau. Dan ta bakin Nurry sai ta buɗe masa wuta da gaske kafin ta samu kan guy ɗin nan. Zafin
kansa yayi yawa da faɗin rai.....
Kan Maanal a ƙasa ta shiga office ɗin, yana zaune a rukunin kujerun office ɗin masu laushi da ƙyawun
kallo. A one sitter yake zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya, sai novel dake hannunsa, gefensa akan coffee table glass
bowl ne cike da fruits nau'i daban-daban masu tsafta da ƙyawun kallo. Sai bottle na ruwa an zuba wani a
kofin. Har ta ƙaraso kusa da shi amma akwai tazara a tsakaninsu bai nuna yasan da shigowar kowa ba.
Yayinda ita kuma idonta ke akan bangon book ɗin hannunsan. Dan ta jima tana neman novel ɗin amma ta
gagara samu, har kuɗi ta biya dan a kawo mata shi amma har yanzu shiru. Sai kuma gashi yau ta gani a
hannun wannan mutumin.
Duk abinda take yana kallonta ta gefen ido, amma bazaka fahimci hakan ba sai ma karatunsa da yake yi
hankali kwance. Yawu taɗan haɗiye tare da gyara tsaiwarta ta ce, “Good Afternoon sir. Gani, ance kana
buƙatar gani na”.
Shiru bashi da alamar tanka masa balle motsawa, sai da yaja fin mintuna biyu sannan ya ɗan ɗago
yana mai kai hannu ya gyara zaman gilashinsa da ƙyau, sai ta samu kanta da kai hannu itama ta gyara nata.
Zuba mata idanunsa kawai yayi, dai-dai ya ɗago suka haɗa ido. Da sauri ta janye natan tana wani duƙar da
kai na girmamawa. Shi kam kallonta yake kawai daga sama har ƙasa, har ta fara jin gundura da kallon
amma batace komai ba.
Sai da ya gama kalleta son ransa sannan ya ɗauke idanunsa, cikin muryar nan tasa ƙasa-ƙasa ya furta, “I
need a drink”.
Karon farko ta zuba masa ido kai tsaye itama, sai kuma ta kalla bottle water ɗin gefensa fuskarta na ƙara
tsukewa. Kamar zatai magana sai kuma mita tuna ta bar wajen. Kai tsaye fright ɗin office ɗin mai ƙyau
sosai ta nufa. Koda ta buɗe sai tai kasare tana kallon komai. Cike yake da kayan drinks kala-kala. Sai fruits
suma kala-kala kowanne anyi packaging ɗinsa. Haka kawai ta samu kanta da taɓe baki, batare data zauna
tantancewa ba ta ɗauka ɗaya ta dawo inda yake. Sai dai me tana ajiyewa batare daya kalleta ba ya furta,
“Bana shan wannan”. Komai batace ba ta juya ta ajiye ta ɗakko wani. Shima tana kaiwa zata ajiye ya sake
furta, “Changes someone”. Nan ma batace komai ba ta juya ta ajiye ta sake ɗakko wani. Shima haka ya ce
mata baya so. Cikin wani irin takaici da jin zafi ta juya, sai kuma ta tsaya cak batare data kallesa ba ta ce,
“Which one do you need?”.
Shiru yay mata bai tanka ba, hakan ya sake ƙullar da ita. Fuuu ta nufi fright ɗin ta sake buɗewa. Wancan
ta dangwarar a inda ta ɗauka, nacan sama ta zubama ido sai dai hannunta bazai kai ba. Ta gwada ɗauka da
ɗiɗɗishe amma duk tsahonta hannunta bazai kai ba. Juyawa tai tana ɗan kallon office ɗin alamar neman
abin takawa, sai ko idonta ya sauka akan wani ɗan glass table da aka ɗaura ƙyaƙyƙyawan flowers a
samansa. Shiko ta nufa ta sauke flowers base ɗin ta ɗakkosa gaban fright ɗin ta ajiye. Da kallon mamaki
kawai ya bita, sai da ta ɗakko yaga da gaske fright ɗin ta nufa ya ɗan waro oily luluu ayes ɗinsa dake cikin
gilashi.
Itako hajjajun babu ko ɗar ta taka ta haye samansa ta shiga jido kalolin lemukan tana tarawa a ɗayan
hannunta. Ba ita zai rainama hankali ba. Bari ta kai masa duk kalolin taga iyakar rainin wayonsa. Tana
gamawa ta juyo da nufin sauka sai kawai tai wani irin yin baya sakamakon kasancewarsa tsaye a bayanta
hannayensa duk a cikin aljihun ya wani zuba mata mayatattun idanunsa kawai. Kaɗan ya rage ta faɗi, da
ƙyar ta iya daidaita tsaiwarta tana tura baki batare data cigaba da iya kallonsa ba. Shi kam nasa idanun
ƙyam a kanta ko ƙyaftawa bayayi. Kasa jurewa kallon nasa tayi, kasancewar ta a saman table tsahonsu ya
dai-daita a yanzu harma ta ɗan zartashi kaɗan. Tun tana jin zata iya daurewa har jikinta ya fara rawa. Ga
sanyin fright ɗin da bata rufeba na busota, ta gaba kuma ya tareta tako ina dan tsaye yake gab da ita sosai.
Ga kuma drinks data tara a hannu suma sanyinsu na shigarta. Wani irin cikowa idanunta sukai da ƙwalla,
cike da sarewa ta saki drinks ɗin suka tarwatse a ƙasa har wasu na faɗa masa a kan ƙafa amma bai motsa
ba.
Zarrrr hawaye suka fara gudu a ƙyaƙyƙyawar fuskar Maanal. Lips dinta na wani irin motsi na son yin
magana amma kuma ta kasa. Karan farko ya ɗan lumshe gajiyayyun idanun nasa tare da taɓe baki kaɗan.
Sai kuma ya kai hannu a hankali ya rufe fright ɗin, yaja jikinsa yabar wajen batare da yace mata komai ba.
Sauka tayi itama jikinta na cigaba da rawa zuciyarta na mata wani irin zafafa mata jin zafisa. Ko kallon
drinks ɗin data zubar batai ba ta nufi hanyar ƙofa tana share hawayenta. Sai dai koda taja handle ɗin
domin buɗewa sai ta jita bam a rufe. Tsaye kawai tai jikinta na sake cigaba da rawa. Hawayenta na ƙara
ƙarfin gudu. Ta ƙara kai hannu taja amma still dai. Ai bama tasan ta wani irin juyowa inda yake ba, sai kawai
ganinta tai a gabansa.
Cikin matuƙar ƙunar zuciya da raɗaɗi ta ce, “Mikake buƙata da ni ne wai? What is your business with
me? ”.
Idan office ɗin ya motsa to shima ya motsa. Nunama yasan da ita a gabansa baiyi ba, karatunsa kawai
yake yi. Hannu tasa ta fisgi book ɗin tai wurgi da shi saman kujera, cikin matuƙar tsiwa da komawa ainahin
Maanal data mutu (😂injita) ta sake matsosa a kausashe, cikin ƴar tsawa ta furta “Ajwaad!! Nace mi kake
buƙata da ni? Kana min abubuwa ina ɗauke kai amma na kula kai ka kasa fahimtar karatun kurma. Dole ne
sai ka kasance in to my life ne? Kasan dai ni ba shasha bace da zaka taka yanda kake so kamar yanda ka iya
ko, kodan kaga nazo ina aiki ne a ƙarƙashin alfarmarka kake ɗaukata a ban san mi nake yi ba? To daga yau
nabar aikin, na bari tunda dama ra'ayina ya sani jin zanyi bawai rasa tallafin rayuwane ba ko talaucin da da
ake kallonmu a ciki....”
A karo na farko da tun isowarta wajen ya ɗago mayatattun idanunsa dake cikin gilashi, gently hankali
kwance ya zuba mata su. Sake hayayyaƙo masa tai har tana nunashi da ɗan yatsarta manuniya tamkar zata
tsokale masa ido. Idanunsa da yake ɗan ƙyaƙyƙyaftawa ya ɗan ja kamar zai lumshe sai kuma ya sake
buɗesu warrr a kanta. Cigaba take da nunasa tana masifarta har baya ma fahimtar abinda take faɗa, tsabar
yanda ta birkice tuni veil ɗinta datai rolling ya warware hakama ɗan kwalin ya zame dogon gashinta baƙi
siɗik dake ɗaure a tsakkiya cikin ƙyaƙyƙyawan ribbon ya bayyana sai lilo yake. Sosai ya maida idanunsa ya
zuba akan gashin yana masa wani irin kallo.
Ina Maanal bata san yana yi ba, masifarta kawai take tana kuka. “Na tsaneka, wlhy na tsaneka Ajwaad.
Bana son ganin ko fuskarka, da nasan ƙaddara zata sake haɗamu a duniyar nan dana roƙa ALLAH mutuwata
kafin hakan. Na cigaba da yin aikin nan ne dan kawai baka isa hanani yin abinda raina keso ba a duniyata a
duk inda naso hakan koda kuwa wajen mallakinka ne......”
Duk da wani irin saukar aradu da kalamanta ke masa a cikin kunne a bazata, matuƙar bazata taji
tattausan hannunsa ya sauka akan yatsar ta dake neman cokale masa ido. Fisgar hannunta tayi tana sake
birkice masa. Sai dai riƙon da yayma yatsar bana wasan yara bane ba. Dan fisga ɗaya ya mata bama wani
da ƙarfi ba sai gata a gabansa a zube. Biyota yay da kallo har lokacin ɗan yatsar nata dai na riƙe a
hannunsa.
“Wlhy koka sakeni kona maka ihu”.
Karo na farko ya saki wani ɗan iskan murmushi yana ɗan ɗage girarsa ɗaya, sai kuma ya sauke ƙafarsa
duka ya ajiye a ƙasan carpet ɗin da take zaune tare da duƙowa sosai kusa da ita gab har tana jin
numfashinsa da ƙarfin turarensa sosai a cikin hancinta. Jikinta taso ja baya sai dai sam yaƙi bata damar
haka. Cikin sake lumshe idanu da buɗesu a lokaci guda ya motsa laɓɓansa ƙasa-ƙasa ya furta, “Bismillah yi,
ba ihu ba? Maza kiyi, ai bana yau ne farko ba daman”.
Cusa kanta tayi cikin ƙafafunta ta dunƙule a waje ɗaya tana mai fashewa da kuka. Ga jikinta na
matuƙar rawa. Tabbas komai dawo mata yake. Ta ƙarfin tsiya da tsiya-tsiya brain dinta da zuciyarta keson
tilastata tuna baya. Bayan data jima da shafewa a tarihin rayuwarta. Bayan da bata fatan koda wata alama
ta tuna shi, bayan da take kallo tamkar RAYUWA A BAYAN MUTUWA. Bayan data jima da tattarashi ta tura
can bayan bayanta ta yanda bazata sake tunawaba har gaban abada. Miyyasa yake son tilastata ne?
Miyyasa bazai mata adalci bane? miyasa yake son sake cuta mata da wannan DAFIN da yay ajalin ainahin
Maanal. Miyyasa bazai gane komai ya canja bane, canjawa irin wadda ke shafe ƙarnuka da zamanoni
tamkar ba'a yisu ba. Kaicon samuwar wannan aiki nata, kaicon amincewarta da yinsa. Ita da kanta ji take
ma ta tsani kanta da kanta a wannan gaɓar.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
4️⃣3️⃣4️⃣3️⃣
______________
........Shima da gaba ɗaya kansa ke juya masa, al'amura masu nauyi da suke lulluɓe a zuciyarsa na sake
zaburowa, a hankali ya saki mata yatsan yana rumtse idanunsa da ƙarfi. Wani irin ratsa zuciyarsa da ɓargo
kukan nata yake yi. Sai dai bazaka taɓa fahimtar hakan a fuskarsa ba idan ka cire idanunsa da sukai
matuƙar kaɗawa. Tawani fannin kuma zai iya cewa kukan yake so tayi, dan zai rage mata nauyin zuciya
dana zafinsa da yasan take ji. Fin mintuna biyar suna a haka kafin ya miƙe a wajen, veil ɗinta dake yashe a
ƙasa ya ɗauka, ƙamshinsa na sake ratsa hancinsa, kanta ya ɗan rankwafo ya yafa mata veil ɗin a saman
kanta batare da yace komai ba ya wuce ainahin office chair ɗinsa, batare daya zauna ba ya ciri ƙaramar
pepper yay ɗan rubutu, sai kuma ya ɗauka shopping bag ƙarama dake a saman desk ɗin. Rigar suit ɗinsa
dake a hanger ya cire itama tare da tattare wayoyinsa. Gabanta yaje ya ajiye shopping bag ɗin nan da shot
note ɗin da yayi batare da yace mata komai ba ya nufi ƙofa. Sai da ya kai hannu zai danna maɓallin buɗe
ƙofar batare daya jiyo ba ya furta, “Ki tabbatar kin shiga restroom kin gyara fuskarki”. Daga haka yay
ficewarsa cike da takunsa na nutsuwa da ƙasaita.
Da wani irin sauri Huznah dake zaune cikin takaici da damuwa ta miƙe. Hakama AS ɗinsa daya san
wannan ba lokacin fitowarsa bane miƙewa yayi. Baiko kalla inda Huznah take ba, sai Assistant ɗin nasa ya
kalla. “Zanje airport ɗaukar su Mamy. Take care of everything”.
“Okay Sir ALLAH ya tsare”.
Kansa kawai ya jinjina masa yay wucewarsa. Har kuma yayi taku uku sai ya tsaya cak jin ana binsa a baya.
Ɗan waiwayowa yay tamkar mai jin ciwon wuya ya zuba mata ƙasaitattun idanunsa da gaba ɗaya suka
sauya kala da launinsu. Dan farin gilashin fuskarsa bai zam ya ɓoye komai ba daga garesu. Kasa jure
kallonsa Huznah tayi, sai ma jikinta dake neman fara rawa. Amma tai ƙoƙarin riƙe kanta da tsiya, sai dai
muryarta na ɗan rawa ta ce, “A zahiri bakayi kama da mai wulaƙanta mutane ba, why ni nake neman zama
ƙasƙantacciya a yayin zuwa ganinka? Please ka duba ni, ka bani dama muyi magana dan ALLAH”..
Karo na farko ya lumshe idanun nasa da buɗesu. Hakan tuni ya zame masa ɗabi'a musamman a yayin
son yin magana. Cikin cool voice ɗinsa mai fidda ƙaramin amo da kasancewa ƙasa-ƙasa tamkar ba namiji
ba ya furta, “Mi kike buƙata?”.
“Kai! Kai nake buƙata AA. Ina son yin magana da kai Please”.
Lips ɗinsa ya ɗan ciza sai kuma ya janye idanunsa daga kanta. Ƙoƙarin wucewa yay batare daya tanka mata
ba yana kallon Designer agogonsa da sai ka gama karaɗewa baka samo sa ba, dan shi duk wani agogon
sakawarsa ana masa shi a companynsa kuma shi kaɗai, sai idan wani ne yace yana so ayi irinsa daga nan
shi kuma yabar saka Design ɗin sai kuma wani. Da sauri ta bi bayansa suka shige cikin elevator daya buɗe.
Anan ɗin ma dubansa tayi da son yin magana sai dai ta gagara sakamakon ganin fuskarsa babu alamun
wasa. A haka suka fito tanata ƙoƙarin ganin ta daidaita tafiyarsu. Aiko hakan yaja hankalin ma'aikatansa
matuƙa. Dan duk inda suka gitta idanu yuuu akansu. Masu ƙus-ƙus nayi masu jinjina kai nayi. Yayinda
zukatan mafi yawansu suka sake yarda da eh lallai da gaske itace boss ɗin nasu zai aura kuwa. Dan abune
da basu taɓa gani ba boss da mace kamar haka. Ina dai ka gansu da wata to lallai abokiyar kasuwanci ce,
dan shi hatta a cikin family baya kula ƴar kowa, in dai kina sama da shi zai yi respecting ɗinki. Suna gama
ficewa sai ƙus-ƙus ɗin ya ƙaru, yayinda wasu suka maida hankalinsu ga hotunan dake akowacce kusurwa ta
Company ɗin na mace mai niƙab da hijjab. Wadda da yawansu sun gagara tantance hoto ne ko zane ne. So
suke su tantance ko wadda suka fita taren ce. Sai dai sam babu wani alamu ko kamanni daya nuna hakan.
Dan baka isa tantance ainahin wacece a hoton ba tako ina....
Yana fitowa drivern sa dake can wajen securitys suna hira ya miƙe da sauri. Sai dai koda ya iso garesa
sai ya miƙa masa hannu murya ƙasa-ƙasa yana faɗin, “Don't worry, give me the key, I want to drive myself”.
Babu musu driver ya rissina ya miƙa masa key ɗin. Sai kuma ya buɗe masa motar da sauri.
“Ka sama mata taxi”.
Ya sake faɗa yana ƙoƙarin shiga motar, kallon Huznah driver yayi, sai kuma ya amsa da sauri cike da
girmamawa. Huznah kam dake tsaye kamar zata saki kuka kallonsu kawai takeyi, tana ji tana gani a gabanta
ya birka motarsa ya fice cike da ƙwarewar iya tuƙi na nutsuwa da cikar kamala....
Lallai yau taga madarar wulaƙanci da babu ko gauraye a cikinta, wato mutumin nan cikin ruwan sanyi
yake tsula maka tsiya babu hayaniya babu hargowa ko yawan magana. Dole ne ta koma Kaduna su sake
shiri kam, amma zata fara bari ta haɗu da mahaifiyar tasa dan taga yaya nata takun itama, hakan zai sa
susan irin shirin da zasu musu su duka.. da wannan tunanin ta ballama drivern harara ta fice da ƙafarta.....
★★★
Maanal ta jima a wajen tana kuka, sai da ta fara jin zuciyarta na mata nauyi a cikin ƙirjinta kafin ta ɗago
kanta da ƙyar, office chair ɗinsa ta zubama ido sosai tamkar shine a wajen, har yanzu hawayen na cigaba
da ziraro mata. Tunanin dake neman tasiri a ranta ta ture da ƙarfin tsiya tare da miƙewa ta nufi restroom
ɗin kamar yanda ya faɗa, dan itama tasan ko giyar wake tasha bazata fita a haka ba ai. Sosai restroom ɗin
ya haɗu, gashi ƙal-ƙal sai ƙamshi yake zubawa kamar ba toilet ba. Ta jima tsaye tana kallon kanta a mirror
ɗin bayin tana hawaye kafin ta wanke fuskar tata ta fito bayan ta gogeta da ƙaramin towel fari tas dake a
bayin. Harta nufi ƙofa ta koma da baya, shopping bag ɗin daya ajiye a gabanta ta ɗauka kasancewar ganin
abinda ya rubuta a takardar daya ajiye a sama, sai kuma ta maida ta ajiye. Nan ma ta juya zata tafi idonta
suka sake sauka a novel ɗin nan nasa. Baki ta tura gaba sannan ta ɗauka shi dai ta ficewarta..
Koda ta fito bata kula kowa ba a wajen ta shiga haɗa ƴan tarkacen kayanta, kallonta kawai su
Zaharadeen suke cike da gulma. Sai Yaqub ne daya miƙe tsaye yana kallonta tun shigowarta ya furta,
“Sister Maanal are you okay?”.
Kanta kawai ta jinjina masa batare da dace komai ba. Kafin ya samu damar sake magana ta kwashi
kayanta zata wuce. Cikin sauri ya bita yana faɗin, “Ina zaki je?”.
“Gida”.
Ta bashi amsa a takaice. Cikin tashin hankali ya buɗe baki zai sake magana a fusace ta ce, “Please Yakub!
Nace ba komai. Leave me alone”. Daga haka tai gaba abinta fuuuu. Shiru yay kawai yana kallonta, gaba
ɗaya fuskarsa ta nuna tsantsar damuwa da tashin hankali. Shin mike faruwa? Mi akai mata? A office na
CEO fa aka kirata! Miya faru acan ɗin?”. Rashin mai bashi amsa ya sashi juyawa jiki a sanyaye ya koma ciki.
Sai kuma ya sake tadda wani abun takaicin, su Zaharadeen ne suke buɗe babin gulmar Maanal ɗin. Wai
maybe ta faɗama CEO tana sonshi ne shine ya koreta a aiki, sai ALLAH ya ƙara suke mata da kiranta mai
girman kai da faɗin rai. Takaicinsu ya saka Yakub ko kulasu baiyi ba......
______________★
“Alhamdullahi ranka ya daɗe aiki ya kammala. Wannan shine cikakken bayani akan ainahin mahaifinta
dama zuri'arta baki ɗaya”. Rabilu ne mai maganar fuskarsa washe da murmushi yana miƙama Sen.. Bukar
bayani akan Maanaal daya binciko kamar yanda ya buƙata. Sosai fuskar sa ta washe da murmushi. Dan shi
kaɗai yasan yanda yake azabtuwa da so da ƙaunar yarinyar nan data mamaye dukkan illahirin jinin jikinsa.
Yanzu haka yau har gaban Mawaad company yasa drivern sa yaje ya faka mota har Maanal ta iso. Fitarta a
motar Shahidah da dukkan abinda ya faru a wajen kan idonsa ne. Ji ya dingayi kamar ya sato ta saboda
yanda tai matuƙar ƙyawu a cikin kwalliyar ta yau.
Rabilu ya cigaba da faɗin, “Su ɗin asalin su ƴan jihar Kebbi ne, ƙaramar hukumar suru a wani ƙauye da
ake kira giro. Mahaifin nata ɗan sanda ne, dan har ya kai matakin DPO amma yanzu ya ajiye aiki
sakamakon doguwar jiyyar da yayi. Ita kuma mahaifiyarta bata tare da shi a yanzu, dan sun rabu shekaru
kusan takwas kenan, a yanzu haka tana auren wani Alhaji Usman Chalawa ne anan kaduna, yana riƙe da su
kuma tamkar mahaifin nasu koma fiye da shi.”
Cike da zumuɗi ya furta, “Rabilu kaje wajen Oler ka amshi key ɗin motar ka sabuwa dal, zuwa dare zan
nemeka idan na koma gida”.
Cikin matuƙar washe baki Rabilu ya shiga godiya harda ɗan zamowa daga visitors chair da yake zaune ta
office ɗin Sen.. Aifa cike da zumuɗi ya bar office ɗin. Kai tsaye gidan Sen.. Bukar ya nufa domin amsar
alƙawarinsa dan yasan baya magana biyu akan alkawari irin wannan daya shafi mata. Zai iya cewa dukan
matan alhajin idan ka cire uwargidansa duk shine ya masa bincike akan sauran biyun. Ya kuma taka rawar
gani akan samuwar auren fiye da zaton mai zato. Sai dai ya fahimci kamar Senator ɗin yafi sakin kuɗi da
ɗoki akan wannan ƴar shilar. To ƴar shila mana. Akan matan Alhaji ai manaal ƴar shila ce. Dan ko jikansa na
farko ya girmi Maanal sosai. Aiko ina sha ALLAHU zai yi iya ƙoƙarinsa dan ganin tako ina Alhaji bai samu
matsala ba, ya kuma mallaki yarinyar da gaggawa. Dan yasan irin wannan kariɓujin arziƙin da ire-irensa
sunta zuwa kenan. Zama kuwa ai ba nashi bane ba....
____________★
Cike da nutsuwa Daddy ke kallon Yazeed. Yayinda shi kuma kansa ke duƙe a ƙasa rauninsa na sake
bayyana akan fuskarsa. Karo na farko Daddy ya ɗan saki murmushi, yayinda tausayin yaron nasa ke ratsa
masa zuciya. Ya jima da fahimtar tsananin so da Yazeed kema Maanal, sai dai bai sake tabbatarwa ba sai a
ɗan tsakanin nan. Musamman yau da yazo masa da roƙo da magiyar janye batun sai nan da wata biyar ayi
aurensa da Manaal. So yake a haɗesa gaba ɗaya anan da sati biyun daya rage shi da Nazeefa. Gyaran
murya yay da gyara zamansa. Hakan yasa Yazeed ɗagowa ya ɗan kallesa.
“Yazeed kasan dai ina bayanka nima ɗari bisa ɗari akan zancenka da Maanal. Sai dai ina son kamar
yanda su Baba Kalla suka faɗa wannan karon naje da kaina da baba nema maka aurenta ga mahaifinta.
Hakan shine zai bada salama game da tujarar mahaifiyarka akan al'amarin”.
“Daddy nima na yarda da hakan, amma dan ALLAH ina sake neman alfarmar haɗewar gaba ɗaya. Nasan
ko'a cikin satin nan zaku iya zuwa ga mahaifin nata, idan kuma ka amince min ni saina fara zuwa na
ganshi”.
Ɗan jimmm Daddy yayi, sai kuma ya shiga jinjina kansa. “Shike nan na yarda da zancen naka in sha
ALLAHU za'a haɗe bikin nan da sati biyun, zan samu Baba da batun shima sai mu saka ranar zuwa muga
mahaifin nata, kai ka tsahirta sai bayan mun dawo ɗin. Kadai je ka cigaba da shirinka na zama angon mata
biyu a rana ɗaya”.
Ƙasa Yazeed yay da idanunsa wani murmushi na suɓuce masa. Yayinda zuciyarsa ke wani irin washewa
da farin ciki mara misaltawa. Ji yake kamar an masa gafarar zunubansa. Yana fitowa ya shiga neman layin
Maanal dan yay mata albishir, sai dai bata shiga ba. Duk da yasan yanzu tana office kasa haƙuri yayi ya
shiga neman Shahidah. Bayan sun gaisa yake tambayarta Maanal fa. Cikin girmamawa ta sanar masa har
yau ba'a dawo mata da wayarta data samu matsala ba ne, amma tana ƙyautata zaton yau za'a kawo mata,
sai dai idan ta tashi zata haɗasu.....
___________★
Shiru kawai Ammie tai tana kallo Daddy dake mata bayanin sabon hukuncin daya sake yankewa akan
dawo da zancen bikin Maanal da Yazeed anan da sati uku. Za'a haɗe ɗaurin auren kawai idan ma bikin
Maanal ɗin ne za'a ɗaga nan da zuwa ko wata ɗaya ne idan ita bata shirya ba to. Sai kuma batun zuwa ga
dangin mahaifinta kamar yanda sukai alƙawari tun farko. A yanzu haka ma yana shirin zuwa su tattauna da
baba ne. Ya sanar mata ne koda sun gama yanke hukunci shi da baban basai sannan taji ba.
Zuciyar Ammie kaikawo kawai take a cikin ƙirjinta, sai dai kamar yanda ta saba dannewa yanzun ma
saita danne ta amsa masa da girmamawa tare da jera addu'ar fatan alkairi. Wannan halayyar nata ke ƙara
masa jin sonta da ƙaunarta. Bayan ya wuce hawaye cike da idanunta tayi kiran Nene, ko gaisawa basuyi ba
ta sanya mata kuka. Sosai hankalin Nenen ya tashi, ta shiga tambayarta abinda ke faruwa a rikice. Sosai
Ammie tayi kuka kafin ta zayyanema Nene komai. Itama hankalin nata tashi yay, harma taji ta gagara furta
komai..
___________★
“Aunty Babba nifa ina son ku haɗu ke da Aunty Majdiya da Aunty Khaleesat kuyi magana da Baffah
akan batun nan. ina so a cikin watan nan iyaye suyi magana, kuma wata biyu kawai nake so a saka, itama
Maanal yau zanyi magana da ita”.
Baki Oum ta buɗe kamar a ɗan firgice zata bama RK amsa idanunta suka sauka akan AA dake kokarin
shigowa, sai dai furucin RK ya sashi tsayawa cak shima..........✍️
_Wannan fa shine cakwakiya, tako ina kowa ya zaburo. Manaal akwai white blood kam🤣. Dangin AA wai
mike damun Yayanku ne?🥱🏃_
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
4️⃣4️⃣4️⃣4️⃣
______________
.......Kallonsa kawai Oum take yi zuciyarta na motsawa da bugawa da sauri-sauri, yayinda shima ya zuba
mata gajiyayyun idanunsa da suka sake kaɗewa. A hankali ya ɗaga ƙafarsa zai juya ya fita ta kira sunansa a
hankali.
“Ajwaad!”.
Cak ya tsaya batare daya juyo ba. Yayinda RK da bai lura da shigowar AA ɗin ba ya juya shima yana
kallonsa. Cikin rashin fahimtar abinda ke faruwa ya saki murmushi da faɗin, “Ni dai ban more ɗa ba.
Malam dawo bafa wata magana bace daban kaima ayi dakai batun son zuwa a nema min auren ƙanwarka
Maanal mukeyi kawai”.
Da wani irin ƙarfi AA ya rumtse idanunsa jikinsa na wata irin tsuma. Da sassarfa ya nufi ƙofa murya a
shaƙe ya furta, “Oum na ɗakko su Mamy” daga haka yay ficewarsa.
Da mamaki RK ya dubi Oum shima, “Aunty mike damun ɗanki?”.
Murmushin yake Oum tayi kawai. Zuciyarta na ƙara raunana da mata nauyi. Cikin son danne komai ta ce,
“Maybe aiki ne ko kuma an kunnosa daga waje. Kaga ka bari zamu tattauna anjima su Aban sun iso”....
___________★
Kamar yanda Sen Bukar ya faɗa zuwa dare ya sake sabon zama da Rabilu. Sun sake tattaunawa sosai
tare da tsaida ranar zuwa Giro domin ganawa da mahaifin Maanal. Yayinda tun a ranar ya sanarma
uwargidansa shifa zai ƙara aure. Dan yau a gidanta yake. Kamar yanda ta saba cikin nuna rashin damuwa
tai masa addu'a da fatan alheri. Sai da ta fito daga ɗakin nasa ta koma nata taci kuka. Ita kaɗai tasan yanda
take matuƙar takaicin aure-auren nan na mijinta. Dan ita macece mai tsananin kishi. Shiyyasa a dukansu
daya auro kowacce jinta take a sabuwar kishiya. A gareta bata yarda da zancen hausawa da kance kishiya
ta biyu ita kaɗai ce kishiyar uwargida ba. Ita duk kishiya sunanta kishiya a wajenta. Sai dai irin matan nan
ne ita masu ƙullata da shanye abu a cikinsu bazaka taɓa jin sun furta da baki ba. Shiyyasa ake mata kallon
mai haƙuri. Amma sam ba haka bane ba, domin kuwa tana nan tana tara abubuwan a rai suna mata
nauyi...
Shiko Sen.. Bukar ko'a kwalar rigarsa, dan tun a daren yama gama tsara komai. A gefe kuma ya saka
babban yaronsa Oler yo shopping na garari zuwa gobe domin yin tsaraba kaikace ganin danginsa zaije
ƙauye ba neman iznin neman auren ba......
_________
Tunda ya baro sashen Oum kulle kansa yay a bedroom ɗinsa. Wani irin ciwo kansa ke masa, ga sanyi
na ratsa masa ɓargon jiki da ƙashi, bai ko iya cire takalman ƙafarsa ba ya faɗa saman gado tare da jan
duvet ya ƙudundune kansa. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa zazzaɓi ya rufesa gaba ɗaya. _(Na tsaneka, wlhy na
tsaneka Ajwaad. Bana son ganin ko fuskarka, da nasan ƙaddara zata sake haɗamu a duniyar nan dana roƙa
ALLAH mutuwata kafin hakan. Na cigaba da yin aikin nan ne dan kawai baka isa hanani yin abinda raina
keso ba a duniyata a duk inda naso hakan koda kuwa wajen ya kasance mallakinka ne.....”)_ wani irin sara
masa kan nasa yayi sakamakon kalamanta da suke maimaita kansu a cikin kunnensa tamkar yanzu ne take
ambatosu, ko a ɗazun ma dakewa kawai yake yi a gabanta. Ji yake tamkar yayta fasa ihu, ihu irin wanda sai
ya janyo girgizar ƙasar da kaf gidajen duniya zasu narke cikin ƙasa. Sai dai ba zaiyi hakan ba, sai ma
ambaton ALLAH da ya dingayi a zuciyarsa...
Dai-dai nan Oum da hankalinta ya kasa kwanciya ta iso sashen nasa. Dan har ta nufi sashen mahaifinsu
ta fasa tayo nan. Ganin babu shi a main falo yasata haurawa sama da sassarfa. Nan ma babu kowa komai
ma a kashe yake tamkar ƙasa. Bedroom ɗinsa ta nufa, tai nocking da kiran sunansa amma shiru. Handle ɗin
ta kama zata buɗe dan zuciyarta na sake tabbatar mata babu lafiya amma sai taji gam. Sosai hankalinta ya
sake tashi ta shiga kiran sunansa cikin damuwa da lallashi. Amma fin mintuna biyar baida alamar amsawa.
Hawaye suka fara ziraro mata cikin rawar murya ta ce, “Haba sweetheart sokake na maka kuka. Ka buɗe
naga halin da kake a ciki Please Autan Oum”.
Nan ɗin ma babu alamar motsinsa, hankalinta ne ya sake tashi, cikin sassarfa ta juya ta fita. Sashen Abah
ta nufa, sallama kawai tayi batare da jiran amsa ba ta danna kai cikin bedroom ɗinsa. Dai-dai ya fito a
wanka, batare da ya kalleta ba cikin barkwancinsa da Fawzan ya gada ya ce, “Ai ni da na cika fam saura
kaɗan na fashe ganin matar gidan yau bata ɗokin dawowata kamar yanda shima ɗanta baiyi.....”
Jin tayi shiru sai ma kamar tana kuka ya sashi fasa nufar mirror da yay niyya ya juyo yana kallonta.
Tsamm yayi sai kuma ya tako a hankali zuwa inda take cike da nutsuwarsa da cikar kamala. “Fateema miya
faru?”. Ya tambaya hankali tashe. Idanunta dake zirar da hawaye ta zuba masa. Da ƙyar ta iya motsa lips
ɗinta ta furta, “Ajwaad. Ya rufe kansa a ɗaki nayi kiran duniya bai amsa ba. Ina jin tsoro, tsoro nake ji Zaki
na, kada yanayinsa na bayane ke son dawowa”.
Ɗan lumshe idanu Abah yay ya sake buɗewa a kanta (Sak ɗabi'ar AA da alama a wajensa ya gada rufe
ido da buɗewa yayin magana😂). Hannunsa yasa ya riƙo nata, cikin yanayin tashin hankalin shima ya ce,
“Oh kenan akwai abinda ke damunsa? Dan a haka yaje ɗakkomu airport fuska kicin-kicin, daga gaisuwa ko
bai sake kulamu ba har muka shigo gidan nan. Wani abu ya faru ne?”.
“Ni dai a sani na babu abinda ya faru a yau ɗin, duk da dai satittikan nan gaba ɗaya gashi nan dai
tunda ya tashi daga zazzaɓin nan na gab da tafiyarku, yau kuma daga office ya wuce ɗaukanku dan da
Fawzan ne zai je sai ya kirani akan akwai meeting na gaggawa da zai shiga dan ALLAH nama Auta magana
yaje ɗaukanku ko Babban yaya. Shi kuma Fadeel ya tara aiki a office saboda zuwa Kanon nan da yay
shiyyasa na turama Autan text akan shi yaje, ya kuma kirani a waya babu wani damuwa a tare da shi yace
min zaije ɗin dan bashi da wani abu mai muhimmanci a lokacin, sai kuma gashi ya dawo yanzu a birkice.”
Cikin furzar da iska mai nauyi Dad ya ce, “It's okay ina zuwa.” closet ɗinsa ya nufa ya saka kaya tare da
buɗe wata loka ya dudduba keys, ɗakko na sashen AA yayi yazo ya kama hannunta suka fito. Suna ƙoƙarin
shiga sashen motar Fadeel da kowa ke kira babban Yaya a gidan ta shigo. Ganin yanda suka nufi sashen
Auta kamar hankali a tashe ya sashi fitowa da sauri shima yabi bayansu ko rufe motar ma bai gama yi ba.
Matarsa data fito daga flat ɗinsu domin tarbarsa ganin inda ya nufa ta ɓata fuska da binsa da harara, har
zata juya a fusace sai kuma ta fasa itama ta nufi sashen AA ɗin dan son ganin mi mijin nata kema gudun
zuwa yi sashen ƙanin nasa mai shegen girman kai.
Lokacin da suka iso su biyun Abah nata ƙoƙarin gwada key a ƙofar bedroom ɗin AA ɗin, yayinda Oum ke
duba sauran bedrooms ɗin da ɗazun rikicewa ta mantar da ita dubawa. Dama bedrooms uku ne a saman,
ƙasa ma uku. Ɗaya a main falo biyu a ɗayan falon.
“Abah lafiya kuwa?”.
Fadeel daya iso ya faɗa a rikice. Batare da Abah ya dubesa ba ya amsa masa da, “Ban san mike faruwa ba
nima Fadeel. Oum ɗinku ce tazo hankali tashe tana sanar min Ajwaad ya kulle kansa a ɗaki”.
Kafin Babban yaya ya samu damar cewa wani abu ƙofar ya buɗe. Su duka afkawa sukai ciki har Oum da
matar babban yaya data iso yanzun nan. Aiko tuni hankalinsu ya sake tashi dan ganinsa a bargo, yayinda
tuni Oum da babban yaya sun haura saman katafaren gadon nasa dake a dunƙule kamar zero. Oum ce ta
yaye bargon dan har fuskarsa ya rufe, hucin zafin zazzaɓinsa ne ya bugeta, sai kuma rawar sanyin da yake
faman yi. Cikin fashewa da kuka Oum ta kamo hannunsa ta damƙe cikin nata tana kiran sunansa......
________★
Kusan zamu iya cewa a position ɗaya AA da Maanal suke a ciki. Dan itama bama ta san a yanayin data
iso gidan ba. Sai maigadi ne ya biya taxi drivern daya kawota. Itako tuni ta shige ciki tana layi saboda
nauyin da ƙirjinta yay mata har numfashinta na seizing. Batama ko ƙarasa shiga cikin ainahin falon ba ta
zube a ƙofa tana ƙoƙarin kiran sunan Shahidah sai dai muryarta sam bata fita. ALLAH ne ya taimaka Linda
ta fito dan tana ƙoƙarin jera abincin su Barrah a d/table kasancewar suna gab da dawowa daga school.
Idanu ta zaro tare da dangwarar da abinda ta ɗakko ɗin ta nufi Maanal da gudu. Ganin numfashinta na
neman barin gangar jikin ta yasa Linda kwara ihu. Ai a guje baba magajiya ta fito daga kitchen tana
tambayar Linda mike faruwa?. Ganin Maanal dake kakarin mutuwa yasa itama ta fasa ƙarar. Sai kuma ta
runtuma waje a guje tana kiran maigadi. Cikin sa'a ta samesa tare da drivern yara da yazo ɗaukar mota zai
tafi ɗakkosu. A guje suka koma ciki su ukun, Linda da Baba magajiya suka cicciɓi Maanal suka fito, a mota
aka sakata, baba magajiya ta shiga itama driver yaja suka fice aka bar maigadi da Linda dan bazai yiwu
subar gidan babu kowa ba kuma.
Maigadi ne ya tunatar da Linda cewar ya kamata ta kira Hajiya ta sanar mata. Sai yanzu itama ta farga
da haka. Lokacin da ta kira Shahidah tana tsaka da aiki, amma haka ta wancakalar da komai cikin tashin
hankali ta fice zuwa asibiti bayan ta kira RK. Cikin tashin hankali ya sanar mata isowar su Maanal ɗin a
yanzu haka. Kana jin muryarsa kasan shima ya gama gigicewa, sai Shahidah ta ƙara ruɗewa itama.
★ A wannan karon ma dai ansha matuƙar wahala kafin ceto numfashin Maanal, sai dai sam babu aman
jini idan ka cire wanda ya ɗan ziraro mata ta hanci kamar haɓo. Shima kuma basuyi wahala wajen tsaidashi
ba. Su Dr Ranjet basu samu nitsuwa ba sai bayan isha'i, dama shi RK wannan karon ma kasa komai yayi
bakamar wancan karon da akai komai da shi ba. Sai dai yana a bakin ƙofar tare da Shahidah da mijinta da
shima ya iso suna zaman jiran tsammani. Fitowar su Dr Ranjet ya saka su dukansu miƙewa. RK kamar ba
likita ba ya nufesa da sassarfa yana tambayarsa yaya take?. Cike da kulawa Dr Ranjet ya dafa shi yana faɗin,
“Calm down doctor, everything is fine”. Kusan su ukun a tare suka sauke ajiyar zuciya mai matuƙar nauyi.
Yayinda Dr Ranjet ya sake kwantar musu da hankali.....
__________★
A ruɗe Oum tacema Babban yaya yay mata kiran Uncle ɗinsu yana sashenta. Fita yay kuwa da sauri, sai
dai yana fitowa motar RK na fita a gidan da gudu. Dan dai-dai ya nufo sashen AA da nufin jin damuwarsa
saboda tunaninsa Oum na wajen mijinta kamar yanda tace masa zataje, sai dai yana gab da shiga sashen
ne Dr Ranjet yay kiransa cewar gafa Maanal an kawo asibiti. Shine ya juya a guje ya faɗa mota ya fice. Fitar
tasa dai-dai da shigowar motar Fawzan shima daga wajen aiki. Matarsa na a gefensa dan itama tana fita
aikin, motarta ta samu matsala ne ta barta a office tai kiransa ya biya ya ɗakkota suka nufo gida. Ganin
babban yaya ya sasu fitowa da sauri Fawzan na tambayar ko lafiya yaga Uncle Rafeeq ya fita a guje?.
“I don't know why! Na fito kiransa ne nima fa”.
“A da alama gaskiya babu lafiya, dan kamarma waya yake hankali tashe. Maybe asibitine suka kirashi
kasan Uncle da patient ɗin nan nashi. Amma lafiya kuwa?”.
“Auta ne babu lafiya”.
Ai Fawzan ma bai samu damar sake cewa komai ba suka nufi sashen AA su duka ukun. Sai dai Babban
Yaya na ƙoƙarin kiran layin family doctor ɗinsu a waya da shima ke aiki a KK HOSPITAL ɗin. Kafin doctor ya
iso su duka sun rufu a kansa hankalinsu duk a tashe. Kallo ɗaya zakaima wannan taron kasan AA ɗin ɗan
gatan dangi ne. Dan amaryar Abah ce kawai babu a wajen. Sai da matar babban yaya ta ɗaga waya tai
kiranta sannan sai gata ta iso. Kusan tare suka shigo da doctor. Itama dai macece ƙyaƙyƙyawa, tana da ɗan
jiki na ƙiba dan har tafi Oum ma. Sai dai Oum ta fita tsayi da haske dan ita fara ce kamar yanda Abah ke fari
tas. Kai hasalima suna kama sosai da Abah ɗin tabbacin auren zuminci ne a tsakaninsu. Hakama duk yaran
kama suke dasu, idan ka cire AA da yake da duhun fata sai dai kamanin fuskar Oum da Abah ɗin na tare da
shi shima.
Duk fitowa sukai aka bar Oum da Doctor yana duba shi. Duk da cikin faɗa yake mitar shi abarsa kar
doctor ɗin ya taɓasa. A barshi haka baya buƙatar kowane magani. Hawaye Oum take tana ƙoƙarin tausarsa
da shafa lallausar sumarsa daya tara take cin kuɗaɗe. Yayinda idanunta ke zubar da hawayen tausayin
yaron nata dan gaba ɗaya yanayinsa ya nuna alamomin tashin ciwonsa. Sam bata fatan hakan, bata son
abinda ya shuɗe suke murna ya dawo. Sun azabtu matuƙar azabtuwa da halin da AA ya shiga a shekarun
baya. Da ƙyar da addu'oi abubuwa suka sassauta. Sai tabon dake zuciyarsa da sun san har ya koma ga
ALLAH bazai warke ba kamar yanda suma nasun yake zaune daram. Sai kuma gashi ƙaddara na neman
sabunta abubuwa cike da ban al'ajabi da mamaki a duka ɓangarorin biyu.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
4️⃣5️⃣4️⃣5️⃣
______________
.........Sai da Doctor yay masa allurai masu matuƙar ƙarfi a cikin drip ɗin da aka saka masa har kala uku a
tare sannan barci ya ɗaukesa. Cikin kwantar ma su Oum da hankali yace musu karsu damu in sha ALLAHU
komai zaiyi normal. Dan dama akwai malaria ne a jikinsa sai kuma damuwa data saka jininsa haurawa
sama sosai, kuma da alama ya kwana biyu da damuwar a ransa amma ya cigaba da jigata kansa da sabgogi
kuma.
Hankalinsu ya ɗan kwanta jin abun da sauƙi, sai dai a ƙasan ran kowa maganar damuwar da yake ciki
ta damesu. Oum da Fawzan ne kawai da suka fahimci musabbabin damuwar zuciyarsu ke suya. Sai dai
basuce komai ba akai dan ko Babban yaya daya dawo Kano basu gaya masa zuwan Maanal gidan ba. Bayan
sun shiga sun gaggansa yana barci fuskar nan fayau sai dai a takure na rashin wal'wala tamkar yana ido
biyu. Yayinda Oum ke zare masa takalman ƙafarsa a hankali. Amsa Babban yaya dake kusa da ita yay ya
ajiye gefe, batare daya zare masa socks ɗin ba ya maida duvet ɗin ya rufe masa ƙafafun a yanda suke. Tie
ɗinsa da tuni ya sassautoshi da kansa dama Oum ta ƙarasa zarewa shima. Sai ƴar rigar saman long sleeve
shirt ɗinsa itama ta ɓalle botiran. Itama shirt ɗin ta rage botira uku na sama. Su dai sauran duk suna tsaye
suna kallonta, musamman Abah dake mata kallo cike da so da ƙaunarta. Matarsa dabance a cikin mata,
idan yace daban yana nufin daban ɗinne a cikin daban. Har yanzu bai iya samun abinda zai kwatanta
Fateeman sa da shi ba. Murmushi ya saki mai sanyi sakamakon haɗa ido da sukai da babban yaya da shima
ke murmushin, sai kuma duk suka janye ya ɗan kalla amaryarsa itama. Itama dai Oum ɗin take kallo
fuskarta da ɗan murmushi. Jiyay itama so da ƙaunarta na sake dasuwa a ransa. Kai shi kam ya gode ALLAH
da samun mata nagartattu na ƙwarai. Su ɗin aljannar duniyarsa ne.
Sallar magrib ce ta fita da su a sashen, amma Oum bata fitan ba sai ma umarni ta bama Fawzan akan ya
kawo mata kayan sallarta nan. Da girmamawa ya amsa mata yana fita. Yayinda Abah dake kallonta cikin
marairaice fuska ya furta, “Amma baiwar ALLAH tunda ɗan naki ya samu barci ai ƙyaji tausayina kizo ki bani
abinci”.
Ɓata fuska Oum tayi tana girgiza masa kai, “Ni dai gaskiya babu inda zanje nabar yarona a wannan
halin, in dai abinci ne ai na kammala Mamy ta shirya maka kuje ku ƙarata”.
Dad daya rasa ma abin cewa juyawa yay yana kallon Mamy, murmushi ta masa kawai da faɗin, “Kaima
kasan ba kulamu za'ai ba ɗan gwal babu lafiya. Mu rufama kammu asiri muje muci abinci dan nikam har
uku huɗu nake ganin mutane”.
Ɗan hararar wasa Oum tai musu tana murmushi. “Eh kwaji da gulmarku dai, dan kawai kanwa na
kawo sai na bar yarona a halin ciwo na koma kanku”.
Dariya sosai Abah ya kwashe da shi, sai kuma ya nunama Mamy hanya yana faɗin, “Kinga Kamilah muje
dan na kula itama uwar ɗan sai a hankali. Dama haka ɗan ya ɗakkomu a airport yana mana mazurai kamar
sabon dan doka da mai laifi.”
“Kwaji dai da shi, ba kulaku zamuyi ba sai mun warke”. Oum ta faɗa tana murmushi. Ficewa sukai
suma suna dariya. Dama tuni matan su Fawzan sun fice. Dai-dai nan Fawzan ɗin ya shigo da kayan sallar
Oum. Ajiye mata yay shima ya fita dan kar ya rasa jami'a.
__________★
Alhamdullah washe gari su dukansu jikin nasu da sauƙi. Musamman ma AA da Oum ke faman riritawa
kamar wani ƙwai. A yanzu haka tana zaune ne bakin gado kusa da shi tana bashi breakfast, sai faman mata
shagwaɓa yake ita ko tana lallaɓashi. Su Fawzan duk sun wuce aiki bayan sun shigo sun duba shi, hakama
Abah tunda ya shigo ya gansa ya fita dan yana da uziri. Mamy ma ta shigo ita da matar babban yaya. Sai
dai bata wani jimaba ta tafi tabar Oum da matar babban yayan dan ita bata aiki Bussines takeyi na kawo
kaya daga Chaina tana rabama ma'aikata. A yanzu haka ma da Oum ke faman lallaɓa shi tana zaune tana
faman musu dariya. Shi dai ba wani kulata yake ba dan tsakaninsa da matan yayyan nashi gaisuwar
girmamawace da mutuntawa. Amma ka gansa yana hira dasu ko wani wasa da dariya abune mai wahalar
gaske dan duk ƙanne suke a gunsa. Kai shifa mai ganin dariyarsa yanda ya kamata daga Oum sai ƴan
uwansa, musamman Fawzan ma da suke kamar wasu friends ba brothers kawai ba. Dan shi Fawzan akwai
barkwanci kamar Abah, saɓanin babban yaya da kusan halinsa ɗaya da AA ɗin.
“Oum Please ki bari haka zanyi amai”. AA yay maganar a hankali yana kwantar da kansa a kafaɗar Oum
ɗin cike da shagwaɓa. Murmushi itama tayi da kai hannu ta shafa kwantaccen gashin kumatunsa dake luf-
luf duk da yau ko gyara bai samu ba.
“To shike nan an barsa haka, ai kamayi ƙoƙari, kaida in baka da lafiya abinci ya zama maƙiyinka duk
sonka da shi. Yanzu sai mi kake buƙata?”.
Cikin lumshe idanu da sake maida muryarsa can ƙasa ya ce, “Barci”.
“To Alhamdullah karɓa wannan ruwan addu'an kasha, Mamy ce tayo maka”.
Ɗan jim yay yana kallon kofin, sai kuma ya ɗauke kansa da faɗin, “Oum ga naki ma ban shanye ba. Ki bari
saina gama da shi”.
“No naƙi wayon, shima kasha ai ba'asan inda za'a dace ba”.
Fuska yaso ɓatawa amma dai ya amsa yasa kofin a baki, bayan yayi bismillah ya shanye yana miƙa mata
kofin. “Yauwa ko kaifa ɗan albarka. Shike nan kwanta abinka ka huta nima bara naje na idan abinda ya rage
kafin ka tashi na nema maka lunch”.
Kansa kawai ya gyaɗa mata yana zamewa a gently ya kwanta. Dai-dai tana tattara kwanikan matar
babban yaya mai suna Saheeba na tayata. Knocking akai tare da sallama, Oum ta amsa tana bada izinin
shigowa dan su duka sun gane mai muryar. RK ne ya shigo cikin takunsa na nutsuwa, suna haɗa ido da AA
ya saki murmushi cikin tsokana ya furta, “Ayya my son ashe an kusa a gangara”.
Harararsa AA ɗin yay yana ɗauke idanunsa a kansa. Yayinda Oum ke dariya Saheeba na tayata. Sai da ya
kai zaune a bakin gadon ya gaida Oum, Saheeba ta gaisheshi da tambayarsa aiki ya amsa mata da kulawa
da tambayarta ina yara. Amsa ta bashi da cewar suna Kano basu dawo ba sai gobe da sassafe zasu taho da
mamanta. Ya jinjina mata kai kawai yana maida hankalinsa ga AA.
“Sorry my dear Son ai ban san abun haka ya kasance ba, sai ɗazun Fawzan ke sanar min ashe jiya ina
ƙoƙarin fita ana kirana na dubaka. ALLAH ya ƙara sauƙi yasa ya zama kaffara”.
Batare da AA ya buɗe idanunsa ba ya jinjina masa kai kawai. Dai-dai nan Oum ke faɗin, “Ai na kira
wayanka da dare ma bayan ya samu barci switch off, ALLAH yasa dai lafiya dan fitan naka a jiya duk sai da
ya dame mu”.
“Wlhy tashin hankali yasa har cajin wayar ya kare ban kula ba Aunty, dama saura kaɗan sanda nazo
nan jiya. Ƴarki ce babu lafiya sukai kirana gata an kawota asibiti, shine fa na tafi hankali tashe kin san ciwon
nata nada haɗari”.
A rikice Oum ta ce, “Wai kana nufin Maanal?”.
Da wani irin mugun sauri AA ya buɗe idanunsa a karo na farko tun shigowar RK ɗin. Idanunsa masu kaifi
da masifar haske kamar an watsa madara duk da halin ciwo da yake a ciki ya zubama bakin RK dake faɗin,
“Yes ita Aunty, wai daga wajen aiki ta koma kawai ta yanke jiki ta faɗi”.
“Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un yaya jikin nata?”. Oum ta faɗa tana kallon AA, suna haɗa ido yay wani
saurin lumshe nashi ya juya musu baya.
“Da sauƙi Alhmdllh, dan yanzu haka ma na barta tana barci. Shiyyasa nace bara nazo naga Autan ki
shima”.
Addu'a sosai Oum take ma Maanal, yayinda Saheeba ke amsawa zuciyarta na kai kawo da maimaita
sunan Maanal ɗin. Can dai taga zata gaza ta tattare kayan data kwashe tana faɗin, “Oum bari naje dasu a
wanke, ki huta zan masa lunch ɗin kawai”.
Kai Oum ta gyaɗa mata da sanya mata albarka. Daga haka ta fice da ɗan saurin da su Oum ɗin sam basu
lura ba. Kai tsaye sashen Mamy ta nufa, shima dai komai ya haɗu ga wani ƙamshi na musamman na tashi,
tana a falonta na biyu zaune da waya a hannunta alamar magana ta gama yi. Shigowar surukar tasu kuma
ɗiya a wajenta dan Saheeba ƴar yayarta ce uwa ɗaya uba ɗaya, zama a iya cewa itace ta haɗa aurenta da
Fadeel ɗin. Ɗan ɗagowa tai ta dubeta sai kuma ta maida ga wayar tata tana faɗin, “Saheeba lafiya kuwa?”.
Zama Saheeban tai kusa da ita gab fuskarta na nuna matuƙar ruɗani. “Mamy inafa lafiya. Kin san ina
can wajen Yaya Ajwaad kamar yanda kikace naje na zauna komai ayi a gabana, sai ga ƙaninta yazo shine
naji wata magana data ban mamaki.....” tsaf ta zayyane mata duka abinda aka tattauna a sashen AA ɗin.
Cikin matuƙar mamaki Mamy ta sake maimaita sunan. “Maanal kuma Saheeba?”.
“Tabbas Mamy sunan nan naji, duk da nasan akwai Maanal da yawa a duniya zuciyata ta kasa yarda ba
waccan yarinyar bace da Yaya Ajwaad ke ƙula fuci. Kin dai san makirci da munafuncin matar nan,
musamman idan kika duba ƙaninta ne yazo da labarin da mai sunan”.
Wani ƙayataccen murmushi Mamy ta saki tare da gyara zamanta na ƙasaita. “Lallai lokaci yayi ashe,
lokaci yayi da za'ai fito-na-fito na haƙiƙa tsakanina da Fateema akan ƳAƳANA. Saheeba! Ki ajiye wannan
batun zamuyisa daga baya, amma ki tabbatar kin bibiyeta idan har zataje asibiti duba yarinyar kuje tare.
Yanzu haka Abdull ne yay kirana zasuzo da matarsa da wata yarinya wai budurwar Ajwaad ɗin”.
Wani mugun faɗuwa gaban Saheeba yayi, har sai da ta waro idanunta waje sosai sannan ta furta,
“Budurwar Ajwaad Mamy? Ajwaad ke da budurwa kuma?”.
“To nima abin dai ya ban mamaki gaskiya. Amma dai mu jirasu suzo ɗin. Kisa ai abinci daga ɓangarenki
dan bana son ƴar tsirkun ta fahimci komai kin santa da bin ƙwaf. Yaya yasha ruwan rubutun?”.
Da ƙyar Saheeba da gaba ɗaya take a birkice ta amsa mata da, “Eh ya sha amma da ƙyar, dan sai da taita
lallaɓashi wai shi nata kawai zai sha”.
Ƙwafa Mamy tayi ranta na ƙuna, sai dai batace komai ba akan haka. Itama Saheeban saita miƙe dan
zuciyarta gaba ɗaya a ƙuntace take. Da haɗa hanya ta isa sashenta, kai tsaye bedroom ta afka tana rarumar
wayarta dake a saman mirror. Bata ko damu da tarin miss calls data samu ba ta shiga laluben layin
mahaifiyarta. Bugu biyu kuwa aka ɗaga. Ko gaisheta batai ba ta ce, “Mama akwai matsala fa, dole ki baro
Kano a yau ɗin nan gaskiya. Sannan Nuratu ta taho Kanon ne?”.
“Ke lafiya kuwa kike min maganganu a gwame? Mike faruwa ko yake shirin faruwa?”.
“Abubuwane da yawa Mama, amma yanzu ina son sanin ina Nuratu take?”.
“Nuratu tana Keffi kema kin san shiyyasa batazo bikin nan na Kano ba, zasuyi bikin birthday ɗin
ƙawarta”.
“Mtsoww wlhy wannan yarinyar gantalinta ya fara isata, tana can wataran zata ji an ɗaurama Ajwaad
aure tunda ita bazata nutsu ba”.
“Aure?”.
“Sosai ma kuwa Mama. Tunda ita wawuyar yarinya ce. Ita tasan wlhy badan faɗi tashin da muke ni da ke
akan batuntaba da tuni Mamy ta canjata da wata. Yanzu dai ki kirata idan taga da hali ta maza ta dawo
Abuja dan Ajwaad baida lafiya tun jiya ko aiki bai fita ba yau. Ga Abdull nan kuma shida ƴar iskar matarsa
ɗin nan mara kunya daya kawoma mutane cikin family bisa ra'ayinsa shi kaɗai wai zasuzo da wata
budurwar Ajwaad ɗin ce, kin san kuma Mamy ita kaɗai ke goyon bayan auren nan nasa dama. Ga kuma
wani batun a gefe da bamu gama tabbatar da shi ba”.
A matuƙar rikice Maman nata ta ce, “Na shiga uku ni Gambo, wane kuma batu ne haka Saheeba?”.
“Humm Mama ke dai kawai sai kin dawo”.
“Dawowa kam ta zama dole dan yanzun nan zan baro kano, yaranki ma sa biyo jirgi gobe dan ni ko
ban samu jirgin ba zan biyo mota kawai”.........✍️
Humm, tofa😌
✨ZAFAFAN DAI ✨
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?
id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
4️⃣6️⃣4️⃣6️⃣
______________
.......Tunda Saheeba ta fita a sashen taketa faman kai-kawo. Wani irin watsal-watsal zuciyarta ke faman
yimata. Tun tana jin zata iya daurewa harta kasa. Fitowa tai a sashen nata ta nufi sashen AA. Yanda ta shigo
fuuu sai kuma tai laƙwas ganin doctor da RK da Oum a ɗakin. A take ta gyara yanayinta ta ƙawata fuskarta
da murmushi. Sai kuma ta kalla Oum tana faɗin, “Na sake zuwa ne kar'a sakani a black list”.
Dariya Oum tayi itama, zuciyarta fes ta ce, “Kamar kin san na fara ayyana haka a raina, tun shigowar
safe ban sake ganinki duba mu ba”.
“To ALLAH ya baku haƙuri na ɗan tsaya kan masu aikin nan ne kin sansu da aikin algus idan basu
gadama ba. Yaya jikin naku?”.
Kallon AA Oum tayi da faɗin, “A jiki Alhamdullah”.
“To ALLAH ya ƙara afuwa”. Mamyn ta faɗa tana kallon AA itama da yay kamar bai ji shigowarta ba. Sai
lokacin ya ɗan ɗago idonsa ya dubeta, da Muryar nan tasa ƙasa-ƙasa ya ce, “Ina kwana”.
Wani irin motsawa zuciyar ta tai na takaici, amma sai ta danne ta sakar masa murmushi da amsawa
da, “Lafiya Lau, yaya jikin naka?”.
A hankali ya amsa da, “Alhamdullah”.
Gaisheta RK yayi shima da girmamawa. Itama ta amsa da kulawa tana tsokanarsa wai shi da ɗan nasa ba'a
san wazai riga wani aure ba. Ƴar dariya RK yay da kallon AA, sai kuma ya bata amsa da, “Karki damu Aunty
muna tafe, dan gara ni na farayi kafin a fara kirana Baba na zaure”.
“Ato ya kamata dai, dan zaman ya isa haka Uncle tururu ɗansa tuzuru”.
Dariya kawai RK yake cike da jin nauyi, dan yana matuƙar girmama matar da ƙaunarta kamar yanda yasan
ita da ƴar uwarsa suna ƙaunar juna. Dan in ba faɗa maka akai ba bazaka taɓa ɗauka kishiyoyi bane. Oum
ma dai dariya take kawai doctor na tayata, gogan kuwa yama lumshe idanunsa dan ruwa doctor ya sake
saka masa saboda sake samun ƙarfin jikinsa. Sallama tai musu ta juya ta fita tana sanarma Oum zataje
taɗan kwanta ta huta. Oum tai mata godiya...
Bayan fitarta Doctor dake kallon AA ya ce, “Ranka ya daɗe BP naka har yanzu yana a sama sosai, dole
zan ƙara maka allurar nan ka samu barci”.
A daƙile AA ya ce, “Bana buƙata doctor”.
“Ai dama ba dole sai kana buƙata ba ranka ya daɗe, jikinka ne ke buƙata. Dan rashin saukar tashi
matsalane gaskiya”.
Baki ya sake buɗewa a ƙufile zaiyi magana Oum ta katseshi. “Kaga doctor yimasa kaji, kai kuma idan ka
sake magana sai na cire maka kunne ɗaya”. Ta ƙare maganar tana hararar AA, baki ya tura gaba kamar wani
yaro, dan shi in har yana gaban Oum jinsa yake ɗan yaronsa har yanzu. Dariya RK yake yi, tare da faɗin,
“Taɓaran banza”. Hararar shi AA ɗin yayi, shima sai ya rama. Haka suke kamar wasu tom and jarry, sam AA
baya Uncle da RK, dan shi sunansa ma yake kira sai idan yaso yake cema Uncle ɗin. To sun tashi ne tamkar
friends, babu wani tazaran haihuwa a tsakaninsu sosai. Sai dai RK ne babba, amma idan yace ya girmesa to
yanzu zasu hau sama kuwa su faɗo dan shi AA ya tsani RK yace ya girmesa. A ganinsa girman da bai wuce
sati Uku ba har wani girma ne. Hanyar ƙofa RK ya nufa yana dariyarsa da faɗin, “Aunty kinga nayi nan
tunda ɗan naki ya samu lafiya har yana min rashin kunya ina matsayin babansa. Na tafi wajen aiki inda ake
son ganina bye”.
Cikin murmushi Oum ta ce, “Rafeeq kadai tasa min yaro dan kaga ba magana zai maka ba. Zuwa anjima
in sha ALLAHU zan kiraka na shigo ba duba Auta ta itama”.
“To ALLAH ya kaimu muna zuba idon ganinki, idan kuma ɗan shagwaɓarki bai bari ba mun yafe zan
kira a waya sai ku gaisa. Dan itama ina ƙyautata zaton zuwa anjima za'a sallameta, yau tunda safe take
mitar ita a sallametan”.
Dariya kawai Oum tayi tana mai girgiza kai, tasan Maanal da ƙiriniyarta, damma taga yanzu kura tayi
lafiya kamar ba Maanal ɗin ba.....
______________★
Jikin Maanal ma Alhamdullah, dan tama hana Shahidah sanarma su Ammie. Dama kuma Shahidahn
ma batai niyyar sanarma Ammie ɗin ba kamar yanda mijinta ya fargar da ita cewar tunda da sauki karsu
tayar musu da hankali.
Abinci Maanal ɗin keci RK ya shigo, sai da ya gaisa da su Shahidah kafin ya maida hankalinsa a kanta.
Cikin tsokana ya ce, “Madam ba tayi”. Ai baima gama rufe baki ba ta miƙa masa plate ɗin. Mi mijin
Shahidah zasuyi ba dariya ba. Uncle Sadeeq ya ce, “Doctor kai baka san dama neman kai take da abincin
ba, an turketane tana ci dan dole”.
Fuskar RK da murmushi ya ce, “Ai naga alama Babban yaya. Irin wannan bani da sauri haka. Ni dai dan
ALLAH kici abinci ki ɗan ƙara kumari”.
Hararar RK ɗin tayi, sai kuma ta tura baki gaba cike da shagwaɓa. Zama Shahidah tai kusa da ita cikin
lallashi ta ce, “Kinga ƙyalesu Auta kinji, bari ma na baki da kaina”. Haka ta amsa ta cigaba da bata cike da
kulawa da so. Sai RK ya samu kansa da shagala a kallonsu. Shi kaɗai yasan yanda yake jim ƙaunar yarinyar
nan a ransa. Komai tayi birgesa yake. Yasan hakan daga ALLAH ne. Dan yana jin feeling akanta irin wanda
zai rantse bai gaɓa ji ga sauran ƴamata ba. Kodan bai taɓa yin budurwa bane oho. Sam shi ada matsoracin
mata ne, babu ruwansa da harkarsu, badan bai cika namiji bane, kawai dai karatunsa na likitanci daya
ƙwallafa rai da aikin nan sun kwashe mafi yawan lokacinsa na rayuwa. Idan ka cire ibada da yake matuƙar
bata hakkinta. Shifa ko irin ƴar soyayyar ƙuruciyar nan baiyi ba. Kuma a turai aka haifesa anan ya girma yay
dukkanin karatittukansa. Gaba ɗaya bai wuce shekara huɗu da dawowa Nigeria gaba ɗaya ba. Amma
ALLAH bai ɗora masa damuwa da mata ba. Shiyyasa shi da kansa yake sake yarda da son Maanal yake bana
wasa ba. Hakama ƴan uwansa kowa murna yake da batun Maanal dan sun tabbatar da gaske son nata yake
tunda shidai ba'a taba kamashi da case na mace ba.
Sosai Maanal ta matsa ita sai an sallameta ta warke. Amma Dr Ranjet ya dinga lallaɓata akan tayi
haƙuri zuwa gobe. Dole badan taso ba ta haƙuran...
______________★
Kusan ƙarfe uku na yamma Abdul da amaryarsa Yaseerah sai Huznah suka iso katafaren family house
ɗin na Ambassador Aliyu Darma. Dan a gidan su Yaseerah Huznah ta kwana. Daga Mawaad Company can
ta wuce ranta a ɓace tana hawayen abinda AA ya mata. Shine Yaseerah taita lallashinta da tabbatar mata a
yau zasuzo Darma's house. Hakan kuwa akai, tun a daren take lallaɓa Abdull akan suje har ya amice. Sai
kuma gasu sun iso yanzu.
Sun sami tarba daga Mamy, ƙyaƙyƙyawar mace ƴar ƙwalisa data gama tafiya da zuciyar Huznah. Kai
tun kafin ma Mamyn Darma's house ya gama tafiya da Huznah. Ta gama sallamawa da jinjina kuɗi irin na
gidan su AA ɗin. Ta kuma yarda kuɗin ma hawa-hawane. Tasan mahaifinta nada kuɗi, tunda suka tashi suke
jin ana sakashi a jerin masu kuɗin jihar Kaduna, kai bama Kaduna kawai ba a dattawan arewa masu kuɗi
za'a iya sako mahaifinsu. Sai dai kuma Baba ma fa da babansa. Ta shaida hakan a yau kuma ta aminta.
Yanda take ta faman sinne kai da kaffa-kaffa da komai sai ya baka mamaki, ko gaishe da Mamy sai da
ta duƙa har ƙasa. Sai Mamyn ce dake binta da kallo ta kamata ta tadata ta zaunar a kujera. Still dai Huznah
ta kasa kallonta. Ita ma dai Yaseerah bata da wata sakewa, dan dangin mijin nata ƙalilan ke sonta, duk da
dai ita Mamyn na sonta. Kawai dai dan Abdull ɗin ya dage sai ita ne yasa suka ƙyalesa. Hakan yasa su biyun
duk suka nutsu, sai Mamy da Abdull ne ke hira. A haka Saheeba ta shigo suka gaisa tare da saka masu
aikinta jere abincin da Mamyn tace tayo a sashenta na tarbar baƙin. Saheeba dai ta danne sun gaisa da su
Yaseerah, sai dai hankalinta nakan duk motsin Huznah ne. Bisa umarnin Mamy sukaje d/table, anan ɗin ma
dai Huznah bata sake ba ita adole mai kunya. Ita dai Mamy sai kallonta take tana murmushi. Dan haka
kawai kuma sai taji son yarinyar a ranta saboda kunyarta da nutsuwa gefe ga ta ƙyaƙyƙyawa. Dan duk
ƙyawun Nuratu da da take kallo dai-dai da AA sai taga ai Huznah ta takata ta shanye. Dama dai a ƴan
kwanakin nan wasu abubuwa na Nuratu sunsa ta fara shakkar haɗa aurenta da AA ɗin, amma bata fito ta
faɗama kowa ba. To tana ganin yarinyar nan itace zata zama raba gardama. Dan kodai ya aurenta ita kaɗai
kota sakashi ya haɗa da Nuratun su biyu a masa auren gata auren huce takaice auren da tasan zai baƙanta
ran Oum fiye da auren su Fawzan.
Bayan sun kammala cin abincin ta umarcesu da suzo su duba AA. Abdull ne ya tambayeta “Baida lafiya
ne Uncle AA ɗin Grandma?” (dan haka yake kiranta kasancewarta ƙanwar kakarsa uwa ɗaya uba ɗaya).
Amsa ta bashi da “Eh son, yau ko aiki ma bai fita ba yana kwance”.
Gaba ɗaya ji Huznah tayi hankalinta ya tashi, dan har fuskarta ta nuna hakan ɓaro-ɓaro, amma dai ta
daure batai magana ba. Mamy dai na lure da ita. Hakama Saheeba dake jin kamar ta shaƙo Huznah ɗin. Sai
faman tsine mata take a zuciya. Sashen Oum suka fara zuwa, Oum ta tarbesu da kulawa kamar yanda ta
saba ma ƴan uwan Mamyn, dan haka cikin girmamawa Abdull ya gaisheta, hakama Yaseerah da Huznah
data kusa zubewa a tsaye da mamaki tana satar kallon Oum. Tabbas bata manceta ba, itace ta gani a gidan
Shahidah tare da namiji mai kama da AA ɗinta. Rashin sanin alaƙarsu da su Maanal ɗin kuma yasa har
yanzu bata sanarma mahaifiyarta ba, gefe kuma ta ɗan shiga ruɗani, shin tsakanin Mamy ɗin da matar
wacece mahaifiyar AA ɗin? A dai kamanni yafi tsananin kama da Oum, shin yaya take ne?. Da ƙyar ta iya
dannewa dai suka baro sashen bayan Oum ta cika su da abin arziƙi, sai dai fa da alama ita Oum bata gane
Huznah ba. Koda yake a gidan Shahidah da suka haɗu ita bawani ta maida hankali a kanta bane lokacin.
Daga nan sashen AA suka nufa kamar yanda Mamy ta sanarma Oum cewar zata kaisu su dubashi. Wani
irin lumshe idanu Huznah tai lokacin da suka shigo main falo ɗin sashen da wani irin ƙamshi mai daɗi ke
tashi. Suna isowa falo na biyu taji zuciyarta na wani kalar tsaitsinkewa saboda haɗuwarsa. Falo kamar bana
tuzuru mara mata ba. Anan Abdul ya dogare, fuskarsa da murmushi ya ce, “Grandma bari mu dakata anan
a masa magana idan zai iya sakkowa mu gaisa. In ba hakaba bara na haura ni kaɗai sai na dubashi kin san
Uncle baya son wargi bakamar Uncle Fawzan ba”.
Murmushi Mamy tayi, dan itama dai tasan maganar Abdull ɗin gaskiya ne. Dan in har ta hau da su
Yaseerah sai yaji haushi. Su Saheeba ma dake matsayin matan yayyansa kuma ƴan uwansa na ƙut sosai
yake tujara idan suka shiga masa koda falon sama ne balle. Yanzu haka ko ɗazun tana jin yanama Fadeel
mitan shi matansu su daina shigo masa har bedroom.
Mamy ce ta haura saman da kanta. Dai-dai AA daya farka daga barcin da Doctor ya sakashi dole ya
fito wanka. Knocking ƙofar da akai ne ya sashi yamutsa fuska cikin yanayin mara lafiya, muryar shi ƙasa-
ƙasa da kamar baya son buɗe baki ya furta, “Ina zuwa”. Daga haka ya ajiye towel ɗin hannunsa da yake
goge sumarsa da ruwa ya jiƙa saboda ciwon da kansa ke masa har yanzu kaɗan-kaɗan ya sakarma kansa
ruwan. Boxer ya saka tare da cire bathrobe ɗin ya saka jallabiya sannan ya nufi ƙofar dan duk zatonsa Oum
ce. A hankali ya buɗe ƙofar, cikin ɗan shagwaɓa ya furta, “Oum sai yanzu, ni nayi fush.......”
Kasa ƙarasawa yay saboda yin tozali da Mamy ba Oum ba. Ta koyi kicin-kicin da fuska tana masa wani irin
kallo, kansa ya duƙar ƙasa yana mai haɗiye busashen yawu ya furta, “Am sorry, nazata Oum ce”.
“Humm” kawai ta furta batare data kula zancensa ba ta juya tana faɗin, “Kasameni a ƙasa baƙi zasu
gaisheka”.
Kallo ya bita da shi, harta fara taka stairs case ɗin. Kaɗan ya lumshe idanunsa ya buɗe, sai kuma ya ɗan
furzar da iska ya koma cikin ɗakin..........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
4️⃣7️⃣4️⃣7️⃣
______________
........Fin mintuna goma bayan sakkowar Mamy sannan ya sakko. Duk da sanye yake da slippers masu
taushi hakan bai hana bayyanar tahowarsa ba. Ga wani mayataccen ƙamshin turarensa mai ratsa zuciya na
rige-rigen shiga hancinansu tun kan su fara ganinsa.
Ai tuni zuciyar Huznah ta fara gudu a ƙirjinta, yayinda take satar kallon hanyar ƙofar upstairs ɗin ta
gefen ido. Bayan wasu ƴan sakanni ƙofar ta buɗe slowly, ya bayyana garesu. Sanye yake da wando da riga
duk baƙaƙe masu kamar kayan sanyin nan dan harda hula a bayan rigar, sai dai bai saka ba ya saketa a
dokin wuyansa ta kwanta. Sam babu wasa ko alamarsa a saman fuskarsa datai wani irin fayau ya ƙara
haske. AA ba fari bane, amma yanada hasken fata da ko'a cikin baƙaƙen irin baƙin nan ne mai matuƙar
ƙyau da shining ga wani glowing da yake tamkar jinin mutanen ƙasar Labanon. Yanada hanci dayay dai-dai
da tsarin tsaka-tsakin fuskarsa daba doguwa can ba, ba kuma faffaɗa ba. Ga shi da cikar gashin gira dana
ido da ko wata macen bazata nuna masa eyelashes ba. Kwantaccen gashin sajensa daya zagaye har
matsaikaitan lips ɗinsa pink shine yafi komai sake ƙawatashi. Kamar koda yaushe idanunsa manne da
eyeglasses ɗinsa fari ƙal da kamar ba'a amfani da shi na ƙara ƙarfin gani. Yanda oily idanun suka sake wani
fita tar-tar kamar an watsa ruwan madara sabon tatsa dole kaji wani iri idan ya kalleka da su. Gashi dogo
masha ALLAH.
Tunda ya gama sakkowa kallon kowa baiyi a cikinsu ba. Sai takowa da yay a hankali zuwa cikin falon
sosai. A kujerar farko dake bangon daya fito ya zauna kawai, sai a lokacin ya ɗan dubi Abdull dake gaishesa
cike da girmamawa. Cikin yanayin ɗan zuba masa ido batare daya amsa gaisuwar ba ya ce, “Ango ne a
gidan namu”.
Murmushi Abdull ya saki mai ƙayatarwa tare da duƙar da kansa yana sosa ƙeya. Cike da jin nauyi ya sake
gaida AA ɗin. AA ya girmi Abdull sosai, dan shi a yanzu bazai wuce 26+ ba gaskiya. Kawai dai an masa
auren gata ne. Sai yanzu AA ɗin ya amsashi da tambayarsa iyalin. Sake duƙar da kai Abdull yay da faɗin, “Ai
Uncle gata nan ma tare mukazo dubaka”.
Batare da AA ya kalli inda Abdull ɗin ya nuna ba ya furta, “Oh Masha ALLAH, Thanks”.
Gaisheshi Yaseerah ta shiga yi da tambayarsa yaya jiki, ya amsa mata a taƙaice still dai bai kalleta ba.
Dan kowa yasan wannan kam ba ɗabi'arsa bace kallon mata ko'a sanda yake a ganiyar samartakar balaga
balle yanzu da wasu dalilai suka saka shi sake kame kansa ga komai, dan AA akwai tsantsar kame girma, ko
wanda suka girmesa sukanga ya cika musu guri balle wanda ya girma. Sai a lokacin Huznah data kasa
numfashi mai ƙarfi ta fara gaisheshi itama, AA akwai iya haddace muryan mutane da riƙeta idan yaso, dan
haka ya ɗan kalla sashen da suke a karo na farko, a mamakinsa kuwa wadda yay tsammanin ce. Wato
budurwar yarinyar nan mai shegen naci da iyayi data takurama rayuwarsa a kwanakin nan. Ƙoƙarin
janyewa yake suka haɗa ido da Mamy data kafesa da nata idanun. Sai kawai ya kautar da kan nasa cike da
basarwa. Haka kawai Mamy ta saki murmushi. Dan ta tabbatar da abinda take son tabbatarwar, da gaske
AA ɗin yasan Huznah ba ƙarya sukai masa ba. Saheeba ma dai sai faman raba idanu take a tsakanin Mamy
da AA da Huznah. Itama kuma taga reaction ɗin AA ɗin a sanda Huznah tayi magana. Tuni hankalinta ya
ƙara tashi, wani kalar tsanar Huznah na ratsa zuciyarta.
AA ne daya miƙe ya katsema kowa tunaninsa. Dan hankalinsa kwance ya nufi ƙofa, sai da ya kama
handle ɗin batare da ya juyo ba ya furta, “Abdull thanks you ALLAH ya baku zaman lafiya”. Daga haka ya
shige tare da maido ƙofar ya rufe. Kusan lokaci ɗaya Yaseerah da Huznah suka saki ajiyar zuciya. Dan ita
kanta Yaseerah ɗin sai yau da take ganin AA ɗin da ƙyau. Rayawa take a ranta (Ashe haka guy ɗin ya haɗu,
ya subahannallah mutum kamar shi ya zana kansa da ƙyawu. Ga aji ga kwarjini. Wannan shine irin mijin da
take fatanma kanta, dan Abdull yana da ɗan irin qualities ɗin kaɗan shiyyasa ta aminta da shi. Ashe ga inda
ake mazan nan na gaskiya. Ya ALLAH gaba ɗaya an wargaza mata dukkan lissafinta. Sai a yanzu ta sake
tantance abinda ya haukatar da Huznah ashe). A ɓangaren Huznah ma sambatu kawai take zubawa a
zuciya. Wani irin ƙyau da kwarjini AA ɗin ya sake mata. ALLAH badan kar ace tayi ƙarya ba daya kalleta da
wannan idanun nasa mai kamar an watsa madara da oil a ciki kaɗan ya rage ta suma. Kai dole dole ne ma
ta mallaki mutumin nan, idan ba hakaba zata iya rasa ranta.
Da ire-iren wannan tunanin suka koma sashen Mamy, kasancewar lokacin sallar Asr yayi Abdull ya wuce
massallaci. Su kuma Mamy ta haura dasu sama a ɗaya daga cikin bedrooms ɗin ta tace suyi salla. Ita kuma
ta nufi nata.....
____________★
Senator Bukar dai yaje Kebbi cikin garin Giro, bai kuma sha wahalar samun ainahin gidan kakannin su
Maanal ba. Dan gidane sananne a cikin garin. Alhamdullah kuma ya samu tarba irin wadda bai mayi zato
ba. Dan cike da farin ciki suka dawo garin Abuja dama jirgi yabi shi da Rabilu da Oler. Yanda yake ta famar
washe baki da zumuɗi ya saka uwargidansa a tashin hankali, dan ta tabbatar ya samo abinda yake so.
Batace da shi komai ba yay shiri ya wuce gidan matarsa ta biyu dan yau itace da shi...
Itama dai a yau ya zazzage mata batun ƙarin aurensa, a ɓangarenta mace ce mara haƙuri da iya shanye
abu, dan haka tun a daren sukaci uwar watsi ƙarshe kowa a part ɗinsa yay barci. Dan ya tabbatar mata
akan Maanal fa zai iya saita mata hanya ne shi ba damuwarsa bane. Dole taja bakinta ta kulle dan tasan
kaɗan daga abinda zai iya aikatawar kuwa.....
_____________★
Yanayin da take jin jikinta Alhmdllh yasa ta ce Shahidah taje gida kawai ta huta yau zata kwana da
nurse. Da har Shahidah ɗin taƙi Dr Ranjet yace karta damu taje ɗin. Dama asibitin bawai suna barin masu
jiyya bane ba ai kawai dai sune oga ke bari. Zuwa yanzu Shahidah ta fahimci asibitin nan mallakin RK ne.
Duk da yanata dojewa bai son su sani. Dan haka koda Dr Ranjet ya ce ogan ta fahimci RK ɗin yake nufi.
Mijinta ne yazo ya ɗauketa, basu tafi ba sai da ta tabbatar ta mata duk abinda take buƙata duk da jikin
nata Alhmdllh sannan. Bayan tafiyar tasu Maanal ɗin na zaune tana karatun novel ɗin data ɗauka na AA
ranar a office ɗinsa, dan yau ta matsama Shahidah ta kawo mata shi asibitin tare da glass ɗinta. Sosai take
zumuɗin karatun book ɗin saboda labarinsa da aka bata. Tayi matuƙar zurfi a karatun dan tana jin daɗinsa,
bata damu da shigewar lokaci ba dan kusan 11 ma da rabi. Sai can ƙasan zuciyarta dake ɗan kawo mata
tunanin ina RK, rabonta da shi tun safe da ya shigo ya dubata a gaggauce ya fice. Tana son tambaya tana
tsoron kar Didi tai mata wata fassara daban dan haka taja bakinta tayi shiru. Sai dai lokaci-lokaci yana zuwa
mata a rai.
Kaɗan-kaɗan wani irin daddaɗan ƙamshin turare ke shigo mata hanci, tun tana fuskewa da cigaba da
karatunta har dai yanda turaren ke sake ƙarfi a ɗakin ya addabeta. Cikin nutsuwarta da rashin rawar kai ta
ɗago idanunta kaɗan tana bin ɗakin da kallo, dai-dai saukarsu inda ƙofa take ƙirjinta yay wani irin motsawa
alamar zuciyarta tayi zallo. Sosai ta zuba masa ido tana masa kallo irin na mamaki ko ruɗani zamuce oho.
Sai dai fuskarta a dake babu alamar wani shock a kanta. Sai ma janye idanun tai a slowly ta maida ga
littafin kamar bataga komai ba.
Gently shima ya lumshe nasa oily idanun da ke a ɗan kumbure kaɗan da kuma ɗan sirkin ja a cikinsu
dan har yanzu basu komai dai-dai ba saboda ciwon kai yaƙi barinsa. Sai dai da ɗan haskensu fiye da jiya da
yake a halin ciwo sosai. Sake buɗesu yay a kanta yana mata wani irin kallo mai wahalar fassara. Fin
mintuna biyar suna a haka baka jin komai a ɗakin sai sanyin ac da aka saka mata kaɗan daya gauraya da
ƙamshin mayataccen turarensa mai kashe garkuwar jiki. Gaba ɗaya kallon ya gundiri Maanal, dan jinsa take
har cikin ɓargon jikinta da magudanan jini. Tuni ta daina karatun kallon rubutun kawai take, sai dai fuskarta
ta sake tsukewa.
A cike da ƙasaita ya miƙe daga jinginar da yay a jikin ƙofar hannayensa duka zube cikin aljihun farin
jeans ɗin sa, daga sama ma baƙar rigace mai hi neck data ɗame masa murɗaɗɗan jikinsa, sai dai ya kawo
jacket mai ƙyau baƙa da adon fari kaɗan a jikinta ya ɗaura. Kasancewar zip ɗin gabanta a buɗe yake har
ƙasa ne ya bayyana rigar cikin da faffaɗan ƙirjinsa zuwa lafaffen cikinsa. Yanda yake takowa takalman
ƙafarsa masu ƙyau da ɗaukar hankali na bada ƙara haka zuciyarta ke motsawa a ƙirjinta da ƙarfi. Cike da
izza ya tura kujerar gaban gadon gab da gadon sosai da ƙafa, kafin ya matsa gab da gadon har Maanal najin
tamkar zai faɗo mata akai sannan ya kai zaune. Yanda ya ɗan rankwafo a kanta sanda zai kai zaunen yasa
hucin numfashinsa dakar fuskarta, yayinda ƙamshinsa ya gama mamaye illahirin iskar da take shaƙa. Dole
ta ambaci sunan ALLAH a zuciyarta.
Anan ɗin ma zaman ƙasaitar yayi, dan ya wani harɗe ƙafafu ɗaya kan ɗaya tare da kwantar da bayansa a
jikin kujerar hannayensa duk biyu dafe da hannuwan kujerar. A har yanzu ɗin ma idanun nasa na'a kanta
ne sai faman lumshesu yake da buɗewa daga cikin fari tas ɗin gilashinsa dake sake ƙawata masa fuska.
Rumtse idanu Maanal tayi tana mai danne dukkan abinda ke yunƙuro mata. Batare data sake ko kallon
sashen da yake ba a kausashe, a kuma tsiwace ta furta, “What are you looking for here?”.
Maimakon bata amsar data buƙata sai kawai ya zuba ma lips ɗinta idanunsa har adams apple ɗinsa na
ɗan motsawa a maƙoshinsa. Wani irin takaici ne ya sake ratsa Maanal. Tai wani irin juyowa da rinannun
idanunta da suka juye lokaci guda ta saukesu a kansa. Slowly shima yaja nashi dake kallon lips ɗinta ya
daidaitasu a cikin natan. Kallon cikin tsakkiyar idanu sukema juna. A hankali a hankali na Maanal suka fara
ƙyalli alamar taruwar hawaye. Wani ɗan iskan murmushin gefen baki ya saki yana sassauta girman
idanunsa dake cikin nata. Tamkar wanda akama dole ya motsa lips da Muryar nan nasa can ƙasa-ƙasa
kamar abin dole ya furta, “Because you need me”.
“Never! Har abada kai baka cikin abinda rayuwata take buƙata Ajwaad”.
Wani ɗan killer Smile ya saki yana mai janye idanunsa gefe, fin sakan biyar sannan ya sake juyo da
idanun nasa a kanta. “Really! You don't need me in your life?”.
“Kana tantamar hakan ne?”.
Ta faɗa a zafafe.
“Sosai ma kuwa? Inda har baƙya buƙatata in you life kuma da baki cigaba da ajiye wannan ba”. Ya ƙare
maganar yana buɗe tafin hannunsa wani sliver agogo ya bayyana. Kallon agogon take zuciyarta na bugawa
da ƙarfi a cikin ƙirjinta, agogonta ne fa, agogon da ta saka a randa zasuje Zaria ita da Ammie da Yaya
Yazeed da Amrah. Tabbas tasan ta ciresa a hannunta, daga haka bata sake tuna ina yake ba. Kai hankalinta
ma sam bai kai garesa ba sakamakon haɗuwa da RK da tai acan ya harmutso ta.....
“Hyy”.
Ya katse mata tunani cike da son tunzurata. Harararsa kuwa tayi ta ɗauke kanta gefe batare da ta ce
komai ba. Murmushin sake samun nasara ya saki kaɗan yana wani ƙanƙance idanunsa a kanta.
“Wannan pretending ɗin naki ya isa haka. K Bestyn AA ce har yanzu, ko ki yarda ko karki yarda
idanunki na nuna hakan ga kowa......”
Wani irin wurgar da littafin hannunta tayi, a bazata kawai ta ganta a gabansa ta dirgo daga gadon. Wani
irin lumshe idanu yay ya sake buɗewa sakamakon shigar ƙamshinta mai daɗi cikin hancinsa. So yana
matuƙar son traditional perfumes, zai iya cewa ma itace ta koya masa amfani da su ita da Oum..........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
4️⃣8️⃣4️⃣8️⃣
______________
........Akan ƙyawawan ƙafafunta da ƙumbunan ke a gyare fes-fes suna ƙyalli ya saukesu. Kafin ya tafi da
kallonsa har saman baƙin wandon data saka irin mai manne jikin nan, yana gab da gwiwarta rigar asibitin
ta bayyana, itace har zuwa sama fara da ɗigo-ɗigon jaa, tsabar neman magana da salon iskanci ya wani
sauke a saman ƙirjinta ya kafe wajen da ido tare da ɗan datse lips ɗinsa. Da sauri ta koma saman gadon
taja bargo ta lulluɓe jikinta gaba ɗaya tana furta, “ALLAH ya isa wlhy da mun kallon da musulunci ya
haramta”.
Murmushi yay mai fidda ɗan sauti sai dai sam haƙwaransa basu bayyana ba. Sai kuma ya taɓe bakinsa
cikin halin ko in kula ya furta, “Daga baya kenan. Idan kin manta bari na tuna miki na san komai A to Z tun
kan ki zama abin kallo. Ko kin manta wannan hannun ya miki wanka, ya wanke miki pupu, ya share miki
majina, ya wanke miki pants, ya wanke miki blood na period. Ya.....”
“That's enough malam. Kuma ka bar ɗakin nan tun kafin na maka ihu wlhy.”
Murmushi ya sake yi yana taɓe baki da wani ɗan ɗage gira. Babu alamar zai ma motsa balle yayi abinda
tace ɗin. Saima cikin tsareta da idanunsa da suka kaɗe ga jijiyoyin kansa duk sun sake fitowa. Muryarsa can
ƙasa ya ce, “Ke baki gajiya da faɗa? Why are you being stubborn ne?”.
Harara ta balla masa da faɗin, “Anyi faɗan da taurin kan, in baka son a maka ka fita rayuwata mana”.
Sai da ya ɗan lumshe idanu ya buɗe akanta. Yanda yake mata wani shegen kallo tamkar idanunsa zasu
narke a kanta ya saka tsigar jikinta tashi, kauda kanta tayi gefe da sauri, shi kuma ya ɗan ciza lips ɗinsa
yana wani jan numfashi a hankali.
“Nima ki fita tawa rayuwan mana. Kinbi duk kin hanani sukuni, kin hanani aure, kin sa duk nabi na tsani
yaran mutane babu hujja”.
Ai bama tasan sanda ta wara manyan idanunta a kansa ba tana harararsa, rasa abin cewa yasata faɗin,
“ALLAH zai saka min sharrin nan da ka min”. Sai kuma ta sake sakkowa a gadon tare da fisgan hijjab ɗin
sallarta ta saka. Ƙofa ta nufa fuuu dan gara dai ta bar masa ɗakin kawai sai yaci kansa yasha baƙin ruwa. Sai
dai me ƙofar gam alamar saida ya rufe sannan. Ranta ne ya sake ɓaci, har takai hannu zata bubbuga sai
kuma ta fasa saboda tunawa a asibiti suke kada ta shiga hakkin sauran majiyata. Dawowa tai inda yake
cikin da tsantsar masifa da tsiwa ta balbalesa da masifa.
Yanzu kam gaba ɗaya dauriyarsa ƙwacewa tai, dole ya kai hannu saman kansa dake wani irin sara masa
da masifar ƙarfi ya dafe, dama tuni dauriya kawai yake yi, shi kaɗai yasan azabar da kan nan ke masa, dan
shi dama a ciwonsa ciwon kai yafi yawa. Sam masifa ta rufema Maanal ido, sai cigaba da zazzaga masa
take, “Please Besty my head ki daina min ihu”.
“Anƙi a daina, tunda baka so ka fita mana, waya kawo ka nan ɗin?”.
“Ya ALLAH” ya faɗa da wata sassanyar murya yana kai ɗayan hannun ma ya tallafe kan gaba ɗaya. Dan
da gaske ji yake kamar kwalwar ciki zata zazzago.
A karo na farko gaban Maanal ya faɗi, dan yanda ya kira sunan ALLAH ɗin da tallafe kan sai kuma
hankalinta ya tashi. A hankali ta fara haɗiye masifar tata tana kallonsa. Yayinda shi kuma ke cigaba da
jujuya kansa a cikin hannayensa yana cigaba da kiran sunan ALLAH, sai kuma ya koma faɗin, “Please Besty
my head, kaina Besty zai fashe ki riƙe min, dan ALLAH ki riƙe min”.
Ai tsabar yanda jikin Maanal ke rawa batama san takai hannunta saman nashi ba, ta ture ta maye
gurbinsa da nata tare da duƙawa a gabansa tana leƙen fuskarsa da faɗin, “Na shiga uku mike damunka?
Miya samu kan naka? Ka tashi muje wajen likita na roƙeka”. Sai hawaye sharrr.
Bai iya ya motsa ba, sai hannunta dake a saman kan nasa da sanyinsa ke wani ratsashi ya sake
dannewa da nasa da ƙyau. Yayinda ita kuma zafin kan da yanda jijiyoyin ke harbawa ke ratsata. Matuƙar
firgici ta shiga, dan tun tana hawaye har kukan nata ya fara fidda sauti. Da ƙyar ya ɗaga idanunsa da suka
gama kaɗewa ya kalleta, cikin motsa lips ɗin da ƙyar tare da ɗan jujjuya kai ya ce, “Stop crying, bafa da
yawa bane”.
Kukan ta sake fashewa da shi da faɗin, “Hakanne bada yawa ba, kaga yanda idonka yay ja kanka yayi
zafi? Nidai ka bari naje na kira maka Rafeeq...” tai maganar tana ƙoƙarin miƙewa da son cire hannunta dake
a saman goshinsa. Da sauri ya riƙo ɗayan hannun nata yana jujjuya kai, sai kuma miya tuna ya saki hannun
yana faɗin, “Am sorry”. Itama kamar wadda ya fargar sai tai saurin janye ɗayan dake a saman kansan, ta
ɗan ja jikinta baya. Murmushi ya ɗan yi, sai kuma ya miƙe still dai hannunsa dafe da kan nasa ya ɗan raɓa
ta gefenta ya zauna a gadon jiyyarta yana faɗin, “Help me naɗan kwanta anan ko zai sauka”.
Batace komai ba ta matsa masa, kwanciyar yay rigingine ya lumshe idanunsa hannunsa dafe da kan
nasa. Tun tana kallonsa daga tsayen harta kai zaune a kujerar daya tashi dan itama sai taji kawai tana wani
irin jin jiri, yayinda baya data shuɗe ke son maimaita mata kanta a zuciyarta. Haka suke ita da shi, da
wahala ɗaya ya kwanta ciwo ɗayan bai kwanta ba shima. In ko ba haka ba dukkan hidimar mai ciwo ɗayan
ne zai yi. Zata iya cewa fara kaiwar AA ɗin lokacin balaga ne yasa Oum ta fara saka idanu akan al'amuransu,
harma takan kasance tare da su batare data barsu keɓewa su biyu kawai ba. Sai dai duk da haka ƙaddara
bata barsu ba. (Ƙaddarah!) Zuciyarta ta maimaita kalmar da amsa kuwwa. Rimtse idanunta tayi da masifar
ƙarfi sai kuma Zuciyarta ta fara zafi, (Eh tabbas batace ƙaddara kawai ba, harda ganganci da son zuciya
daga AA ɗin, eh son zuciya, koma tace zalunci......) Hawaye suka shiga solalo mata masu shegen zafi. Zaram
ta miƙe daga gaban nashi ta nufi window jikinta na rawa. Yanda ta tura kujerar da ƙarfi harta faɗi ya sanya
AA buɗe idanunsa da ƙyar. Kallo ya bita da shi, sai kuma yay saurin rumtsewa jin abinda take faɗa cikin
kuka mai tsanani daga inda take....
“Dan ALLAH ka tafi, ka tafi nesa dani bana son ganinka. Ka barni naci gaba da rayuwata cikin salama.
Namaka alkawarin zan bar aiki a companyn ka. Bana son tuna komai, bana so, ka daina kusantoni, ka
barni, dan ALLAH ka barni na roƙe ka Ajwaad....”
“Besty!” ya faɗa a can ƙasan maƙoshi daga bayanta batare data san sanda ya baro gadon yazo wajen
ba. Kuka ta sake fashewa da shi tare da durƙushewa a wajen, “Ka daina kirana da wannan sunan, ka tafi
kawai, ka tafi Ajwaad....”
“Zan tafi, amma ki saurareni kona minti biyar ne”.
“Bazan iya ba, baka da sauran space na lokacina, sam baka da shi.” sai kuma ta juyo tana daga
durƙushen ta haɗe hannayenta waje guda alamar roƙo🙏. “Na roƙeka ka barni Ajwaad. Ka yi nesa dani, bana
buƙatar jin komai daga gareka, bazan iya baka komai ƙanƙantar lokacina ba a yanzu”.
Da ƙyar ya iya haɗiye abinda ya riƙe masa maƙoshi, ya lumshe idanunsa da sukai mugun kaɗewa mai
ban tsoro daban tashin hankali ya sake buɗewa a kanta. Cikin wani irin murya mai matuƙar laushi da sanyi
ya ce, “Kin fi son mu cigaba da kasancewa a wannan matsayar kenan? Mu cigaba da ɓatama waɗanda ke
bibiyar rayuwarmu lokacinsu. Yes muna ɓata musu lokaci ne kema kin sani, dan in har bani ne MIJINKI ba,
wani bai isa ya zama ba!!.” ya ƙare furucin ƙarshe a kausashe.
Ɗago kai tai da sauri tana kallonsa da jajayen idanunta. Shima ɗin kallonta yake da wani mugun kallon
tabbatarwa. Amma ta dake a kausashe ta ce, “Mi kake nufi Ajwaad?!”.
Shima a kausashen ya ce, “Abinda kikaji na faɗa shi nake nufi. In dai ni Ajwaad Aliyu Darma ina numfashi
a doron wannan ƙasar, wani banza wofi bazai taɓa aurenki ba Maanal. Dan haka tun kafin dare yay musu ki
sanar da su suje su nema matan aurensu. Ki kuma sani ko mutuwa nayi kika auri wani in sha ALLAHU sai na
hanaku zaman lafiya da fatalwata. Idan kuma kinji wasa bismillah, ga fili gamai doki”. Ya ƙare maganar yana
miƙewa da kaɗa mata yatsarsa manuniya a saitin fuska tamkar zai tsokale mata idanu.
Miƙewa tai itama a gabansa tana huci ga hawaye na zirara mata da gudun tsiya. Cike da tsiwa ta riƙe
ƙugu da duka hannayenta biyu tana kallonsa babu ko gezau. “A tunaninka kana da wani ƙarfin yin duk
abinda ka faɗa? Ka lalata min rayuwa sannan kai tunanin hanani auren wani? Shike nan mu zuba, nace mu
zuba ni da kai dan ALLAH ɗan halak ka fasa, ka saka a ranka ni kuma Maanal Habib Umar Giro zanyi aure,
kuma zan auri wanda kake da kusanci da shi wato Rafeeq. Ka fara shiri nan da wata biyu kacal, wata
biyu....” ta ƙare maganar tana karkaɗa masa yatsarta itama da raɓashi zata wuce. Ai a wani irin fusace a
kuma bazata taji an damƙo hijjab ɗinta an fisgota baya. Babu zato ta jita manne a jikin bango, duk da ko
kaɗan jikinsa bai taɓa nata ba yanda yay mata rumfa da ingarman jikinsa saboda ya fita tsaho da cikar jiki
nesa ba kusa ba, babu ta inda zata shaƙi iska ya masifar sake hargitsata. A kausashe a kuma faɗace, dan
gaba ɗaya taswirar ƙyaƙyƙyawar fuskar sa ta canja. Ga jijiyoyin kansa sun sake fitowa, idanunsa sun masifar
kaɗewa irin mai ban tsoro ɗin nan tamkar an watsa jini a cikinsu. Da kakkausar muryar da bata taɓa
tunanin ya mallaka ba ya ce, “Idan kikace zaki zuba WASAN da ni kema kin san kece zaki sha wahala wlhy.
Amma bismillah mu zuba ɗin, sai dai ki sani wani ɗan iska bai isa shiga GONAR dana jima da shiga ba har
abada, yanda na fara mallaka ni zan cigaba da mallaka har ƙarshen numfashi.” Daga haka bai sake cewa
komai ba ya juya ya fita a fusace kamar wani mafaraucin soji a daji.
Yana gama maida ƙofar ya rufe tai wani irin zubewa a wajen ta fashe da kuka jikinta na rawa. Kuka take
sosai, kuka irin mai zuwa da dukkan ƙarfinka dana zuciya. Kuka mai ban tausayi. Ita wannan mutumin kema
alfahari da abinda yay mata a baya, ita yake ma iƙirari akan abinda ya aikata mata. Ita Maanal. Wlhy dolene
ta tabbatar masa shi ba kowa bane, bai kuma isa komai ba, tabbas zata tabbatar masa, dole ne ma ta
bbatar masa, ta hanyar auren RAFEEQ ne kuma kawai zata tabbatar masan.
Ta jima a wajen tanayi, sai shigowar nurse ɗin dake kula da ita ne ya kawo ƙarshen yanayin. Hankali
tashe tazo ta tadata a wajen, da taimakonta ta maidata gadon tana jera mata tambayoyi akan ko jikin nata
ne. Kanta kawai ta iya girgiza mata. Sai kawai nurse ta shiga lallashinta, dan AA ne ya turota dama.
Daɗaɗan kalamai ta dinga faɗama Maanal masu kwantar da zuciya, a hankali a hankali ta fara tsagaita
kukan har tai shiru. Hawayenta ta share tas tare da sake yin lamo a gadon. Nurse ɗin ma tayi tunanin ko
tayi barci ne sai ta lallaɓa ta fita dan akwai abinda zata ƙarasa sannan ta dawo.
Kamar jira Nurse ɗin na fita RK na shigowa. Yayi sallama har fin sau uku da knocking amma shiru, sai ya
ɗan kalla agogonsa da tunanin ko tayi barci. Ganin lokaci yaja sosai sai kawai ya yarda tayi barcin ne. Ƙofar
ya ɗan tura ya leƙa, can ya hangota kwance a gado a lulluɓe, sai dai mi wani ƙamshin turare da ya san bai
taɓa jinta da shi ba ne ya bugosa. Sai da gabansa ya faɗi, ai ba shiri ya shigo ɗakin da sauri. Tabbas ƙamshin
turaren ne, turaren da in bai ƙarya ba a wajen AA kawai ya san shi.
(AA!) Zuciyarsa ta sake maimaita masa sunan da amsa kuwwa. Sai kuma ya shiga waige-waige a ɗakin
kamar zaiga AA ɗin a ciki. Duk abinda yake Maanal na jinsa, amma ta dake tai likimo kamar mai barci, dan
bata son ya ganta a yanayin da take sam. Jin ya fice da sauri yasa ta lumshe idanunta da ƙarfi sauran
hawayen dake a ciki suka wani zubo shaaa.....
____________★
Da ƙyar ya iya fita a taxi ɗin ya nufi gate ɗin gidan nasu, dama satan fitar yayi. Daga fitowa sallar isha'i
ya maƙale yaƙi komawa ciki. Sai da ya tabbatar Abah da yayunsa sun shige sannan ya fito a massallacin ya
tari taxi ya nufi asibitin dan kawai ya ganta. Tun safen da RK yazo gidan da batun nata ciwon zuciyarsa ta
kasa samun nutsuwa. Ji yake kamar ma nasa ciwon ya dawo sabo ne. Sai kuma gashi ya dawo a wannan
bahagon halin yanzu.
Da mamaki security daya buɗe masa ƙofa ke kallonsa. Sai dai shi ko kallon nasa baiyi ba ya wuce flat
ɗinsa. A hankali ya maida ƙofar ya rufe yana sauke ajiyar zuciya ganin kowa bai gansa ba. Sai kuma ya dafe
kansa dake matuƙar sara masa har yanzu tamkar zai cire. Yana shigowa falo na biyu yay wani irin turus
ganin Mamy zaune. Zuba mata ido yay sai kuma ya ɗan wawwaiga kamar mai neman abu. Dan wani irin
tsarga zuciyarsa kallon da take masa yake yi. Amma sai ya dake kamar yanda ya saba. Idanunsa ya maido
kanta cikin sautin muryarsa mai fita ƙasa-ƙasa ya ce, “Mamy kina buƙatar wani abu n....”
Hararar data wullo masa ta hanashi ƙarasawa. Sai ma duƙar da kansa da yay kawai.
“Daga ina kake?”.
Ta faɗa da kakkausar murya. Sam AA ya tsani ƙarya, baya sonta baya shiri da mai yinta. Gara idan bazai
faɗi gaskiya akan abu ba ya gwammaci yin shiru kawai. Haushi ne ya turniƙe Mamy, cikin baƙin ciki da
ƙunar zuciya ta wani daka masa tsawa. “Ajwaad bada kai nake ba ne?! Kasan dai bana son wannan banzan
halin naka na iskanci ko? Nace daga ina ka fito??”.
“Mamy Please my head”
Ya faɗa yana kai hannu a saman kansa. Harara ta balla masa duk da zuciyarta ta motsa da yanda yayi ɗin.
Amma sai a faɗace ta ce, “A'a your heart ba head ba. Ni zaka rainama wayo kama pretending ko. To wlhy
bara kaji, idan ma wani abu kuke ƙullawa kai da ita to ka dawo cikin hankalinka, in ba hakaba wlhy kaine
masha wuya. Dan har yanzu har gobe kai har ƙarshen rayuwa ina akan bakana. Yanda ƴan uwanka suka
auri zaɓina kaima dole hakan zakayi. Dan haka ka sani na zaɓa maka yarinyar da sukazo tare da
Abdulhakeem ɗazun a matsayin mata, a cikin satin nan za'aje nema maka aurenta. Kuma wata biyu kacal
za'a saka...”
Ai da wani irin bala'in sauri ya kalli Mamyn, ta watsa masa harara cike da tabbatarwa........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭_*
[2/11, 8:42 PM] Maryam anas: *_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
4️⃣9️⃣4️⃣9️⃣
______________
..........“Haka na faɗa kuma haka za'ai. Sannan wacece Maanal ɗin da wannan yaron Rafeeq ke magana
ɗazun?”.
Wani irin sake bugawa zuciyarsa da ƙirjinsa da kansa sukai a lokaci guda. Ya tsatstsareta da kaifafan
idanunsa da suka gama jirkicewa gaba ɗaya kamar zai haɗiyeta da su. (Maanal! Waya gaya mata zancen
Maanal? Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un.....)
“Sai ka gama tunanin zaka faɗa min wacece ita?!”.
Ta sake faɗa a tsawace kamar zata falle fuskarsa da mari..
Da sauri ya kai duka hannayensa biyu ya dafe kansa. Sai kuma yay saurin zubewa a kujerar dake kusa da
shi jin jiri na neman zubar da shi a wajen. Ɗan tsai tai tana kallonsa, kamar zata matsa garesa sai kuma,
fuuu ta nufi hanyar kitchen tana faɗin, “Idan ka gama pretending ɗin iskancin kazo ka saman ka faɗa min
wacece ita. In ba hakaba ni zan bincika, kuma ka bari har ya kaimu ga hakan wlhy sai ranka yay
mummunan ɓaci a gidan nan. Zuwa safiya kuma idan ita uwar taka da uban naka suka tambayeka game da
Nuratu da Huznah dan ALLAH kace baka so kaga yanda zan maka. Dan ko ka yarda ko baka yarda ba sai ka
auresu dole su duka kuma a rana ɗaya”. Daga haka tai ficewarta ta kitchen ɗin dan dama tanan ta biyo....
______★
_____________★
WASHE GARI ba ƙaramin tashi hankalin RK yay da ganin yanda idanun Maanal suka kumbura ba. Gasu
sunyi jazur. Amma koda ya tambayeta sai tace barci ne bata samu isashe ba sai gab da asuba. Badan ya
yarda ba ya barta. Zama yay da kansa ya haɗa mata tea kamar yanda yay a kwana biyun nan, amma sai
tace ta ƙoshi, ita so take dai su sallameta.
“Karki damu in dai sallama ce in sha ALLAHU yau za'a sallameki. Amma dan ALLAH ina son muyi
magana Maanal”.
Yanda ya kira sunan nata in serious yasa ta kallesa. Sam kuwa babu wasan data sani akan fuskar tasa. Sai
hakan ma yaso bata mamaki, kamar ba RK sarkin tsokana ba. Itama nutsuwar tayi yanda ya kamata. Kofin
shayin ya miƙa mata, babu musu ta amsa. Tare da cema “Thanks” a hankali.
“Karki damu wannan aiki na ne. Maanal ina son muyi magana akan lafiyarki. Dan haka a matsayin
likitanki nake tare dake anan.”
Kanta ta jinjina masa. Shi kuma ya sake gyara zama sosai da sake nutsuwa. Maanal kin yarda da
ALLAH?”.
Nan ma kanta ta jinjina masa.
Ya ce, “Alhamdullah, ina son yanda kika yarda da ALLAH shi kaɗai bashi da wani abokin tarayya ki yarda da
cewar komai naki a hannunsa yake. Kuma shi mai iko ne akan komai. Maanal magana ta gaskiya ciwon
dake tare dake baya buƙatar komai ƙanƙantar tashin hankali daga gareki, domin ciwo ne mai haɗarin
gaske. Nasan rayuwa bata kasancewa sai da JARABAWOYI a cikinta, domin suna tafiya ƙafa da ƙafa ne da
fitar numfashin mu. Amma duk sanda abu ya faru damu ya wuce yana da ƙyau mu manta da shi kamar
ba'ayi ba. Tabbas ban san minene lulluɓe da rayuwarki ba, sannan ban san minene musabbabin ciwonki
ba. Amma ina roƙonki ko sau ɗaya ki samu wani ki tattauna damuwarki da ita nauyin zuciyarki zai ragu.
Sannan ki sake miƙa al'amuranki ga ALLAH, ki ƙara ruɓanya ibadarki da addu'oi muma in sha ALLAHU zamu
tayaki kinji. Amma ki kwantar da hankalinki, ki daina barin damuwa na miki yawa akwai haɗari, dan
ciwonki na neman kaiwa wani mataki musamman a tsakanin nan da yake yawan tashi. Dan ALLAH ki cire
komai kinji. Ke mai haƙuri ce na sani, kuma jarumace dan a ɗan zamana dake na karanci ƙyawawan halaye
daga gareki masu yawan gaske. Ƴan uwanki na sonki, ki daure ki bama kanki farin ciki, suma zasu samu
farin ciki”.
Murmushi tayi a karo na farko, sai kuma ta kallesa wani abu mai nauyi na narkewa daga cikin ƙirjinta.
Tabbas zuciyarta bata son kowane ɗa namiji da sunan soyayya. Amma abubuwa da yawa daga RK na
birgeta. Mutum ne shi mai sauƙin kai, sam bai ɗauki rayuwa da girma ba. Komai nashi so simple, burinsa
ya bama kowa farin ciki koda shi bazai yi farin cikin ba, ko a wajen ma'aikatan asibitin nan takan ji suna
hirarsa da yabonsa akan tausasawa kowa duk da kasancewar asibitin MALLAKINSA....
“Nifa wannan kallon ALLAH narka ni yake yi Baby”. Ya faɗa yana wani karyar da kai. Murmushi ta saki a
karo na farko, sai kuma ta kauda idanunta a hankali ta maida su ƙasa ta rissinar har lokacin da murmushi a
kan fuskarta. Kusan minti ɗaya sannan tai magana batare data sake kallonsa ba.
“Nagode sosai Yaya Rafeeq. Nagode da irin kulawar da kake bani batare da gajiyawa ba. Nagode da irin
haƙurin da kakeyi da ni duk da abubuwa da nake maka da dama....”
“No! no no please ni ban taɓa miki abu dan ki gode min ba. Dan haka kibar gode min. Kuma yaushe na
zama Yayanki ne ma?”.
“Yanzu mana”.
Ta faɗa tana ɗan waro idanunta dake a kumbure sosai, gasu da ja har yanzu. Dariya sosai ya shiga yi, da
sauran dariyar a fuskarsa ya ce, “A'a nagode a barni a matsayin da na kawo kaina dai. Ke duk tarin yayun
nan naki. Ga Yazeed, ga Fadeel, Fawzan, AA, Uncle Sadeeq, Uncle Hamza haba ai sai daɗin ya miki yawa
idan na ƙaru”.
“Kai dai kace baka son yin ƙanwar da ni kawai na haƙura”.
“Ni bance ba. Amma dai a barni a wancan matsayin, idan ma zan zama yayan a bari sai anan gaba kin
shigo daga ciki”.
“Hummm”.
Kawai tace tana cigaba da juya spoon a cikin shayin daya bata. Fin minti ɗaya sai kuma ta ɗago ta ɗan
kallesa. Ganin kallonta yake shima sai ta ɗan kauda idanun ta. “Yaya Rafeeq ka shirya yin aure yanzu?”.
Mugun faɗuwa gabansa yay dan abin yazo masa a bazatar da baiyi zaton ji daga gareta haka cikin sauƙi
ba, duk da bai san ma'anar yimasa tambayar ba. Cikin nutsuwar ban mamaki ya ce, “Miyasa kika mun
wannan tambayar Maanal?”.
Ƙasa ta ƙara yi da kanta, tana mai kokawar ƙarfafa kan nata da danne dukan abinda ke neman
rinjayar shawarar data gama yanke ma kanta tun a daren jiya. Ajiyar zuciya taja mai nauyi kafin ta saki
murmushi mai ciwo. “Ka amsa min kawai, ka shirya yin aure yanzu?”.
“Ban san miyyasa kika min wannan tambayar ba Maanal, amma tabbas na shirya yin aure, dan na isa
yinsa, da ban shirya yin aure ba ALLAH bazan tunkareki da sunan soyayya ba. Saboda alƙawari naima kaina
bazan taɓa ɓatama kowacce yarinya lokacinta ba in har ba aurenta zanyi ba. Na daɗe ina addu'ar a duk
sanda zan so wata ɗiya mace ya kasance aurenta nake so zanyi”.
Sosai ta kafesa da ido, sai kuma ta wani lumshesu da sake buɗesu a kansa. Cikin son taushe muryarta
dake neman fara yin rawa ta ce, “Ina son zuwa Kaduna a weekend ɗin nan. Kuma ina son na ɗan huta a
can....” sai kuma ta ɗan yi shiru. Cikin zaƙuwa RK yace, “Uhumm ina jinki”.
Murmushi ta sake saki mai ciwo idanunta dai na kallon ƙasa. “Na baka dama kaje ku gana da Daddy
akan batun auren mu”.
Ai ba zuciyar RK ba, hatta ɗakin ma ji yay yana masa girgiza. Yayinda wasu irin hawaye masu azabar zafi
suka silalo da gudun tsiya a kumatun Maanal. Ƙarar tarwatsewar abu da basu san ko minene ba ta ratsa
kunnunwansu. A tare duk suka dubi ƙofar, dan tanan ne abun yay ƙara. Plates ɗin abinci ne suka watse a
ƙasa.
Dubansu suka maida ga wanda alama ta nuna daga hannunsa plates ɗin suka suɓuto...........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?
id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
5️⃣0️⃣5️⃣0️⃣
______________
.........“Subahanalillahi Naufal ya akai haka?”. Oum ta faɗa tana kallon Naufal first born ɗin babban Yaya
kenan da a safiyar yau suka dawo daga Kano shi da sauran ƙannensa biyu ƴammata. Kafin Naufal da yay
ƙwalƙwal da idanu alamar zai yi kuka ya bata amsa ta maida dubanta ga AA da yay tsaye a ƙofar duk ya tare
ko'ina babu ma ta yanda zata iya shigowa. Sake leƙo fuskarsa tayi daga bayan san da take sai kuma ta kalla
direction ɗin daya zubama idanun. Kallon cikin ido suka zubama juna shi da Maanal.. sai dai kafin ta iya yin
wani yunƙuri RK da tuni ya baro inda yake yazo ya kama Naufal ya ɗaga gudun kar ya taka fasashshen plate
ɗin daya tarwatse shi kaɗai ya katseta da faɗin, “Alhamdullahi ai babu ma abinda ya zube kamar plates ɗin
ne suka suɓuto kawai daga basket ɗin, inaga tuntuɓe yayi ne”.
“Ai kasan Naufal da wautan tsiya. Tun da naga ya figo basket ɗin da gudu nasan komai zai iya faruwa.
Baka dai ji ciwo ba ko?”. Tai maganar tana kallon Naufal ɗin dai. Kansa ya ɗaga mata cike da shagwaɓa ya
ce, “Oum Uncle ne fa ya kusa sawa mu faɗi”.
Yanda yay maganar yana kallon AA yasa duk suka kallesa suma. Taɓa AA Oum tayi, dan gani tai ma kamar
baya motsi, sai dai kuma tana taɓa shin ya juyo ya kalleta, hannunsa ta kama cikin nata ta rumtse da ƙyau,
sai kuma ta juya ga Naufal da RK kema dariya da faɗin, “Ko kuma kai ka kusa sakawa ku faɗin ba. Aunty ai
banyi zaton yanzu zaku ma taho ba.
“Rafeeq ai bana wasa da Baby na sam. Balle kace yau za'a sallameta shiyyasa nace in sha ALLAHU da
wuri zanzo. Sai kuma Auta da nake son yaga likita yau shima”.
Karo na farko RK ya dubi AA sosai. Ganin yanda idanunsa sukai masifar kaɗewa ya ce, “Ya Salam badai
kan nasa bane har yanzu?”.
“Shine kuwa wlhy yaƙi sauka, jiya haka ya kwana a wahale”. Ta bashi amsa tana jan hannun AA ɗin
zuwa gaban gadon da Maanal take. A kwance take yanzu ta juyama ƙofa baya, hakan yasa Oum zama a
bakin gadon kusa da ita. Shi kuma yay tsaya kawai daga gefen Oum yana kallon ƙofa dan yaƙi sake kallon
Maanal. Kujera RK ya tura masa cike da kulawa ya ce, “Zauna anan bara na duba Doctor Rasheed ɗin
muga. Ai da kun sanar min da gida yazo ya samesan”.
“Yayi ƙoƙari ne ai Rafeeq, kwana biyun nan yanata zaryar zuwa gidan, kuma dama yace idan bai sauka
ba yau asibiti ya kamata yazo ya duba shi da ƙyau shiyyasa”.
Jajantawa RK ɗin ya sake yi kafin ya juya ya fita yana jaddadawa AA ya zauna. Sai dai ko kallonsa yaƙiyi
balle ya zauna ɗin. Yana daga tsayensa duk da hajijiyar da yake ji na jujjuya masa kai. Oum kuwa data riƙo
hannun Maanal a hankali ta shiga kiran sunanta. Hakan yasa cikin dauriya da jarumta Maanal da tuni ta
goge hawayenta tas ta juyo ɗin. Suna haɗa ido da Oum ta sakar mata murmushi, sai kuma ta tashi zaune ta
shige jikinta cike da shagwaɓa ta ce, “Oum ni nayi fushi sai yanzu”.
“Oh oh my baby kada kiyi fushi kinji, ayima Oum afuwa yaya jikin naki?”.
“Naji sauƙi Oum. Yaya Rafeeq ma yace zasu sallameni yau”.
“To Alhamdullah ALLAH ya ƙara afuwa. Tun jiya naso zuwa shima sai Auta ya kwanta shiyyasa”
“Hy Aunty”.
Naufal ya faɗa yana ɗagama Maanal hannu fuskarsa da murmushi. Murmushin itama Maanal ɗin tai masa.
Sai kuma ta ɗaga masa hannun itama ta ce, “Hy Handsome”.
Farin ciki ne ya kama Naufal jin an kirasa Handsome, dama Uncle AA ne kawai ke kiransa da sunan.
Gaban gadon ya ƙaraso sosai. Ya ce, “Nagode Aunty da kika kirani Handsome. Kun zama biyu kenan ke da
Uncle.” yay mata nuni da AA.
Batare data kalli AA ɗin ba taima Naufal murmushi kawai. Gaisheta yaron yay da tambayarta yaya jiki, ta
amsa masa da kulawa tana zaunar da shi kusa da ita. Sai kuma ta kalla Oum tana faɗin, “Yana kama da
babban Yaya sosai”.
Dariya Oum tayi a karo na farko, idonta akan Naufal ta ce, “Kodai Auta. Dan komai na Naufal Auta ne
sak, duk da dai dama suna kama da Fadeel ne shima ɗin, amma Fadeel ai fari ne, shiko Naufal irin fatanku
gareshi ke da Auta”.
Maimakon Maanal ta amsa zancen sai ta basar ta hanyar shagwaɓe fuska ta ce, “Oum mi kika dafo
min?”.
Dai-dai Oum zata bata amsa RK ya shigo. Idonsa a kansu sai kuma ya kalla AA, da kulawa ya ƙarasa
garesa yana faɗin, “Wai baka zauna ba. Ko duk ƙulafucin Oum ɗin kaka ne kazo ka tsaya mata a kai kamar
zaka koma ciki kai da ɗayar Autar tata. Common malam zauna kada ka faɗi”. Yanda baiyi magana ba tunda
ya shigo yanzun ma bai tanka ba, sai dai ya zauna ɗin dan shima yasan in ba hakan yay ba tabbas gab yaje
da zubewa a ƙasa, sam kuma baya son cigaba da tada hankalin Oum, dan kwana biyun nan da baida lafiyar
nan har rama tayi, ga shi itama tana fama da kanta.....
____________★
A Kaduna kam shirin kai lefe ake gidan su amarya. Shi ango ma baya nan yana Lagos kwana takwas
kenan. Kaya ne na garari aka shirya na kuma fariyya. Jiya yini guda masu shiryasu na aikin nan. Akwatina
set ashirin daa huɗu cif, kaloli daban-daban. Kuma kowane set zaka samu kusan akwati biyar ko uku harda
masu goma sha biyu. Ga galleliyar mota new model a 2023 sabuwa dal a ledarta. Hajiya Basariyya dai tana
nane dasu a gabanta ake komai duk da zuciyarta a ƙuntace take, amma yafi yarda data danne ayi komai
akan idonta, Ammie ko yanda ba'a gayyaceta ba bata saka kanta a sabgar ba daga ita har Sakina da har
yanzu take a gidan. A yau ɗin ma sai suka ƙirƙiri zuwa gyaran jiki abinsu. Duk bidirin shirin kayan da akai
basa nan. Aiko Hajiya Yaya da ƴaƴanta suka samu na zaginsu wai Ammie tana hassada ne saboda ba
ɗiyarta bace ba. Koda suka dawo gidan haka suka cigaba da habaice-habaicen su Ammie tayi kamar ma
bata jisu ba...
Washe gari tun sassafe gidan ya fara tara dangin Hajiya Yaya. Sai wasu a dangin Daddy dake ɗan ɗasawa
da Hajiya Yayan. Yanda gidan ya cika saika ɗauka bikin ne ma ya fara. Har lokacin kuma babu wanda ya zo
ya cema Ammie tazo ga lefe kota shirya zuwa kai lefe, ita kuma tayi biris da kowa bata saka kanta ba. Bayan
sallar azhar suka cika motoci goma cif sai ta amarya dake tsakkiya da toyota hilux da aka zuba kayan lefen a
ciki. Haka suka tafi a jere gwanin sha'awa, duk inda suka gitta sai an tanka kuwa. Dama haka suke so, gari
ya ɗauka ko'ina ayi zancen wannan aure. To ALLAH ya cika burinsu dan kuwa an fara, sakamakon ƙannen
Yazeed kaf da wasu a dangi tun jiya sun gama watsa wannan lefe a kafafen yanar gizo tako ina.. A can gidan
Aunty Sabuwa ma gida cike yake tanƙam da ƙawayenta ƴan duniya da dangin mijinta. Anyi abinci kala-kala
domin tarbar baƙi duk da kuwa aurene na dangin juna. Cikin abinda baifi mintuna ashirin ba anguwar ta
gama rikicewa, dan kuwa kiɗa suka saki sosai da dj ɗinsu da suka tanada. Kafin a ɗan sarara a shiga buɗe
kaya, masu video nayi, masu hotuna nayi, masu guɗa nayi harda ƙawayen amarya. Dan babu kunya hatta
amaryar ma tana a gidan abinta sai washare baki take da jin kanta sama ƙololuwa, dan tasan ita kam ta
wuce tsara sai dai ta taya ƴan baya da addu'a kuma, amma 2025 kam tata ce...
Tukuyci na miliyan ashirin aka bama ƴan kawo lefe suma da tarin kayayyakin snacks da akai packaging,
sai drinks da ruwa katon-katon, dambun kaji, danbun jan nama, soyayyu da gasassun raguna a ƙyafe guda
biyar. Lallai wannan al'amari ya kai duniya tasan da shi. Dan kuwa ba garin Kaduna kawai ba duniya ce ta
ɗauka sakamakon yanda komai ke yawo daki-daki a media tako ina. Dan hatta tarbar da suka samu da
shagalin da akai a gidan Aunty Sabuwa shima anata ɗorawa. Hakama tukuyci da kayan alatun da aka
maƙare musu motar da ta kawo kaya shima dai duk an ɗora. Hakan ya sakama jama'a kwaɗayi da shirin
son ganin yanda wannan shagalin biki zai kasance na ƙwarya tabi ƙwarya. Wanda kuma suka san ainahin
waye uban amaryar dan bai kai ko kwatar dukiyar uban ango Alhaji Usman Chalawa ba nata mamakin
hidimar da su ma su Aunty sabuwar sukayi.
To kowa dai na son yaga yanda za'a kwashe kam, dan in dai har kawo lefe kawai duk akama waɗan nan
hidimomin ai taron biki kam dole ko mu ƴan kallo mu kasance a cikin shirin shan kallon (😂 lolz)....
______________★
Sosai kasancewar su Oum a asibitin ya ɗan ragema Maanal nauyin da zuciyarta tayi. Dan ma hankalin
Oum ɗin ya rabu biyu saboda AA. Dan shi ma bayan Doctor ya dubashi sosai sun ɗan kwantar da shi amma
yace na yini ɗayan ne kawai. A wannan yanayin Shahidah ta iso asibitin ta samesu. Tayi farin cikin ganin
Oum sosai. Kasancewar an hana kowa zama a ɗakin da AA yake dan suna son ya samu barci sosai duk sai
suka tare anan ɗakin Maanal ɗin. Sai bayan sallar azhar da AA ya farka Oum ta nufi can. A lokacin ita kuma
Maanal ta samu sallama. Koda suka gama tattare kaya zuwa mota Shahidah tasa Maanal gaba tai domin
duba AA. Bata so hakan ba, sai dai bazata iya musu da Didinta ɗin ba. Musamman daya kasance RK na tare
da su ne.
RK ne ya fara shiga bayan yayi knocking an bashi izinin shiga. Sai Maanal, Shahidah a ƙarshe. Oum na
zaune a kujera, shi kuma AA na kan gadon ya jingina da filo Oum zata fara bashi abinci a baki, sai faman
ɓata fuska yake alamar baya son cin abincin ko kuma duk ciwon ne oho masa. Plate ɗin abincin Oum ta
ajiye tana kamo hannun Maanal da faɗin, “Masha ALLAHU ƴan matana anyi sallamar dai?”.
Kai Maanal ɗin ta jinjina mata a ɗan shagwaɓe. Ita kuma tayi murmushi da faɗin, “To Alhamdullah,
ALLAH ya ƙara lafiya yasa kaffara ne.”
Amin RK da Shahidah suka amsa da shi, kafin Shahidah ta maida hankalinta ga AA daketa kallonta. Duk
da yasan dama zai iya ganin nata, amma sosai mamakinsa ya bayyana amma ya gagara iya cewa komai.
Wannan ba komai bane daga halayensa, dan haka Shahidah bata damu ba, sai dai zafinsa da suke ji tun na
shekarun baya akan ƴar uwarsu taji yana taso mata. Komai dawo mata yake kamar yanzu ne yake faruwa.
Da ƙyar ta iya dannewa ta tambayesa jikinsa. Karan farko yay ɗan murmusa, irin guntun murmushin nan
mai tabbatar da ƙunar zuciya. Tabbas yaga tsanarsa a bayyane akan fuskar Shahidah, hakan na nufi har
yanzu suma basu mance komai ba, basu mance abinda ya faru ba suna riƙe da shi a ransu fiye ma da
Maanal. Baiga laifinsu ba, dan ko shine hakan zai yi, amma inama zasu fahimcesa kamar yanda Oum ta
fahimcesa bayan ya zauna da it.....
Maganar RK ce ta katse masa tunaninsa, ya ɗan kallesa sai kuma ya janye idanunsa yana jinjina masa
kai. Baya son sakama ransa tsanar ɗan uwansa kodan daraja da kimar Oum, amma tabbas zafinsa yake ji,
kishinsa yake ji mai tsanani akan Maanal. Ta yanda ya gwammaci ya dinga masa shiru akan abubuwa da
dama fiye da yin magana.
Sai yanzu Maanal da tunda tai masa kallo ɗaya bata ƙara ba ta furta, “Ya jiki?”. Daga haka tai shiru.
Shima sai bai amsa ba, ya dai ɗago idanunsa ya kalleta kawai. Yana ƙoƙarin janyewa akai knocking ƙofar.
Shahidah ce ta amsa sannan ta bada izinin shigowa. A hankali aka turo ƙofar, yana sanye cikin lallausan
farin yadi da yay masa matuƙar ƙyawu, sosai kamanninsa da AA ke a bayyane, ta fuska da ɗabi'u. Sai a
shekaru ne kawai suka banbanta da hasken fata. Ɗan ja yay ya tsaya turus yana kallon Shahidah da itama
take kallonsa, sai kuma tai saurin kauda idonta. Shima janyewa yay ya maida ga Oum, sai kuma ya sake
waresu akan Maanal da itama take kallonsa. Cikin kasa daurewa ya ce, “Oum kinga mi nake gani?”.
Murmushi sosai Oum ta saki mai ciwo, sai kuma ta jinjina kanta da faɗin, “Na sani Fadeel. Shahidah ce
da Lillyn ka”.
“Wai da gaske ne kenan?”.
Yanzu kam har sai da hakwaran Oum suka bayyana a waje, sai kuma hawaye suka ciko mata idanunta. Da
ƙyar dai ta iya dannewa ta sake bashi amsa........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
5️⃣1️⃣5️⃣1️⃣
______________
.......Matuƙar mamaki Babban Yaya ya shiga da jin komai daga bakin Oum da RK. Sai satar kallon Shahidah
yake da jinjina mamakinsa akan canjawar Maanal. Ta ƙara tsaho duk rashin jin nan da rawar kai babu
yanzun. Hakan ba abun mamaki bane ba, musamman idan aka tara yanda abubuwa suka kasance zama a
iya ganin fiye da hakan daga Maanal. Nan fa ya tasa Maanal da tambayoyi har ma da Shahidah duk da shi
ɗin ba gwanin yawan magana bane ba.
Maanal ce mai amsa masan, dan itama Shahidah tana amsa ɗai-ɗai ne. Itafa Family ɗin nan idan ta
cire Oum a ciki da Fawzan da Abah da Mamy bata jin sauran a ranta yanzu. Sai ma wani kalar zafinsu da
take ji, amma darajar Oum yasa taketa ƙoƙarin dannewa dan Oum ta cancanta. Ana cikin hakan sai ga
Fawzan shima ya iso, bayansa matarsa ce Nibras, sai Saheeba matar babban Yaya hannunta riƙe da ƴar
budurwar yarinya mai tsananin kama da su Babban yayan. Sai budurwar yarinya ƙyaƙyƙyawa a ƙarshe biye
da su hannunta ɗauke da irin box ɗin nan da ake saka kayan abinci. Ambatar sunan Lilly da Shahidah da
Fawzan yayi ya saka Saheeba kallon sashen da sauri. Kallon ido cikin ido sukaima juna da Shahidahn. A take
fara'ar fuskar Saheeba ta ɓace ɓat. Itako Shahidah ta janye nata cike da basarwa tana bama Fawzan amsar
maganarsa. Ita dai Nibras bata sansu ba a zahiri. Amma sunayen da aka ambacesu da shi ya sata
tsatstsaresu da idanunta, dan ta ɗan san labarin dangantakar tasu da familyn Darma a wajen mahaifiyarta.
Sai dai kuma bata da tabbacin waɗan can ɗin ne ko wasu daban.
Ita ko budurwar data shigo a ƙarshe gaba ɗaya hankalinta naga AA ne. Dan tuni ma ta kai gaban gadon
babu ko kunya ta zauna a kusa da shi. Sai dai hararar daya jefa mata ta sata miƙewa tsaye zambar tana
faɗin, “Sorry Yaya”.
Komai baice mata ba, ita kuma bata nuna damuwa ba ta ɗan rissina tana gaisheshi da tambayarsa jikin
nasa. Sai kuma ta jawo kujera dake can jikin ɗayan gadon dake a ɗakin dan gado biyu ne Naufal na barci a
wajen ta zauna kusa da shi sosai. Dai-dai nan Shahidah ta miƙe tana faɗin, “ALLAH ya ƙara lafiya bara mu
wuce Maanal ta samu ta huta.”
Wani irin ɗagowa budurwar mai suna Nuratu tayi jin sunan Maanal a karo na farko. Sai a yanzu ta kalla
Oum kasancewar Maanal ɗin na'a jikin Oum kamar ƴar mage. Tabbas bata san Maanal ba a zahiri itama a
wancan lokacin na ƙuruciya dan ita ta rayune ba'a gidansu ba, yayar babansu ce ta riƙeta suna zaune a
Lagos. Bayan rasuwar mijinta ne suka dawo Abuja, amma tasan komai na labari tsakanin yarinya mai suna
Maanal da Yaya AA ɗinta. Burin ranta, da take fatan ya zama miji a gareta tun a randa ta fara tozali da shi a
Lagos. Ƙoƙarin tuna inda tasan fuskar Maanal take yi, dan haka ta kafeta da idanu. Ƙirjinta ne yay masifar
bugawa lokacin da suka haɗa ido da Maanal dake miƙewa Oum riƙe da ita. Sarai Maanal ta ganeta ita,
hakan yasa ta janye idanunta cike da basarwa. Itako Nurry ta kasa janyewa dan ta gane Maanal itama, itace
yarinyar da suka haɗu a wajen saloon ranar Sunday ɗin data gabata. Jitai jikinta kawai ya fara rawa,
zuciyarta na bugawa da sauri-sauri saboda tsoron abinda take hasashe, cikin rawar murya da suɓutar baki
ta furta, “Wai itace Manaal ɗin da nake jin labari a gidan su Mamy na Kano Aunty Saheeba?”.
Ba Saheeba data ambata ba, hatta su Babban yaya sai da suka dubeta, shi kansa AA wani kalar mugun
kallo ya zuba mata ita da yayar tata Saheeba duk da matar yayansa ce. Sai kawai jikin Saheeba da Nurry ya
kama tsuma. Cikin daburcewa Saheeba da kallon rashin mutuncin da Babban yaya ke jifanta da shi gana AA
a gefe ya gama rikitata ta ce, “Wlhy ni ba wani bad abu na sanar mata akanta ba. ALLAH ma ne shaida bani
na gaya matan ba. Nuratu ko'a bakina kika ji?”. Ta juya tana kallon Nuratu da zuciyarta ke mazari. Dan ta
fahimci itama katoɓarar data nema yi. Sai dai kuma wani irin jin tsanar Maanal ke sake haɗa wutar guguwa
a can ƙasan ranta. Kai ta girgiza ma Yayar tan, sai kuma ta ce, “No nima fa ba ina nufin wani bad abu bane
ba wlhy ko aka sanar min a kanta. Kawai na faɗa ne ta yanda zan tabbatar da ita ɗin ce bawai dan wani abu
ba.”
Fawzan ne ya girgiza kansa kawai da katse yanayin ta hanyar faɗin, “ALLAH ya ƙyauta to. Amma
wannan maganar ma baida wani amfani. Ƙanwata muje na saukeku gida ko”. Ya ƙare maganar idonsa akan
Shahidah. (Da ada ne catake ita ba ƙanwarsa bace). Suyita musu da jayayya, dan da gaske Fawzan ya girma
Shahidah ɗin da kusan shekara uku, kusan ma za'ace AA ne sa'anta. Amma ta girmesa itama da wasu
watanni. Alaƙar Shahidahn da babban Yaya yasa suke ƴar jayayyar da Fawzan ɗin sarkin barkwanci da
tsokana.
Murmushi Shahidah tai masa da faɗin, “A'a mun hutasheka Yaya Fawzan. Da mota ma nazo shiyyasa
nace shima Rafeeq ya huta abinsa.”
Sai a lokacin RK da komai ke masa kaikawo yay magana. Maanal da tuni tai gaba ya kalla. Dan ita ko
kallon Nurry batai ba balle wani dake ɗakin akan maganganun. Hasalima bata nuna tasan anayi ba, tunda
tabar jikin Oum tai hanyar ƙofa abinta. Kai kawai ta jinjinama RK da sakar masa ɗan murmushin daya sake
tokare maƙoshin AA tai ficewarta. Itama Shahidah sai kawai ta bita tana wani jin sake tsanar wannan
family.
Biyosu RK yay da sauri, hakama Oum. Dakatar da RK Oum tayi, kafin ta ƙarasa inda Shahidah ke
ƙoƙarin buɗe motarta ta riƙo hannunta. Da sauri Shahidah ta juyo, sai kuma ganin Oum ya sakata sakin
murmushi. “Lah Oum ko munyi mantuwa ne?”.
Fuskar Oum cike da damuwa ta ce, “Ba mantuwa kukai ba Shahidah, haƙuri zan baku. Dan ALLAH kada
abinda yarinyar can Nuratu tayi ya dameku. Nasan koda wani abu taji ba wanda kuke tunani bane ba. Dan
dukkan abinda ya faru sirrine da iya mu da ku muka sanshi. Ni......”
Da sauri Shahidah ta shiga girgiza mata kai, “No Oum dan ALLAH kar kice komai. Mu tsakaninmu dake
sai addu'a da fatan alkairi. Kamar yanda tun farko muke miki kallon uwa yayar Ammie haka har gobe
wannan matsayin naki bai goge ba a zukatanmu. Bamu taɓa riƙeki a ranmu ba. Kosu wlhy albarkacinki
dana Abah da Mamy suke ci har muke jin komai ya wuce kamar bai faru ba. Abinda ya faru ƙaddararmu ce
mu duka da ku, babu kuma wanda ya isa ya iya canjata ba gashi komai ya wuce kamar ma bai faru ba”
“Na sani Shahidah, amma idan na tuna nakan ji na tsani dukkan kaina wlhy. Kuma ina sha ALLAHU
addu'ar da nake tsahon shekaru bazata taɓa tafiya a banza ba. Da izinin UBANGIJI sai Ajwaad ya gyara
ɓarnar da yay da kansa. Gaskiya kuma saita bayyana. Abinda duk ke a ɓoye zai fito fili”. Kuka ya sarƙe
Oum...
Rungumota Shahidah tayi, yayinda Maanal tai saurin shigewa mota hawaye na gudu akan fuskarta.
Jikinta sai rawa yake yi. La'ilaha'illa antas-subahanaka inni kuntu minazzalumin ta dinga ambata. Tsohon
lokaci har bata san mi Shahidah da Oum suka cigaba da tattaunawa ba Shahidah ta shigo mota. Komai
basu cema juna ba sai murmushin da Maanal ta ɗan sakar ma Oum dake mata magana ta ɗaga mata
hannu....
Komai dake faruwa a idanun RK ne dake tsaye daga can nesa da su. Shifa gaba ɗaya an ƙarasa kulle masa
kai. Yau ya fahimci lallai akwai wani babban al'amari daya shiga tsakanin wannan zumuncin. Sai dai
miyyasa kowa ke son ɓoyewa ne? Anya bai kamata ya sani ba? To idan ya sani amfanin mi sanin zai masa.
Kawai yana son Maanal hakan ya wadatar da shi. Idan lokacin ya san komai a tarayyarta da Darma Family
yayi yasan zata sanar masa duk da ƴan uwansa ne jininsa na kusa kuwa. Koda Oum ta iso inda yake bai
tambayeta komai ba. Sai ma murmushi da yay mata yana mai nuna mata hanya alamar suje. Zuba masa
idanu Oum tayi sosai, sai kuma a hankali ta furta, “Rafeeq! Da gaske kana son Maanal?”.
Idanunsa sosai ya waro a kanta, sai kuma ya narke fuska cike da nuna damuwa ya ce, “Haba Aunty,
wane irin tambaya ce wannan mai tarwatsa zuciya. Kema shaida ce ban taɓa kawo wata yarinya gareku da
sunan soyayya ba. Miyyasa kuke ganin komai na kamar ba serious ba?”.
“Sam ba haka bane ba Rafeeq. Nasan kai mutum mai son wasa ne. Amma ban taɓa kallon al'amuranka
a matakin rashin serious ba. Itama tambayar na maka itane kawai.”
Kansa ya ɗan jinjina da faɗin, “In sha ALLAHU Aunty zan tabbatar muku da babu wasa akan batuna
da Maanal. Dan yanzu haka ma ta bani damar zuwa Kaduna na gana da Daddynta a next week”.
Cak Ammie ta tsaya gabanta na faɗuwa. Dan lips ɗinta har ɗan rawa yaso farawa amma tai ƙoƙarin dai-
daita kanta da ƙyar. Sai kuma ta sakar masa murmushi kawai da faɗin, “Masha ALLAH, idan mukaje gida
zamuyi magana”....
Koda suka dawo ɗakin sun sami babban yaya nata zuba faɗa ma Nuratu. Ta inda yake shiga tata nan
yake fita ba. Sai shigowar Oum datai masa magana ya tsagaita. Amma duk da haka a fusace yace su wuce
su koma gida ba'a buƙatar sake ganinsu a asibitin ma. Haka Saheeba da Nibras da ita Nuratun suka fita
ransu a ɓace suma. Sai dai babu damar magana dan tabbas babban yaya da AA basu san wargi ba. Koshi
Fawzan dake da yawan barkwanci bawai ya saki kansa bane raini ya shiga tsakaninsa da Matarsa ma balle
ita Nuratun. Hatta da ita Saheeba dake matsayin matar babban yayansu da suke matuƙar girmamawa babu
raini a tsakaninsu dan matsayin ƙanwa take a wajensa.. Anan suka bar yaran, dan tuni Anum maƙalƙale
take da jikin Fawzan dama tun fara faɗan Daddynta. Shi ko Naufal har yanzu yana barci ne.......
____________★
Koda suka iso gida daga Shahidah har Maanal basu sake tada maganar nan ba. Shahidah tayi hakan ne
kawai dan gudun tadama Maanal hankali, sai da ta shiga ɗakinta tai kiran Amaal suka tattauna. Sun jima
akan wayar suna magana har Maanal ta shigo sannan Shahidah ta yanke kiran dan bata son tasan da
Amaal ɗin take waya. Itama Maanal bata damu da sanin dawa Shahidahn ke wayar ba. Sai ma zama da tai
a bakin gadon nata.
“Har kinyi wankan?”.
Kai Maanal ta jinjina mata cike da ƙarfin hali. Sai kuma tai ɗan murmushin san kore damuwar nan ta
ƙarfin tsiya sannan ta furta, “Naga mutiniyarki na haɗa kaya fa ko Kaduna zataje ne itama?”.
Da mamaki Shahidah ta ce, “Wai Huznah?”.
Kai Maanal ta jinjina mata. Ita kuma tace, “Humm to ita dai ta sani, ai garama ta koma ɗin dan nikam
wannan gantalin nata na tayar min da hankali musamman a kwanakin nan data san Yazeed baya Abujan.
Narasa mi yarinyar nan take yi a garin nan?”.
Murmushi kawai Maanal tayi amma taƙi gayama Shahidah gaskiyar abinda ta sani akan Huznah ɗin.
Badan bata son ta sani ba sai dan bata son sako al'amarin mutumin (AA🤣) da Huznahr ke bibiya sam a
al'amuranta. Sai ma kawai ta basar da zancen ta hanyar faɗin, “Didi nima ina son zuwa Kaduna a weekend
ɗin nan”.
“Amma Auta kinfa san satin ne bikin Yazeed”.
“To minene a ciki Didi. Dan ana bikin yaya Yazeed kuma sai naƙi zuwa Kaduna?.”
“Baƙya gudun abinda zai iya zuwa ya dawo”.
“In sha ALLAHU babu komai Didi. Kawai ina kewar Ammie ne sosai wlhy. Sannan ina son Rafeeq yaje su
gana da Daddy dan na bashi damar hakan”.
Da sauri Shahidah ta dubeta. Harshenta har harɗewa yake wajen furta, “Maanal akan mi kike son
Rafeeq ya gana da Daddy?”.
Ɗan jimm Maanal ɗin tayi tana kokawar saita kanta da danne duk wani yinƙurin raunin da zuciyata ke son
bayyanawa akan fuskarta, sai kuma ta saki murmushin karfin hali. Kanta tsaye ta ce, “Na bashi damar
neman aurena”.
“What!! Neman aurenki fa kika ce Manaal? Rafeeq ɗin? Shifa ɗin ɗaya daga cikin zuri'ar su Ajwaad
ne??”.
“Tabbas hakane Didi. Shiyyasa ma na bashi wannan damar. Sannan kin manta ne, alaƙar dake tsakanin
Oum da Rafeeq tafi ƙarfi fiye da wadda ke tsakani da su. Dan haka na yarda na amince zan auri Rafeeq in
sha ALLAHU”. Daga haka ta miƙe ta fice daga ɗakin ko waiwayen Shahidah data saki baki da hanci da ido
tana kallonta batai ba.........✍️
_Nifa
😆 a wata gaɓar rasa abincewa nake 😆 ._
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
5️⃣2️⃣5️⃣2️⃣
______________
.........Wani irin kalar zubewa Shahidah tayi a saman gadonta kamar wadda aka kwashema dukkan ƙarfi da
zuciya a lokaci ɗaya. Kalaman Maanal na mata wani irin kai-kawo dai-dai da bugawar zuciyarta. Sai kuma
kamar wadda aka zabura ta lalubo wayarta. Kira ta sake dannama Amaal. Aiko bugu ɗaya ta ɗaga dan
dama tun ɗazun nemanta take itama amma ta gagara samunta....
“What! Rafeeq fa? Maanal kuwa nada hankali? Kota manta alaƙar dake tsakanin Rafeeq da Ajwaad
ne?”.
“Nima na faɗa mata hakan wlhy Amaal. Amma ta nuna min ai alƙar dake tsakanin Oum da Rafeeq tafi
ƙarfi akan wadda ke tsakanin Rafeeq da su Ajwaad. Ni wlhy nama rasa wane tunani zanyi. Dan tabbas
akwai ƙura babba. Anzo gaɓar fa da dole Ammie tasan halin da ake ciki kin san dai Auta da taurin kai da
kafiyar tsiya”.
“Amma kin san zamusha faɗa akan ɓoye matan da mukai. Sannan na faɗa miki jiya naje gidan na
samu Daddy na shirin zuwa Kebbi domin ganawa da waɗan can mutanen na Giro. Na tabbatar kuma yau
ɗin nan sun tafi ma shiyyasa nake ta nemanki tun safe. Yanzu haka can gidan zanje dan Hameed ya kirani
ya sanar min Ammie na ciwon kai yau gaba ɗaya a kwance ta yini kuma yaga Daddy ya fita daga wajenta da
safe kamar a fusace. Kinga ko ya tabbata akan zuwa Giro ɗin ne maybe ta nuna bata so ko”.
“Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un Amaal komai zai iya faruwa kam. Wannan wace irin gaɓa ce mai
rikitarwa da tada hankali. Aiko muma bamuga ta zama ba dole na ɗauka hutu Kona kwana huɗu ne muzo
Kadunan gobe idan ALLAH ya kaimu. Daga nan kawai har biki”.
“To gaskiya hakan ne ya kamata kawai ku taho. Bara naje naga halin da Ammien ke ciki”.
Jiki a sanyaye Shahidah ta amsa ta da to kawai suka yanke kiran.
Bata leƙa Maanal ba sai bayan sallar magriba, ta sameta tana karatun Alkur'ani. Zama tai dan haka
Maanal tana kaiwa inda ya kamata ta tsaya ta dakata. Duban Shahidah tayi da da faɗin, “Didi kina son wani
abu ne?”.
“A'a Auta, ina Huznah take?”.
Sai da Maanal ta ɗan taɓe baki sannan tace, “Naga Yaseerah ta kiranta yanzun nan ta saka hijjab ɗina ta
fita a rikice. Ban san mita gaya mata ba amma da alama Yaseerahn na wajen gidan nan ma dan naji tana
cemata gata nan zuwa ba sai ta shigo ba”.
Kai kawai Shahidahn ta girgiza da faɗin, “To ALLAH ya ƙyauta. Dama zance miki ne inaga gobe in sha
ALLAHU zamu wuce kadunan gaba ɗaya”.
“Didi aikinki fa? Wani abu ya faru ne?”.
“Babu damuwa zanma Abban Barrah magana ya nema min hutu na kwana huɗu tunda oga na abokinsa
ne. Kinga idan biki ya tashi sai mu taho gaba ɗaya kawai”.
Magana Maanal taso yi, sai kuma ta ce, “Okay ALLAH ya kaimu to”......
_____________★
A ɓangaren AA kam shima bayan wucewar su Maanal ya matsa aka sallamesa. RK yaso ƙin yin hakan
amma ina. Ganin yana neman birkice musu Oum tace yasa a sallame san kawai. Sun iso gida Mamy da
Abah na shirin zuwa asibitin dubashi. Dan shi Abah yau yaje gidan gwamnati tunda safe sakamakon kiran
daya samu daga mataimakin shugaban ƙasa. Ita kuma Mamy ta fita dan ko kai AA ɗin asibiti bata san anyi
ba sai da ta dawo ko sashenta bata shiga ba taci karo da Abah ya fito zaije asibitin. Shine yace ta juya suje
dan yasan halinta zata iya ƙin zuwa saboda kawaici. Bata ce masa komai ba suka nufi motarta data ajiye
yanzu, dai-dai nan kuma sai ga ƴan asibitin ma. Sai kawai suka runguɗa zuwa sashen Oum dan AA yace shi
can zaije baya son sashensa. Can ɗin kuwa aka nufa da shi har ɗakin Oum. Anan suka zagaye sa cike da
kulawa da tsantsar soyayyar da kowa ke masa a gidan....
★★★
Abdul-hakeem mijin Yaseerah yazo gidan kawoma Mamy saƙo data manto a wajen mamansa shi kuma
yaje gidan ta bashi ya biyo Mamyn dashi ya samu batun ciwon AA ɗin bai sauka ba da har yau ya kaisa ga
zuwa asibiti. Shine ya kira matarsa Yaseerah yace tazo itama ta duba shi sai su koma gidan tare. Ita kuma ta
kira Huznah ta kuma biya ta ɗakkota a gidan Shahidah kamar yanda mijin nata ya bata umarni. Koda suka
shigo kai tsaye sashen Oum suka nufa dan har lokacin itama Mamy na acan dama duka ƴan gidan har su
Saheeba da Nibras da Nuratu. Mai aikin Oum Mamy ta saka shigowa da su Abdul ɗin har falon sama na
Oum.
Duk suna a falo, idan ka cire AA dake can bedroom ɗin Oum da yay barci. Sai Babban Yaya da bai dawo
gidan ba tun baro asibiti da yay ɗazun. Nibras da Nuratu na'a falon ƙasa suna girki. Nuratu ce ta fara cewa
zata girka ma AA abinci kamar yanda uwarsu da suka kira suna gaya mata abinda ya faru a asibiti ta basu
shawarar yi. Sai ita kuma Nibras ta ce itama zatayi dan wani irin tsanar Nuratu take ji tuni batun yanzu ba.
Abinda ma ke ɗan sassauta mata ƙinta ganin yanda shi AA ɗin baya wani shiga sabgarta. Itama dai taci kuka
bayan dawowar tasu daga koro sun da akayi daga asibiti. A hakan ma ba wani tarihin Maanal ta sani
cikakke ba game da alaƙarta da AA, amma ta ɗauki aniyar bugar cikin Fawzan ta sani yau dan tasan irin
matakin da zata ɗauka akan Maanal ɗin da dukan ahalinta ma. Dan itafa a yanda take jin AA a ranta ALLAH
ko mahaifansa da su Fawzan zata iya kawarwa ta mallakesa ita kaɗai.
Su Huznah sun hawo Nibras da Nuratu dake a kitchen basu sani ba. Sai da har su Abdull sun gama
gaishe da Abah da Mamy da Oum Abah na tsokanar Abdull sannan suke haurowa da kayan abincin da suka
shirya harda mai aikin Oum. Sannu Oum da Mamy ke musu, duk suka amsa tare da tambayar Mamy ina
za'a kai masa abincin. D/table Mamy tace su ajiye. Dan haka duk suka ajiye a can ɗin. Juyowar nan da
Nuratu zatai tana magana da Abdull sai idanunta ƙuru-ƙuru a cikin na Huznah da tun shigowar Nuratu
falon mamaki da ruɗani suka baibayeta. Cikin kuwa ɗan waro ido na nuna mamaki Nuratu ta ce, “Kai wai
wa nake gani kamar Huznah?”.
Murmushin ƙarfin hali Huznah ɗin tayi, sai kuma ta sinne kai ƙasa wai ita kunyar surukai na wajen ta ce,
“Nice Nurry”.
Idanu Yaseerah da Abdul-hakeem suka haɗa. Yayinda Mamy ta saki wani murmushin jin daɗin ganin
Nuratu da Huznah ma kenan sun san juna. Dan haka sai kawai ta miƙe tana faɗin, “Kunga muje can kafin
Maman ɗan nan tace zamu hana mata shi barci”.
Dariya Oum tayi dan sanin da ita Mamy take. “Oh abun ma harda ƴar sharri. To shike nan kuje ɗin dai
dan kuwa ban san a tada shin”.
Mamy ma dariyar ta sake yi. “Ai nasan gaskiya na faɗa”.
Shima Abah dariya yaketa musu. Haka Mamy ta fice tare da su Huznah. Nuratu ma tai wuff ta bi
bayansu. Suna gama fitowa daga apartment ɗin Oum ɗin caraf Nuratu ta riƙo hannun Huznah dake kusan
ƙarshe. Cak Huznah ta tsaya, sai kuma ta juyo tana kallon Nuratu. Murmushi ta sakar mata da faɗin, “Oh
oh friend ashe kece? ALLAH duk kin saka mamaki yama rufe ni da ganinki gidan nan kodai gidanku ne?”.
Nuratu da zuciyarta keta watsal-watsal a ƙirji ta ce, “Eh gidanmu ne. Amma ba inda aka haifan ba.
Gidan da zanyi aure kenan, kuma wanda zan aura ɗin ma kuka zo dubawa. A ina kika san Abdul-hakeem?”.
Tsabar yanda zuciyar Huznah tai wata girgiza har taurari ta dinga gani na mata yawo a cikin ido. Cikin
rawar baki ta ce, “Waye zaki aura ɗin?”.
Cike da gadara da alfahari Nuratu ta bata amsa da, “Ajwaad Aliyu Abubakar Darma, wato AA Darma”.
Ai zabura gefe Huznah tayi tana mai fisge hannunta daga cikin na Nuratu, sai ko gata jikin bango kamar
mage ta gamu da kare a kwanar da babu hanyar ɓillewa. Yanda tai ɗin ya saka Nuratu kafeta da ido itama
zuciyarta na wantsalawa a karo na biyu. Sai kuma ta matsa gaban Huznah tana faɗin, “K jira-jira wai badai
dama Yaya AA kike bibiya ba?. Babbar bala'i wai dama shine kika bamu labari?”. Bata jira amsar Huznah ba
tai saurin fara danna wayarta ta latso hoton AA dake cikin wani lallausan farin yadi da yay masa shegen
ƙyau ta nuna mata. “Shine wannan?”.
Jinjina mata kai Huznah tayi a mutuƙar harmutse.
“Kambu are you mad? Wai dama mijin aurena kike bibiya. Ehhhh ahhh lallai kin taro match yarinyar nan.
Yau naga baƙar shegiya ubanwa ya aiko ki?”. Tai maganar da nufar Huznah gadan-gadan tana neman kai
mata hannu ta shaƙota. Hannun nata Huznahr ta riƙe caraf, a dai-dai nan Fawzan ya iso wajen.
“Kai kai kai lafiya?!!”.
Ya faɗa cikin daka tsawa. Dan shima abinda Nuratun tayi a asibiti har yanzu haushin bai bar ransa ba.
Dakatawa Nuratu tai daga shirin shaƙe Huznah. Sai dai cikin wani irin ihu da hargowa ta ce, “Yaya Fawzan
wai har wannan tsinanniyar ce zatace tana son Yaya AA. Son shi take amma tazo ta raɓu da jikina inata
bata shawarar yanda zata sameshi. Ni wannan ƴar iskar zata maida bahuwa. Na rantse da ALLAH yau saina
haɗa miki jini da majina ta yanda bazaki taɓa sake sha'awar yima kowa ƙwacen saurayi ba dan ........” ta
ƙarasa da ashariya mai girman gaske tana sake zaburowa kan Huznah.
Cikin ƙanƙanin lokaci rikici ya harƙume a tsakaninsu da hayaniyar ta saka su Mamy fitowa. Hakama
Oum sai gata da Abah harda masu aiki duk sun yo waje. Itama Nibras da Saheeba haka. Wani irin jan
faratunnan ƙarin da Nuratu tayi a hannunta tai a saman fuskar Huznah,tun daga wajen kunnenta har zuwa
bakinta. Ƙara Huznah ta saki na azaba tana mai dafe fuskarta da duka hannuwan biyu jikinta na rawa. Aiko
cikin tashin hankali Mamy da Oum sukai kan Huznah ɗin, ita kuma Saheeba ta riƙe Nuratu. Mugun ciwo
Nuratu taima Huznah , dan yanda kasan tsagar yarbawa irin na farkon ƙarnin nan haka suka kasance har
sanda huɗu na yatsunta. Jini tuni ya jiƙe wajen abinka da farar fata jiki kuma babu wahala.
Ai Fawzan baima san ya kwashe fuskar Nuratu da mari ba. Yana ƙoƙarin sake kai mata wani Abah ya
riƙe hannunsa yana mai girgiza masa kai. Kuka Huznah take sosai na azaba, hakama Nuratu kukan marin da
Fawzan ya mata take yi. Sai dai bakinta bai mutu ba sai sake jadadadama Huznah take idan bata fita a
sabgar AA ba ALLAH sai dai ta kasheta. AA nata ne ita kaɗai. Yanda taketa surutai yasa kowa ya fahimci
akan AA suke faɗan, dan in ka cire Mamy da su Abdul-hakeem sai ita Saheeba babu wanda yasan alaƙar
Huznah da zuwa gidan ma.
Dole Abdull da Yaseerah da jikinta duk ke faman rawa suka kama Huznah zuwa mota domin kaita
asibiti. Ita kuma Saheeba taja Nuratu sashenta. Nibras da bayanin Nuratu ya sata jin wani irin ƙaiƙayin
baƙin ciki a zuciya fuuuu ta wuce nasu sashen itama. Sai Mamy da Oum da Abah da Fawzan kawai aka bari.
Cikin ɓacin rai Fawzan ya ce, “Wannan yarinyar sam bata dace da Ajwaad ba wlhy Abah. A haka kuke son
aura masa ita tana abu kamar ƴar daba. Daga zuwan yarinya taji mata wannan mugun ciwon a fuska. Haka
dama ɗazun a asibiti tayi akan Lilly, tana wani tambayar wai ba itace tasan labarinta ba, uwar mi ta sani to?
Mi aka gaya matan akan su Shahidahn”.
Cike da mamaki Abah ya ce, “Wace Lilly da Shahidah?”.
“Lilly dai daka sani Manaal da Shahidah na Kano”.
Wani irin girgiza zuciyar Mamy tayi, haka Oum ma sai da ta ɗan rumtse ido. Yayinda Abah ya furta,
“Fawzan kasan mi kake faɗa kuwa? Da gaske kake yi?”.
“Wlhy Abah da gaske nake yi. Itama an kwantar da ita a asibitin ne shine suka shigo duba Auta”.
Wani irin lumshe idanu Abah yayi zuciyarsa na masa nauyi a cikin ƙirji........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
5️⃣3️⃣5️⃣3️⃣
______________
........A ɓangaren Maanal kuwa bayan fitar Shahidah text ta turama RK dan tana son su ƙarasa maganar da
suka fara. Ko minti biyu ba'a cikaba kuwa da tura saƙon sai ga kiransa ya shigo. Kamar bazata ɗauka ba ta
dai daure ta ɗaga ɗin tare da saka hans free kawai. Sallama tai masa da sassanyar muryarta da a yau
rauninta ya sake fita fili. Shima sai ya amsa mata da tashi sassanyar muryar. Tare da faɗin, “Gani a
compound ɗin ku”.
Sosai mamaki ya kama Maanal, harta kasa ɓoyewa sai da ta furta, “Wasa kake amma?”.
Murmushi yayi mai sautin da har taji, “Da gaske nake my queen, dama ina gidan kusan minti goma
kenan bana son takura miki ne kawai, harma ina shirin juyawa sai kuma ga saƙonki”.
Ajiyar zuciya Maanal ta sauke, zuciyarta na sake ƙarfafata akan RK ɗin. Tabbas bata buƙatar yin rayuwar
aure da kowa. Hasalima bata da burin yin auren kwata-kwata. Amma tasan iyayenta da ƴan uwanta bazasu
bari ba. Sai kuma Ajwaad, dole ne ta tabbatar masa da abinda yake ganin bazata iya ba. Zatai auren a cikin
zuri'arsa kodan tabbatar masa da wannan Maanal ɗin ta yanzu tafa banbanta da wadda ya sani a baya.
Miƙewa kawai tayi ta ɗan gyara hijjab ɗinta na salla da har yanzu bata cire ba, sai ɗan turare data ƙarama
jikinta ta fita. Babu kowa a falon dan su Barrah na tare da Abbansu basu dawo gidan ba. Kitchen ta shiga ta
ɗauka ruwa a tray da glass cup. A karo na farko ta nufi falon baƙi sannan ta fita compound inda RK yake.
Iso tai masa zuwa falon baƙin, hakan sai ya sake bashi mamaki sai dai baice komai ba ya bita.
Koda suka shiga ita ta zuba masa ruwa da kanta sannan ta zauna. A karan farko da yaji ya kasa
daurewa ya furta, “Gaba ɗaya sai mamaki kike bani. Gani nake kamar bake ba”.
Guntun murmushi kawai Maanal tai masa. Sai kuma ta kallesa. “Idan kiɗa ya canja itama rawar canjawa
take yi ai. Ina son ka san yanzu muna akan gaɓar serious ne”.
“Hakane. Nima hakan nafi so mu kasance ɗin Maanal. Na kuma ji daɗi da godema ALLAH daya kawo
mu wannan gaɓar ɗin.”
A hankali ta haɗiye ƴan kwallar data ciko idanunta. “Ɗazun mun fara magana sai dai bamu ƙarasa ba,
shiyya nace kazo yanzu dan in sha ALLAHU kamar yanda na sanar maka gobe zan wuce Kaduna.” batare da
jiran amsarsa ba ta miƙa masa diary ɗin data shigo da shi a cikin wata kyakkyawar bag. Amsa yay yana ciro
sa daga jakan, sai kuma ya ɗan jujjuya shi a cikin hannunsa sannan ya ɗago ya kalleta. Itama shi take kallo,
dan haka ta janye nata idanun.
“Na yarda da kai fiye da yanda kake zato. Badan komai ba sai dan wasu dalilai. Sannan kai ɗin koba
komai jinin Oum ne. Wadda nake kallo uwa nagartacciya bayan mahaifiyata. Kaje da wannan zaka samu
dukkan tarihin rayuwata data shuɗe a ciki, dan in har akwai abinda na rage ban rubuta ba to zai kasance
ƙalilan ne, ko kuma baida muhimmanci. Bayan ka gama karantawa zaka iya sake tun-tuɓar Oum dan sake
samun gamsuwa. Daga nan sai ka yanke dukkan hukuncin daya dace koyaya ne zan amshe shi. Dan ALLAH
in har baka gama karanta shi har ƙarshe ba kada ka kirani a waya, kada kazo kaduna.” daga haka ta miƙe
tsaye, shi dai kallonta kawai yace yama rasa abin cewa.
“Dare ya farayi sai da safe”
A karo na farko ya ɗan ja numfashi ya fesar, sai kuma ya jinjina mata nasa kan yana miƙewar shima. Haka
suka fito a tare kamar wasu kurame. Dai-dai nan motar Abdull ke shigowa gidan. Duk tsayawa sukai suna
kallon motar har wanda ke ciki suka gama fitowa. Da mamaki RK ya furta, “Abdul-hakeem”. Sai kuma ya
juya yana kallon Maanal. Itama shi ɗin ta kalla, tare da faɗin, “Ka sanshi ne?”.
Kafin ya bata amsa Yaseerah ta fito da Huznah, fuska duk facin bandage musamman ɓarinta na dama.
Nufarsu RK yayi, dan haka badan taso ba itama tabi bayansa. Duk da Abdull yayi mamakin ganin RK a gidan
sai ya danne, sai da suka gaisa RK yake tambayar abinda ke faruwa idonsa akan Huznah. Bayani Abdull yay
masa a taƙaice. Kamar RK ɗin zai yi magana sai kuma ya fasa ya juya yana kallon Maanal.
“Inaga ni bara naje, ki musu iso ciki ko?”.
Kai kawai Maanal ta jinjina masa, sai kuma tai masa ALLAH ya kiyaye hanya tai gaba abinta batare da tace
ma su Yaseerah komai ba.. Suma komai basu ce ɗin ba suka bita kawai, yayinda Abdull yake ta satan kallon
Maanal ɗin. A ransa yana raya aji da nutsuwar yarinyar, gata ƙyaƙyƙyawa da wani skin nata mai ɗaukar
hankali da yay ƙaranci ga matan wannan zamanin da suka maida kansu fararen dole da bleaching.....
Gaba ɗaya Shahidah kasa cewa komai tai da bayanin Abdull ɗin. Dan Yaseerah taso su ɓoye amma
Abdull ya kware zance ga mijin Shahidah abinsa, dan shi dai namiji ne babu ruwansa. Godiya sukai musu,
suma suka miƙe suna musu sallama dan dare ya fara. Dama ita Maanal bama ta tsaya a falon ba ganin
kallon ƙurullar da Abdull ɗin ke mata a kaikaice duk da kuwa hijjab ne a jikinta har ƙasa. Ko bayan
wucewarsu da Huznah ta shigo ɗakin Maanal bata kulata ba, tanata ma haɗa ƴan abubuwan da zata wuce
da su Kaduna ne kawai. Itama Huznah ɗin bata kulata ba tai kiran mamanta a waya. Basu wani jimaba
sukai sallama dan ta sanar mata ne kawai zata dawo Kaduna gobe....
_______________★
A Kaduna kam kamar yanda Daddy ya faɗa sunje Kebbi garin Giro asalin tushen su Maanal. Sai dai an
samu saɓani tsakaninsu da manyan da ya kamata su gana da su. Dan kuwa an tabbatar musu kakarta da
babanta da baffanta sunje Kaduna, wani kuma babban Senator ne ya aiko aka ɗaukesu a mota wai zasuje
wajen Asiya daya tabbatar musu yasan a inda take.
Rasama abin faɗa Daddy yay, Dan ya rasa yanda zai fassara zancen musamman akan batun senator da
suka ce. Haka dole suka baro garin gwiwa a sage. Basu iso gida ba sai dare, zuwa lokacin kuma kowa yay
barci, sai dai hakan bai hanashi zuwa ya sami Ammie a sashensa ba tana jiransa. A kallo ɗaya da yay mata
ya fahimci hankalinta a matuƙar tashe yake kuma.......
___________★
Washe gari Shahidah, Maanal, Huznah da yara suka tashi da shirin wucewa Kaduna. Dan yaran ma
babansu yaje school ɗinsu ya daidaita komai. Jirgin ƙasa zasu bi, dan haka Uncle Sadeeq ɗin da kansa ya
kaisu train station bayan sallar zuhur. Basuyi ko mintuna goma ba suka wuce. Koda suka iso Kaduna Amaal
ce tazo ɗaukarsu. Dan ita kaɗai tasan da zuwan nasu sai Hajiya Basariyya. Itama saboda Huzna ne ta sani
ɗin.
A dai-dai sashen Ammie Amaal tayi parking motarta. Bata ko gama kashewa ba Huznah tai ficewarta
daga motar. Da kallo duk suka bita, sai kuma Amaal ta taɓe baki da faɗin, “Wawuya kawai”. Babu dai
wanda yace komai tsakanin Maanal da Shahidah. Sai ma ficewa da sukai daga motar suma. Itama Maanal
bata jira su ba tai sashen Ammie da sauri, dan kewarta take sosai, burinta kawai ta ganta a jikin Ammien.
Da sallama ta buɗe ƙofar, sai kuma ta ɗan tsaya turus tana kallon yarinyar dake ƙoƙarin buɗe ƙofar itama
alamar zata fito. Yarinyar Maanal ta zubama ido. Dan sam bata santa ba. Itama dai yarinyar kallonta take
yi. Sai kuma ta nuna ƙofar dake da takalma kusan ƙafa goma tana faɗin, “Ki shigo mutanen gidan suna ciki.
Muma baƙi ne yau muka zo”.
Kamar Maanal zatai magana sai kuma ta jinjina kai kawai tayi gaba, a ranta tana maimaita zancen
yarinyar da daga gani zatai ɗan karen surutu. Sallama ta sake yi bayan yarinyar ta matsa ta bata hanya,
batare da jiran amsa ba kawai ta shiga ɗauke da handbag nata tana faɗin, “Ammie, Hameed, Waleed wai
duk kuna in......”.
Turus ta haɗiye sauran maganar sakamakon saukar idanunta akan Ammie dake zaune kanta a sunkuye
kamar ma tana kuka. Da sauri ta saki bag ɗin hannunta ta nufeta, a gabanta ta durƙusa tare da riƙo
hannunta tana mai leƙa fuskarta. “Ammie miya sameki kamar kina kuk....?”.
Nan ma ta kasa ƙarasawa ganin fa da gaske kukan Amma keyi. Amma sai Ammie ɗin ta sakar mata
murmushi da sake jimƙe hannunta cikin nata tana ƙoƙarin sharce hawayen da ɗayan hannun. Ina tuni
Manaal da zuciyarta ta tsarga tai wata irin juyawa tana kallon wanda ke cikin falon. Nene ta fara kalla. Sai
Daddy, sai wani dattijo daya sata ɗan sakin baki, tana kai dubanta ga wanda ke a gefensa ta miƙe zambar,
jikinta har wani tsuma yake ta nuna tsohuwar dake a gefen mutumin da ta zuba mata idanu. Sai dai kuma
ta kasa ma magana lips ɗinta ne kawai ke ɗan karkarwa. A hankali Ammie ta riƙo hannun nata cikin
tsawatarwa ta ce, “Manaal minene haka kike yi. Ki zauna ki gaishe su”.
“Ammie never!!”.
Ta faɗa wani irin kuka dake zuwa maka batare daka shirya ba na kufce mata. Hannunta dake cikin na
Ammie ta warce ganin mutumin ya yunƙura ya miƙe da alama wajenta zai nufo. Tuni tai ƙofar dake cikin
falon da gudu abinta tana sakin wani irin kuka mai ban tausayi da taɓa zuciya. Duk kallo suka bita da shi.
Yayinda mutumin ya furzar da zazzafar iskar bakinsa maƙoshinsa na wani irin kaikawo a wuyansa da sauri-
sauri alamar shiga tsananin damuwa. Tsohuwar nan ya kalla, itama kallonsa take cike da damuwa. Kanta ta
ɗan girgiza masa. Sai ya sake furzar da huci mai kauri yana komawa ya zauna a inda ya tashi saboda
maganar da tsohon nan yay masa.
Nene ce ta katse shirun nasu da faɗin, “Kuyi haƙuri mu bata lokaci zata huce. Kunga ana saka ran sai
ma gobe in ALLAH ya kaimu zata iya tazo gata ma tazo yau babu zat.......” Sauran maganar ta maƙale
sakamakon shigowar Shahidah da Amaal dake dariya Barrah da Haneeff biye da su... Sororo Amaal da
Shahidah sukai suma cikin wani yanayi, sai Shahidah ce tai ƙarfin halin juyawa ta ɗan kalla Ammie. Ganin
kan Ammie a gefe ita bama kallon ta inda suke take ba ya sakata maida kallonta ga Amal da itama ta ɗago.
Sai kuma duk suka maida kan suka duƙar ƙasa fuskokinsu na sake bayyanar da fushinsu. Nene ce tai ƙarfin
halin musu sannu da zuwa. Sai kuma ta nuna musu wajen zama na kujerun dake kusa da su.
Wani irin tsuma jikin Babu dake tsaye kamar ma wanda ya daskare yake, gashi ya zubama Amal da
Shahidah idanu kawai...
“Shahidah bakuga baƙi bane?”.
Nene ta faɗa cikin son katse musu yanayin. Kallonta duk sukayi, da ido tai musu nuni da mahaifin nasu.
Wani irin taunar lips Amal tayi, sai kuma tai yunƙurin barin wajen tana hawaye. Ganin haka yasa itama
Shahidah yunƙurawa zata bar wajen da sassarfa, amma sai carab Babu ya riƙo hannunta. Cak ta tsaya
hawayen da take riƙewa na rige-rigen zubowa.
“Shahidah”.
Ya kirata cikin tsananin taushin murya da sanyi. Hawayenta ta share tare da juyowa cikin dakiya ta
kallesa. Hannun nata ya saki, dan duk da ba kallon raini ta masa ba ko wulaƙanci har tsakkiyar ransa yaji
nauyi da tasirin kallon. Batace masa komai ba itama tabar wajen tabi ƴar uwarta data shige ɗakin Ammie.
Duk abinda ke faruwa a idon kowa ne harda Daddy dake a falon, hatta Ammie datai uwar watsi da su tana
kallonsu ne ta gefe ido......
Tsohon nan ne yayi murmushi, da faɗin, “Masha ALLAHU girman ɗan mutum ba wuya. Shekara bakwai
da wasu watanni kawai da bamu gansu ba sai duk suka canja mana kamar ba su ba”.
Murmushi Nene ta sake yi mai faɗi, “A sosai su Maanal duk sun canja musamman ma Maanal ɗin. Dan
wannan gaba ɗaya ba waccan Maanal ɗin da kowa ya sani bace ba. Sai dai muyi fatan kuma yanzu ALLAH
ya kawo miji na gari”.
A tare suka amsa da Amin. A hankali Ammie ta miƙe tana faɗin tana zuwa. Babu wanda ya dakatar da ita
ta nufi ɗakin da Maanal ɗin ta shiga, dan tafi tsoron yanayinta fiye da na Amaal da Shahidah. Gashi taga su
ɗakinta suka shiga, ita kuma Maanal nasu ta shiga.....
Fitowar ta daga bayi dai-dai da shigowar Ammie ɗakin. Juyawa tai da sauri zata koma cikin bayin
Ammie ta dakatar da ita.
“Maanal!”.
Cak ta tsaya sai dai bata juyo ba. Sai ma hawaye dake rige-rigen zubowa daga idanunta wanda dama su
takeyi tunda ta shiga wankan. Cikin ɗacin murya da fitar sautin kuka ta ce, “Ammie waya kawosu garemu?
Mi sukazo yi mana? Mi suke buƙata kuma yanzu a garemu. Ko anan ɗin ma sun zo su koremu ne? Sun zo su
sake tozartamu a idanun mutanen arziƙinmu na nan ne suma? Ko sunzo su sake shegantamu su aibanta
ki.....” kuka yaci ƙarfinta ta kasa cigaba da maganar. Hannu Ammie takai ta share hawayen da suka wanke
mata fuska itama. Tare da matsowa kusa da ita, hannunta ta riƙo tare da juyo da ita suna fuskantar
juna...........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
5️⃣4️⃣5️⃣4️⃣
______________
......... “Maanal!”.
Ammie ta kira sunanta cikin rawar murya tana mai share mata hawaye da sakin murmushi mai ciwo. Da
ƙyar ta sake ƙoƙarin yin magana amma ta kasa saboda muryarta dake neman sarƙewa. Sai kawai ta jawo
Maanal ɗin jikinta ta rungumeta tsam-tsam. A tare suka saki kuka mai ƙarfi.
“Ammie kice su tafi, bana son ganinsu wlhy. Sam bana ƙaunar sake ganinsu a rayuwata. Ko tunasu nayi
ƙara jin tsanarsu nakey.....” yanda take magana cikin kuka itama Ammien cikin kukan ta ce,
“Shiiiiii bana son irin wannan maganar sam Maanal. Shi ɗin mahaifinku ne. Ita ɗin kakarku ce. Sunada
muhimmanci mai girma da hakki a kanku. Koma mi kike tunani ki bari kinji, wannan tsakanin ni da su ne.
Kuma ai komai ya wuce ko”.
“Bai wuceba Ammie, bakuma zai wuce ba, har abada kuma bazai wuce ba. Ni dai kawai su tafi. Idan ba
hakama zan bar musu gidan. Gara na wuce na koma Abujan. Idan sun wuce sai na dawo”.
“Babu inda zaki je Autana. Kin san yanda nayi kewarki kuwa. Wata nawa ban ganki ba sai video call da
bai gamsar dani. cikin lallashi Ammie take maganar, tare da kama Maanal suka koma bakin gado. Sosai
take matuƙar ƙaunar Autar ta, dan ita ta fuskanci jarabawa guda uku ne a lokaci ɗaya. Shiyyasa ta fisu
jigata da galabaita. Ga babbar jarabawar ciwo mai haɗari da take tare da shi. ALLAH ma dai ya ƙaddara
tana da sauran kwana da tuni ta zama tarihi a cikinsu. Shigowar Nene ya katse Ammie daga lallashin
Maanal ɗin. Kofin hannunta ta miƙama Maanal ɗin da faɗin, “Ga masoyiyar taki tunda kun mamemu,
muda ke muku shirin zuwa wani satin biki sai kawai ku diro mana yau babu notis ja'irai kawai”.
Hannu takai ta share hawayen da suka gagara tsaya mata. Fuskarta a ƙwaɓe ta ce, “Ni garin ya isheni
Nene kuma ina kewarku sosai.”
Cike da dabara irin ta manya Nene ta sanya dariya da dungure kan Maanal. “Ja'ira baki son garin
amma gaki nan kinyi ƙyau ai. Nifa har wani ɗan ƙiba naga kinyi ma, ji kumatu dan ALLAH ko Asiya?”. Ta ƙare
maganar da kallon Ammie tana jan kumatun Maanal. Murmushi Ammie tayi cike da ƙara jin ƙaunar Nene
dake tamkar mahaifiyarta a yanzu, ta matuƙar taka rawar gani akan lamarin Manaal musamman a sanda
take a halin mutuwa da rayuwa. Ta jinjina kanta da share sauran hawayenta tana faɗin, “Sosai kuwa Nene.
Autah tayi ƙiba ba kamar sanda ta dawo sarvese ɗin nan ba. Ga fatanta yay wani kwanciya luff abinta halan
ma bata tunawa damu ne a can”.
Da sauri Maanal ta waro idanu akan Ammie, sai kuma ta shagwaɓe fuska da faɗin, “Kai Ammie kema
kina biyema Nene ko?”.
Dariya Nene da Ammie sukayi a tare. Nan fa suka cigaba da tsokanar Maanal har sai da sukaga ta ɗan
sake tasha kunun gyaɗar da Nene ta kawo matan. Ammie da kanta ta ɗakko mata kaya ta tashi ta shirya.
Tana ƙoƙarin maida towel ɗin datai wankan cikin toilet Daddy yay sallama....
___________★
A bala'in hargitse Hajiya Basariyya ke kallon Huznah. Hakama sauran ƴan uwanta. Sai kuma duk suka
zaburo kanta suka baibayeta suna tambayarta accident tayi?. Babu wanda ta iya amsawa a cikinsu, hakan
yasa Hajiya Basariyya ta kama hannunta kawai suka shiga bedroom. Kamar jira take suna shiga ta rungume
mahaifiyar tasu tana mai fashewa da kuka. Ƙanƙameta itama Hajiya Basariyyar tayi hankalinta na ƙara
tashi. Sai dai bata iya cewa komai ba har sai da Huznah tai kuka sosai sannan. Ruwa ta bata tasha kafin ta
tambayeta abinda ke faruwa.
Huznah bata ɓoyemata komai ba daya faru tun daga zuwanta Abuja har yau da suke tahowa. Shiru tayi
tana nazarin komai daki-daki. Ta jima shiru kafin ta miƙe tana cema Huznah, “Tashi kije kiyi wanka zan saka
Afrah ta kawo miki abinci da magani, sai kisha ki kwanta ki huta zamuyi magana anjima”.
Kai kawai Huznahr ta jinjina mata itama....
Ɗaki Hajiya Basariyya ta shiga tare da ɗaukar waya tayi kiran aminiyarta. Bugu biyu kuwa ta ɗaga, ko
gaisawa basuyi ba ta ce, “Aminiya akwai matsala fa?”.
“Matsala kuma Aminiya! Tami?”.
Tsaf ta zayyane mata komai da Huznah ta sanar mata. Cikin jinjina al'amarin Maman Yaseerah ta ce, “Eh
lallai akwai matsala. Dan kuwa Darma family da su Majdiya jini ɗaya ne, auren zuminci ne tsakanin Aliyu
Darma da babbar yayarsu Fateema. Amma Aminiya miyyasa tun farko baku sanar min cikakken sunan
yaron ba?”.
“Wlhy nima iyakar abinda na faɗa miki shi na sani, itama kuma Huznahr na tabbatar shi kaɗai ɗin ta
sani”.
Ajiyar zuciya Maman Yaseerah ta saki, sai kuma ta jinjina kanta da faɗin, “Aminiya wannan maganar tafi
ƙarfin waya kizo kawai”.
“Okay in sha ALLAHU cikin satin nan kafin a fara bikin nan zanzo. Ai dole ma na shigo dan na fahimci
al'amarin nan shiri yake so na haƙiƙa. Babu ruwana da wata alaƙar yaron da Majdiya, koma ya suke sai
Huznah ta mallakesa tunda tana sonshi kuma yana da kuɗi”.
Dariya Maman Yaseerah tayi daga can, sai kuma ta ce, “Ina bayanki wlhy. Ni kin ma tuna min miya faru
ne wai naga jiya Alhaji ya dawo da dare, yau kuma da safe naji suna waya da Alhaji Usman akan zai zo
kadunar”.
“Wlhy bamu san abinda ke faruwa ba muma. Tashi mukai kawai muka ganshi a gidan. Ina shirin naje
na bincika da safe sai kuma ga baƙi anyi ban san daga ina ba, naga dai ya shiga dasu sashen Asiya, yanzu
kuma sai ga ƴaƴanta da Huznah”.
“To aiko kiyi azamar bincikawa. Dan al'amarin kamar ba ƙarami bane, ina kuma ƙyautata zaton wannan
baƙin sun fito ne daga zuri'ar ita Asiya da yaran nata ne”.
“Iye! Ya akai kika sani?”.
“Ba tabbatarwa nayi ba nima. Amma ga Alhaji nan na shirin tahowa Kaduna ɗin ma, amma lallai akwai
abinda ake ɓoye muku”.
“Tab ɗin cakwakiya kenan, a lallai dole ne na bincika, ko dama shiyyasa naga tun jiya Uwar ɗan ke cika
da batsewa, ban san miya faɗa mata ba mai gidan, haka itama Asiyan duk tayi sukuku”.
“Humm munafukai, wannan gida naku ai sai ku, na tabbatar akan auren ƴayan nasu ne”.
“Wlhy fa sai mu. Kinga bara naje kozan samesa a sashen nasa zan kiraki daga baya. Amma ki farama
Malam bayani akan al'amarin dai kafin na shigo, dan ƙilama zuwa gobe zan shigo kawai in sha ALLAHU”.
“To shike nan hakan ma yayi, sai na jiki”.
Daga haka sukai sallama kowa ya ajiye wayar. Shiru Hajiya Basariyya tayi zuciyarta cike da tambayoyi fal.
Sai dai rashin makamar riƙewa yasa ta tattara komai ta ajiye gefe. Fitowa tai ta shiga ɗakin Huznah. Sai ta
sameta ta fito wanka tana shafa mai. Zama tai har sai da ta kammala ta shirya ta taimaka mata taci abincin
tasha magani ta kwanta sannan ta tashi ta fito. Sashen Daddy ta nufa, amma sai ta samu yana tare da baƙi.
Haka dole ta fito bayan ta gaidasu dan ya haɗe fuska ta yanda bataga wajen wargi ba balle samun damar
yin halin nata na munafunci..
Shima Daddyn ɗan girgiza kansa kawai yay yana mai kai ɗauke idanunsa daga kallonta. Dan yaji a ransa
wani tsegumin ne kawai ya kawota......
____________★
*_TUNA BAYA.._*
Sautin kukanta a maimakon sallama daya karaɗe gidan ne ya saka mahaifiyarta da ƴan uwanta fitowa
kusan a lokaci guda. Sai dai babu wanda yay magana sai ido da suka zubama ɗan saurayin yaron dake goye
da ita a bayansa da ita kanta mai kukan.
Kallo ɗaya yay musu batare da yayi magana ba ya ƙarasa ga tabarmar dake a jingine jikin bango ya
ɗauka ya shimfiɗa. Kafin ya sauketa a hankali tamkar mai tsoron yaddata ƙasa. Ita kam kamar wadda ta
ɗosana a kan wuta. Yana direta a saman tabarmar ta wani sake ƙwallarewa da ihun kukan nata. Cikin ɗan
nuna rikicewa da sake bayyana damuwarsa akan fuska ƙarara ya juyo gareta. Ƙafar da take ɗangalewa ya
riƙe. “Banace kiyi shiru zan rama miki ba. Na rantse miki daga nan gida kawai zan shiga na ɗauka kekena
har gidansu sai naje na rama miki. Sannan na masa dukan tsiya”.
“To ni ka tashi kaje”. Ta faɗa cikin taɓara da ƙara ƙarfin ihun kukanta. Bama ta gama rufe bakin ba ya
miƙe. Fisha ya kalla matar dake tabbatar da mahaifiyar yarinyar ce saboda kamanninsu. “Ammie dan
ALLAH ki saka min ruwan zafi a ruwa yanzu zanje na dawo zan gasa mata ƙafar”.
Cikin sauri Ammie tai ƙoƙarin dakatar da shi ta hanyar kiran sunansa. Sai dai ina har ya fice da mugun
hanzari da sassarfa. Kanta ta ɗan dafe tare da maida dubanta ga ƴar budurwar da zata iya kai shekaru
goma sha ɗaya. “Amaal! Kinga maza bisa gida kicema Oum-Fadeel karta barsa ya fita”.
“To Ammie!”. Yarinyar ta faɗa cikin hanzari itama tana fisgar hijjab. Dai-dai nan Ammie ta dawo da
kallonta kan yarinyar data sake wani ƙwallara uban ƙara tana tittirza ƙafafu da faɗin, “Ni dai kar a hanashi.
Sai ya ramomini....”
Tsawa Ammie ta daka mata. Tare da nunata da yatsa. “Idan baki min shiru ba na rantse da ALLAH zan
tsantsama miki jiki da magribar nan. Ai dama tunda naga kun jima baku dawo ba nasan kina can ɗaukar
maganar da kika saba. Shima Ajwaad ɗin sakarai dake biye miki, kin tashi kin cire uniform ɗin ko sai na ci
ƙaniyarki....”
Kuka ta sake fashewa da shi amma bamai sauti ba yanzu dan tana tsoron Ammie. Sai kuma ta nuna
ƙafar tana faɗin, “Ammie nafa karye ne a ƙafar...”
“Karyewa?”.
Ɗayar yarinyar da zata kaiwa sa'an saurayin yaron, idan ma ta girmesa kaɗan ne dake tsaye tana kallonta ta
faɗa kafin ma mahaifiyar tasu ta amsa.
“Eh wlhy Didi. Ba Najib ɗin gidan Maman Ayna bane ya bugeni da keke mun fito islamiyya. Kuma
shine yaƙi tsayawa harda cema Besty wai in ya isa yazo ya rama min”.
Shigowar Amaal da wata ƙyaƙyƙyawar mata mai kama da yaron sosai yasa babu wanda ya tanka mata.
Matar ta nufeta tana faɗin, “Subahanallahi Baby na miya faru?”.
Fuska ta taɓe tana satar kallon Ammie, sai kuma ta ɓarke da kuka tana nuna ƙafarta da shigewa jikin
matar da takai kusa da ita zaune. “Oum ba Najib bane ya karyani a ƙafata. Kuma na kasa tafiya sai da Besty
ya goyoni ma”.
Sosai Oum ta shiga faɗa tana dudduba ƙafar da faɗin in fa har taji ciwon da gaske bazasu yarda ba.
Ammie da taga abin nasu bana ƙare bane ta katseta da faɗin, “Aunty ALLAH ki daina biyema iskancin
Manaal. Ni yanzu ma sonake nasan baki dai bar Ajwaad ya fita ba ko?”.
Kafin Oum ta bata amsa Amaal ta ce, “Wlhy Ammie ya tafi, inata kiransa ko kallona baiyiba ma ya
kwashi keke da gudu”.
“Innalillahi banga ta zama ba”. Ammie ta faɗa tana shiga ɗaki. Babu jimawa sai gata ta fito da hijjabi a
hannu. Sai lokacin Oum ta dubeta tana dariya. “Wai ina zaki je?”.
“A binsa zan mana. Sai na bari a cutar min da yaro tunda ke naga kinama ɗaukar abun bada
muhimmanci ba, in dai kika biye ta wannan yarinyar wataran sai ta saka har ke an kai station ɗin ƴan
sanda” Bata jira amsar Oum ba ta fice abinta.
Fitowar Ammie a gidan dai-dai da isowar Ajwaad a kekensa rigarsa ta islamiyya a yage. Fuskar nan ciɗin-
ciɗin ga goshinsa ya ɗan kumburo kaɗan, sai gefen lips ɗin da jini kaɗan shima. Da sauri ta nufesa tana riƙe
keken da faɗin, “Innalillahi Ajwaad, yanzu faɗan kaje kayo saboda ALLAH. Anya wataran Manaal bazata
saka a maka dukan da zaka kasa tashi ba a anguwar nan?”.
Cikin ɓacin ran da muryarsa dake fita can ƙasa-ƙasa ta kasa ɓoyewa ya ce, “Ammie ciwo fa yaji mata
a ƙafa, sai na ƙyalesa yaci bulus? Ko yanzu ban ƙyalesa ba sai na jera sati ina masa duka”.
Ƙasa magana ma Ammie tayi ta zuba masa ido kawai. Har ya shige shi da keken gidan bata iya ta motsa
ba. Wannan abota na bata mamaki tsakanin Manaal da Ajwaad. Wata irin abotace mai ban mamaki da
tsayawa a zuciya. Basu kasance sa'anni ba dan ya girmeta sosai kusan shekara bakwai ne tsakaninsu ma,
sannan basu kasance jinsi ɗaya ba. Amma akwai wata irin shaƙuwa a tsakaninsu da sam babu ita a
tsakaninsu da ƴan uwansu na jini ma. Ita abun har tsoratata yake yi.........✍️
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
5️⃣5️⃣5️⃣5️⃣
______________
.......Su ɗin ƴan asalin jihar Kebbi ne, a garin Giro dake ƙarƙashin Suru LG. Aiki ne ya kawo mijinta nan cikin
Kano kasancewarsa jami'in ɗan sanda. Ba Kanon suka fara zama ba. Sun zauna jihohi kusan uku a tsahon
shekarun aikinsa. Sai dai shekara biyu data wuce aka maidosu nan cikin Kano suke zaune a anguwar
sharaɗa. Yaransu uku ne duk mata. Shahidah itace ta farko, sai Amaal. Sai Manaal. Lokacin da sukazo Kano
shekarar Manaal huɗu kacal, amma sai baƙar fitina a cikinta da shegen surutu. Manaal irin yaran nan ne
masu shegen wayon tsiya da ɗan karan surutu kamar an musu ƙauri da kan akku. Ga ɓarnar masifa da jan
faɗan tsiya. Sam bata ragama ƴaƴan jama'a dan ko anfi ƙarfinta saita ƙwaci kanta da cizo da bula ƙasa ko
jifa. Gata suke mata matuƙa kasancewar itace kamar auta a gidan yanzu. Kowa ya kwaso abunsa zai ce
Maanal. Musamman ma mahaifinsu da suke kira Baabu.
Dawowarsu cikin Kano sun samu abubuwan cigaba da dama, ciki harda ƙarin girma da Baabu ya samu,
ita kuma ta fara kasuwancin turarruka da gyaran jiki irin na mata. Inda suke sabon wajene da aketa gine-
gine, dan ko gidan dake a jikin nasu ma ana kan gina shi ne ba'a kammala ba. Sai dai an kusa kammala
aikin. Hakan yasa kusan kullum zakaga mai gidan yazo da yaransa maza uku musamman ma weekend. Jefi-
jefi sukan ɗan gaisa da Baabu idan anyi sa'a yana gida ko ya dawo wajen aiki. A haka ranar wata asabar
yana gida suka tashi da shirin yin alala da yace yana buƙatar ci. Ammie ta kammala gyara wake ita da
Shahidah da zata kai markaɗe. Sai kawai Maanal ta sanya rigima itama zataje. Cikin haushi Shahidah ta ce,
“Dama kin bar damun kanki dan babu inda zanje dake. Haka kawai muje kita jibgar yaran mutane a gidan
markaɗen kamar ranar da kika fasama ƴar mai markaɗen kai”.
Ihu Maanal ta sake ƙwallarawa tare da zubewa ƙasa tana burgima akan ita wlhy sai taje fa. Dai-dai nan
Ammie ta fito da bulala da nufin tsula mata amma sai Baabu ya hana ta hanyar amshe bulalar ya ɗaga
Maanal daga ƙasan. Daga haka ya fita da ita a gidan yana lallashinta. A dai-dai lokacin motar makwafcin
nan nasa ta iso anguwar. Baabu bai wani maida hankalinsa ba dan baima san shi bane kasancewar bawai
ya wani riƙe motar tasa bane. Sai da yay parking a gaban gidan nasa ya fito tare da matasan samarin
ƴaƴansa uku sannan Baabu ya maida hankalinsa kansa. Sun gaisa cikin mutunta juna, yayinda suma yaran
suka gaida Baabu da girmamawa. Ya amsa musu da kulawa yana mai shafa kansu, yayinda shima babansu
yakema Maanal wasa.
“Ƴan samari yaya sunanku?”.
Cewar Baabu yana shafa kan ƙaramin su. Babban ne ya bashi amsa da. “Ni Fadeel. Wannan Fawzan. Sai
Auta Ajwaad.”
“Masha ALLAH, ALLAH ya albarkaci rayuwarku manyan gobe.”.
A tare suka amsa da Amin. Yayinda mahaifinsu keta faman murmushi saboda surutun da Maanal ke zuba
masa. Sai kuma can ta kalla Ajwaad dake ta faman cin chocolate ɗinsa, cikin ɗan tura baki ta ce, “Kai yaron
nan bazaka tsammin alawanka bane. Inata haɗiyan yawu amma sai sha kakeyi rowa haramun dai”.
Ba ƙaramin dariya ta basu ba. Banda Ajwaad ɗan kimanin shekaru goma sha ɗaya daya wani yamutsa
fuska ya harareta ya ɗauke kansa. Sai Baabu da ya ɗan harareta shima. Amma ita ko'a jikinta ta maida
kallonta ga Babansu ta na sake faɗin, “Abbansu kace masa ya tsammin raina ya biya”.
“Kinga manta da shi Babyna. Muje na baki ina da ita da yawa. Daga yau kuma kema ni Abbanki ne ba
nasu su kaɗai ba.”
Cike da murna tace, “Eh”.
Gaba yay da ita zuwa motarsa. Ya fiddo chocolate uku ya bata biyu a hannu, tare da ɓare ɗaya ya sake miƙa
mata. Cike da jin daɗi ta amsa. Tare da juyawa ta murguɗama Ajwaad baki da faɗin, “Mai rowa ɗan wuta.
Nima kuma ga nawa”.
Harararta nan ma yayi. Yayinda su Fawzan sukayi dariya. Shiko Baabu duk kunya ta ishesa. Ƙarfin halin
Maanal da banne a rayuwa. Shegen surutunta da wayonta da suka girmi shekarunta na tada masa da
hankali. Duk inda ake neman fitinannen mutum aka samu Maanal an rufe littafi kawai. Sai dai yana mata
fatan idan ta ƙara girma ta canja daga hakan.. ƙiri-ƙiri da zai shiga gida yace tazo suje taƙi. Dole babu yanda
ya iya ya barta wajen Alhaji kamar yanda ya roƙa.
Yini guda Maanal na tare da Alhaji Aliyu Darma, Tare da yaransa uku da tuni ta saki jiki da su.
Musamman Ajwaad da tunda ya fito da kayan wasansa ta naniƙe masa. Lokacin da rana tayi sai ga
Shahidah da kula cike da alala an kawo musu. Sosai Alhaji Aliyu ya nuna jin daɗinsa tamkar ya ari baki dan
godiya. Anan ma Shahidah tayi-tayi Maanal ta bita suje gida amma taƙi. Dole ta barta itama ta tafi. Sai da
akai la'asar sazu tafi sanan su Fawzan suka rakata har gida da ledan kayan ciye-ciye da kulan da aka kawo
musu alala sukai godiya. Yayinda ita kuma ta shiga kuka saita bisu, sai da Baabu ya mata tsawa sannan ta
nutsu. Dan a duniya Maanal na tsoron hargagi musamman na Baabu..
Wannan rana itace sanadin tarayyar waɗan nan ahali guda biyu. Dan kuwa washe gari sai ga itama
mahaifiyar su yaran ta biyosu domin yin godiya. Anan ne kuma ta tarar da Ammie nama wata amarya
gyaran jiki, itama tace ai sai ai mata kuwa.. tunda tazo Maanal na manne da ita. Kasancewar yaranta ita
duk maza ne tana masifar son ƴar budurwar yarinya, shiyyasa tana ganin Maanal da jiya tasha labarinta a
wajen ƴaƴanta yarinyar ta shiga ranta. Ga wayonta da surutunta na sakata nishaɗi. Yau ɗin ma dai da ƙyar
aka raba Maanal da su, musamman Ajwaad da wasansu na yau yafi na jiya armashi. Dan yau ya saki jikinsa
ba kamar jiyan ba. Haka yake bashi da saurin sabo sam, akanyi baƙi a gidansu kwana da kwanaki babu
ruwansa da su, dan shi yarone mai irin shegen tsantsenin nan, ga zuciyar tsiya da ƙulafucin iyaye. Ammafa
idan ya soka to yaso ka kenan. Idan kuwa baka masa ba to babu abinda zakai masa ka birgesa ko kaja
ra'ayinsa da shi. Shiyyasa a yau ɗin ma mamakinsa ya kasa barin Oum ganin yanda ya saki jiki a gidan
tamkar a gidansu. Dan duk inda kaga Ajwaad yaje yaci maka abinci kansa tsaye to lallai yanayi da masu
gidan....
★★★
Kafin Alhaji Aliyu ya kwaso iyalansa su tare a sabon gidan nasu daya haɗu matuƙa gaya shaƙuwa da
zuminci mai ƙarfi ya shiga tsakaninsa da iyalan Baabu ta yanda har suna kallon kansu tamar wasu ƴan uwa
na jini. Oum ba itace kawai matarsa ba, ashe tana da amarya ma, sai da suka tare su Ammie suka sani.
Bayan tarewar tasu kuma sai al'amarin ya ƙara ƙarfi fiye da tunanin mai hasashe. Ba shaƙuwar ahalin biyu
ne kawai abin mamaki ba. Wadda ke a tsakanin Ajwaad da Maanal tafi zama abin kallo ga kowa. Dan takai
a yanzu ako ina ɗaya yake ɗaya na wajen, shiyyasa idan baka sani ba baka taɓa gane ainahin gidan
kowannensu. Dan takai yanzu ma Maanal taƙi zama a makarantar da take yi da yan uwanta. Da safe anta
dagama kenan tace ita Ajwaad zata bi tasu makarantar. Anyi lallashin, an daka, anyi kurarin duk a banza.
Hakan yasa Alhaji Aliyu roƙar Baabu damar maida Maanal makarantar su Ajwaad ɗin, kasancewar itama
tana tare da Nursery, primary harda da secondary ne a tare. Daƙyar Baabu ya yarda dan bashi da yanda ya
iya, haka aka maida Maanal makarantar su Ajwaad amma a ɓangaren Nursery. Shiko yana a primary 3 ne.
To ashe rigima bata ƙare ba, dan kuwa Maanal sam bata zama ajinsu saina su Ajwaad. Anyi-anyi amma
taƙi, da malaman sukaga tanada ƙwalwar karatu matuƙa, dan duk abinda akayi kafin kace me ta ɗaukesa a
kanta harma tafi wasu ƴan ajin sai kawai aka ƙyaleta. Dan koma an kaita can ɗin ba zama take yi ba, sai dai
taita jibgar ƴaƴan jama'a tana kukan ita dai wajen AA zataje. (Dan itace ta saka masa AA daga ji Oum ta
faɗa ta kama ta haye tana kiransa AA).
Hajiya Maanalu mai abin mamaki kenan. Dan daga Nursery 2 dai tuni tayi jumping zuwa primary 3
abinta. Hakama a islamiyya tuni ta koma ajin su Ajwaad. Dambe da rigima kuwa sai abinda ya ƙaru. Duk da
tana a cikin waɗanda suka girmeta kullum cikin takalar tsiya take. Taimaka rashin kunya kace zaka daketa
ka gamu da Ajwaad. Dan duk abinda zai taɓa Maanal a duniyar nan Ajwaad baya ƙaunarsa. Hatta Ammie
idan ta daki Maanal sai taga fushi a fuskarsa. Idan ko su Shahidah ne duk da sun girmesa koda yake kusan
sa'an Amaal ne yana girmeta kaɗan sai fa yarama mata. Idan kuwa yana gidan tai laifi Ammie tace zata
daketa sai yaje yace shi a dakesa a maimakonta, idan kuma ta riga ta ritsata tana duka zaije ya kareta shi a
dake san. Idan abu aka bama ɗaya ɗaya bazai taɓa cinsa ba sai ɗaya na nan. Hatta da kaya ya koma yanzu
iri ɗaya ake musu, idan kuma ya banbanta na mace da namiji kamar atamfa, lass, yadi to dole a ɗakko kala
guda. Ajwaad shine tsifar kan Maanal, shine rakata kitso, shine wankin ƙananun kayanta irinsu pant, hula,
vest da sauransu. Haka shima nashi idan zai yi tare zasuyi tana jagwalgwalo. Tun ana ɗaukar abun nasu
wasa har kowa ya fahimci ba wasan bane aka kawo ido aka zuba musu. Sai dai iyayen na matuƙar kulawa
da duk wani motsinsu saboda tsoron bin wata hanya mara ma'ana da a yanzu har yaran akan samu a ciki....
Alhamdullah a yanzu dai haka Maanal nada shekara tara cif a duniya, yayinda Ajwaad keda goma sha
biyar. Suna a ajin ƙarshe na primary. Kasancewar Ajwaad nada tsayi kamar ƴan uwansa tuni ya tserema
Maanal a girman jiki fintinkau duk da dama can ya fitan. Itako tana tsaka tsaki a tsayi saboda bata gama
girma ba, gata muguwar siririya kamar ka hureta ta zube a ƙasa. Zuwa yanzu shaƙuwarsu ta sake wuce inda
ake tunanani, baka isa kaji kansu ba. Hatta abinci tare suke cin abinsu. A hakan ma dan ana tsaye a kansu
wasu abubuwan da yawa ana ƙoƙarin hanasu da tunatar da su halacci da haramcin dake a tsakanin iyakar
da alaƙarsu zata yiwu. Kuma Alhamdullah suna fahimta da kiyaye abubuwa da dama duk da bawai sun
balaga bane ba. Garama shi Ajwaad alamomin hakan sun fara kusantoshi yanzu...
__________________★
Yanda take tura baki gaba ya sashi tsayawa yana kallonta. Sai kuma ya ɗauke kansa ya maida ga
agogon falon. Ganinfa idan ya biye mata makara zasuyi ya sashi duƙawa. Dariya ta saki da siririyar
muryarta kafin ta ɗane bayan nasa. Lunch box ɗinta da school bag ɗin dake ajiye ya tattara ya ɗiba sannan
ya miƙe. Dariyarta tasa Ammie dake kitchen leƙowa. Takaici ya sata tsayawa kawai tana kallonsu, sai da ya
kai ƙofa yana ƙoƙarin fita ta dakatar da shi.
“Yanzu Ajwaad bazaka hutama ranka ba dai?. Ka sauketa ta taka da ƙafarta, dan ubanta ba tun jiya ta
taka ƙafar ba”.
Cikin yanayinsa na sanyin murya ya ce, “Ayya Ammie ALLAH ƙafan bai sakin mataba har yanzu. Bari
muje su yaya Fadeel na jiranmu a mota”. Kafin ma ta sake cewa wani abu harya fice. Kai kawai Ammie ta
girgiza tana komawarta, dan babu abinda suke buƙata yaran nan sai addu'a. Idan ta tuna mutuwa zata iya
ɗaukar wani a ciki tabar wani har tausayi suke bata. Idan kaga Ajwaad na farin ciki ko surutu to tare yake
da Maanal. Dan duk rashin son maganarsa sai da ta sakashi ringa yi, idan ma baiyi ba addabarsa take har
sai ya tanka zata barsa. Kokuma taje ta takalo masa faɗan da dole ya tafi ramo mata......✍️.
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
5️⃣6️⃣5️⃣6️⃣
______________
........Tuni su Fawzan har sun shiga mota. Da sauri driver ya amshi kayan hannunsa, shi kuma ya ƙarasa gaba
ya buɗe ya sakata dan nan ne wajen zamanta dama. Sai da ya gyara mata skirt ɗin ta sannan ya rufe ya
zagaya kusa da ƴan uwansa ya zauna. Cikin tsokana da dariya Fawzan ya ce, “Oh oh Lilly bestyn Auta (Dan
haka suke kiranta). Auta bestyn Lilly. Idan yaran nan kuka girma munada kallo a anguwar nan wlhy. ALLAH
yasa dai kar ku haɗiye juna ko ku ƙone mu saboda eh......” ya ƙare maganar cikin shaƙiyanci. Banza Ajwaad
ya masa, sai ma ƙoƙarin fiddo books ɗin Maanal yake yana dubawa. Yayinda Fadeel da suke kira (Babban
yaya) yay ƴar dariya, hakama driver. Tsagal Maanal ta ce, “Yaya F minene eh...? Kuma sai mu cinye kammu
kamar mayu”.
Dariya Fawzan ɗin ya sake kwashewa da shi. Tare da faɗin, “Lilly ba yanzu zaki san eh.. ba. Sai nan gaba.
Ke dai ALLAH yabar tare”.
Cikin rashin damuwa tace, “Amin”. Sai kuma tai kneeling a kan kujerar ta saitin Ajwaad da yay kamar
baya a motar tana lekensa. Cike da shagwaɓa ta ce, “Besty!”.
Ɗagowa yay kawai ya kalleta batare daya amsa ba. Wuyansa ta nuna masa tare da faɗin, “Baka sa tie
ɗinka ba fa”.
Kansa ya maida ya cigaba da gyara mata abinda batai dai-dai ba a assignment ɗin da aka basu da tayi,
dan jiya fushin faɗan da yayo mata bai tsaya ya koya mata ba sai Amaal ce ta mata. Kafin a hankali ya ce,
“Zan saka sai mun sauka”.
“Ohhh”.
Ta faɗa tana cigaba da kallonsa. Duk abinda taga zai gyara mata sai tayi tambaya. Shi kuma ya bata
amsa. Har ya kammala ya maida books ɗin shima ya maida hankali a kanta. Gaba ɗaya ta addabesu da
surutu. Baka jin muryar kowa sai tata. Sai ko dariyar driver da Fawzan masu tayata dan shima Babban Yaya
halinsa kusan irin na Ajwaad ne. Baida yawan magana. A haka dai har suka iso makarantar dan akwai ɗan
nisa. Kasancewar a tsohuwar anguwarsu makarantar take. Ƙyawunta da son da suke mata yasa iyayen basu
canja musu ita ba. Kullum driver zai kawosu ya dawo ya ɗaukesu.
Yanzun ma dai shine ya goyata, Fawzan ya taya shi da ɗaukar bags ɗin su da lunch box ɗin abinci data
kasance ɗaya. Sai da ya rakasu har aji da kayan sannan ya wuce sashensu na yan secondary inda baban
yaya Fadeel ya nufa. Ajwaad kam na sauke Maanal a mazauninsu dan kujerarsu ɗaya ta jawo bag ɗinsa. Zip
ɗin baya ta buɗe ta ciro gogaggen tie dan uniform ɗin nasu kamar suit suke. Sai dai na mata skirt ne na
maza wando. Zama yay a kujera tana daga saman desk ya miƙo mata wuyansa. Tsaf ta ɗaura masa dan tuni
ta iya. Idan ka gansu dolene su birgeka kamar ba ƙananan yara ba. Ta gama ta gyara masa rigar da faɗin,
“Wai Besty mi akai maka kake ta fushi. Inma dan ƙafatace ba nace maka na daina jin zafin ba. Tun jiya fa ka
daina dariya why?”.
Shiru yay baice mata komai ba. Hakan yasa takai hannu saman sumarsa daya gyara ta shiga
harmutsata. Hannunta yay ƙoƙarin riƙewa amma taƙi ta bari. Dole sai da yay dariyar da take so sannan ta
barshi. Cikin dariya ya ce, “Besty wannan wane kalar kuturun wulaƙanci ne”.
Itama cikin dariyar ta amsa masa da, “Kamafi ƙyau a haka ALLAH”.
Rankwashi ya kai mata, ta kauce. Yay ƴar ƙwafa da faɗin, “Zan rama ALLAH ya kaimu Friday”.
“Mi zakayi?”.
Ta tambaya tana ƙoƙarin ɓare lollipop daga cikin ledanshi.
“Meyi baya faɗa ai”.
Ya bata amsa yana fige alawar ya saka a baki. Hararsa tayi, shima ya rama. Sai kuma suka ƙyalƙyale da
dariya. Saida sukayi mai isarsu sannan ta zare alawar daga bakinsa ta sha. Sake maida masa tayi a bakin.
Haka sukaita yi har suka shanye kafin malami ya shigo musu su nutsu kamar basu ba.
Kowa yasan a ajin basa taɓuwa. Maanal rashin kunya da tsokanar masifa, gashi itace ƴar ƙaramar
ajin dan duk sun girmeta tunda rigimarta ce ya kawota cikinsu ba shekarunta ba. Ka taɓata ka haɗu da AA.
Yanada zuciya ga ƙarfi, dan in har ka taɓa Maanal ka taɓoma kanka kuwa. Gashi da shegen naci akan faɗa
dan baya barin saita kwana. Surutun Maanal yasa kullum sai an sakata a cikin ƴan surutu na ajin. Idan kayi
surutu naira ashirin, in sha ALLAHU kafin a tashi sai ta tara ɗari biyu. Idan ance ta bayar taƙi biya, idan
shugaban ajin ya biye mata suyi faɗa AA ya kamashi ya daka. Dole class master ɗin su ya maida
shugabancin ajin akan Maanal ɗin, aiko tunda ta samu damar nan take tsula tsiyarta. Ta cikama ƴan aji
kunne da surutu su suyi ta maka sunanka. Azo biyan kuɗi kaƙi biya Ajwaad yay maganinka. Hakan yasa ake
tsoronsu, ta gefen ƙoƙari kuwa sune masu zuwa na ɗaya dana biyu, basu taɓa tsallake wannan positions
ɗin ba. Ada kafin Maanal tazo ajin AA ke ɗaukar na farko, wata yarinya na ɗaukar na biyu. Amma tunda
Maanal tazo shikenan fa matdayin yarinyar ya rushe. Kullum sune dai su biyun nan, babu ƙoƙarin da wasu
basuyi ba ganin an turesu amma abin ya gagara.
Ada saboda kalar fatarsu tazo ɗaya kowa ɗauka yake Maanal ƙanwar su AA ce ta jini. Duk da babu ta
inda suke kamanni na halitta sai dai fatansu yana kama sosai. Sai da tafiya tai tafiya kowa ya fahimci yanda
alaƙar take. Duk da su ɗin yara ne da yawan mutane kai tsaye suke fassara alaƙar zuwa wani abu daban.
Duk da su dai yaran babu wani abu makamancin hakan a tattare da furucinsu na baki, mawuyacine ma ace
su sun san minene wata soyayya, amma hatta iyayensu na ganin zuwa nan gaba Wannan shaƙuwar zata iya
rikiɗewa ta koma hakan....
★★★
Kamar kullum ƙarfe uku dai-dai aka tashe su. Suna ƴan farko-farkon fitowa. Dan sun san driver ɗin su
baya wasa. Ƙarfe biyu da rabi yake isowa. Uku a gate take masa. Ilai kuwa sun samesa inda yakan jirasu
kullum. Dan su Fadeel ma har sun rigasu fitowa. Cike da tsokana Fawzan dake kallonsu ya ce, “A'a ƴar
gurguwar Besty an warke ne?”.
Ƙafar tata ta kalla sai kuma ta kalla Bestyn nata. Harararta yay itako ta ƙyalƙyale da dariya tare da
matsawa kusa da Fawzan. Nuni ta masa daya duƙo dan ya fita tsayi nesa ba kusa ba. Haka suke dogaye dan
iyayensu ma duk dogayene. Shiyasa ko shi AA ɗin dake 15 years ya shallaketa sosai. A cikin kunne ta
gwargwaɗama Fawzan, “Dama fa dan ya goyani ne Yaya F. Dan yanzu idan nace yamin goyo sai yace wai na
girma. Kaga yanzu ai na samo dabara”.
Mi Fawzan zaiyi ba dariya ba. Harda kwanciya jikin mota. Yayinda Maanal ta shige mota da sauri itama
tana tata. Tsaf AA ya fahimci abinda ta faɗa dan yana kallon motsin bakinta. Dan haka baice komai ba ya
saka bags ɗin su da lunch box ɗin cikin booth kawai shima ya buɗe motar ya shiga. Dai-dai nan Yaya Fadeel
ya iso shi da abokinsa. Ta saitin da Maanal take abokin nasa ya ɗan leƙa yana tsokanarta dan mutuniyarsa
ce. Kafin ya mika mata chocolate da in dai suka haɗu sai ya bata. Cike da ɗoki ta masa godiya tare da bye-
bye. Ta buɗe chocolate ɗin ta, kamar yanda suka sabama juna duk abinda ɗaya ya samu sai ya raba da
ɗaya ta raba biyu ta juya ta miƙama Ajwaad rabi duk da tasan ba lallai yasha wannan ba. Ilai kuwa
maimakon ya amsa harararta yayi ma. Ta taɓe baki kamar zatai kuka da faɗin, “Wai miyasa baka son amsar
abun hannun Ya Abdull ne Besty?”.
Banza ya mata bai tanka ba. Maimakon hakan ma sai ya ciro headphone ɗin daya saka a kunnesa. Dariya
Fawzan yay da faɗin, “Kishi mana Alaji. Kinga Lilly bani nasha tunda shi na mazan ya motsa”.
Bata wani fahimci mi Fawzan ɗin ke nufi ba ta miƙa masa duka chocolate ɗin ta juya itama a dole tayi
fushi. Shiko ya ce, “Uhhm gaba takaini, ban nasha faɗan masoya hutu”.
Harararsa Babban Yaya yayi. Cikin ɗan zaro ido ya ce, “Babban Yaya mi kuma na maka kai kuma?”.
“Kai bakinka bashi da linzami ko?”.
Cewar Fadeel ɗin.
“To ayi haƙuri babban yaya na daina”.
Shiru motar tayi babu wanda ya sake magana har suka iso gida....
Fuuuu ta fice batare data kalla kowa a cikinsu ba ta shige gidansu. Shima motar ya buɗe batare da ya
jira an shiga cikin gida ba kamar yanda aka saba ya shige da ƙafa. Oum na zaune a falo ya shigo. “Oum
good afternoon ”. ya faɗa a taƙaice yana shigewa ɗakinsu, dan su duka su a ɗaki ɗaya suke amma kowa da
gadonsa. Da kallo Oum ta bisa, sai kuma ta girgiza kai kawai dan tasan ɗayan biyu ne fushin Auta. Kodai
wani ya taɓa Maanal, ko shi da ita sun samu saɓani. Shigowar su Yaya Fadeel ya katse tunaninta. Su duka
ita suka nufa, cike da shawagwaɓa suka zauna a gefe da gefenta kowanne yasa kansa a kafaɗarta duk da
sun fara zama samari, koma muce sun zama. Dan Fadeel yana shekarar ƙarshe ne a secondary, Fawzan na
aji biyar. Fuskarta ɗauke da murmushi ta shafa kawunansu dake cike da suma. “Da alama yau sojin gidan
nan sunyi laushi, dan fuskar baban Commondo ya nuna.”
Dariya Fawzan yay da faɗin, “Oum wancan Commondo ɗin naki ba gajiyace ta maisheshi haka ba.
Saɓani ya samu da rabinsa, bakiga sun barmu da dakon kayansu ba”. Ya ƙare maganar yana nuna school
bags ɗinsu da lunch box ɗaya da suke zuba abinci.
Cikin ƴar dariya Oum ta ce, “Ai zancen gizo baya wuce ƙoƙi. Tana ina ita to?”.
Yanzu kam Fadeel ne yay ɗan murmushi da bata amsa da, “Itama tayi gida. Wannan yaron naki da alama
zaiyi kishin tsiya Oum. Shike nan shi babu wanda ya isa ya raɓu Maanal koda da wasa ne. Ki lura da ko mu
dan baida yanda zaiyi ne kawai. ALLAH ki ringa masa addu'a ALLAH ya sassauta masa”.
Sosai Oum ta saki murmushi mai ƙayatarwa. Kafin ta miƙe tana faɗin, “Kuna sakama autana ido a
gidan nan. Tunda baya so a raɓar masa half ɗinsa a bar masa kayarsa mana”.
Miƙewa sukai suna dariya suma. Kowa ya nufi ɗakinsa domin yin shirin islamiyya kuma....
★★
A ɓangaren Maanal itama dai haka ta shiga gida a kumbure. Su Shahidah dake dawowa tun ƙarfe biyu
daga tasu makarantar suna tsakar gida suna wankin uniform. Da kallo suka bita dan ita ko kulasu batai ba.
Koda ta shiga ciki ma bata nema inda Ammie take ba duk da tana jin motsinta a kitchen. Ɗakin Ammien ta
shige dan ita nan ne wajen zamanta. Ɗakinsu kullum cikin faɗa take da su Shahidah da neman fitina da su,
su sakata abu taƙiyi, su daketa Ajwaad ya rufesu da azabar masifa kamar Shahidah bata girmesa ba. Ganin
haka yasa Ammie maidota ɗakinta ita sai aka zauna lafiya. Duk da a hakan ma idan neman maganar ta ya
tashi takan shiga ɗakin nasu tayi ɓarnarta son ranta ta fito. Suyi magana tace ita sharri sukai mata mi zatai
a ɗakin nasu da babu komai sai tarkace.
Gado ta faɗa ta sanya kuka, tafi mintuna goma har sai da Ammie tazo tana mata magana. Da farko ƙin
tashi tayi ma sai da ta daka mata tsawa sannan ta tashi a firguce dan tana tsoron tsawa matuƙa. Cikin
haushi Ammie ta ce, “Wane kalar shashanci ne kuma wannan zakizo kinama mutane kuka daga dawowa.
ALLAH Manaal ki maida hankalinki a gidan nan. Ke kullum girma kike amma kina sake maida kanki
wawuya. Baki da lafiya ne?”.
Kanta ta girgiza alamar a'a. Sai kuma ta sake matso hawayen da suka taru mata a manyan idanunta da
kai kasan idan ALLAH ya kai ta zama budurwa ba ƙaramar ƙyaƙyƙyawar yarinya za'ai ba. Dan ko yanzu
mutane da yawa kance za'aga ƴammata a wajen nan. Maanal irin yaran nan ne masu shiga rai lokaci guda.
Balle gata da baki da rawar kai kuma. Uwa uba tsiwar tsiya...
Tsaki Ammie taja da sake faɗin, “To uwar miye kika shigo kinama mutane kuka?”.
Fuska ta sake ƙwaɓewa da faɗin, “Ba Besty bane ba. Kawai dan Ya Abdull abokin Babban yaya ya bani
chocolate na bashi yaƙi ya sha, shine kuma yake fushi da ni bayan ban masa laifin komai ba”.
Kasama magana Ammie tayi, ta zuba mata idanu kawai cikin wani yanayi. Bazata gaji da faɗa ba
al'amarin yaran na bata tsoro, tun basu tafasa ba suna neman hanyar ƙonewa. Gefe ta ture tunanin batare
da ta sake cewa komai akan batun ba ta juya zata fita. “Ki tashi kiyi wanka kizo ga abinci dan lokacin
islamiyya ya kusa”.
Jitai kamar tace bazata je islamiyya ɗin ba. Amma tasan faɗar hakan na nufin Ammie yin tamaula da
rayuwarta. Dan mace ce mai zafi sosai da sam bata ɗaukar wargi.......✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭_*
[2/11, 8:42 PM] Maryam anas: *_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
5️⃣7️⃣5️⃣7️⃣
______________
........Tamkar haɗin baki ta ɓangarorin biyu su duka sun tasa abinci gaba sun kasa ci. Yanda Ajwaad ke can a
gaban Oum yana faman juya ɗan abincin daya zuba a plate anan ma haka ne ga Maanal. Oum dai ta ɗan
lallashi Ajwaad, harta amshi spoon ɗin ta shiga bashi da kanta. Sai dai laumarsa batafi huɗu ba yace mata
ya ƙoshi a shagwaɓe. Lallaɓashinsa ta shiga yi amma yace shi fa ya ƙoshi kamar ma zaiyi amai yake ji. Babu
yanda ta iya dole ta barsa ya miƙe yana goge baki bayan ya saɓi bag ɗin islamiyyarsa. Dan su duka ukun
sanye suke cikin uniform. Da kallo yayun nasa suka bisa da Mamy da itama take a falon, sai dai sam
hankalinta bama a kansu yake ba. Sai dai babu wanda yayi magana har ya shiga store dake jikin kitchen ya
fito, da alama akwai abinda ya ɗakko. Oum kawai ya kalla cikin sanyinsa ya furta, “Oum kimin addu'a sai na
dawo”.
Fuskarta da murmushi ta ce, “ALLAH ya tsare Autana. ALLAH ya bada ilimi mai albarka. ALLAH ya
daidaita tsakani kai da Besty”.
Idanunsa masu haske ya ɗan waro waje, sai kuma ya juya da sauri zai fice abinsa. Ai ko Fawzan ya
kwashe da dariya. Yayinda Fadeel yay murmushi shi da Oum, Mamy dai kamar ma bata san sunayi ba.
Harya saka ƙafarsa ɗaya waje Oum ta kira sunansa. Juyowa yay batare daya amsa ba.
“Mamy fa?”.
Oum ta faɗa babu wasa a fuskarta. Juyawa yay shima ya kalla Mamyn, sai kuma cikin sanyinsa da magana
ƙasa-ƙasa ya furta, “Mamy sai na dawo”.
Karan farko ta ɗan juyo ta kallesu su duka, sai kuma ta ɗauke kai a taƙaice ta ce, “ALLAH ya bada sa'a”.
Daga haka ta maida hankalinta a kallonta. Murmushi Oum tayi, zuciyarta na sake cika da so da ƙaunar
kishiyar tata da takema kallon ƴar uwa. Yayinda Ajwaad ya fice abinsa yana amsawa...
Da ƙafa ya fito dan makarantar tasu babu nisa. Hakan yay dai-dai da fitowar su Shahidah Maanal biye da
su. Bai tanka musu ba suma basu tanka masa ba. Sai da suka ɗan gota shi sannan ya lura da Maanal dake
binsu a baya kamar bata so. Kallon juna sukayi kusan na sakan goma. Sai kuma kowanne ya ɗauke idonsa.
Shi ya fara yin gaba like baima ganta ba. Itama sai tai nata gefen, sai dai duk da hakan a jere suke tafiya
cikin tazara a tsakkiyarsu ta yanda ba lallai ka yarda tafiyar tasu ɗaya bace.
A aji ma koda suka zauna babu wanda ya kula wani. Sai da kusan minti uku sannan ya ciro kwalin drink
da babban biscuit ya ajiye gabanta bayan ya buɗe kowanne. Batare da yayi magana ba ya ɗauka Al-qur'ani
ya hau bitar karatu. Itama sharesa tayi taƙi ɗauka taci. Sai ma ta ɗakko littafin koyon larabci mai ɗauke da
hotuna na zane-zane ta hau zana color. Cikin haushi ya ƙwace littafin ya sake tura mata biscuit ɗin da lemo.
“Bana ci”.
Ta faɗa a kumbure tana kalmashe ƴan hannayenta a ƙirji ta da juyar da kanta gefe. Cikin haushin shima
ya ce, “K kin iyama mutane laifi ki fisu zuciya. ALLAH idan baki ɗauka kin ci ba sai na bar ajin nan.”
Tasan zai yi abinda yafi hakan. Dan haka bayan ta gama harare-harare ta ɗauka ta fara ci. Ajiyar zuciya ya
saki a hankali yana sake maida hankalinsa ga Alkur'anin. Yanda taci da yawa ya sake tabbatar masa bata ci
abinci ba. Yasan wannan halinta ne. In har tana fushi komi za'a bata in dai ba shine ya bataba bazata ci ba.
Sauran wanda ta rage ɗin ta miƙa masa, babu musu ya amsa shima ya fara ci, wani ɗan guntu daya gutsira
ya rage a hannunsa ta kamo hannun nasa ta saka a baki. Sai ya dungure mata kai. Dariya ta ƙyalkyale da
shi. Hakan shima ya saka shi sakin dariyar. Kamar basu ba kuma sai suka warware. Bayan ya gama sukai
bitar Alkur'anin tare kafin malami ya shigo musu.....
Koda aka tashi suka fito a jere Shahidah da Amaal kallonsu kawai suka tsaya yi, hakama Fawzan daya fito
kallonsu yake yana dariyar shaƙiyanci. Maanal ce kawai ta tura baki gaba, shiko gogan bai kulashi ba yay
gaba riƙe da bags ɗinsu. Koda suka iso gida su duka gidan su AA ɗin suka shiga. Tun a ƙofar falo Maanal ke
ƙwala kiran Oum. Sai dai Oum na ɗaki bata amsa ba. Haka ta shigo ta nufi hanyar ɗakinta. Sai dai kafin ta
shige sukaci karo da Mamy dake fitowa daga kitchen. Dakatawa Maanal ɗin tayi, tare da faɗin, “Mamy ina
yini”.
Amsa mata Mamyn tayi da kulawa, tare da tambayarta makaranta. Maanal ta ce, “Alhamdullah” tana
wucewa ɗakin Oum. Shima Ajwaad dake biye da Maanal ya gaishe da Mamyn, batare data kallesa ba ta
amsa kawai tana wucewa abinta. Ɗan Binta yay da kallo, ganin kamar zata juyo sai ya ɗauke kai ya shige
ɗakin Oum abinsa.
Oum na sallar magriba Maanal baje a gadonta. Ya ajiye bags ɗin nasu yana kallon Maanal ɗin. “Malama
sallan fa?”.
Ya faɗa yana hararanta. Baki ta tura gaba da faɗin, “Zan huta ne na gaji. An jima ba sai nayi ba”.
Harara ya sake zuba mata, batare da yayi magana ba ya wuce toilet ɗin Oum, alwala ya ɗauro ya fito,
gadon ya nufa, inda Maanal ta sake bajewa tana lumshe ido alamar barci ma take son yi. Duka hannayensa
biyu yasa ya jawo ƙafafunta ƙiyyyy har ƙarshen gadon, ita kuma ta buga ihu tana kai masa duka da faɗin,
“Ni ka barni ba nace zanyi ba anjima”.
Ko kulata baiyi ba ya direta a tsaye, cike da tsiwa ta dubesa zatai magana ya ce, “ALLAH kika sake magana
sai na ɓata miki rai. Wuce alwala konaje na haɗaki da Babban Yaya ko Ammie”.
A duniya Maanal na tsoron Babban Yaya da Ammie, dan sune ke cimata ƙaniya a zauna kafiya. Cikin jin
haushi ta cire ɗan hijjab ɗinta ta jefa a gadon Oum sannan ta wuce bayi fuuu. Shima ficewarsa yay batare
daya sake kulata ba. Koda tayo alwalar kusa da Oum tazo tayi sallar itama...
Koda aka idar da sallar shi da Fawzan suka dawo, direct ɗakin Oum suka shigo, sun samu Maanal a
saman jikinta kwance tana mata surutu. Fawzan ya gaida Oum, shima Ajwaad haka. Amsawa tai fuskarta
da murmushi tana kallon Ajwaad, sai kuma ta kalla Fawzan suka saki murmushi. Ajwaad ɗin na kallonsu,
amma bai tanka ba ya zauna kusa da Oum ɗin shima yana ɗakko bag ɗin Maanal na islamiyya. Sai da ya
gama fiddo books ɗin duka sannan ya kalla Maanal dake ta surutu wa Oum.
“Parrot tashi kiyi aikin islamiyya idan anyi isha'i mayi na boko”.
Cikin ɓata fuska alamar fushi take da shi har yanzu, “Tace ni kayi min barci naje ji”.
“Ko mutuwa ko?”.
Ya faɗa cike da gatse. Tashi Maanal tai zaune idanunta cike da ƙwalla tana kallonsa. Sai kuma ta kalla
Oum da faɗin, “Oum kin gansa ko, so yake ma na mutu ya huta ban girma naga ya zama kamar Daddy da
Baabu ba”.
Da ƙyar Oum ta danne dariyarta, “A'a in sha ALLAHU Auta bazaki mutu ba sai kinga girman Auta ya
zama kamar Daddy da Baabu. Yo ina dalili Auta gaskiya ka bari. Ƙuruciya tare tsufa tare in sha ALLAHU”.
Dariya Fawzan ya sanya da faɗin, “Wato Oum soyayyar nan fa na tafiya da ni.....”
Harararsa Ajwaad yayi, sai kuma ya rufe books ɗin zai tashi Oum tai saurin kama hannunsa ta maida
shi ta zaunar tana gumtse dariya. Sai kuma taima Maanal nuni data matsa suyi karatun. Ƙarfin dariya
Fawzan ya ƙara tare da miƙewa ya fice yana faɗin, “In dai nine ma nayi nan. Bara dai naje mu daidaita da
Amaal nima kozan samu Besty na”.
Filo Oum ta ɗauka ta jefa masa. Ai ko ya ƙarasa fita a guje. Shi dai Ajwaad bai kulashi ba. Sai aikin da
suka fara shi da Maanal na islamiyya. Basu tashi ba kuma sai da aka kira magrib. Ana idarwa ya dawo suka
ƙarasa suka fara na boko kuma anan falo. Dan Oum sam bata barinsu su biyu a ɗaki, shiyyasa ma aka saka
camara a ɗakinsu duk da ba'a taɓa kama ko ɗayansu da wani halin rashin tarbiyya ba gaskiya....
Da ƙyar Maanal ta bari suka kammala homework ɗin nan. Abinci ma tace ta ƙoshi sai da Oum ta
lallaɓata ta bata tea. Ai ko tana gamawa ta ɓingire a jikinta ta hau barci. Sai da barcin yay nisa Ajwaad yazo
ya ɗauketa ya kai ɗakin Oum ya kwantar, dan yasan ta gaji ɗin kam, kuma yanda tayi barcin nan duk bala'in
dama za'ayi ayi bazata yarda tayi wanka ba.
Dama haka take, kusan rayuwarta raba dai-dai ce a tsakanin nan gidan su Ajwaad da can gidansu. Dan
ko kayanta a rarrabe suke saboda ko'ina a gidajen biyu tana zama. Wani lokacin sai tai sati bata leƙa
gidansu ba sai kewarta ta ishi Baabu ne ya aiko a kirata sannan. Idan kuma ƴan arziƙin na kanta kullum sai
taje ta gaida Ammie da Baabu ɗin. Idan kuma aljanun nata suka koma can gidansu kullum zata zo ta gaida
Oum ne......
_________★
A kwana a tashi asarar mai rai. Yau ga su Maanal da yin graduation na gama primary. Zokaga rawar kai
wajan mutuniyar. Balle da taji Oum ta shirya musu party ita da Bestyn nata. Duk da dai shi ya nuna baya so,
amma Oum tace babu fashi sai tayi tunda Maanal naso. Babu yanda ya iya dole shima ya sakko aka hau
shirye-shirye. Ammie kanta ba son fatin take ba, dan tasan hanyar kashe kuɗi kawai Oum ta ƙirƙiro ma
kanta. Dan koda ta sanarma Babu ma kai tsaye yace shifa gaskiya bai da kuɗi. Cikin sanyin murya ta ce,
“Aunty ce fa dama ta shirya musu bawai kuɗi zaka bayar ba. Naga ya kamata ka sani ne shiyyasa”.
“Oh to ALLAH ya taimaka. Dan nima ina da nawa uzirin ne ma shiyyasa. Tunda hutun nan mai tsayine
ina son muje gida gaskiya. Gwaggo nata magana akan hakan”.
Wani irin faɗuwa gaban Ammie yayi, a take zufa ta shiga tsatstsafoma goshinta. Ganin ya juyo yana
kallonta saboda jin tayi shiru tai saurin gyara yanayinta tayi ɗan murmushin yaƙe. “Kai amma nasan yaran
nan zasuyi murna sosai. Musamman ma Maanal da tunda aka baro garin ba'a koma da ita ba shekara
kusan shida.......”
“Oh ke baki murna kenan?”.
“A'a haba yazance bana murna ni da garinmu. Baka fahimceni bane ba dai”.
Komai bai sake cewa ba sai shigewa toilet ma da yayi dan dama shirin wanka yake yi. Jagwab Ammie
takai zaune zuciyarta na wani irin farfashewa a ƙirjinta. Gaba ɗaya jikinta rawa yake. Tabbas ta cancanci tai
kewar tushenta, sai dai rasa wani giɓi da babban ƙalubalen data baro yasa mata jin tsoro da rashin son
zuwa garin. Sai dai tasan ko giyar wake tasha bata isa bijirewa umarnin mijin nata ba kuma ɗan uwanta. Jin
motsin zai fito yasa ta miƙe da sauri ta fita a ɗakin, tana mai ƙoƙarin danne komai..........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
5️⃣8️⃣5️⃣8️⃣
______________
.........Babu bai sake bi takan bikin su Maanal ba, yama maida hankali a shirya musu tafiya gida. Yayinda
Ammie taketa ƙarfin halin yin nata shirye-shiryen itama batare da su yaran sun san mi ake ba. A haka ranar
juma'a akai partyn da Oum ta shiryama Maanal da Ajwaad. Abin kamar wasa sai gashi ya ƙayatar. Anci
ansha yara sun sha bidirinsu musamman Maanal da ko zama ta huta batayi. Shi kansa AA duk ta takurama
rayuwarsa. Haka dai aka tashi gab da magriba, tsabar gajiyar da Maanal tayi a inda tai sallar magrib anan ta
ɓingire barci. Kallonta kawai Oum tai tana murmushi, dan a tare sukai sallar a ɗakinta. Ɗaukarta tai cak ta
maida saman gadonta ta kwanar, ita kuma ta cigaba da lazimin ta.
Bayan idar da sallar isha'i su Ajwaad suka shigo harda Aban su. Kai tsaye ɗakin Oum Abah ya shigo. Yakai
zaune bakin gado fuskarsa da murmushi yana kallon Maanal ya ce, “A'a anan surukar taki tai barci?”.
Dariya Oum tayi tare da faɗin, “Kaji Aban su da wata magana suruka kuma?”.
Murmushin sa ya sake faɗaɗawa shima da faɗin, “Eh mana. Ai abunne na Maanal da autanki akwai ban
mamaki. Zan so wannan abotar tasu ƙarshenta ya kasance hakan”.
“To ALLAH ya zaɓa abinda yafi alkairi. Idan hakan ta kasance zanfi kowa farin ciki Gandanga. Dan har
cikin raina nake jin matuƙar ƙaunar yarinyar nan wlhy”.
“Nima haka yarinyar ta shiga raina sosai. Badan kar ace ma na cika zumuɗi ba nifa da a yanzu zan
ɗaura musu aure kawai”.
Dariya sosai Oum keyi. Shima Aba na tayata. Sai da sukai mai isarsu Oum tace, “Ayi haƙuri dai a barsu
sukai hankalin kansu. Kar a tauyesu musamman ita da take mace. Gara shi namiji ne yana da damar auren
fiye da ita”.
“Hakane kuma kema kinyi magana. Kinga nama shafa'a ɗazun Baban nasu ke sanar min zasuje gida
hutun nan ma, dan mahaifiyarsa tana kewarsa sosai.”
“Kai masha ALLAH, ai ni har ƙoƙarin su nake gani ma. Musamman Ammien Shahidah. Garama shi tace
yaje kusan sau uku. Amma ita tunda suka dawo Kano bataje ba hakama yara”.
“Abin ne sai a hankali ai. Kin san idan iyali sukai nauyi tafiya ma wahala take yi. Balle wannan aikin nasu
na ƴan sanda sai a hankali. Kwanaki ma kamar zasu masa transfer ALLAH dai ya taimakesa aka samu canji.
Hankalinsa ya tashi sosai dan yace baya son yawon da yake da yaran musamman a yanzu da suka fara
girma”.
“Yana da gaskiya. Ita kanta takance ALLAH yasa ko ya samu canjin wajen aiki ya barsu su anan Kano
dan tana jin daɗin zaman garin......”
Sallamar Ajwaad ta katse Oum. A tare suka amsa masa da bashi izinin shigowa.
“Lafiya Autana?”.
Oum ta faɗa tana kallonsa. Fuska ya ɗan yamutse kamar zai saki kuka ya ce, “Oum kaina ke ciwo. Kuma ina
jin yunwa”.
“Ya rabba. Autana badai duk kai kawon nan baka ci abinci ba?”.
Kansa ya ɗaga mata alamar “eh”.
Da sauri ta kama hannunsa suka fice tana jan salati. Aba ya mike yana musu dariya....
___________★
Sosai su Ammie suka shirya wannan tafiya. Yayinda su Shahidah keta zumuɗi banda Maanal da tace
idan fa bada Ajwaad ba babu inda zataje ita kam. Babu wanda ya tanka mata dai akan batun. Su dai sun
cigaba da shirinsu kawai.
A ɓangaren Ajwaad ɗin ma tunda yaji batun tafiya jikinsa yay sanyi. Da farko shima ya nuna son binsu.
Har ya samu Oum da maganar tace ita dai babu ruwanta ya sanarma Aba. Bai Musa ba ya samu Aban da
batun. Amma sai ya kwaɓesa akan maganar. Kai tsaye ya sanar masa bazai iyu ba. Suma zasuyi tasu tafiyar
zuwa Adamawa suga gida...
Tafiya ta tabbata, amma ansha fama da badaƙala kafin Maanal ta yarda. Sun tafi tana kuka kashirɓan
kamar zata shiɗe. Shima uban gayyar da taurin kansa yasa baiyi kukan ba da farko yana ganin sun wuce ya
shige ɗaki ya kwanta a gadonsa sai ga hawaye. Daga ƙarshe da zazzaɓi ya yini ranar. Har washe gari sai da
aka sanya masa ƙarin ruwa.
A ɓangaren Maanal ma kuka taci sosai har sai da Babu ya mata buyagi, itama ƙarshe zazzaɓi ya rufeta.
Taita kwara musu amai a mota. Haka suka isa Kebbi tayi ligiff a wahale. Anan suka ɗan tsaya aka dubata.
Washe gari suka ɗauki hanyar Suru da shima keda ɗan nisa daga nan cikin birnin Kebbi ɗin. Dan a ranar ɗin
ma basu isa ba sai da zuhur..
Gari ne tsaka tsaki a komai. ba ƙato bane can sosai. Ba kuma ƙarami bane ba. Suna da wutar lantarki
sannan akwai titi har a cikin garin. Kusan zaka iya samun duk abinda kake so naci ana saidawa musamman
wanda ake mu'amala da shi ako ina kamar su kayan sanyi, kayan marmari, nama, da ire-iren hakan.
Mutanen garin na neman ilimi gwargwadon iko, dan suna da manyan mutane sosai a ƙasar da ake damawa
da su a gwamnatin jahar dana tarayya. Daga Suru hanyar Giro suka ɗauka, nan kam basu isa ba sai yamma
sosai. Giro dai ƙaramin garine, amma ƙauyene mai ƙyau da ƙayatarwa. Tun kafin motar Babu ta isa labari
ya iso gidansu. Lokacin da motarsa ta tsaya tuni yara sun zagayeta cike da zumuɗi musamman ganin harda
baƙin fuska da basu sani ba. Dan duk sanda aka haifesu wasu kuma sukai wayo Ammi bata garin.
Tun daga waje zaka san gidan ƙaton gaske ne. Dan ƙofa ce wangamemiya ƙwarai da gaske. Sai ƙatuwar
bishiyar ceɗiya da kufan wutar makarantar allo irin ta tsangaya an zagayeta da dutsuna. Gefenta kaɗan
massalaci ne da ɗakuna a jere kusan guda goma ko muce shaguna da jikin bangonsu duk alluna ne. Jiki a
sanyaye Ammie ta fito fuskar ta ɗauke da murmushin ƙarfin hali. Yayinda su Shahidah keta kalle-kalle suna
son tuno abinda suka manta musamman ma ita da aka tafi da ita da ɗan wayonta. Tuni yaran sun fara
kwasar kayayyakin suna shiga dasu, yayinda su kuma suka bisu a baya Babu biye da su. Ɗakuna ne guda
biyu masu kallon juna a farkon shiga. Ana hannun dama ke buɗe wani dattijo mai farin gashi fatt zaune kan
buzu yanata rubutu a wani ƙatoton allo. A hanli Ammi ta cire takalman ƙafarta zuciyarta na mata ɗan sanyi,
ganin haka yasa suma su Shahidah cirewa, yayinda Maanal ta dogara tana kallonsu...
“Barka da hutawa Baffah”.
Ammie ta faɗa a hankali kanta a duƙe dai-dai tana shiga cikin ɗakin. Sai lokacin tsohon ya ɗago ya ɗan
kallesu fuskarsa da murmushi. Cikin kamala da tausa harshe ya furta, “Lale da mutanen garin dabo”.
Murmushi Ammie ta sake yi hakama Babu da ya shigo riƙe da hannun Maanal data dogare a ƙofa. Sai da
suka kai zaune tsohon ya sake faɗin, “Ashe zaka cika alƙawari Habibu ka kawo min iyalanka na sake gani
kafin na koma ga ALLAH?”.
Sosai Babu ya sake sunkiyar da kansa cike da girmamawa ya furta, “Ai min afuwa Baba, ai min afuwa”.
Murmushi tsohon yay mai faɗin gaske. Sai kuma ya miƙama Maanal dake ta faman kallonsa cikin zare ido
hannu alamar tazo gareshi. Da sauri ta matsa jikin babanta tana maƙe kafaɗa alamar bazata je ba. Turata
Babu yay yana mai daka mata tsawa. Cikin harshen turanci ya ce, “Wuce kije mana ban son raini”.
Duk da tsohon bajin abinda Babu ya faɗa yay ba sai yay murmushi. Dan ya fahimta ganin yanda Maanal
ta zabura jiki na karkarwa ta matso inda yake sai dai duk a ɗarare. Bai ƙiba ya kama hannunta ya zaunar a
gabansa. Cikin tausasa harshe ya furta, “Wannan shi ake gudu dama ai Habibu. Shiyyasa muke kwaɗayin ku
ringa matso da iyalan naku gab damu koda lokaci-lokaci ne”.
“ALLAH ya huci zuciyarku Baba”.
Babu ya sake faɗa da sauri. Cikin sanyin murya itama Ammie ta nema afuwa. Kafin ta ɗora da gaishesa
cikin girmamawa. Ya amsa mata da kulawa tare da tambayarta bayan rabuwa. Hakama su Shahidah duk
suka shiga gaishesa. Hannu duka ya miƙa musu alamar suzo garesa. Babu musu duk suka matsa. Sai da duk
ya taɓa kawunansu sannan ya tambaye su sun ganesa?. Kai tsaye Shahidah tace ta ganesa. Amma Amaal
na ɗan inda-inda. Ta dai san ta sanshi sama-sama. Sai dai a wancan lokacin bai kai haka tsufa ba. Gashinsa
kuma bai furace kamar yanzu ba. Murmushi yay da akazo kan Maanal da yana tambayarta kawai ta fashe
da kuka. Itafa harga ALLAH tsoronsa take ji. Musamman wannan farin gashin nashi dogo sosai daya zagaye
ƴar ramammiyar fuskarsa. Ga farin rawani ya naɗa akan nashi. Lallashinta ya shigayi tare da bata farar
alewa dake cike da wata ƙwarya a gefensa. Badai ta sha ba amma ta daina kukan.....
Sun jima a wajensa dan har duhu na neman rufawa kafin su shiga cikin gidan. Lallai ƙaton gaske ne da
sassa daban-daban. Tarin manyan turamen daka dake a ƙarƙashin bishiyar dalbejiya a farkon shigowa
gidan zai tabbatar maka da hakan. Sai runbuna da ake ajiye abinci da aƙalla sun kai kusan ashirin. Yara ne
sosai a haka ma dan mangariba ta rufa ne wasu basa gida. Sai mata da akalla sun kai goma sha biyar dake
tsaitsaye wasu ma daga su sai karin ƙirji. A hakan kuma ƙalilanne a matan gidan, waɗan nan wanda bazasu
iya haƙuri bane saboda zumuɗin son ganin Ammie da yaranta.
Itama Ammien ganinsu yasa tuni ta manta da fargabarta. Fuskarta da murmushi ta nufesu. To suma dai
bakunan nasu a washen suke. Duk da dai wasu fara'ar tasu bata kai ciki ba. Su dai su Maanal na raɓe jikin
Babu da matan nan keta faman yima sannu da zuwa. Garama Shahidah da Amaal na ƙoƙarin gaishesu da
kalmar “Ina yini”. Lallai shekara shida ba kwana shida bace. Suma sai kallon yaran suke da mamakin
canjawarsu. Sun yi girma kuma sosai musamman ma Maanal da aka tafi da ita daga garin tana ƴar shekara
biyu. Yanzu ko gashi tana ƴar budurwa shekara takwas ai ba wasaba su a wajensu. Dan yara sun ma fara
kula samari. Kamar Shahidah kuwa masu sha biyar ai sun haihu ta biyu kota farko dana biyu a ciki. Kamar
Amaal mai sha uku sune amaren wannan shekarar..
Har sashen gwaggo akai musu rakkiya. Inda anan ne ɗakin da Ammie tai rayuwa a ciki yake. Wajene
aka dan katange da ɗakuna guda uku. Ɗaya na Gwaggo mahaifiyar Babu ɗaya nata. Sai ɗayan na kishiyarta
da bata wuce wata biyar a gidan ba ta fita. Fitar tata ce kuma ya ƙara mata baƙin jini a gidan da ma wajen
surukar tata da bata samu sassauci ba sai da suka bar garin da zama. Gwaggon na saman wani ɗan dutse
daga ƙofarta tana alwala. Sau ɗaya ta ɗago ta kallesu ta maida kanta. Amma haka Babu ya nufeta fuskarsa
da fara'a yana faɗin, “Barkanki da wannan lokaci Gwaggona”.
Ganin haka itama Ammi da sauri ta matsa ta tsugunna tana faɗin, “Sannu Gwaggo! Mun sameku
lafiya?”.
Maimakon ta amsa su su duka a daƙile ta jefama Ammie wani kallo ta maida idanunta akan su Shahidah
dake tsaye suna kallonsu sannan ta maida ga Babu ta sakar masa murmushi. “Babana kasha hanya”.
Murmushin ƙarfin hali yayi dan abinda taima Ammin ya ɗan sokesa. Sai dai bai nuna ba ya danne abinsa
ya maida mata da murmushin yana faɗin, “Aiko dai Gwaggo. Bara na je salla gashi har za'a shiga damma
ina da alwala”.
Kanta kawai ta jinjina masa. Ya miƙe yana kallon su Shahidah dake rakuɓe suna kallon Ammie dake duƙe
kanta a ƙasa har yanzu. “Ku kuma kukai tsaye anan. Ku shigo mana”.
Jikinsu a sanyaye suka ɗaga kawuna. Shi kuma ya fice batare daya waiwayesu ba zuciyarsa duk babu
daɗi. Yasan dole sai haƙuri, dan hutun nan sam bazai zame musu na farin ciki ba sai abinda suka gani.
Tsakaninsa da mahaifiyarsa babu wata damuwa. Amma yanda takema matarsa da yaransa abun na
damunsa matuƙa. A ganinsa matarsa bata cancanci hakanba kodan hallacin iyayenta a garesa ya kamata
Gwaggo ta rangwanta mata. Amma ina, ya rasa wace irin ƙiyayyace wannan mai zafi........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
5️⃣9️⃣5️⃣9️⃣
______________
__________
.........*_SU WAYE SU AMMIE?:-_* Alhaji Umar da mutane sukafi sani da Alhaji Umar Giro ɗan asalin jihar
Kebbi ne a garin Giro dake ƙarƙashin Suru LG. An haifesa a babban gida da yay suna matuƙa a cikin garin
Giro saboda kasancewarsu manyan mutane masu ƙarfin ilimin addini. Su kusan ashirin da bakwai
mahaifinsu ya haifa, maza sunfi yawa, dan mata huɗu ne kawai a cikinsu, sauran su ashirin da uku duk
maza ne. Malam Ibrahim shine mahaifinsu, sai iyayensu mata su uku. Ta tsakkiyar itace mahaifiyar Alhaji
Umar, shi kaɗai kuma ta haifa a duniya, sauran ƴaƴa ashirin da shida duk na matan biyu ne. Dan matarsa ta
farko haihuwarta goma sha ɗaya amma ƴaƴa goma sha shida duk nata ne. Sai amarya nada goma cif duk
da itama dai wasu sun rasu a ciki.
Kishi sosai ake zubawa a gidan Malam Ibrahim, hakan yasa ƴaƴansa suka tashi da zafin ƴan ubanci. Kowa
ɗan ɗakinsu kawai yake so. Wannan aƙidar tafi wahalar da Umar, dan shi kaɗai shi mahaifiyarsa ta haifa
shiyyasa sam baya wani jin daɗin zaman. Yasha wahala ƙwarai da gaske a hannun ƴan uwansa, har takai
karatun ma baya fuskanta dan anan cikin gidansu suke ɗaukar karatu wajen mahaifinsu, ƴan uwansa
manya kuma sune gardawa a yanzu.
Ganin yanda Umar ɗin ke cikin tsangwama da ƙyara yasa mahaifinsu ɗaukarsa ya bama wani amininsa
shima malami ne amma a can cikin birni, yanada tarin almajirai kuma Alhamdullah ana karatu.
Mahaifiyarsa tasha kuka, amma hakan yafi mata kwanciyar hankali akan zamansa a gidan. Umar ya koma
cikin birnin kebbi, kuma Alhamdullah yana samun ilimi, ya kuma kwantar da hankalinsa sosai dan Malam
Khamisu ya saka shi cikin ƴaƴansa babu banbanci. Ƴaƴan malam Khamisu su suna karatun boko, hakan
yasa shima Umar aka saka shi a boko.
Zamu iya cewa Umar ya fara karatunsa cikin nasara, kasancewarsa yaro mai basira cikin ƙanƙanin lokaci
yay zarra. Ga kuma ilimin addini shima alhmdllh. Umar na zuwa Giro akai-akai saboda mahaifiyarsa, dan
haka canjin da rayuwarsa ta samu a bayyane yake ga kowa. Cigabansa na saka ƴan uwansa sake jin
tsanarsa da hassadarsa su da iyayensu, sai dai babu yanda zasuyi. A haka ya gama secondary school ya fara
jami'a, yana level 2 ALLAH yay ma mahaifiyarsa rasuwa. Ya shiga tashin hankali matuƙa daga shi har
mahaifinsu, sai dai babu yanda aka iya da hukuncin UBANGIJI. Bayan rasuwar mahaifiyarsa ya sama ransa
dangana ya maida hankalinsa ga karatunsa, har ALLAH yasa ya kammala jami'a. A kuma wannan lokacin
ALLAH yay ma uban riƙonsa Malam Khamisu rasuwa shima. Umar ya sake shiga ruɗani, dan komai ya fice
masa a rai. Dan haka ya tafi yin sarvese ɗinsa nesa da Kebbi. A jihar Niger cikin garin Minna Umar ya fara
Sarvese, inda anan kuma ALLAH ya haɗashi da matar aure. Lubabatu yarinya ƙyaƙyƙyawa mai ilimin addini
da nutsuwa. Gata da haƙuri da tarbiyya. Cikin ƙanƙanin lokaci soyayya ta ƙullu tsakaninta da Umar da
hidimar ƙasa ta kawosa garin Minna. Lubabatu su biyu ne a wajen mahaifinsu, daga ita dai ƙanwarta
Shamsiyya. Suma ALLAH yayma mahaifiyarsu rasuwa matar uba ke riƙonsu, suna matuƙar shan wahala a
hannunta. Hakan yasa Umar na nuna yana son Lubabatu mahaifinta ya bashi.
Cikin ƙanƙanin lokaci aka gama komai, dan kafin ya gama sarvese har ranar aure an saka musu. Yana
kammalawa akasha biki. Nan Giro aka kawo amarya family house ɗinsu, dan ba auren nasu kaɗai akai ba
harda wasu a cikin ƴan uwansa da suma akayi duk a ranar. Sai da aka gama shan biki, bikin da aka nuna
matuƙar banbanci dan sam Umar baida wani gata a cikinsu, gashi itama Lubabatun duk sai a hankali tunda
basu da wani gata suma sakamakon rashin uwa. Haka dai akayi biki aka gama, amare suka tare da
mazajensu. Umar baya son zama a Giro, amma saboda kunyar mahaifinsa ya kasa magana. Ga aiki ya samu
a Kebbi, sai ya zam dole ya koma Kebbin sai weekend yake zuwa. Sam Lubabatu bata jin daɗin zama a cikin
waɗan nan ahali, dan kishi da ƴan ubancin da ƴan uwansa ke nuna masa duk sai ya tattaru ya koma kanta a
yanzu. Ga matan ƴan uwansa suma sun sakata a gaba, facalanci mai muni ake zubawa a tsakaninsu.
Musamman ma da Matar yayansu na biyar wanda Umar ke bimawa a wajen mahaifinsu mai suna Talle.
Talle irin matan nan ne masu mugun hali da hassada da ƙyashi, duk wani cigaba tafi son ace itace da shi.
Yaranta biyu a gidan, Habibu da mace, sai ƙaramin ciki da take laulayi. Tayi matuƙar tsanar Lubabatu a
gidan, dan tafisu wayewa da cigaba. Ita tayi karatun boko har zuwa secondary kuma gana addini dan tayi
sauka. Suko mafi yawansu musamman ma Talle kota allon bata nutsu tayi ba sai talla. Sosai matsi yayma
Lubabatu yawa, dan matan ƴan uwan mijin nata sun haɗe mata kai bisa jagorancin Talle. Koda yaushe tana
a ɗaki babu sakewa, idan kaga farin cikinta sai idan Umar na gidan. Ba kuma wai zaman nasa na hana ai
mata abu bane, a'a farin cikin da yake bata a gidan ne kawai ke sauƙaƙa mata baƙin cikinsu. Ana haka ta
samu ciki, haka taita rainonsa har lokacin haihuwa, sai dai ALLAH baiyi mai rayuwa bane wajen haihuwa ya
rasu. Itama tasha wahala, wahalar data saka Umar roƙon mahaifinsu ɗaukarta su koma cikin Kebbi, dan
kuwa tana naƙuda matan gidan babu wanda ya kulata wai ai bata gaya musu ba. Wannan yaja tasha
wahala har ɗan ma ya rasu. Sai da Malam ya shigo gidan ne yake ji a wajen yara ransa ya ɓaci yasa aka kira
wata unguwar zoma dake anan kusa da su. Ɗari bisa ɗari Malam Ibrahim ya basa goyon baya. Aiko ya
tattara matarsa suka wucewarsu. Wannan abu ya baƙantama mutanen gidan rai sosai musamman irin su
Gambo, sai dai basu da yanda zasuyi sai haƙuri.
Komawa Kebbi tama Lubabatu daɗi matuƙa, dan hayar gida madaidaici Umar ya kama musu. Ya kuma
nema mata admission ta koma makaranta. Alhamdullah komai Lubabatu na samu yanzu, bata da wata
damuwa. Ga Umar abubuwa nata zama masa. Dan ya shiga harkar kasuwanci tako ina kuɗi ke shigo masa.
Sosai yake ƙoƙarin taimakama mahaifinsa dama ƴan uwansa duk da basu taɓa nuna jin daɗin abinda yake
musu ba, sai dai Haruna mijin Talle shi da yake dama tun can yana son Umar, kasancewar sun tashi ne a
tare. Matarsa ce da mahaifiyarsu da ƴan uwansa kan canja masa tunani wasu lokutan. Amma a yanzu sai
yake ƙin biye musu suka ƙulle da Umar ɗin har ya fara jan ra'ayinsa ya fara kasuwanci shima anan dai Giro
ɗin. Abinda Haruna ɗin yayi ya ƙona ran matarsa da ƴan uwansa, amma ya nuna musu shifa babu abinda
Umar yay masa dan haka babu ruwansa da ɗaukar ma kansa hakkin ƙuntata masa. Wannan abu da
Harunan yayi yasaka mahaifinsu farin ciki, ya dinga saka masa albarka kuwa.
Shaƙuwar Haruna da Umar tasa Umar ɗin cewa Haruna ya bashi Habibu ya saka shi a makaranta, babu
musu kuwa Haruna ya bashi yana faman godiya. Sai dai rigima ta ɓarke dan Talle tace bata yarda ɗanta ya
koma hannun maƙiyinta ba. Shi ko yace bata isa ba dan ya bashi kuma babu yanda zatai. Rigima tai rigima
har Haruna yama Talle saki ɗaya, ya kuma ɗauki Habibu ya bama Umar. Sai da akaita roƙonsa Talle ta ma
kusa gama idda sannan ya maidota.
Rayuwar Habibu ta inganta, dan Lubabatu da zuciya ɗaya ta riƙe Habibu kamar ba uwarsa ce ba ta
gallaza mata. Habibu ya fara boko da islamiyya, kuma Alhmdllh yana fahimtar komai Dan yaro ne mai
ƙwazo. Yana son Lubabatu da Umar, dan yanda suke tattalin rayuwarsa har ji yake sunfi masa iyayensa,
saboda Talle masifaffiyace har su ƴaƴan nata ba daɗi suke ji ba. Sai da Habibu ya kammala primary sannan
ya fara zuwa Giro, dan malam ne ya saka wannan dokar saboda sanin halin uwarsa. Duk da cigaban da
Habibu ya samo bai hana Talle nuna tashin hankali da son ganin ɗanta ya dawo gareta ba. Sai dai kuma
babu yanda ta iya, dan Haruna ya tabbatar mata idan tai masa hauka sauran matan huɗu ma da take dasu
zai kwashe ya bama su Umar ita kuma ya saketa. Wannan furuci ya tada mata da hankali dole tai shiru,
amma ta koma yima Lubabatu habaici da gorin haihuwa dan ita tun wancan haihuwar bata sake ba har
yanzu. Yanda take mata gorin haihuwa haka sauran matan gidan suma suka fara, sai ya zam sam kwanakin
da sukai a Giro bai mata daɗi ba, bama su gama cika kwanakin ba tace ita dai zata koma. Haƙuri malam
Ibrahim ya dinga bata kamar ba surukarsa ba. Ita kuma tace ba komai baba. Haka dai suka dawo Giro harda
Habibu. Ashe ALLAH mai rahama mai jinƙai tana maƙale da ciki harna wata biyu.
Ta raini cikinta cikin aminci da yarjewar UBANGIJI, babu kuma wanda yasan da shi sai da ya shiga wata
takwas Baba Haruna yazo Kebbi ya ganta da shi. Ya taya ɗan uwansa murna matuƙa, yana dawowa Giro
kuwa ya fasa zance. Ashe shi Baba yasan da cikin, dan Umar ya sanar masa amma yay shiru dan ya fahimci
yanda Umar yake rayuwa a cikin yan uwansa da matansa, da yanda itama matarsa ke fuskantar ƙyara da
hantara wajen surukansa. Aiko wannan batun ciki sai da ya ɗaga musu hankali, musamman Talle, dan da
farko ma saida ta jefa cikin da mummunar kalmar data saka Haruna marinta. To babu dai yanda suka iya,
haka ALLAH ya sauki Lubabatu lafiya, ta haifo ƴarta mace. Habib yafi kowa farin ciki dan ya samu ƙanwa.
Giro baba yace su dawo ai suna, haka kuwa akayi duk da Lubabatu bata so ba, amma darajar baba zata iya
yin komai. Shagalin suna akai na garari na faɗa aji, dan Umar ya kashe kuɗi batuƙa, ta yanda a lokacin
kowama ya fahimci lallai ya kama ƙasa, dan lokacin tabbas kuɗi na shigo masa Alhamdullah. Sosai
mahassada su kuma suka zuba hassadarsu, dan su Talle dai habaici suke. Wai ai ta banza, idan ana son
nuna musu anyi kuɗin miyyasa bata haifi namiji Magaji ba. Babu wanda ya kulasu, dan sune jahilai. Bayan
suna da sati ɗaya suka shirya komawa Sokoto saboda makarantar Lubabatu data Habib, amma sai Talle tai
tsalle ta dire Habib bazai koma ba. Nan ma ubansa Haruna yace bata isa ba tayi kaɗan. Haka tana ji tana
gani suka tattara suka wuce suka barsu da ƙunar zuciya...
Bayan haihuwar Asiya Lubabatu bata sake ko samun ciki ba, dan haka ta maida hankalinta akan yaranta
biyu, wato Habib da Asiya. Gata suke musu matuƙa daga ita har Umar ɗin. Ga tarbiyya suna samu mai
inganci. Sosai Habib ke son Asiya, dan ita yake kallo a matsayin ƙanwarsa uwa ɗaya uba ɗaya ba ƙannansa
na Giro ba. Yakan je Giro ɗin, wani lokacin ma harda Asiya. Amma sam babu mai nunama Asiya soyayya sai
baba kawai da Baba Haruna. Sai ko shi Habib ɗin dake zama yayta kaffa-kaffa da ita duk da kuwa hakan
baya hana Talle dukanta da hantararta. Dan gaba ɗaya ƙiyayyar da takema Lubabatu da Umar ta koma kan
Asiya yanzu. A haka Umar ya kammala karatunsa. Ya nuna yana sha'awar aikin ƴan sanda. Aiko babu musu
Baba Umar ya sama masa. Ya fara aikin babu jimawa Asiya ta kammala secondary ta fara jami'a itama. Sai
kawai Baba Umar ya yanke shawarar haɗasu aure, koda ya tuntuɓi Lubabatu murna tayi sosai, dan
acewarta wa suke da shi bayan Habib ɗin dazai riƙe musu yarinya, Habib tarbiyyarsu ne hakama Asiya,
suna ƙyautata musu zaton alkairi. Wannan magana tata ta ƙara masa ƙwarin gwiwa ya nufi Giro da batun.
Anan ma Baba yayi matuƙar murna da sanya masa albarka, hakama baba Haruna. Amma sai Baba yace
suyi shiru da zancen kawai sai ranar ɗaurin aure. To dama akwai bikin jikokin gidan da za'ayi har su bakwai,
saboda yawan family ɗin da wahala kaga an tashi auren yara an aurar da ɗaya ko biyu. Hakan kuwa akayi,
aka fara taron biki batare da kowa yasan dana Habib da Asiya ba. Har ita Asiya da Habib ɗin kuma. To dama
yanzu indai za'a aurar da yara a gidan Baba Umar shike yin komai na hidimar batare da gajiyawa ba, duk da
ƴan uwansa basu taɓa gode masa ba sai ma zaginsa akan kullum baya musu. Baba Haruna ne kawai
mahaifin Habib ke ganin ƙyautatawarsa.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
6️⃣0️⃣6️⃣0️⃣
______________
........Ba ƙaramin tashi hankalin kowa yayi ba lokacin da akaji a ɗaure-ɗauren aure harda Asiya da Habib,
tab ɗin jan inji mata. Ai a ranar kowa yaga ainahin Talle a wannan gida. Tayi tujara ta fitar hankali, tai tsalle
ta dire akan bata yarda ba kuwa. Aiko Baba Haruna yace idan bata yardaba kuwa sai dai itama ta koma
gidansu da zama. Ansha rikici kam bana wasa ba, harma wanda basu san ainahin matsalar gidan ba da
takurar da Umar ke fuskanta da iyalansa kowa ya sani yanzu. Baba ne dai yasa Baba Umar da Lubabatu da
tsirarun danginta da sukazo biki, dan ƙanwartace ma kawai Shamsiyya da itama yanzu tayi aure a Kaduna
harda yaranta biyu. Sai dai mijinta yana tafiya da ita Lagos shiyyasa sukan daɗe basu haɗu ba.
Dama dai an tsara ma amarya da ango gidan zamansu anan Kebbi, dan haka can suka tare su. Sudai
suna musu addu'a da fatan zaman lafiya da zuri'a mai albarka. Alhamdullah Habib na nunama Asiya
kulawa, duk da kuwa a yanayin nasu kamar dai babu wanda ke son ɗan uwansa da kalmar soyayya sai dai
ƴan uwantaka, kawai iyayensu sun musu shigar sauri ne tunda basu tambayesu ba. Amma kuma bazasu
taɓa iya musu da su ba dan haka suka haƙura suka amshi juna kamar babu komai. A farkon zaman tarbiyya
da ilimi ne kawai ke jagorantar zaman auren, amma a hankali sai Asiya ta fara son Habib, so kuwa mai
tsananin gaske, tun bai fahimci ƙanwarsa ta faɗa soyayyarsa ba har ya fahimta. Dan haka ya sake ninka
kulawar da yake bata. Bawai shima Habib baya son Asiya bane ba, yana sonta shima sosai, sai dai shi Talle
mahaifiyarsa itace matsalarsa. Dan yana samun matsi a gurinta a duk sanda yaje Giro akan sai ya saki Asiya
komai daren daɗewa. Irin wannan abubuwan yasa yake jin bai son zuwa Giro ɗin ma, Asiya kuwa tunda
sukai aure bai yarda taje ba. Sai ya fake da karatun da take yi. Baba ne kakansu idan ya samu lokaci yana
shigowa Kebbi, shima Baba Haruna haka, dama ko zasuso zuwa sai dai domin su. Itama dai Asiya ta mayi
mahaifiyarta Lubabatu, dan sai da tai shekara biyar harta kammala karatunta ma da service sannan ALLAH
ya bata ciki, babu irin tujarar da Talle batayi ba akan wannan rashin haihuwa amma kowa yay uwar watsi
da ita har shi ɗan nata Habib. Dan yanzu ma ba'a Kebbi suke ba an maida shi aiki Zamfara can suke da
Asiya. Sosai Baba Umar da Mama Lubabatu sukai farin ciki da samuwar cikin ƴar tasu, hakama kakansu
Baba Ibrahim da Baba Haruna mahaifin Habib. Gambo kuwa sai taita aibanta cikin har sai da Baba ya
tsawar mata.
Ciki ya girma suka dawo Kebbi haihuwa, inda ALLAH ya sauki Asiya lafiya ta haifo ƴarta mace mai kama
da ita da kakarta Lubabatu. Babu ta inda yarinya ke kama da Habib gaskiya. Oho hakan bai damu Habib ba,
farin ciki yake shima ya samu ɗiya jininsa. Hakama Lubabatu da Baba Umar da Baba Haruna suna farin ciki
da samun jika. Giro aka koma akai suna saboda Baba, sunan daya haɗa hargitsi da farin ciki duk a lokaci
ɗaya, dan kuwa Talle ana kai mata ƴa ko taɓawa batai ba sai cewa tai ba ƴar Habib bace, dan babu ta inda
tai kamanni da shi. Wannan magana ta tada ƙura matuƙa, ƙura irin wadda a karo na farko Baba Umar ya
zuba tsiya irin wadda ba'ayi zaton ya iya ba. Dan sai da Talle ta raina kanta kuwa. Murmushi Baba yay tayi
dan shi kansa daya haifi Baba Umar bai san ya iya faɗa haka ba, saboda bayayi, shi mutum ne mai sanyi da
nutsuwa. Wannan tujara da Baba Umar yayi tasa aka samu sassaucin ƙarasa taron gagarumin sunan lafiya.
Ana kammala taron suna suka tattara suka koma, Habib ya wuce Zamfara yabar Asiya anan tana
wankan jego ita da jinjirarta mai suna *_Shahidah_*, sai ya koma zuwa musu weekend har suka kammala
wankan ta koma can Zamfarar wajensa. Bayan komawar tata ne ALLAH yay ma mahaifin mama Lubabatu
rasuwa. Hankali tashe suka wuce Minna ita da Baba Umar. Wannan tafiya itace ta canja komai daga
rayuwar Asiya Umar Ibrahim Giro (Ammie) itace ta canjata daga sarauniya ƴar gata zuwa baiwa da
ƙaddarorin rayuwa suka zagaye, dan kuwa a hanya Baba Umar da Mama Lubabatu suma sukai haɗari,
babu kuma wanda ya shura a cikinsu tun a wajen dan gawawwakinsu aka kawo Giro. Kamanta irin tashin
hankalin da Baba da Baba Haruna da Habib da Asiya suka shiga ma ɓata lokaci ne. Dan Asiya komawa tai
kamar ta zare ma. Sauran jama'ar gidan kuwa bazaka iya cewa ga abinda ke cikin zukatansu ba akan
wannan rashi. Bayan rasuwar su Baba Umar da sati biyu shima Baba ALLAH yay masa rasuwa. Dan tun da
yaga gawar Baba Umar da Lubabatu a kwance jikinsa ya rikice, abinka da dama ga tsufa. Asiya tayi kuka har
ta rasa hawayen zubarwa. Dan tasan ta rasa dukkan gatanta a family ɗin su sai Baba Haruna kawai ya rage
mata sai kuma Habib da ƴar ɗiyarta. Haka dai aka sha alhini komai ya lafa. Habib ya ɗauka Asiya dan su
koma Talle tace bai isa ba, ai kuma Asiya ta dawo Giro da zama kenan. Hankalinsa yay matuƙar tashi
hakama na Asiya. Gashi ta kafa matsa tsaurara dokoki ciki harda in Baba Haruna ya tambaya yace shine
yace zai barta ta ɗan huta. Idan ba hakaba ALLAH sai ta tsine masa. Wannan kalma ta girgiza Asiya Ammie
tace zata zauna kawai. Ta dinga lallashin mijin nata. Haka badan yaso ba ya shirya ya koma Zamfara ya
barta a Giro.
Rayuwa a Giro ga Ammie rayuwace mai tsanani da takura da damuwa. Tasha wahala matuƙa a hannun
Talle da suke kira Gwaggo. Gaba ɗaya Ammie ta fita a hanyyacinta kamar bata taɓa shiga ajin makaranta
ba. Ga Baba Haruna baya iya magana a yanzu saboda Talle ta danne masa kai a gidan teacher. Habib na
zuwa weekend, amma bai isa sauka ɗakin Asiya ba. Ko da dare idan ya shiga domin kwanciya babu kunya
Gwaggo ke zuwa ta buga musu tace ya taso ya koma ɗakin soro ya kwanta, inda ɗakin Baba kakansu yake.
Haka babu yanda zai yi zai fito. Tom dai kuma UBANGIJI ya nuna mata ita bata isa hana abinda ya hukunta
ba. Dan kuwa sai ga Asiya Ammie da ciki, gashi bata yaye Shahidah ba. Ta shiga tashin hankali, dan
mutanen gidan ƴaƴa da iyaye sun tasata a gaba da zagi da habaici wai mayyar miji jarababbiya tayi
gwanne. Abin kuma tsoro da firgici Gwaggo tace ai ciki bana Habib bane tunda ba kwana yake a ɗakin ba,
dama ai Shahidah ma ba ƴarsa bace. Magana kamar wasa ta nema zama babba. Dan har gari ya ɗauki
wannan zance. ALLAH gafurin rahimun sai ga Baba Haruna ya dawo hankalinsa a lokacin, dan kuwa asirin
Gwaggo ya sakesa. Shine ya bama Asiya kariya har ya sake yina Gwaggo saki ɗaya. Ya rage saura igiya ɗaya
a tsakaninsu kenan. Wannan saki shine fa ya sake haddasa wutar ƙiyayya tsakanin Gwaggo da Ammie. Da
ƙyar dai Mahaifiyar Baba Haruna tasa ya dawo da Gwaggon dan ƴar ƙanwarta ce dama auren zumunci akai
musu. Gwaggo ta dawo amma ta ƙara ninka ƙiyayyarta ga Ammie, sai dai a yanzu Baba Haruna na tsaye
akan al'amarin Asiyar, dan ya ma fara shirin Asiya tabar giro tabi mijinta. Amma sai ta haihu kodan yanayin
samun cikin.
Haka Asiya taita rainon ciki cikin matsi da takurar surukarta. Ga Shahidah dake ta fama da ciwo. Babu
mai taimaka mata a gidan har tsoffin gidan saboda Gwaggo ta zama boss ga kowa. ALLAH ya sauki Asiya
lafiya ta sake samun mace mai kama da ita itama kamar Shahidah. Aiko Gwaggo ma ta sake aibanta jinjira
tace ba ɗiyar Habib bace. Sai da Baba Haruna yay mata tas. Baba Haruna shine ya tsaya akan komai akai
suna yarinya taci suna Lubabatu, amma sai suke kiranta Amaal koma ace Asiya da Habib ke kiranta. Dan su
dai ƴan gidan Lubabatu suke cewa. Zuwa lokacin an ma Habib transfer zuwa Maiduguri. Dan haka ana
gama bikin suna ya sake shirya komawa. Sai Baba Haruna yace ya ɗauki matarsa su tafi. Hankalin Gwaggo
ya tashi akan hakan amma Baba Haruna yace bata isa ba kuwa Habib kamar ya tafi da iyalinsa ya gama.
Hakan yama Habib daɗi, ya ɗauka Asiya da yaransa biyu suka wuce abinsu, suka bar Gwaggo na tujara.
Wannan tafiya ita ce ta samawa Ammie sauƙi, suka koma Maiduguri da zama ta samu damar rainon
yaranta cikin aminci, anan ta koya gyaran jiki da haɗin turarruka. Shekararsu biyu a Maiduguri aka sake
masa transfer zuwa jihar Nasarawa. Nan ma ya kwashesu suka koma. Anan ɗin ma shekararsu uku aka sake
maida shi Sokoto, zuwa lokacin kuma bata sake haihuwa ba. Yaransu Shahidah da Amaal sunyi ƙyau abinsu
yara kamar ka lashe, dan Ammie ma ƙyaƙyƙyawa ce kamar mahaifiyarta. Dole kaga yaran nan sai ka tanka,
dan kamar wasu ɗiyan hamshaƙin mai kuɗi bana ɗan sanda mai ƙaramin muƙami ba. Shima Habib yana
son yaransa, sai dai irin mutanen nan ne shi da bai cika jan yaro a jiki ba, komai dai na buƙatar rayuwa yana
tsaye a kansu. Dan ko ita Ammie bazata ce ga wata soyayya a bayyane da yake nuna mata ba. Baya dai
takura rayuwarta ko hanata duk abinda take so, ba kuma ya nuna mata tsantsar soyayya a zahirance. Ga
wanda ma bai sansu da ƙyau ba idan yaga rayuwar zamansu sai ya ɗauka tana a cikin matsin rayuwa ne.
Sun tattaro sun dawo Sokoto, a lokacin Shahida nada shekara bakwai, Amaal nada shekara biyar da wasu
watanni dan tsiransu da Shahidah kaɗanne. Saida sukai sati biyu a Sokoto sannan suka je Giro. Babu wanda
bai firgita da canjawar Asiya da yaranta ba. Dan ta koma ƴar gayunta kamar batai rayuwar Giro ba. Tuni
kishinta da hassada ya shiga zukatan jama'ar gidan kamar yanda suka dingama mahaifiyarta Lubabatu. A
ɓangaren Gwaggo ma babu abinda ya canja, dan ƙiyayyar Asiya sai wacce tai gaba. Haka su Shahidah ko
kallo basu isheta ba dan tace ita ba jikokinta bane ba uwarsu dai tasan inda ta samo su. Hakan na ma
Habib ciwo amma baya cewa komai. A wannan zuwa kuma Gwaggo ta tsira sai Habib ya ƙara aure, dan a
haifa masa namiji. Kai tsaye ya nuna mata bashi da wannan ƙarfin, dan shi dai bamai kuɗi bane, dukiyar da
yake juyawa kuwa kowa yasan ta Asiya ce da iyayenta suka bar mata duk da ma dangin nasu sun kusa cinye
rabi da kwata. Aiko ta tujaresa da masifa da bala'in daya sashi tattara matarsa da ƴaƴansa suka koma
abinsu. Sai kuma suna komawar sai ga Asiya da ciki. Yayi farin ciki matuƙa, ya kuma shiga addu'a da fatan
ALLAH yasa Asiya ta haifa namiji dan shima fa yana son a haifa masa namijin, ga maganar mahaifiyarsa ta
sake kwaɗaita masa abun a rai. Kawai dan bashi da ƙarfin aure ne. Amma tabbas a ransa yana son ƙara
auren ma. Dan yana ɗan neman mata batare da Asiya ta sani ba, tun kafin yay aure yake yi, bayan aurensu
ya rage sosai sai dai kuma ita dama zina masifa ce. Faratane mara wuya, amma indai ka fara sai ALLAH ya
soka da rahama kake dainawa.
Ammie tayi rainon cikinta cikin aminci da kulawa, har ALLAH ya kai cikin watan haihuwa ta haihu lafiya.
Ta samu ƴa mace ma a wannan karon. Sai da Habib yaji wani iri a ransa, sai dai kuma yana ɗaura idonsa
akan yarinya yaji ƙaunarta ta shigesa. Dan ita kam tayo kamannin mahaifiyarta da ƴan uwansa, ta kuma yo
kammaninsa ta bangarori da dama da suke a bayyane........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
6️⃣1️⃣6️⃣1️⃣
______________
.........Wannan karon ma dai Giro suka koma suna, sai dai babu wanda ya nuna murna da wannan haihuwa
kamar ta Amaal daga Baba Haruna sai uban jegon sai kuma su Shahidah dake murna an haifa musu ƙanwa.
Wannan karon dai Gwaggo babu damar aibanta yarinya tunda tana kama da ubanta a abubuwa da dama.
Amma hakan bai hana sako batun haihuwar ɗa namiji ba data fahimci yana tasiri a zuciyar ɗan nata. Haka
dai akai bikin sunan babu wani armashi sosai sukai shirin komawa Sokoto amma sai Gwaggo ta hana wai su
zauna anan suyi wankan jego. Ganin yanda bata kawo tashin hankali ba a sunan yada baba Haruna tunanin
ta sauya ne. Dan yanzu ta ɗan rage wasu abubuwan a zahirance saboda tsoron kada ta tsinke ƴar sauran
igiyar ɗaya dake a tsakaninsu. Ta koma zuba rashin mutuncinta ta ƙasa, dan Habib ta koma takuramawa
akan sai ya ƙara aure, ita kuma Asiya ana mata a kaikaice.
Shima dai Habib wannan karon bai damu ba ya barsu anan ya kuma yarda da batun ƙara aure, dan ya
samu damar sheƙe ayarsa da sabuwar karuwarsa da suka haɗu anan Sokoto ɗin kwanan nan. Zama kamar
wasa ya nema zama gaske. Dan bayan gama wankan jegon Maanal Habib bashi da niyyar cewa su shirya
komawa Sokoto, sai dai yana zuwa duk ƙarshen wata yay musu weekend ya koma. A haka aka tado batun
aurensa. Auren daya bama kowa mamaki ya kuma saka Ammie a tashin hankali. Amma sai Baba Haruna ya
dinga kwantar mata da hankali da nasiha ta sakama kanta dangana kuwa ta rungumi ƴaƴanta. Cikin
ƙanƙanin lokaci akasha biki kuwa, yarinya ƙarama da bata wuce shekara sha bakwai ba. Inda Ammie ta
burge kowa shine tattara komai ta watsar kamar ma ba ita akama kishiyar ba. Sai shima kansa Habib ɗin ya
dinga kiyaye duk wani abu da zai taɓa mata zuciya ba kamar yanda Gwaggo taso ba. Itama yarinya da aka
ɗoro akan rashin kunya da zata dinga yima Ammie sai ta dinga jin shakkarta. Abinda ya ragema amarya
armashi samunta ba'a cikakkiyar mace da Habib yayi ba, dan tun a daren farko sai da tasha maruka a
wajensa a ɗaki batare da sanin kowa ba. Ko sati kuma bai cika ba na amarci ya tattara ya koma wajen aiki.
Aiko akaita gutsiri tsoma wai Ammie ce tayi wani abu, dan Gwaggo har ɗaki ta sameta ta mata wankin
babban bargo. Ita dai batace komai ba. Habib bai zo gida ba sai da yay wata guda kamar yanda ya saba, ya
kuma murje idonsa ya sauka ɗakin Ammie, itako tanata roƙonsa bai kulata ba, ana cikin haka sai ga
Gwaggo har ɗaki, tas taima Ammie da zaginta akan muna fuka ta tasa ɗanta gaba har ɗakin amarya Sailu.
Ai ko ranar ma maimakon ta samu kulawa a wajensa sai duka taci a banza, dan ya fahimci bata da kunya,
Habib kuwa irin mazan nan ne da basa ɗaukar raini, shi hatta macen bariki tai masa hauka duka take ci a
wajensa, Ammie ce kaɗai ta tsira da irin wannan halin nasa, duk da yana shan marinta itama a wasu
lokutan. To ataƙaice dai wannan aure bai rufa wata biyar ba a wani zuwa ya saki Sailuba saki har uku. Nan
fa gari ta ɗauka Ammie ce ta koreta. Babu kalar abunda Ammie bata gani ba akan wannan rabuwar auren
amarya da mijinta, ƴan gidan suka kara tsananta, na Gwaggo kam ai ba'a magana. Ga Habib bashi da
niyyar cewa su shirya subar garin har sai da Maanal ta shiga shekara ɗaya da rabi sannan akaima Habib
transfer zuwa Kano. Aiko Baba Haruna da'a yanzu ya fahimci Habib na neman matan banza yace ya tattara
matarsa da iyalansa su wuce tare. Gwaggo ta nuna bata yarda ba, Baba Haruna ya nuna mata shima bata
isa ba. Kamar Habib baya so haka ya wuce da su Ammie Kano, dan yasan an rage masa jin daɗinsa ne
kawai. Anan ya samu gida ya kama musu haya, daga baya kuma ya saye shi da kuɗin Ammie na gado, shine
dalilin komawarsu da zama garin Kano. Tunda suka koma kuma basu sake zuwa Giro ba sai dai shi yazo sau
uku sai yanzu shekara kusan shidda kenan dan tun Maanal nada shekara ɗaya da wasu watanni da kaɗan
ya rage sukai biyu. Ita dam bata san Giro ba bata san ƴan Giro ba....
________★★★
Babu wanda ya sake bi takan su Ammie a gidan duk da wasu suna son kawo musu abinci suna jin tsoro
ne. Anan ƙofar ɗakin sukai sallar magrib da isha'i. Sai kusan tara saura Babu ya shigo tare da Baba Haruna.
Ganinsu a inda ya barsu su da kayansu ya sosa masa zuciya sosai. Baba Haruna kam a fusace ya shiga ɗakin
Gwaggon. Sosai ya mata tas da abinda tayi ɗin, ya kuma tabbatar mata wlhy a wannan karon idan tace
zatai wani abu to ta tabbatar shi bazai ɗauka ba ƙofa a buɗe take gareta. Wannan kalmar na tayar mata da
hankali akan mijin nata. Dan tasan igiyar nan ɗaya tak ke riƙe da aurensu yanzu. Bakuma zata so ace ya
tsinketa a yanzu da suke a shekarun tsufa surukai cike da gari ba. Shi da kansa ya fito ya shiga dakin dake a
mallakin Ammien, ɗakin duk tarkace ne ma a ciki, dan haka ya fita babu jimawa sai gashi da almajirai kusan
biyar, su ya saka gyaran ɗakin, shi kuma Babu ga fita nema musu abinci da maganin da Maanal zata sha
dan zazzaɓin ya dawo. Dandanan aka gama gyara ɗakin, aka kawo katifa da tabarmi aka saka musu. Harda
turaren wuta na tsinke baba Haruna ya ɗakko a ɗakinsa aka kunna, dan yanzu shine ya mayi mahaifinsu a
gidan, shine ke da almajirai yake koyarwa, dan haka ya koma ɗakin zaure inda suka samesa na mahaifinsu
da zama kenan. To da yake tunda yaga Gwaggo na niyyar kashe katifar dakin Ammien sai ya saka aka
ɗauketa ya maidata can ɗakin nasa aka lulluɓeta, sai idan Babu yazo ake kawo masa, daya tafi kuma yasa a
maidata can.
Gajiyar tafiya tasa basu ma wani iya cin abincin kirki ba dan ma harda shayi, suna son yin wanka basu
san yaya zasuyi ba, dole suka hakura suka kwanta a haka. Dama ita Maanal tuni tayi barci abinta, duk da
barcin nata bana daɗi bane ba. Washe gari dai sun ɗan samu kulawar mutanen gidan sakamakon ganin
Baba Haruna tsaye akan al'amarin su. Dan har koko an kakkawo musu a wasu sassan. Duk da ma dai su
yaran sun kasa sha sai Ammie ce tasha. Kosan da Baba Haruna da bread ya saya musu kawai suka iya ci, sai
naman jiya da Babu ɗin ya saya musu basu ci ba. Yanda Maanal ta tashi da zazzaɓi sosai dole Babu ya
ɗauketa zuwa asibiti. Ƙarin ruwa suka saka mata dan jikinta duk babu ƙarfi, hakan yasa suka jima can har
sai bayan zuhur ya dawo da ita. Anan ne yake sanarma Ammien Abban Fadeel ya kira shi sun gaisa, itama
Oum nata nemanta wayar a kashe.
Sai lokacin Ammie tama tuna da wayar tata, ta bincikota a bag sai taga ashe ta mutu ma babu caji. Dole
ta bama su Shahidah tace suje waje su nema yara su rakasu inda ake caji sukai mata. Badan sun so ba suka
fita, dan basa ƙaunar ganin hararar da Gwaggo ke musu da kallon tsana. Sai zuwa yamma suka amso mata
tai kiran Oum, lokacin Maanal ta tashi a barci amma sai ƙunci take taƙi kula kowa abinci ma sai da Ammie
tace zata zaneta sannan taci sa kaɗan. Amma yanzu tana jin ance Oum tai wata irin zabura tazo ta nanuƙe
Ammie. Dole Ammie ta taƙaita gaisuwar da suke da Oum ɗin ta bata wayar, dan yi take ma kamar zata
warceta. Oum na jin muryar Maanal itama ta saki murmushi...
“Oh oh! My Baby I miss you”.
Cike da zumuɗi Maanal ta ce, “I miss you too Oum. Oum ina Besty?”.
Dariya Oum tayi tana mai jinjina kanta idonta akan Ajwaad dake kwance a gadonta, tunda yaji ta ambaci
sunan Maanal shima ta kafeta da idanunsa. Wayar ta miƙa masa tana faɗin, “Gashi nan kin barsa da ciwon
kewa”.
Baki Maanal ta tura gaba, cike da shagwaɓa ta ce, “Oum ai nima banda lafiya ina ciwon kewarsa”.
Dariya Oum ta sanya, hakama Shahidah da Amaal. Ammie kama sai ta girgiza kanta kawai. Ganin su
Shahidah na mata dariya ta tashi tana harararsu da murguɗa musu baki ta fice a ɗakin. Ammie na kiranta
akan ta kawo mata wayarta kar tai mata ɓarna bata dawo ɗin ba. Gwaggo na tsakar wajen nasu tana
haɗama dabbobinta dusa, suna haɗa ido da Maanal ta harareta, itama ko ta rama da murguɗa mata baki
ta ɗauke kanta. Ai sai Gwaggo tai mutuwar tsaye da mamakin wannan fitsararriyar yarinya. Ita zata harara
ta rama wannan jaririyar ƴar?.
Oho ko'a jikin Maanal, dan kujerar Gwaggo dake a ƙofar ɗakinta ta zauna abinta. Sai kuma cikin
shagwaɓa ta ce, “Besty!”.
Wata irin ajiyar zuciya Ajwaad ya sauke yana lumshe ido da ya zame masa ɗabi'a duk da ƙarancin
shekarunsa. Sai kuma a cikin muryarsa mai sanyi da zurfi ya amsa da, “Oummyim!”.
“Haushina kake ji dan na tafi na barka? Banfa da lafiya nima, yau har asibiti Babu ya kaini akamin karin
ruwa”. Ta ƙare maganar muryarta na rawa alamar son yin kuka. Tashi zaune Ajwaad yayi sosai, cikin
damuwa ya ce, “To kar kiyi kuka, nima banda lafiyan ai, jiya saida aka min ƙarin ruwan”.
Kukan ta sakar masa kuwa, da faɗin, “Besty nidai kace Babu ya dawo dani wajenka. Ni bana son nan.
Akwai muguwar mata a garin. Yanzu ma ka ganta sai hararata take...” kuka sosai yaci ƙarfinta
Sosai hankalin Ajwaad ya sake tashi daga can, sai ƙoƙarin lallashinta yake yi amma tana ƙara ƙarfin
kukan harda tutturza ƙafafu. Ga Gwaggo ta zuba mata wani shegen kallo. Kukanta yasa Shahidah fitowa.
Sai dai suna haɗa ido da Gwaggo ta koma ciki da sauri. Dama a tunaninsu ko wani abu akama Maanal ɗin
tunda sun san halin muguwar kakar tasu sai a hankali ce. Sosai Maanal take kuka har sai da Oum ta amsa
wayar daga hannun Ajwaad da duk ya rikice da kukan nata itama tana lallashinta da tabbatar mata Bestien
nata zaizo ya sameta. Da ƙyar tai shiru sannan Oum ta maida ma Ajwaad waya suka cigaba da hirarsu mai
cike da shirme da shiririta musamman ga Maanal dan ko yaya shi Ajwaad ya ɗan tasa ya fara hankali....
Sam rayuwa a Giro batama Ammie da yaranta daɗi. Maanal ce ma dai babu ruwanta, tashin hankalinta
kawai ace ta yini batai waya da Ajwaad ba. Anan ne zaka ganta kamar mara lafiya. Amma da sunyi waya sai
ka walwalarta ta dawo. Sai ma ta fice wasa cikin gida abinta. Maanal dai dama jaruma ce a fagen iya faɗa
da tsokala, anan ɗin ma duk da matsin da suke a ciki bata canja ba. Dan kuwa jibgar ƴaƴan mutane take yi,
idan kafi ƙarfinta kasha ƙasa a cikin ido. Gwaggo kuwa idan ta harareta itama ta rama. Ɗakinta kuwa kai
tsaye take shiga tace tana son abu kaza. Idan Gwaggon ta korota da zagi taƙi fitowa. Kota warto abinda
take so ɗin ta fito a guje. Wannan hatsabibancin nata yasa Gwaggo tafi tsanarta fiye da kowa. Kullum cikin
aibantata take da zaginta. Abin na damun Babu da Ammie sai dai babu yanda zasuyi, dan Ammie tama
Maanal faɗa akan shiga harkar Gwaggon amma yarinyar nan data faki idon Ammie sai tasan abinda taima
Gwaggo. A haka dai sukai sati uku a Giro, duk sun fita hayyacinsu sunyi baƙi sun rame saboda rashin abinci
mai inganci. Suna a kwana na ashirin da biyar Babu yazo ma Ammie da batun wai zai yi aure. Sannan suma
kawunan sa sunyi magana akan Shahidah da Amaal ya kamata a musu aure dan sun isa, musamman ma
Shahidah data fara zama uwar mata. Dan haka sun yanke hukuncin ita Shahidah ta auri Lado ɗan wajen
Badaru. Ita kuma Maanal Ƙasimu ɗan wajen Sagiru. Wani irin tashin hankali ne ya ziyarci Ammie. Ita ba
auren Babu ɗin ne damuwarta ba, batun Shahidah da Amaal.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
6️⃣2️⃣6️⃣2️⃣
______________
.......Kuka sosai Ammie ta sanya ma Babu da roƙo da magiya, amma sai ya nuna mata shima bada son ransa
bane. Dan bazai so yaransa suyi rayuwar garin ba, ba kuma zai so a yanke musu karatunsu ba. To amma
bazai iya jayayya da ƴan uwan mahaifinsa da ƴan uwansa ba. Ina sam wannan batu bai shigi Ammie ba.
Dan tasan wannan ba umarnin kowa bane sai Gwaggo. Hankali tashe taje ta samu Gwaggo da kuka da
roƙo, sai Gwaggon ta rufeta da zagi ta kuma juya maganar. Dan kuka ta sanya da kururuwa wai Ammie ta
sameta har ɗaki tana mata gargaɗi idan bata saka Babu ya janye batun ƙara aurensa ba sai tabi dare ta
kasheta. Dandanan wajen ya cika da mutanen gidan harda makwafta. Kasancewar Ammie nada tabon fitar
kishiya yasa kowa ya yarda da batun Gwaggo. Nanfa akaita cancana magana da zagin Ammie har saida
Baba Haruna ya shigo gidan ya tsawatar.
Sam Ammie bata san miya rufema Babu ido ba, yana dawowa gidan Gwaggo ta faɗa masa ƙarya da
gaskiya sai ya hau ya zauna. Aiko ya birkice mata yayta tujara a tsakar gida mutane naji, shi bazai yarda a
raina masa mahaifiya ba. Ai ba a kanta aka fara kishiya ba. Shi ya gaji da baƙin halinta. Idan bata gode masa
ba bata tsine masa ba. Shekara nawa yana zaune da ita zaman haƙuri badan ya taɓa jin sonta a zuciyarsa
ba ko sau ɗaya. Sai dan kawai kar ace yama iyayenta rashin halacci ya kasa riƙeta. Shima namiji ne, yana
son ya auri wacce yake so, yana son haihuwar ɗa namiji.. kai tujara dai kala-kala data sanya Shahidah da
Amaal kuka sosai. Ita dai hajiya Maanal hidima bata san ma anai ba. Tana can tare da Baba Haruna daya
fita da ita gaisuwa gidan wani abokinsa. Ammie tayi kuka har ta godema ALLAH, taji inama iyayenta na
raye, ashe duk zaman da take da Babu ba soyayyarta a ransa har zuwa yanzu...
Anyi haka da kwana huɗu Babu baya kulata hakama ƴan gidan kowa ya ƙara ɗauke mata wuta ita da
ƴaƴanta sai ga batun yima Shahidah da Amaal wai baiko. Ranar ji Ammie tai kamar tabar duniya ta huta.
Karon farko ta sami Baba Haruna da roƙo. Yayi mamakin jin bada son ranta ake shirin auren yaran ba. Dan
shi Babu ya nuna masa komai da amincewarta ne. Lallashinta yayi akan hakan, yace taje zai zauna da ƴan
uwansa akan al'amurin. Wannan ya sakata ɗan jin sanyi a ranta. Sai dai me, koda Baba Haruna ya zauna da
ƴan uwansa duk sai suka kasa fahimtarsa, ƙarshe ma mahaifiyarsa da har yanzu tana a raye duk da ta tsufa
sosai ko tafiya bata iyayi sai tace idan bai bari amma yaran nan aure ba bata yafe ba. Hauka ake yara sunyi
zagada-zagada ace an barsu babu aure. Ko so yake suna a musu irin yanda Umaru yay ma ita Asiya ɗin
kamar ƴar arna sai da ta shekara ashirin a gida. Wannan yasa dole Baba Haruna ya bar maganar, ya kuma
dinga lallashin Ammie. Ina hankalin Ammie ya kasa kwanciya, dan ko maƙiyinta bazata so ya kasance cikin
wannan zuri'ar ba balle ɗiyanta. Balle kuma yara ƙanana kamar su Shahidah. Inama ƙudan yake ballantana
romonsa.
Komai yama Ammie tsanani, dan sun tabbatar mata bazata koma da su Shahidah ba. Maanal ma za'ayi
mata miji da lokaci yayi su dawo da ita gida. Ranar da aka saka ranar auren daya kasance sati huɗu kacal
Ammie batai kwanan lafiya ba. Dan jininta hawa yayi ƙololuwa sai a asibiti ta kwana. Duk da wannan halin
da take ciki sai zaginta mutane keyi wai kishi ne. Tana kishi dan mijinta zai ƙara aure. Babu wanda yay mata
uzuri akan ƴaƴanta da ake shirin musu auren fin ƙarfi. Washe gari ta ɗan samu dai-daito, iya tunaninta ta
rasa wazata tunkara ya taimaketa ya kuɓutar mata da yaranta, ƙanwar mahaifiyarta Shamsiyya kawai ta
sani, itama a yanzu bata san duniyar da take ba. Dan tun bayan rasuwar iyayenta bata sake ganinta ba.
Minna kuwa dama ba zuwa take ba tunda babu wanda ta sani sai kakanta ko'a lokacin, sai matarsa mara
mutunci, yanzu kuma babu shi wajen wa zataje?. Wannan mutanen sune dangin mahaifinta, su kawai ta
sani. Sai su Oum da suka zame musu ƴan uwa yanzu a garin Kano. A wannan karon kam sai kawai ta yanke
shawarar kiran Oum ɗin, dan itace kawai mafitar data rage mata.
Bayan ta gama zayyanema Oum komai tana kuka itama Oum ɗin kukan take. Da ƙyar suka lallashi juna
Oum tace ta saurareta zatai magana da Aban Fadeel in sha ALLAHU za'a kuɓutar da su Shahidahn daga
wannan auren. Wannan waya itace ta sanya Ammie jin ɗan sanyi a ranta, har jininta ya ɗan sauka aka
sallameta daga asibitin a ranar....
Washe gari kusan azhar saiga Amaal data fita sayo mata fura ta dawo cike da ɗoki. Kallonta Ammie da
Shahidah keyi, sai kuma Shahidah ta ce, “Ke kuma ina furan? Kin san fa Ammie bataci komai ba ga magani
zata sha”.
Zama Amal tayi da faɗin, “Yanzu zan koma na sayo, Abah na gani a waje tare da Ajwaad”.
Da mamaki Shahidah ta ce, “Aban Kano wai?”.
Cike da zumuɗi Amal ta amsa mata da “Eh”.
Ba ƙaramin waro ido Shahidah tayi ba. Yayinda Ammie ta saki murmushi mai faɗi tana rufe idonta sai ga
hawaye sharrr. Da sauri tasa hannu ta goge kafin yaran su gani, wata irin ƙaunar Oum na ratsa mata zuciya
da ruhi. Kallon Maanal dake barci sukai, Shahidah ta ce, “Lallai yau da bidiri a gidan nan ga Bestyn Maanal
a Giro”. Dariya Amal tayi tana matsawa kusa da Maanal ɗin ta shiga tadata. Da faɗa kuwa ta tashi, dan
dama faɗan sukai da wata yarinya a gidan ta fasama yarinyar baki shine Ammie ta daketa tai barcin dole.
Dan uwar yarinyar har sashen tazo tana faɗin bazata yarda ba sai ta daki Maanal, yarinya duk tabi ta
addabar musu yara. Haƙuri Ammie taita bata amma matar nan sai da ta gama cima Ammie mutunci da
gori sannan tabar sashen. Hakkanne ma ya saka Ammie kasa cin abinci dan kanta wani irin ciwo yake mata
mai zafin gaske......
A cikin gidan ma tuni labari ya kai musu daga bakin yaransu. Kasancewar duk suna a ainahin babban
tsakar gidan kowa na ayyukansa. Masu surfe, masu sakar mahucin kaba, bamu hira, masu sana'oinsu. Sun
ɗauki ƙus-ƙus ɗin zance sai ga wani almajiri ya shigo hannunsa niƙi-niƙi da kaya wani matashin yaro biye da
shi. A zahirance dai yaro ne, dan dudu bai wuce shekaru goma sha ba. Sanye yake cikin ƙananun kaya na
jeans daga wandon har jacket ɗin saman duk sky blue. Sai rigar ciki data kasance red haka ma belt ɗinsa da
boot ɗin takalmansa. Ƙyaƙyƙyawar fuskarsa sakaye da farin siririn gilashi mai shegen ƙyau da a kallo ɗaya
zaka fahimci mai tsada ne duk da kuwa na ƙarin gani ne. Tafiya yake a nutse babu hayaniya balle garaje,
kallo ɗaya kuma yayma tarin matan dake cike da tsakar gidan ya kauda nasa idon ganin yanda suka zuba
masa idanunsu har yana jin tsigar jikinsa na tashi.
Cikin muryarsa mara ƙarfi da hayaniya ya gaishesu a jimlace batare da ya damu da sunji ko basu jin ba,
shi dai yana biye da almajirin nan da kai tsaye ya nufi sashen Gwaggo. Suna gab da shiga sai ga Maanal a
guje ta fito har tana ture almajirin. Kanta tsaye Ajwaad tanufa, shima da ya jiyo ihunta tuni ya tsaya cak
yana kallonta. Ko damuwa da yanda jikinta yay buɗu-buɗu da ƙasar danben da sukai kafin tayi barci ma
baiyi ba. Tuni ya buɗe mata hannayensa tazo ta shige jikinsa. Yako ɗagata camak sama yana juyi da ita
illahirin fuskarsa na washewa da wani irin sassanyar murmushi daya bama ƴan gidan mamaki. Dan daya
shigo sam babu alamar fara'a a tattare da shi. Sai da yay juyi sosai da Maanal dake ƙyalƙyala dariya kafin ya
sauketa, sai kuma ta sakar masa kuka. Zuru yay yana kallonta, sai kuma ya kai duƙe a gabanta dan ya fita
tsoho sosai, duk da kasancewarsa yaro shi ɗin dogo ne kamar sauran yayunsa da mahaifinsu. Tuni fuskarsa
ta koma ta tsuke daga murmushin da yake, idanunsa farare tas da kamar an watsa madara sun fara canja
launi.
“Is something bothering you?”. Ya tambaya kamar wani babba yana tsatstsareta da idanunsa. Ƙara
ɓarkewa Maanal tayi da kukan iskanci, tare da faɗin, “Ni tare dakai zan koma. Bana son nan mugaye sunyi
yawa. Kullum su Safare sai sun dakan, Ammie ma haka, su Didi ma suyita zaluntata. Wicked old woman ɗin
can taita min harara da zagina tana cemin shaiɗaniya. Kowa cutata yake anan ƙauyen Baffa ne kawai ke
sona da saya min kayan daɗi. Kuma dama na faɗama su Lami duk randa kazo saika rama min duk abinda
suke min.”
Sosai ɓacin rai ya bayyana a fuskar Ajwaad. Har yama ji ya kasa magana. Dan shi fa idan kana son kaga
ainahin fushinsa to kuwa ka taɓa Maanal. Ko Ammie da Babu dan baida yanda zayi ne kawai....
“Ajwaad!”.
Sassanyar muryar Ammie ta saka shi janye idanunsa daga kallon Maanal ya maida ga Ammien.
Murmushi ta sakar masa da faɗin, “Kaga tashi kaji karka biyema wannan ibilishiyar. Kadai san halin
mutuniyar taka maza taso”.
Dan Ammie ce kawai ya tashi, hannunsa riƙe dana Maanal suka shiga. Su Shahidah na masa sannu da
zuwa yana faman balla musu harara. Amaal daba barin saita kwana take ba itama tai saurin faɗin oh har an
kai maka munafuncinmu kenan?”.
Caraf Maanal dake naniƙe da shi ta murguɗa mata baki da faɗin, “E ɗin an faɗa, kuma duk abinda kuka
min sai ya rama min har ma Ammie ko Besty?”. Tai maganar tana kallon AA. A hankali ya jinjina mata
kansa, sai kuma ya ce, “Amma banda Ammie”. Fuska ta ɓata sai kuma ta sanya kuka tana turza ƙafafu. “Ni
dai harda ita Besty, kullum fa sai ta dakan, yanzu ma ta daken ta sani barcin dole.....”
“An dake kin, oh ni Asiya nima ƙarar tawa kika kawo wajen Ajwaad ɗin?”. Ammie ce tai maganar tana
ajiyewa Ajwaad ruwa a gabansa. Sai kuma ta zauna idonta na harar Maanal ta ce, “Karma ka bari ta ɓata
maka rai kaji Ajwaad. Yarinyar nan tabi ta fitini ƴaƴan mutane a gidan nan, kullum babu ranar banza saita
fasa kan wani ɗan kota jawo min magana. Fitinar Maanal ta isheni wlhy. Kuma ALLAH in baki min shiru ba
zan miki duka agaban Ajwaad ɗin”.
Sarai Maanal ta san halin Ammie, tanada zafi akansu, sanyinta akan Babu ne kawai da mutanen gidan
nan nasu. Muƙut ta haɗiye kukan tana mai lafewa a jikin Ajwaad. Cikin maganar nan tasa sanyi-sanyi ya ce,
“Ammie kiyi hakuri, amma idan bata ramawa ai sai suyita dukanta. Yanzu ma jiba duk yanda ta rame tai
baƙi”.
Baki Ammie ta saki tana kallonsa. Yayinda Shahidah da Amaal ke kwasar dariya. In dai Ajwaad ne zai yi
fiye da haka akan Maanal, dan haka Ammie ta ce, “Shike nan ai dama kai ke ɗaure mata ƙugu, amma dai
kubi a hankali, dan ina tsoratar muku randa hajar mai gari zata tsinke”.
Babu dai abinda Ajwaad yace, amma Maanal sai tura baki take yi. Koda aka kawo masa abinci bai iya ya
nutsu yaci ba sai da ya dinga bama Maanal a baki. Itama sai ta dinga amsar spoon ɗin tana bashi. A haka
Baabu da Aba suka shigo. Suma dai tsayawa sukai kawai suna kallonsu, sai kuma suka kalli juna suna
murmushi. Al'amarin yaran na ƙara tasiri a zukatansu. Cike da farin ciki Maanal ta tafi ta rungume Aba.
Shima ya ɗauketa yana dariya da faɗin, “Oh oh my Baby, Autar Oum kuma Bestyn Auta”.
Dariya Maanal ta sanya da jin wannan kirari na Aba, hakama Ammie da Baabu. Zama Aba yay da ita a
jikinsa tana masa surutu, shiko yana biye mata dan harga ALLAH yana ƙaunar yarinyar, yanama ɗansa
sha'awa da fatan wannan kusancin da shaƙuwar ya kasance musu har girma su kasance ma'aurata, duk da
shi fa ko'a yanzu da su Baabu zasu amince wlhy baiƙi a ɗaurama yaran aure ba kawai. Yana dannewa ne kar
ace ya cika azarɓaɓi, ba kuma asan mi gobe zata zo da shi ba.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭_*
[2/11, 9:48 PM] Maryam anas: *_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
6️⃣3️⃣6️⃣3️⃣
______________
.........Sai da Aba yasha furar da Ammie ta kawo masa sannan suka zauna tattaunawa. Gently Ajwaad ya
miƙe idonsa akan Maanal dake tama Aba surutun Giro har yanzu. Nuni ya mata data tashi, ta maƙe masa
kafaɗa bakinta a sama. “A'a ni ban gama ba Aba labari ba. Ka zauna na ƙarasa masa sai muje na nuna maka
su Hanne dake dukana ɗaya bayan ɗaya ka musu duka har ɗakunan uwayensu”.
Harararta Ajwaad yayi, sai kuma ya sake tsuke fuska. “Idan baki taso ba ALLAH nan zan barki mu wuce
ni da Aba”.
Ai baima gama rufe baki ba ta miƙe zaram, sai kuma ta kalla Aba kamar zatai kuka. “Aba ai dai dani zaku
tafi ko?”.
Da ƙyar Aba ya gumtse dariyarsa da faɗin, “Sosai kuwa. Ai ƙafar bestynki ƙafarki har Kano. Oum ɗinku
ma tace karna sake na baroki”. Sosai ta shiga dirga tsallen farin ciki, sai kuma ta nufi Ajwaad ta kama
hannunsa. “Besty muje kafin Aba ya gama kama yaran can su Hanne jina-jina. Dan bazan tafi ban bar
fuskokinsu da tabon da zasu dinga tunawa da ni ba, dole kuma asan Bestyna mai ƙarfin ILIYA ƊAN MAI
ƘARFI YAZO”.
Komai bai ce ba ya riƙe hannun nata shima suka fice. Kai kawai Baabu ya girgiza, yayinda Abah ya fashe
da dariya. Ammie ma murmusawa kawai tai da jerama Maanal ɗin addu'ar shiriya a zuciyarta. Bayan sun
tsagaita da zancen su Maanal Aba ya gyara zama yana fuskantar Ammie.
“Ammien Amal ki kwantar da hankalinki, dan mun tattauna da su kuma ga shi Habib ya fahimta. Duk da
dai an kai ruwa rana akan batun su Shahidahn gaskiya. Dan sai da nai katoɓarar nuna musu ai su
Shahidahn nada mazaje a hannu, ba kuma su kowa bane sai yarana Fadeel da Fawzan sannan suka amince,
amma da sharaɗin nan da wata shekarar za'ayi biki”.
Cikin matuƙar mamaki da ruɗani Ammie ke kallon Aba da Baabu. Muryarta har harɗewa take wajen
faɗin, “Amma Yaya sufa su Fadeel ba'asan ra'ayinsu ba”.
“Ai basu ya dace asan ra'ayinsu ba Ammien Amaal. Su su Shahidah sune ya dace asan nasu ra'ayin
saboda sune mata sune zasu zauna da su. Suko maza ne ai, sannan ni nasan daga Fadeel har Fawzan basu
da bakin ƙin yarana zuƙa-zuƙa masha ALLAH, sai ma godiya ya kamata suma ALLAH da samun su a cikin
sauƙi dan Shahidah da Amaal duk matan manya ne”. Ya ƙare maganar cike da barkwanci. Ammie zata sake
magana Aba ya katseta. “Aifa magana ta ƙare Ammien Amaal, fatanmu ki saka albarka kawai dan ALLAH.
Sai kuma batun shi Habib, ina son ki kwantar da hankalinki kiyi hakuri kiyi koyi da ƴar uwarki Fateema, zai
ƙara aure bawai yana nufin ya bar sonki bane ba. Mu maza ALLAH ya saka mana son ku ku mata kuma fiye
da ɗaya a zukatanmu. Wani lokacin ba gazawarku bace ba, daɗin zama da kune ke kawo hakan. Kiyi haƙuri
kinji, in sha ALLAHU sai kinci ribar haƙurinki kuma na tabbatar miki bazan taɓa bari Habib ya wulaƙantaki
ba. Shima kuma nasan bazai ko kwatanta hakan ba koda da wasa ma.”
Ajiyar zuciya Ammie ta sauke a hankali, dan ta fahimci dai shi nashi auren na nan daram. Fuskarta da
murmushi ta ce, “Wlhy babu komai yaya. Ni dama ba nashi bane damuwata. Karatun yaran nan ne da
kuma banbanci wannan rayuwar da basu tashi a ciki ba. ALLAH ya sanya albarka ya bamu zaman lafiya baki
ɗaya. Baga Aunty ba ita da Mamy ai kosu ababen koyine a gareni idan ma ban tashi naga mhaifiyata da
abokiyar zama ba. Dan haka ku daina tausata ma dan bashine dalilin son kuzo ɗin ba”.
“Na sani Asiya, ko shi Habib ya yabi ƙyawawan halayenki yanzu a gaban iyayenku, in sha ALLAHU kuma
zakiyi nasara a rayuwarki”.
Murmushi Ammie tayi, hakama Baabu. Sai kuma Aba ya haɗasu ya cigaba da musu nasiha su duka biyun.
Daga ƙarshe yace shi zai wuce dan zasu kwana a Sokoto da safe su kama hanyar Kano in sha ALLAHU. Idan
kuma sun sami jirgi a daren nan ma zasu wuce. Sai dai kuma da Maanal fa zasu koma bazai bar Auta a
cigaba da dukar musu ita ba.
Dariya sosai Ammie da Baabu suka sanya. Baabu ya ce, “Humm kaima kasan rigimar ƴar taka ai, ALLAH
ta addabi kowa a gidan nan. Hatta da Gwaggo bata bari ba. Dan bata tsoron kurarin Gwaggo sam, shiyyasa
kullum sai sunyi faɗa.”
Sosai Abba ke dariya. Yana mai sake jinjina rashin jin Maanal. Dan shi dai a ƴar fahimtar da yayma
Gwaggon a iya yau kawai yaga kamar tana da zafi sosai. Sannan rashin ƙaunar da takema Ammie da yaran
nasu a bayyane suke. Dan da ƙyar fa aka tankwarata akan batun su Shahidah ɗin nan. Shiko batun auren
Baabu cewa tai idan yace zai bijire sai ta tsine masa wlhy. Dan haka da sauri Abban yace ai bama za'ayi
hakan ba wannan kam sun karɓa. Shi yana ɗauki alƙawarin yin komai. Shine fa aka rabu lafiya, koda yake
ko yanzu da suka shigo sashen nan yana kallonta tana harararsa, dan suna yin sallama ta shige ɗaki abinta
kamar bata gansu ba. Amma a hakan Aban yace zai shiga ya sake gaisheta. Badan Baabu yaso ba ya masa
rakkiya har cikin ɗakin, anan ɗin ma sama-sama ta amsa musu duk da kuwa Aban na janta da hira tana
basar da shi.....
★★
Maanal da Ajwaad kam koda suka fito haka ta dinga nuna masa yara abokan faɗanta, har cikin ransa yaso
rama matan amma baba Haruna da ALLAH yakai idonsa ya janyesu su duka biyun zuwa ɗakinsa. Shi yayta
jansu da labari bayan ya basu zuma da magani a cikin a wani ɗan ƙoƙo yace su sha duk da su basu fahimta
ba sun ɗauka zumarce kawai. Daga Maanal har Ajwaad na matuƙar son zuma, dan wajen shi ma za'ace
Maanal ta koya. Aiko hankali kwance suka hau sha, ko nace Ajwaad na sha yana bama Maanal Baba
Haruna na musu labari. A haka Aba da Babu suka fito suka samesu. Maanal na jin zasu tafi ta fara kuka
itafa sai tabi Besty. Babu kalar lallashin da Baba Haruna bai mata ba tace ina itafa sai Kano. Haka dole suka
sake komawa cikin gidan aka shiryata tai sallama da mutanen gidan hannunta maƙale a cikin na Ajwaad.
Dan ko shirin ma shine yay mata da kansa, su Amal ma dai da basu san yanda aka canja komai ba yanzu
idanunsu duk sunyi ƙwal-ƙwal, ji suke kamar suyi ta Maanal ɗin amma babu dama. Zuma da dabino da
mazarkwaila mai yawa Baba Haruna ya haɗama Ajwaad da Maanal na tsaraba. Haka aka musu rakkiya har
cikin mota. Ko'a kwalar rigar Maanal bata damu da barin su Ammie da Babu da sauran ƴan uwanta ba,
tana baya a tsakkiyar Aba da Ajwaad suka wuce tanata ɗagama ƙawayen faɗanta hannu dan tace sun
shirya ta yafe musu😆..
__________★
Bayan wucewar su Maanal sabuwar tujara Gwaggo ta kafa a gidan, dan sai da taima Ammie zagin ƙare
dangi na fitar hankali. Daga ƙarshe tace an sake matso da bikin Baabu nan da kwana huɗu juma'a kenan.
Duk da abin na dukan Ammie haka ta dinga dannewa. Sai ta shiga ɗaki tai kuka. Dan ma yaranta na
tausarta da lallashi dan Baabu kam ma dai takan yini bata sakashi a ido ba. Ba'a nan yake kwana ba. Tunda
sukazo Giro bai kwana tare da ita ba. Ita da yaranta suke kwana, sai dai ya ɗan shigo musu a tsaitsaye
saboda tsoron Gwaggo ma baya jimawa yake ficewa. Sai dai in suna buƙatar abu tai kiransa a waya. Idan
kuma ya sayo sai dai a shigo da shi a ɓoye kosu Shahidah suje su amso su ɓoyo a hijjab. Maanal ce kawai
ba'a ƴar haka da ita. Dan itafa bata tsoron Gwaggo. Idan tai mata tsawa ta murguɗa baki da ƙugu tai gaba
abinta, haka Gwaggo zataita rantsuwar sai ta dake ta, sai ta sumar da ita. Duk kuma yanda zatai lambon
kamata bata yarda, dan tsaf take cajama Gwaggo kai. Duk da taji haushin tafiya da akai da ita taji daɗi ta
wani fannin, dan ta hutama da fitsararta...
Yau ɗin ma dai kuka sosai Ammie taci kafin ta dake zuciyarta, dan Babu tun daga rakkiyar su Aba har
yau bai dawo gidan ba. Da alama ma Sokoto ɗin zai kwana....
_________★
Alhamdullah su Aba sun iso Kano lafiya. Duk da a lokacin anata shirin shiga sallar isha'i ne. Dan basu
baro Sokoto ba sai da akai magrib. ALLAH ne ya taimake su suka samu jirgi mai zuwa Kano a daidai lokacin.
Tuni Maanal tayi barci a jirgi, dole Ajwaad ya goyota suka fito tana a bayansa, sai Aba riƙe da ledar
tsarabarsu dan ma sunƙi ɗakko kayan da yawa. Dan dama jirgi suka bi da zasu je. A sokoton ne abokinsa
kuma ɗan uwansa ƙanin Oum amma cousin da suka fara sauka a gidansa ya bada mota driver ya kaisu Giro
dan shi anan Sokoto yake zaune da iyalinsa. Aiki ne ya cillarosa nan kuma.
Alhamdullah nan ma sun samu babban yaya (Fadeel) da drivern dake kaisu school na jiransu a airport
ɗin. Yana hangosu yay saurin nufosu, shima baida yawan fara'a, dan halinsu kusan ɗaya da Ajwaad. A
fuska ma sunfi kamanni, duk da dai su duka ukun suna tsananin kamanni da Abba da Oum, kasancewar su
ɗin iyayen nasu aurene na zuminci, zumuncin ma na kusa kusa sosai, shiyyasa suke kamanni ɗaya, dan duk
family ɗinsu haka suke da wannan kamannin. Su har alfahari suke indai ɗa na tsatsonsu ne koda an auro
uwarsa bare baya ɗakko kamanninta sai nasu saboda ƙarfin jininsu. Koda Babban yaya ya gaishe da Aba ya
maida hankalinsa akan Ajwaad da son taimaka masa ya amshi Maanal ɗin dake bayansa kansa ya girgiza
alamar ya barta.
Hakan ya saka Babban yaya da Aban yin murmushi kawai. A haka suka ɗinguma zuwa ga mota. Driver ya
gaida Abba cike da girmamawa sannan suka shiga, Abba da Ajwaad da Maanal dake barci a kusan jikinsu
su biyun na baya. Shi kuma babban Yaya ya shiga gaba kusa da driver. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso gida,
inda suka samu tarba daga Oum da Mamy da Fawzan. Sai dai Oum tayi mamakin ganin harda Maanal, dan
batai tunanin zasu bari a taho da itan ba kamar yanda Ajwaad ke faɗin da ita zai dawo gida. Mamy dai bata
tanka ba, dama kuma babu wanda yay tunanin tankawar tata dan dama haka take ita shiru-shiru. Ba komai
ne zakaji bakinta a gidan ba. Garama idan suna hira da Oum ko Aba zaka jita cike da nishaɗi kamar ba ita
ba. Amma akan yaran babu ruwanta da sabgarsu. Sosai take nuna kawaici da kara bama zaka taɓa tunanin
tana da wata alaƙa da su ba...
Ɗakin Oum Ajwaad ya kai Maanal, Oum ta taimaka masa ya kwantar da ita bisa gado. Kwanciya ta
gyara mata da rufa mata duvet dan ɗakin akwai ac. Batare daya zauna ba ya ce, “Oum naje wanka, jikina
duk babu daɗi”.
Murmushi Oum ta masa, dan kowa yasan Ajwaad da tsaftar tsiya dama a gidan. Idan yana wani ƙalƙalin
saika rantse ba yaro bane ƙarami ɗan shekara sha... Komai nashi zaka samesa kwaf-kwaf da kulawa kamar
wani babban saurayi maji ƙarfi. Idan Ajwaad yay ado dole ka tsaya kallonsa. Sam bai damu da manyan kaya
irin namu na malam bahaushe ba. Dan duk juma'a ma sai ankai ruwa rana da shi yake yarda ya saka.
Garama idan Maanal ta saka masa rigima ta ɗakko da kanta tace ya saka sai ya saka. Dan duk da baya so
Aba bai taɓa tsamesa a ɗinkin manyan kaya ba. Yanda akema su Fawzan da Babban yaya haka shima ake
masa su, shiyyasa ya tarasu tab wadrobe yana ado dasu.
Yana shiga ɗakin nasu Fawzan Sarkin tsokala ya fara tsokanarsa da dariya. “Ah-ah kaga baban soyayya,
kaga Auta na Auta, Besty kuma na Besty. Wai yanzu nan dan ALLAH ko kunya baka ji ba Auta kaje gidan
surukai ka ɗakko Lilly? Oh kai wannan wane kalar abin kunya ne haka?”.
Harara ya ballama Fawzan ɗin yana wucewarsa bayi batare da ya tanka masa ba. Aiko Fawzan ya shiga
kwasar dariya har sai da Babban yaya ya shigo ya tsagaita. Koda ya maimaita na Babban yaya dalilin dariyar
daya tambaya murmushi kawai yayi shima, dan shi kansa soyayyar autan nasu da Bestynsa na ƙayatar da
shi, da. Haka yana musu fata da addu'ar ɗorewa a haka har girma su kuma kasance ma'aurata kamar yanda
kowa ke tofa albarkacin bakinsa akan dangantakar tasu.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭_*
[2/11, 9:48 PM] Maryam anas: *_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
6️⃣4️⃣6️⃣4️⃣
______________
.........Duk suna a d/table suna dinner Maanal ta fito tana faman murzar ido alamar yanzu ta tashi. Fawzan
ne ya fara ganinta. Dan haka cike da shaƙiyanci ya furta, “Oyoyo Bestyn Auta, bada kanki a sare kije gida
kice ya faɗi. Kaga surukar Oum da Abah”.
Daina susan idon Maanal tayi ta tsaya tana kallon sa da farko kamar mai mamakin ganin kanta a nan
ɗin. Yayinda suma duk suka zubo mata ido suna kallonta musamman Ajwaad. Oum kuwa da Abah
murmushi suke yi, hakama babban yaya. Mamy kuwa kamar bata a wajen abincinta kawai take famar ci.
Hannu Oum ɗin ta miƙo mata alamar tazo gareta. Da gudu kuwa ta iso ta shige jikin Oum ɗin, sai kuma ta
saki kukan shagwaɓa.
Shi ko Fawzan ya wani tuntsure da dariya yana faɗin, “Oh oh yau naga ikon rabbu surukar Oum
shagwaɓaɓɓiya kenan, an dawo zakuma a ɗaura daga inda aka tsaya ko”.
Rankwashi Oum ta kai masa sakamakon ɗagowar da Maanal tayi cike da taɓara da tsiwa ta ce, “Oum
kinga Yaya F ko, kice ya daina ni Babynki ce ya bar cewa suruka bana son sunan”. Yanda tayi ɗin sai da ya
bama kowa dariya. Dan shi kansa Bestien nata wani guntun murmushi ya saki kawai ya cigaba da kallonta.
Ita ko ta cika tayi fam dan duk zatonta ma surukar wani mugun sunane da ake gudu. Gwalo Fawzan ya
mata da faɗin, “Anƙi a daina ɗin, da wani bakinta kamar na tsuntsu”.
Kuka sosai ta buɗe baki zata sanya, Abah ya saka hannu ya ɗauketa cak yana hararar Fawzan. “Kinga
ƙyalesa kinji babyn Oum ɗinta. Kin san dama shi bashi da aiki sai neman faɗa da mutane in dai Fawzan ne.
Shiyyasa ma bazanje da shi saudia ba sai ke da bestyn ki kawai”.
Cike da farin ciki Maanal taima Fawzan gwalo da harara. Sai kuma ta hau murna za'aje dasu saudia ita da
Bestyn ta. Da wannan lallashin Abah ya kashe rigimar, ya saka mata spoon a abincinsa sukaci tare...
Bayan sun kammala cin abincin ta gama tsiyaya musu surutunta Oum tajata zuwa ɗakinta tai mata
wanka. Kaya gareta fal a gidan, anan ɗakin Oum da ɗakin su AA a cikin kayansa. Tana cikin shiryata Ajwaad
ɗin ya shigo hannunsa riƙe da kayan tsifa. Tana ko kallon hannunsa ta ɓata rai dan bata ƙaunar kitso sam.
Fuska a marairaice kamar zatai kuka ta ce, “Besty kaina na ciwo”.
Harararta ya ɗan yi yana kaiwa zaune a bakin gadon Oum da faɗin, “Idan an gama zaki sha magani”.
Sosai ta tura baki gaba, sai kuma ta kalla Oum dake gumtse dariya. “Oum dan ALLAH kaina bada zafi ba?
Taɓa kiji ma”. Dariya sosai Oum ta fashe da shi tana taɓa kan, “Gaskiya Babyn Oum babu wani zafi, kanki
yayi datti ki daure a tsefe kinji, jibi ƙasa a cikinsa tule. Ko baki son kuje Saudian da Abah yace?”. Jiki a
sanyaye ta ce, “Ina so Oum”.
“Yauwa ton daure kinji ƴar albarka. Ai Auta bazai miki da zafi ba kin sani ko? Gama chocolates bari na
baki kije anayi kina ci baza kiji ma anayi ba har a gama”.
Da wannan lallashin ta yarda badan taso ba. Haka suka fito hannunta ɗauke da ɗan bowl da Oum ta
haɗa mata kayan kwaɗayi, ɗayan kuma Ajwaad ya riƙe mata. Tsakar gida suka fito tacan baya inda garden
ɗin gidan yake, wajen akwai ni'ima sosai dan an gyara shi yanda ya kamata. Ga kujeru an shirya domin
hutawa harda na yara, sai lilo da dai kayan wasan yara. Koda suka zauna sai da ya ɓare mata chocolate ɗin
ya bata wayarsa sannan ya fara mata tsifar. A hakan ma yana farawa ta ɓata fuska zatai masa kuka. Sai da
shima ya ɓata fuskar da faɗin, “Oh nacema Abah ɗin mu wuce mu barki?”.
Da sauri ta girgiza masa kai.
Ya ce, “To oya malama nutsu”.
Baki ta tura gaba da faɗin, “Niba sunana malama ba”.
Murmushi yay a karo na farko, tare da jan hancinta ya ce, “To Bestyn bestyn ta ko?”.
Cike da jin daɗi ta ce, “Yes”.
Ƙaramar dariya yayi, sai kuma ya buɗe baki alamar ta bashi chocolate ɗin. Cirowa kuwa tai ta saka masa a
bakinsa, ganin ya ɗan ɓata mata yatsun yasa shi kama hannun nata ya lashe wadda ta maƙale. Murmushi
tai da faɗin, “Kwaɗayi”.
“Ai ke kika koya min”.
Ya bata amsa yana murmushin shima. Sannan ya fara mata tsifan. Tana kallon cartoon ɗin daya sanya mata
tana masa surutu da juyowa ta bashi chocolate ɗin da sauran kayan ciye-ciyen. Shi ko yana biye mata.
Dama in kaga Ajwaad na zuba surutu da murmushi to lallai Maanal na a wajen kuwa tabbas. Baya wasa da
al'amarinta ko kaɗan. Idan ka gansu dole su birgeka kamar ba yara ba. Haka dai aka gama tsifan, wajen taja
kuma aka hau faɗa, sai da ya riƙeta da ƙyau sannan ya iya taje mata, ita ko tana kuka da faɗin babu
ruwanta da shi kada ya sake kulata. Dariya ya dinga yi shi dai bai kulata ba sai da ya gama ya ɗaure mata da
ribbon duk da yayi datti. Dan cikinsa uban ƙasa ne na faɗan data dinga kwasa a Giro, a hakan ma wai kusan
kitso na fin biyar ne akan nata a zuwansu. Koda suka dawo cikin gidan fushi ta dinga masa, sai ta koma kula
Fawzan shiko Ajwaad ɗin ya sharesu. Hakan da yake yi idan tana tare da wani a cikinsu yake sa suke faɗin
suma yana kishi da su akanta..
_____________★
Washe gari suna gama breakfast Ajwaad ya tasa Maanal gaba zuwa wajen kitso. Ita ko tana faman
kuka da faɗin bafa zataje ba. Sai da ƙyar Oum ta lallaɓata ta yarda bayan ta mata alƙawura. Koda suka fito
tsakar gida inda ɗan kekensa yake sai da ya hau itama ta hau daga gabansa tanata cika baki da iska. Shi dai
bai kulata ba yaja keken suka fito. Ai tun daga gida har zuwa shagon Aunty Saloon duk inda suka gitta sai
an musu magana. Dan Maanal fa cele ce a anguwar tasu saboda tsabar fitinarta da neman faɗa. Yara ɗai-
ɗai ne batai rigimar da taja Ajwaad ya jibgesu ba.
Da farin ciki Aunty Saloon ta tarbesu tanama Maanal oyoyo da dawowa. Itako ta ɓata fuska taje jikin
Ajwaad ta maƙure idanunta cike da ƙwalla. Dariya Auntyn ta fara yi da faɗin, “Maanal ke baki girma da ƙin
kitso? Haba ƴar gatan Ajwaad Bestyn ta. Shi gashi yana son yaga ana gyara masa ke da kitso ke kuma baƙya
so”.
Baki Maanal ta sake turawa gaba da kallon Ajwaad, shima kallon nata yake yi. Sai ta sake ɓata fuska
zatai kuka. A hankali ya kai durƙushe gabanta ya dai-dai tsahonsu hannayensa duka akan kafaɗarta cike da
lallashi ya ce, “Ba kin min alƙawari bazakiyi kuka ba? Ko kina son yaran anguwar nan su ganki su samu abin
raina ki da tsokana”.
Kanta ta girgiza masa hawayen dake cike a idonta na gangarowa. Hannu yasa ya share mata, “To kada na
ƙara ganin hawayen nan. Inba hakaba kuma na fasa shiga secondary ɗin tare dake”.
Da sauri ta haɗiye kukan, cikin rawar murya ta ce, “To bana bari ba”.
“Yauwa my sweet Besty. Faɗa min mi kike so naje na saya miki? Ko awaran can?”. Ya nuna mata waje can
tsallaken titi da mai awara ke ta soyawa. Kanta ta jinjiina masa. Shima sai ya miƙe tare da kama hannunta
ya kaita saman kujerar wanke kan ya zaunar, fita yayi tana kallonsa daga nan. Bai wani jima ba ya dawo da
awaran a leda. Lokacin har Auntyn Saloon tayi shirinta na fara wankema Maanal ɗin kai. Dan duk ta fito da
kayan shampoo ɗinta da suka zo dasu a cikin ƴar bag. Haka komai na Maanal a tattale yake ga Ajwaad. Sam
bai yarda a mata amfani da kayan wankin kan wajen saloon ɗin ba, duk abinda yasan ana buƙata idan
sukaje shopping da Abah ke kaisu duk ƙarshen wata zai ɗakkosa. Dan shi dama ko a wajen shopping ɗin
zakaga duk abubuwan da yake ɗakkowa na Maanal ne. Ƙalilan zaka samu nashi. Kujera ya jawo gabanta
sosai ya zauna, dan yasan bazata yarda ba sai anyi darun. Bai bata awaran ba ya ajiye gefe yacema auntyn
Saloon ta fara. Kuka Maanal ta fara ƙoƙarin farawa ya girgiza mata kansa, sai tai shiru. Haka dai aka wanke
kan yana riƙe da hannunta da lallashi kamar wata ƴar mitsilar yariya can ba ƴar shekara kusan takwas ba.
Koda aka gama shi da kansa ya goge mata kan da towel ɗin da sukazo da shi ya ɗaure mata shi, sannan ya
dinga bata awaran a baki ana busar da kan. Da aka zo kitso kam daru aka sha na haƙiƙa, dan dole sai da ya
riƙeta, amma a hakan yasha cizo a hannu da bibbigewa. Kitson ma ba wani mai yawa ba dan shikku ne.
Sosai ya mata ƙyau aka saka mata bet. Maanal akwai gashi Masha ALLAH, dan sun biyo Ammie ne cikar
gashi da tsaho kamar ba nasu ba.
Sai faman sauke ajiyar zuciya take idanu sun yi jazur saboda kuka ta kama hannunsa tana dubawa,
dan duk sayin ƙananun haƙwaranta. Sake fashewa tai da kuka tana shafa cizon da kallonsa, shima idon
nasa duk ya kaɗa saboda kukan nata. A hankali ya ce, “Minene kuma? Ba'an gama ba?”.
Hannunta na bin wajen cizon ta ce, “Da zafi ko? Muje na amshi magani wajen Oum na baka”.
Murmushi yay mata da girgiza kansa, sai kuma ya shafa kitson nata da yay ƙyau sosai ya ce, “Babu zafi
fa. Jiba yanda kanki yay ƙyau. Ya kamata ki daina kukan kitso Besty kin girma.”
“To ai Oum ta ce idan na girma zan daina ”.
“Wane girma kuma ya rage Besty. Secondary fa zamu shiga ai kin girma ko. Ba kiga ni idan kika rakani
wajen aski bana kuka ba”.
A sanyaye ta ce, “Zan bari. Besty muje gida zanyi barci”.
Kansa ya jinjina mata tare da miƙewa. Cikin girmamawa ya kalla Auntyn Saloon dake kallonsu cike da
sha'awa da mamakin irin wannan al'amari tamkar ba yara ƙanana ba. Godiya ya mata ya ɗauka bag ɗin
sannan ya duƙa Maanal dake faman lumshe ido ta hau bayansa. Kekensa ya kalla sai kuma ya kalla Auntyn
Saloon ɗin. “Aunty zanje na kaita sai na dawo na ɗauka”.
“To babu damuwa Ajwaad sai ka dawo. Ka gaishe da Hajiya. Maanal daru sai kuma next”.
Maanal dai bata kulata ba, sai ma sake lafewa da tai a bayansa dan barci take ji sosai. Tana fita wanda ke
a cikin shagon suka fara gulma. Aunty Saloon dai dariya take yi da sake basu labarin wannan shaƙuwa ta
Maanal da Ajwaad dake birge kowa a layin tamkar ba yara ba...
Kafin su iso gida har tayi barcin. Oum da Mamy na falo suka shigo. Muskar Oum da murmushi ta miƙe
tana faɗin, “Ai na sani dama da barci zaku dawo gidan nan. An sha darun ma yau kenan?”.
Fuskar Ajwaad da murmushi shima ya ce, “Tab Oum miza'a fasa. Duk na sha cizo”.
Dariya Oum ɗin tayi da faɗin, “In ba Bestien taka ba wazai cijeka a zauna lafiya Auta. Maza jeka ka
kwantar da ita to”.
Ɗakin Oum ya kaita ya kwantar, sai da ya rage acn ɗakin ya cire mata ɗab hijjabinta sannan ya fito. Oum
na tambayarsa ina kuma zaije yace zai ɗakko kekensa ne. Daga haka ya fice. Mamy dai bata saka musu baki
ba. Yana kuma fita suka ɗora da hirarsu da suke yi ita da Mamyn hankali kwance cike da farin ciki kuma
kamar ba kishiyoyi ba. A haka Ajwaad ya sake dawowa ya samesu. Ɗakinsu ya wuce yana tambayar ina su
Fawzan. Oum tace sunje aikan datai musu ne. Daga nan zasu duba malaminsu na islamiyya suji yaushe
zasu koma. Dan tun wancan satin ya kamata su koma matar ya sayyadin ta haihu, haihuwar kuma tazo da
matsala shine ya ƙara hutun, sai dai bai sanar da ranar komawar ba taka maimai. Ciki ya shige suma su
Oum ɗin suka miƙe dan lokacin salla yayi.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭_*
[2/11, 9:48 PM] Maryam anas: *_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
6️⃣5️⃣6️⃣5️⃣
______________
.......Abah bai samu zama da su Oum ba sai daren yau akan batun daya faru a Giro. Komai bai ɓoye musu
ba daya faru A to Z har hukuncin daya yanke akan Fadeel da Fawzan. Sosai tausayin Ammie ya sake baibaye
Oum. Dan tamkar ƙanwa uwa ɗaya take jin Ammie a ranta ba maƙwafciya kawai ba. Ɗari bisa ɗari kuma ta
bada goyon baya ga hukuncin mijin nasu. Ta kuma yabama dattakonsa. Itama dai Mamy ta jimanta
al'amarin ƙwarai da gaske. Akan batun yara kuwa ta nuna kawaici kamar yanda ta saba. Daga ƙarshe ma
miƙewa tai tana faɗin, “Wannan maganarku ce Oum, mu ƴan ALLAH ya sanya alkairi ne”. Daga haka ta fice
tabar falon.
Da kallo duk suka bita. Kowanne na sake jin ƙaunarta a cikin ransa daga Oum ɗin har Abah. Mamy abar
alfahari ce a garesu, dan suna matuƙar alfaharin shigo da ita cikinsu. Tana da wasu irin nagartattun halaye
masu matuƙar ƙayatarwa a zahiri. Oum da Abah sun cigaba da tattaunawa, kafin suma su miƙe bayan sun
gama yanke yanda zasu fahimtar da yaran nasu batare da sunga an ƙasƙantar da su Shahidah a idanunsu
ba.
A ɓagaren Mamy kuwa koda ta shiga ɗakinta kasa tsaye da zaune tayi. Ta jima a haka kafin ta ɗauka
waya tayi kira. Ba'a wani jimaba kuwa aka ɗaga. Sallama tayi tana kaiwa zaune. Sai kuma ta ɗora da
gaisuwa.
“Yaya mutanen nan ban san mi suke so dani ba. Shike nan ni bani da wani ƙarfin iko akan ƴaƴana ma.
Daga mijin har matar kamar tare suka auro ni? Nifa na fara kaiwa gaɓar da zan nuna ma matar nan ina
buƙatar ƴaƴana nima. Sai dai ya sakan ko itama tayi zuciya ta haifi nata.......” kuka ya sarƙeta.
Numfashi aka sauke mai nauyi daga can, kafin cikin isa a furta, “Kamila! Dama wannan shine abinda aka
dinga guje miki tun farko. Amma kika kasa fahimta soyayyar mutumin nan ta rufe miki idanu. Daga baya
aka sake nusar dake illar sakar mata yaran nan tun suna zanin goyo nan ma kika kasa fahimta ke wai
neman soyayyar miji. Ai gashi nan, ƴaƴan da mijin duk suna a hannunta ke baki amfanu da komai ba sai
baƙin ciki da damuwa. Kin san wacece Hajiya Fateema kuwa akan mijin nan nata? Dukkan fa bincike sai da
nayi a kansu. Akwai matsananciyar soyayya da shaƙuwa a tsakaninsu tun ta ƙuruciya. Tun fa tana ƴar
shekara goma sha a duniya aka aura masa ita. Shi ya raineta, gida ɗaya suka tashi, shi ya koya mata komai
taya dama kike tunanin zaki shiga wannan gidan ki samu farin ciki? Haihuwa da kike ganin bazatayi ba?
Humm irin su Alhaji Aliyu Darma da kike gani ba wannan bane a gabansu....”
“Yaya ni dai naji. Koma minene dai ya riga ya faru ai. Kawai yanzu ina buƙatar dawo da yarana
hannuna kota ƙarfin tsiya. Musamman Ajwaad. Wlhy yaron nan yi yake tamkar ma bai san muna da alaƙa
ba. Har tayata kishi yake fa. Dan ALLAH ki taimkeni”.
“Hummm ai wannan yaron taƙadari ne daga gani. Kuma ba kowa ya busar masa da zuciya ba sai ita. Ga
shegiyar yarinyar nan da suke ƙalatar juna ƴar maƙwaftanku, kai na tsani yarinyar nan da uwarta wlhy
saboda aminiyar Fateema ce”.
“Wlhy Yaya na fiki tsanar Asiya. Dan haka koma mi za'ayi sai dai ayin wannan haɗin auren bazai yiyu ba.
Sai kace ma ita na haifamin ƴaƴan kenan”.
“A da'alama kam ita ɗin kika haifamawa. Ba kuma makircin kowa bane sai na Hajiya Fateeman. Kinga
idan yaran sun auri ƴaƴan Asiyar ai itace zata cigaba da juyasu ko. Ke wannan fa ƙulline babba wlhy. Amma
karki damu zamuyi maganinsu. Kizo ki sameni gobe”.
“Aunty sai dai weekend. Dan yanzu ina cemasa zan fita zai iya zargin wani abu kin dai sanshi da kaifin
tunani. Amma weekend zan tambayesa zuwa kitso sai na zo”.
“To hakan ma yayi ALLAH ya kaimu. Kidai kwantar da hankalinki”.
“Humm Yaya kenan, amma in sha ALLAHU zan yi ƙoƙari sai anjima”....
___________★
SU WAYE SU OUM?.
Abah da Oum jini ɗaya ne. Makusanta sosai dan kuwa da mahaifiyarta da mahaifinsa uwa ɗaya uba ɗaya
suke. Kunga kenan su cousins ne. Asalinsu ƴan jihar Adamawa ne, a wata ruga da ake kira RIGAR DARMA.
Baffa Ishaq Darma da Gwaggo Halima sune tushen zuri'ar. ALLAH yayma Baffah Ishaq Darma arziƙin kiwo
da noma matuƙa gaya. Dan yana da shanaye, tumaki, awaki, raƙuma, harma da dokuna da shi kansa bai
san adadinsu ba. Sannan yana noma da ake kira noma ba wasan yara ba tun duniya na kwance. Yaransu
huɗu. Mata biyu maza biyu. Abubakar shine babba, suna kiransa da suna Sardauna. Sai Umar, sai Maryam,
sai auta Khadijah. Baffah Ishaq baiyi karatun boko ba daga shi har matarsa. Amma hakan bai saka ya tauye
yaransa ba daga yi. Su duka sunyi karatun boko mai zurfi har matan. Kafin Sardauna ya fara aure bayan
kammala degree ɗinsa na farko. Ya auri ƴar aminin Baffa Ishaq da yakema kallon tamkar ɗan uwa. Ansha
shagali matuƙa irin na nunama tsara a wancan lokacin, amarya da ango suka tare acan cikin garin
Adamawa. Bayan auren Sardauna da kusan shekara huɗu sannan Umar shima yayi tare da Maryam a rana
ɗaya. Shima Umar ya auro ne daga ɗiyar dangi anan cikin Rigar Darma, ita kuma Maryam aka aura mata
wani ɗan Alhaji da suke huɗɗa da baffah tsahon shekaru. Yana zuwa ya sayi dabbobi masu yawan gaske a
duk ƙarshen shekara, a hankali zuminci ya ƙulle tsakaninsa da Baffan har suna kallon kansu tamkar ƴan
uwa (mutanen da kenan masu girmama alkairi). Shi wannan Alhaji dai yana zuwa daga jihar Kano ne,
asalinsa kuma ɗan garin Kura ne. Ɗansa ɗaya tal a duniya mai suna Kasheem. Yana karatu a turai. Yazo
wani hutu gida Nigeria ya biyo babansa nan Adamawa shine ya ga Maryam itama a lokacin tazo hutun
makaranta daga Yola. Aifa yace yaga mata, Baffa kuma yace ya bashi halak malak. Ansha biki nan ma na
nunama tsara, Umar ya tare da matarsa anan Rigar Darma, ita kuma Maryam aka wuto da ita Kano.
UBANGIJI mai hikima shakara ɗaya tak ALLAH ya sauki matar Umar lafiya, har kuma lokacin yayan su
Sardauna ALLAH bai bashi haihuwa ba shi. Dan matarsa ko ɓatan wata ma bata taɓa yi ba. Kaf family sunyi
murna, sun kumayi farin ciki, an sha shagalin suna shanaye sun sha wuƙa da ƙananun dabbobi yaro yaci
suna Aliyu (Abah kenan😂).
UBANGIJI mai rahama matar Abubakar bata yaye Aliyu ba sai ga wani cikin. Dole aka cire Aliyu daga
nn, sai kawai matar Sardauna ta amshesa ta yaye. Daga wannan yaye ne kuma bai sake dawowa wajen
iyayensa ba su Baba Sardauna suka cigaba da riƙo tunda su har lokacin ALLAH bai kawo iyaka ba. Matar
Umar ta sake haihuwar namiji yaci sunan Hamza, shima bata yaye ba ta kuma samun wani cikin. A taƙaice
dai sai da ta jera yara huɗu duk maza sannan itama Maryam ALLAH ya kawo ciki. A kusan tare kuma suka
sake haihuwa da matar Umar da tai mace a wannan karon. Itama dai Maryam ɗiya mace ta haifa da taci
suna Fateema (Oum kenan😂).
Itama Maryam matar Babban Yaya wato Sardauna suka kawoma yayen Fateema. Bakuma su sake
waigawa ba dan a lokacin ne ma suka bar ƙasar. Hakan da sukai na nufin suma sun barma Sardauna
Fateema har abadan. Wannan abu ya saka Sardauna da matarsa kukan farin ciki da sake jin ƙauna da
soyayyar ƴan uwansu. Basu haihu ba amma gashi suma sun mallaki ƴaƴa. Bayan nan itama Auta Khadijah
tayi aure anan cikin garin Adamawa. Itama kuma babu jimawa ta fara haihuwar. Itama kuma ɗanta na fari
haka ta mallakama Sardauna shi kamar yanda sauran ƴan uwanta biyu sukayi. Sai kuma cikin hukuncin
ALLAH fin shekara goma sha sai ga matar Sardauna da ciki. Zamu iya cewa wannan zuri'a basu taɓa tsintar
kansu a irin farin cikin da suka samu kansu ba na wannan tsakanin. Dan tuni Maryam ta baro ƙasar waje
tazo gida Nigeria. A lokacin yaranta biyu da Kasheem Kura bayan Fateema da sukai ƙyauta. Majdiya,
Sulaiman. Itama Khadijah nada biyu bayan Sa'eed da sukai ƙauta ma Sardauna. Sai matar Umar nada biyar
bayan Aliyu da sukaima Sardauna ƙyauta suma. Ansha matuƙar shagali da bidiri na wannan ciki har ALLAH
ya kaishi haihuwa aka haifo ƴan biyu duk maza. Kwantata muku irin shagalin da akai ai bashi misaltawa.
Musamman Aliyu da Fateema da Sa'eed da akai ƙanne.
Zuwa yanzu Aliyu ya fara zama saurayi, dan yana da shekara kusan goma sha bakwai a duniya. Yayinda
Fateema keda goma sha ɗaya cif. Akwai wata irin shaƙuwa da ƙaunar juna a tsakanin Fateema da Aliyu mai
ban mamaki. Sun tashi tamkar wasu tagwaye duk da Aliyu ya bata shekaru sosai. Soyayyar ce mai ƙarfi irin
wadda zaman rubutata ma jan lokaci ne. Gashi suna matsanancin kamanni dan ita Fateema ta ɗebo dangin
mahaifiyarta ne gaba ɗaya. Sauran yaran Maryam kuwa sun biyo mahaifinsu Kasheem Kura sosai. Hakama
yaran Umar ƙannen Aliyu kaf ɗinsu sun ɗebo gida ne, babu wanda ya biyo mahaifiyarsu, suma yaran
Khadijah duk suna kamanni da danginta. Sai su ƴan biyu. Wannan yasa suke jin alfahari akan su jininsu
nada ƙarfin da suke ɗebo kamannin gida ne. Yanda su iyaye ke kamanni da juna haka suma ƴaƴan duk suka
ɗebo. Hatta da yaran Maryam dake kamanni da mahaifinsu sun ɗebo wasu abubuwan nasu, ita dama
Fateema gaba ɗayanta sune.
Soyayya da shaƙuwar Aliyu da Fateema yasa Baffah Ishaq bama ƴaƴansa shawarar haɗe yaran aure
saboda gudun shaiɗan a tsakaninsu, dan shaƙuwar tayi yawa matuƙa komai zai iya faruwa. Babu kuwa
wanda yayi musu akayi hakan. Fateema nada shekara goma sha biyu da wasu watanni, Aliyu nada goma
sha tara da wasu watanni aka ɗaura musu aure. Akai kuma shagalin biki irin na gata sai dai sun tare anan
gidan Baba Sardauna ɗin dan yace yaransa bazasuyi nesa da shi ba. Balle kuma gasu yara ƙanana basu kai
ƙwarin da za'a barsu su kaɗai ba tukkuna. Soyayya ta ƙara ƙarfi a tsakanin Fateema da Aliyu, yayinda a gefe
suke ta karatunsu ga kuma kulawar iyaye. Aurensu nada shekara uku ALLAH yayma gwaggo Halima rasuwa.
Kaf wannan zuri'a ta Darma sunji wannan mutuwa matuƙa, sunyi kuka har sun rasa hawaye musamman
ma Baffa Ishaq Darma daya rasa mata ƴar uwa uwar ƴaƴansa. Bayan rasuwar tata kuma shima duk sai
lafiya tai masa ƙaranci. Shekara biyu tsakaninsu shima yace ga garinku nan. Matuƙar ruɗani wannan family
sun sake shiga, har takai Baba Sardauna da Baba Umar sun kasa jin daɗin zaman garin Adamawa sukayo
hijira zuwa Kano. A lokacin shekarun auren su Aliyu biyar cif a duniya. Fateema nada sha shida, Aliyu nada
ashirin da uku. Ya kammala karatunsa na jami'a, ita kuma zata shiga ss a sakandire.
Shekarar da Fateema ta kammala sakandare a shekarar ALLAH ya bata ciki. Murna da farin ciki ba'a
magana. Dan wannan zuri'a na matuƙar son haihuwa. Sosai cikin ke bata wahala, kullum tana nane da
Ummanta. (Matar Sardauna) Dan soyayya take musu ta haƙiƙa da sam bama su san ainahin ba itace
mahaifiyarsu ba sai lokacin da akai musu aure. Hakan kuma bai sa sun canja daga soyayya da ƙaunar da
suke mata ba. Itama kuma haihuwar da tai baisa ta sassauta soyayyar da take musu ba a matsayin ƴaƴa har
gobe. Haka dai akai wannan rainon ciki Fateema kullum na sashen iyayensu. Har abun na damun Aliyu dan
idan yana son ya kasance da ita sai yayi mata wayo da ƙyar tazo nasu sashen da aka ware musu a gidan. A
haka ALLAH ya kai wannan ciki lokacin haihuwa. Sai dai yazo da doguwar naƙuda. Tun ana hasashen
haihuwa a kusa har al'amarin ya fara bama kowa tsoro aka yanke shawarar yimata theater. A wancan
lokacin matuƙar tsoron theater akeyi dan kodai a rasa ɗa ko a rasa uwa. Dole da wahala cikin biyun nan
ɗaya bai kasance ba sai idan duk suna da tsohon kwanan ne uwar da ɗan. Aliyu kuka ya sanya akan bai
amince ba, sai da likita yayta lallashinsa da su Baba Sardauna sannan da ƙyar ya amince aka shiga theater
da Fateema.......✍️
_(Ina fatan dai kuna gane kan labarin😆. Fateema itace OUM a yanzu, Aliyu ne ABAH a yanzu😂)._
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
6️⃣6️⃣6️⃣6️⃣
______________
.........Alhamdullah bayan dogon zaman jira da fargaba da kasancewa a tashin hankali an samu nasarar ciro
yara ƴan biyu a jikin Fateema duk maza. Sai dai ɗaya bashi da rai, rabin jikinsa ma har ya ɗan fara ruɓewa.
Wannan yanayi ya saka farin ciki da alhini a wannan zuri'a duk a lokaci guda. Sai babbar damuwarsu sanin
halin da Fateema ke a ciki kuma. Dan Doctors ɗin dai since su basu lokaci. Haka suka sake koma a yanayin
damuwa da taraddadi musamman ga Aliyu har zuwa washe garin safiyar ranar. Dan wajen ƙarshe sha biyu
aka samu nasarar farfaɗowar Fateema. Dama wannan shine tsaikon da likitocin suka samu na zahiri. Zuwa
yanzu kam kowa ya warware, farin cikin kowa ya fito a bayyane, anatama juna barga da addu'a ga jaririn da
ya rage, wanda ma bai zo da ran ba ana masa addu'a.....
Watan Fateema ɗaya cif a asibiti aka sallesu, jikinta da sauƙi sosai, sai dai yanayin cs na wancan lokacin
ba dai-dai yake dana yanzu na zamani ba. Sai ya kasance wasu tsarabe-tsarabe kan biyo baya da har
mutum kan iya ɗaukar dogon lokaci yana mafa da jiyya sama-sama har komai ya zama normal. Zuwa
lokacin tuni an raɗa sunan jariri da aka barsa da sunansa wato Hussain. Dan Hassan ɗinne baizo da rai ba
kasancewar shi aka fara cirowa. Raɗin suna kawai akai, sai bayan sallama aka shirya taron suna. Ansha
shagalin kam mai birgewa da nunama tsara, sai dai maijego na dauriyane kawai dan sam bata jinta cikin
isashiyar lafiya har lokacin. Sai dai bata son ɗagama mijinta da ƴan uwanta da iyayenta hankali, shiyyasa ta
cigaba da daurewa har taro ya tashi lafiya ta cigaba da wankan jegon da Umma ke mata da kanta. Wato
matar baba Sardauna. Sun gama wankan jego lafiya, dan kusan ma arba'in biyu sukayi, ta ɗan zaga dangi
harda Saudiya ita da Aliyu sukayo sati uku sannan suka dawo. Abin ƙaddara satinsu biyu da dawowa
Hussain ya fara wata mura mai ban tausayi, murar fa ko numfashinsa da ƙyar yake fisga. Hankali tashe suka
wuce asibiti da yaron, sai dai UBANGIJI shi mai hikima ne, a daren shima yabi ɗan uwansa. Kuka rurus Aliyu
ya dinga yi, amma a mamakin kowa Fateema ko ɗigon hawaye, sai ma ta koma itace ke lallashin mijin nata
kuma ɗan uwanta. Bayan rasuwar Hussain da kusan wata biyar sai ga Fateema ta fara laulayin sabon ciki.
Murna a wajen Aliyu ba'a magana ko kwatantawa. Hakama sauran ahalinsu kowa na fatan alkairi da
addu'ar ALLAH ya inganta. Sosai wannan ciki yazo ma Fateema da tsanani fiye dana ƴan biyu, dan bata sati
guda a gida sai a asibiti, ƙarshe dai suka riƙeta a asibitin domin samun bedrest. Dan haka kawai saita dinga
bleeding, doctors sunyi iya ƙoƙarin ganin sun shawo kan matsalar amma al'amarin ya gagara, har takai
mahaifin ta dake matsayin babban likita a saudia wato Kasheem Kura ya nufo Nigeria da kansa. Shine ya
tsaya akan matsalar, inda ya fahimci ƴar tasa tana fuskantar babbar ƙaddarane mai girma. Ya shiga tashin
hankali amma haka ya daure ya jure ya fito fili yama uban riƙonta da uwar riƙon ta da mijinta bayani akan
dole ne fa a raba Fateema da wannan ciki, dan sam mahaifarta bazata iya riƙeshi ba. Hasalima sai an
rabata da mahaifar kanta sakamakon ciwo mai haɗari data kamu dashi, in ba hakaba kuma ciwon zai fara
girma wataran a wayi gari ya harbi dukkan illahirin jikinta. Amma idan sunyi ƙoƙarin cirewa yanzu in sha
ALLAHU an rabu kenan.
Wannan al'amari ya matuƙar ɗagama kowa hankali, musamman ma Aliyu. Amma lafiyar matarsa tafi
masa duniya da abinda ke cikinta. Dan haka babu wani ja'inja ya amsama Abbu cewar kawai a cire ɗin.
Haka kuwa akayi, aka cirema Fateema cikin da dama bai wani zauna da ƙyau ba, aka kuma cire mata
mahaifa. Wannan shine ya kawo mata sanadin yin doguwar jinya ta kusan watanni takwas, kafin ALLAH ya
bata lafiya komai ya daidaita tamkar ma ba'a taɓa yi ba. Har kuma lokacin bata taɓa sanin an cire mata
mahaifa ba. Bayan samun lafiyarta abu na farko shine nema mata gurbin shiga jami'a da Baba Sardauna
yayi ana BUK. Dan danan kuwa ta fara karatunta. Dan Fateema yarinya ce mai hazaƙa matuƙa da son
karatu.
A randa ta fara shiga makarantar ɗaukar darasi a ranar suka fara haɗuwa da matashiyar budurwa da
bazata wuce sa'arta ba, in ma ta girmeta baifi da shekaru uku zuwa huɗu ba. Kamila Shu'aibu ƙyaƙyƙyawar
yarinya, baƙace amma baƙinta mai ƙyau ne. Tana da matuƙar sanyin hali da rashin son yawan magana.
Wajen zama ya fara haɗa su da Fateema a ranar farko, Fateeman ce kuma ta samu Kalima. Bayan ta mata
sallama fuskarta da murmushi tai nuni da kusa da ita tana faɗin, “Sis... Kozan iya zama?”.
Murmushi mai sanyi Kamila tai mata itama, tare da nuna mata wajen ta ce, “Bismillah mana ki zauna”.
Murmushi Fateeman ta sake mata sannan takai zaune da faɗin, “Thanks you”. Daga haka babu wanda ya
sake shiga sabgar ɗan uwansa suka maida hankalinsu ga malamin. Tun daga wannan ranar sai ya zam duk
wanda ya riga wani zuwa a cikinsu sai ya tanadarma ɗan uwansa waje a kusa da shi. Tun abin na musu
kamar wasa har shaƙuwa ta fara tasiri a tsakaninsu. Sai dai babu wanda yasan komai daga rayuwar ɗan
uwansa, karatun kawai suke yi har tsawon watanni. A hutun farko da suka farayi har aka dawo akaci kusan
sati biyu babu Kamila, hankalin Fateema ya fara tashi ta fara bincike a wajen ƴan ajinsu, sai dai kowa kance
shi bai san inda Kamila take ba ba tare ake ganinsu ba. Kamar wasa Kamila ta shafe watanni har biyu bata
dawo school ba. Har Aliyu ya fahimci matsalar Fateema ya tambaye ta. Bata ɓoye masa komai ba ta sanar
masa, shiko dama yasan labarin Kamila a wajenta tun farko. Haka domin farin cikinta yazo har makarantar
ya tayata bincike har ALLAH yasa suka samu wanda yasan gidan su Kamila ɗin. Shine yay musu rakkiya.
Sosai Kamila ta shiga matuƙar mamaki tare da jin ƙaunar Fateema a ranta. Suka rungume juna suna
kuka. Aliyu ne ya shiga basu baki, inda sai a lokacin Kamila ta ganshi. Mutuwar tsaye tayi dan lallai bawan
ALLAHn ya haɗu, ya kuma daki zuciyarta da nashi tsarin, amma sai ta danne. Da farko tayi zaton yayan
Fateema ne kawai saboda tsananin kamanni da sukayi, dan haka ta gaisheshi da girmamawa da kiransa da
sunan Yaya. Shima ya amsa mata kadaran kadahan dan babu wata mace dake birge Aliyu sai Fateemansa.
Hatta sauran yara matan family ɗinsu sam baya sakar musu fuska. Anan soro aka masa shimfiɗa, su kuma
suka shiga daga ciki.
Su Kamila talakawane sosai, sannan tana rayuwane a hannun kakarta Iyale. Ashe ciwone ya kwantar da
Iyalen ita kuma Kamilar ke jiyyarta shiyyasa bata koma makaranta ba. Ta wani gefen kuma babu kuɗin da
zataje tai buƙatun makarantar ma. Dan mahaifinsu kaɗai Iyale ta haifa, su uku kuma suka haifa duk mata.
Mahaifiyarsu ta rabu da babansu tuni saboda tsananin rayuwar talauci da suke a ciki. Yayi yunƙurin
ƙwacesu a hannunta amma sai ALLAH ya bata nasarar guduwa da yayarta da ƙanwarta. Ita kuma a lokacin
tana hannun Iyale dan tun yaye dama take anan. To a yanzu hakan dai ance Maman nasu na Saudia tana
tukari, suma ƴan uwanta biyu na'a tare da ita. Babansu na son karatu shiyyasa ya tsaya mata cewar zatayi,
dan baya son nan gaba ƴan uwanta dake a wajen mahaifiyarta su fita cigaban rayuwa. To da ƙyar da ya
ALLAHU aka haɗa kuɗin makarantar ta fara saboda takardunta sunyi ƙyau, sai kuma gashi tunkan aje ko'ina
karatun na neman fara tangal-tangal, dama Sakandire ɗin ma dayaya aka gama, mahaifiyarta ce ke turo
kuɗi. Ɗan tsakanin nan kuma ta ɗauke musu wuta saboda roƙon da Iyale ke mata akan ta dawo garesu
kodan ƴaƴan dake tsakani.
Zuwan Fateema da Aliyu gidan shine ya zamewa Kamila rahama da tarin alkairi, dan kaɗan daga
tarihinta da Fateema taji ya ɗaga mata hankali, suna dawowa gida ta sanarma Aliyu komai tare da roƙonsa
ya taimakawa Kamila ta koma makaranta. Baiyi musu ba kuwa ya taimaka da iya nasa ƙarfi Baba Sardauna
ya ƙarasa sauran shi kuma. Hakan ya zama sanadin komawar Kamila makaranta, aka kai Iyale asibiti, aka
kuma bama mahaifinta jari ya fara sana'a tare da tsaya masa ya ƙara aure. Wannan hidima mai ban
mamaki daga ahalin Fateema shine ya sake dunƙule Fateema da Kamila waje ɗaya, wadda zuwa yanzu ta
fahimci Aliyu mijin Fateema ne Kuma yan uwane na jini. Tayi kuka sosai dan harga ALLAH Aliyu ya shiga
ranta sosai, amma ta dannema zuciyarta tare da ƙoƙarin ciresa a ranta duk da tasan abu ne mai matuƙar
wahala.
Haka wannan abota ta cigaba da tafiya, shaƙuwa da zumunta mai ƙarfi na ƙara tasiri a tsakanin Kamila
da Fateema. Har takai Kamila kanzo gidan Sardauna tai kwanaki a wajen Fateema. Babu wanda ya taɓa
ƙyamatarta ko ƙyararta balle kallon banza. Ƙyautata mata suke da iya iyawarsu har ma da iyayenta. Suna da
shekara biyu sun shiga farkon ta uku a jami'a hankalin Fateema ya fara tashi da ganin bata sake samun ciki
ba. Ta fara takurama Aliyu suje asibiti amma sai yay biris da ita. Ta cigaba da masa naci daga ƙarshe yace
babu inda zaije. Haihuwa ta ALLAH ce kuma lokaci ce. Idan sukai hakuri lokaci yayi zai basu. Shi ba
haihuwar yake so ba ita yake so. Sam kalamansa basu gamsar da ita ba, dan haka ta samu Kamila da
ƙorafin. Amma itama Kamilar kasancewar bata san komai ba sai ta lallasheta da bata shawarar ta bisa a
hankali ta kuma cigaba da yin addu'a. Hakan kuwa akayi, Fateema ta sake yin haƙuri, sai dai kuma ta kasa
daurewa dan sosai take son haihuwa. Musamman daya kasance ta ɗanɗana haihuwar da daɗin ɗa a hannu
taji. A wata ranar juma'a ta zagaye taje asibiti batare da sanin Aliyu ba. Acan ne fa ta jiyo abinda ya sakata
yanke jiki ta faɗi dan tashin hankali, dan sai nemo ahalinta akai suka sameta a nan.
Hankalin Aliyu da Baba Sardauna da Umma ya tashi jin abinda Fateema tazo ta binciko, dan haka suka
rufeta da faɗa musamman ma Aliyu, yayinda ita kuma take kuka mai ban tashin hankali da tsuma zuciya.
Dole suka koma lallashinta kuma. Kwananta biyar a asibitin aka sallameta, ta koma gida da sabuwar jiyyar
zuciya. Sai dai mijinta da iyayenta na tsaye a kanta da lallashi daban baki da nasiha. Dan har malami
sukutum Aliyu ya ɗakko mata yay mata doguwar nasihar yarda da ƙaddara ga bawa. Alhamdullah hakan
yayi tasiri zamuce, dan ta rage damuwa sosai. Gefe kuma ga Kamila itama tana sake tausar zuciyarta. Yin
haka babu jimawa mutanen Saudia sukazo hutu gida, a lokacin kuma aiki ya maida Dr Kasheem Kura Paris
dan haka sukazo hutu gida daga nan kuma can zasu wuce. A wannan ɗan zama ne Maryam (Mahaifiyar
Fateema kenan ta asali) ta nutsu wajen yima ƴarta Fateema nasiha da nusar da ita karta sake saboda
ƙaddaratta ta tauye ɗan uwanta kuma mijinta daga samun ƴaƴa daga wata matar, ta barshi ya ƙara aure
duk wadda ta zo ta haifa kamar nasu ne su duka. Tun wannan nasiha na tada hankalin Fateema saboda
dunbin soyayyar da takema mijinta harta fara tasiri saboda tausayi da ƙaunar da take masa ta haƙiƙa ce.
Bayan tasha fama da yaƙi da kanta da tsananta addu'a bayan wucewar iyayenta da ƙannenta biyu ta
tunkari Aliyu da batun ƙara aure. Wayyo ai ranar Fateema taga ainahin abinda ake kira tujara. Dan rufe ido
Aliyu yay ƴamata tas, ya kuma tabbatar mata idan ta sake tunkararsa da wani batun ƙara aure sai ya ɓata
mata rai fiye da haka. Shi yace mata yanada sha'awar zama da mace fiye da ɗaya ne. Koya sanar mata
rashin haihuwarta matsala ce ga rayuwarsa. Ita yake so ai, zai kuma cigaba da rayuwa da ita a haka har
ƙarshen rayuwa........✍️
_🥲Tofa rikitata_
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
6️⃣7️⃣6️⃣7️⃣
______________
.........Bayan yin hakan kamar Fateema ta haƙura tabar Aliyu, zuwa wani lokaci kuma saita dawo da zancen.
A wannan gaɓar ma sunyi rikici sosai da har ya kaisa ga kai ƙararta ga Baba Sardauna da Ummu. Dole sukai
zama dasu domin sasanta rikicin. Sai dai a wannan sasanci ma bawai Fateema tabar wannan rikici bane,
dan ko'a gaban su Baba Sardauna tace tana akan bakanta. Shima yace yana akan bakansa. Fateema ta
cigaba da naci da takurama Aliyu akan batun aure da yaƙin son fahimtar da su Baba Sardauna dalilinta. Tun
kowa bai fahimceta ba har aka fara goya mata baya. Musamman da taga su Baba Sardauna kamar basa so
sai ta shirya tai tafiyarta gidan Kakanninta wato Alhaji Lawan mahaifin Kasheem Kura. Sai da ta bari
hankalin Aliyu yay masifar tashi sannan ta bayyana kanta bisa tasota gaba da Baba Lawan ɗin yay suka zo
gidan Baba Sardauna. A wannan zamane suka tattauna sosai Baba Lawan ya nuna musu Fateema ta fisu
gaskiya, ya kuma kawo hujjoji da dole suka amsa kodan kasancewarsa Uba ga harsu su Baba Sardauna ɗin.
Duk da haka har a lokacin shifa Aliyu bai gamsu ba. Amma baice komai ba. Sanin halinsa yasa anan
Fateema tace ayita ta ƙare dan karma yace ya fasa. Ya zaɓa a ƴaƴan dangi duk wadda tai masa in ma a gefe
ne ma duk taji ta gani. Ai ko a fusace Aliyu ya balbaleta da cewar shi bai son kowa. Ita da tace taji ta gani
sai ta kawo matar tunda ita zai aurowa dan ita ta damu. Dariya kawai su Baba Sardauna sukayi, dan sun
tabbatar fa Aliyu bai ƙaunar batun ƙara auren nan sam. Aiko Fateema bata gusa ba tace to ga ƙawarta
aminiyarta Kamila, tasan halinta tasan tushenta ta kuma yarda da tarbiyyarta. Wani mugun kallo Aliyu ya
watsa mata kuwa. Itama ta murguɗa masa baki ta ɗauke kanta dan zuciyata ta gama rufewa ita dai kawai
Aliyu yay aure su samu yara ace nasu ne.
Anan ma Aliyu yaso tirjewa. Amma sai su Baba Sardauna sukaita lallashinsa da ƙarfafashi. Badan yaso
ba ya amsa kawai. Ammafa suna komawa sashensu ya balbale Fateema da faɗa itako ta masa banza. Ita dai
tunda burinta ya cika yaje yayta yi. Anyi haka da sati ɗaya Fateema ta shirya taje har gida ta tunkari Kamila
da zancen. Ruɗewa Kamilar tayi.
“Haba Fateema wace irin maganace wannan. Shin kina zargin ina son MIJINKI ne komi?.....”
Hannu Fateema tai saurin ɗaga mata. “Kinga Kamila kada ki sauya min magana. Ni ban taɓa zarginki da
koda kwatankwacin hakan ba. Hakama mijina nasan wanene shi, dalilin ƙara auren ne kawai ya taso masa.
Kamila da'aje a auro wadda ban san halinta ba tazo ta rabani da shi ba gwara wadda na sani nasan halinta
tasan nawa ba. Ina sonshi Kamila so mai tsanani, bazan so wadda zata zo ta cutar damu ba, domin
maganar aure fa ake ba hutu ko zaman wucin gadi ba. A gaba ɗaya na hanga na hango kece kawai
halayenki sukai min dai-dai da rayuwar mijina. Na kuma tabbatar miki zai soki kamar yanda yake sona in
sha ALLAHU in har kin cigaba da zama akan ƙyawawan halayenki. Ba tallarki nai masa ba, haka kema ba
tallarsa nake miki ba. Cancantar kasancewar mu a inuwa guda mu uku kawai na hango. Ki taimaken Kamila
kada kice a'a, dan cewar a'a ɗinki na nufin wata da ban sani ba zata shigo min gida. Bai zama lallai ta
kasance mai ƙyawun zuciya irinki ba. Maybe ta rabani da shi, maybe ta maidani gefe maimakon farina ya
koma ganin baƙina da kasawata. Amma ke fa. A tsahon shekaru uku da muke tare ina jinki tamkar jinina,
tamkar wata twin sister ɗina da muka tashi tare muka girma tare. Dan ALLAH ki tausaya min, ki auresa kizo
ki haifa mana yara mu haɗu mu rungumesu tare. Mu rainesu tare, mu basu tarbiyya tare, su tashi a
tskaninmu tare. Ba'a auro wadda kota haifi ƴaƴan zasufi ƙarfina ba, su ringa min kallon matar uba ba uwa
ba. Please na roƙeki”. Kuka ya sarƙe Fateema. Itama Kamila kukan takeyi, sun jima a haka kafin Fateema ta
miƙe ta tafi, tare da bata damar yanke hukunci....
To bayan dai kai ruwa rana da faɗi tashi, da kace nace da ƙyar dai Kamila ta amince bisa tsayawar ƴan
uwanta biyu da suka dawo Nigeria a lokacin tare da mahaifiyarsu. Sosai farin ciki Fateema ta nuna da
amincewar Kamila, taje har gida tai godiya. Anan ne suka fara sanin juna da sauran ƴan uwan Kamila da
kuma mahaifiyarta da a yanzu itama take ƴakin neman komawarta ga mahaifin su Kamila ɗin.
An fara shigi da fici akan auren Aliyu da Kamila, sai dai shi ango ya tare gabas ya tare yamma akan shi
babu ruwansa. Da ƙyar ma ya amince yaje yaga Kamila a gidansu sau biyu. Dai-dai da lefe da sadaki duk
Fateema ta biya. Dan kaf Family ɗin Baffa Ishaq Darma nada kuɗaɗensu a asusun bankuna tun daga manya
har yara. Kamar yanda Fateema ta buƙata babu wanda ya saka mata hannu a hidimar wannan aure itace
tai komai da kuɗaɗen asusun bankinta. Sai abincin taron biki ne da abubuwan da suka biyo baya Baba
Sardauna ya sauke mata akan dole ba dan taso ba. Haka dai aka ɗaura Auren Aliyu da Kamila. A kuma
lokacin ne Baba Sardauna ya bama Aliyu gidan zama, dan yace yakamata shima ya koma nashi da iyalinsa
yabar gidan gandu. Hakan baima Aliyu ba, amma baya iya musu dole ya amsa. A sabon gida aka kai amarya
Kamila, ita kuma Fateema tace sai bayan kamar wata guda zata tare. Da kanta taima ango rakkiya gidan
amarya. Sai kuma bayan ta koma gida taci kuka harta godema ALLAH. Daga baya kuma ta maida komai ga
ALLAH taita sallolinta harta samu natsuwa zuciyata tai fayau kamar ba ita ba. Sai ma walwalarta ta ninku a
safiyar ranar. Har Aliyu da yazo gidan ya nuna jin haishin yanda ya ganta cikin farin cikinta. Wai ai bata
kishinsa ta masa auren dole. Bayan dariya kawai bata kulashi ba ita dai. Tunda dai taci nasara sai fatan
kuma ALLAH ya azurtasu da abinda ake nema...
To da farko dai zaman Aliyu da Kamila babu wani armashi. Dan bai taɓa kulata a shimfiɗa ba. Baya sakar
mata fuska. Baya zama suyi hira. Takurar Fateema ma ke sakashi zaman gidan amaryar da cin abincinta dan
yasan idan yaje can wajenta ba bashi zatai ba. Gashi ta saka masa takunkumin bayan sati ɗaya ta ƙara masa
sati uku wata guda zai yi a wajen amarya. Su Umma kuma sun goya mata baya. Hakan kuwa dole ya cika
wata gudan nan a wajen Kamila sannan Fateema ta tare a gidan, har lokacin kuma bai taɓa kusantar
Kamila ba. Itako Kamila hankalinta a tashe yake, dan bata tabbatar tana son Aliyu so mai tsananin gaske ba
sai a yanzu da suka zama ma'aurata. Yanda yake mata, ko duk motsinsa Fateema dai yasa ta fara jin kishin
Fateema mai tsananin gaske a zuciyarta. A ganinta ba'ai mata adalci ba. Idan ance Fateema tasa aka aurota
to ai dama bawa baya wuce ƙaddarasa. Tun ran gini tun dan zane. Koda sawar Fateema koda rashin sawa
dama ALLAH ya ƙaddara sai Aliyu ya ta zama mijinta. Wannan zafin kishi daya fara taso mata yasa ta
tunkari mahaifiyarta da ƴan uwanta da batun, maimakon su tausheta su lallasheta su kuma sai suka fara
ɗorata a hanya mara ɓillewa. Aiko ta mitsithtsike ido ta nunama Aliyu bafa zata yarda ba. Dan yanzu
matsayinta ɗaya da Fateemar da yake damun mutane da batunta. Tofa wannan abu ya tayar ma Aliyu da
hankali, yo tunkan aje ko'ina kenan ma. Tab ɗin jan inji mata, ai dole yayma tufƙar hanci. Nan fa ya zauna
ya warware Kamila tsaf da rashin mutunci, yo har a gayama bafillace zuciya da baƙar magana. Uwar watsi
sukai yace taje gida za taga aike. Hankalinta ya tashi sai kuma duk ta gigice. Ita ina taga ƙafar tafiya gida
tabar wannan daular da kowa ke mata barka da arziƙin shigowa. Sannan ma auren sati uku kawai ai
wannan abun kunya ne da ko'a mafarki bata fatansa. Dole fa ta zubar da makaman yaƙi ta shiga neman
afuwa da rusar kuka da ban haƙuri tana tabbatar da sharrin shaiɗan ne. Hakan ma bai saurareta ba, yace
saifa ta tafi. Haka kuwa dole ta tafi gida batare da kowa ya sani a dangin Aliyu ba. Amma sai dai me, a ranar
iyayenta suka maidota, suka kuma duƙufa bama Aliyu haƙuri suma da tabbatar masa ƙuriciyace ke damun
Kamilar kawai. Amma yay mata afuwa ko Fateema kada ya bari tasan wannan al'amarin dan ALLAH. Suka
kuma masa alƙawarin canjawar Kamilar fiye da yanda yake buƙata.
Badan dai Aliyu yaso ba wannan wuta ta mutu a haka. Sai dai kuma ya sharɗanta ma Kamila sharuɗai
masu tsauri game da Fateema in har tana son cigaba da rayuwa a cikinsu. dole kuwa ta amsa da hannu
bibbiyu tayi biyya. Sai dai kuma acan ƙasa ta ɗauke karatun uwarta da ƴan uwanta tsaf. A haka Fateema ta
tare gidan itama. Da gaske Kamila ta kwantar da kai fiye da zaton Aliyu. Tana bin shariɗɗansa sau da ƙafa.
Bawai shariɗɗansa kawai ba, da gaske Fateema mugun kwarjini take mata, dan matar nada wata irin baiwa
da nagarta mai ban mamaki. Ga ƙyaƙyƙyawar zuciyar zama da kowa da gaskiya. Sai dai bata son raini, bata
son munafunci da wulaƙanci. Wannan abinda Kamila ta sani ne tuni, dan haka ta shirya yaƙar Fateema da
su har ma da Aliyu. Sannu a hankali kuwa suka fara tasiri, dan duk wata hanya ta gwaji Aliyu yabi akan
Kamila game da zamansu bai kamata da kowane laifi ba. Sai ma yanda take bin Fateeman ya fara saka
masa jin nutsuwar zama da ita. A gefe kuma ga Fateema kullum damuwarta da fatanta taga Kamila da ciki.
To tsakanin mace da namiji kwance a ɗaki ɗaya sai ALLAH, yau da gobe kuma bata bar kowa ba. Dan
sannu a hankali dai Kamila taci nasara akan Aliyu cikin dabaru da kissa irin na mata ya maidata cikakkaiyar
mace. UBANGIJI kuma mai hikima da yin yanda yaso a lokacin da yaso ba'a rufa wata biyu da Kasancewar
tasu a ƙarƙashin inuwa ɗaya ba sai ga Kamila ta fara laulayin ciki. Ya rabba zokuga murna ga Fateema. Sai
ma ka ɗauka itace da cikin. Gaba ɗaya ta kwashe kulawarta kacokan ta maida kan Kamila. Hatta shi kansa
Aliyun yanzu ba wani yana samun lokacinta bane, har ya fara kishi da hakan sai da ta zauna ta lallashesa.
Bawai baya farin ciki da cikin da Kamila ta samu bane, a'a yana dannewa saboda baya son ko yaya zuciyar
Fateemansa ta sosu. Dan haka ya barma zuciyarsa nasa farin ciki ita ya bari take nata a bayyane dama
zuciya. A haka kwanci tashi ALLAH ya sauko Kamila lafiya, ta haifo ɗanta namiji mai tsananin kamanni da
Aliyu da Fateema tamkar sunyi kaki, dan in baka sani ba kazo saika ma ɗauka Fateeman ce ta haifi yaron.
Wannan shine ƙalubale na biyu daya sake girgiza Kamila da ahalinta, sai dai sun shanye a cikinsu suma
sunata fatan alkairi. Sai ma ɗaukar jinjiri da Kamila tayi domin sake samun fada ga Aliyu tun a randa ta
haifesa ta damƙawa Fateema tare da alƙawarin mallaka mata shi na har abada. Ta kuma sake maimaitawa
a gaban Baba Sardauna da Umma da dukkan ahalin Aliyu da nata ahalin. Ranar kuka sosai Fateema tayi da
sake jin ƙaunar Kamila. Tana ji a ranta lallai batayi zaɓen tumun dare ba. Hakama Aliyu wata sabuwar
soyayyar Kamila ce yaji ta soki ƙahon zuciyarsa tayi tasiri a ciki tare da mamaye komai. Duk wanda zai so
Fateeman sa to har abada zai dawwama shima kam yana sonshi da ƙaunarsa ne.
Haka dangin Aliyu da Fateema ma suka zo aka haɗu akasha shagalin suna yaro yaci suna Fadeel
(Babban yaya 😂).
Bayan shan shagalin suna aka bar masu ɗansu. Gaba ɗaya Fadeel a ƙarƙashin kulawar Fateema yake. In
dai ka ganshi a hannun Kamila to lallai za'a bashi abincinsa ne. Sai ko dare yayin yin barci. Amma dukkan
wahalhalu na raino da kulawa Fateema ce. Kai hatta daren ma yana fara kai watanni shida ya koma kwana
hannun Fateeman. Dan ALLAH yayisa bamai fitina ba. Tama kai ba wani ya damu da shan nn bane ba.........
✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
6️⃣8️⃣6️⃣8️⃣
______________
.........Fadeel da kansa ya yaye kansa. Dan wata irin shaƙuwace a tsakaninsa da Fateema da ita yakema
kallon uwa ta haƙiƙa ba mahaifiyarsa ba. Yayinda Fateema ke nuna masa wata irin soyayya mai girma da ko
ɗan data haifa a cikinta iyaka kenan. Son Fadeel take da zuciya ɗaya, so irin wanda koda wasa bata taɓa
kawoma ranta ba itace mahaifiyarsa ba balle tunanin cuta masa. A haka suka kammala karatunsu. A
lokacin Fadeel nada shekara uku, har lokacin kuma Kamila bata sake samun wani cikin ba. Sai kuma ta ɗan
shiga damuwa. Idan Aliyu yayi magana saita nuna masa tana son haihuwar domin cikama Fateema burinta.
Sotake ta cikama Fateema ɗaki da ƴaƴa ta yanda zata kwaranye mata ƙishirwar su. Idan ta faɗi hakan na
saka Aliyu sake jin ƙaunarta mai yawan gaske. Sai dai kuma a zuciyar Kamila sam wannan ba shine gaskiya
ba, tana faɗar ne domin sake farautar zuciyar Aliyu kawai, so take ya sota fiye da soyayyar da yake iƙirarin
yima Fateema, so kuma take ta haihun ta yanda zata mallake komai daga garesa, dan ta san dai komansa
nata ne tunda itace mai haihuwa.
To ALLAH bai sake kawo haihuwar nan ba sai da Fadeel ya shiga shekara ta huɗu sai ga wani cikin. Zo
kafa murna da farin ciki a wajen Fateema (Oum) kamar yanda Fadeel ke kiranta yanzu. Kamila kuma
(Mamy) Aliyu (Abah). Hakama dangi nata mata fatan alheri musamman ta ɓangarenta. Fatansu shine ta
sake haihuwar namiji, haka itama kanta wannan shine fatan nata. Ga Oum da Abah kuwa basu da wani
zaɓi, duk abinda ALLAH ya bada so suke yi. A haka dai ciki ya shiga watan haihuwa, ranar na zuwa ALLAH ya
sauketa lafiya ta haifo ɗanta namiji again. Ya ALLAH burin Mamy da zuri'arta ya cika, dan sun san ta kuma
gama kama gida da mai gida. Ga Abah yayi murna ya kumayi kukan tausayin Oum a ɓoye kamar yanda
yake yi a ɓoye tun haihuwar Fadeel. Ga Oum kuwa ko'a jikinta, dan ko sau ɗaya bata taɓa jin hassadar
Mamy ba akan tazo ta haihu a gidan ita bazata haihu ba. Ita tun bayan kukan samuwar ƙaddararta bata
sake zama ta damu kanta da tunanin shike nan bazata haihu ba, balle saka kanta a damuwa. Tuni ta
fawwalama UBANGIJI komai, ta kuma amshi jarabawarta da hannu biyu, kullum cikin godema ALLAH take.
Tayi imanin maybe haihuwar ba alkairi bace a gareta shiyyasa UBANGIJI ya jarabceta da yankewarta da
wuri. Kuma ai ba sai ka haifi ƴaƴa da cikinka bane suke zame maka ƴaƴa, ɗa na kowa ne, maybe ma bazaka
amfani wanda ka haifa ba sai na wani, nakan kuma wani ya amfana. Wannan yasa bata taɓa jin wani
ƙaiƙayin hassada ga haihuwar Mamy ba. Dan zuciyarta duk ɗaya take ɗauka...
Kwana biyu da wannan haihuwa Mamy ta fahimci kamar Abah bai murna da haihuwar ba, sai
hankalinta ya fara tashi, da dare ya shigo mata sai da safe ta daure cikin damuwa take masa tambaya. Ya
jima shiru kafin ya kai zaune tare da ɗaukar jaririn ya rungume a jikinsa. Cikin kulawa ya ce, “Kamila ba
farin cikine bana yi ba. Nama fi kowa farin ciki kuma ina cikin godiyar UBANGIJI daya bani abinda arziƙina
ko ilimina baya badawa balle tarin dangi da nasabarsu. Zuciyata ce kawai, zuciyata ce ke tsananin tausayin
Fateema. Kamila Fateema MATAR ƘWARAI CE RABIN ADDINI, ke shaida ce akan ta da ƙyawawan halayenta
a ɗan rayuwar da kikai da ita ta ƙawance har zuwa ta zaman gidan nan. Munci buruka da yawa tsakanina
da Fateema akan ƴaƴanmu, sai dai ashe ba haka UBANGIJI ya ƙaddara mana ba. ALLAH sarki Fateema
baiwar ALLAH, koda wasa koda ganganci ban taɓa ganin damuwa ko jin ƙyashin samuwar haihuwa daga
wata ba ita ba a gidan nan......”
Takaici da zafin da zuciyar Mamy keyi akan kalamansa na yabo ga Oum ya sata saurin katsesa ta hanyar
faɗin, “Dan ALLAH ka daina faɗin Fateema bata haihu ba, ka daina raba ɗayan biyu akan yaran nan da
Fateema. Tabbas ni ce nai rainon cikinsu da naƙudar su kawai, amma tun kafin suzo duniya mallakin
Fateema ne. Ka shaida ni Kamila kamar yanda na mallaka ma Fateema Fadeel da alƙawarin bazan taɓa
canja hakan ba koda a kan fuskata shima wannan jinjiri ɗan kwana biyu na mallakashi ga Fateema har
abada. Da zarar na yayesa ta ɗauka nata ne, kai in ma zata sha wani abu ne ta shayar da shi da kanta ni
tama amshesa yau ikonta ne”. Hawayen ɗaci da tiririn fitar kalamanta da iyakar bakinta suke banda
zuciyarta suka shiga silalo mata....
Tabbas kamalanta ratsa ɓargo da zuciyar Abah suka dinga yi, har bai san ya jawota jikinsa ya rungume
taba, sai jera mata addu'oi yake hawaye na zuba masa shima. Sosai ƙaunarta mai yawa take sake samun
gurbi a dukkanin jinin jikinsa bawai a tsokar zuciyarsa kawai ba. Baiyi ƙwairon baki ba ya shiga jera mata
kalamai masu nauyin gaske da ta jima tana ƙishirwar jinsu da buƙatar saurare daga garesa. Shi ɗin dai shi
Aliyu da tun a haɗuwar farko ta kamu da soyayyarsa. Duk da so da ƙaunar da takema ƴaƴanta guda biyu
masu tsananin kamanni da shi ta gwammace ta sadaukar koda na wuccin gadi ne domin samunsa shi da
zuciyarsa gaba ɗaya. Daga baya sai tayi haƙin ƙwatar ƴaƴanta a tsakaninta da Fateema. Dan tabbas wannan
ƙyautar duk biyu a iya fatar bakinta take bawai a zuciyarta ba. Amma ta fahimci dolen dole sai ta yita kafin
ta samu zuciyar mijinta da dukkan kulawarsa fiye da wadda yakema Fateema. Dan haka zatai dauriya da
juriya na wani lokaci...
Haka kuwa akayi, shima jinjiri da yaci sunan Fawzan Mamy ta tabbatar a gaban kowa ta mallakawa Oum
har abada. A wannan gaɓar kam Oum kukan da tai har sai da ta dinga bama kowa tausayi, dan kuka ne na
farin ciki da dukkan jin ƙauna dake fita tun daga zuciya. Ita kanta batama san inda zata ajiye martaba da
kimar Mamy ba zuciyarta. Ƴan uwan Mamy kam da mahaifiyarta sun balbaleta da masifa da nuna mata
kuskurenta. Amma sai tayi murmushi kawai tana mai kallonsu...
“Ku daina min kallon wawuya sarai nasan abinda nake yi. Amma bazaku gane ba sai a nan gaba kaɗan.
Domin kuwa fatsa na jefa a kogi tare da ƙananun kifaye a jikin fatsar dan samun damar shaƙo manyan
kifaye mamiyo. Har yanzu baku san wanene Aliyu akan Fateema ba....”
“Oh ke a naki haukan kina nufin duk kinyi hakan ne dan samunsa da matarsa?”.
“Tabbas hakane Mama, dan ta hakan ne kawai zan mallaki Aliyu da komai nasa, ta hakanne Aliyu zai bani
dukkan yarda da aminci. Ta hakanne zan saka Fateema a kwalba na rufe rufewa ta har abada. Daga ƙarshe
na dawo da ƴaƴana hannuna cikin sauƙi. Shiyyasa ma na sake tabbatar mata a gabanku a gaban Aliyu, a
gaban dangisa haihuwata ma ta gaba mallakar Fateema ce. Zan bata ƴaƴa uku kafin wanda zasu biyo bawa
su amsa sunan nawa....”
“To idan kuma haihuwar ta tsaya miki daga ukun kuma fa Yaya?”.
Autar su ce tai tambayar. Kallonta Kamila tayi da murmushi. Sai kuma ta dafata da faɗin, “Humm Gambo
kenan, ina ji a jikina sai nayi haihuwa ɗai-ɗai har goma anan gidan, dan na sadaukar da uku kuwa ai ba
komai bane, bama sadaukarwa bace ba ajiyar ce. AJIYA A DUHUn da FATEEMA bata sani ba. Dan komai
daran daɗewa sai ƴaƴana sun dawo gareni a gabar da Fateema ke murna da jin alfaharin zata amfana. Zan
bata fili ne a yanzu ta gama min wahala da su iya iyawarta, ni kuma na mora kayana a lokacin girmansu”.
Murmushi kawai Gambo tayi dan ita kam ta gamsu da bayanin Kamila, yayinda yayarta da mahaifiyarsu
kawai suka girgiza kawuna, dan suna ji a ransu lallai Kamila ta tafka babban kuskure. Kuskuren da bazata
fahimci kuskure tayi ba sai anan gaba....
To koma dai yaya ne Mamy ta cigaba da shayar da Fawzan shima, yayinda komai nashi ke'a hannun
Oum, shan nn kawai ke kawosa tamkar yanda akai da Fadeel. Shi Fawzan ba kamar Fadeel ba, ba yaye
kansa yay ba, yana da shekara ɗaya Mamy ta sake samun ciki, wannan shine dalilin yayesa gudun samun
matsala. Nan ma Abah da Oum suka cigaba da kula da ita da kaffa-kaffa, dan wannan cikin ma sai yafi bata
wahala fiye da na Fadeel da Fawzan. Ga cikin da tsirfar tsiya, yana son wancan baya son wannan. Tun yana
watanni biyar yay wani irin girma na tsiya kai kace tagwaye ko ƴan uku ta ɗauka, dan Oum da Abah har
tsokanarta suke akan wannan karan kodai ƴan uku ne ko twins. Murmushi kawai take yi akan batun, amma
a can cikin ranta tana ma kanta fatan hakan itama. A lokacin da cikin ya shiga watanni bakwai sai wahalar
ta ninku matuƙa. Har takai bata iyama kanta komai sai da taimakon Oum da Aba. A haka aka shiga watan
haihuwa da ƙyar, har ALLAH ya kawo ranar haihuwar. Ansha gumurzu, gumurzu na haƙiƙa dan kwananta
biyu akan gwiwa kafin a na uku ALLAH ya sauketa lafiya. Wannan karan ma dai namiji ne sargaɗeɗe mai
kamanni da ƴan uwansa, sai dai shi ya ɗan ɗakko duhun fatar Mamy saɓanin Fadeel da Fawzan dake farare
tarr dasu tamkar mahaifinsu da Oum. Jaririn nan ƙato ne na gaske, dan bayan fiddosa hatta ma'aikatan
asibitin zuwa kallonsa suke da mamaki. Haka dai aka sallamesu suka koma gida, a wannan karon ma dangi
tako ina sun cika gida anata huɗar arziƙi.
Ƙalubale na farko akan wannan haihuwar shine tunda Mamy ta ɗaura idonta akan jinjiri wata kalar
ƙaunarsa mai zafi data bambanta data ƴan uwansa ta shigeta. Ƙalubale na biyu tun a asibiti yaƙi kama nn.
Ƙalubale na uku Abah da kansa suna dawowa gida gaban ƴan uwanta da nasa ya sake tisama kowa
alƙawarin Mamy na ranar haihuwar Fawzan akan mallakama Oum wannan ɗan ma a karo na uku, dan haka
ya sake tabbatar musu wannan alƙawari na nan daram bai canja ba. Sai dai suyima Mamy addu'a kuma da
fatan alkairin ALLAH ya kawo ƴaƴa na gaba da suma zasu kasance matsayin nata mallakin. Ƙalubale na
huɗu shawarar da Umma ta bada akan tunda jinjiri yaƙi kama maman Kamila bazai yiwu a barshi a haka ba
fa sai a koma asibiti, koda aka koma asibitin sai likitoci suka fahimci fa akwai matsala ne, matsalar canjawar
kalar nn Mamy daga fari zuwa yellow, dole suka shiga binciken ainahin matsalar, suka kuma bada shawarar
sai dai a shayar da yaron madara gudun kada a shiga hakkinsa, dama gashi yanata kukan yunwa. Ita kuma
aka ɗorata akan magani da tabbatar musu in sha ALLAHU komai zai wuce ta samu lafiya kamar ba'ai ba. Jin
haka sai Umma tace baza'a bashi wata madara ba Oum ce zata sha magani ta shayar da shi. Baba Sardauna
ya yarda da wannan shawara ta matarsa, hakama Abah da sauran dangi. Dan haka mahaifin Oum wato Dr
Kasheem Kura da kansa ya aikoma Mamy ingatattun magunguna tun daga Paris da zai bata ruwan nn. Dan
su basu zo ba a lokacin babu jimawa da sake haihuwar matarsa (Maryam kenan mahaifiyar Oum ina fatan
kuna fahimta). Itama ta samu ɗa namiji cikin na huɗu da yaci sunan Rafeeq. Oum bataje ba saboda yanayin
da Mamy ke ciki a lokacin.
Cikin amincin UBANGIJI Oum nashan magani kuwa sai ga ruwan nn mai ƙyau. Aiko ta hau shayar da
jinjirinta da yaci suna Ajwaad. Yayinda aka bar Mamy da jiyyar zuciya da kukan ɓoye. Gashi kuma babu
yanda ta iya, dan ita dai tai alƙawarin nan babu wanda ya tirsasata, a zahiri kuma taƙi nuna ma kowa
damuwarta saboda neman soyayyar Abah da take ganin saita wannan hanyar kawai zata iya samunta. Ita
dai Oum ranta fes, ƴaƴanta uku cif sun kammala, tsakaninta da UBANGIJI sai godiya. Sai kuma aminiyarta
Kamila da har abada take jin a ranta bata da kamarta a wannan duniyar idan ka cire iyayenta da iyayen
riƙonta da mijinta. Ƙaunar yaran nan uku take da zuciya ɗaya, da iya gaskiyarta. Bata taɓa jin ƙaiƙayin
cewar ba itace ta haifesu ba. Kai ita mantawama take da ba itan ce ta haifesun ba. Dan a zahirance dai
Mamy kawaici take yi. Bata taɓa jingina kanta da yaran koda wasa. Sai ta faki ido ta dinga aibanta Oum a
zuciya, gefe ga tsananin kishinta da take ji da hassadar finta komai na rayuwa da tayi. Wanda ada can
iyakar kishin soyayyar mijinta Aliyu kawai take ji. Amma bayan auren data sake fahimtar wacece Oum a
wajen Aliyu da nasarorin rayuwa dana iyayenta ke da shi sai hassadar hakan ta shigeta.
(Wannan hassadar al'adace kamar a zukatan matanmu akan kishiya. Ya rabba ALLAH ka yaye mana
hassada dan mugun dafi ce mai kassara rayuwa da cigaban cikinta)........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
6️⃣9️⃣6️⃣9️⃣
______________
.........To rayuwa fa ta fara shuɗawa. Abubuwa da yawa nata faruwa. Ciki harda yaye Ajwaad da Oum tayi
bayan cikarsa shekara biyu cif yana sha daga jikinta. Tuni ta sanyama Ajwaad Auta, tunda dai Mamy da
kanta ta tabbatar da iya gejin abinda zata bata kenan haihuwa ta gaba tata ce. Autancin ko yabi Ajwaad tun
da ƙarancin shekaru. Dan ALLAH yayisa irin yaran nan masu tsananin ƙulafucin iyaye. Sam baya ƙaunar
koda wasan wasa Oum tayi nesa da shi. Wani lokacin ko toilet ta shiga yana ƙofar bayi yana jiranta har saita
kammala abinda take ta fito. Idan zataje wajen Abah kuwa a ranar girkinta sai fa da wayo da dabara idan ta
tabbatar barcinsa yayi zurfi can cikin dare. Wani lokacin kuma dashi dole take tafiya ta kwantar da shi a
falo ko in barcin nasa yay nisa ta maidosa cikin ƴan uwansa. Akowane motsinsa shi dai Oum ce. Gashi da
shegen ƙiwa tun yana watanni biyar zuwa shida baya yarda da kowa sai Oum sai Fadeel idan yaso. Amma
ko Abah da Mamy basu isa taɓashi ba ya hau ihu yana bin Oum da kallo yana kuka. Sanda ya cika shakara
ɗaya da wasu watanni kuwa idan ka takura sai ka ɗaukesa cizo zakasha ta yanda dole ka saukesa ya koma
wajen uwarsa. In ma anguwa suka fita bai yarda wani yako taɓasa daga jikin Oum. Baba Sardauna ne ma ke
ɗan samun wannan alfarmar shima ana ɗan yarda da shi saboda yana bashi irin chocolates ɗin da yake so.
A haka ya cika shekara huɗu aka saka shi a makaranta kamar sauran ƴan uwansa. Duk da su an sakasu tun
suna da shekara uku-uku, shiko ƙulafucin uwa ya hanashi. A yanzun ma dai badaƙala ake sha dan baya
ƙaunar zaman makarantar, yata kuka kenan da kiran Oum! Oum! Shi akaisa wajen Oum ɗin sa. Shi gida
zaije wajen Oumyn sa. Karatu yaƙiyi ya hana sauran yara yi. Duk wanda ya nuna kulawarsa da son
rarrashinsa ya danƙarama yaro cizo sai an rabasu da ƙyar. Ganin haka yasa makarantar suka bada shawarar
a ƙara masa lokaci ya ƙara wayo, dan inma ba hakaba bafa karatun zai yi ba. Dole su Oum suka yarda da
hakan, amma tana ƙoƙarin masa a gida ita da Fadeel musamman na ɓangaren addini. Gashi kuma da
ƙwaƙwalwa Masha ALLAH.
Sai da Ajwaad ya cika shekara bakwai a duniya sannan Mamy ta sake samun ciki, a lokacin yana zaman
makaranta da ƙyar dan yana a nursery 2 ma. A islamiyya kuwa Alhamdullah ya tashi da ƙwazon karatu
kamar sauran ƴan uwansa biyu. A wannan karon abinda ya fara tadama Mamy hankali kamar Abah bai
damu da cikinta ba kamar ukun can na farko, sai Oum ce ma ke dama-dama da ita da bata kulawa. Idan tai
magana yace to mikuma ya rage shida keda uku rigis, ai sai fatan alkairi da addu'ar ALLAH ya sauketa lafiya.
Wannan furuci nashi na cimata zuciya, amma haka take dannewa ta maida abin wasa. A haka ta shiga
watan haihuwa, a kuma lokacin Abah ya fara musu gini dan yace wannan gidan ya musu kaɗan ga zuri'a
suna tarawa. A wata juma'a Mamy ta sauka lafiya ƴan biyu duk maza. Musalta muku irin farin cikin da
wannan ahali suka shiga a wannan karon ma ɓata lokaci ne. Anyi shagalin suna kamar yanda akai na baya,
duk da Mamy taso ace na wannan karon yafi na bayan armashi kodan biyu data santalo. Haka dai suna ya
tashi lafiya yara sukaci sunan Hassan da Hussain. Dan tace bata son a canja mata suna a barsu da nasu.
Duk da a wannan karon Mamy batace ta mallakama Oum su ƴan biyu ba bata fasa yin hidima a gareta da
jinjirayen ba kamar yanda ta saba. Dan har takai Ajwaad na nuna kishinsa a fili, sai dai suyita masa dariya
kawai. Bayan yaye su ƴan biyu da wata uku Hussain ya fara laulayin haƙora, ya dinga gudawa irin na haƙora
mai wahalarwa. Abin ALLAH kwana biyu kacal a wannan halin UBANGIJI ya ɗauke abinsa. Duk da rasuwar
yaro ce ta girgiza wannan ahali, dan daga Oum har Mamy kuka rurus sai Abah ne ke lallashinsu, da ƙyar
suka haƙura suka sabarma kansu da rashinsa. Sai kuma tunda Hussain ya rasu shima Hassan lafiya ta masa
ƙaranci. UBANGIJI mai rahama da jin ƙai shima bai cika kwana arba'in ba yabi ɗan uwansa. Ai neman
zautuwa Mamy tayi, da ƙyar ake tausarta. Sai dai kuma babu yanda ta iya da hukuncin ALLAH.
Tun bayan rasa ƴan biyu ko ɓatan wata Mamy bata sake yi ba. Har suka tare asabon gidansu da a yanzu
suke ciki wanda ke maƙwaftaka da nasu Maanal. Zuwa yanzu tsanar Oum Mamy keji mai zafi a ranta,
amma a zahiri bazaka taɓa fahimtar hakan ba, gefe ga uwarta da ƴan uwanta dake zugata. Ba Oum kawai
ba, hatta duk wanda Oum ke huɗɗa da shi Mamy ta tsanesa. Dan haka bata taɓa son Ammie da su Maanal
ba. Amma koda wasan wasa bata taɓa nunawa a koda fuskarta ba. Sai ma nunawa take kamar tanama
Oum kawaici musamman akan tarayyar Maanal da Ajwaad dake a bayyane ga kowa. Ita ko Oum soyayya
takema Mamy ta gaskiya da kuma zuciya ɗaya, jin girmanta take da kimarta ta yanda zuciyarta koda
hasashe bata taɓa kallon munininta ba. Kai a yanzu koda Abah yazo yace da Oum ga munin Mamy to
tabbas bazata amince ba. Ta bata matuƙar yarda da gaskiya ta yanda bata ko jin wani ɓurɓushin kishita a
ranta. Kai sam bama ta mata kallon kishiya sai ƴar uwa. Hatta da sirrinta bata taɓa canjawa daga yanda
take sanar mata ba a sanda suna amintaka da ƙawance. Komai buɗema Mamy take da zuciya ɗaya ta nema
shawara. Kuma a cikin ƴan uwanta kaf babu wanda ya taɓa kallon illar hakan dan suma yarda ɗaya suka
bama Mamy saboda ɗunbin hallaci da yakana da dattakon data nuna ga Oum ɗin. Lallai Mamy ta samu
fada da soyayya tako ina daga zuri'ar Baffa Ishaq Darma. Yarda suke mata ta gaskiya, basa taɓa banbantata
a matsayin bare a cikinsu, basa taɓa banbantata tsakaninta da Oum dake matsayin tasu. Kai sai suyi mata
abu basu yima Oum ba musamman ma mahaifinta Dr Kasheem Kura. Dan shi yakance Mamy itace ƴarsa.
Oum kuwa ta Baba Sardauna ce.
Itama a zahiri ta riƙe dukkanin abinda zasu kalleta da wannan mutuncin, duk da zuciyarta cike take da
shirin maido da ƴaƴanta gareta komai tsahon lokaci da rayuwa zata bata. Hakama duk damar data samu
daga Abah da yarda bata gamsar da ita ba, kullum cikin sake harin ninkin baninkin ɗinta take yi. Duk da
kuwa ta wawashi kaso mafi girma daga soyayyar tasa. Dan tun fara girman su Fadeel Oum ta sake sallama
mata Abah ɗin kaso saba'in cikin ɗari, ita kuma yake riƙe da talatin cike da kawaici da dattakonta. A yanzu
ko tafiya Abah zai yi da ita ne. Idan wani abu ya taso kai tsaye Oum zatace yaje suyi da Mamy ita bazata iya
yin nesa da yaranta ba. Tun abin na bama Abah haushi har ya haƙura ya sallama dan ya fahimci mai raba
Fateema da ƴaƴan nan nata sai dai ALLAH. Musamman Autan ta uban ƴan ƙalata da ƙulafucin uwa.
Duk da Oum bata taɓa fitowa ta sanar ma yaran ainahin mahaifiyarsu ba tana nuna musu girma da
darajan Mamy a garesu. Kullum cikin cusa masu soyayyarta take a zukatan yaran cike da hikima. Tana
ƙawata musu girma da kimar Mamy a zukatansu. Tun abin baya tasiri a ransu harya fara. A hankali Fadeel
da Fawzan suka ɗan fahimci wani abu kaɗan bamai yawa ba. Sai dai hakan bai taɓa canja musu Oum ɗinsu
a matsayin da suke kallonta ba. Ita dai suka sani, ita kuma suke kallo da matsayi irin na uwa da mahaifiya.
Amma suna girmama Mamy da bata hakkinta da mata soyayya kamar yanda Oum ta koyar da su take ma
kan koyar da su ɗin. Shi dai oga Ajwaad Auta Oum ɗinsa kawai ya sani. Shi uban kowama ya mutu har
liman in dai za'a bar masa Oum ɗinsa. Farin cikinsa ce ita, sannan duniyarsace. Bai haɗa soyayyarta data
kowa ba a duniya...
Wannan halin na Ajwaad na cima Mamy rai matuƙa, dan ALLAH ya jarabceta da soyayyar Ajwaad fiye
da duk sauran yaranta. Ƙaunar yaron take har ƙarƙashin zuciyarta. Ga shi kuma hankalinsa san baya a kanta
yana akan maƙiyarta ne. Shiyyasa take sake jin ninkuwar zafin Oum ɗin matuƙa. Gashi ta fahimci itama
Oum ɗin tanama Ajwaad wata irin soyayya mai girman gaske. Hakan na nufin bayan Aliyu sun sake yin
tarayya akan abu guda kenan. Wato soyayyar AJWAAD ALIYU ABUBAKAR DARMA...
_MUN SAKE DAWOWA DAI CIKIN LABARIN RAYUWAR AJWAAD DA MAANAL DATA GABATA_😀
*GIRO:-* A Giro dai an ɗaura auren Babu da amaryarsa Safarah. Safarah yarinya ƙyaƙyƙyawa mai busashen
ido. Dan cikakkiyar ƴar tallace a tashoshin motoci na yankin ƙauyen Giro da cikin Suru. Musamman a
ranakun kasuwanni. Kai har cikin Kebbi idan ta kama suna zuwa kawo kayan sayarwa ita da ƙawayenta.
Gwaggo ta zaɓama Babu ita ne dan a cewarta itace dai-dai da Asiya. Anko sha biki, dan su Ammie sun sha
kallo. Bajinta sosai Gwaggo tayi a bikin dan dabbobinta har goma ta saka a kasuwa. Bayan tarewar amarya
a nan dai gidan ɗakin dake a tsakanin Gwaggo da Ammie ango yasha bidiri. Dan Babu dai kura ne ba'a
bashi ajiyar nama. Duk da ma dai abin bai masa armashi ba saboda samun Safarah ba'a cikakkiyar
budurwa ba ita dai. Amma tsabar iya bariki na yarinyar nan da dudu shekarunta goma sha tara ne a duniya
sai ta dinga zumbuɗa masa ihu da kururuwa ita a dole tana shan wahala. Wannan ihu ya tadama Ammie
hankali, bawai akan kishi ba, duk da bazatace bata kishin mijin nata ba. A'a saboda su Shahidah ne. Dan
takai yaran nan sai da suka farka a barci suma. Yayinda itama kanta Gwaggo data fito tsakar gida a wannan
tsohon dare take faman kiran sunan Babu da gargaɗinsa akan wai yabi Safarah a hankali, ya dai san
yarinyar ƙarama ga mutuncinta ta kawo. Wannan abu shine ya taru ya saka Ammie kuka dan su Amaal nata
jera mata tambaya akan ko mi ya samu amaryar haka. Sai dai bata kula yaran ba, daga ƙarshe ma ta musu
tsawa suka kwanta. A ranta dai tana sake godema ALLAH da su Abah suka wuce da Maanal. Dan tabbas
kaɗan daga aikinta tama fita itama koda safe ta tsare Babu ɗin da tambayoyi.
Wannan kuka da amarya tasha da ihun iskanci yasa kowa ya yarda ta kawo mutuncinta. Shi ko Babu tai
masa ɗaurin goro dan bashi da damar musawa. Ga wata irin kunya da nauyin Ammie da ALLAH ya
jarabceshi da ita. Dan ƙiri-ƙiri ya kasa yarda ya haɗa ido da ita a wannan yinin baki ɗaya. Ko hanya suka
haɗa duk sai ya daburce. Itako Ammie ta dake abunta ko'a fuska bata nuna masa ba. Amma a dare na biyu
saita tura Amaal da Shahidah kwana ɗakin Zainabu ɗaya daga cikin matan gidan, kasancewar tasan mijinta
baya gari. Dan gara ta nesanta yaranta da shiyyar gaba ɗaya kafin su fahimci abinda ke faruwa.
Aiko Ammie tayi dabara, dan daren yau ɗin ma bata canja zani ba. Sai da Safara tayi duk iya yinta ta
hillaci Babu ya kasance da ita. Gashi dama ta ɗirki magunguna shima an ɗirka masa ta hanyar abinci. Ai sai
ihun ya zama nasu su biyu yau ita da shi. Kai jama'a wannan iskanci dami yay kama haka. Cewar Gwaggo
cikin mitar son yin barcin da suka hanata. Amma da safe ko'a fuska bata nuna ba saima kulawa take bama
amarya ta musamman dan Ammie taji haushi. Sai kuma Ammien ta tabbatar mata ita ɗin ƴar halak ce dan
bata nuna damuwarta ba koda a fuska. Kasancewar daren jiya ta kwana salla da karatun Alqur'ani sai ta
tashi sakayau zuciyarta cike mamaye da farin ciki. Musamman daya kasance da safe ta kira Oum a waya
sun sha hirarsu harda Maanal dake ta faman bata labaran daɗin da Oum da Bestyn ke ciyar da ita. Shi
kansa Babu ɗin sai yanayin na Ammie ya sake jefa shi a ƙaulani da ɗunbin kunyarta da shakkarta ma..........
✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
7️⃣0️⃣7️⃣0️⃣
______________
Wannan zanen agogon shine tushe kuma sila na ginuwar buri mai girma a zuciyar Ajwaad game da
Maanal akan harkar zane-zane musamman agogo....
____________★
Sosai Giro tama Ammie zafi, zafi mai tsanani ita da yaranta. Dan haka ta roƙi Baabu komawa Kano. Da
farko ya turza, saboda gwaggo ta sakashi a ɗaki ta kitsa masa cewar yabar Ammie ta cigaba da zama anan
Giro. Itako a karo na farko tattara kayanta tsaf dana yaranta washe gari ya fita shi da amaryar tasa da
Gwaggo zuwa can gidansu wai babanta babu lafiya ta baro Giro bisa taimakon Baba Haruna. Taso ta kwana
a kabbi. Sai dai rashin mukulli dan yana a hannunsa yasa haka suka fallo hanya. Cikin amincin UBANGIJI
suka iso cikin Kano kusan tara na dare. Sai da suka shiga gida ta kira Oum ta sanar mata. Sosai Oum tayi
mamaki, amma sai ta ture mamakin ta kwantar da Maanal datai barci a jikinta ta fita. Kitchen ta shiga ta
haɗa musu abinci sannan ta kira Abah a waya Fawzan ya mata rakiya.
Sosai hankalin Oum ya tashi da ganin yanda duk Ammie ta rame ta lalace. Gashi suna haɗa ido kawai
Ammie ta sakar mata kuka. Jiki na rawa ta ajiye abincin ta rungumeta tana lallashi. Sai da tayi kukan sosai
sannan Oum tace ta tashi tai wanka. Wankan duk sukayi sukaci abinci, sannan Oum da Fawzan suka koma
gida. Damuwa fal kan Oum. Washe gari rijib Ammie ta tashi da ciwo, dole suka wuce asibiti. Aiko aka basu
gado dan likitocin sun tabbatar da jininta ya hau sama matuƙa. Sai da Ammie tayi kwanaki huɗu sannan
aka sallemta suka dawo gida. Washe gari cikon na huɗu sai ga Baabu da amarya sun iso. Ammie batayi
mamaki ba, kuma batace komai ba, duk da taga da wani wutar bala'i da rashin mutunci yazo garin. Dan
babu kunya ya rufeta da zagi harda mari wai ta taho bada izninsa ba, ta raina masa mahaifiya miye-miye.
Ko ci kanka batace da shi ba, hakan sai ya dake hasalashi ya fara nemo hanyar da zai musguna mata ta
mangantu ya juye mata abinda ke a ransa. Ɗaki uku ne kacal a gidan, nata, nashi, sai na yara. Haka ya
murje ido yace ta koma na yaran ita amarya ta zauna a nata. Ammie ta ce wannan ne kuma bai isa ba. Dan
ita ba wulaƙantacciya bace, ba gori ba gidan nan mallakinta ne idan ya manta tunda da kuɗinta aka
sayeshi. To dama fa ta samu, haka Baabu ya dinga zuba tijara har sai da Abah yazo ya fiddashi a gidan aka
samu masalaha. Daga ƙarshe dai dole amarya ta zauna a ɗakin shi.
Tun wannan dawowa komai ya canja, canji mai ban mamaki daga ma'auratan dama gidan kansa.
Musamman daga Baabu. Hatta ƴaƴansa yanzu ja baya suke da shi, dan abu kaɗan zakayi ya hauka da zagi.
Ranar ma ƴar lelen tashi Maanal har duka taci, aiko ta haɗa inata-inata ta koma gidan Abah. Tafi sati bata
shigowa gidan nasu kafin ta saki jiki kuma ta manta bisa tirsasawar Ajwaad ta koma shigowa. Ga amarya
dai babu wata matsala. Ta kwantar da kanta yana fahimtar komai daki-daki kamar babu komai. Sai dare ta
ishesu da ihu ita da miji. Wannan abu shine mafi girma tadama Ammie hankali, dole ta maida kwanan su
Shahidah gidansu su Oum gaba ɗaya. Dama yanzu batun miji Ammie bata da shi a gidan, Baabu yana tare
da amaryarsa tunda suka dawo. Sai da suka cika wata ɗaya cif sai gashi da takarda wai ya saki Ammie saki
ɗaya.
Murmushi kawai Ammie tayi da faɗin, “ALLAH yasa haka shi yafi alkairi, amma kuma babu inda zanje.
Zan zauna na cigaba da rainon ƴaƴana har lokacin aurensu sai dai kai ka bar min gidan tunda dama nawa
ne”.
Wannan furuci nata shine ya kawo tashin hankali, tashin hankalin da dole sai da Abah da Oum suka
shiga yanzu ma. Da ƙyar dai aka sasanta bayan Abah ya nusar dashi illar abinda yake shirin aikatawa. Shine
fa ya maida Ammie. Haka aka cigaba da haƙuri Ammie bata da miji, bata taɓa tada kai ta kallesa ba har
tsawon shekara biyu. (Kenan dai tun da amarya ta tare😭) Ko'a fuska Ammie bata nuna masa damuwarta,
karatunta kawai take na Islamiyya da take zuwa da kula da tarbiyyar yaranta da sana'arta. Dan takai yanzu
ma itace ke ciyar da kanta. Zuwa yanzu su Maanal fa an shiga secondary, Dan suna aji biyu ma duk da da
ƙyar suka amsheta saboda sunce tayi ƙarama da yawa, yayinda Shahidah ke shirin kammalawa ita da
Fawzan, babban yaya kuwa ya wuce ƙasar Saudiya karatu.
Amarya bata shiga sabgar Ammie, itama bata shiga tata, dan a zahiri bata da matsala da ita sai da
Babu, sai dai tushen matsalar daga gare ta ne tazama macijin sari ka noƙe ne kawai. Har lokacin kuma dai
babu ciki, sai da ta shiga shekara ta uku sai ga ciki, nan fa su Babu aka shiga murna da addu'ar haihuwar ɗa
namiji. Ita dai Ammie ko tari bata musu ba, duk taɓarar iskancin da amarya keyi bata nuna tasan suna
numfashi a gidan ba ma. Sai da ciki ya shiga wata biyar sannan ya ɗauketa suka wuce Giro, dawowar da
basu sake yi ba sai da ta haihu akasha shagalin suna a Giro dan buri ya cika an haifi Namiji. Ashe duk
wannan abun da ake Baabu na cikin Kano, tunda ya kai amarya gida Gwaggo ta sharɗanta masa hanashi
komawa wajen Ammie wai har sai in matarsa ta haihu. Ammie bata taɓa sanin haka ba sai bayan
dawowarsu da jinjiri da Gwaggo, wai itama ta dawo nan Kano da zama, ashe aure dai ya ƙare tsakaninta da
Baba Haruna duk kuma akan Ammie ne, dan bayan tahowar su Ammie a wancan karon ansha fitina Baba
Haruna ya saki Gwaggo shine fa ta ɗau alwashin yanda ya saketa itama sai an saki Ammie, idan kuwa ma
ba'a saketan ba sai ta ɗanɗana fiye da abinda itama ta ɗanɗana. Wannan duk shine tushen matsalar da
suke ciki a yanzu shiyyasa Amarya data san komai ta koma gefe ta nutsu tana shan kallo dan tace faɗan na
manya ne ba nata bane.
Dawowar Gwaggo Kano ba ƙaramin tashin hankali su Ammie suka shiga ba ita da yaranta. Musamman
Maanal mai bakin tsiwa datai matuƙar tsanar Gwaggo, kuma a zahiri take nunawa bata ɓoyewa. Yayinda
Gwaggo itama ta tsani Maanal fiye da su Shahidah, ta kuma tsani Ajwaad, dan shima a dalilin ƙin Maanal
da su Ammie daya ga Gwaggo nayi ƙuru-ƙuru ya sashi tsanar matar, dan sam Ajwaad baya son mugu da
mugunta. Rayuwa tayi tsanani wa Ammie, uwar miji, da miji da kishiya sun saka rayuwarta gaba data
ƴaƴanta. Shekaru kusan huɗu bata kwanciya da miji, baya shiga ɗakinta. Yanzu kuma haihuwar namiji tasa
kullum cikin aibanta mata yara suke da shegantasu, dan akwai randa Baabu da bakinsa yace yana
tantanamar ma su Shahidah ƴaƴansa ne. Wannan abu ya girgiza Ammie, ya sakata kuka mai tsanani da
sake jin sabuwar kewar iyayenta data rasa. Amma ya zatai, haka ta haƙura ta share hawayenta ta barma
ALLAH komai. A wajen Oum da Abah kawai take samun sauƙi da soyayya da ƙauna ita da yaranta.
Kammala secondary ɗin Shahidah yasa Abah tada zancen aurenta da Fadeel. Dan yace za'a fara nasu,
ita kuma Amaal sai Fwazan ya kammala. A ɗan tsukun Fadeel yazo gida hutu, dama can shi da Shahidah
tuni sun ƙulle, dan haka aka saka ranar aurensu ya koma saudia. Bayan komawar tasa Shima Fwazan ya
shiga lallaɓa Oum akan kawai a haɗe nasa dana Amaal lokaci ɗaya dana Babban Yaya, sai su tafi jami'ar
tare. Dan shi rashin ƙyawun result daya samu yasa dole ya ƙara shekara ɗaya a ƙasa sai da ya canja ssce
ɗinsa duka. Duk da a lokacin ita Amaal na ss2 sai yace kawai tayi exam ɗin itama su wuce tare. Oum ta
tunkari Abah da zancen, yay shiru yana nazari, sai zuwa can yace ta bashi lokaci zai yi magana da Baabu,
kuma zai kira Baba Haruna a waya....
____________★
Kamar yanda suka saba tashi sallar asubahi kullum yauma hakanne. Saida Fwazan ya fara yo alwala
sannan babban yaya ya shiga. Ajwaad shine ƙarshe, sai wani ciccin magani yake. Ya girma sosai a tsaye, dan
a yanzu shi da mutuniyar tasa suna js3 ne. Suna shirin tafiya ss. Shekarun girma sun gama bayyana mai,
dan har wani ɗan tsigin gemu ya ajiye (kamar jelar tsatso inji Ibro. 😂 ALLAH ya gafarta masa da iyayenmu
baki ɗaya 🙏).
Yanda yake tafiya kamar mara laka a jiki ya saka Fawzan sarkin tsokana faɗin, “Wai na Lilly kodai barcin
nan bai isheka bane ba?”. Harrarsa kawai ya ɗanyi ya wuce abinsa, dama Fawzan tsokana, Ajwaad
miskilanci. Haka suke kullum, sai ya ƙuresa ne yake tanka masa. Juyawa Fawzan yay ga babban yaya dake
canja kayansa zuwa jallabiya, shi kam tako ina ya zama cikakken saurayi, ga cikar kamala da nutsuwa ta
sake baibayesa, duk da shima Fawzan ɗin tsokanar ce kawai, amma a nutsensa yake. Har sun kammala
shiryawa yau ma Ajwaad na cikin bayi, babban yaya ya dubi fawzan da faɗin, “Wai mike damun auta ne
yanzu?. Da babu wanda ya kaishi himma shirin fita sallar asuba, amma tunda nazo garin nan naga sai mun
fita yake fitowa”.
Murmushi Fawzan yayi da ɗan sosa kai, sai kuma ya ɗage kafaɗa da faɗin, “Maybe yana wani uzirin ne”.
“Kamar ya?”.
Shiru Fawzan yayi saboda fitowar Ajwaad daga bayin a tunaninsa sun fita ɗin. Turus ya tsaya yana
kallonsu, suma duk sai suka zuba masa ido........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
7️⃣1️⃣7️⃣1️⃣
______________
.........Wani irin gumtse baki Fawzan yay yana danne dariyarsa da tsiya-tsiya. Idanunsa ƙyam akan sumar
kan Ajwaad da yake gogewa da towel, a jikinsa kuma rigar wanka. Aiko Ajwaad yay wani irin masifar yin
kicin-kicin da fuska tamakar zai sakar musu kuka. Yayinda Babban Yaya daya gama masa kallon tsaf shima
ya ɗauke idanunsa yana murmushi. Hanyar fita ya nufa abinsa yana faɗin, “Ka same mu a falo idan ka
shirya, dan kullum Abah yana maganar rashin fitowar ka tare damu, yana ganin kamar ma baka samun
sallar”. Daga haka ya fice bai jira amsar sa ba. Shima sai Fawzan yabi bayansa, sai da yaje ƙofa zai fita
sannan ya ɗan juyo ya sake kallon Ajwaad ɗin da har yanzu ya kasa motsawa daga inda yake. “Ka lallaɓa ni
na faɗama Oum a haɗa auren ka da namu ka huta da wannan wankan asubar wlhy, dan Lilly dai ta isa aure
shekara goma sha biyar ai ba laifi”.
Wata muguwar harara Ajwaad ya wurga masa, dan haka suke kamar abokai, to dama tsiran nasu ba
wani yawane da shi ba. Ficewa Fawzan yay da sauri yana sake gumtse dariya. Koda ya fito inda babban
yaya ke jiransu sai ya haɗiye dariyan. Kallonsa babban yaya ya ɗanyi sai kuma ya kauda kai. Cikin ɗan jin
nauyin abinda zai faɗa ya ce, “Tun yaushe Ajwaad ya fara wannan wankan asubar?”.
Batare da Fawzan ya kallesa ba shima ɗin ya ce, “Ai tun bayan wucewarka saudia babu jimawa. Kaga
kuwa fin shekara biyu kenan”.
Karan farko babban yaya ya dubi Fawzan ɗin, “Amma su Oum sun sani?”.
“Haba babban yaya yaza'ai su sani. Nima da muke ɗaki ɗaya baifi shekara ɗaya dana fahimta yana yi
ba. Kuma ban taɓa nuna masa nasan yanayi ba. Sai dai cikin hikima na sake nusar da shi sake nesanta
alaƙarsa da Lilly duk da zuwa yanzu duk abinda ya haramta garesu basa yinsa. Kamar taɓa jikin juna,
shigowa ɗakin mu sai da dalili, yimata tsifar kai da wanke mata underwear, zama kusa da juna gab, itama
kuma Oum tana matuƙar saka musu ido akan hakan. Duk da Alhamdullah suma tuni duk wannan
abubuwan sun daina shi gaskiya”.
“Alhamdullahi naji daɗin hakan, amma duk da haka soyayyar dake tsakaninsu mai ƙarfi ce, barinsu a
haka tunda har alamu sun nuna shi mai yawan buƙata ne yana da ƙyau su Oum su musu aure kawai, hakan
shine babbar masalaha. Duk da nasan yanayin da yake ciki normal ne ga duk namiji irinsa dake a irin gaɓar
waɗan nan shekarun na farkon balaga. Amma da alama shi yana cikin jinsin da al'amarinsu keda girma,
dan ni da kai duk bamu tsinta kammu a irin wannan yanayin mai tsanani haka ba gaskiya”.
“Tabbas hakane babban yaya. Kuma kayi tunani mai ƙyau. Sai ka samu lokaci kafin ka koma kuyi
maganar da Oum”.
“In sha ALLAHU ”.
Ya faɗa yana miƙewa saboda fitowar Ajwaad. Babu wanda ya yarda ya kalla a cikinsu saima faman sake
haɗe fuska yake yi. A tare suka fita gwanin sha'awa, hakan yasa Mamy da tun fara maganar tasu take tsaye
tana jinsu ta sauke wani irin nannauyan numfashi. Dama ta fito ne daga sashen Abah zata koma nata
ɗakin. Shi kuma ya fita ta ƙofar baya zasu haɗu da yaran su wuce massallaci...
A haka ranar Ajwaad ya yini yana faman fushi da kowa. Sai da Maanal ta shigo bayan azhar ta samesa a
falo kwance. Sunje anguwa ne ita da Ammie tun safe, sai yanzu ne suke dawowa. Ko gida batabi Ammie
sun shiga ba ta bama Amaal kayan da suka sayo a kasuwa na haɗin turare da Ammie keyi da kayan gyaran
jiki ta shigo gidan su Ajwaad ɗin. Dan tasan zai shiga gidan nemanta. Itama kuma missing ɗinsa take ji sosai
duk yau baya ganshi ba kasancewar fitar sassafe sukayi.
Itama dai tayi girma Masha ALLAH. Dan maƙerin bufurci ya fara bayyana kansa gareta ƙirji masha
ALLAH. Tayi tsaho ƙyawunta ya sake fitowa. Sai dai tana nan kamar a hure babu wani ƙiba. Sai da ta zauna
a kujerar kusa da shi tana faɗin, “Wash ALLAH na ni Manalu”. Sai kuma ta ɗan dubesa ganin baiko motsa
ba har lokacin idanunsa a lumshe. Ƙaramar harara ta masa, sannan ta ɗauke goran ruwan daya aje kusa da
shi yasha kusan rabi ta buɗe ta shanye sauran tana sauke numfashi da ajiyar zuciya. Sauran ɗan ruwan
daya maƙale a goran ta zazzaga masa saman ƙyaƙyƙyawar miskilar fuskarsa. Dole idanunsa suka fara
motsawa kafin ya buɗesu a hankali a kanta. Sai ta sake zuba masa ƴar harara, a shagwaɓe ta ce, “Besty ni
kake wani shahararrenwa?”. Ta ƙare maganar da tura baki. Sake lumshe idanun yay tare da ɗan matsesu
waje guda, sai kuma ya buɗe. Shima hararrar tata ya ɗanyi, kafin can ƙasa-ƙasa ya furta, “An shareki ɗin. Ni
da kika tashi fitarki kin sanar dani zaki fita?”.
Sai da ta sake tura bakin sannan ta ce, “To ba Ammie bace tace sai na rakata kasuwa. Kuma ko lafiya
ma banda shi cikina namin ciwo ga zazzaɓi ina ji amma tace langyare nake son yi mata dan tace na rakata.
Shine kawai na bita gashi nan kaina ciwo yake min kuma ina jin ciwon cikin har yanzu”.
Yanzu kam yinƙurawa yay ya tashi zaune da ƙyau. Cikin bata dukkan hankalinsa da damuwa a fuskarsa
ya kai yatsansa ɗaya saman goshinta. Zafi kuwa rauu dan idanunta ma har sun sirka. Miƙewa yay kamar da
ɗan faɗa-faɗa yana faɗin, “Shine kuma kika zo nan kika zauna baki nema wajen kwanciya da magani ba?”.
Komai batace ba sai ɓata fuska data sake yi. Rankwashi yay kamar zai kai mata a saman kai sai tai sauri
ta kauce tana matse ido. Bai rankwashe tan ba sai harara daya zuba mata ya wuce ƙaton fright ɗinsu dake
a dining. Sai gashi ya dawo da first ald box ɗin su da goran ruwa marasa sanyi. Zama yay a inda ya tashi
sannan ya buɗe box ɗin yana duba magungunan ciki. Maganin zazzaɓi ya ciro ya bata, harta kai zata zuba a
baki ya dakatar da ita da faɗin, “Kinci abinci?”.
Kanta ta ɗan girgiza masa. A shagwaɓe tace, “Shayi kawai nasha, sai wani ɗan a wara a kasuwa kuma
nayi aman shi”.
“Kina wasa da kanki ko?”.
Ya faɗa a hasale. Ita dai batace komai ba. Cikin ɗan haushi-haushi yace, “Kisha maganin na samo miki tea
kisha sannan kici abinci dan cikinki yanzu ya gama cinkushewa”.
Maganin ta zuba ya bata ruwa ta sha, kafin ya miƙe zuwa kitchen ɗinsu. Tea ya haɗa ya fito batare da
yayma Mamy dake a kitchen ɗin tana girki ita da masu aiki magana ba. Itama ko kallonsa bata yi ba. Oum
bata nan ita da Babban yaya sukaje gidan Babba Sardauna shine ya tuƙata. Fawzan kuwa yana ɗaki yana
barci abinsa. Lokacin daya dawo ya sami Maanal ta kifa kanta a hannun kujera tai shiru, ta cusa hannunta
ta riƙe cikinta. Cikin sauri ya ƙaraso yana kiran sunanta. Cikin dauriya ta ɗago idanunta har sun kaɗa, sai ta
sakar masa murmushi dan bata son tayar masa da hankali.
“Cikin ne?”.
Da sauri ta girgiza masa kai tana amsar shayin da faɗin, “A'a barci ne kawai ke ɗibata”.
Badan ya yarda ba ya barta, sai dai ya zuba mata ido tana shan shayin. Ai kamar jira tana gama shan
shayin ta miƙa masa cup ɗin cikin yay mata wani irin ƙullewa. Ba shiri ta dafe shi da duka hannayenta tana
fasa ƙara. Wani irin zabura AA yay a rikice yay kanta, sai dai ya kasa sauke hannunsa a jikinta sai faman jera
mata tambaya yake jikinsa na rawa. Dai-dai nan kamar an jeho Oum da Babban Yaya sai gasu sun shigo,
itama Mamy da mai aiki da ƙarar Maanal ɗin ta isa kunnesu suka fito daga kitchen ɗin. Duk kan Maanal
ɗin sukayi, dan harta faɗo ƙasa tana haure-haure. Kafin ma kace mi ta sassanƙame musu alamar suma.
Hankalinsu ne yay masifar tashi musamman Ajwaad da Oum. Sai Babban yaya ne yay ƙarfin halin faɗin,
“A kaita mota suje asibiti”.
Da sauri Oum ta ce, “Kira Doctor dai Fadeel”. Baiyi musu ba yay kiran Family doctor ɗinsu. Yayinda tace
ma Ajwaad daya rikice shi kuma ya ɗaukar mata Maanal zuwa ɗaki. A saman gadon Oum aka shimfiɗar da
ita sannan Mamy ta shafa mata ruwa. Wani irin wahallen numfashi ta kawo, sai kuma ta fashe da kuka tana
matse cikinta da damƙe hannun Oum. Isowar Doctor ta sakasu fitowa aka bar Oum da Ajwaad da yaƙi
fitowa. Bayan doctor ya dubata ya tabbatarma Oum zata fara first period nata ne fa. Allura yay mata har
biyu, cikin ƙanƙanin lokaci sai barci. Daga ita har Ajwaad ajiyar zuciya suka shiga saukewa a jajjere. Kafin
Oum taima doctor daya sake musu bayanin komai godiya. Sai da ya fita ta samu damar kiran wayar Ammie
ta sanar mata. Addu'a kawai Ammien tayi ta cigaba da aikinta tana sauraren masifar da Gwaggo keyi tunda
ta shigo gidan. Dama duk randa ta fita kasuwa ta sayo kayan sana'arta babu zaman lafiya. Gwaggo ta dinga
zage-zage kenan da jifan Ammie da munanan kalamai harda faɗin bin maza take fita yi. Ammie dai bata
kulata ba dan dama haka take yi yanzu. Hatta shi kansa Baabu ɗin ta tattarashi ta watsar a gefe kawai.....
__________★
Har akai la'asar Maanal na barci a ɗakin Oum, a kuma lokacine rikici ya ɓarke can a gidan su Maanal
tsakanin Ammie da Babu. Dan amaryarsa ce tai kiransa a waya ta tsara masa ƙarya da gaskiya akan wai ga
Ammie ta saka Gwaggo a gaba tanata zagi. A fusace ya baro wajen aiki ya nufo gida. Babu wani
ƙwaƙwƙwaran bincike kawai yana zuwa ya kama marin Ammie. Shine Amaal ta fallo ta sanar ma Oum. A
rikice ta wuce gidan ko Mamy bata sani ba....
Ana idar da sallar Asr ɗin shima Ajwaad ya nufo gida. Dan hankalinsa duk yana kan Maanal. Kansa
tsaye ɗakin Oum ya nufo, hakan yay dai-dai da farkawar Maanal a firgice. Silmiyowa tayi daga saman
gadon Oum ta durƙushe ƙasa, hakan yasa Ajwaad ƙarasowa gareta da sauri yana tambayarta. Sai dai
batako samu bashi amsa ba ta shiga kwara amai. Gaba ɗaya duk sai ya rikice yanata jera mata sannu. Itako
aman take sosai. Sai da ta gama ta koma gefe ta kwanta yaraf tana maida numfashi. Sannun yaketa jera
mata, yanda fuskarsa ta koma sai ka ɗauka ma shike ciwon. Sai kuma ya miƙa mata hannu yana faɗin,
“Tashi muje ki wanke baki”.
Kanta ta girgiza masa. Da ƙyar ta iya furta, “Zan huta tukkuna”. Bai matsa mata ba, ya fita ya ɗakko abu
ya fara gyara wajen. Ya gama ya maida komai zai dawo ɗakin yaci karo da fasa ƙararata. Ai a ɗari ya ƙarasa
faɗowa ɗakin. Tana a inda ya barta, sai dai kallon hannunta take da duk ya ɓaci da jini. Hannun ta nuna
masa tana sake fashewa da kuka, sai kuma ta miƙe a galabaice tana kallon gadon. Ashe har nan akwai jinin
lurane basuyi ba tun ɗazun. Ganin tana niyyar nufar ƙofa yay saurin riƙota. Cikin son ganin ta kwantar da
hankalinta ya ce, “Relax!”.
Kuka ta sake fashe masa da shi tana ƙoƙarin fisge hannunta, “Na shiga uku Besty jini fa? Jini Oum kizo
jini”.
“Nace ki nutsu ko!!”.
Ya faɗa a tsawacen daya sakata nutsuwar dole. Sai dai jikinta rawa yake sosai tana cigaba da kallon
hannun. Bakin gadon yace ta zauna amma taƙi, sai ya ƙyaleta kawai. Batare daya kalleta ba dan haka kawai
yaji kamar yana jin nauyinta ya ce, “Ki jirani anan ina zuwa”. Daga haka ya nufi toilet ɗin Oum. Ruwa masu
zafi ya haɗa mata, sannan ya sake dawowa inda take. Har yanzu tanata kallon hannun tana hawaye. Murya
ya kwantar kamar bashi ke faɗa ba ɗazun.
“Kinga ki nutsu Besty ba wani ciwo bane ba fa. Dama doctor ya sanar mana zaki fara proud ne
shiyyasa kike jin ciwon ciki. Shine sai yanzun yazo. Ki tashi kije bayi ga ruwa can na haɗa miki ki cire
wannan kayan ki gyara jikinki kafin Oum ta dawo taje wajen Ammie ne. In kuma kina son sai kowa yazo ya
ganki a haka ne to?”.
Da sauri ta girgiza masa kai tana miƙewa ta faɗa Bayin........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂_
7️⃣2️⃣7️⃣2️⃣
______________
........Ajwaad bai ji ƙyanƙyami ba ya cire bedsheet ɗin samman gadon Oum ɗin ya samo ruwa da omo da
towel ya goge inda katifan ta ɗan ɓaci. Haka ya ɗaga katifan shi kaɗai ya juyata sannan ya ɗauka sabon
bedsheet ya canja. Wadrobe ɗin Oum ya buɗe side ɗin da kayan Maanal suke a cike fal ya ɗauka mata
kaya, tare da pant. Sannan yaje bakin toilet yana sanar mata idan ta fito ga kaya nan ta saka, ta kuma bar
kayan data cire ɗin zai zo ya wanke”. Bata dai amsa shi ba ya nufi hanyar fita. Har yaje ƙofa sai kuma ya
dawo da baya sakamakon saukar idonsa akan ledar da Oum ta aiki Amaal ta kawo mata ɗazun, Ledar ya
ɗauka ya buɗe ya ciro abinda ke ciki. Bai fahimci miye ba, dan haka ya karanta bayanin jiki. Ganin audigar
mata ya sashi maidawa ya ajiye, sai kuma ya sake ɗauka ya sake buɗewa. Ledan ya fasa ya ciri ɗaya ya
ɗauka pant ɗinta sabo da ya aje ya saka kamar yanda ya fahimta. Daga haka ya fice.
Bayan tsahon lokaci Maanal ta fito jin motsin fitarsa. Kasa zama tayi gudun karta ɓata wajen, sai dai
tanata bin gadon da kallo ganin ya canja kamar komai bai faru ba. Haka jiki a sanyaye ta ƙarasa ga kayan
daya ajiye mata. Sai idonta ya sauka akan pant ɗin da ya sakama part ɗin. Sosai tawaro idanunta waje, sai
kuma ta tunzura baki gaba da faɗin, “Besty ALLAH baka da kunya”. Ta ƙare maganar da murguɗa baki, sai
kuma ta ƙarasa ta ɗauka pant ɗin ta saka dan tana ganin yanda Didin ta suke amfani da shi ai. Kayan ta
saka tsaf tanata kumbure-kumbure. Sai kuma ta ɗauka wayarsa data riga tasan password ɗin ta buɗe.
Hayewa gadon Oum tai ta sake kwanciya. Dan wani kalar jirin barci take ji sosai. Takai mintuna goma da
kwanciya akai knocking ƙofar. Umarnin shigowa ta bada sai ga Bestyn ta. Ɗauke yake da tray a hannu, suna
haɗa ido ta risinar da nata. Shima baiyi magana ba ya ajiye abincin kawai ya wuce toilet ɗin Oum ɗin kamar
wasu masu jin kunyar juna. Kayan data cire ya tattare hadda p ɗinta dake a ɓace sosai. Tsabar rashin
hankali da rashin wayo irin na Maanal maimakon ta wanke sai shima ta bar masa saboda yace tabar masa
kayan data cire. Abin mamaki Ajwaad Sarkin ƙyanƙyami da tsantseni sai gashi tsaf ya wanke kayan har sau
biyu kafin ya sakasu a injin wanki harda bedsheet ɗin Oum ya wanke fes. Sannan ya wanke bayin ya fita da
kayan can backyard ya shanya amma banda p ɗin daya shanya anan toilet ɗin. Zuwa lokacin Maanal ta jima
da komawa barci. Sai ma ɗauke tray ɗin abincin yay ya ajiye gefe sannan ya fice ɗakinsu domin yin wanka...
★Rai a ɓace Oum ta dawo gidan tare da Ammie dake wani irin kuka mai ban tausayi saboda abinda ya
faru a gidansu Maanal ɗin. Da farko bata lura da canja kayan Maanal ɗin ba dana bedsheet sai da ta zauna
idonta akan trayn dake ajiye. Hannu takai ta taɓa wuyan Maanal, sanyi ƙalau zazzaɓin ya sauka. Barcinta
take hankali a kwance. Ajiyar zuciya ta saki mai kauri, sai kuma ta maida dubanta ga Ammie.
“Kiyi haƙuri Asiya kukan nan ya isa. Kada kanki yazo yana miki ciwo. Tashi ma kiyi wanka ki shirya gidan
baba zamuje. Dan na fahimci wannan karon sai na dangana al'amarin Habib da baba tukkuna, tunda baya
gane yaren Aban su Fadeel da nawa.”
Kai kawai Ammie ta jinjina mata, ta tashi ta shiga toilet. Ita kuma ta buɗe wadrobe ta ɗakko mata wata
sabuwar atamfa da bata taɓa sakawa ba da gyale da duka abinda zata buƙata sannan ta fita. Harta nufi
ɗakin Mamy sai taci karo da Ajwaad. Sannu ya mata, ta amsa tana kallonsa ganin shima ya sauya kaya.
“Fita zakayi ne Auta naga ka canja shiga?”.
Kansa ya girgiza mata, “A'a Oum, wancan sun ɓaci ne”.
Ɗan jimm tayi sai kuma ta ce, “Mamy fa?”.
“Tana ciki tunda kika fita. Oum ina kikaje wai?”.
“Naje nan wajen Ammien ku ne, yanzu ma zamu sake fita da ita gidan Baba. Idan Mamy ta tashi ka sanar
mata, ga kuma Maanal nan na barci.....”
Kansa kawai ya jinjina mata. Ita kuma ta juya ta koma ɗakinta ranta duk a dagule.
__________★
Shigar Baba Sardauna a cikin al'amarin Ammie yasa aka samu sauƙi tsakaninta da Babu a lokacin. Ga
gwaggo ne dai babu abinda ta fasa wulaƙanci yima Ammie take iya iyawarta. Tunda kuma ta ƙyalla ido taga
Maanal ta fara jini sai ta fara surutai, yara duk sun zama iyayen mata miye-miye. Saboda ƙwaɗayin Ammie
kuma duk sun laƙema masu kuɗi, indai kwaɗayi abun yine suyi tayi watarana sai amma yaran cikkunan
shege a titi. Babu wanda ya kula gwaggo da zatunkanta sai Maanal, rashin kunya ta mata sosai ranar har
sai da ta saka Gwaggon kuka. Sai Ajwaad ne yazo yasa Maanal barin gidan da ƙyar. Aiko gwaggo ta haɗata
da Babu yace sai ya daketa. Jin haka Maanal ta daina shigowa gidan har kwana huɗu.
A yammacin ranar Maanal ta nema jini ta rasa. Tana son gayama Oum tana jin kunya. Gashi bata shiga
gidansu saboda Babu yace zai daketa. Kawai saita yanke shawarar samun Ajwaad, ɗakinsu ta leƙa, babu
kowa sai babban yaya dake barci, dan haka ta fito. Can harabar gidan ta nufa, inda ta wuce Mamy da
ƙanwarta da suke kira Maman Saheeba suna hira. Kallon banzar da Maman Saheeba ke mata yasa ko
gaisheta bayi take ba idan tazo gidan. Dan haka yanzun ma bata kulasu ba har Mamy ɗin ta wuce garden
neman Ajwaad. Tasan shi baya yawo, indai ba aikensa akai ba to zaka samesa ne a garden yana karance-
karance daya ɗaukama kansa yanzu. Wani lokacin har faɗa suke yi dan ita karance-karance haushi yake
bata, ya rage bata kulawa, bata san miyyasa ba bai son su cika kaɗaicewa daga ita sai shi a yanzu. A hankali
ta zare novel ɗin dake a hannunsa, fuska ya yamutse tare da ɗago idanunsa ya saukesu a kanta. Zama tai
kamar zatayi kuka tana kallon littafin, sai kuma ta sake kallonsa idanun nata cike da hawaye.
“Besty wai mike damunka kwana biyun nan. Sosai ka canja min, musamman tsakanin nan. Ka ɗauka
dukkan hankalinka ka maida ga karatun novels. Baka son mu zauna muna hira mu kaɗai, ko assignment
zamuyi sai kace sai a gaban Oum ko Mamy. Kana yin abu kamar ma baka son ganina.”
Maimakon amsa mata sai kawai ya lumshe idanunsa masu haske sosai ya sake buɗewa a kanta. Tsohon
lokaci kafin ya motsa lips ɗinsa kaɗan ya furta, “Babu komai yanayi ne kawai”.
“Yanayi?”.
Kansa ya jinjina mata kawai. Kamar zatai magana sai kuma ta fasa. Fuska taɗan shagwaɓe tare da faɗin,
“Besty akwai matsala fa?”.
Cikin ɗan tsireta da idanu ya ce, “Tami?”.
Sake shawaɓe fuska tayi ƙasa-ƙasa kamar mai tsoron a jita ta ce, “Na daina ganin jinin, kuma ALLAH
kunyar faɗama Oum nakeyi. Ina son zuwa wajensu Didi ina tsoron Baabu ya kama ni”.
“Oh nine baƙya jin kunya?”. Ya faɗa yana tsatstsareta da idanu.
Sai da ta waro idanunta waje sosai sannan ta ce, “Kai kuma zanji kunya Besty? Kai fa Besty nane. Ni dan
ALLAH ka gaya min yaya zan gane ya ɗauke ɗin kenan naje nai wanka. Kuma ai irin wankan da aka koya
mana a islamiyya zanyi ko?”.
Idanunsa kawai ya rumtse yana datse laɓɓansa da ƙarfi da haƙori. Miyyasa yarinyar nan bata ganewa ne
wai? Taɓa shin da tai ya sashi dawowa hayyacinsa. Ta sake marairaice fuska. Sai kawai ya samu kansa da
bata amsa. “Naji zan faɗa miki. Amma lokaci yayi da zaki fara fahimta”.
“Fahimta? Mizan fahimta?”.
“Ba komai”.
Ya faɗa yana miƙewa. Tashi tai itama ta bishi, amma sai yay mata nunin ta koma ta zauna. Zaman tayi, shi
kuma ya fice a garden ɗin. Babu jimawa ya dawo da takarda ya bata. Kafin yace mata, “Tashi kije na rubuta
miki komai”.
Batai musu ba ta miƙe, hannu ya miƙa mata. Idonsa akan novel ɗinsa dake hannunta. Sai da ta tura baki
gaba sannan ta miƙa masa ta wuce....
Kwana biyu dayin haka zazzaɓi mai zafi ya kwantar da Ajwaad. Zazzaɓin daya sanya har sai da ya
kwanta a asibiti. Kwanansa biyar aka sallamesa. Ana sallamarsa kamar jira itama Maanal ta fara nata
ciwon. Tasha jiki sosai kafin itama ALLAH ya bata lafiya..
_________★
Zancen da Fawzan yayma Oum itama ta samu Abah da shi, shi ba mutum bane mai son takurama
yaransa. Sannan yakan nutsu akan abu idan sunzo masa da shi ya dubi halaccinsa da haramcinsa a wajen
UBANGIJI. Sosai yay nazari akan batun ya kuma nema shawarar Baba Sardauna. Ɗari bisa ɗari Baba
Sardauna ya bada goyon baya shima akan hakan, dan tunda har Fawzan ɗin ya furta ai masa auren ai
masan kamar shine yafi komai dacewa. Dan haka su Abah suka shirya zuwa Giro. Sun kuwa je. Alhamdullah
Baba Haruna ya basu auren Shahidah da Amaal, basu baro ba kuma sai da suka bada komai har sadaki. Aka
kuma tsaida ranar aure. Kasancewar Baabu ya zama abinda ya zama yasa sai da suka dawo Abah ya sanar
da su daga shi har gwaggo. Wannan al'amari yay matuƙar ƙona zuciyar gwaggo dan itafa duk wani jin daɗin
duniya bata son ganin Ammie a cikinsa.
A ɓangaren Mamy kam komai batace ba, sai ma addu'a datai da sanya albarka kawai. Haka ƴan uwanta
ma albarkar suka saka. Babban Yaya ya koma makaranta, haka Ajwaad da Maanal ma. Yayinda akema
Fawzan nasa shirin yin sabuwar jarabawa shi da Amaal. A haka aka shanye watanni kusan biyar, su Amal
sun kammala exam, akai bikin saukar Maanal da Ajwaad tare da walimar data ƙayatar. A wajen wannan
walima ne Baba Sardauna ya ɗarsa nasa burin akan Ajwaad da Maanal. Sai kuma bayan kwana biyu dayin
walimar yazo har gidan abinda bai cika yi ba. Zaunar da Oum da Abah da Mamy yayi, bai ɓoye musu komai
ba akan batun da yazo da shi na son haɗa auren Ajwaad ɗin da Maanal tare da ƴan uwansu. Ya kuma kawo
musu hujja mai ƙarfi akan abinda ya hango game da shaƙuwar yaran. Dan gara ya kasance akwai igiyar
aure a tsakaninsu gudu sharrin shaiɗan saboda kusancinsu yayi yawa. Gashi kuma suna a wata gaɓa ce mai
ban tsoro akan duk wani yaro dake a wannan shekarun musamman ma shi Ajwaad da Babban Yaya ya
sameshi ya warware masa komai akan halin da Autan yake ciki tun kafin ya koma, shiyyasa ya saka ido
shima ya fahimci komai ya ya kuma tabbatar. Su duka ukun babu wanda ya musa ko jayayya akan abinda
Baba Sardauna yazo da shi. Sun kuma gamsu da cewarsa akan ai shiru da batun kada a sanarma Ajwaad
ɗin da Maanal. Su kuma barsa da Baabu shi zai yi magana da shi.
Haka kuwa akayi, Baba Sardauna ya kira Babu har gidansa sukai magana ta fahimta. Ya kuma gamsu
shima ya bada goyon baya. Bayan haka Baba Sardauna yay kiran Baba Haruna shima a waya suka tattauna.
Shima kuma ɗari bisa ɗari ya gamsu. Daga haka aka fara shirin bikin ƴan gata su shidda. A ɓangaren Babu
babu wani ƙwaƙwƙwaran shiri, dan gwaggo da Amaryarsa sun gama zugesa tsaf ta bayan fage. To dama dai
Abah yayi niyyar shiryama yaransa biyu gida da kansa. Shi ko Ajwaad dama sai sun kammala secondary
za'ayi biki. Oum kuwa duk wani abu da uwa ya kamata tayi ta ɗauki ɗammarar yin komai, duk da haka
Ammie ta sameta da abinda ke a hannunta, ta kuma nema shawararta akan tunkarrar Babu da gadonta da
iyayenta suka bari. Oum ta bata goyon baya badan zata amshi kuɗin a hidar yaran ba, sai ɗan abinda take
shiryama zuciyarta. Tana shiri akan in har aka kammala bikin yaran to lallai koma miza'ayi dole Babu ya saki
Ammie. Dan ta gaji da ganinta cikin wannan zaman zaluncin da ƙuncin. Ita ba kwanciya da miji ba, ita ba
ƴancin aure ba, duk ta lalace ta rame ta fita hayyacinta. Kamar ba Ammie ƴar gayu ƴar ƙwalisa ba. Sarkin
tsafta da gyara jiki. Tofa dole ne su taya mata ta amshi hakkinta a wajen Babu tun yanzun.
Babu wasa kuwa Ammie ta tunkari Babu da batun kadarorinta da komai ma da iyayenta suka bar mata
akan son yin hidimar biki, abinda ya tadama Babu hankali kenan, dan kuwa ya salwantar da kaso biyu bisa
ukun wannan dukiya, suma kuma dangi sun ci. Shi kansa kaso ɗayan daya rage ma yana a ƙila wakala ne
kawai. Ƙin cema Ammie komai yay a lokacin, face kalmar “Yaji”. Yay gaba abinsa. Bata damu ba, ba kuma ta
kawo komai a ranta ba tunda rayuwar daya ɗauka ma kansa kenan a yanzu..........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070